Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fadila ce za a harba, so stop blaming ursef kajih dana? Yace thank u Mummy. Duk suka fice, Zayd ya bi bayansu don nema musu masauki duka... ***** Maysah nakan sallaya ta idar da sallar maghrib, jawad kuma na kan gadon da fadila ke kwance har zuwa yanzu bata farfado ba, rashin farfadowanta ya fara bashi tsoro, ya riqo hannunta yana murzawa a hankali, ya na magana me kama da sambatu, inda yake cewa ke me tsiwa, kika sake kika mutu sai na biki, toh meye amfanin rayuwata idan kin mutu?ai ban gama jan bakinki ba idan kika murguda min bakih, so its early for u to die, sai kuma ya fara hawaye, kamar an tsunguleshi ga goge hawayen idanunsa ya dan daga murya yace ke dallah ki tashi. Kamar tajishi, cikin ikonAllah fadila ta bude idanuwanta a hankali, ta sauke su fes kan Jawad da sauri ta hade rai tare da murguda mishi bakih. Da sauri jawad ya hada bakinshi da nata. 5⃣4⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Fadila ta daddage ta gantsara ma jawad cizo a bakih, ya dan saki karah ya saketa, ta sake murguda mai bakih, shi kuma ya ja bakin a hankali, yace you are Okay, Dont make me worry too much about u like dis, sai a sannan komai ya dawo ma Fadila, ta tuno cewa harbinta akayi, ta sa hannunta ta shafih kafardarta taji bandage, da sauri tace Ya Jawad someone was trying to shoot u, yace shhh, save ur strength i know wat happened, a halin yanzu an kama su, amma sunqi magana, sunqi fadan wanda ya turo su, but it wont be long before they expose who sent dem. Tayi ajiyar zuciya, Fadila,e kikeso?ina ke miki ciwo? Ta murgudi bakih, tace ni ka kaini gida, ni ka kaini maiduguri, ina son ganin tsoho da Mummy, yace karki damu, su tsoho na nan kd, basu dade da tafia ba, Gobe zasu dawo kinji? Ta gyada kai a shagwabe, yace look who's here, ta kallo inda yake kallo, tayi yunqurin tashi tace Maysaaah, yayi saurin maida ta, yace ke mallama koma ki kwanta, Maysah da ta tsaya kallonsu don kalar Soyayyar su ta birgeta, ta qaraso kan gadon ta riqo hannun fadila Tace sannu sis, ya jiki? Fadila tace yaushe kikaxo? Kwana nawa anan? Kwananki 2, ta zaro ido, tace m happy to see u sis, Maysah tace same here, get well soon kinji? Fadila ta turo bakih tace ni fa ba abunda ke min ciwo m okay. Jawad yace yauwa baby haka nakeso, ta harareshi tace mallam ni ba baby bace sunana fadila, yace yarinya bari a sallame mu mu koma gida, sai na yi maganin ki, ai kinsan halina. Fadila ta koma ta kwanta kan cinyarshi inda taga kanta da farko ba tare da tankashi ba. Shi kuma ya shiga shafar kanta fuskarshi dauke da farinciki. ***** Washegari su Tsoho da iyalanshi suka dawo, sunji dadin ganin fadila ta ji sauki don ynz ma Zaune take Jawad na bata abinci a yangance take amsa. Tsoho yace tunda ta farfado da alamun ta warke, yau xasu koma, Baba hassan yace Jawad ya maganan Gunmen din? Har ynz ba su fadi wanda ya turo su ba? Yace Eh baba basu fada ba, ni ban masan me ake ciki a yanzu ba, Zaid yace yanzu idan na rakaku zanje Police Station din naji abinda ake ciki, Hajia babba dai ta sha jinin jikinta ganin Jawad ko kallonta beyi ba balle ya gaisheta, ga Zaid nan ma fushi yake da ita, ta na son jikokinta, Sai da Tsoho yace ayi addua don nemar lafiyar fadila da karfi tace Ameeen, amma hakan be sa Jawad kallonta ba. Haka dai yan Maiduguri auka tafi, Zaid ya shaida ma Maysah suma yau din