Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 11
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TARKON MUTUWA Abdulaziz Sani madakin Gini Typing:- prince auwal auzab Post:- AA Misau Littafi na daya 1 Part 1A . Awani zamani can baya mai tsawo daya shude alokacin da akeyin mulkin kashin dankali wato manya sune asama,kanana sune a kasa. awannan lokaci zalunci ya yawaita sam babu adalci,doka bata aiki sai akan talaka,mara karfi,da makaskanci. adaidai wannan zamanine akayi wata nahiya wacce ta shahara a duniya aharkokin kasuwanci,karfin mulki da yawan da yawan al'umma. kasar da tafi dukkanin kasashen dake nahiyar daukaka itace bindal. duk wani dan kasuwar dake mu'amala da birnin indai yanason ya tsira da mutuncinsa da kuma dukiyarsa to dole ya kasance ribar da zai samu akullum ya rabata gida uku.kaso daya shine naka kaso biyu kuma sai ya kaiwa sarki shamsal sarki shamsal ya kasance gawurtaccen jarumi mashahurin mayaki wanda babu kamarsa anahiyar gaba daya domin atarihin jarumtakarsa ba'a taba yi masa rauniba a yaki ko a gasar jarumtaka. yana iya shafe sa'a goma sha biyu yana yaki batare daya gajiba yace yana iya yin tafiyar kwaba bakwai acikin gudu batare daya tsaya don ya huta ba sai dai kawai ya daga battar ruwa yasha yaci gaba da gudun. kai idan sarki shamsal yayi wani abun na bajinta ko jarumtaka sai kaga kamar ba mutum bane shi. aljanine komai yawan mayaka yana iya tarwatsa su ya kashe na kashewa,masu gudu su gudu don tsira da rayuwarsu. abangaren zalunci kuwa masu hasashe sun tabbatar da cewa babu wani sarki anahiyar wanda yafishi zalunci,domin shi yan uwansama sarakai cin zalinsu yakeyi bare talaka. idan ya kyallara ido yaga wani sarkin da kyakkyawar mata saidai kawai ya aika masa da ya kawo masa ita da kansa. idan sarkin yaki kawota zai iya rasa ransa ko mulkinsa don haka yana rawar jiki zai kaita. batun haraji akan talakawa kuwa babu inda aka tsananta shi sama da birnin bindal ko yaya talaka yayi laifi yanzunnan zaisa azaneshi ko kuma akai shi kurkuku ayanke masa hukuncin shekara biyu ko fi. atakaice dai inbanda sarki shamsal da fadawansa,da kuma yan barandars babu mai kwanciyar hankali acikin birnin bindal. acan karshen birnin bindal abangaren kudu akwai wani makeri wanda ake kira da suna satyan. makeri datyan tsohone tukuf domin shekarunsa sunkai dari da biyar kuma tun baifi shekara taraba aduniya ya kware a harkar kira kuma ya shahara domin gadon sana'ar yayi. yana da shekara taran mahaifinsa ya rasu. shikuma yaci gaba da aiwatar da aikin mahaifin nasa. hatta makaman yakin gidan sarautar sarki shansal amakerar satyan ake kera su ba'ataba samun wani sabani ba atsakaninsa da gidan sarki shamsal ba.sarki shamsal bai taba ganin tsoho satyan ba,haka shima bai taba ganin sarki shamsal ba. akar kashin tsoho satyan akwai yara ma'aikata kimanin su saba'in da daya kuma duk suna samun abin da suke rayuwarsu a karkashinsa. albarkacin kayan yakin dayake kerawa masarautane yasa ba'a tsananta masa haraji ba,kuma tun azamanin mahaifin sarki shamsal haka abin yake wakana. tsoho satyan yana da matan aure guda daya wacce itace girma ya kamata domin shekarunta sunkai saba'in. allah ya albarkacesu da yaya biyu kacal aduniya,mace dana miji. macen itace babba shekarunta sunkai ashirin da biyar,ana kiranta da suna sadirat. sadirat macece kyakkyawa daidai gwargawado mai kyan siffa ta taso da farin jini sosai wajen samari amma saboda itace kadai ke taimakon mahaifiyarta a ayyukan gida bata son tayi aure harsai kaninta