Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yake mata gaskia ne, ita kuma ta aminta da zuwa yanzu ta kamu da sonshi, Toh meyasa ba xata yafe mishi dab qaramin laifin da ya mata ba? Ta rungumi mijinta wanda take ma Zazzafan So ba tare da saninta ba? Toh dai lokaci yayi da bygones will be bygones, zata rungumi mijinta zabin Allah a gareta, fatan ta Allah ya kara Hada kansu, ta tashi ta bude kofar ta ta fita, karfe 12 da rabi, ta san Yasuraj ya dade gurin aiki, da ya kan dawo cin Abinci, amma tun bayan abin da ya faru ya daina dawowa, don ya san ko ya dawo ba zai ganta ba saboda kulle qofarta da tayi, shikuma be son ya takura mata, ya fi so ta sauko don kanta. Bilkisu ta shiga kichin ta hada abincinta mai rai da lafiya, ta dawo ta ta sake wanka ta yi kwalliya ta dawo parlo ta kunna tv, binibini sai ta kalli agogo. Kamar daga sama sai gashi ya dawo daukan wasu files da yake da buqatansu a gurin aiki emeegency, yayi mamakin ganinta zaune a parlor, suna hada ido ta kauda kanta, Tace Sannu da Zuwa, murmushi Yayi zuciyarshi cike da jin dadi yace Yauwa Billy nah, erhm daman na yi mantuwa ne, bari nashiga na dauko, be jira amsarta ba ya shiga daki dauko files din, sai gashi ya fito, Billy bari na tafi sai na dawo, ta dago kai ta kalleshi, tare da marairaicewa tace ga fa abincinka nan fa? Wani dadi ya mamaye zuciyar Suraj, yace tohm sakko min dashi nan, ta miqe a yangace ta nufa dinning din ta kwaso kayan ta zo ta zube gabanshi, ta shiga zuba mishi fried spagetti da vegies sauce, ta tsiyaya mai lemu a cup, ta miqe zata tafi yayi saurin riqo hannunta, ta zuba mai idanuwanta, ya ce sorry i cant eat alone, ta ce sorry m not hungry, yace ai baki isa ba, ya zaunar da ita kasa kusa dashi, yace cikin ki beyi kama da wanda yaci abinci ba, bata sonyi mai musu sai tyi shiru, haka ya dinga ci ya na bata a bakih, tun tana kunya har ta daina ta xage tana ci, sai da suka ci plate 2suka sha lemunsu ta tashi ta kwashe kayan, binta yayi kicin, ya rungumota yace Billy m so sorry for-ta katse shi ta hanyar sa yatsunta biyu kan bakinshi tace yaya, let bygones be bygones, lets forget d last nd focus on d future, ya ji dadi sosai, yace Billy please let me teach u how to love me, tace no need, coz i already love u, Ohmy God, i love u so much Billy, nd u wont regret loving me, Dagata sama yayi kamar baby ya nufa dakinsa da ita, zuciyarta ta shiga dukan 3 uku, a tsorace tace Yaya, files dinka, yace shhh forget d files i dont need dem again. Abuja Zaid din ya tafi aiki kuma kinsan be dawowa Sai 3 nd dis is just 1, kuma kinsan ki yana nan he cant do anything, he's under my control, so muje na fanshe bakin cikin da wannan shegiyar Amirar ta kunsa min jiya kan Rumaisah, Badiyya ce ke maganar nan, Mamar tace wlh Tunda nake ba a taba min cin fuska irin na jiya ba, na tsorata da yarinyan nan, da qyar in ba ta aiki da mutanen boye, amma tunda Annobar ta tafi muje mu ci uban Rumaisahn, Suka fita da ga dakin suka nufa na Maysah, tana kwance tana barci sbd yau ba lectures, Jin wayar redio tayi a jikinta, da sauri ta miqe tana salati, ganin Badiyya da mamanta tsaye ko wannensu riqe da Wayar redio, hantar cikinta suka kada, Muryar badiyya taji yau ina me cetonki? Tace me namuku Aunty? Tambaya kike? Suka shiga lafta mata a jiki, ta saki ihu tana kuka, dukkanta suke kamar Allah ya aiko su, abunku da mutun fari tuni suka farfasa mata jiki, hakan be sa sun