Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Toh kiyi gaggawar sanar da ita k'ila ta sauya Akalar Adduarta, Fadila ta buga tsaki da karfi, tace rashin sani ya fi dare duhu kai an gaya ma-- Amal tayi saurin rufe mata bakih tare da girgiza kanta, Jawad ya kalli Amal yace ai da kin barta ta nuna miki ba ta da tarbiya, ko da ba a aura mata ni ba na girme mata nesa ba kusa ba, ya juyo ya kalli fadila yace Ke kuma kar ki daukeni kamar sakarai, ko ki ga kina mun abubuwa ina kallonki, idan nace zan bigeki karya ki xanyi, the next time da zan miki magana kikace zaki mayar min ko kice zaki min rashin kunya wallahi sai kin gane baki da wayau, sai kin gane masifar ki ta k'arya ce, ya wuce ya barsu, Fadila da zuciyarta ke ta tafarfasa, gashi Amal ta dade mata bakih da hannunta ta hana magana ai wlh da sai ta mayda mai ta ga abun da zai mata, kambu ance mishi tayi kama da wands mazajensu ke dukansu? Ai wlh da sunyi dake dake. Sai da Amal ta ga shigewar Jawad ta sake fadila, fadila ta balla mata harara. Amal ta kalli fadila tace don girman Allah kar ki kulasa idan yanayi, don Darajan iyayenki, ta dinga hadata da Allah har sai da ta sakko, tace InshaAllah zan shigo, don ina son na gaya miki wani abu, nan fadila ta mata Alqawarin ba zata ce komi ba. Amal ta juya da danta suka bar gidan, ta lura dukkansu na da Zafih,a ranta tace InshaAllah sai kunyi zaman lapya, sai kunso junanku don Wallahi kunyi matuqar dacewa da juna, sai kun kasance masu Alfahari da junanku. Allah ya bamu rai da Lafia Amin. Lagos Shigowan sa gidan kenan ya ganta zaune a parlor tana cin Abinci tana kallo, ko sallamarsa bata amsa ba, Yunwa yakeji Kamar me don beyi break ba, yace Hanifa don Allah taimaka min ds Abincin nan, Banza ta mai,da ya ga bazata kulashi ba ya mik'e ya shiha kicin don zubowa, aiko tsalle tayi ta dauke dan cooler, ya kalleta yace lpy? Eh ita ta kawo hakan ni ban dafa abincin nan da kai ba, nawa ne, kai ma sai ka dafa naka, ya kalleta yace haba Hanifa me sa kike min haka? Ni fa mijinki ne, aiko wannan kalamin da yayi ya tuno mata da ta rabu da Mu'ammar har abada fah, nan ta zage ta rufe ido ta shiga yayyafa mai ruwan masifa, bawan Allah Zayyad sai da yayi nadamar dawowa gidan, haka ya bar mata gidan ya wuce TANQUIEEZ EATERY don cin abinci.Restaurant din na Best friend dinsa ne me sunan Fatiti amma customers sun fi saninta da Madam Atutu, ba ya son Abincin saidawa amma yana son abincinta don ta iya sosai, gata da Tsafta, Ga ma'aikata masu tsafta da ladabi, Matashiya ce da ba ta wuce 25years ba, dukda ita din Yare ce amma kyakyawa ce ga kirki, tunda Zayyad ya fara Aiki a Lagos suke shiri, Restaurant din nan na ta ne, yawanci sai da daddare take shigowa shagon don itama ta na zuwa aiki a wani company. Kusan a tare suka yi parking a restaurant din, Hararansa tayi tace Ango ka sha Kamshi sai yau ake ganinka? Yayi murmushi yace Fatiti yunwa nikeji muje ki ban abinci, suka shige ciki ta kaishi VIP table, da kanta tayi serving dinsa, ta zauna kusa dashi, sai da ya cinye abincin nan tas kafin ya dago kansa, tana nan ta kura mai ido, tace Ehennn ina jinka, ya kalleta cike da mamaki, yace menene? Tace mid to tell me wat ur problem is? u look disturbed. Zayyad yace Its my wife, cike da mamaki tace d bride? Wat happened? Nan ya kwashe komai ya gaya mata farawa daga yanda akayi auren har zuwa ynz, ta nisa