Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dukkan tsiya be yi ba, ya daga hannu zai mareta, tayi saurin cewa babban balaeen chan, wlh tlh ka tabani sai na rama, sai munyi duke duke koni ko kai cikin gidan nan(jimun ikon Allah sai kace wata me qarfi), Jawad ya fara zare belt din jikinshi zai ma fadila duka, da sauri Maysah ta fito, bata zaci abun yayi zafi haka ba, Ta janyeta daga gaban Jawad Haba Fadila wats ur prblm? Yajawad din kike ma tsawa haka, da qarfi fadila tace ma Maysah Quite just shuttup md watch him flog me, Kai kuma idan har baka dakeni ba baka cika Jawad Mudassir Zailani ba, Aikam Jawad ya daga belt zai shauda mata Mu'ammar ya qaraso gun da gudunshi tare da riqe belt din, Ya ja Jawad baya, yace cool down man, ba girmanka bane, huci jawad kawai yakeyi Fadila tace ai da ka bar shi ya daken niko na shayar dashi mamakin rayuwa wlh, Jawad ya zabura Mu'ammar ya riqo shi, wai kai meke damunka ne? Sai kace baka san halin jikokin hajia Ama da umma hajja ba? Ai ba da'a ne dasu ba, basu da kunya, Fadila ta ma Mu'ammar kallon tara saura kwata, tace aiko muke da da'a da kunya, ga babban marasa kunya nan, masoyan ku da Bilkisu da Haneefa, idan kuwa babban mara da'a kuke nema toh ga Amira, jikokin waye? Last i checked jikokin Hajia-- maysah tayi sauri rufe mata baki, Ta kalli su, Tace Yajawad, Ya'ammar don Allah kuyi haquri, ba don halin mu ba, Jawad ya yarda belt dinshi, yana ma fadila kallon tsana yace Amar lets go, i dont like dis Girl at all, fadila ta gantsara ma maysah cizo a hannu, maysah ta saketa da sauri tana yarfa hannu, Fadila ta riqe qugu, hey, i dont need-inshort i dont want to be liked by someone like u, as a matter of Fact, i dont like u either, tana kaiwa nan ta ja hannun Maysah ta wurgata cikin mota, ta zagaya ta shiga ta fincike motar ta yi reverse yare da barin unguwar gabaki daya. (Eeelerh u get lever oooo)👻 1⃣3⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕By 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Maysah tace ina zaki kaimu? Ki tsaya, Fadila tayi parking tare da sauke ajiyar zuciya, first of all kar da ki qara yi man haka, Shikuma Jawad din ya qara gigin tabani yagani, zan bashi mamaki wlh, Maysah tace kiyi haquri sis let it pass, fadila tace ya wucei, Maysah tace let me drive, ba musu fadila ta fito ta koma sit din Maysah ita kuma ta koma ta shige tare da jansu suka nufa Gida. ***** Jawad ke hada kayanshi, shi zqi koma Gombe, tunda uwashi ta haifeshi ba a taba Embarassing dinshi haka ba, kamar ace yarinya kamar wannan fadilar ta gaya mai magana be ma ta komai ba? Dole yake barim garin, haka ya bar Gidan be ma kowa Sallama ba har bilkisu. Ba wanda ya san anyi, Mu'ammar be fada ma kowa ba, Maysah ma haka. Bilkis tayi tayi ya fada mata abin da yasa shi tafiya ya qi fada, sai kuma ta sa kuka wai satin shi 3 bezo weekend ba, gashi yau friday bazaizo ba? Bayason kukanta yace kar k damu zan biyo Jirgi InshaAllah Yau din nan, just to see u, don ni zaman Maid ya Isheni, dadi kamar xai