daina ba, illah qara tsaula mata da sukeyi, Da qarfii sukaji ance Badiyyyyaaa, chak suka tsaya, suka waiga don tavbatar da abun da kunnensu ya jiye musu, Zaid ne tsaye bakin kofa, idanuwansa sun rikide sun koma jaaa, Gaban badiyya ya fadi, bata taba ganin fushi kwance a idon zayd kamar yau ba, ta tsorata da yanayinshi, a hankali ya tako har inda Maysah ke kwance ta na kuka, ya dagota, ya share mata hawaye tare da girgiza mata kai, alamun tayi shiru, hannunta ya riqe gam ya yi gaba tana biye dashi a baya suka bar dakin.. Fans me kuke ganin zayd zai ma badiyya da uwarta? 4⃣9⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Har chan dakin shi ya jata, Ya zaunar da ita kan gado, ya tsura ma jikinta ido inda ya farfashe, ya bude kit dinshi na magunguna ya dauko wasu pain killers , ya bude firij ya dauko ruwa, ya ballo magaganu yace bude bakinki ba gardama ta bude ya samata ya kwarara ruwa ta hadiye, ido ya tsura mata, maqale ya ga hawayen idanuwanta na xuba, ya sa hannu ya share mata fuska, sannu kinji?ki kwantar da hankalin ki, i wont let anyone hurt u again kinji? Mamakin shi takeyi ta kasa magana, Miqewa yayi ya ja kafarta ya daura kan gado, yace sleep kinji? Ki huta, ba gardama ta rufe idonta, Zama yayi ya tsura mata ido ya shiga tunanin abun da ya faru a office. Misalin karfe 11 na ranan Yau Xaune yake yana diba wasu patients, yaji kanshi ya mai nauyi kamar zai rabe biyu, xafi sosai, sai da yayi excusing kanshi yaje common room da kyar, kan ya kai kusan minti 30 yana ciwo, kafin ya ji ciwon kan ya dauke dif, daidai nan ya shiga tariyo abubuwan da suka wakana tsakaninshi da badiyya tun yana london haduwarsu da komai, har zuwa yau, kanshi ya dafe ya na maimaita Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Wacece Na aura? Badiyya? Karuwa? Allah na kasance Mashayi amma ban taba aikata Zina ba, Allah na tuba, meyasa na Auri Mazinaciyya? Me ya kaini har na kaiga auren badiyya? Na yi wa Tsohona gardaman, na ruguza mai Akidarsa, Na mai rashin kunya, na juya wa Zabinsa baya, Oh Allah, Tsanar Badiyya ce danqare a zuciyarsa, tuna abunda ya faru tsakanin matar Sam da uwar Badiyya ya shiga dawo mai jiya, Yau kam sai mamar badiyya ta bar mai gida, ita kuwa bazai kara barin ta tafi ta ko nan da kofa ba balle taje tayi akuyancinta ta kwaso cuta ta shafa mai shikuma ya shafa ma baiwar Allah Maysah. Da sauri ya fito daga common room ya isa parking lot, ya finciki motarsa yayi gida, kansa dauke da tunani kala kala, isowarsa gida ya ga irin Dukkan da suka yi ma Maysah nan ya qara jin tsanar su dole xai yi maganin su tunda har suka taba Zabin tsohonsu.. Tie din wuyarshi ya fincike, ya bude firij ya dauko kwalbar giyar R2A, ya bude, Maysahn da take lura dashi tayi sauri miqewa tare da riqe mai Hannu tana cewa donAllah yazayd kar ka sha, wani kallon da ya mata ya sata yin lakwas, bata taba ganin yanayinshi a haka ba, Yace kwanta kar kuma ki sake ki fito, haka ta koma ta kwanta, tare da runtse ido, ya daga kwalbar giyar nan ya kwankwadi kayanshi, chan ya fara jinshi a sarararin samaniya, wani murmushi ya sake tare da bude er jakkar laptop dinshi, Chargern laptop din ya dauka ya na hada hanya ya fita daga dakin, dakinsu badiyya ya banka, a tsorace suka dago, dama ynx ta gama shafa turaren nan zataje dakinshi, turaren ya daki hancin zayd, wani irin wari yaji, kanshi ya sara, ya Nufosu kamar Zakihn da ya kwana 2be ci abinci