zasu koma da laasar. Fadila ta sa Maysah ta kira mata Amal, baa yi 15mins ba sai ga Amal da mijinta Rufa'i, mijin Amal yace da Jawad wlh baka kyauta mana ba, a matsayin mu na Makwafta mu ya kamata mu riga kowa sani, abu har an kwana biyu ba muji ba? Jawad yace kuyi hqri, tunda akayi abun so daya na koma gida, kuma ban dade va, suna cikin fira sai ga Zaid ya dawo, suka gaisa da Rufa'e, zayd yace da Jawad ya tashi suje police Station, Jawad yace aa bros, kai dai kaje, ni ina nan da matata, fadila ta murguda bakih tare da hararashi, hakan da tayi ya basu daria dukah, Maysah tace Ya Jawad kuje kawai, trust me zamu kula maka da matarka, kaga ma maman Irfan, tana nan ko? Amal ta gyafa kai, tace uo wife us safe, ya danyi shiru kafin ya kalli fadila yace baby naje? Ta murguda baki tace sai ka dawo, ya xo ya bata peck suka juya zasu fita, har waigen ta ya ke juyowa yanayi. *POLICE STATION* Har ynz sunqi magana sir, Zayd ya ce suna ina? Wani kofur yace suna nan cikin interogation room, Zayd yace i want to see dem, be sha wahala ba aka barsu su ka shiga, suna nan an daure su gam su 3, Wurin dan karamin Zayd ya nufa, ya ce kai, wa ya turo ku ku kashe Kani nah? Mutumin ya dago zai yi ma Zaid rashin kunya, yana dagowa suka hada ido da shi, eye in eye, sai ya dauke fuska dob Zaid din ya mai wani irin kwarjini, Allah ya ma Zaid wani baiwa, duk iskancin da tsagerancin mutum ya hada ido da zayd sai ya raina kanshi, hakan ta faru a yanzu don zaid ya juye ya koma terror dinsa, barin ma da ya amshi bindiga ya saito kan mutumin, Zaid yace ka ganni nan, i care less abt u, is either u tell me who ur boss is, or i will shoot u, tuni mutum ya rude kallo daya ya ma zaid ya san zai aika, murya na rawa yace pls dont shoot, i will tell u what happened, Gambo Kashe Arna da aka daddaure aka yi selotaping bakinshi ya fara jijjiga yana zaro ido, alamun be so a tona ubangidanshi. Mutumin da ya ce sunanshi killerman yace Ranar wednessday, Oga ya kira mu, yace zamu mishi aiki Officer yace waye oga? Killer man ya nuna Gambo kashseArna da hannu, yace na boss dinshi ne, shi time din yana lagos, so kuma aikin Emergency ne, shi ne ya tura mu gurin shi Boss din, ni da frnd dina muka je Guest house dinshi don mu ganshi ya bamu bayannin yanda yake so aikin ya kasance, so boss be ji dadi da ya ganmu ba, don yace shi yafi yarda da aikin Oga Gambo, i assured him dat he has nothing bto worry about, don Oga trained me well, ni ne nayi Gadonshi a wannan Sana'ar, so nan boss ta bamu Full Address na Gidan Jawad, nd his picture, we asked if he's married or living with his parents yace no he is living alone, nan muka tabbatar mishi by d end of d day Jawad zai mutu. So sai nace mishi me yake so a mishi? Sai ku Amsar min Documents din da yayi signing na Contracts, sai ku kasheshi, bance kuyi robbing dinshi for money, i will give u Enough, i dont want any mistakes. Nace kar ka damu Boss, zakaji sanarwar mutuwar jawad kafin jibi. Muka tafi mukaje ni da abokina, bansan yadda akayi polisawa suka shigo ba, mu kaji tsoro sosai, so we ran for ourlives tho we were captured. Officer yace toh kuna nufin ba ku ku ka harbi ba? Then who did?Killer man yace Oga ne, Ashe tym din da muka tafi gidan Jawad tym din ya dawo daga lagos, akan hanyar ne na sanar dashi gamu nan zamuje chan, so sai ya biyo bayanmu. Shi kuma yayi harbi. Zaid cikin daga murya yace