Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
qarfi ne tun kafin a haife mu akeyinshi, sai nake ganin kamar wuta za a qara ma lamarin, tunda duk basu jituwa bane, maganin kar a fara kar ayi, Baba Hassan ya girgiza kai yace aa ina ga hakan ne maslaha a cikin wannan gaban, dole muke kawo qarshen wannan Gaban kuma inaga wannan ce hanyar da zai sa a samu sulhu, So ina ga Baba hakan daidai ne, Baba Gambo yace Hakan daidai ne kuwa baba, sai dai a roqa Allah ya daidaita tsakanin mu duka, M.Zailani yace Hussaini ka fahimci abun da Yayanka yace? Baba Hussaini ya gyada kai, yace wannan gaskia ne, daman bawai naqa bane ina gani kamar ba za a daidaita ba, baba hassan yace always pray for d best broda. Yace toh Allah ya sa mu ga da kyau. M.Zailani yace toh shkn tunda har kun amince da Raayina. Hakan zaayi (ni nace me zaayi tsoho? Harara ya wurgo ni da ita) ******** Maysah da Tsoho suna zagaya gida, ya na bata labarin Soyayyar shi da Aishalle, tana ta daria yace muje mu kaima Yayanki Ziyara, Tace wanne daga ciki? Yace muje dai, rabon da Tsoho yazo bangaren samari Har mantuwa ta manta, kai tsaye dakin farko ya qwanqwasa ya shiga, Zayd ne kwance da fara singileti ba bacci yakeyi ba amma daga ganinshi buge yake, ga kwalbar giya ta Gulder da Star ya shanye, Gefenshi Diyya ce kwance tana bacci, Tsoho firgici Maysah firgici, tsaf tagane wanda tayi fada da amira ce shekaran jiya, lallai Abun Yazayd ya girmama, har gadon baccinshi yake kawaota, Allah ya shirya! A hankali Tsoho yace Giyah? Ga mace Kwance a cikin Gidana? Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Zayd ya miqe duk da ya dan tsorata amma da yake dan dunia yace me ran qarfe lafia ka shigo Sassan mu? Ko nema na kakeyi? Tsoho ya share yace ziyara kawai na kawo ma, Amma bari muje kafin ya ce komai Maysah ta riga tsoho fita, jikinta rawa yakeyi, har suka koma Sassan tsoho basu tanka wa Juna ba, Duk Zuri'ata Zaidu kaine Daban Allah ya shiryaka Dole na muku Aure, dole nake aurar daku duka, Ya Allah kai mana da kyau. ****** Fadila da Suraj a dakin hajia Ama suna Soyewa, tana zuba mai shagwaba Wai gaskia ba zai tafi kano week din nan ba, yace baby kiyi hqr so kike a koreni a wajen aiki? Tace ba sai a maka transfer ba? Yace ina kike so mu zauna idan munyi aure? Ta daga kai sama tana tunani tace Kaduna, yace daman tunanin mu daya, kar ki damu da hannuna na zana gida a kaduna har an fara gini fadila tayi ihun murna tace thank u mysuraj, Sarkin Gida ne ya shigo da Sallama yace Tsoho na kiran ku, suraj yace mu suwa? Yace dukkan ku na cikin dakin nan, har da Hajia Ama, taro ne na gaggawa, suraj yace toufa Allah ya sa lapya, fadila gaya ma su hajia a ciki da su Islah, aka sanar dasu duka. Kowa ya Hallara abun mamaki harda yayyinsu da matansu da sukayi aure na nesa ne kawai babu to lapya inji Islah?duk suka zazzauna, One by One tsoho ke kallonsu, daga matayensa zuwa yaransa zuwa jikoki harda masu musu Abincin GANDU, Tsoho ya gyara Murya Ina Zaidu?? Jawad yayi qarfin halin cewa yana Dakih, be ji aikena bane? Jawad