hatyan yayi,saboda shi matarsa zata zauna agidan ta dinga kula da mahaifiyarsu. ita kuwa dauketa za'ayi akaita wani gidan. tsakanin sadirat ban bancin shekara hudu ne wato yanzu hatyan yana da shekara ashirin da daya kacal aduniya, allah daya gari banban ka kadan hatyan bai gaji harkar kira ba.tun daya taso da kuruciyarsa babu abinda ya keso sama da harkar farauta don haka kusan kullun da koyaushe yana cikin daji. tun safe idan yafita farauta baya dawowa sai rana ta fadi. wani ikon allah kuma sai ya zamana yana da nasibi matuka a harkar domin baitana fita farauta ya dawo babu wani abu ba. sai an ganshi ya kamo babbar dabba ko babban tsuntsu. tun hatyan nada shekara tara aduiya aka gane cewa sadauki ne domin tun asannan yake iya gumyrzu da manyan dabbobin daji kuma ya kashesu da hannunsa. wannan baiwa da allah ya bashine ta sanya shi kansa sarkin mafarauta na birnin ya jashi a jikinsa kuma ya kaunaceshi ainun hakannenama yasa ya rinka taimaka masa da yan sirrikan daji dana tsafi domin samun tsari Akullum abin da sarkin mafarautar ke nunawa hatyan shine ya boye sadaukantakarsa kada mutane su sani saboda al'adar sarki shamsal itace. duk sa'ad da yaji ance ga wani sadauki ya taso a birninsa saiya tura a sirrance a kashe shi. ba komaine ya jawo hakanba face bokayensa sun gaya masa duk ranar da aka sami wani sadauki mai irin baiwarsa ta jarumtaka dajuriyar yaki da gudu to shine zai karbi mulkinsa bisa wannan daliline duk dabbbar da hatyan ya farauto da hannunsa a daji sai ya boyeta acikin buhu ya kaita gidan sarkin mafarauta shine zai sayar masa da dabbar ya bashi ya bashi kudinsa don kada a gane cewa shine ya kashe dabbar. duk sa'ad da hatyan ya shiga daji farauta baya yarda wani ya ganshi alokacin da yake gumurzu da manyan dabbobi. aboye hatyan yake baiwa kansa horon gudu dana sarrafa makami. tun yana da shekara goma sha daya idan ya kasa tsere da dabba komai karfin gudunta saiya kure mata gudun ya rafketa. hatyan na iya shafe kwana ashirin yana gudu a daji batare da ya tsaya don hutawa ba ko cin abinci ba sai dai kawai ya sha ruwa. wato dai hatyan har yafi sarki shamsal juriya a wajen gudu. abinda sarki shamsal yafi hatyan kawai shine karfin damtse da kwarewar yaki da sanin makama.amma kuma hatyan yafishi zafin nama. a duniya babu abinda hatyan keso da tsananin kauna sama da yayarsa sadirat domin ko kuda baya son yaga ya sauka ajikinta.da nufin ya taba lafiyarta. duk saurayi ko kuma wani dan iskan daya kuskura ya taba sadirat da hannunsa to sai hatyan ya batar da kamanninsa ya kai masa ziyarar dare ya sare masa hannunsa ya mai dashi musaki. bisa wannan dalililine maza ke tsoron latsa sadirat. wayanda dama suke sonta da aure tsoron zuwa wurinta suke. lokacinda tsoho satyanyaga cewa kokadan dansa baya sha'awar harkar kira sai farauta sai hankalinsa ya dugunzuma ainun saboda tunanin cewa duk ranar daya mutu babu wanda zai gajeshi saidai yaransa shikenan sana'ar tabar gidansu. akan hakane ya rinka matsawa hatyan yana son yayi masa dole akan yabar farauta. koda ganin haka sai hatyan yaje ya sanar da sarkin mafarauta abinda ake ciki. dajin haka sai sarkin mafarauta ya taso dakansa yazo gidan satyan dama can sun kasance aminan juna sai dai shi sarkin mafarauta ne shekarunsa basufi tamanin da biyar ba. lokacin da sarkin mafarauta da satyan suka kadaita acikin turaka kuma suka gaisa saiya dubeshi yace yakai abokina kayi sani cewa kowanne da yana da irin baiwarsa. danka Allah baiyishi makeriba,mafarauci ne masu iya magana sunce