sosai gun tunani, tace Zayyad bani nan ds kwana 2, i will find u a solution yayi godia sukayi sallama. Abuja Zaid ne zaune kan kujerarsa a office bayan ya gama ganin patients dinsa, Mu'ammar ne zaune gefensa, Zaid yace muje gida ko Ammar? Mu'ammar yayi dan guntu tsaki yace noo bana son ganin wannan maysah din, Zaid yayi dan murmushi yace kai ina ruwanka da ita? Ni bana son ganin abinda zai hadani da yan dakin Hajia Ama. Yanzu zaid daria yayi har da riqe ciki, ka dauki abun da zafih, ynz ba ma wannan ba, dole sai kayi tafian nan? Inaga idan ka zauna ba sai ka kulata ba koh? Kamar ni nan gaisuwa kadai ke hadani da yarinyan nan, idan na ga dama ko gaisuwar ba zai hada mu ba, kayi xamanka, Mu'ammar yayi guntun tsaki yace ni i've made up my mind, i just need to be alone, so nake nayi forgeting sister dinka don yanzu ta haramta gareni, Zaid yace shisa ni ba ruwana da wani soyayyah, balle ynz na zama abun tausayi, jus look at u Amar, duk ka rame kayi bak'ih coz of dis worhtless love. Amar yace ba zaka gane ba, not evryone is like u, Zaid yace toh ita yarinyan chan zaka barta, zarian, alla alone? Tsaki ya buga, yace ni ina ruwana da ita? I dont care abt her, idan sun gaji sa raba auren da kansu, Shisa zanyi tafiana ba tare da na gaya ma kowa ba, balle a chusa min bakin ciki, ko su Mummy sai na tafi zan sanar dasu. Zaid yace when is ur flight? Yace nan da 8:00pm, kana ma da time, muje mu zagaya sai na kai ka Airport... (Bayan wata daya ) Nidai Zaid Gaskia na Kaqagara muyi aure, wallahi ni sai na ga kamar baka sona, kamar ba aure na zakayi ba, Zaid pls help me i really want to be ur wife, Zaid yayi shiru yana tunani, ko giyar wake ya sha ai ya san ba zai iya tunkarar Danginsa da wannan batu ba, Aure? kuma bareh? Kukan da ta keyi ne ya maidosa daga tunanin da yakeyi, Haba Zaid ina ta magana baka tankani ba? Zaif mesa kake min haka? Ko don kaga ina sonka? Girgiza kai yayi, tare da riko hannuwanta, haba Diyya, kinsan dai gidanmu ba a auren bareh koh? Ina neman hanyan da zasu barih muyi aurene, kuma kinsan bazan je wani guri a daura min aure ba, ba zan yi aure ba tare da sanninsu ba, tace idan basu amince ba fa? Yace sai muyi Adduar amincewrsu, tashi ki kira min yarinyar nan, wacce yarinya? Ya kalleta yace matar gidan, A ranta tace Zaid dan iska ne, ji yanda yake sha min Kamshi, toh ko me dai zakayi sai na aureka ta shiga har dakin Maysah da ke kwance ta qwala mata kirah, firgigit ta tashi kasancewar yanzu ta gama shan wanki maman diyya, ta dan rusuna Naam Aunty, My Zaid na kira tana kaiwa nn ta juya, ita ko Maysah jiki na rawa ta bi bayanta, watan daya da wani abu ba ta taba jin Zaid yayi kiranta ba. Zubewa tayi, Yazayd ina wuni? Be amsata ba, yace kingane, ina so muyi magana ne, ta tattaro hankalinta ta ce toh Yazayd, ya kawar da kai, Gobe Zamuje Maiduguri, ta dago da murna ta kalleshi, tunda kika zo gidan nan na taba miki kallon banza ko harara ko kyara ko wani abu? Da sauri ta gyada kanta, yace Good, a ranta tace baka taba ba, amma karuwarka da mamanta sun maidani Baiwa, Jin muryarshi tayi yana cewa, Zan yi Aure!! Zan auri Badiyyah, Dam Gabanta ya fadih, Nd ke zaki taimaka min gun Tsoho, hawaye suka cika Idonta Fal, So Gobe idan munje, na ma tsoho bayani ya kawo min Gardama, toh sai ki san abinda zakiyi kingane? Ta gyada kai, yace tashi ki tafi, jiki a sanyayye ta bar dakin, Aure? Ko