ya miqe bari na kirashi, yace kai Jawad Zauna, Ya kalli inda mata suke yace RUMAH jeki kira yayanki Zaid, gabanta ya fadi haka ta miqe tayi Sassan Samari, ta kusa minti 5 tana tunannin yanda zata shiga dakin, sai tayi jihadin Sallama da qarfih, fitowanshi wanka kenan, daga shi sai towel, yace waye? Shigo, ta shiga saurin rintse ido tayi, ya daure fuska ke Lapya? Uban me ya kawo ki dakinah? Tace kayi haquri, Tsoho ke kiranka, kowa na chan kai kadai ake jirah, tana kai wa nan tayi saurin fita yayi dan jimm tabbas ya san meeting din nan nashi ne, ya dan firgita amma dayake namijin dunia ne ya dake ya zira jallabiyansa yayi cikin gida da takunsa. Ya shiga wakeken parlorn da Sallama, Gabanshi ya fai ganin idanuwa akansa, duk ya tsargu ya sha jinin jikinsa, kusa da Jawad Ya zauna. Tsoho yayi Bismillah tare da guntun muqqadima da sallama duk aka amsa mai, Ya fara cikin maganarsa ta manya : Ahh, batare da bata lokaci ba, kamar yadda kuka sani a wannan Zuriah tawa, idan Namiji ya fara aiki, Mace ta gama sakandire ana masu aure, kuma ni ke zaban musu mataye da mazaje, kuma DOLE abi umarni nah, kasancewar ina da Zuriah da yawa nake hada aure uku uku, ko hudu hudu wata sain har biyar biyar, wannan abu ne da kuka sani ba sai na dinga nanata shi ba a duk lokacin da zanyi hadi, Bana Zaa aurar da Mutane 12, maza 6 mata 6, gaban Masoyan nan 12 yabada HINGIM, fargaba ya shiga zuciyoyinsu, kunsan dai duk maganar da na yanke ta zauna, ko da yake ban yi tsammanin musu daga daya daga cikinku ba don na san kunsan Qaidojin Gidan nan, ba a soyayyah ko auren bare, wacce ko wanda M.Zailani ya zaba shine magana. Gabansu ya sake yankewa ya fadi Tsoho ya cigaba da jawabi, Toh na riga nayi tsarina kamar haka ; ZAYYAD na baka HANIFA, SAMIR na baka AMIRAH SURAJ na baka BILKISU MU'AMMAR na baka ISLAHULKHAIR, JAWAD na baka FADILA, ZAYD na baka RUMAYSAH. Tashin hankali, Firgici, Rudani, Kurumta, Makanta, Bebanci ya dirar ma Masoyan nan 12lokaci Guda ba sa gane komai ba sa jin komai ba sa fahimtar komai ba kuma sa ganin komai... Shin wannan Hadin Zaiyiwu? Shin Wannan Gaba zata tsaya kuwa? Shin Akwai Sulhu tsakanin yan Dakin Hajia babba, da Dakin Ama da na kuma Umma Hajja? 👻This is just the Beginning👻 A Cigaba?? 1⃣7🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 ⃣ GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee 💕Biebee Isa💕Parlorn yayi tsit kamar ba kowa cikinta sai qarar fanka, Tsoho ya cigaba da magana, kuma zaa daura auren nan ranar jumaah me zuwa ma'ana nan da kwana 7, firgigit suka dawo hayyacinsu kallo daya zaka masu duka zaka ga tashin hankali a fuskokinsu, Jawad ke maimaita sunan fadila a bayyane tare da kallon inda yammatan ke zaune kuka yaga rabin ransa bilkisu keyi, zuciyarsa ya hau zafi da ya hango fadila rakube tana cizgar kuka, lokaci daya ya tuna rashin kunya ta da shirga mishi, nan da nan haushin ta da tsanarta suka darsu a ransa da sauri ya girgiza kai wlh ba zaiyuwu ba da sake. A bangaren Mua'amar kuwa Tunani yake yama za ayi ya auri watan da ba Hanifa ba, ai