wai who are we talking? Who is dis motherfu**er dat wants my bro dead? Da sauri killerman yace sunanshi Alhaji Haladu Maidala NNPC, Iya rudewa da kaduwa Jawad ya shiga, yana mamakin Alhaji Haladu, mutumin da ya ke girmamawa kamar mahaifinshi, mutumin da yaje bi sau da kafa, baba ma yake ce mishi, shine yake so ya ga bayanshi? Me ya mishi haka? Zaid ya juyo ya kalli jawad yace u knw someone by d name Haladu? Kai kawai ya girgiza mai Alamar, Eh, Zaid ya kalli Officer yace you guys shud go get Dis Haladu of a guy, or i will, nd if i do i will be d one to kill him, DPO yace no sir, lets do dis d right way, ka bar hukuma tayi maganinshi, Zaid yace hukuma ai bata hukunta babban mutum kamar Haladu, nasan zaayi cukucuku a barshi ya fita, DPO yace na tabbatar maka wannan case dib bazaayi cukucuku ba, don daga sama aka kira mu, daga chan Lagos aka kiramu, kaga kuwa magana na hannun manya, dole a saka Haladu behind bars, Good inji Zaid, Nan take aka bada order din aje a zo da Haladu, motoci 3cike da yansanda suka tafi chapko shegen. Ba kuma su sha wahala ba gurin gane inda yake, suka nema ya bisu a hankali yaso kawo musu gardama, nan wani police mara mutunci ya chafko wuyarshi, aka saka mai Ankwa aka tasa qeyarshi sai police Station, Haladu ya kalli sergeant yace waya baku damar ci mun mutuci gaba mutane haka? Do u know who i am? Jawad ya fito ya kalleshi yace Baba me na maka kakeso kaga bayana? Me na taba ka? Where did i ever go wrong? Alh Haladu yayi mamakin ganin Jawad, duk a zatonshi an kashe shi, yace forgive me Jawad, wallahi ban taba sonka ba, duk abun da nake maka munufurci ne, zuwan ka NNPC ka min illa babba, ka kwace min matsayina a gun gwamnati, da maaikata, komai sai dai a ce Jawad, ka fara dakusar min da tauraruwata da ta haska diniyan nan, duk inda ya kamata aga Haladu Maidala ba a ganinshi saidai aga Jawad Zalani, Alhalin nafi Shekaru 20 ina aiki a wannan Maaikatar, shisa nace kawai bari na ga bayanka, Jawad ya kalleshi cikin tsana yace its not my fault dat m more hardworking dan u, Hassada ce matsalarka, da ace ka gaya min haka da na bar maka aikin kwatakwata, don mu ba matsiyata bane, Jawad ya juya ya fita daga Office din, Zayd ya kalli DPO yace sunyi filing case akanshi, so sun makashi kotu, nd kuma kar a bada belinshi har lokacin, Alhaji Haladu yace Noo, pls dont do dis to me, Zaid ya kalleshi galala yace; this is wat u get wen u mess with a Zailani. Cambridge England A hankali ya bude idonshi, ya sa hannu ya shafa kanshi, qaton bandage ya ji, nan Dr ya shigo tare da mutumin da ya buge shi,You are finally up inji Dr, murmushi kadai Amar yayi, What happened? Last i check i checked i was brot here, dr ya mai bayanin duk abun da ya faru, tare da gaya mishi yanda aka sha wahalan neman jini, da kuma yarda yaruwarshi tazo aka bada jini, da sauri yace who? Dr yace she said she's yo relative, she was here earlier but she left after being sure that she's all okay, da sauri yace did she leave a message or something?Yes she left her number incase something came up, may i have d number, Dr ya bude file dinshi ya ba Amae number, ganin sunan Islah ya fito kan wayar yasashi cixge drip din hannunshi,yace i gotta go, Dr yana kiranshi amma be tsaya ba, sai da ya bar Asibitin. Straight Cambridge University ya nufa. ******** What? Kika ba wannan mugun jinin ki? Inji zaineema da ta tsani Mu'ammar don