Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels GIDAN GANDU Biebee Isa Hausaebooks Creat:- Shuraih Usman Ku shiga shafinmu na facebook domin samun wasu kayatattun littatafan ta hanyar bibiyar wannan adireshi na yanar gizo www.fb.com/hausaebooks GIDAN GANDU 1⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Tsaki Haneefa ta qara bugawa a karo na biyu, yanzu mu kullum haka zata dinga samu latti? Bilqeesu tace Aifah, inda sabo ai ya ci ace mun saba, ta cika nawa, Hanifa tace wlh baxa ta sabu ba, bari mu dawo daga makaranta wlh mu samu Tsoho mu gaya mishi, Islahulkhair da ke gefen su ba ta tanka musu ba, cikin damuwa Fadila tace Mallam Audi donAllah ka qara mata horn, kafin Mallam Audi ya qara Horn suka hangota tana sauri cikin yanayinta na sayih ta fada cikin mota qirar bus, Mallam Audi Ina kwana, ya amsa mata cikin murmushi, tace kayi haquri wlh banga Socks dina bane, yace ba komai shigo muyi ta tafia kar mu bata wani lokacin. Ya ja mota ya bar haraban wakeken gidan da ke qunshe sashe sashe.. Kusa da Islahulkhair ta zauna gefenta Fadila ce riqe da keypoint tana karatu, Ta ce hey Sisters, sorry i kept u waiting, Fadila ta dago ta kalleta, cike da zolaya tace Allah ya nuna mana ranar da zamu daina jiran Maysah, kin cika nawa, tace wlh banga safata bane ta kalli Islah tace yadai sisi? Murmushi ta mata tace lafya u will never change will u? Daria ta mata ta kama kunnenta tace sorry, ta kalli su Hanifa da bilkis a gefe tace duk ina kwananku, a tare suka buga tsaki tare da hararta, ba ta damu ba don idan da sabo ta saba. Mazan da ke zaune su hudu a chan baya tace Whatsapp bro, daya kawai ya amsata sauran 3 hararata sukayih. Ta kalli Na'imah da bakinta ke sake tana jalalar da miyau tace Nimcy a rufe bakin mana, kar ki bata gaban hijabinki, cikin tsiwa nimcy tace anqi a rufe din, sa'idawa masu bacci da ido daya, tace Allah baki haquri ta ciro littafinta ta shiga dubawa don yau suke fara NECO exams... Jikokin Alhaji Musbahu Zailani kenan masu rubuta Jarabbawar qarshe ta makarantar Sakwandire na TopOnwards Science College Maiduguri, Su 10 cif zasuyi graduation bana... *************** Assalam Alaikum tsoho me ran qarfe, Tsohon da ke zaune kan Sofa kyakyawan gaske ne, kadan ya rage ya cika shekaru chasa'in cif a duniya, tsufansa me kyau ne, gyara zaman gilashisa yayi yace Hanifa ce da Balki? Eh mune, amma bilkisu nake ba balki ba, yayi daria yace ja'ira, ya jarabawar? Suka ce toh Alhamdulilahi, duk suka yi shiru, Tsoho yace me bakin shan qwai menene? Naga magana a bakin ki, Hanifa ta zumburo baki, tace kaga dai tsoho ka bar ce man me bakin shan qwai, yace toh ai naga kun kasa magana, ku fada matsalarku a magance maku ita, Ke Me Gadon zinare menene? Bilkisu tace daman Tsoho qara muka kawo ma, Haneefa tayi charaf tace tsoho mu dai mun gaji, wao kullum sai Maysah ta samu latti, gashi mun fara jarabawa, wlh idan bamu bi a sannu ba wata rana sai an hana mu zana harabawa saboda latti, Mu gaskia da sakel, a san yadda zaayi damu, ko a sama mata me kaita ta qarata chan da lattin ta, Tsoho yayi jimm yace kuyi haquri, kunsanta da