Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 11
kuma zata gyara kuskurenta, don kar in yi musu da shi ya sa na tashi na dauki gyalena na yafa a kan doguwar rigar da ke jikina na bi bayanshi zuwa dakin nata na kalli zirga-zirgarta na gaisheta kafin na nemi wuri na zauna a kan shimfidar da na samu ya riga ni zama. To ki yi ki kawo mana. ruwan zatin mana, ya yi magana saboda ganin bata gama kammala abubuwan ba, ta ce to ta kawo ta ajiey taje zata zauna kadan ta rage ta hau kan cinyar shi in banda ya yi hanzarin kawar da jikinshi ina jinda nan din ta zama, nan da nan naji zuciyata ta yamuise wani bangaren na ta ya rinka rayamin cewar so take ta una miki cewar nan din wurin zamanta ne kokari mai yawa na yi kafin na dawo da kaina ga natsuwata nan taek kuma nayi ta tunawa kaina da cewar matarshi ce matar sai ce a hankali na zuba ruwan zafi a kofi na tsoma ifton a cikin a soma sha. Wane irin karyawa ne wannan Maryam? Kina mufin duk abubuwan da ke nan ba za ki ci komai ba sai ruwan lifton, daurewa na yi in banda haka da nayi mishi kuka na dago idanuwana do in yi mishi magana karab suka hadu da na Rumasa'u itama ni take kallo ba kuma kallon dadi ba ne watakila 'yar kulawar da ya nuna ne ba ta yi mata dadi ba, sai yau muka ga juna ido da ido daga ganin da nayi mata a asibiti da suka zo duba babana zuwa yau din ta zabge sosai sai dai in aka barni sai ince tafi kyau a hakan don da ta bar kanta ta ajiye teba mai yawa. 125 A hankali na ce.mishi, na manta ne na fito ban yi brush din bakina ba ko inje in yi in dawo? Har ya ce eh ban san abin da ya tuna ba sai naga ya miko min kwano guda daya na karba na dawo na ajiye na shige bandakina na kwanta cikin zuciyata ina tunanin ba zan sake yarda ya dorani a kan cinyar shi ba wato dama shi dabi'arshi kenan dora mace a kan cinya to na daina yarda in hau.nan take naji zuciyata tana raya min Wasu al'amuran da nan take na ji babu abinda nake so iri in yi kuka shi ne Tmutumin da nalke so a rayuwata na yi ta bunn auren shi sakacinshi da sharrin baba Lantana su ne suka taru suka yi sanadin da burin nawa bai cika ba a wancan lokacin har yaje ya auri wata matar ya Soma yi mata abubuwan da ya kameta a ce ni kadai zei yi wa, motsin shigowar da ya yi ya sani nayi amza na share hawayena amma duk da haka sai da ya gane kukan nakeyi, me ya saIneki? Na yi shiru zuwa dakin nata ne bakya so? Nayi maza na ce mishi a'a, to menene? Na ce mishi bana jind sdi ne, to in bakya jin dadi sai ki yi kuka ba za ki gaya min ba? Ko dai wani abu yana yi miki ciwo ne, nayi amza na ce mishi a'a, a kaiki asibiti nas ake cewa a'a Isiyaku ya siyo min maganin zazzabi. Ya ce in to ki yi wanka ki yi kwalliya in ganki in ji dadi na ce mishi to a haka na wattsake, ana gobe zai fita dakina ma sai da ya sake takurani ya yi yanda ya so da rannan kam kuka nayi ta yi msihi saboda na kasa hakuri in jure tun yana rarrashina har va soma mita wato kenan baki gamsu da adalcin da nake vi miki ba kenan ko So kike in tattara hannu in zuba miki ido ina kallonki, banyi magana ba iyaka dai ranar ya koma dakin Rumasa'u ni 126 kuma na kwana tare da Inna shi ne ya cew yaya Ibrahim kar a ga bata dawo ba zata tayani kwana yace mishi to. Tunda karyawar safe ta zama ka'ida za mu yi ta tare har da shi sai ya zama ka'ida kullum sai ta san abinda tayi ta bata min rai da na yi tunani naga abin bana karewa bane sai na yi maza na cire abubuwan da nake ganin tana yi mishin a raina tunda dai ni ba zan iya yi mishi hakan a gabanta ba bale ince zan rama. Satina uku da zuwa gidan aka soma azumin watan ramadan babu yanda banyi da shiba ya barni in je in yiwa babana barka da shiga watan mai albarka ya ki wai shi ya je ya yi mishi hakan itama yaya Dija ban jeba bata zo ba nayi aike har na gaji na hakura taki zuwa sai ana gobe zamu tafi umarar da aka yi ta rikici akan tafiyar da yace zai yi da ni