Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hawaye, Cikin damuwa Zayyad yace pls Hanifa, lemmie help you, ko karfin magana bata da, amma da yake jinin hajia babba na cikin bargonta, tayi qoqarin bude bakih tace I dont need your help... _Bibilicious Biebee_ 3⃣1⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕tsura mata ido yyi yana kallonta, chan ta cije bakih tare da fadin Waiyo Hajiarmu, da sauri Zayyad ya kira wata nurse a waya ta shaida mai gata nan tafe, Hanifa ta jigata amma taqi yarda Zayyad ya taimaka mata, Har isowan nurse din tana nan kwance da sauri nurse din ta shiga agaza mata, bayan ta gano bakin zaren neh, ta mata Allura, ta rubuts magunguna tare da ce mai kar ya tada hankalinshi, period ne wands ke xuwa ma mata everymonth. Ita nata da hakan yazo, Zayyad ya tausaya mata sosai, har ya na tunanin dama zai iya dauke ciwon ya maida ma kansa da yayi, don shi Allah yayi shi da tausayin mace, Yanzu duk month haka zata kasance? Allah sarki Allah ya baki lpy. Zaria Ko da ya iso Zaria, Staright gidan Ammar yayi, yana sakawa da warwarewa, har ya danna horn a gaban gidan, cikin rawar jiki me gadi ya budeh, Islah ta leqo ta window, ganin Yayanta ne ya sa ta fita da gudu, yana parker motan ya fito, Islah ta rungumeshi tare da fashewa da wani irin kuka me tsuma rai Suraj ya rungumi k'anwarsa, yana bubbuga mata baya alamun rarrashi, tayi shiru tana ajiyar zuciya, ya ja hannunta har parlo, Ya kalleta yace Isi meya fadu dake? Nan ta kwashe komai ta gaya mai, Ran Maza ya qara baci, ohh baki san cewa baya ma kasar ba? Ta dago rinannu idanuwanta ta kalleshi, baya kasar? Ina yaje? Suraj ya mike, yace i dont know, nd i dont care, all i knw is dat u wont sleep a day here again, je ki kwaso kayan ki, da gudu ta shuge dakih A gurguje ta hada kayanta cikin Katoton Akwati, ta dauki duk wani abun da zaats amfana, ta qwala mai kirah, yaya i need help here, zuwa yayi ya ja akwatin tare da fadin ragguwa, tayi daria tare da kulle ko ina, suka fita ta ba ma mai gadi key, Mai gadi na son tmby amms ganin ba fuska ya sa shi yin shiru, haka suka dauki hanyar Kano. Ba su rufe Awa 3 suka shigo kano, Bilkisu na nan zaune, Islah ta shigo da Sallama, kallo daya ta musu ta watsar, sai dsi ta amsa sallamar chan ciki, Islah tayi murmushi kisuwa matar yaya, ta kalleta ta harara, Islah dai ta zauna tana jiran suraj ya shigo, Sai ko gashi da Akwati, Bilkisu ta miqe tayi hanyar daki, ya kalleta yace madam a nuna ma Isi dakinki inda zata kwana koh? Harara ta banka mai tace ba shegiar da zata kwana min dakih, Yayi azaman damk'o wuyanta, da sauri Islah tace haba Yaya ka barta mana, ni ko a parlor sai na kwana, Suraj ya ja kayanta Ya tura dakin Bilkisu yace idan har bazaki iya kwana daki daya da ita ba, to u have to choice ko dakina ko parlor, Allah ya sawwaqe na kwana dakin ka, kuma ba zaa zo gidana a sani kwanan parlor ba Wlh ta buga tsoki ta shige dakin, Suraj yayi murmushin takaici yace yau zaki gane baki da wayau, yayi niyyar