kashe Bilkisu ta shiga kichin don hada ma Yajawad Abinci. Kafin ta shiga ta tsara kwalliya. ****** Badiyya ce ta fito daga Airport din Garin London, kasancewar ba yau ne ta fara zuwa qasar ba, ta sha zuwa da Alhazawarta, Taxi ta tsaida tare da fadawa ciki, tace ya kaita cikin gari, sai da sukayi tafia me nisa kafin ta sauka ta biyashi, sannan ta tsaida wani Taxi din, tace Ya kaita Illford shopping center, ya kaita ta sallameshi, ta shiga ciki, wurin Babban wuri ne, ba shagon da babu, wurin bangaren yara ta nufa, ta siya Toys da kaya, kafin ta matsa ta shiga lodo chocholates, tayi siyayya sosai kuma ta kashe kudi, Fitowa tayi ta tsaida Cab, tace akai ta Rand Street, Ba ajima ba suka iso Unguwar, ta lumshe ido tana tunano kwatancen gidan Zaid Ali a qwaryar boka. Ta na tunowa ta na ma me mota kwatance sai ga su har gaban Gidan, a lokacin har dare ya farayi, ta biyashi tare da kinkimar leda ta yi qofar gidan, hannu ta sa ta danne Bell din. ***** Wata hadadden yarinya nagani da ba ta wuce 20years ba tsaye kan stool, gaban ta wani ne da alamun dai mijinta ne hadadde ne me cikar kamala, tie ta ke ciremai, shi ko sai kissing kumatunta yakeyi yana mata waqan My short wifey, tana mutsu mutsu tace Yazayd kaga dai ka Bari, sauri nake da wanne zanji da rigiman babies dinka ko da rigiman Ka? A lokacin ta gama kwance tie din, ya sunkuceta cike da so da qauna yace Yarinyata,bazan gaji da fada miki ina sonki ba, i love u so much. Hanyar daki yayi da ita sukaji an dann Bell, Zarah tayi sauko wa daga jikin mijinta, tace I will get dis, i think mummyn becky ce, kaje ka fara shower din kafin nazo, idan kagama ka fara masu Miemee da Biebie, tana fadan hakan ta na tafia don bude qofa, unlocing qofar tayi tare da bude qofar, Gabanta ya yanke ya fadi, mamaki ya cika Zarah, hasken da ta qara besa ta qi ganeta ba Baki na rawa tace Ba--diyyah, Badiyya a ranta tace shegia guntuwa sai kyau take qarawa, a fili kuwa murmushi tayi tace Hello Baby Zarah, its good to see u too, ta raba ta shige gidan tare da barin matar gidan a waje, zarah ta shigo tana qoqarin qaqaro murmushi sannu da zuwa, ta shiga kicin ta kawo mata juice da cookies, Zayd ne ya sauko yana Yarinyata ke da waye? Maman becky-- maganar ta maqale a fatar bakinshi sakamakon ganin wata yayi kamar Badiyya, Badiyya ta miqe ta tako kusa dashi, murya qasa qasa tace Hello Luv, Zarah tayi saurin shan gabanta, me ya kawoki Gidan na? Diyya tayi murmushi tace mutum yana tare da wanda yakeso, nazo qasar ne, shisa nace sai nazo na gaidaku, ban kyauta ba? Zarah tace kin kyauta mungode, now leave, Diyyah ta kalli Zaid Ali tace how rude of ur wife, is dis how she treats ur visitors? Zaid ya jefeta da wani irin mugun kallo, yace badiyya ki bar gidan nan, tace not until i have wats rytfully mine back, Zarah da qarfih tace kina hauka, wasu yara yan duguiw guduiw kyawawwa suka fito da gudu daga wani dakih, Badiyyah ta nufesu tare da rungumesu, Hello sweethearts, look wat i bought for u, ta miqa musu ledojin tsarabar da