wata biyu ba suyi ba? Wani xuciyar kuma na ce mata ai gwara suyi auren da suyi ta irin wannan Zama na Haramun da sukeyi. Haka ta kwana tana kuka, tunda tayi aure takeson Ganin Tsohonta, Ammanta, Umma hajjanta, da Hajia Amanta, Sai dai kwatakwata bata Murnar zuwa Maiduguri, ji tayi kamar tace mai ba ta zuwa, sai dai ba zata iya ba, ba ta da yanda xatayi sai Roqon Allah ya sa mijinta ya auri Karuwarsa... Maiduguri Suna isa gidan Straight dakin Hajia Babba suayi har ita Maysah din, kasancewar an sanar dasu zuwan, an shirya musu kayan tarba da yawan gaske. Wani abun haushin har da ita uwar badiyya Hajia Babba ina Aljannah ta sa zaid, shi ko sai wani qamshi yake sha mta, Allah ya dora mata son Zaid, ta fi sonshi duk cikin jikokinta, ta saki Zaid da ta hango badiyya ta rungumeta Ga Yar Gayu ga Yar gayu, Badiyya tace ga hajiarmu, ta nuna uwarta da yatsa tace Hajiarmu ga mamata, Hajia Babba akaje aka rungume uwar badiyya tana ga maman yar gayu, ta kalli Maysah ta wurga mata mugun harara, Maysah ko tunani take ina Hajia babba ta san Badiyya? Bayan an zazzauna ne Hajia Babba tace ku zo ku ci abinci koh? Suka miqe duka wani harara ta wurga maysah dashi irin me Alamun ban dafa da ke ba, Zaid na kallonsu, cikin saa ko suka hada ido da Maysah, baki na rawa tace bari na shiga cikin gida, ta juya be tanka ba sai hajia Babba tace da dai ya fi miki don wlh ko dandano ba kici, Girgiza kai kawai Zaid yayi, nan suka hau fira da su Badiyya kamar tun da sun son juna. ***** Sai da ta leqa parlorn, kamar yadda ta zata yana Zaune kan kujerarsa, juyowa yayi suka hada ido, murmushi ta sakar mai tare da fadin Assalamu Alaikum Tsoho na nan?? Shima dariar yayi, yace Aa Baya nan, da gudu kuwa ta nufeshi shi ko ya bude mata hannuwa tashige jikinsa ya rungumeta, sai da ta yi hawaye don ko tayi missing dinsa fiye da kowa, Ya dago ta ya shafi kanta RUMAH kece nan? Ke da maigidanki kukazo? Shine baki sanar min ba? Ita murna ya hanata cewa komai, sai daria mara sauti take tayi, Agogon dakin ya buga Karfe 2:00 na rana, yace ai tun da kinzo, jeki sakko min da tiren abincin chan, yau a tsakiyar parlo zamu ci abincin rana, haka kuwa akayi suka ci suka sha sukayi nak, ta kwashe kayan, tace bari nayi cikin gida, ban shiga sashen kowa ba, Tsoho yace ina maigidan naki? Ta qaqalo murmushi tace yana nan shigowa. Yauwa in kin shiga ki turo min babanki yazo na sashi aiki, Tace toh A hanyar fita taci karo da Hajia Babba da su Zaid na biye da ita, kanta a qasa ta wuce su, Da Sallama suka shiga parlorn, Tsoho cikin murna mara misaltuwa yake ma Zaid kirarin Likita bokon turai, Sannu ka da zuwa, Zaid yayi murmushi ya durfana gaban tsoho, Barka da Rana Tsoho mai ran karfe, Shafa kansa yayi yace Zaidu, muna lafiya? Lfy qalaw Tsoho, ya karfin jiki? Tsoho yayi wani shuumin murmushi yace ahh jiki da sauki, Hajia Babba ta katse su, Alhaji baka ga da Bakih muke ba? Ya dago ya kalli Badiyya da mamarta lokaci guda yaji ya tsanesu duka, amma da yake shima dan dunya ne yayi murmushi yace ina na lura dasu, Durkusawa sukayi sauna kwasar Gaisuwa, ya amsa ba laifi. Ya kalli Hajia Babba, Karime ina muka samu Bakih? Ta dan sosa Qeya tana so ta san inda zata fara, sai chan tayi dabarar cewa Alhaji Amaryarka ce da mamanta, Yayi murmushi yace Amaryata? Ke kina son tsoho? Kin yarda ki zauna cikin tsoffin mata na? Wayaga Auren buta, ita ko badiyya