ba zai mayuwu ba da sauri ya rarafa gaban tsoho tare da ririqe mai kafa, yace tsoho, kar kayi mun haka, ka taimakeni ka bani Haneefa, haneefa ce rayuwata. Baba Mudassir yace kai Mua'amar meye haka?Tsoho ya daga ma baba mudassir hannu yace, barshi ya gama, ina jinka Amar, ko kunya be jiba ya cigaba da cewa tsoho ka taimakeni, kaji tausayina ya qarashe fadi tare da kuka me zafih da ya kubce masa, Tsoho ya shafi kanshi a hankali yace kayi haquri, na san menakeyi, Wata rana zakayi Alfahari da wannan hadin nawa, Girgixa kansa yayi da qarfi tare da runtse idanuwa, Samir ma ya matso yace tsoho danAllah kar ka rabani da Islahulkhair ya xa ayi ka hadani da Amira? Damm gaban Amira ya yanke ya fadi, bata qin samir hasalima ita bata yi baqincikin wannan hadin ba, fargabanta daya Samir Islah yakeso, to idan samir ya qita to wa zai sota? Suraj zaiyi magana Baba Hassan ya wurga musu harara shi da Zayyad ba shiri sukayi gum, Shi ko Namijin duniya wato Zaid, ko a jikinsa don ya san wannan abu ba zai yuwu ba, ya ma xaayi ya auri wannan qaramar yarinya? In short ba me mun auren dole, ni banda mata da ta wuce badiyya so tsoho ma zai tashi daga wannan mafarki coz it will never happen.**** Tsoho ya bi su duka da Ido, Kuka sukeyi ba mazan ba ba matan ba, Idonshi ya tsaya kan Ruma ganin hawaye kwance kan fuskar Maysah yasa zuciyarsa sosuwa, ya furta a hankali Rumah zo nan, a hankali ta miqe ta nufa gunsa, yace Rumah me ya saki kuka? Rumah bakya son wanda na baki? Kuka me tsuma rai ta fashe da shi. A hankali daidai yanda zaijita taceTsoho kar ka mun haka, ya zaayi ka hadani da Yazayd? Tsoho ko ka manta rannan da-- da sauri ya katseta ta hanyar sa hannu a bakinshi, ta girgiza kai, ta dan daga murya ba zan yarda ba tsoho, ba zan yarda ba, Mashayi? Mazi--- tasss kakeji, Baba Abbakar ya kasheta da mari, abunda be taba yi mata ba kenan, Maysah ta dago idanuwanta da suka rine sukayi jazir ta kalli babanta, a hankali tace Appa ya nuna ta da yatsa, yace ke kin isa Tsoho yayi miki zabi kice ba kyaso? Toh idan ni na haifeki baki da mijin da ya wuce Zaid, sai anyi auren nan, sai dai ki mutu Rumaysa, cikin isa da gadara Zaid yace wai wani zaid din? Ni fa ba zan auri wata yarinya a dangi ba, ina da wacce nakeso, Uncle Abbakar ya wurga mai wani mugun kallo, duk tsagerancin Zaid sai da ya ji shakkun Babban Maysah. Hajia Babba dake zaune ta gama cika pal, tace ai ba qarya yayi ba, duk cikin wannan hadi ba wanda xaiyuwu, babu yanda xaayi ni ko jikokina su hada iri da dangi Aljanu da Mayu, to Alhaji tun wuri ka chanza wannan maganar don wallahi ba zaiyuwu ba, wannan maganar maganar nosense ce, maganar banza, jikana ya auri jikar Hajjo ko Aishalle? Sai dai a mafarki wollai, Parlorn yayi shiru, ta inda Hajia babba ke shiga ba ta nan ta ke fita ba, sai bambami take tayi. Kowa ya xuba mata ido, sai zagezage take tayi, Miqewa yayi Qyam sakamakkon jin kanshi da ya sara Qirjin shi ya shiga yi mai zafih ya sa hannu ya dafe, ba wanda ya lura dashi don hankaliksu na chan gun Hajia Babba da ke ta faman