Nawar tsiya, zan mata fada, amma maganar raba tafiya duk bata taso ba, tun lokacin yayyunku da sukayi aure tare ake kaisu makaranta kunga lokaci guda ba za a bar wannan qaidar ba, Hmm ai daman munsan baka san laifinta ka fi sonta cikin jikoki, da sauri yace haba yan jikoki na, wlh duk daya na dauke ku, ku bari zanyi shawara da iyayenku, ku saurareni kunji? Sukayi godia suka mai Sallama. ******* Ta kalleshi tace Tsoho tunda nagama karanta ma Jaridar bari naje nayi karatu dukda bamu da paper Gobe sai Jibi, yace RUMAISA'U Meyasa kike sa 'yan uwanki latti? Kullum ke kadai suke jira, ko so kuke a hanaku shiga makarantar! Duk cikin lallabi yake mata magana, ta yi raurau da fuska tace, kayi haquri InshaAllah zan daina, yauma don safata ta shige wani gurin ne ai da bansamu latti ba, yacr donAllah ki daina kinji? Tace InshaAllah, yace yauwa idan kin shiga cikin gida ki kiramin Hajia Babba, tace toh Tsoho ta miqe ta fita, a ranta tace InshaAllah sai na riga kowa shirin makaranta jibi, ba za a qara jirana ba sai dai na jira...Tayi Sassan Matan tsoho domin kiran Hajia Babba, da Sallama ta shiga dakin Hajia babba ce da Abida (Maman Hanifa) a dakin, suna ganinta sun ka bata fuska, ta gaida su ba wanda ya amsata, tace Hajia Babba tsoho na kiranki, ba ta jira ta ce komai ba, ta fice don bata son jin zagin da za a jefi kakar ta dashi ba. Anty Abida ta buga tsaki tace jikar Mayu kawai. Hajia Babba taja tsaki tace wanda suka gaji tsiya game da miqewa don ansa kiran mijinta Tsoho. ******* Gidan Alhaji Musbahu Zailani, wanda yan unguwa da sauran mutane ke ma laqabi da GIDAN YAWA, gida ne katon gaske gari guda ne, me qunshe da sashe sashe, su biyu kachal mahaifan su suka haifa, shida Qaninshi me suna Rabi'u iyayensu asalin yan qasar Chadi ne yan Shuwa Arab, Shekara 2 kachal ya ba qanenshi. İyayensa sunyi hijira zuwa qasar Nigeria garin Maiduguri inda suke sana'ar sirfani da dinki,Bayan Rasuwan Mahaifansu Musbahu ya rungunmi qaninsa suka cigaba da wannan sanaar dinki, har Allah ya buda musu, sun samu İlimi me inganci na arabi da boko. Kafin suka fara habaka Sanoin su ta wani sigar.. Har suka zama matasan Attajirai. A kasuwan da suke Sanaarsu, Akwai Wata yarinya Karime da ke kawo musu tallan fura fura, yau da gobe ya sa suka saba da Musbahu har suka fara Soyayyah, ba ayi wata wata ba ya kai gaisuwa gun iyayenta, yace ba su da kowa a Qasar nan sai qaninshi. Mahaifin karime yace bakomi an bashi karime, ana haka ne diyar kishiyar Maman karime ta shigo daga tallan Goro, ta gaidasu, Baban yace sannu Hajjo kin sha rana shiga kan kabad ki dauko samira na nan da abinci kici tace to, Rabiu ya bi bayanta da kallo chan yace Baba wannan fa? Yace hajara kenan, qanwar Karime ce, amma ba uwarsu daya ba, uwarta ta rasu, sukace Allah ya ji qanta, Baban ya miqe yace ina zuwa, ya shige ciki, Musbahu ya lura Akwai magana bakin qanenshi, yace yaya dai Rabiu? Yace Yaya wannan yarinyan ta man, bansan ko babanta ze ban ita ba, Musbahu yace bari yazo a kwatanta daman gwara kayi auten kaima, ko da baban ya dawo Musbahu ya sanar dashi buqatar qaninsa, Mallam yayi shiru