bin ta daki ya lallasata Islah ta tsaida shi, haba yaya, ai ba a biyewa, Bilkisu qanwarka ce fa, zakaji dadi Yayanta ya duke nih? Ka kwantar da Hankalinka, zan kwanta parlo, wlh bazaki kwanta a parlo ba, saidai ki kwana chan dakina nisai na kwanta a parlo, tace ok none of us will sleep here, i will talk to bilkisu. Suraj yace dnt waste ur tym sis, she's never going to change, dnt forget she's got hajia babba's blood running thru her veins, Islah daria tayi tace i will try my best. ****** Kan Gado ta iske ta, zama tayih kusa da ita tare da riqo hannunta, bilkisu ta harareta tare da janye hannunta, Islah ba ta daddara ba ta sake riqe hannunta tare da murmushi, ta cire baki ta kira ta, Bilkisu, ba ta damu da rashin tankata ta fara magana, Bilkisu, u are my lil sister and i love u so much despite d fact dat u hate me much as u hate my brother, tun muna yara mu ka tashi da tsabar junan mu ba tare da sannin tak'amaiman abun da ya sa mu ke kin jinin junan mu, yes zamuce babu shiri tsakanin iyayenmu da kakaninmu, Shekara da Shekaru maganar arziki bata taba shiga tsakanin mu ba, fadan yau daban na Gobe ma daban. Gashi har munyi aure, I got married to u brother, nd u got married to mine, ji dai saboda kiyayya, Yayanki ya tsallake ni ya bar Kasar ba tare da sanina ba, saboda tsanar daya mun bema son ya bude ido ya ganni cikin gidansa, tunda aka kaini betaba kwana gidan ba, ji dai zamanki da yaya suraj, babu wata magana me dadi, ki kalli girman YaSuraj ki maida mishi magana,kiyi mai rashin kunya, kuma kina sane da wannan auren anyi shi ne har abada, idan kina tunanin Yajawad xai dawo miki, to ki cire wnnan tunsnin, theres NO chance dat we'll all get back to our lovers, Mesa ba zamu cika ma Tsoho burinsa ba? For how long zamu cigaba da wannan rayuwa? For how long xamuyi tayin gabar nan? Think Bilkisu, think, i knw u have a good heart, itsjust dat u let Anger controls u. Kiyi tunani Bilkisu. Tana kaiwa nan ta haye gado ta kwanta, Jikin Bilkisu yayi Sanyih, ta san duk abin da takeyi ba daidai bane, duk abinda Islah tace hakan ne, zama tayi tana tunanin Rayuwa, Abun da ta kasa ganewa shine Suraj ne mijin ta na har abada, ta bar tunanin Jawad, lokaci daya hawaye ya fara sintiri a idonta, dama tun Asali Bilkisu bata da nayi sai abunda Hanifa tace tayi, bar ta dai da riqo idan ka mata laifi, Hanifa ke controlling dinta, daga karshe Kwanciya tayi gefen Islah. ****** WasheGari Bilkisu na tashi ta shiga kicin ta hada musu breakfast, abun da bata taba yi ba, wato hada abinci da Suraj, sai da ta kammala ta shiga dakih, har ynz Isi na bacci da yake tana fashin Sallah, Bilkisu ta shuga wanka, ta fito tana shiryawa ne Islah ta tashi, tare da fadib matar yaya good morning, harara ta sakar mata amma irin hararan nan na wasa me murmushi, Islah a ranta tace Alhamdulilah, ta fara sakowa, toilet ta shiga ta shirya. Misalin Qarfe 8 ya fito parlo, Ganin Coolers akan dinning ya sa shi mamaki, ko da yake kila lil sis dinshi ce ta hada musu break