masifa ita ba zata hada iri da dangin mayu da Aljanu ba , Hanyar Qofa ya nufa hannunsa dafe da qirjinsa, ji yayi qaffafuwansa sun gaxa daukar sa jiri ya fara dibarsa, sai ji suke Timmm Tsoho ya Xube qasa, nan aka shiga rigerigen nufan inda tsoho yake, Baba Hassan ne ya sa hannu wurin hancinsa be ji tiririn nishinsa ba, cikin kaduwa ya ce A dauko mota, Jawad Zaid Muammar Suraj da Samir ne suka fita da gudu don dauko mota hankalin su Ya tashi ganin ba alamun Numfashi tattare da tsoho, Suko matan kuka suka sa barin ma Maysah, ita ko Hajia Babba kuwa kururwa take tana cewa waiyo Mallam Kar ka mutu ka barni, kayi haquri kar baqin cikinmu ya kasheka, ka tashi Mallam. Baba Usman ne yace haba Hajia ce miki akayi ya mutu? Tayi saurin cewa Auuu be mutu ba? Be tanka ta ba anan ne Suraj Ya shigo ya ce baba ga motan nan gaban parlor, nan su jawad suka shigo ko wannensu ya dauko motarsa, nan Zaid ya cicibe tsoho shi kadai yayi wajeh dashi, bayan motan da ke parke gab da parlon ya shimfideshi a baya, kowa ya samu mota ya shiga Suraj kuwa da Tsoho ke bayna motarsa ya zagaya ya ja Motar sai Asibitin Dr Munnir na Alheri Hospital. Convoy akayi, saboda kidima Hajia babba da Hajia Ama, da Umma Hajja mota daya suka shiga, motar Zaid, Iya rudewa sun rude, hajia Ama da Umma hajja dai hawaye suke don tun rasuwar Baba Rabi'u basu qara ganin tashin hankali ba irin na yau, ita kuwa Hajia Babba bata fasa ihu ba tana Allah kar ka kashe Alhaji, Allah ka raya shi, Waiyo ni karime, Zaidu ba a iso bane? Zaid da ya qulu sosai, yana son Tsoho sosai yana fargaban rasa shi amma wannan matar ta cika mai kunne, tsawa ya daka mata yace idan ba ki min shiru ba zan zubar dake a nan, da sauri ta kama bakinta. ***** Islah a bayan mota riqe da hannun Maysah riqe da hannun Fadila a bayan motan Samir, Amira na gaba kowannen su Hawaye ke bin kuncinsu, tunda suke a rayuwansu ko ciwon kai basu taba ganin yayi ba. Amma yau shine harda yanke jiki ya fadi, Suna cikin matsanancin tashin hankali wanda roqonsu Allah ya tashi kafadar Tsohonsu.. *** Ko da suka isa Asibitin Already Dr's and Nurses na jiran su a entrance don tun a hanya Baba Gambo ya kira Dr Munnir ya Sanar dashi komi. A haka aka daura tsoho a kan gado aka jashi zuwa A&E wato Accident and Emergency. Tsoho Allah sa a Dace 1⃣8⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu by🏠by 💕Biebee Isa💕 💕Biebee Isa💕Biebee💕Biebee Isa💕 Da sauri Liktoci suka du'kufa gurin ceto ran tsoho, Zuriarsa na wajeh hankalin su tashe yake, kowa da kallan tunanin da yake, Hajia Babba sai kai kawo take binibini ta lewa dakihn, Hajia Ama kuwa ta kame guri guda da tsura ma dakin ido, bayan kamar rabin awa, Dr Munnir ya fito yana shar'ce gumi, da sauri suka xagaye shi, ya kallesu ya girgiza kai, yace ku muje office. Har wasu dai suka riga Dr shiga ofishin shi, nan da aka zazzauna, wasu kuma na tsaiytssye don duk Girman Opishin Dr ya gaza dauke Iyalan Zailani.. Dr ya kalli Manyan Yarsn Tsoho, Yace ya akayi haka? Su Baba Hassan duk suka zaro ido? Yace ya kuka bar Ciwon Zuciya