harda sinna kai ita wai nan kunya tajih, Ai Alhaji sun dade da daidaitawa da Zaid, shine sukazo gaidaka, Ba tsohon ba, har shi Uban gayyar sai da yaji faduwar Gaba, Tsoho ya maze yace ban fahinceki ba, ita ko tace Budurwar Zaidu ce, ita yakeso ya aura, Tsoho yayi shiru, na wasu sakwanni, kan Zaid a Kasah kamar na kirki, yace idan na fahimce ki karime, ita wannan ya nuna diyya ita ce budurwar zaid wacce zai aura, ita kuma wannnan uwarta ce, sunzo gidansu saurayi kawo gaisuwa?? Cikin murnar Tsoho ya fahimceta ta gyada kai Eh hakan ne Alhaji, Tsoho yace toh ba a gidan nan ba. Duk suka dago suka kalleshi, Bangane ba, Tace ke karime ki fita idona, ke sakara ce, wannan ce kike so Zaidun ya aura? Toh ba zai faru ba, ya kalli Badiyya yace yarinya, kije ki nemi miji kiyi aure ba dai zaidu na ba, badiyya ta rarafa ta kama kafar tsoho, donAllah Grandpa kayi min rai, i love Zaid alot, Tsoho ya kalleta, yace Ke er bariki, bazan aura miki zaid ba, wai Grandpa, zaki zo kina nun karairaye, ni ba yaro bane, ke ga er boko koh? Toh Bature ma yaci ubanshi, hajia karime tazo ta dago badiyya dake ta kuka tace haba Alhaji menene haka? Zaid da jikinsa yayi sanyi ya daure yace Diyyah, ta dago ta kalleshi, ya cire key a aljihunsa ya miqa mata, go home, i got dis okay? Zaid pls help me, dont let him do dis to us, u knw i cant leave wothout u, yace Diyyah kije, i want u to trust me, i will find us a way i promise. Ya kalli mamar yace mom kuje gida zanzo, ta miqe tana hararar tsoho ta ja hannun diyarta, Tsoho yace oho dai agayas akai kasuwa, Zaid ya daure fuska kamar be tava daria ba, fuskar nan daure tamau, tsoho yace ni wannan daure dauren da kakeyi be shigata, kazo ka bugeni sai na san kanayi, in banda rigima irin taka, ina kai ina wannan fyarinyar? Dukaduka yaushe akayi aurenka? Kai a ce kayi shekara 10 da aure ance maka zan yarda ka auri bareh ne?, balle duka ko wata 2 baka rufa ba da aure. To udan mafarko kake ka tashi. Ni Musbahu Zailani ba zan yarda ka auri Bareh ba. _Bibilicious Biebee_ Add 2⃣9⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Zaid ya juya ya kalli Tsoho yace Ina so ka aura min Badiyya, ina sonta, da ka aura min Wannan yarinyar nayi biyayya na xauna da ita duk da na tsani na bude idanuwa na naganta cikin gidanah, amma saboda biyyaya ko kallon banza ban taba mata ba, ds Su Mu'ammar suke ta kuka suna hadaka da Allah kar a hada auren nan, ban ce komai ba ni, yanxu kuma nazo ina roqonka ka aura min Badiyya kana ce min aa, bakai min adalci ba, tunda na bi umarninka, to nima a bani zabina, tsoho Yayi shiru yana nazarin maganganun zaid, chan yace Zaidu da dai a cikin gida ka ga mace to ina iya aura ma, amma Bareh ne bazan aminta ba, Ba ka taba ganin an auri bareh ba, toh ba kuma zaa fara daga kanka ba, Zaid yayk wani shuumin murmushi, ba a taba auren bareh ba? To kakar yarinyan nan micece? Inace bare ceh? Er wata qasar ma, ko kana zaton bamu da labarin Uncle Abbakar da yaje karatu Russia ya aurota? Naga itama din bareh ce, Tunda har ka yarda ya aurota, nima hakan zaka yarda na aureta, Tsoho ya bude bakih galala, Zaid ni kake gaya ma magana? Hajia babba tace ai ba batun gaya magana sai gaskia, shi Habubakarin finshi yayi da ya auro tubabba? Uncle Abbakar da Maysah da ke tsaye bakin kofa suka qaraso ciki, duk zancen da sukayi a kan kunnenshi, ya kalli hajia babba rai a bace