ba, Badiyya ta tsorata, idon zayd a halin yanzu cike yake da fushi, rashin imani, da rashin tausayi, bata gama tunaninba sai jin wani abu me kauri tayi a bayanta, ta gantsare baya kafin ta sake ihu, mamar na cewa hava zayd matark- jin nata a baya ne ya hanata karashe zance da takeyi, ya shiga laftarsu da chargen laptop din kamar Allah ya aikosu, sai da ya dukkan kawo wuqa, sai da ya ga sun rungume juna a qasa sun ma kasa kuka sbd azaba, sai da ya gaji don kanshi kafin ya daina dukkansu, cikin yanayi na maye ya kalli uwar badiyya yace na baki 10mins ki bar min gidana, ke kuma, ba inda zaki, ya hada hanya ya fice dakin ya koma dakinsa ya zube kan Maysah ya fara bacci, da qyar ta janye jikinta daga gareshi tana kuka, cire mai Takalma da socks tayi, ta gyara mai kwanciyar shi, ta koma Gefe tana kallon Zayd, Ya Allah ka shirya Yaya Zaid. ENGLAND Asad ya shigo dakin bayan sub mai izinin shigowa, heyy dear, zainee tace hey, Ya kalli Islah yace hello princess, murmushi kawai ta mai, yace hop u guys are prepared for today's Awards? Zaineema tace i wanna come but Islah said we're not coming, so we are not comin. Asas ya marairaice fuska ya matsi kusa da islah ya zauna, yace d time u told me u'r not interested in me, i was so hurt, i felt so bad, nd since den i never talked to u about it, coz i respect ur feelings, i trust u not to hurt my feelings, if u dont want to see me hurt please come, ur presence is needed, yana kaiwa nan ya miqe ya fice daga dakin, Zaineema ta dawo kusa da Islah tare da riqe mata hannu. Islahulkhair meyasa kike haka ne wai? Wannan taron na kasar ce baki daya fa? Duka Universities din ENGLAND ne, kuma anan xaayi balle kice ba kyason tafia me nisa, kar ki manta an gayyaci manyan Celebrities gun taron nan, tun last month ake ta maganar EnglandHighschoolsAwards, Asad na da kirki, tunda har ya kaiga roqon mu muje ai sai muje ko, kuma na san ya riga da ya siyan mana tickets, kuma da tsada, kar yayi asara pls, just dis one time please, ta kalleta tace fine, zamuje shikenan? Yauwa my frnd. Bari na kira Asad na sanar dashi. Kudai kuka sani ***** 7pm Islahulkhair ta shirya cikin wata doguwar riga milk colour me touches din cofee brown, ta daura dankwalinta brown color, tayi matuqar kyau don har kwalliya zaineema ta mata da qyar, sunyi kyau kamar mene, takalma me tsini ta sa suna jiran Zuwan Asad, Sai ko gashi yashigo da Sallama, sandarewa yayi ganin islah, don ta mai kyau, Zainee tace Asad? Yayi saurin dauje kai, islah tace give me that look again nd i promise u m not coming, ya ce sorry, shall we? Yayi gaba suka bi bayanshi. suka isa gurin taron, Wurin qato ne, an hallara, wasu daga cikin Manya manyan celevrities wanda ake ji da su a duniya sun hallara, Makarantun Jamio'in kasar England sun hallara. Har an fara gudanar da Awards din, yanda abun yake za a kira Celebrity ta fito ta fadi category din award din, da sunan makarantar da za'a ba da kuma wanda ya chanchanci award din, sai ka tashi kaje ka amshi kyautarka. Haka aka tayi, Su Islah sun duqufa wurin kallo, da an kira sai su taba, amma zuwa yanzu ba su ji ankira makarantarsu ba, Islah ta gaji don anyi nisa da yawa, tace Zainee kin ga har 10 yayi, kice mai yazo ya kaimu gida, Zainee tace pls bari 10:30 yayi. Ji sukayi ance, "Ladies and Gentlemen, to present this award for d category of MOST UNIQUE, Please welcome Justin Bieber nd Nicki Minaj, Rafraf wuri ya hau