don yasab strongheaded Bilkisu ba zatayi ba, da Karfih yace Isiiiii, Islah tace Yaya ka fito? Yace yup. Ta ja hannun Bilkisu bayan ta gama shiri, tace zo muje parlo, Bilki ta bata rai tace kije kawai, haba mana matar yaya, ki ajiye wannan pride din gefe, ur husband is awake, Bilkisu ta tunzura, kinga dai bana so koh? Ya haquri, zo muje parlorn, da qyar ta bita parlorn, ya bisu da ido, sunyi matuqar kyau da kama da suka jero, Islah ta lura da mayatacen kallon da suraj ya bishi da su. Suraj ya mazeh yace Islah naji girkin ki na qamshi zo kiyi serving dina i cant wait to eat lil sis cooking, islah tace Yaya, i dint cook dis food, cikin mamaki yace who did? Ta daga kafadu tace ur wife did. Bilkisu ta dauke fuska kamar bata san da zamansu a parlorn ba, Suraj ya kalli bilkisu, wato yau yaci darajar Islah har break aka yi mishi, yaji dadi amma ya share yace Islahulkhair yi sauri ki karya, don yau nake son na dawo ba kwana zanyi ba, Bilkisu na san cewa ta bishi amma girman kanta ya hanata, haka suka gama breakfast suraj ya sa kayan Islah mota, Islah ta rungumeta tana jin hawayen bilkisu a kafadun ta, amma batace mata komai ba, har bakin mota ta raka Islah batare da ta kalli Suraj ba, ta koma ciki da gudu sakamakon hawayen da ke niyyar fito mata, bro donAllah muje da ita, tunda ba kwana xakayi ba, ya girgiza kansa, ta bashi tausayi, yace gwara tayi zamanta lil sis, sai nan gaba ita da maiduguri, idan ba haka ba Hajia Babba da Aunty Sadiya za su kara chusa mata wasu abubuwan banza a rai, na samu ta fara sakkowa. Islah ta jinjina kai. Haka Suraj ya bar gate din gidan suka kama Hanyar Maiduguri. 3⃣2⃣&3⃣3⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Abuja Da Kyar ya samu ya zame jikinsa daga jikinta, ya fara gajia da jarabbar Badiyya, shikenan ita ba ta da wani aiki sai wannan, gashi sai kiransa akeyi a asibiti, yau shine Dr on Call, ya kalli Agogo Karfe 10 da rabi, tsaki yayi ya shiga wanka, ko da ya fito tana nan kwance kamar ruwa, tsaki ya sake bugawa, a gurguje ya shirya cikin suit dinshi, ya bar gidan. Maiduguri Fitowar ta kenan daga Sassan Umma Hajja ta ga wani mota kamar motar YaSuraj ya danno kai, shi din ne k'ila da bilkisu donsu biyu ne, ta fada a ranta, ta tsaya tana kallo har sukayi parking, Islah ta fito suka hada ido, ai da gudu suka rugo suka rungume Juna Maysah tace Hey Sis, me kikeyi a Maiduguri? Noo i shud be asking u d same, Suraj yace Maysah ba ta ganni bane, da sauri Rumaysah ta sake Islah ta qarasa gunshi tana daria, sorry Yasuraj, wlh i was carried away, ina wuni! Suka gaisa tace ina mutan gidan? Suna Sassa, Amma Aunty Hussaina (maman su Islah) ds Aunty Hassana sunje biki, islah tace toww, bari na kai gaisuwa gun Tsoho, i missed him alot, taja hannun Maysah sukayi gaba, Suraj ya daga murya Isiii wa zai daukar miki wannan k'aton Akwatin? Tayi daria haba bigbro, ka qarashe ladarka mana, yace zaki sani, suna tafia Maysah tace Islah wat ar u duin here har da qaton Akwati? Islah tace kar ki damu