yace Raijana ba tubabba bace, a musulmarta na ganta, ya kalli Zaid yace Zaidu, zaid ya kasa dagowa su hada ido da Uncle Abbakar, don shi Allah ya mishi kwarjini, qaryan tsageri ya kalli baban maysah ya mai tsageranci, Zaid dai ya amsa ba tare da dagowa ba, Uncle Abbakar yace Lokacin da naje karatu russia, sai da nayi shekaru 5 kafin na dawo gida, mu ba mu samu gatan dawowa gida hutu kamarku ba, wanda duk lokcin da kuka so dawowa kuke dawowa, Ganin shekara 5 ba nan kusa bace, gudun kar na fada ga halaka yasa na auri Raijana, mamar matarka, sai da na dawo su baba suka san nayi aure, na sha fada amma da na nusar dashi dabarata tayi aure ya fahimceni, kagane? Zaid da yaji kunyan Uncle Abbakar ya lullubeshi be ce komi ba. Badiyya kake son aure koh? Sunannta kenan? Ya gyada kai, Uncle Abbakar ya durqusa gaban tsoho ya shiga hadashi da Allah, da Magiya kala kala na kan ya bar Zaid ya sake aure, Maysah ma ta durqusa ita ko harda kuka, ganin kukan da takeyi ne ya sa Tsoho cewa sai yaje yayi tayi, ni ba ruwana cikin alamuaaran zaid, na zare hanuna daga duk wani shaani nashi, Zaid ya matso yace ayi mun haquri tsoho, na tuba, na mata Alqawarin aurene, banso ta dauke ni a matsayin mayaudari, Tsoho yace kai dai kasani. Uncle Abbakar yace kace mata ta turo magabanta ni zan tsaya ma, ni zan aura maka ita, Da sauri zaid ya kalli Baban matarshi, yayi saurin sadda kai kunyar uba da 'yarsa ta lulubeshi, wasu irin mutane ne wannan?Wani uba zai ma diyarsa kishiya? Wata mata zata roqa ayi mata kishiya? Jin muryan Uncle Abbakar yayi inda yake cewa kaji ai, ina so na gana da magabatanta, zaid yace nagode Allah ya qara girma. Wayarsa ya ciro ya sanar da Badiyya ta zo da Magabanta ta yanzu, cikin doki ta sanar da uwarta, cikin rawar jiki sukaje suka kwashi Kawuninta da basu dauke su a bakin komai ba, wani kawunta yace sai yau kuka san damu? Sai da aurenta yazo kuka san amfaninmu? Nan badiyya da uwarta suka shiga bada haquri don basa son abun da zai hana auren nan, sai da suka cikasu da kudih kafin suka bisu, niko nace dama Mace ke tura magabatan ta ba maza ba?😒 **** Bayan an sanar da yan gida akwai daurin aure a parlon Tsoho, bayan an hallara nan take Uncle Abbakar ya daura Auren Badiyya da Zaidu bisa sadakin Naira dubu 100 lakadan ba ajalan ba, uncle Abbakar ne waliyyin ango, gaban tsoho akayi komi sai dai tak ce ce musu ba, tausayin Rumarsa yakeyi. Bakin Badiyya kamar gonar auduga, yau ta zama mallakin Zaid, sai yashe haqora take tayi a dakin hajia Ama. Ita ko Maysah kulle kanta tayi dakin Ammanta tana ta ruzgar kuka, tausayin kanta takeji, anya batayi ganganci ba? Allah gani gareka. Haka ta dauro alwala ta dinga jera nafilfili Allah ya kawo mata sauqi a kan har bacvi ya kwasheta kan dardumanta, bata farka ba sai Assalatu. Zaid ya shigo dakin badiyya tayi tsalle ta rungumesa, ya dagata ya juya,cikin murna yau gani na zama taka, bantaba tunanin hakan ba, har na cire rai fa, zaid ya ja hancin ta yace i told u i got dis dint i? Yes u did ma hubby, yace kun shirya? Tace ehhh, yace breakfast fa? Ta mai fari tace its too early, yace toh mu tafi, tace mom tace xa mu barta anan, zata biyo mu daga baya, akwai abun da zatayi a nan din, yace ba laifi, ya shiga dakin hajia Babba ya gaidata ya mata sallama yanaso ya iso Abuja da wuri, don yau Monday, ta musu rakiya, suka shiga sashen su Zaid, ya gaida Mamarsa