ta musu, Miemee ta kalli uwarta tace Mummy who is she?? Zarah tace miemee do u remember dat monster dat was chasing u in ur dreams?? Da sauri ta gyada kai Tace is she d monster mummy? Zarah ta daga mata kai alamun Eh, da gudu miemee ta ja er uwarta biebee sukayi daki. Badiyya ta dago cikin duniyanchi tace dats very brave, kina brainwashing yaranki, mesa baki fada musu m dia daddy's first love ba? Zaid ya daka mata tsawa Enough, get out now before i call d cops, nd u knw here u dont bribe cops, so ki fita tun muna shaida juna Badiyya, Zarah tace u are asking her nicely, ta finciko badiyya ta wurgar a waje kamar wasu kayan waki, ta koma da sauri ta dauko ledojijinta ta watsa mata su a fuska ta nuna ta da yatsa stay away frm my husband. Kika sake dawowa gidan nan zakiga abunda zai faru dake.Ta kullo qofar sa qarfih. Zaid ya sunkuceta yace karki damu, she isnt going to ever come back, nd if ta qara dawowa, she is going to face me not u. Ta rungume shi tace i love u yazayd lets go nd calm ur babies down yayi murmushi tare da nufar dakin yaran da ita👻(wanda basu karanta Akwai Lokaci na biebee isa ba, ku nema ku karanta). **** Kuka Badiyya keyi sosai, wai itace nan? Mqewa tayi tana bin hanya tana kuka, Zarah nd Zayd must pay for dis, wayarta ta ciro ta latso Bokanta, tana kuka tace Boka sun wulaqantani boka ina so kayi musu--- shiru tayi ta bi wani gu da kallo, Numfashinta qiris ya rage ya dauke sakamakon wanda ta gani tsaye daga gefe sanye da 3qtr da top sai Hula Qube ta mazan hausawa, waya yakeyi kuma da harshen hausa, Boka yace hello hello diyyan shagali kina jina? Da sauri Badiyya tace zan sake kiranka, ta share hawayenta ta nufa gurinsa tun da ya dago kai ya kalleta be dauke idonsa ba, ya cigaba da wayarsa Jawad kasan dai banda manyan kaya? Ka dinko min kuma kace ma tsoho ba sai ya biyoni ba, cikin satin nan zan dawo, Bye i gotta go. Daidai nan Badiyya ta fashe da kuka da sauri ya qarisa gunta Hey Miss, are u okay? Ta girgixa mai kai, wat happened to u? Cikin kissa tace yau na xo banda ma sauki, kallonta yayi yace kina jin hausa ne dama? Ba gashi nayi kaji ba? Muje na sama maki masauki, tace bansan kowa ba, pls take me wit u, bansan hannun da zan fada ba, kaga kai musulmi ne danuwana pls ka taimakeni ya danyi guntun tsaki yace da uban wa ya kawo ki nan din? Tace wlh Grads naxo, ya tsaida musu Cab, ya shiga gaba ta fada baya da sauri, Wooow take fada a ranta, wannan gayen ya hadu,ban taba ganin hadadden gaye kamarshi ba, yo wannan ai ya fi wanda tazo qasar danshi kyau, Ai dole zatayi aiki kan wannan, dole take samun wannan a matsayin Miji, tana tunane tunanenta suka iso wani dan qaramin gida, Ya fito ta bi bayanshi ya bude suka shiga, har dakin shi ya kaita, yace ki kwana a nan kafin gobe na sama miki gurin zama, ta yi mai far da ido, tace Nagode sosai Allah ya saka da Alheri. Ya miqe zai fita, tace Bawan Allah kai dan Nigeria ne? Ya daga kai eh, wani gari yace Maiduguri, tayi farr da ido, laaa ashe dan garin mu ne, pls ya sunanka? Cikin