yace baqi taku ba, amma Hajjo bata da kowa sai Allaj sai ni, Hajjo tasha wahalar kishiyar uwa, ta na kan sha, Zan baka hajjo amma sai kayi man Alqawarin cewa zaka riqe man ita da amana, da sauri Rabiu yace wallahi na amince baba, zan riqe maka ita da amana. Yace toh shikenan na baka ita bayan Sati 2 kuzo a daura aure. Sunyi murna gaba ki dayan su... ******* Da daddare Mallam ke gayama maman karime yadda sukayi da meson Karime, murna fal ranta, Allahu Akabar, ashe zan ga Auren Karime nah, kai madalla madallah, yace ai ba auren karime kadai zaki gani ba, harda na hajjo, take Annurin fuskarta ya dauje dif, tace bangane ba, yace Qanin Musbahu ke son Hajjo kuma har na bashi ita, maman karime ta daka tsalle ta re da riqe qugu tace Kam babban balaeen chan.... 2⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Sai kuma ta fashe da kuka, yanzu mallam ni zaka tona wa asiri? Eyi? Yace bangane tona miki asiri ba, dan ka ga ba ni na haifi hajjo ba shine zaka aurar da ita ko neman shawara bakayi? Ynx idan tayi aure wazai na kai mun talla? Ko ni kakeso na fita tallan da kaina? Takaici ya hana mallam magana sai kawai ya fice ya bar dakin... ***** Tadihn su sukeyi irin ta masoyan da, Hajjo ta shigo da Sallama a fuskarta, Musbahu ya amsa da murmushi, yace Amaryarmu, nan da nan karime ta hada gabas da yamma, tace wato Rabiu ba xai janye ba koh? Me zaayi da wanda ba a san asalinsu ba? Hajjo ta shige cikin gidan da sauri tana matsar qwallah, Musbahu ya bata rai yace haba karime me yasa kike haka neh? Sai kace ba Mahaifinku daya ba? Charrr uban, Allah ya sawwaqe, daman wayace ma baban mu daya? To tsaya kajih yanda abun yake, da ita kishiyar maman mu ta shigo gidan nan, Agola ce, kuma da ta rasu, shine babana ya riqeta, ni kadai ral mahaifana suka haifa, Musbahu yace najih dai, be kamata kina nuna qyamarki gareta a fili ba, ko kina kishi ne don ta fiko kyau, wani mugun ashar ta lalayo ta dinga zage zage da qyar ya lallabata tayi shiru. Ya shaida mata gobe zasu je Chadi don sanar da kawunninsu auren su, ta mai Allah ya kiyaye ****** Ko da Su Musbahu suka isa qasar Chadi suka tarar da Kanin Mahaifinsu Ya rasu me dakinshi batafi wata 2 ba itama ta rasu, Musbahu ya kalli Rabiu yace kaga Rabiu inaga mu tafi da su Mudassir da labaran Nigeria, yara ne ba su fi shekaru 10 ba su da kowa yanzu sai mu, yace Yaya duk yanda kace hakan zaayi... Haka kuwa akayi Washegari suka kama hanyar Nigeria. bayan kwana 2 aka daura auren Musbahu da Karime, da kuma Rabiu da Hajjo. Dan madaidaicin Gida ya kama musu, suka zauna tare da yanuwansu Labaran da Mudassiru, Musbahu yace Karime ta riqe su, fir taqi ita bazatayi bautan yara ba tun kafin ta fara samun nata, haka Rabiu ya kwashe su ya kaima Hajjo su, ta amshe su hannu bibiyu. ***** Bayan Shekara daya. A daddafe ta szuwa ta kai kanta bangaren Karime, kuka takeyi tana kiran Yaya ki taimakeni, bayana zai balle, Karime da ke zaune tana tamnar cingam ko kallo bata isheta ba, nan Hajjo ta xube tana murqususu, amma karime bata ce mata ci kanki ba, Tunda Hajjo ta samu ciki Karime ta ji wani tsanarta ya shigeta, jin