da Babansa, badiyya tana ta jin kunyan qaryar, nan suka musu Sallama, har zasu tafi Zaid yace muje muyi ma Tsoho Sallama Badiyya ta turbune fuska, tace i dont like dat old man, Zaid ya galla mata harara yayi gaba, bata da wani choice din binshi a baya, Da Sallama suka shiga parlorn, yana zaune yana lazimi, Zaid ya durqusa itams hakan tayi, sai da yayi minti 30,kafin ya shafa, Zaid ya ce Barka da Asuba Tsoho, ba laifi Tsoho ya amsa amma ba kamse yadda yake mai da ba, Badiyya da ta gama quluwa da shanya sun da yayi ta gaisheshi tana harareharare, lpy kawai yace mata, Zaid yace Tsoho dama yanzu zamu wuce Abuja, kasancewar yau akwai aiki ban dauki excuse ba, Allah ya Tsare kadai tsoho yace, Zaid ya Amsa da Amin ya miqe har sun kai bakin qofa Tsoho ya cire bakih yace Zaiduu, Zaid ya juyo tare da amsawa, tsoho yace Rumah fa? Zaid ya fara inina shi ya mance da wata Maysah, ya shafa qeyarsa yace ita ta na nan, sati me zuwa zan zo na dauketa, Tsoho ya daga kai Alamar toh, Zaid yayi saurin barin parlorn dan kar tsoho ya jaza mai Aiki.. Tsoho kam takaicin Zaid yayi, yana son zaid sosai amma wannan abun da yayi kawai yaji zaid ya sire mai, ya mai ciwo, Duk cikin jikokinsa ba wanda ya ma gata kamar Zaid, don tunda ya aura ma Zaid Maysah yasan ya mishi babban gata, samun Rumah a matsayin mata Alheri ne babba, Amma da yake Zaid sakarai ne, be gano hakan ba, tsoho yace bakomai Duniya ce, Duniya ce zata ladabtar dakai. Yana cikin tunanin zuci Rumah ta shigo da Sallama ya amsa mata cikin sake fuska. Kallo daya ya mata yasan ta sha kuka sosai, tausayinta ya lullubeshi, Nan ta zauna suka shiga hirar yaushe gamo ba tare da ya sanar da its tafian Zaid ba Abuja Karfe 5 suka shigo gida, Badiyya ta gaza sukuni burin ta ta samu Zaid a yanzu, tun cikin mota take ta shafa shi, sai da ya dakatar da ita, yace wai so kike muyi accident? An riga an daura auren nan m all yours, i think u can wait har mu isa gida, if not i can find a place park my car nd u suit urself, ganin gatse ya mata ya sa ta shafa mai lafia. Tun a parlor ta fara shafashi tana kissing, haka dai ya biye mata har badiyya ta samu cikar burinta. Zaid ya ga salo salon iskanci, lallai kam badiyya tayi nisa. Sai a yau ne ya tabbatar da ya auri karuwa. _Bibilicious Biebee_ 3⃣0⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Kaii I cant take dis anymore, da sauri ta janyo wayarta ta shiga laluben wayarshi. Kano Bilkisu ina abinci nah? Ta kalleshi ta watsar, sai da ya maimaita mata kana ta dago ido ta kallesa, tace ban dafa da kai ba, ya kalleta cikin mamaki yace sabida mey? Sbd ni ba baiwar ka bace, kuma ai naga kana da hannu koh? Zuciyya ta ci Suraj, haqurinsa be kai ta dinga gasa mai magana ba ya qyaleta ba, yau ya lashi takobi sakko mata da wannan rashin kunyar da girman kan nata, Shaqr mata wuya yayi ta sakeh ihuu, ya daga hannu kenan zai mareta wayarsa tayi kara, guntun tsaki yayi ya wulla Bilkis gefe, ya zaro wayarsa, Lil sis screen din ya hasko da hoton lovely K'anwarsa yasa ya dauka da sauri, Hello Islah? Ya kike? Jin muryan yayanta ya sa ta fashe da kuka be tsuma rai, nan da nan Suraj ya rude, Islah? Are you Ok? happened to you? Cikin kuka tace yaya Wlh m not alryt, come get me outta dis hell, ina Mu'ammar? Kinsan i dont have dat ryt to pick u up, tell me is Mu'ammar hurting u? Yaya tinda aka kawo ni so daya na ganshi, rannan ma