qosawa yace Sunana ZAID MUDASSIR ZAILANI👻👻 1⃣4⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Badiyya ta maimaita sunan Zaid sunanka? Ya ce eh sunan kenan, ya bar mata dakin, badiyya ta fada gado tana murna, Zaid ya tafi Zaid ya dawo, wannan zaid din yafi Zaid Ali kyau da wayewa, to su zarah a jiqa zaid a sha na sami wanda ya fi shi komai, daman wanin halin ga Allah baiwa ne wannan zaid din bazan yarda ya kubuce mun ba, haka ta kwanta tana me farincikin wannan sauyi da Allah ya mata. ***** Zaid M.Zailani jikan Alhaji M.Zailani, da Hajiya karime da ga Mudassir da Abida Fari dogo me cikar halitta, Shekarunsa 28, a yanzu ya gama karatun likitancinsa a nan Oxford University, Zaid ya cika komai saidai matsalarsa Daya shaye shayen da yakeyi da taurin zuciya, be bin mata, a ganinsa mata matsala ne, yanmatan turawa sun sha chusa kansu gunsa amma ya na basarwa, Tina kadai yake saurara itama Iyakarsa da ita romance be zarcewa da yaga ta na neman wuce gona da iri zai tsallaketa, Zayd be shakkar kowa abunda ya sa agaba shi yakeyi, ba me chanza mai raayinsa tun yana qarami, ko Jawad sai dai ya shafa mai lafiya gurin Kaffiya, sun Sha fada da Zayyad, Lokacin da suke makaeanta Zayyad na mai nasiha kan shayeshaye, amma sai ya fara mai masifa yana fadin its a free world, so kowa yayi harkan gabanshi, duk Zuri'ar M Zailani daga iyayen zuwa jikokin ba me shan ko da sigari ne, sai Zaid, be fiye shan taba ba sai Giya, shan giyansa ma na masu aji yakeyi, sai dare yake sha. Hakan ya kasance a yanzu, fridge ya bude ya dauko kwalbar Giyyanshi ya fara kwankwada, yana lumshe idanuwa. Badiyya ce ta fito daga dakih ta na neman kicin Ganinshi tayi kwance kan 1sitter, daga shi sai singlet, nan da nan diyya ta kwadaitu da shi, haka ta haye Zaid, cikin bacci yaji ana shafanshi, ya miqe da sauri idanuwansu suka qanqance, Zaid ya hankadeta, cikin tangadi yace keee, are u trying to rape me?? Diyya ta mai far da ido, ta sa hannunta kan bakinta tace mai shhhh, ya koyi shirun, ta fada kanshi ta shiga kissing dinshi, ya biye mata, tana qoqari zuge mai belt yayi saurin watsar da ita a qasa, ya nuna ta da yatsa dont even think abt dis. Yayi cikin daki ya barta yashe a qasa, side smile Badiyya tayi tace muje zuwa. Daki ta bishi ta ganshi yashe kan gado, gyara mai kwanciya tayi ta zo ta baya ta runguneshi, suka yi bacci, assalatu ya tada Zaid, ganin Badiyya yayi rungume dashi tana sharar bacci, komi da ya faru jiya ya dawo mai, ya qare ma Badiyya kallo, kyakyauwa ce, daman akwai masu kyan nan a Naija, well haka yake son mace wayayya, ya miqe ya shiga toilet yayi wanka tare da dauro alwala, be tada ta ba ko da yayi sallah, ya shiga kicin dan hado musu brk fst, 8am ta fito Tana wannan yauqi tana kwarkwasa ta zube jikinshi,ta bashi peck G'mrn My Zaid, be hanta abunda take mai ba, m so hungry, yace i cooked u brkfast, tayi farrr rwly? Show me, Yace i will if u let me, ta gane me yake nufi ta daga shi da sauri, ya riqo hannunta ya kaita har kichin, suka zauna suka ci