sis sai dai mun zauna. Haka suka qarasa parlorn Tsoho, Hajia Babba ce zaune kusa da Tsoho suna cin Tuffah, Sallama sukayi tsoho ya dago ya amsa, sai kuma ya fadada murmushin shi, Rumah wacece na ke gani kamar Islahulkhair. Itace tsoho, Islah ta qarasa gunsa tare da daura Kanta kan cinyarsa, tsoho ya shafa kanta yana daria, Islah kin yi kewa na da yawa, nima haka.tayi murmushi ta durqusa ta gaida kakar mijinta hajia babba, sai da Hajia Babba ta gama hura hancinta kafin ta amsa, ko uban wa ya kawo ta? Bata gama tunani ba sai ga Suraj yayo sallama, Tsoho yace kai Surajo yanzu kaima kake tafeh? Suraj ya shigo ya duqah yana kwasar gaisuwa. Tsoho ya amsa cike da jin dadi, irin jin dadin da yakeji a duk lokacin da jikokinsa suka zo gaidasu, yana sonsu sosai, Rumah yau baki be rufuwa an ga Yar uwa, maysah tayi murmushi, Islahulkhairi ina Mijin naki? Ko sai ya gama gaida iyayensa kafin zaizo gaisheni, Damm gaban hajia babba ya buga. Islah tayi shiru, yace ina Mu'ammar din ne wai? Da qyar Islah tace ba tare muke ba da Yaya Suraj nake, A'aha chan kika bark mijin naki? Suraj yayi saurin cewa ai yayi tafia ba ya ma qasar, hajia karime tayi saurin tashi don barin wurin, sai dai tsoho ya katse mata hanzari. Karime ina Mu'ammar yaje? Yands tsoho yayi maganan zaka san cewa ransa a bace yake, ta fara inda inda, Ai ya danyi wata tafiya ne, amma ya kusa dawowa, tsoho cikin bacin rai yace Mu'ammar ya ya bar kasar nan ba tare da sanina ba? Tayi karaf tace Ai ba dadewa zaiyi ba, ke karime, ki fita idonaba dadewa zaiyi ba? Toh mesa ba a gaya min ba? Ke kinsani me sa baki sanar dani ba? Tace yi haquri na Shafa'ah ne, ya juya ya kalli Islah ke Islahulkhair me yasa me tafi dake ba?kyarma ta fara yi don bata taba ganin bacin ran tsoho kamar na yau ba, Suraj yace ki bude baki kiyi magana, ta lura shi suraj ko a jikinsa, ta kasa magana karshe sai ta fashe da kuka. Suraj yace Tsoho bari dai kaji maganar gaskia, tun da aka daura auren nan aka kai Islah Zaria bata saka Mu'ammar a ido ba, be taba zuwa yaji ya take ba, ya ta kwana ko me take buqata, haka ya barta ta dinga kwana a gidan ita kadai cike da tsoro da fargaba, bata taba sanar da kowa ba, Hajia babba ta fara borin kunya yo dama ya zaiyi ya kwana gida daya da ita, ya rantse ya maya ba zai iya kwana rumfa daya da ita ba don ko ba sonta yake ba, ina dalili? Sursj ya harzuqa, wato mu da muke kwana da wanda ba ma so miye kashe mu? Ko ce miki akayi muna sonsu? Maysah ta ce Yasuraj kayi shiru DanAllah, kayi haquri kabar maganan, Hajia Babba tace bar tsinannen, bar shi ya cigaba, karshe ma ya bugeni, da wannan gaya min magana da yakeyi, Islah dai kanta a kasa tana kuka.. Sallamar baba hassan da Baba Umar yayi daidai da sake Sallatinsu, Baba hassan ya qaraso da sauri yana fadin hawaye? A idon baba? Waya sa baba kuka? Gabaki daya suka juya kallonsu ga tsoho, abun mamaki hawaye kwance a kumatun tsoho, hajia babba tace hawaye? Lallai abun ya girmama, baba Umar ya zube gaban tsoho yace Allah ya