tafi da ihu, Islah ma ta gyara zama, yau gata ga best artiste dinta JB, JB da Nicki minja suka hau kan stage suna daga ma mutane hannu, Nicki minaj ce ta fara dan surutai kafin JB yace tonyt its not about us, tonyt its about d "Most Unique" d Award for the "Most Unique" goes too.. suka hada bakih shida Nicki Minaj Sukace From CAMBRIDGE ENGLAND, ISLAHULKHAIR ZAILANI, Ihuuu yan CE suka sa don sunsa wacece Islah indeed shes unique, Ihu Zaineema takeyi har da miqewa tsaye, ta kalli Islah da ke zaune ta rafka uban tagumi da alamu bata san wainar da ake tonawa ba, zaineema ta zungureta, tace bakya jine? Islah tace meye? Nan JB ya qara maimaitawa, Islah Ta bude bakih tace what? Zainee ta gyada kai tace go get it, Islah ta kalli Asad ta san aikin shi ne wannan, jiki ba qwarih ta miqe kamar zata fadi qasah tana tafia, idanuwa aka zuba mata ana binta da tafih, har ta zo kan steps din dake gaban hall din, Justin bieber ya sauko daga kan stairs din ya miqa ma Islah hannu, bata san lokacin da ta sake murmushi ta miqa mishi nata hannun ba ya taimaka mata ya hauda it kan matakalar benen da be wuce 10 ba, Nicki minaj ta rungume Islah tare da bata Award dinta, shima JB din rungumetan yayi tare da janta gun Microphone don ta bada speech. ***** Zaune yake yana shan cofee, ya dinga chanza channel din Tv har ya tsaya kan Channel EE, da alamu awards ake, shi ya zata films Awards ne shisa ya bari, sai da ga baya ya fahinci ashe EHSA akeyi, tsaki yayi ya ce shirme, yazo chanzawa kenan yaji muryan nicki da jb suna kiran Islah, kamar zai chanza sai dai ya tsaya yana kallo ya ga wacece wannan islah, ganin an haskota tana tafia a yangance, gabanshi ya yanke ya fadi, zuciyarshi ya shiga dukkan 3uku, ba abun da ya fi daga mai hankalin irin yadda ya ga JB ya riqo hannunta har da rungumeta. Kanshi na fitarda tiririn Zafih. Ba zato ba tsammani sai gani hawaye yayi a idonsa, a hankali ya ke tambayan kansa shin mafarki nakeyi!!? Nikuma biebee nace kai kuma a suwa danwake a hotel? Wanene wannan Jamaa? Gidan Gandu 5⃣0⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Tagumi yay hannu bibiyu yana kallon ta Tunani kala kala, haka ya cigaba da kallan ikonAllah cikin bacin rai, Islah ta fara Speech dinta kamar haka "OMG! Standing beside NickiMinaj and Justin bieber is like a dream come true, i never in my widest dream thought of seeing them dis close to me, too many people to thank, Thank U Asad for everything, thanks roomie Zaineema, ily, nd dis Award is for all the Nigerian people studying in Cambridge University, M only their representative, Coz we all are Unique, Naija no dy carry last " Raf raf gurin ya kaure da tafii, ta sake rungume Nicki minaj ynx dai ba ta rungume JB ba, suka matsa gefe tare da kangawa aka dauke su hotuna, a yangancen ta koma mazaunninta, Zaineema ta rungumeta cikin murna, har a ka cigaba daga inda aka dasa. ****** Ajiyar zuciya ya sauke me karfi, tunanin Me takeyi a Cambridge? Its obvious mana, Karatu takeyi, amma ya akayi tsoho ya barta ta zo karatu nan? Don ya san tsoho be barin mata fita waje karatu balle kuma ita da aurenta? Wata zuciyar tace Kasan ko an raba auren? Damm gabanshi ya fadi, da sauri ya ba zuciyarshi amsa, ba a raba, tsoho be raba aure, ya koma ya zauna, amma duk yadda yake tunanin be damu ba karya yake, hankalin shi ya gaza kwanciya, da sauri ya shiga dakin baccinsa ya bude case din shi cinki rashin kwanciyar