tare, harda feeding juna, cikin kwana 3 badiyya ta siye zuciyar zaid, haka yake son Matan Naija su kasance a waye, kullum suna maqale da juna. Badiyya ta fahimci Zaid, iyakanshi Romance. Sai ta daina zaqewa tana biye mai yanda yakeso. ******* Ta kalleshi cike da qauna tace My jawad, wats troubling u dis days? Yayi faking smile yace bakomai baby, tace me ya sa ka tafi ba tare da kamin bankwana ba lst 3weeks? Kuma da kazo last week ba mu samu munyi magana ba, me ya faru? Yace bakomi kissu na, tace har ka fara boye mun abu ko ya jawad? Noo baby ba haka bne toh menene? Nan ya kwashe komai ya gaya mata game da abunda ya hadasu da fadila, bilkisu ta tashi tana huci kam balaee, Shine ka qyaleta? Yace hey babe chill mana, ya wuce, tace wlh be wuce ba, ya kamo hannunta duka biyu yace nace ya wuce ko? Ta ce naji, ta miqe ta barshi zaune.Dakin Aj ta shiga ta na huci ke lpya? Tace kinji kinji, ta kwashe komai ta gaya mata ita ma tace balaee, harda Ya'amar dina aka ma rashin kunya, tashi muje sassan su.suka fita gabaki daya. ***** Hajia Ama zaune tana bare gyada, su Bilkisu suka shigo, sai da gaban hajia ama ya fadi don ba zata iya tuna ranar qarshen da suka shigo sassanta ba, Ba su da niyar gaisheta, tace mai gado lapya? Bilkisu ta watsa mata harara hanifa tace ina maras kunyan jikarki? Fadila nake nufi Hajia Ama tace ba sa nan suna chan gidan Yayanku hafiz dukkansu 3, yayansu dai ba yayanmu bq, don mu ba hada jini da mayu da aljanu ba, hajia Ama tace kuyi hqri, Bilkis tace idan bamuyi hqr ba hauka zamuyi? Suraj da Zayyad da suna cikin dakin Ama, tun shigowar su sukejin su, Suraj yace yaran nan basu da kunya, ya fita Zayyad ya bi bayanshi, ke uban wa kuke ma magana haka? Hanifa ta kalleshi galala ta watsar, dan ubanki nikike ma wannan kallon? Tace an kalla din, bilkis tace ke kika tsaya kulashi, ni ai idan na raina bola ko shara ba zubawa cikinta, tass kakeji ya kamtseta da marih, ya juya ya ba hanifa nata Allah ya isa mugu azzalumi shege daniska, charr ran maxa ya baci, belt ya ciro ya fara shauda musu, Zayyad ya qwace su yace ku gudu, yaja shi yana haba, meyasa ka biye musu, hajia Ama ma fadan biye musu da yayi takeyi. Da gudu suka yi sassan Hajia Babba suna kuka, hankalinga ya tashi, da qarfi ta fito, wai waye, uban me kuke ma kuka? Nan suka shirga mata qarya da gaskia, wai Zayyad da Suraj ne suka kullesu suka musu dan banzan duka, ko dankwali bata sa ba tayi sassan Hajia Ama da sauri masifa na cinta, Aishalle yau sai kin ci buhun ubanki, kika sa jikokin ki suka ma bayin Allah duka ko? Nima yau sai munyi na mu, Ama ta fito, suraj da Zayyad na bayanta, tana kar ku sake kuce komai, kuna jina? Ama ta kalleta tace kiyi hqr yaya karime, ba haqurin da zanyi, shegu mayyu wanda suka gaji maita, sai na daka ki yau cikin gidan nan, tayo kanta gadan gadan ta maqure nata wuya, Suraj ya finciko hajia babba ya watsar a qasa, wani irin Ihuuu hajia babba ta sake kamar an sa Lasfika, daidai nan Jawad ya iso, yana zuwa ya sakar ma Suraj nushi a hanci, suraj