haushinta daya ya zaayi hajjo ta samu ciki? Ita bata samu ba? Ta sha kai ma cikin hari tun yana qarami amma bata samu nasara ba, Kishinta takeyi Sai kace kishiyoyi, ta dinga juyi a qasa amma ko kallo bata samu ba daga karime, maqociyarsu ce Umm Afeef ta shigo gidan da Sallama, ganin hajjo a qasa yasa ta qarasa gunta tana sallami, me ya sameki haka? Ko naqudar ce? Sannu, ta kalli karime tace kedai bakiji dadin rayuwarki ba, wai shin mini daya kuke aure da zaki nuna mata wannan halin ko in kula? Karime tace Maman Afeef wlh ki fita idona zamu kwashi yan kallo dake. Cikin wahalaliyar muryan hajjo tace umm afeef marata, bayana, ta fita da gudu tana fadin ina zuwa Bata tsaya ko ina ba sai gidan Unguwan zoman garin Ummu Anisa, ta ce ki temaka haihuwa tazo ma hajjo, ai ko da gudu suka fito suka nufa gidan, har ynx hajjo na qasa ta na mutsu mutsu, maman Anisa tace kamata mukaita ciki, Karime tace Waaa? Ai wlh ba zaa shiha da najasa dakina ba, ummu Afeef ta buga tsaki tace in fitsari banza ne, kaza ma tayi, Ummu anisa tace rabu da marar tausayin nan kamata mu kaita bangarenta, nan suka bar karime na ta zazaga masifa. Suna ko shiga daki Hajjo tayi wani yunkuri ta santalo danta, Kai Masha.. Maman afeef ba ta rufe baki ba sai ga wani dan ya fito, cikin murna tace Yan biyu-- sai ga wani dan ya kuma fitowa, Guda maman afeef ta sake da qarfih, ummu aneesa sai sannu take ma hajjo, kafin aka gyara hajjo. Da yaranta maza kyawawa kamar babansu. Ummu Afeef ta fita waje da sauri taga karime na labe tana leqe, ummu afeef tayi shewa tace samun Yan uku sai 'yar baiwa, Karime ta dafe qirji tace na shiga uku, Yan uku? Maman afeef na fita ta samu almajiri kayi maza kaje kasuwa kace ma malam Rabiu hajjo ta haihu ta samu yan uku. Da gudu almajiri ya ruga. Karime kuwa kamar tayi hauka, sai sambatu take tayi, Hajjo ta haihu? Ta samu yan uku? Kuma maza? Jar ubanchan, wlh bazata sabu ba. Da balaee nima sai na haihu cikin watan nan hka ta dinga haukanta... Da gudu Rabiu da Musbahu suka shigo gidan, kallo daya zaka musu zaka san suna dauke da tsantsar farin ciki, Hajjo har tayi wanka tayi kyau abunta, Rabiu ya kwaso yayan ya rungume, ya miqa ma yayanshi, Musbahu ya amshesu tare da musu addua, Allah shi rayaku.. Nan ummu aneesa tace a bar hajjo ta samu bacci, Yan gidan kuwa Labaran da mudassiru sai murna suke tayi Nene Hajjo ta haihu. Musbahu ya shiga cikin Gidanshi jiki na rawa yake ta qwalawa Karime kira yana Karime karime, Hajjo ta haihu har daki ya bita yana gaya mata, Yan uku ta samu, kuma duka maza, Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, shi be ma lura da yanayinta ba, yace wai baki san hajjo ta haihu bane ba? Cikin tsawa da masifa tace Tou Sai Me? Ya dan kallota, karime lafiya? Ta miqe tace ita ta kawo hakan, ta sabi zaninta ta bar gidan, shiko Musbahu tunani yake me yayi zafi haka? ***Rannan suna Yara sukaci suna Hassan Hussaini da Gambo, Yaran nan abun so ne gurin Jamaa, har yau Karime bata leqo ta gansu ba, Rabiu wani kuka ta musamman yake ba matarshi, Hajjo na shan wahaln yan ukun nan, ba wanda ke tayata da rainonsu, sai Mudassiru da