hankali yake neman MTN sim dinsa, sim din da tunda yazo qasar be sake waiwayanshi ba, ya dauko hannu na rawa ya sa, Contact ya shiga, ya dinga bin lambobin wayansa da ido daya bayan daya, wa zai kira? Wa ya isa ya tunkara da maganar Islah, wani kunyan abun da yayi ya mamaye shi, number bilkisu yayi dialling a dayar wayan, unfortunately wayan kashe take, kamar yayi kuka, da sauri yace bari na kira Samir, ba zai rasa masaniya ba, ai numbern Samir be ma shiga don be ma qasar, ai be isa ya kira suraj ba don kunya. Haka ya dinga bin number en gidan nan duk ba sa shiga, ihu ya sake da qarfi, yanda ya ga dare haka ya ga rana.. Sai wurin asuba bacci ya kwashe shi.. Kaduna Karfe 8 na Safe ta fito daga dakinta sakamakon kwankwasawar da taji ana mata a kofa, ta fito, direban Jawad ta gani, suka dan gaisa, yace kin shirya koh? Cikin mamaki tace na shirya ina? Yallabai yanzun nan da xaifita yce min na kaiki KASU zaku zana post ume, Kambu fadila tace a ranta, wai me mutumin nan ke nufi da ita ne? Gidan ya kwana, ta tuna wurin 11 sunyi clashing a kichin, amma ya iya furta mata ta shirya zataje post ume ne yake ganin asara? Shine zai aiko mata da me gadi? Haka ya mata na zuwa Maiduguri to lallai ya kaita bango, ba za ta yarda da irin haka ba, ganin idan taqi zuwa PostUme din ta ma kanta ne, daman yadda take son karatu, idan ta ce ba zataje ba karatun ya tafi kenan, sai dai ta daure, tace haka ake zuwa musu post ume din? Yace ai ke credentials dinki kawai xaki dauko, sauran abun buqata yanzu ya miqo minsu a file. Mamaki take yaushe YaJawad ya fara mata processing Makaranta? Chan kuma tayi tsaki, koma meye yau sai an yi ta ta qareh, bata son aiken da yake mata. Lagos Mai makon kafa ta warke sai kafa ta kunbure, hanifa taci kuka har ta gaji, da ita da Yazayyad din ba wanda yayi tunanin goce wane, sunyi zaton normal turgude wa ne, haka aka kwana aka yini, Zayyad ko nan da kofar gida ya qi zuwa, ji yake kamar ya dawo da ciwon kafar jikinshi, shi ke mata komai, ya yi abinci ya dauketa ya kaita toilet, ya jirata ya fiddota, Hanifa cikin ranta tace Yana da Kirki, ya dinga shafar mata kai har bacci ya kwasheta, a haka Tsoho ya kira Wayar Zayyad, Ringing daya, ya dauka da sallama, Allah ya ja da ran tsohon mu, Mallam Zayyad, dadi mata ya sa ka shareni na kwana daya, ko ka kira kani ya muka tashi yau? Zayyad ya dan marairaice, Allah ba tsoho haquri, Matarka ce bata lafia, Dadi yaji har ransa, tunda yake kiran jikokinsa wannan ne karo na farko da suka maida mai magana me dadi, a ranshi yace Allah ya sa ciki ne, amma a zahiri sai cewa yayi SubhanAllah, me ya sameta? Wlh jiya ne ta turgude kafa, yau kuma kafar ta kunbure sunntum, SubhanAllah, Ince ka kaita an dubata? Zayyad yace aa tsoho, ina dai shafa mata magani, amma ynz da na kusanto kafar, ta dinga ihu kenan, tsoho cikin damuwa yace Zayyadu ta goce ne, ka kawo min ita yau a diba kafar nan, kafar tayi tsami, cikin damuwa Zayyad yace an gama tsoho, bari naje na ga idan zan samu tickets, yauwa Allah ya sawwaqe, ganin har yanzu bacci takeyi ya sa shi fita siyan tickets kafin ta farka.. Kano Fitowa sukayi hannun su maqale da juna gwanin ban sha'awa, Kallo daya zaka musu kasan masoya ne masu tsannanin son junansu, sai da ta rako shi gaban mota kafin ta bashi brief case dinshi, tace Allah ya kare min kai Ya suraj, Allah ya bada saa, sosai yaji dadin adduarta ya janyota ya rungume, yace Amin