ko 20 mins beyi ba, kayanshi ya kwasa ya bar gidan, What? Inji Suraj, u mean to say ke kadai ce a gidan for 1month 15days? Ya shiga ciki da sauri yace so sorry sis gani nan zuwa, key kawai ya dauka ya fitow, ya na fadin i promise u duk inda Amar ya shiga a garin zaria sai na binciko shi, he's going to pay for hurting u. Bilkisu ta fashe da daria, Suraj ya kalleta, goodluck in finding ya Ammar, ba Zaria zaka tsaya ba, ka hada da Kasashen wajeh, dan be K'asar kallonta yayi sosai, zuciyarsa na mai zafih, ransa ya baci sosai, a hankali ya furta me kike nufi? Ko tausayi tace gani yayi ba zai iya zama da ita ba, kuma an fi karfinshi an hana shi sakinta, shisa ya bar Qasar kuma ba zai dawo ba har sai yaji kun raba auren. Idanun Suraj sukayi jaaaa, ya ga bata lokacin shi yake yi nan gun bilkisu ya fita a fusace ya ja motarsa ya bar gidan ya kama hanyar Zaria. Nidai nace Suraj a dai bi a hankali, Allah ya tsare ya kai ka lapya.. Bauchi Ya Samir pls ka samo min Islamiyya na dinga zuwa, zaman gidan ba dadi, nikadai a ciki, idan ka fita sai dare, pls yasamir, kallonta kawai yayi so daya ya wuce be ce da ita qala ba, haushi ya isheta ta miqe ta nufa dakinsa tajishi a kulle, nan ta fashe da kuka tana ta buga kofa amma yayi biris da ita, abunda samir yake mata ya fara isanata, anya zata cigaba da haqurin nan?? Kaduna Ko da ta bude K'ofa Fadila ta gank tsaye, Amal ta harareta ta shige ciki, fadila tayi murmushi, tace haba Mummy Bon wai fushin ne haka? Wai ba gashi na zo ba? Amal tace sai da aka kusa wata zaki zo? Tace ai min haquri, ina Irfaan? Tace yana bacci, nan suka zube a parlo suna ta fira, cikin dabara Amal ta tambayi fadila ya zaman ta yake da Jawad, Fadila ta kwashe komai ta gaya mata har sillar auren su,da rashin jituwarsu tun kafin ayi auren, Amal ta nisa ta na tunani, ji labarin nan kamar a fim, tace Fadila listen to me and listen good, Ba zaki biye ma Jawad kuyi ta xaman nan ba, kin dai ji abun da tsoho yace, ba saki cikin auren ku, whch means u guys are stucked together forever u need to learn how to leave with eachoda, nd love eachoda. Fadila ta zaburo, me kike so kice min mummy bon? Ni zan kai kaina gunshi? Na roqe shi ya soni? Kindaiji me ya ce kwanaki koh? Ke ganau ne ba jiyau ba, so ki bar wannan maganar, ba zan taba kwantar da kaina na bishi ya wulaqantanni ba wlh, so bar ma wannan zancen,Amal tayi murmushi, Fadila kenan, ba nufi na kenan ba, namiji sakarai ne, kamar yaro yake sai yanda kikayi da shi, ke fa mace ce, akwai yan dabarun mata da zaisa hankalinsa karkatowa gunki, Fadila ta miqe a fusace tace No thanks, kar Allah ya sa hankalin nasa ya karkato gurina, muyi ta zama haka har dunia ta nade for all i care, Amal ta na mamakin zafin kai irin na fadila, amma she wont give up har sai ta ga ta shirya wadannan maauratan. Lagos Riqe take da cikinta tana Murqususu, hawaye na bin kuncinta, ta gama galabaita, ta kawo ma kanta mutuwa, yarda kasan tana ciwon Naquda, ta nayin scramps sosai, amma na wannan month din yayi worst, Waiyo Allahn ta, da qyar ta shiga toilet ta watsa ruwa, tana jan jiki ta fito daure da towel dafe da cikinta, jiri ya dibeta ta zube a qasa, Shigowar sa kenan ya ganta a K'asa, da gudu Zayyad ya K'arasa gun hanifa, Hanifa hanifa, are you ok? Kamar ta ga wani dodo tayi karfin matsawa, ya sa hannunsa zai dago ta, ta buge mai hannu tana

Chapter 8 of 20