Islah ta gaya mata waye Mu'ammar a gareta, Islah tace Eh zaineema, he was running outof Blood, nd kuma ba inda ba a nema O- ba, ba a samu ba, so i helped, Zaineema xatayi magana sukaji ana kwankwasa kofar, islah ta tashi ta bude, ganinshi tsaye ya sa ta mamaki, a ranta tace wato ya warke kenan? Islah nagode, Allah ya saka miki da Alheri, naji dadi sosai, haka ake so ka zama mai yafiya idan aka maka abu, dis shows dat u'v forgiven me, dakatar dashi tayi ta hanyar daga mai hannu, tace haka mukayi da kai? Kar ka ga na maka donating blood ya sa ka fara jin dadi, ko ka yi tunanin na mance abun da ka mun, to ka sani har yanzu ina jin haushinka, har yanzu ban son ganinka, har yanzu na tsaneka, it doesnt change anything. taimakon ka kawai nayi, ko ba kai ba naga wani na neman taimakona na zan bashi, don na gaji taimako wurin Kakata, Islah me zanyi ki yafe min? Wallahi na kamu da sonki, ta tabe bakih tace shisa ake so idan mutum zaiyi abu ya dinga tunanin abunda zai faru Gaba, dubeka yanzu u look miserable, u left me Ya Amar, yace M here now, tace too late, ka koma gurin hanifar ka, yace haba Islah ya kike magana Haka? Kar ki manta hanifa matar wani ce, ba kyau, islah ta tabe bakih, tace ka manta soyayyarku? Har shan jinin juna kukayi saboda shaukin so, Amar yace kar ki maida hannun agogo baya, ni da hanifa mun zama history, Hanifa mace ce, ta dade da zubar da wannan digon jinin months ago gurin period dinta, nd u knw wat matters d most now? I hav ur blood running through my veins, shine abunda yafi muhimmanci gareni a yanzu. _Bibilicious B 5⃣5⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕DonAllah Islah ki bani wani chance, wallahi ba zakiyi nadama ba, We'll start afresh, we'll build our home, a new life here, saboda karatunki m willing na xauna a nan har sai kin kammala, i wont cut u off, jus gimme ds one chance, Islah ta kalleshi galala, tace ba ka da abun da zaka ce min, ta shige ciki tare da banko kofah. Ran Mu'ammar in yayi dubu ya baci, ya zaayi ya tsaya yarinya kamar Islah ta dinga wulakanta shi? Amma kuma be kamata ya ji haushi ba don laifi ya mata take hukuntashi, but Dole zai koma Naija cikin week dinnan, don ya san Tsoho kadai ne zai daidaita tsakaninsu, amma ta ya zaije ya samu tsoho da wannan zancen? Da wani ido zai kalli Tsoho? Ai ido da kunya, but InshaAllah zai kokarta ya je dai cikin satin nan. ****** Islah ina tunanin abunda kike ma Ya'amar is too much, wlh naga yayi nadama, har ya fara ban tausayi, kinsan wani bazai taking nonesense dinki ba, amma shi tunda ya san shine me laifi nd he wants to make it up for u, beyi fushi ba, amma shawara zan baki, ki haqura haka nan, ki zauna da mijinki ki manta da komai, Islah ta kalli qawarta zaineema, tacd Zainee what he did cant be forgiven dis soon, Zainee ta tabe bakih tace A dai bi a hankali kar garin jan Aji ajin ta tsinke, Islah tace haba dai ai wuce naaan... Kaduna Zaid da Maysah sukayi shirin dawowa Abuja, har bakin mota jawad ya rakosu, ya rungume Zaid ya na mai godia sosai, Zaid yace dont be silly bro, kar ka mun godian komai, Maysah tace Ya Jawad a kula min da kanwata, lalala matata ce kanwarki? Tace eh mana, na bata 11days, yace bawa ni tace ka tambayeta, ya maqe kafada kamar wani yaro ba wani, wayon yayi yawa, ya zaayi ku girmi miji kuma ku girmi mata?Zaid yayi daria, yace Kyaleshi kinji Ruma, shiga mota mu tafi kar