ranar wanka ba'a boye cibi to yau zan sanar dakai wani babban sirri akan danka wanda baka taba saninsa ba. ahalin yanzu duk fadin garinnan inbanda sarki babu wani jarumi wanda yafi hatyan sadaukantaka,karfin gudu da juriyar wahala adaji. kasani cewa tun yana da shekara tara yake iya fada da manyan dabbobin daji ya kashe su yakawo su gidana na sayar masa dasu ba tare da kowa ya sani ba. nine nake sayar da abubuwan daya farauto. yanzu haka ya tara kudade masu dunbun yawan da sun wuce dinare dubu dari biyar amm tsoro yakeji yazo ya sanar dakai. kasani nayi bincike acikin hallarar tsafina nagano cewa wannan yaro naka nangaba sai ya zama babban mutum akasarnan don haka idan har sarki ya sami labarin jarumtakarsa kasheshi zaiyi babban abindayafi tayar mini da hankali shine zafin zuciyar hatyan. ina tsoron ranar da wani abu zai hada shi da gidan sarauta. indai aka tabashi bazai hakuraba tunda kana ganin abinda yake yiwa samarin da suke yiwa 'yar uwarsa sadirat wargi. a yanzu haka ya janyo kowa tsoronta yakeji awannan garin. ka tuna cewa sarki shamsal yana da azzalumin da wanda shima shekarunsa basufi na hatyanba yana da muguwar al'ada tayiwa mata fyade. a garin nan yarima zainur yayiwa yan mata sama da yam mata guda dari fyade. kuma ko magana iyayen 'yan matan sukayi sai a kashesu. mahaifinsane ya daure masa gindin yayi duk abinda yaga dama saboda yana sonsa fiye da komai aduniya. ina tsoron ranar da yarima zainur zai yi arba da sadirat, na tabbatar da cewa bazai kyaletaba idan kuwa ya taba ta sai hatyan yayi masa mummunan hukunci. sa'adda sarkin mafarauta yazo nan a jawabinsa sai tsoho yaji hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe. daga can saiya dago kai ya dubi sarkin mafarauta yace yakai abokina kayi sani cewa dangane da batun sadirat bani da wata fargaba saboda kullum sadirat na gida bata zuwa ko ina saboda ko yaushe itace takeyin ayyukan gida. kaga kenan babu yadda za'ayi ta hadu da zainur tunda babu abinda zai kawoshi nan ko batun kayan yakin gidan sarauta akwai wakilin kayan wanda shi yake zuwa ya karba. ni yanzu kawai damuwata akan hatyan ce. me zai hana ka dauke mini shi daga garinnan gaba daya ka turashi can wani garin. wajen abokan sana'rka yayi rayuwarsa a can,tunda ni na tsufa tawa ta kare, mahaifiyarsu ma girma ya soma kamata. abinda muke buri kawai shine muga auren 'ya'yan mu kafin ajalin mu gashi su biyun sun shaku da junansu ainun basa son rabuwa idan har za'a dauke hatyan daga garin nan lallai a hada su tare. ni ina gane wannan ne kadai hanyar da zamubi mu tserar da rayuwar hatyan data yar uwarsa daga sharrin sarki da dansa. saboda haka a yau dinnan idan hatyan ya dawo daga farauta ka taho dashi mu zauna gaba daya tare da mahaifiyarsu mu sanar dasu hukuncin da muka yanke. yan kudin da hatyan ya tara sun ishesu su gudanar da sabuwar rayuwa a wani gurin amma babbar shawarata itace subar wannan nahiyar gaba daya. lokacin da tsoho satyan yazo nan a jawabinsa sai sarkin mafarauta yakamu da tsananin tausyinsa har kwalla ta zubo masa ya sunkui da kansa kasa yace inda matsalar take shine tayaya kake tsammanin hatyan da yar uwarsa sadirat zasu iya barinku kai da mahaifiyarsu su tafi can wata nahiyar su zauna alhalin kuna raye baku mutu ba? koda wannan tambaya sai hankalin satyan ya dugunzuma ainun. nantake hawaye me yawa yazubo masa yace rabuwarmu dasu a wannan lokaci itace tafi alheri atsakaninmu idan kuma sukaki su tafi to anan gaba zasu yi tafiyar dole ayayin da babu mudin cikin rashin