Billy nah, sai da ya bata hot kiss kafin ya ja motarsa ya wuce, ta bi bayanshi da so da kauna, ta koma ciki cike da jindadi.ji tayi wayarta na qara kan dining, da sauri ta qarasa don tunanin ta Ya suraj ne, ko yayi mantuwa, gani number +44 ya tabbatar mata da Islah ce, ta dauka, hello, sabanin Islah taji, ji tayi yace Hello Chuss, Duniya shi kadai ke ce mata chuss, da murna tace Ya'Ammar? Kaine? Kana London ne? Are u ok? Ya Mu'ammar? Dan guntun tsaki yayi yace zan amsa miki tambayoyinki but before den, An raba aure na da Islahulkhair? Tmbyr ta zo mata a bazata, amma taji muryar shi like he's serious, tace aa yaya ba a raba, yace na ganta nan England, ya akayi haka? Ta kwashe komai ta gaya mai, kunya yaji matuqa, yaya gaskia baka kyauta ba, ya marairaice yace U knw u are my only sister u ar d only one dat can help ur bro, pls ina son details din inda take zaune like now, tace now dai? Yace do dis for me pls, tace ok Yaya bari ma duba dakin Yasuraj nagani, don naga wani files me dauke da sunanta, idan babu zan kirata na mata siyasa har sai ta fada mun, yauwa darling sis, remember noone must find out, ko ita, tace kar ka damu yaya, bani minutes i will get back to u. Ta shiga da sauri ta dubo file din, kamar yadda take tsammani hakan yake, duk wasu important informations kan Islah a Cambridge ta samu, harta numbern Room mate dinta akwai a takardun, da sauri ta mai texting, tnx kawai ya mata replying. Cambridge England Karfe 9 ya mishi a Cambridge, don bala'e train ya biyo daga london zuwa Cambridge tafian kusan 1hr 30mins, be sha wahala ba gurin gani dakin su Islah, kasancewar yau Saturday, ya fi minti 10 gaban dakin, gabanshi na dukan 3uku, ta ina xai fara? Sai ynz yake tmbyr kanshi me zai ce mata? Sai da yayi shahada kafin ya kwankwasa kofar, zuwa tayi ta bude qofa, sanye take da dan nytgown, Goodmorning? Zaineema ta amsa cike da faraa, how can i help u? Errhm m looking for Islahulkhair, i hop i dint missed d room, ta fadada murmushinta tace and u are??? Oh m Mu'ammar m her--- ya rasa me zaice, uo her wat ta katse shi? Da sauri yace brother, zaineema tace dagaske? Mamaki yayi ta iya hausa yace dagaske kuwa, tace bismillah, ya shigo ya zauna kan kujera, tace ya gida ya su Tsoho da ya suraj? Yayi dariaa, duk kin sansu kenan? Tace eh kaine ba sani ba gaskia, ko da yake Kasan Gidan naku GIDAN GANDU ne sai hada da paper nd biro. Yayi dai yaqeh, so yake ya tmby islah, zainee tace ohh ta dan fita m sure batayi nisa ba, ynz za ta dawo don ko break ba muyi ba, yace ok, fira Zaineema ta ke janshi da amma be jin komai, binta kawai yake da Eh ko Aa, jin an kwankwasa kofar ya sa zaineema cewa that must be her, Mu'ammar yace Wait pls, ta tsaya yace i will get d door, bari na bude mata, tace sure, Mu'ammar ya nufa kofar gabansa na faduwa ya bude, sandare wa sukayi gabaki daya da suka hada ido, suka tsaya kallon kallo, mamaki fal a ransu, shi tunanin chanzawanta yake, ita kuma mamakin ganinshi take, rabawa tayi ta gefe ta shige ciki ta barshi bakin kofa tsaye, Zaineema kinsan ynz su Freya suke cewa wai sai sun hada party, partyn mene? Tace wai partyn kawo "Most Unique" Cambridge, Zainee tayi daria tace dolee ne ai, erhm ba wannan ba, bakiga bakon ki bane? Islah ta bata rai baqo wani irin baqo kuma? Tace ke da er iska ce, baki ga YaMu'ammar tsaye ba? Ta dan kalleshi a wulaqance tace waye haka nan? Au wannan? Gaskia ban sanshi ba, zaineema