muyi dare, ta shiga mota zaid ya ja motar suka bar haraban Asibitin, jawad na ta daga musu hannu har suka fice, shi kuma yayi hanyar Dakin da aka kwantar da Fadila. _Bayan kwana 10_ Amal ce ta shigo dakin da basket a hannu, Jawad yace su Mummy Bonbon sai a juya a koma gida don An sallame mu, tace barka, wato kaima sunan nan ya shiga bakinka koh? Yace ehmana tunda baby haka take ce miki nima haka zan dinga ce miki, fadila na jinsu bata tanka musu ba, Amal tayi daria tace, Toh zaman me kukeyi? Eh discharge letter zaa kawo mana sai muyi ta tafia. Tace ok, suna zaune sai ga nurse tazo, Jawad yace tasa wasu attendants suzo tayasu kai kaya mota. Wata nurse ta nurse ta shigo da wheelchair, Jawad yace wannan fah? Nurse din tace na patient ne, za ta hau a kaita mota, jawad ya zabga mata harara yace matata ba gurguwa bace, we dont need it, jawad ya nade hannun rigarsa ya sabi fadila sama kamar wata baby ko kunyan Amal be ji ba yayi waje da ita, ya na tafia yana cewa baby gida zamuje kinji? Ta murguda bakih tace ai naji komai ko mallam? Yace wai idan bakiji bane sai na qara fada miki. Ta turo bakih, ya duqa yayi kissing dinta, tace ya jawad wats dis? Nan ya dan karkata ya bude back seat, yace kar ki daina murguda min bakih ki gani. Ya kalli Amal dake ta musu daria yace Hajia muje koh?tace ina zan bi wadannan fightlovers din? Kar ka damu da mota nake zan bi bayanku? Yayi daria ya bude driver seat, yace kinsan kawar taki yar rigima ce, ya dan kalli Fadila ta ko galla mai harara, yayi daria ya shiga motar. ****** Tun bayan dawowansu gida, jawad Ke kula da matarsa, har Amal tace zata samo musu mai aiki Jawad yace kar ta damh, its his duty to take care of his wife, musamman aka bashi break a gurin aiki, sun ma kori Alhaji Haladu a aiki don ana Zarginsa da Murder Case, Jawad ya na kula da fadila, ita kuwa sai Shagwaba take zuba mai san ranta, shi kuma yayi ta lallabata yana biye mata, don jin ta yake kamar jinin cikin hantarsa, A zaman da sukayi a asibiti ne ta fahimci cewa Jawad na da saukin kai, da kuma barkwanci, uwa uba ga iya Soyayayh.Wani azababben sonsa ke shigarta, har tana jin Jawad cikin ranta. Maiduguri Tsoho ya kura ma kofar parlornsa ido yana so ya tabbatar da idonsa ba gizau yake mishi ba, Mu'ammad da ya kasa karasowa ciki saboda kunya ya zube guiwa bibbiyu yana hawaye, Shi din ne inji Tsoho, Amar ne, tsoho ya kauda kansa gefe, da rarrafe Mu'ammar ya qaraso cikin parlorn ya kama kafaffun tsoho duka yana neman gafararsa, Tsoho ka Yafe min, na tuba, lh na tuba, ba zan sake ba, kayi min rai, Tsoho na da saurin karaya, ga shi kuma yana son jikan sa sosai, nan da nan ya ji tausayin Mu'ammar, ya dagoshi ya rungume, Amar, ba ka kyauta min ba, Amar yayi saurin daga kai, na sani tsoho, shisa nake neman gafarar ka, Tsoho yace na yafe maka. Amma ka gaya min dalilinka na barin gida, Abunda Mu'ammar ya gaya ma Islah shi ya kara gaya ma Tsoho, tsoho ya jinjina kai, yace ba kyauta ba, in banda wauta irin taka nisa da gida zne zai sa ka manta soyayyar wata kuma ka kuma fara soyayyar wata?yanzu kana sonta ita islahr?da sauri Amar yace fiye da komai tsoho, kuma gashi kafin dawowarka na tura ta karatu, Mu'ammar yace karatu har ina? Tsoho yace kusa daku chan Ingila, muammar ya jinjina kai, sam be nuna ma tsoho ya ga Islah ba ko ya san inda take ba. Tsoho yace ka tashi kaje, zanyi shawara. Mu'ammar ya mike ya