Labaran, ganin hakan ne Karime ta sami Rabiu da kuka wai ita dai a bata mudassir da labaran, ita tana cikin kadaici, waye waye, Rabiu be ce komi ba yace su koma gun karimen, Musbahu ya so tambayar ba a si kawai sai ya share. Karime ta cigaba da riqonsu don kawai kar Hajjo ta moresu, a hankali a hankali ta dinga chusa masu tsanar Hajjo. ******* Abu na Allah cikin Shekaru yaran hajjo 6 har da yanuku kasancewar duk shekara take haihuwa wani abun Allah yaranta duka maxa, Bayan Yan uku ta samu Ahmad da Ibrahim, sai auta Hafiz har yau Karime ko batan wata ba ta taba yi ba, an bi Malaman anbi yan tsibbu da bokaye amma a banza. Musbahu na san Yaran Yanuwansa sosai, ya sa yan uku da Amad makaranta Islamiya.. *** A bakin kogi me kallon boader ya hango er yarinya na kuka gashin kanta ya rufe mata fuskarta da sauri ya qarasa yace ke me akayi maki? Dago kanta tayi Ya Salam!! Aljana ce ko mutun? Cikin hausarta da be fita tace wlh mutun ce ni, ya sunanki? Sunana Aishalle daga ina kike? Masu kamen bayih ne suka kamo mu shine ni na gudo nayo nan, ke er wace qasa ce? Tace kamaru, yace ina iyayenki? Ta matse qwallah tace sun rasu da dadewa, yace ta shi na siya miki abinci, na saki kwalekwalen da zai kaiki har kamaru, da sauri ta girgiza mai kai,Tace wlh ba zanje ba, banda kowa a chan, bauta mukeyi a gidan sarki, kuma na gudu da na koma zaa fille mun kai. Ka barni a nan kawai, Musbahu ya tausaya mata qwarai, yace zakije gidana? Da sauri ta daga mai kai, yace toh biyo ni, ba gaddama ta bishi, sunyi tafiya kadan kafin suka isa gida, tun daga soro yake qwala ma karime kira, ta fito, kai mallam ya kake kwala man kira kamar wani watan ramadana-- turus ta tsaya ganin Alajana da gudu tayi daki ta na fadin bayanka Musbahu bayanka Aljana, yayi daria yace keee mutum ce, ta dan leqo tace daga ina? Ya kwashe komai ya gaya mata, shine nace ta zo ta xauna a gidan nan, Ashar ta saki, Wannan Alajanar zata zauna dani? Wannan Mayyar? A gidan nan? Wlh ba dai gidan nan ba, Musbahu ya fusata yace Gidan ki ne ko nawa? Toh sai ki hanata xama gidan nan idan kin isa.. Zuciya ta ci karime ta daka tsalle ta damqo gashin Aishalle Add 3⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 GIDAN GANDU💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Aishalle ta sake ihun wahala, Musbahu ya chapko karime ya hadata da bango, ya ja hannun Aishalle yayi waje da ita, karime na kwance kasa amma bakinta be daina furta zagih da batanci ga Musbahu ba, Wurin Hajjo ya kaita, tayi sauri fa lullube jikinta da zanih, yace hajjo ga yarinya nan danAllah aba ta abinci kuma tayi wanka a bata kaya, Hjjo tace toh Yaya, Yace Aishalle ki saki jikin ki, ba abunda xai sameki anan, ga qanwata na zata kula da ke kinji? Aishalle ta gyada fuska,usbahu ya sakai ya fice,Hajjo tace zonan kinji qanwata? Aishalle ta matsa kusa da hajjo tana dari Dari don ta tsorata da alamarin karime, Jan hannunta tayi ta kaita har daki, ta zubo mata faten doya ta bata, sosai taci abincin nan. Sannan ta bata kaya ta sata tai wanka. Kwanan Aishalle 5, ta sake da hajjo da yaranta, ita ke kula da Hafiz auta, wanka