beyi watawata ba, ya rama nan dambe ya kaure, Zayyad yazo da niyyar rabasu, Jawad ya kaimai nashi nushi a baki, nan zayyad ya zuciya ya rama, sai abun ya koma 2in1, Ihu su hanifa keyi hajia babba nayi, Hajia Ama tayi saurin shiga sassan Umma hajja don ta ga ko su baba Abbakar na nan, fadan qarfi akeyi anan fadila, Maysah da Islah suka shigo gidan, ganin fadan maza yasasu sakin kuka duka, Maysah tayi sassan Tsoho da gudu, bawanda ya iya shiga fadan sbd duk mata ne, Islah tayi boys qrts don neman Yasamir. Har jawad ya far habo ga jini ta baki. ***** Shigowan shi gidan kenan, daga nesa ya hango su suna dambe, hango jawad yayi yana firda jini, danuwanshi uwa daya uba daya aka ma wannan taron dangi? Balaeee, yarda trollynsa yayi ya cire er whyt top dinsa yayi wurgi da ita, ya ruga da gudu, wani tsalle yayi ya chafko zayyad ya hadashi da bango, ya finciko Suraj ya dinga kaimai nushi, abunka da wanda ke gym'n Jawad ya dago kai ya kalleshi ya sakar da murmushi suka tarar ma Suraj, suna duka, daidai nan Tsoho ya iso gurin Ba kasafai yake fitowa daga parlornsa ba, amma yau shine har sassa, Su hanifa sai kuka akeyi, hajia babba na ganin tsoho ta qara fashewa da kuka, Samir ya rugo da gudu tare da Mu'ammar zasu shiga filin dagan Tsoho ya musu alamu su tsaya, tsoho yace ku bar fadan nan, Ku bari nace, Jawad ya bar dukan Suraj, shi ko wannan cigabawa yayi da kilar suraj kamar Allah ya aikoshi, tsoho ya qara cewa nace ka bari ko? Ai da alamu be jin tsoho, da qarfi Tsoho Yace ZAIDU👻👻1⃣5⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 by💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Ture Suraj yayi tare da zuwa ya dauko rigarsa ya nufi sassan su, duk suka bishi da kallo, Tsoho ya kalli Samir tare da miqa mai wayarsa ya ce kiramin Dr Munnir, hannu na rawaSamir yayi dialling no din, ringing daya ya dauka ya miqa ma tsoho, Allah ya qara ma tsoho tsawon rai, Dr muna lpy? Ya amsa, yauwa danAllah kazo ka duba min yara na nan, yace toh gani nan zuwa, Tsoho yace kowa ya tafi sashensa. Zayyad ya kama suraj ya kaishi dakin Ama, aka watse. Ba a jima ba Dr yazo, a duba Suraj, ya bashi pain reliver Tsoho yace aje a duba Jawad, ko da Dr yaje sashen hajia Babba korarsa tayi tace ba sa buqatar likita munufukan banza.. ****** Har kwana 2 shiru kakeji, kowa yayi zaton Tsoho zaiyi magana akan fadan shekaran jiya qala be ce ma kowa ba, kamar baayi ba, Be qullaci kowa ba, ko da Zaid yazo gaisheshi be nuna mai komai ba faramfaram, yana mai wasan kaka da jika, har suna sa ran Tsoho zai masu magana amma be ce komai ba. Hajia Babba ji take da Zaid, duk cikin jikoki ta fi yi dashi, amma gurza mata RM yakeyi, mamanshi Abida ma tafi sonsa. ***** Lamarin Gidan ya qara tuburewa sabon Gaba ya qara qulluwa, Samarin Gidan kuwa zumuncin su ya baci, dama suke zumunci a gidan amma tin bayan fadan nan ba me cewa dan uwansa qala, Gaba me qarfih suka dauka da junansu. Duk wa'annan abubuwan da suke Tsoho na sane da su. Ya samu su Ido, yana tunanin shikuma haka Qaddararsa