rungume tsoho yace Nagode. Ya fita, sai da yaje dakin Hajia Ama da duk sassan dakinta ya gaidasu duk suna mamakin dawowarsa da kuma sauyi da yayi na zuwa gaishe su, kafin ya shiga Sassan Umma hajja da Sassan dakinta duka ya gaishesu, suma dai mamakin Shi sukeyi. Sassan su ya nufa wato sassan hajia Babba, ba ta nan taje sunan jikar wata kawarta, A kofar parlor yayi Sallama tare da kutsawa ciki, Hanifa ce zaune kan carpet da alamun ta ji sauki kafar ta warke, da sauri ta kalli wanda ya shigo tace Yaya Mu'ammar? Murmushi ya mata a yanxu banda so na yanuwantaka, ba wani son da yake mata, ita ma din haka don ta maye gurbinsa da Zayyad, tace sannun da zuwa, yauwa Hanifa, ina mutan gidan? Wallahi sunje suna, me ya sameki a kafa? Tayi murmushi tace wlh turgudewa nayi na dan goce anma naji sauqi sosai, Allah sarki ina maigidan naki? Tace yanzu ya fita, Bilkisu ce da Suraj sukayi Sallama, Ganin Mu'ammar tsaye yasata qarasawa da gudu, oyoyo ya'amar, mu'ammar ya dagata sama yana juyawa, oyoyo lil sis i missed u, me more bro, Mu'ammar ya ajiye Bilkisu ya miqa ma Suraj hannu don suyi musabaha, suraj yayi kicinkicin da fuska, bilkisu ta mishi Alama da ido, haka dai ya daure ya bashi hannu, suja gaisa, be yarda Mu'ammar yaja shi da fira ba ya fita waje don har yanzu yana jin haushin abunda ya ma qanwarsa. Kafin kace kwabo magana ta zagaya Gidan Gandu Mu'ammar ya dawo. Da labari ya iske hajia babba a gidan suna dole ta musu sallama ta dauko hanya don ganin Jikanta.. Abuja Sir, Senior Consultant na neman wa yanda suka gama housemanship, sakon da ya iske Zayd kenan a office dinshi Yace okay, gashi nan xuwa, ya miqe Ya nufi Conference room na meeting din Doctors, Senior Consultant na nan tsaye ya na Congratulating dinsu akan gama programme dinsu da sukayi for almost a year, zai gaisa dakai sai ka fada mishi sunanka, da aka zo kan Zaid, ya bashi hannu suka gaisa, yace i am Dr Zailani, Mutumin ya kura ma zaid ido, yana son tunano sunan, yace Dr Zailani as in Dr Zaid Zailani? Xaid ya yi murmushi yana mamakin yanda akayi ya san sunanshi Zaid, don duk asivitin dr Zailani ake kiranshi dashi, yace yes sir, Dr james yace are u married? Zaid yace yes sir, Dr yace after dis, meet me in my office, Zaid tace ok sir. ****** Zaid zaune gaban Desk din Dr James, Dr James yace Dr Zailani, ina so muyi wata magana dakai, but m not sure dai, but before dat whats d name of ur wife? Ba tarw da Zaid ya kawo komai a ransa ba yace Rumaisah Abubakr Zailani, dr james yace ohh, daman nace m not sure, sorey for d diaturbance u can go, Zaid yace no problem sir, but why dd u ask? Dr James yace 2weeks back akwai wata da tazo private hospital dina da daddare bearing d name Badiyya Zaid Zailani, Gaban zaid ya yanke ya fadi, i am familiar wth hausa names but bantaba jin irin sunayenta ba, dy are unique, shisa da kamin introducing kanka as Dr Zailani i tot she's uo wife or ur sister. Zaid da zufa ya shiga tsatsafo mai yace Dr, Me ya sameta? Was she sick? Dr ya tabe bakih, yace d girl is too arrogant she dint listen to me wen i was advicing her about HIV and AIDS, Zaid ya xaro idanuwanshi baki na rawa yace is she?? Dr James yace Yes She's HIV positive. Luuuu Zaid ya fadi sumamme. Gidan Gandu 5⃣6⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Da sauri Dr James ya tari gaban Zaid, ganin idanuwansa bude ya sashi zaton ko mutuwa yayi, ya