fahimta sarkin mafarauta yace nifa bangane me kake nufiba satyan yace banaso ka fahimta din amma dai lallai ka tilasta hatyan ya dauke yar uwarsa su bar nahiyar gaba daya kuma su manta damu. idan darabon zamu sake ganawa zamu gana nan gaba ni da mahaifiyar tasu zamuyi jiranku idan hatyan ya dawo daga farauta koda gama fadin haka sai satyan ya mike tsaye ya kama hannayen sarkin mafarauta ya tashe shi tsaye suka kurawa juna ido sannan yace nagode abokina nagode da wannan shawara daka zo mini da ita da kuma wannan sirri na dana daka baiyana mini. tabbas kai masoyine na kwarai bazan taba mantawa dakai ba Allah yabar wannan zumuncin namu wanda tun iyaye da kakanni yake gidan makera da gidan mafarauta mun zama tamkar jini daya. kayi sani cewa inaji ajikin bazan dadeba ajalina zai riskeni. ajalina yana kusa donhaka nabar maka amanar iyalina. kayi iya kokarinka wajen karesu da basu shawara ta gari lokacin da makeri satyan yazo nan azancensa sai hawaye ya zubowa sarkin mafarauta ya rungumoshi yana mai cewa. na rantse da girman iyayena zan rike wannan amana taka hannu biyu har izuwa karshen rayuwata. sai da suka jima suna zubar da hawaye sannan sarkin makera ya yi masa sallama ya tafi. a can gidan sarauta kuwa da farkon yammaci sarki shamsal ma zaune acikin dakin shakatawa tare da matarsa suna shakatawa sai ta dubeshi tace yakai mijina kayi sani cewa duk sa'ad dana kalleka sai naji farinciki ya turnikeni saboda nice nake auren sadaukin jarumin da babu kamarsa awannan nahiya. kuma nice nake da sarkin da babu kamarsa a daukaka da arziki. nice ke auren zakaran da ya lashe gasar jarumtaka sau ashirin da daya awannan nahiya gaba daya. har yanzu kaike rike da kambun wannan gasa koda sharifa matar sarki tazo nan a zancenta sai farin ciki ya turnukeshi ya bushe da dariyar murna sannan ya dubeta yace hakika duk abinda kika fada gaskiyane barima ki gani sarki shamsal ya mike tsaye ya shiga cikin turakarsa ya bude wata katuwar akwatu wacce rabonsa da budeta shekara guda kenan tun da nadawo daga gasar jarumtaka wacce akayi abirnin rum yana bude akwatin saiga wani kambu amma na hular sarautane wanda akayishi da zallan farin lu'u lu'u. wannan kambun jarumtakar ya ciwo a shekarar data wuce sarki shamsal ya dauko wannan kambu ya tawo dashi falo domin ya nunawa sharifat. adai dai wannan lokacine yarima zainur ya shigo falon da gudu cikin murna yanakwallawa sarki kira. bisa tsautsayi kuwa sai sukayi karo da juna wannan kambu ya subuce daga hannunsa yafadi kasa. take kambun ya tsage kuma ya rabe gida biyu. al'amarin daya yi saurin fusata sarki kenan baisan sanda yasa hannu zai zabgawa yarima zainur mariba amma sai ya kasa. koda ganin haka sai hawaye ya zubowa zainur ya durkusa bisa gwiwoyinsa agaban sarki yana neman afuwarsa yana cewa abbana kayi mini gafara. tabbas wannan kambu yanada matukar daraja a wajenka domin tunda kuruciyata kawo izuwa girmana baka taba yi mini fada ba bare kayi yunkurin zagina amma yau har kayi yunkurin dukana. idan har ka yafe mini to ka bani dama na kai wannan kambu inda za'a gyara shi da kaina. koda yarima zainur yazonan azancensa sai jikin sarki shamsal yayi sanyi don haka sai yakama kafadun yarima zainur ya tasheshi tsaye cikin murmushi yace........ .mukasance daku gobe idan Allah ya kaimu TARKON MUTUWA Abdulaziz Sani madakin Gini Typing:- prince auwal auzab Post:- AA Misau Littafi na daya 1 Part 1B . Shikenan dana na yafe maka amma ka sani cewa duk fadin kasarnan babu wanda zai iya gyara wannan kambu ya dawo inda yake face makeri satyan. ka nemi zamhas mai kula da makaman yaki ka bashi wannan kambun yaje ya kai masa. zainur yace A'a ai hannun daya bata wannan kambu shi zai aishi gyara don haka sai dai na nemi zamhas ya rakani gidan makeri satyan saboda ban taba zuwa ba. dajin haka sai sarki shamsal yayi murmushi yace amma kayi ladabi ga tsoho satyan kada kayi wani abu mara kyau agareshi domin makusancine ga mahaifina kuma amintaccensa shiyasa nima nake daraja shi. zainur yayi murmushi yace lallai zan zamo mai kyauta tawa a gareshi. nan take yarima zamnur ya juya ya fice daga cikin falon rike da kambun jarumta tsagagge. zainur bai zame ko'ina ba sai gidan s zamhas yana zuwa ya nuna masa matsalar da aka samu. kuma ya bukaci ya rakashi gidan makeri satyan. babu yadda zanhas baiyiba akan yarima zainur ya hakura da zuwa shi ya bashi yakai ya gyaro amma sai yaki ya nace saidai suje tare. nantake aka kawowa yarima zainur da zamhas dawakai suka hau sannan dakaru guda ashirin suka take musu baya suka fice daga ciikin gidab sarautar. daga gudan sarautar zuwa gidan makeri satyan tafiyace ta sa'a guda don haka sai da yarina zainur suka iso gidan inda suka iske makeri satyan a zaune akofar makerarsa yana hutawa yaransa nata faman aiki. koda satyan ya hango zanhas tare da yarima da kuma dakarun sarki sun dufafo kofar gidansa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun, tsoro ya baibayeshi,jikinsa ya kama kyarma nantake abubuwa biyu suka fado masa arai abu na farko da yayi zargi shine duk yadda akayi anyi wani kuskure babba akayan da aka kerawa sarki shine ransa ya baci ya turo akamashi abu na biyu kuma dayazo masa arai shine anya kuwa ba bokayene suka gayawa sarki cewa hatyan ne yaron da zai karbe karagar mulkinsa cikin matukar karfin hali satyan ya mike tsaye yana dogara sandarsa da kyar ya taryesu yana marhaban cikin girmamawa yarima zainur ya sauko daga kan dokinsa ya rissina akaron farko a rayuwarsa yagaida satyan. bakomaine yasa yagaida satyan ba sai saboda dalilai guda biyu. dalili na farko shine yaji mahaifinsa ya fadi darajarsa awajensa abu na biyu shine kuma shine yana da son yaga ya gyara masa wannan kambu jarumta yayi kyau sosai tamkar bai taba tsagewa ba yadda dan sarki ya gani zaiyi matukar farin ciki. batare da bata lokaciba yarima zainur ya dauko wannan kambu ya yi masa bayanin abida ke tafe dasu. koda jin haka sai farinciki ya kama tsoho satyan domin ya fahimci cewar duk abubuwan da yake zargi basu bane. satyan ya karba ya duba shi dakyau sannan yayi murmushi yace ai acikin rabin sa'a kachal za'a gama gyara wannan kambu kamar yadda yake da babu wnda zai iya gane cewa ya taba karyewa. kodajin haka sai yarima zainur ya kamu da frinciki nantake satyan ya jasu izuwa makerarsa yasavaka hura wuta inda sukuma suka koma gefe daya suka zauna akan kujeru suka zuba ido suga yadda za'a gyara wannan kmbu cikin rabin sa'a. kafin cikar rabin sa'a tsoho satyan ya gama gyara wanan kambu sai gashi kambun ya koma daidai yadda yakevkuma ya kara kyau sai sheki da walwali yake. nan dai satyan yayi sauri ya basu kambun ya sallamesu burinsa kawai subar kofar gidansa su tafi. awannan lokaci rana ta fadi gari ya soma duhu kuma lokacin dawowar hatyan daga farauta yayi. har su zainur sun hau kan dawakansu zasu tafi keanan sai sadirat ta fito daga cikin gida dauke da ruwan sha aciikin tuluna da kofi bisa wani faranti zata kawowa satyan. dama kullum a wannan lokaci take kawo masa ruwan sha saboda tu'ammalin da yake da wuta a makera A wannan