huci ranka babanmu, ka fada mun wanne daga cikin yaranmu suka sa ka kuka mu tsine musu su bi dunia. Ya kalli yaransa islah da suraj yace wallahi sai na tsine ma ku in dai a dalilin ku baba ya zubda hawaye. Tun Yarintata har girmana ban taba ganin hawayen baba ba sai yau, ba abun da zai hana nayi muku bakih, da qyar tsoho yace Umaru, baban suraj ya kalli tsoho, yace kullll na qara jin kace xaka ma dan cikin ka baki, ka bari, ba ka san hadarin bakin mahaifa ba? Shi dai be ce komai ba, ya kalli Baba Hassan, yace Hassan jeka kiramin Labaran koma dai kira min kowa a gidan. Baba hassan ya fita jiki na rawa, hajia babba kuwa jikinta yayi sanyih matuqa, tunani takeyi wabi hukunci tsoho zai yanke don taga ya dauki abun da Zafih... Lagos Hanifa ya jikin naki? Wata uwar Harara ta zabga mai, yace Allah ya bki haquri, zan fita ne idan da akwai abun da zan siyo miki sai ki fada, ko tanka shi batayi ba ta tashi ta bar mai dakin ta shigewarta toilet,zama yayi bakin bedside drawer tare da dafe kanshi, oh Allah yanzu shi kuma haka zai cigaba da rayuwars? Hanifa fa qanwar qanwarsa ce, don ko ya girmi Zaid, ya kuma girmi Jawad amma yana tolerating din hallayarta. Wayarsa ya jawo ya kira besty dinsa, ringining daya ta dauka, hello Atutu, yes Ango, kina ina ne? Ina gida, kasan ina shirin tafia, ina zaki? Tace gobe zan tafi Umrah ya dnyi jim, tace anything? yace yes lets meet up pls, tace now? Yes like now where? Yace ur eatery, tace ok i will jus dress up, see you there, ya miqe ya fita ya shige mota sai TANQUIEEZ Eatery, Befi 15mins da zuwa ba itama ta iso cikin shigarta ta alfarma. Ta zauna Ango lafiya? Haka ka koma? Yace Fatiti ya znyi da Hanifa? Bata sona, ba ta qaunata, ba ta mun magana, shekaranjiya she fell sick kamar zata mutu, tana ta murqususu kamar zata shideh, nazo cikin tashin hankali ina tambayarta wats wrong wlh fati in kin tanka itama ta tanka, na zo zan taimaka mata ta tashi, yanda kika san wuta ya tabata tayi saurin janye jikinta, nace let me help u hanifa, qiriri qiriri naga tsanata a kwayar idonta, yarinyan nan ta kalle ni taxe she doesnt need my help, zayyad ya qarashe maganarsa kamar zaiyi kuka. Atutu tayi shiru tana nazari tare da tausayin abokin nata, tace Zayyad ka cigaba da haquri da Addua, InshaAllah she will come to her senses, nd nasan tana sonka, ya girgiza kansa no, bata sona i can see hatred in her eyes, tace we will find out if she loves u or not. Yace how?? Tace we will make her jealous... ********* Duk sunyi zaune sunyi tsuru tsuru kowa na son ji me ya faru, barin ma aunty hussaina da ta shigo ynz, ganin Islah da suraj gaban Tsoho ya sa hankalinta tashi, Allah kasa taron nan ban dan su bane, Allah yasa ba laifi sukayi ba. Tsoho ya kalli Baba Labaran(Baban Mu'ammar) Da Aunty Sadiya yace Labaran kunsan da tafiar Mu'ammar kasashen waje? Baba labaran ya rasa ta cewa ya fara inda inda, Ke Saadiya da izinin ki Mu'ammar ya bar matarsa ya bar kasar? Tayi shiru, ya juya ya kalli yan parlorn ya zayyane musu