take? Gaban da Iyalansa keyi na matuqar damunsa. Amma InshaAllah komi yazo qarshe, yasan abinyi.. **** Haka ne bigbrosamir abubuwan gidan nan ya rinchabe, kowa gaba yakeyi, ni ba abunda ya damen da gaba kowa nawa ne, yace shiya sa kike burgeni ba ruwan ki da 'yan ubanci,tace kaima ai haka bigbrosamir shisa nake sonka, yayi daria, yanzu ka fa da mun wannan shigar zai burge Yazayd? Samir yace sis na fiso ki bar mgnr Zaid, tayi rau rau da fuska zatayi kuka, ba zan mishi ba ko yasamir? Ba zaiso ni ba? Duk ta bashi tausayi don yasan ta na son zaid, yace kar ki damu zai soki, bana so kikai kanki ne, na fiso ya zo gunki tace toh shkn bigbrosamir, zan kama kaina. ***** Ta shigo Gidan da motarta, Taci gayu sosai, ta fito ta na taku daidai, fitowar Amira daga sassan Umma hajja kenan taga baquwar fuska, Amirah ta nufeta da murmushi sannu da zuwa, Badiyya tace yauwa, Amirah tace gun Hajja Ama kika zo ko umma Hajja? Badiyya tayi far da ido, ko daya, gun Zaid nazo da fatan yana nan, Nan da nan fuskar Amira tayi dif, tace bashi kike binshi ko tara? Diyya tayi dan murmushi yan dunia tace ko daya naxo ansar zuciyata ne da ya sace min, da fatan kinsan inda ya ajiye shi, in ran amira yayi dubu ya baci, tace ke shegia eriska me bin maza har gidansu, ki bar gurin nan ko wlh na miki tunbur kuma na lalada miki dan banzan duka Badiyya tayi daria, ke yarinya, kinsan dai ni ba tsarar ki bace ko? A banza zan baki shekaru 5 ko 6, zan miki uzuri daya dan naga kina kama da myzayd, nd kamar kina hauka da sai kinyi nadamar furucin nan, Amirah tace na rantse da Allah ina iyawa, idan kin san mutuncin kanki ki bar gidan nan ynz, in ko ba haka ba, zaki ga Haukana don mugun bugu zan miki, na kareraya ki, na kaiki asibiti na kuma yi jinyarki, Daria sosai badiyya keyi, Amira ta kwnace dankwali au daria ma na baki ko? Tayi dammara, daidai nan Maysah ya qaraso gun da gudu ta sha gaban Amira, Haba Amira me ya hadaki da baquwa? Wannan er iskar zata shigo mana gida tai mana karuwanci, wai her Zaid, ko uban wa yabata yazaid din, haba Amira kiyi hqr mana, ke dalla matsa matsoraciya, tsayuwar rin wannan cikin gidan nan balaee ne, Ji gashin doki, ji man kanti ji matsatsun kaya, wlh kamar jikar bokan tudun qarfe, ai wlh sai ta bar gidan nan ynz ba anjima ba, kafin Allah ya jarrabe mu da Kwarantsa cikin Gida, Maysah tace haba Amira, ita ko diyya daria kawai take, Maysah ta juya ta kalli diyyah haka kurum taji gabanta ya fadi, ko me ya sata faduwar Gaba oho? Ta dai daure tace baiwarAllah kiyi haquri danAllah, Yazayd kike nema? Bari a dubo maki shi, ta ja hannun Amira, daga nesa suka hango Yazayd din na jogging, ita ko badiyya ta qarasa gun shi, shikuma ya daga ta sama suka rungume juna, Haka kurum Maysah taji gabanta ya tsananta bugawa, Amira kuwa baki ta bude galala, kaiii Rumguma? Tsanar Yazayd da karuwa (sunan da ta samata)ya shigeta, meye haka, gabansu suke iskanci? Bata ga komai ba sai da taji badiyya nacewa haba Zayd kai da kace zaka nemeni har kwana 5 shiru? Nayi missing dinka, ina