da wanki, haka kuma zata tasa su Hassan gaba tayi ta basu tatsunniya, kullum Musbahu Sai ya shigo ya ga ya take, Duk zaton karime Aishalle bata gidan, don ba shiga sassan hajjo takeyi ba balle ta ganta. Kuma ta hana su mudassir shiga balle su kawo mata rahoton gulma. Wasa wasa har Aishalle ta samu wata 2 a gidan Rabiu, tayi clean ta qara wani irin kyau me firgitarwa. Kuma tana son yaran Hajjo har ranta, da taimakon Hajjo Aishalle ta iya abinci da wasu gyaran da ya kamata ace mace ta iya. Haka suke zaman su cikin aminci da yarda da juna.. ****** Yaya kana ganin karime baza ta bamu matsala ba? Musbahu yace Rabiu ni ba raggon maza bane, na isa da gidana, Kuma bawai zan auri Aisha bane don na ci mutuncin karime sbd bata haihuwa ko wani abu, aa zan auri Aishalle ne don ina matuqar sonta kuma dan raya sunnan manzo. Rabiu yace toh shkn Allah shi sa a dace.. Hajjo ce ta ma Aishalle bayani, tace Mamman Hassan ba wai zan muku musu bane, amma wallahi ina tsoron matarshi, hajjo itama cikin damuwa tace kar ki damu kowa da halinsa zai zauna. Allah dai ya sa mu dace.. Yau ana sallahn jumaa aka daura auren Musbahu Zailani da Aishalle, bisa sadakin silallan zinari 5, Hajjo ta gyara Aishalle, da daddare Musbahu ya shigo Sashen qaninshi yace ma Hajjo ta shigo da Aishalle sashen karime zai hada su, sai da gaban hajjo ya fadi kafin tace toh Yaya ga mu nan zuwa. Wuce wa yayi sashen karime, tana xaune ta na shan rake ko Isha'i ba tayi ba. Mallam sannu da zuwa, tace yauwa karime rake ake sha, e wlh zaqin tsiya kana sha? Yace aa, yo daga ina kake haka sai uban qamshi kake zubawa, rabon da na ganka tun safe? Kafin yace komai su hajjo suka shigo da sallama ya amsa, karime tace wai meye? Da daddaren ma ba za a barka ka zanta da mijinka ba? Hajjo dai bata ce komi ba, Aishalle kuwa gabanta ya tsanta bugu, hajjo wace ce wnnan sai noqe noqe take kamar manahuka? Musbahu yace Karime, tace naam mallam, zaki tuna fuskar nan? Hajjo bude mata fuska, Hajjo ta bude mata fuska, karime tayi zumbur ta miqe, oh Allah Musbahu wai kai ina kake samo aljanai masu tsigar mayu! Haka kwanaki ka kawo wata mayyar, ai gwara wanchan akan wannan! Wannan ai kynta ya shahara, danAllah kiyi haquri baiwarAllah, ai kuma Allah ya hallice ku Duk da bansan me mijin nawa ya miki ba amma kiyi haquri, ta ba musbahu daria sai da ya dan dara, yace Karime wannan ce na kawo miki ita kwanaki sunanta Aishalle, kuma a yau ta zama matana saboda na aureta, Karime ta daka tsalle ta chakumo wuyanshi,/Ni zaka munafurta ni zaka ci ma amana? Idan ka isa Allah ya tsinen, babban balaeen chan, sai ta sakeshi ta wawuro sandan rake ta maula wa hajjo a baya, hajjo ta gantsare baya, ta yo kan Aishalle, yau sai na daddaki kashin babba buraubaki, Cikin zafin nama musbahu ya damqota ya jefar ya nuna ta da yatsa, karime ki kiyayeni karime ki fita idona, ta yo kanshi ta chakume shi, na rantse yau sai ka sakeni idan baka sake niba ba ka haifu ba, wlh sai ka saken, yace karime na sake ki saki daya, ihu ta sake da qarfih tace na shiga uku, daman basona kqke ba? Shege tsinanne laananne, ta figi zanenta ta bar gidan