komai abun da ke faruwa tsakanin Islah da Amar, wuri ya dauki salati, Aunty Hussaina sai da tayi hawaye sbd tausayin diyarta. Baba labaran ya ce ayi haquri Alhaji, mun tuba, a yafe mu. Tsoho ya kalli baba labaran yace Labaran idan ban isa da kai ba, ban haifeka ba ai na isa da matarka kuma nine na haifeta. Kuma ina tunanin ya ci ace an sanar dani tafiar Mu'ammar, da sauri baba labaran yace donAllah kar kace haka wlh tallahi bamu da uba sai kai, ni da danuwa na Mudassir ba mu da wanda ya fika, kaine uban mu, kar ka juya mana baya. Ni kaina bansan da tafiar Mu'ammar ba sai rannan da zai tafi, ka yafe min. Tsoho ya tabe bakih yace kira min Mu'ammar a wayah, nan fa daya duk gidan ba me numban Mu'ammar, tun tafiarsa be kira kowa ba, Baba labaran ya rantse be da numban Mu'ammar don be kira sa ba, Aunty Sadiya ma tace ba ta da numbern shi. Tsoho yayi shiru ya kalli Islah yace kiyi haquri Islahulkhair, Mu'ammar ya bar qasar nan saboda be son bude ido ya ganki koh? Yana so har sai na gaji da ganinki na raba aurenku koh? Toh ga sako zuwa ga Mu'ammar, ni Musbahu Zailani ba zan raba auren Islahulkhair da Mu'ammar ba, Idan ya dawo nan kusa falillahil Hamd, idan ko be dawo ba, ko shekaru dubu zai yi qasar waje to ya san da saninsa cewa Islahulkhair na nan da aure, ko da xai sake wani auren ba tare da saninmu ba, Auren Islah na kansa, Akwai Aurenshi akanta, kuma Auren nan har abada sai dai in daya ya riga daya mutuwa, ku isar da saqona gunsa in ma hanani numbarsa kukayi to a Banza, ku tashi ku tafi na sallami Kowa. _Bibilicious Biebee 3⃣4⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Islahulkhair zatayi magana Babanta Ya girgiza kansa ta ja bakinta tayi shiru, haka suka fara fita daga parlon tsoho, Hajia Ama ta ja Islah sashenta, ta dinga bata magana ta hanyar Waazi da kalamai masu sanyaya rai, ta rungumeta tace kar ki sa komai a ranki, ki tafi sassan ku ki huta kinji? Maysah ku je, Maysah ta ja hannun ta sukayi Sassan Baba Umar, Islah tace ke Maysah baki gaya min ynda zamanki da yazayd ya kasance ba, ina fatan zaman naku da sauki, Maysha tace hmmm kinji kinji, ta kwashe komai ta gaya mata tun daga barinta gidan tsoho da yanda suka biya suks dauki diyya har zaman bautan da ta ma diyya da uwarta xuwa dawowanta nan, Islah ta jinjina kai, lallai kinyi qoqari, ynz sai da yaxayd ya auri karuwarsa? Ke gwara muyi zaman mu nan da mu koma gidajen mu muna kwasar bakin ciki. Kinsan qazantar da baki gani ba toh maidata tsafta. Maysah ta jinjina kai Allah ya mana da kyau tace amin. Mu danno Fadila. Ringing daya biyu ta dauka, Amaryar Ya Amar Islah tace banza ki hau IMO muyi VideoCall tace ok, Nan suka fara video call, Islah tace Guess what? Fadila tace ke banason guessing games tell me, Islah ta hasko mata Maysah Ihu fadila ta saka tace noway, wlh ba zan yarda ba, ke kikaje Abuja? Ko ita ta zo Zaria? Wait kamar dakinmu na Sassa, suka kyalkyale da daria, wai wat are u two doing in Maiduguri? Its a long story my sis, dallah ku gaya