tunanin ko ka mance ni? Cikin sigar lallashi yace so sorry my diyyah, wlh i was busy ne, har yau ban siya sim ba shisa ban nemeki ba, but its a good thing u came over, i'm glad to see u, ya akayi kika gane gidan? Ta mai far da ido, kasan familyn Zailani ba boyayye bane, yace haka ne, Sai sannan Zaid ya lura da Meerah da ke tsaye wata a gefenta ba tare da ya kalli Maysah ba, ya kalli Amira yace ke ya ma sunanki?? Amirah ta watsa mai wani mugun harara, Badiyya tace kai honeybunch ur sis is hilarious, ya danyi gyatsine yace haka take bata da hankali, ya qara kallon Amira yace Zo ki kai Badiyya gurin Hajia Babba kice mata baquwa tace, Badiyya tace Oh no dear, ba yau ba, i jus came to check on u, but next time musamman zanzo gaida Inlaw's na, yayi dariar jin dadi yace yauwa sweety, ya ja hannunta ya rakata har mota, Amirah da Maysa suka bisu da ido, Maysah na tir da wannan hali nasu, Ameerah kuwa takaici da baqin ciki kamar tayi kuka, Maysah ta ja hannunta ta fizge tayi dakin Yasamir,Yana ganinta ya miqe tsaye yace lilsismeerah menene waya tabaki? Ta na huci, bigbrosamir daman Yazayd dan iska ne? Ynz wata tazo gidan nan nemanshi kaga yanda ya rungumeta? Ta kwashe komai ta gaya mai, Samir yace toufa, shima Zaid da rigima yake, yasandai ba wanda zai aura mishi bare, kar ki damu kece matarshi, na auri wannan? Allah shi kyauta na aureshi, kai kaga abunda sukeyi? Ai wlh bazan aureshi ba, shi gashi wayayye. Yayi karatu turai ya zama chris tucker, toh wayewa ma ya ci ubanshi, Samir daria ya fara, isit funny bigbrosamir? Ni ynz wa zai aureni? Kowannen ku is in lov? Kuma ni ba zan auri daniska ba wlh, kar kuma Tsoho yace zai zaban mun daga cikin yayyinmu wanda sukayi aure. Shidai Samir har yagaji da surutan Amira, ya daiyi shiru yana jinta, wani Lokaci tabashi daria wani Lokaci ta bashi takaici, shidai yace Allah ya shirya Amira nikuma biebee nace Amin👻 n by biebee GIDAN GANDU 1⃣6🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 ⃣ GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Hajia Babba, Hajia Ama da Umma Hajja zaune a parlor, Tsoho ya kalli Ama yace Aishalle me ya faru sati 2 da suka wuce? Aishalle tayi murmushi don ta san ko ba dade ko ba jima sai yayi maganar, nan ta kwashe komai ta fadi mai tun daga shigowan su Hanifa har fadan, Tsoho ya jinjina kai, Charaf hajia babba ta chafe, baka da labarin rashin ta idon da Fadila ta ma Jawad, rashin kunya da zage zage, amma be ko kalleta ba balle ya duketa, toh shi suraj ya hade bilkin da hanifan ya zane, shi ko zaid ya zo ya lakada mai na jaki ai dan'uwa befi danuwa ba. Tsoho yace shikenan, Allah shi kyauta, ku tashi ku tafi, ya kalli Umma hajja, yace ki turo mun Hassan Hussaini da Gambo tace to Mallam hajia babba ta buga tsoki, M.Zailani ya gyada kai Allah ka shirya. ******* Baba Hassan, B.Hussaini da B.Gambo zaune a kasa kan carpet, Tsoho yace toh kunji hukuncin da na yanke ya kuka gani? Baba hussaini ya nisa yace anya Baba wannan abu xai yiwu, kasan gaban nan me

Chapter 4 of 20