tace ke ni fa bansan haka, yaxo ya na nemanki, yace shi yayanki ne kuma wlh yana kama da Yasuraj, Islah cikin fada tace Zaineema whats ur problem? Ko wani jakkin tom dick nd harry yazo ya ce miki shi danuwa nane sai ki yarda? Kin fin sanin yanuwa na ne? Toh ki fitar dashi tunda ke ki ka shigo dashi don ni ban taba ganin irin me hallitarshi ba... 5⃣1🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 ⃣ Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Zaineema ta kalli, ba wani alamun wasa a fuksar Islah don tsakaninta daAllah take ita ba ta sanshi ba, Mu'ammar da yayi tsaye ya na sauraron zancen Islah, ya kasa cewa komai, jin muryan Zaineema yayi tana cewa Mallam danAllah ka tafi, tace ba ta sanka ba, Mu'ammar ya marairaice yace wlh ta sanni, ni yayanta ne, fushi takeyi dani, amma zanso ta saurareni ta ji me xance mata, zainee tace danAmlah mallam ka fita, zaiyi magana kuma sai ya fasa, ya juya ya fita, Islah ta bi bayanshi da kallo kafin ta buga tsaki da karfi, ranta a bace, tambayoyi Zaineema ke san yi mata amma sai ta share. Bawan Allah ashe ba tafiya yayi ba, yana nan zaune kan wasu kujeru da ke nesa da dakin ya yi tagumi hannu bibbiyu, tunani yake yi ga hawaye maqale a idonsa, yana kallon mutane. Karfe 3 agogonsa yace, awan sa 5 zaune kan kujerar nan yana neman mafita, gani yayi sun bude kofar dakin sun fito tare, sanye suke da jallabiya da mayafansu, da alamu unguwa xasu, ba ta da wata damuwa, haka suka dinga tafia wasu na daga ma Islah hannu itama tana mayar musu da martani, a ransa yace shes popular, miqewa yayi da sauri ya je ya sha gabanta, tamau ta murtuke fuska, yace Islahulkhair hear me out please, ki saurareni kina wulaqantani, hararshi tayi ta ja hannun Zaineema suka wuce da sassarfa ya bita ta re da riqo hannunta, ta na juyi wa ta kamtse shi da mari, Dont u touch me, ka kyaleni koh? Nace ban sanka ba, leave me alone koh? Dalibai suka juyo suna kallon su, duk aka xagayesu, rai a bace yace Ni Islah kika mara? Tace ka sake yunqurin tabani sai na maka wanda ya fi wannan, rai a bace yace amma kin iya ba qaton arne jikin ki ya rungumeki koh? Don ni mijinki na taba hannunki ki ka mareni? Ta fara kuka, tace ka damu ne? Meye dameka? Da ni da banza daya muke a gunka, banda wata amfani, ka ha'inceni da ka barni cikin tagamemen gida har wata 6 don kawai ba ka sona, sauran yanuwan mu da suka zauna da zabin da aka musu gaya min mutum daya da ke son daya, ai tun da Ya jawad ya yarda ya zauna da fadila su da basa shiri ko kadan, ina ga zaka iya zama dani ni da ko kallon banza be taba hada mu ba, amma kai sbd tsanar tayi yawa ba ka iya kwana dani rumfa daya, sbd tsana ni kadai har wataAi ina ga ko kwance ka ganni da kato ba abinda ya dameka? Ba ka damu dani da ba, kuma kar ka damu dani yanzu ba, ka rabu dani kawai nayi rayuwata, ta na kaiwa nan ta koma daki da gudu ya bita da kallo, yana hawaye kwata kwata yasan be kyauta mata ba, zai bita zaineema ta dakatar dashi tace let her be, itama ta wuce Mu'ammar ya juya ya nushi iska cikin haushi, sai a sannnan ya lura da turawan da sukayi dandazo a gurin suna kallonsu amma ba su fahimci ko me suke cewa ba.. Abuja Ruma, Ruma, kiran da taji Yaxayd na kwala mata, ta fito da sauri murmushi dauke kan fuskarta, yace yau nake gama housemanship dina, Allah ya sa bakya da lectures ki rakani asibiti, dadi taji ya ziyarce zuciarta, yo ko tana da lectures

Chapter 14 of 20