min, nan Maysag ta kwashe labarinta ta fada ma Fadila, Islah ma ta fada mata nata, Fadila ta hau masifa, ke Maysah haka kike dama? Duk da bani san jawad wlh be isa ya kawo min karuwa da uwarta nayi hidima da su ba, kambu, kin hadiye da yawa, sanyin zuciyarki tayi yawa haqurin ki yayi yawa, gashi yaso ya ajiyeki, lallai, kaii dangin hajia Babba ba suyi ba, Shine Ya'ammar ya tsallake qasar ko? To yafi ruwa gudu, kar ya tsaya kasar sin ya qara gaba, Amma wlh banso hukuncin da tsoho ya yanke ba, tsoho na shiga haqqinmu, da sauri Islah tace keee yi shiru, kar ki sa su baba su tsine mana, duk suka yi daria. Maysah tace Eeelerh ya zamanki da Yajawad, fadila ta kyaba bakih, tace ni ina ruwana dashi ba abunda ya dameni dashi. Kowa harkar sa yakeyi. Suka ce laaa Allah shi kyauta. ***** Ya Suraj ne ya leqo yace kuna ina?ni zan juya, Islah da Maysah suka fito, Yaya ka kwana mana, noo Isi, i need to go now, toh Allah ya tsare, wai Maysah me kikeyi ne anan ko kema Zaid din ya bar qasar ne? Duk suka sa daria tace Aaa yaya aure ya qarah, Suraj ya zaro ido yace Aure? Waya aura? Tace wata Badiyya ce, suraj da mamaki yace Bareh? Tsoho ya yarda? Tace ehh amma Appa ya daura auren, suraj ya girgixa kai ya na mamakin uncle Abbakar da ya daura auren kishiyar diyarsa. Suka rakashi ya ma Umma hajja bankwana, suka shiga sashen Hajia Ama, sannan sukayi sashen Tsoho inda tsoho yace Suraj ka ji tsoron Allah, kar ka Wulaqanta Bilkisu don kaga Mu'ammar ya wulaqanta Islah, kowa yayi da kyau zai gani, Suraj yace InshaAllah Tsoho ya mai sallama... Bayan wata 3(3months later) Ba abunda ya sauya nadaga Rayuwar Xuriar Zailani, ko wanne na chan na fama, Duk lokacin da hanifa zatayi period dai ta sha wahala, yanzu ya abun ya shahara har suma takeyi, ta gwammace ta mutu da Zayyad ya taimaka mata a cewarta. A bangaren Samir da Amira kuwa kullum Amira sau ta bibiyeshi tana mai magana, wani zubin ya amsata wani zubin kuma ya watsar da ita, abun ya dameta, amma ba taba gaya wa kowa ba, kusan da cewa Amira tayi sanyih ba Amirar da bace, Suraj da Bilkisu kuwa fada ya ragu tsakaninsu, Bilkisu za tayi abinci dashi, amma ba ya ganinta, rayuwar dakih ta komayi, zata gama abinci kafin ya da wo aiki da ta gama zata shigewarta daki, shi ma da ya dawo xai ci abinci yayi dakinsa, be nemanta don yana jin buruntunta a cikin dakih. Jawad da Fadila kuwa ba Uhm ba Uhm Uhm, kowannensu jiran dan uwansa yakeyi ya tanka su hau sama da masifa, amma kowannensu na kame kai, ba ruwan kowa da kowa, in ma ya fita be dawowa sai chan dare, ita kuwa da ta gaji da xaman kadaici sai tayi shigewarta gidan Amal maman Irfaan, Amal ta zaunar da ita tana mata nasihohi da waazin haqqin miji, amma fadila kunnen uwar shegu takeyi da ita, maganan ya shiga tanan ya fita tanan. A fannin yan Abuja, Ango da Amaryarsa, cin karensu sukeyi ba babbaka, Badiyya ba ta da wani aikinyi sai neman zaid, shi ko Zaid ya qi jin abubuwan da take mai, ba dare ba rana, har beson dawowa daga aiki, in ma ya dawo