ya ma Tsoho mummunan kamu farat daya? Duk suka dau sallalami, Ya kuka yi wannan sake? Hajia Babba tace wlh baqin cikin mu ne, Waiyo ni kaina. Zaid ya watsa mata mugun harara, ya cigaba da cewa, munsamu mun shawo kan matsalan da qyar. toh gaskia Dole ku kiyaye bacin ran sa, dole kuke mai abubuwan da yakeso, nd ku nisantar da shi daga abubuwan da baya so, Nd dolenku kumai abun da yakeso kafin ya farfado, don gudun hakan na iya sa wa zuciyarsa ta buga farat daya. Gaban kowan nensu ya fadi, Mu'ammar ya girgiza kai ya fita daga dakin, Jawad ya bishi hakan nan Zaid. Duk aka bisu da ido, Dr yace idan kuma kun gaji da hidimar sa tunda ya tsufa ku barshi kawai ya mutu, Hajia babba ta zunduma uwar ashar, Dr kaci Kwal Ubanka, mu barshi ya mutu fa kace? Yace ahtoh, ai don ina ganin abunda ya ke so me girma ne, ba zaiyuwu ba, tace Dole kuwa zai yuwu, dole a aurar dasu ga maqiyansu,. Ke kima waanan jikokin naki magana, dole suke aurensu ba don na so ba, sai don ceto ran Mallam. Ta miqe tare da fadin tashi dan Usmanu, muje mu ga yaran nan. Balki ku biyo mu duk suka bi bayanta jiki a sanyaye, ya rage daga Zuriar Umma hajja sai na hajia Ama cikin ofisihn Dr. Dr ya miqe yace toh bari na barku ku zanta. ***** Ai wallahi ba zan yarda na auri wata Islahulkhair ba, Ya zaayi ma hakan? Da sauri Aunty Sadiya ta riqi danta tace Amar baka fini Tsanar wannan hadin ba ban qi ayi tashin hankali ba don a fasa auren nan, but bamu da choice, i love my Father, i cant watch him die, please sonn, u nd bilkis will listen to me and marry dem for a short period of time, da Yaji sauqi xaka saketa ka auri Hanifar ka kaji? Kema dole muke matsa ma Suraj ya sakeki kinji? Bilkisu ta na kuka tace indai wannan zaisa Tsoho ya tashi ya ji sauqi toh wlh ko waye xan aure shi. Aunty Sadiya ta rungumeta yau diyata. Its just for a short period of time. Aunty Abida ta kalli nata yaran tace dat goes same for d u three, Zaid, Jawad, Hanifa bama son wannan hadin but we love our Father. Shine Gatanmu da duk wanda muke taqama dashi. We cant let him die. I knw y'll love Tsoho nd Ya'll sacrifice for him ryt suka gyada kai, then do dis for him okay? Nd remember its just for a short period of time... Aunty Zainab rungume take da dants Samir daga chan gefe Baba Gambo na kallonsu cike da takaici, kuka ko Samir kamar mace? Amirar Annoba ce? Aunty Zainab ta kalleshi ta mai Alaman ya fita, Baba Gambo yayi gaba. Ta shafa summar kansa tace *Samir* yace Mami kiyi shiru, dole zan Auri Amira don ceto ran tsoho Amma dole zanyi kukan rabuwa da Islah. Mamin tace haba Samir, abunda yayi Islah shi yayi Meerah, ka duba ka gani, da sauri yace wlh shes nothing like dat-- yi shiru mana. There are times da zaka so abu sai Allah ya hanaka don ba Alheri bane a gareka, sai ya Musanya maka da abun da yafi Xama Alheri, Maybe Islah ba Alheri bace a gareka, Maybe Amirar ce Alheri, kuma ita Allah Ya tsagaa rabonka da ita. Think wise son, u are d bravest i've ever seen, ya qirqiro murmushi yace i will marry Amira. Tayi murmushi tasan ba ya amince