da gudu ko tsoron dare bata yi. Ya kalli Hajjo tace Hajars kiyi haquri ni na jamaki ko? Tace bakomai Yaya, yace nagode ki jeki wanke fuskanki kar ki sa su hassan damuwa tace to yaya nagode sai da safe, Aishalle Allah ya tashe mu lafiya. **** Bayan Wata Biyar Zama suke cikin so da qaunar juna, abu na Allah Aisha na dauke da cikin Wata 4, Hajjo na kula da ita sosai, su Hassan na sonta Goggo Amarya suke ce mata, Hafiz na ce mata Goggo Ama sbd shi yana da tsamin baki, haka kuwa kowa ke ce mata Goggo Ama, su Mudassir kullum suna gidansu karime suna kai mata rahoton abun da ke wakana cikin gidan, ta dau alwashin raba Aishalle da gidan nan amma bokanta ya shaida mata Aishalle ba zata taba barin gidan nan ba, kuma ya hango yaranta da jikokinta cikin wannan gidan, kuma duk wanda Musbahu zai aura a bayan Aishalle yake don sonta a cikin jininshi yake, Hankalin ta ya tashi ainun, babban baqin cikinta be wuce yanda Musbahu yayi watsi da ita, a tunanin ta zaizo yace a maida aurensu amma shiru, gashi uwarta ta rasu, abinci ma gagaranta yakeyi, haka ta samu babanta tana kuka tace sai dai yaje ya ba Musbahu haquri a maidota, yace shifa ba inda zaije, ba zata maidashi tsohon banza ba Nan ta fashe da kuka tana tirje tirje, don yaga uwarta ta rasu shisa be damu da ita ba, ya fi son hajjo, duk da Hajjon ba diyarsa bace, tsakanin da da mahaifi sai Allah, zuciyarsa ta karaya, yace zai ma Musbahu magana. Da kanshi yaje kasuwa gurin Musbahu, Musbahu yace haba baba ai da ka aika an kirani yace bkmi, nan ya gaya mai abunda ke tafe dashi, ya danyi jimm baba yace idan baka so dole ta haqura bawai ina maka dole bane, yace lahh bakomi wlh ni ko ynx a shirye nake a maida auren mu. Haka kuwa akayi ba a jima ba aka maida auren, bayan ya samu Aishalle ya mata bayani ta nuna mai bakomi, amma ta shige dakih ta ci kukanta hajjo na lallashi,. Daga bangare a ka fidda ma Karime dakih ciki da parlo, rananr da tare su Mudassir dadi kamar ya kashe su uwar dakinsu ta dawo, nan ta rada musu wanih abu kunne suka hau shewa... ****** A yau Aishalle ta suntulo danta kyakyawa me kama da babanshi da taimakon hajjo da na umm aneesa, ko kallo basu ishe karime ba, amma hauka ne kadai batayi ba, takaicinta ya akayi Ama ta riga ta haihuwa kuma namiji? Musbahu baki har wuya yau ya gudan jininshi, Rannan suna da yaci suna Aliyu. A rannan ne karime ta tashi da wani kitifi wai ita ba ta san qanshin ragon da ake soyawa, maqota basu bi kanta ba don sun san halinta sai da suka ga tana amai suka temaka mata, a ka kira ummu aneesa don ta dubata, gwajin farko ta gane karime na da juna biyu. Aifah tun lokacin karime aka fara salon iyayi da kankamba, ba ta san wannan ba ta san wanchan. Har Allah ya sauketa lafiya, amma tayi baqin cikin ganin mace ta haifa, Musbahu ya nuna farincikin shi ranar suna diya ta ci suna Abida. To daga nan Aishalle da karime suka fara gasan haihuwa, duk shekara sai sun haihu, sai da Karime tayi mata 2 Sadiya da Zainab kafin tayi namiji daya Usman, ita kuwa Aishalle bayan Aliyu ta haifi Umar da Abubuakar sai mace daya Maryam tun daga maryam Ba

Chapter 1 of 20