lokaci sadirat na sanye da wata matsatstsiyar riga wacce ta bayyana dukkan surar jikinta. koda yarima zainur ya kyallara ido yaga sadirat sai ya dimauce ya kama hadiyar yawu kamar mai jin kishirwa. ya dade yana neman inda zai jika makogaronsa saiya yi katari da rafi. nanfa yarima zainur ya kasa sakarwa dokinsa linzami ya tafi ya kurawa sadirat idanu kawai. ita kuwa sadirat koda taga ya kura mata idanu sai tayi sauri ta sunkui da kanta kasa. ta wuce izuwa wajen satyan ta masa ruwan ta zuba masa a kofi kamar yadda ta sabayi masa domin yasha. amma sai taga shima ya kasa shan ruwan. hannunsa dqke rike da kofin sai karkarwa yake kuma sai kallon yarima yake kawai. awannan lokacin sadirat ta tuno da labarin da takeji a kan yarima cewar in dai yaga mace ya kyasa ta sai yayi mata fyade. nan take itama hankalinta ya tashi ta rasa abinda zatayi. lokacin da zamhas yaga yarima.ya dimauce :isa ganin sadirat sai ya fara rokonsa akan su tafi ya tuna masa kan sarki fa ya gargadeshi kada yayi wani abu ba daidai bq daidai awannan gida duk da wadannan maganganu na zamhas sai yarima ya rinka jinsu tmkar tatsuniya acikin kunnensa don haka ko kallonsa bai ba barema yayi aiki da shawarar tasa. sadirat ta taso daga gaban mahaifinta satyanvtazo zata gifta ta gaban yarima domin ta ta shige gida kawai sai yarima ya duro daga kan dokinsa ya sha gabanta ya kai hannu ya kamo hannunta. tana waigowa saita zabga masa mari. cikin tsananin kaduwa dakaru,zamhas,da satyan suka wangame baki suna mamakin al'amrin. ita kuwa sadirat saita dakawa yarima tsawa tace shin ka zata ni irin matan daka saba wulakantawa ne agari har da zaka taba hannuna? toka sani kusantata ba karamin hadari bane agareka saidai kaje kanemi wadanda basu da gata ka wulakanta su. koda sadirat tazo nan azancenta sai yarima zainur ya shafa kumatunsa sannan ya bushe da dariya. lokaci guda kuma sai turbune fuska tamkaranvaiko masa da sakon mutuwa ya dubeta yace . yake wannan yar talakawa ki sani cewa ko mahaifinabai taba marina ba babu wani mahaluki daya taba zagina ba bare ma yadakeni. amma yau gashi kin mareni agaban mutane kin muzanta darajata damutuncina. to kisani na rantse da darajar uwata da ubana yanzu a gaban wannan tsoho naki zan yi miki fyade kuma na karya wannan hannun naki daya mareni na sareshi da takobina. kafin sadirata tayi wani tuni yarima zainur yasa hannunsa guda ya maketa a fuska. saboda karfin dukan saida ta baje akasa ta kasa mikewa. yayinda jini ke zuba a bakinta. koda ganin abinda ke faruwa.sai tsoho satyan ya mike tsaye da sauri ya taho domin ya hana yarima idda nufinsa. aikuwa yana zuwa daf dashi ya zare wuka ya luma masa aciki kuma ya doki kirjinsa da karfi ya fadi can gefe yana kakarin mutuwa. koda zanhas yaga abinda ke faruwa saiya zaburi dokinsa da gudu ya bar dakarun awajen saboda yasan cewa abinda zai biyo bayan wannan al'amari ba karami bane. lokacin da sadirat taga yarima ya cakawa mahaifinta wuka aciki ya fadi a kasa yana kakarin mutuwa saita tsandara ihu ta mike zumbur ta ruga gareshi amma sai yarima ya sake maketa ta zube kasa shi kuwa sai ya kamata da kokawayana kokarin cire mata tufafi. adaidai wannan likacine mahaifiyar sadirat ta fito daga cikin gida aguje saboda jiyo ihun yarta da tayi. koda ta fito sai tayi arba da gawar mijinta sannan kuma taga yarina ya danne yarta suna kokawa . nantakesai jiri ya debeta ta sulale kasa sumanmiya. yarima yaci gaba da kokarin yage rigar sadirat amma sai ya kasa saboda tana kai masa duka da hannayenta harma