dagoshi yaga jikinsa da nauyi, ajiyar zuciya ya dake da ya lura akwai rai jikin Xaid, sai a sannan ya lura ashe ba suma xaid yayi ba daskarewa yayi lol, fiffita ya shiga yi ma Zaid, hawaye kawai ke sunturi a idon Xayd, nan Dr ya fara zargin wani abu, ko dai badiyyar matarshi ko yaruwarsa? Ya dan kalleshi a sanyayye yace Zailani let me get u help, Dr na fita, Zaid ya sulale ya bar office din Dr James, yana hada hanya yana tangartangar kamar xai fadi ya nufi motarsa, ya ma rasa tunannin da xaiyi, ya fincika motarsa sai gida, a hanya Zaid ya sha kwalbar giya ta kai hudu, irin gudun da zaid ke shararawa ya wuce misali, fuskar shi bacin raine zallah, Allah kadai ya kawo Zaid gida lafia, be ma iya jiran megadi ya bude mai gate ba ya fito ya shige, tun daga Gate Zaid yake kwalla ma Diyya kira har ya shigo parlo, Badiyyan da yanzu tayi baqih ta rame ta ji kiran xaid agogonta ta kalla ko 1 beyi ba, lafia toh ya dawo gida yanzu? Ta miqe tazo parlo, da karfin hali tace swthrt ka dawo, tayi Yunqurin Rungumeshi, Fayau ya taske ta mari, ya qara marinta, cikin ihu tace Zaid me na maka ka tsaneni haka? Cike da takaici yace me kika man? Har kina da bakin tambayan me kika min? Ya shiga kwallo da ita ta na kuka, duka ko ta ina yake mata, da hannunsa da kafar sa, harda su nushi. Tunda tayi parking tasan cewa gidan nan babu lafiya, da sauri ta ftp tayi cikin gida, da gudu ta qarasa ta riqo Zaid, Haba Yazayd, kayi haquri, xaid ya daddage ya ture Maysah iya kar karfinshi ta fadi kasa rajagab, ya cigaba da cin uban badiyya ta kwala ihu. Maysah bata daddara ba ta miqe ta qara nufoshi tana jan hannunshi, yana juyowa ya kamtse ta da marih, ya ja hannunta ya wurgata dakinshi, yace stay outta dis, ya dawo yana cire belt din jikinsa ko a haka ya bar badiyya ta ci duka, Zaid ya shiga laftar badiyya, a yanxu kasa kukan tayi, cikin tsawa yace ni kika cuta badiyya?ni kika shafa ma HIVand AIDS? Da sauri Badiyya ta dagi ta kalleshi, yanzu ta gane dalilin dukar nan, tana mamaki ya akayi Xaid ya gane, tayi karfin halin cewa Myzayd, kayi haquri pls, we can spend d rest of our lives together, Dr yace if we can abide by d rules we are safe, Zaid pls forgive me, we can live long, Akwai hanyar da zamu morewa rayuwa nd even have kids of our own, Ya zabga mata belt a gadon baya, ta saki ihu, Allah ya sawwaqe na, ke ki haifa man yara? Allah ya kiyaye Mazinaciya ta haifa min yaro, ni ba dan iska ba, ban taba Zina ba, Diyya tayi wani murmushi tace yes kai ba mazinaci bane, Amma kai mashayi ne a wurin Allah daya muke, so gwara ka sakko mu rufa wa juna asiri aikin gama ya gama, yau ko sai kin san kin auri mashayi dan giya wani nushin da Zayd ya ma Badiyya a baki sai da bakin ya fashe hancin ya fara habo, ya yarda belt din ya hau ruwan cikinta na SAKEKI, BADIYYA SAKI 3 sai dai kanjamau ya kashe ni da na cigaba da zama dake, ya dinga jibgarta yana nusarta ba sassauta wa,. Rumaisah ta fito da gudu fuskarta yayi jaaa, idonta cike da hawaye, ta gama jin komai, kuma idan ta bar Yazayd zai iya Badiyya, Iya karfinta ta tattaro Zaid jikinta, da qyar ta iya turashi daki ta kulle, ke zabin tsoho zo ki budeni kafin na hada dake, kizo ki budeni, Maysah ta ki kulashi, tazo gurin da Badiyya ke kwance ta na nishi sama sama, tace Aunty Badiyya Kiyi kokarin tashi na kaiki Asibiti, Badiyya ta girgiza kai na, tace pls Maysah ki yafe min,

Chapter 16 of 20