da Amira ba ne Aa sai dai don kawai ya faranta ran maminsa. **** Toh ni ba sai nace muku komai ba, duk nan kun mallake hankulanku, nd kunsan whats right, so i trust u to do the right thing, Baba Hassan ne ke wannan maganar.Umma Hajja tace ai na san Yan jikoki na da ladabi da biyayya, masu son Farincikin Uwayensu, nasan ba zasu bar son zuciyarsu ya shiga cikin wannan Lamarin ba, Baba Hussaini yace toh ya kuka ce? Hajia Ama tace ai nasan jikokinmu sun Amince, don suna son wannan tsohonsu sosai koh? Rumaisah tace idan akwai wanda yafi makaho makanta, kurma kurumta gurgu gurgunta, zan aureshi don ceto ran tsoho, wanda ya soni ya qaunace ni, Fadila ta kalli Suraj, tace nima na amince zan auri YaJawad duk da na san aurensa baraza na ne a kaina, Amma ina son Tsoho sosai, dole nake haqura na ba Tsoho abunda zaisa sa farinciki. Islah na matsar kwallah tace Zan auri Ya Jawad. Zayyad yayi karaf yace muma mun Amince zamu auri Hanifa da Bilkis Allah ya sa hakan yafi zama Alheri Aka Amsa da Amin. Hajia Ama ta kalli Baba hussain tace na gaya muku yan jikokina Akwai ladabi Biyyaya. Yace ai nagani Allah muku Albarka Ameen... Hajia Babba ta shigo da zurianta a bayanta fuskokinsu murtuk, suka zazzauna. Dr Yashigo yace toh duk kun shirya ba Tsohonku abun da yakeso? Sukace Ehhh. Yace toh MashaAllah. Allah ya tashi kafadun shi. Yace kuma a barshi ya huta, yana so kowannensu yaje gida don be son hayaniya. Haka Baba Hassan ya sa aka tattarasu akwa maida Gida. Da qyar Hajia Babba ta amince zata tafih. Daga shi Sai Baba Ussaini suka tsaya... GASKIAN LAMARIN. Kwana 2 kafin (2days Back) TSOHO zaune da Family Doctor dinshi Dr Munnir, kuma amininsa wanda ya san duka Sirrin Tsoho da yanayin GIDAN GANDUnsu, , amma Tsoho ya girme mishi nesa ba kusa ba, don ko tsaran su Baba hassan ne, Tsoho yace Dr bansan yanda za'ayi yi na hada auren nan ba, don kasan dan yanzu ka haifeshi ba ka haifi halinsa ba, suna iya bijire mun suce tunds basu na haifa ba zasu mun rashin ta ido balle dukkansu soyyaya suke, toh ina tsoron su ki Amincewa. Dr ya nisa yace Akwai Shawara idan zaka iya, Tsoho yace me ke nan? Dr ya sausauta murya ya ma tsoho qusqus a hankali me kama da rada, Tsoho yayi daria yace hakan ma zaayi, ta wannan hanyan zan magance duk wata matsalata. Zanga idan Zasuyi man Hallacin na, Zangani idan ina da mahimmanci a rayuwansu, naji dadin shawarar nan amma taya zanyi na zube qasa har na dauke numfashi na? Yace kar ka damu, akwai maganin da zan baka ka sha, be da illa. Zai taimaka maka gun aiwatar da qudurinka, kuma idan aka kawo ka asibiti, da drip din da Allurorin da zaka sha duk masu Amfani ne ga me lafiyayyen jiki kamar su Bcomplex d.s. so kar ka damu, ba abun da zai shafi Lafiarka. Tsoho yayi murmushi yace nagode likita Allah ya sa mu dace yace Amin...Toufa jamaaa kuna jin wannan plan din na Tsoho? Duk yabi ya tada ma Zuriarsa hankali🤔🤔 nidai nace kaiii Tsohon nan Namijin Duniya ne👻. _Bibilicious Biebee_ 1⃣9⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 Gandu Gandu 🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Sai da Tsoho yayi Baccin Awa12 kafin Maganin bacci ya sake shi, A lokacin Daga Dr sai Baba Yan 3, Dr munnir yazo yana duba shi, DrMunnir ya kashe ma tsoho ido alamun komai daidai. Sai yace MashaAllah jiki ta warware, ina ma iys sallamanka. Amma zan barka ka dan huta, Tsoho yace me zai zaunar danih tunda naji sauqi kunsan da ina cikin hayyacina ai da ba a kawo ni nan ba. Dr yayi daria yace haka ne. Nan ya rubuta musu takadar Sallamah, Baba Hassan ya kira Suraj yace kazo kai maida mu Gida. ***** Kowa yayi murnan ganin tsoho ya tako da Kafarsa. Barin ma maysah da take kukan murna, don ta ba Tsoho mutuwa. Sashensa yayi Hajia Babba sai rawan Jikin Alhaji me kake so? Alhaji me za a maka? Yace wanka zaiyi, nan BabaAbbakar ya umurce kowa da a bar Tsoho ya huta... WASHEGARI Tun daga nesa ta hangoshi bataso ya cimmata sai ta qara sauri, tun jiya take avoiding dinshi, da gudu ya tankarota, yana kiran Fadila, haba Fadila ki tsaya mana, Ya qaraso, Fadila y are u avoiding me? Tace Ya Suraj yace shhh, fadila Tsoho ya ji sauki, ba abunda ke damunshi ynz, lets run, lets leave dis place, muje wani wuri a daura mana Aure, i cant do without u, kukan da take boye ya kubuce, sai da tayi me isarta ba tare da ya hanata ba ta girgiza mai kai, tace Yasuraj wallahi tallahi ina sonka, zan auri Ya Jawad and zaka auri Bilkis, idan muka gudu, mukaje aka daura mana aure me mu kayi kenan? Mu bijire ma iyayen mu? Bakin cikin mu ya kashe tsoho? Gaban ya cigaba da wanzuwa frm generation to generation? If we leave, they will be seperated forever, maybe this f only way to End our Family's Malice, Ka roki Allah ya sa hakan yafi Alheri, And Allah ya ba mu ikon rungumar wannan Kaddarar, tana kaiwa nan ta ruga da gudu. Tayi sashensu, A hanya ta ci karo da Bilkisu da ta fito daga Sashen Tsoho, taja ta tsaya, Bilkisu na watsa mata harara, tace listen to me Fadila kar ki ga kamar Gobe Zaki zama Mallakin Yajawad kice zaki zake, ki kira kanki matarshi, to bari kiji Yajawad nawa ne, Aurenku suna ne kingane? na dan wani lokaci ne, idan komai ya daidaita zai sakeki ya aureni, so i want u to keep ur distance, ban yarda ayi seducing masoyina ba. Fadila tayi murmushi ta shar hawayenta. Tace Bilkisu bana son Jawad bana kaunarsa toh mesa xanyi tunanin Jan hankalinsa ko ra'ayinsa? Kuma da kike cewa nan ba da jimawa ba zai sakeni, kin ga na miki kama da wadda zata zama bazawara in future? in kinso ki ka she aurenki ki zama bazawara, ki sami wani miji amma badai Jawad ba, i dont love him but i will make sure dat he never ever gets back to u get dis into your thick skull Jawad ya miki nisa. tayi gaba ta barta bakih bude tana mamakin karfin Halin fadila ita da ba sonsa take ba. ***** Islahulkhiar kwance a green carpet din field din Gidan idonta lumshe, tana tuna moments dinta da Samir, time din da suke kwallo, ko kwallon kwando ko skipping rope, Maganar Hajja Ama ta tuna inda take cewa _kuyi haquri da wa'enda aka zaba muku, ku roki Allah ya sa sune Alheri, ku Maida Soyayyar