ta sami nasarar fasa masa baki. koda ya shafa lebensa yaga jini sai ya fusata ainun ya gabza mata wawan naushi a fuska take ta baje kasa sumammiya. duk wannan abu dake faruwa dakarunsa da suka rakoshi suna kallonsa amma an rasa wanda zai hanashi makotan makeri satyan kuwa sun firfito daga gidajensu kowa ya noke a kofar gidansa ya zuba ido kawai yana tausayi. abinka da mara mutunci da kunya a gaban mutanen satyan ya yunkura da nufin afkawa sadirat ya lalata mata rayuwa kawai sai yaji andaka masa tsawa . koda ya waiga afusace saiyaga wani dan matashi dan saurayi ya falfalo da gudu izuwa kansa bakowa bane face hatyan . sarkin mafarauta ya biyoshi da gudu yana kwalla masa kira amma yaki tsayawa ashe tun daga nesa hatyan ya hango mahaifinsa kuma ya hango mahaifiyar sa kwance agefe guda sannan yaga yar uwarsa sadirat don haka saiya zare takobinsa ya falfalo da gudu yana ihu . shi kuwa sarkin mafarauta kokarinsa shine ya hanashi abinda yake shirin aikatawa. koda dakarun guda ashirin suka hango hatyan rike da takobi tsirara ya dufafo yarima sai suka yi ca izuwa kansa ai kuwa bai fi saura taku ukuba su hadu sai hatyan yayi tsalle sama ya sare musu kawunan su duka su ashirindin suka fado kasa matattu daga kan dawakansu . dayansu bai bai shuraba ganin abin daya faru garesune yasa ya kasa ida nufinsa akan sadirat don haka sai shima ya zare takobinsa ya juyo ya fuskanci hatyan suka fara kallon kallo alokacin da hawaye yaci gaba da zuba daga idanun hatayn. yarima zainur katone nagaske kuma shi ma jikinsa amurde yake cike da kwanji da jijiyoyikai da gani kasancewa yagaji sadaukantaka . cikin tsanannin fushi hatyan ya dubi yarima zainur yace nine hatyan daga wannan tsohon daka kashe ga mahaifiyata nan bansan halin da take cikiba. kuma ga yayta nan agabanka ka sumar da ita kana shirin ka yi mata fyade . kasani inada labarin duk irin rashin mutuncin dakake yiwa yan mata agari na rantse da girman gawar mahaifina daga yau bazaka sake yiwa yan mata fyadeba kuma kamar yadda kakashe ubana nima saina kashe ubanka agaban idanunka. . Zamu dakata anan TARKON MUTUWA Abdulaziz Sani madakin Gini Typing:- prince auwal auzab Post:- AA Misau Littafi na daya 1 Part 1C . Koda jin haka sai yarima zainur ya bush da dariyar mugunta lokaci guda kuma ya murtuke fuska yace kai yaro karyarka tasha karya. koni bazaka iya kashewa ba ballantana mahaifina wanda ya gagari dukkan jarumai da sarakan da suke wannan nahiya. kasani cewa nima tun ina yaro karami yake koya mini kuma na gadoshi a jarumtaka don haka kayi shirin mutuwa yanzu. yarima zainur nagama fadin haka ya ruga da gudu izuwa kan hatyan . shima hatyan sai ya ruga kansa suna haduwa suka uguntsume da azababben yaki. tuni a wannan lokaci sarkin mafarauta yaje ya rungume gawar abokinsa satyan yanata faman usa kuka da bakin ciki. daga chan kuma sqiya saki gawar satyan yakoma kan matarsa ya shiga duddubata sai yaga ashe itama ta mutu.akwai alamun zuciyarta ce ta buga farat daya. duk wannan abu da yake faruwa mutanen unguwar na tsaye acan gefe daya suna kalloakan firgici har labari ya fara riskar wadansu unguwannin dake kusa da mutanen sai ciccidowa suke wajen. adaidai wannan lokacin da hatayan da zainur suka kachame da masifaffen yakine sadirat ta farfado daga suman da tayi. koda taga sarkin mafarauta akan gawar iyayensu. saita fashe da kuka ta zuba idanu kawai taga yadda yakin zai kasance hatyan da zainur suka wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin fushi da jarumtak. amma

Chapter 1 of 11