ya ga zata matsa mai sai dai ya tsallake ta ya wuce ys shige dakinsa ya kulle, in ko ya mata haka har kuka take mar. Islah ko da Maysah sunyi qibarsu ba su da wata matsala, kullum suna tare da tsoho, Mu'ammar na chan wata uwa dunia ba wanda ke ds labarinsa. Tsoho ya sama Zaid ido be kirashi ba be nemeshi ba, jira yake ya gudun ruwansa ko xaizo daukar matarsa ko ba zai zo ba. A gun Zaid kuwa tsakanin sa da Allah ya manta da wata Maysah, tunda ya bar maiduguri ve qara waiwayenta ba sai Yau Asabar. Daga shi Sai Diyyarsa cikin mota, Kadan ya rage su iso Maiduguri, Gun Maman diyyar sukaxo, wai bata jin dadi ita diyyar zata rakata India, so shi zaid din gobe zai koma Abuja, ko da suka iso Gidansu Zaid suka wuce duk da diyyar bataso hakan ba, straight dakin Hajia Babba tayi shikuma yayi Sassan Tsoho, Ganin mutum sukayi qiqam a kansu, Aunty Abida tace ina muka samo wannan kuma? Hajia babba ta duba tace Laaaah Er gayu ce, diyya ta qaraso hajiar mu ina wuni, lafya lao er gayu, ta kallo Aunty Abida tace Sannu, Aunty Abida tace yauwa, Hajia wacece wannan? Hajia babba tace ban son tsiyar banza, Badiyyar ce baki gane ba? Mtsw Er gayu ke da zaidu kuke tafe? Ina zaidun yake? Ta tabe bakih, yaje gun wanchan tsohon, Aunty Abida tace keee iya bakinki, baban namu ne wanchan? Baki da tarbiya koh? Badiyya ta mata wani mugun kallo, har ga Allah bata gane itace mamar zaid dinta ba, Hajia Babba tayi karaf tace ke Abida ban son wulaqanci, baqonka annabinka, Hajia wani irin iskanci ne wannan? Baban namu ne wanchan? Ke Abida tafi sasshenki, Anty Abida ta fita ranta a bace, duk rashin kirkinta ta na son Tsoho, wai wannan ce matar Zaid? Lallai ta mata kallon tsoro da farko. Mata kamar karuwa, ji uban gashin doki a kai, wai ita zata kalla tace mata sannu, ta tuna yarinyar arxiki Maysah kullum sai ta shigo gaisheta, idan ko zata gaidata sai ta zube qasa ta ce Ina kwana Mummy, amma ko kallo bata isheta ba, kuma babanta zata ce ma wanchan, wato shi ba komai bane, Tayi qwafa tace bakomi, koma menene Zaid kai ka ja mun da ka auri fitsararriya. **** Tsoho me ran karfe, Yace Wani kamar Zaid, yace ba kama bane, nine, yaxo ya kwashi gaisuwa, tsoho yace daman ana ganinka? Rabonka da nan wata kusan hudu kenan, Zaid ya shafa kansa, kayi haquri Tsoho wlh aikine, yace toh oo ni dai na zata amaryarka ta sa ka mance da mu kamanta da matarka da ka bari anan. Dam Gaban Zaid ya fadi, ya maimaita kalmar mata a ransa, be dinke ba sai da yaji sallamar Maysah ta shigo da sauri tana tsoho zskaci Kwadon Rama? Gabanta ya fadi da suka hada ido baga lurs dashi ba, shi ko sai a sannan ya tuno da cewa Yarinyar nan na nan. Da sauri ta saita nutsuwarta tace YaZaid ina wuni? Kazo lafiya? Be kai ga Amsawa ba sai jin badiyya yayi tana cewa Myzayd kazo mu tafi pls, kasan mama na chan itakadai ba ta jin-- maganan ya maqale a fatar bakinta Idonta ya kaiga Maysah, ta qara hakse ta ciko sosai. Kallon da take mata ne yayi yawa hakan yasa Maysah shan jinin jikinta

Chapter 9 of 20