masoyan ku a kansu, ku maida Soyayyar Masoyanku Soyayyar yanuwantaka don ku Yanuwan juna ne Allah muku Albarka_ islah ta matse hawaye tace Allah kasa Ya Mu'ammar shine Alheri a gareni. Tsaki taji an buga tsuuu Ta na dagowa taga Amira da Hanifa. Amira tace lallai kam kin ma kanki Kiyamul laili, gwanda da kika haqura da Yasamir, don nice matar da aka zaba mai. Gwara da kika dangana Allah hada kanku da Ya Mu'ammar din Islah ta girgiza kanta ta miqe ta kakkabe jikinta tayi gaba don bata son hayaniya. Hanifa da qarfi tace aikin banza, ko me zakiyi Ya Mu'ammar ba zai taba sonki ba, ni yake so ni kadai, jini na ke gudana a zuciyan shi, da komi ya daidaita zai sakeki ya aureni, dan ba zai taba hada iri da dangin mayu da aljanu ba. Chak Islah ta tsaya, kamar ba zata yi magana ba kuma sai ta dawo da baya, ta tsaya Daf da Hanifa tace, Wai tada jijiyoyin wuya na meye ne? Naga dai tsoho ya san dake ya zaba mishi ni? Duk da jinin naki na gudana a jikinshi, ki bari ya sakeni mana yazo ya aureki kafin ki gaya min magana, but as far as m concerned ni zai aura Gobe, nd m d choosed person its not my fault dat m more beautiful and talented dan u, its not my fault dat i'm chosen for him, so Maybe tsoho ya ga rashin dacewar ku ne ya zaba mishi ni, if u have a problem go meet Tsoho, amma idan zaki bi shawara ta, ki koya ma kanki Son YaZayyad don Ya Muammar will never ever come back to u, tana kaiwa nan tayi gaba ta barsu baki sake, chan kuma Amira ta pashe da daria, kaii ashe Islah na da baki haka? Wai its not her fault😂 wato wato shes more talented nd more beautiful dan u, ooo Islah got attitude, Hanifa takaici goma da ashirin, ashe wannan haka take? Ai bata taba zatan zata tanka mata ba, Ga haushin darian mugunta da Amira ke mata. Ji tayi kamar ta sa Ihu don takaici. ******** A yau Jummaa Wurin Huduba Liman yayi sanarwa za a Daura auren Jikokin me Masallacin nan, ana buqatar kowa ya tsaya bayan an Idar da Sallan Jummah. Haka kuwa akayi, ana Idarwa aka daura Auren ZAYYAD da HANIFA, ZAID da RUMAISAH, JAWAD da FADILA SURAJ da BILKIS, SAMIR da AMIRA da kuma MU'AMMAR da ISLAHULKHAIR bisa Sadaki dubu Hamsin lakadan ba Ajalan ba, aka shafa kuma aka wadata su da Rengem na shinkafa(lol) Tsoho baki har kunne, Angwayen kuwa kadaran kadahan duk da Mu'ammar da Jawad ba su tsaya daurin auren ba. Nidai nace oho dai an riga da an daura. Ko da ku ko baku sai da Tsoho ya Daura muku aure👻 _Bibilicious Biebee_ 2⃣0⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Daren da Aka daura Auren abu dunia ya ishe Sabin maauratan, da Angwaye musamman Amaren, daga Zaid sai Amira kadai ne basu da wata damuwa sosai ko wannensu na sashensu jikinsu duk yayi sanyi. Kuka wiwi Rumaysa keyi, Shikenan me afkuwa ta afku, YaZayyad ya mata nisa, yanxu YaZayd ne mijin ta. Allah ka ba ni ikon Cin wannan Jarabawar. Amma ce ta dafata da sauri ta share hawayenta don bata so Amma taga kukanta hankalinta na iya tashi, Amma ta mata murmushi cikin hausarta da har yau be fita tace Maysah kuka kike yi koh?

Chapter 5 of 20