har sai da babanshi ya sa baki cikin maganar shine wai tazo yi min sallama, na sunkuyar da kaina kasa na ki kallonta naki yarda kuma nayi shiru in daina kukan da nake yi mata, wata uku? Wata uku bamu ga juna ba amma baki yi marmarin ganina ba? Baki kuma ji tausayina ba? Tayi murmushi, to yi hakuri Maryamu yi hakuri Merona ai Meron Alhaji Ahmad kwanaki talatin din nan da kikayi a gidanshi kinga yanda kika zama? Ko da yake dai shima naji babansu yana cewa wai kwanciyar hankali dai shine wani abu banga yanda Alhaji Ahmadu ya zama ba amma zai yiwu ne inyi tayi muku zirga-zirga a gida? Yanzu ma ba ki ji ana cewa kullum sai na aiko Inna ta kawo miki magani ba da sassafe? Na daga ido na kalleta saboda jin maganar tata tayi maza ta kawar da zancen ta hanyar fadin in kin yi dawafin Umra kiyi addu'a Ubangiji ya baki 'yan 127 tagwaye, ban kulata ba na shiga daki naje na kawo mata abinda nake nufin kawo mata watakila sai gab da salla mu dawo watakila sai bayan sallar ki yi wa su Inna sayaiya ta ce min to. Sati uku cif mukayi sai ana gobe salla muka dawo, kudin sadakina da wanda baba Abba Gana ya bani kyauta ya ce a kawowa 'yar uwata ta sai min abinda ya dace su yaya Dija ta kawo min da zamu tati da su na sayo ra rai masu kyau don ma naki karbarj aka gudan da Mubarak ya bani na ce ya rike su. Hirar da Mubarak ya yi min a car wanda a ciki ya tabbatar min da labarin da baba Sumaye ta taba bani na cewar ba ummanshi ce mahaifiyarshi ba ya sani yiwa ban gaya mishi ba, nayi rabon tsaraba na dai dai mahaifiyar tashi sayaiya mai yawa don tsarabarta sai dai gwargwado na kuma yi rabon har da mutanen Gaidan na aika musu da shi. A wannan lokacin ni da Mubarak anarci sosai mukeyi saboda duk abubuwan da a farkons l'amarin suke masu tsanani da sanya faduwar gaba a tsakani sun zamo masu sauki a yau da sanya nishadi in tsaya fadin ji da ni yake yana tarairayata ya zama tamkar sakarci ne zanfi gwammacewa in ce muku duk abinda yake so shi nake yi mishi. Ashe duk wannan kwaramniyar da wannan kai kawon Maryam ashe dai ke din matatace, ince mishi eh yallabai ni taka ce da rabon dai kawai za a ji jiki ne, sai ya yi maza ya ce a1 babu komai ba gashi yanzu ya wuce ba darussan da muka koya tare da mu kuma suna nan 128 Zamu rkesu iya tsawon rayuwarmu? in ce mishi eh, sa ya ce to ai shi kenan. Kwananmu shida da dawowa randa mka dawo ya sauka a dakin Rumasa'u ne ni ma ranar ban wani damu sO nake in dan samu sararawa ya yi kwana biyu ya dawo wurina ranar ma ina hutun sallah ya yi biyu yau koma can ya sake yin wasu biyun ranar zan karbeshi ya shigo wurina da safe akwai wata mas'ala ne? Na ce mishi, a'a ni kin fara ealla ikuwa? Na sake ce masa a'a har ya juya zai tafi sai na ce mishi da ina so in rokeka wata alfarma, ya juyo yana kallona, kamar wace iri kenan, nace so nake ka sa a kaini jaji ina so inje wajen su Inna. Ya danyi shiru kadan kafin ya ce min, to ki saurareni na ce mishi to ya juya ya tafi. Banda vvannan girkin da nayi da ya koma wajen Rumasa'u zai sake dawowa wurina sai muka tafi. Wajen karfe hudu da rabi muka isa duk da ya ce sammako zamu yi mu isa wajen sha daya ko sha biyu in mukayi la'asarm u wuce Kaduna gidan Abdulhamid mu kwana a can ban san yanda akayi sarnmakon bai yiwu ba. Hirar baki ba za za ta iya fahimtar da mutum ya gane irin son da Mubarak yake yiwa mahaifiysarshi ba sai yaje inda take da zama yaga irin gatan da yayi mata shi ba mutum ne ma yawan magana a kan mahaiñyarshi baa ssannan bakina da nashi sai ya tabbatar min da cewar yana dadewa baije wurinta ba a dalilin babu wata shakuwa a tsakaninsu ya santa ne bayan ya girma har ya soma karatu a jami'a ya nemeta don kanshi ita bata taba waiwayowa ta kalleshi ba watakila an bata mata rai ne ya sa tayi mishi hakan watakila kuma don ta ga ta haifi 129 wasu mnasu yawa ne ya sa ta hakura da shi tunda shi kadai ne. Cikin natsuwa na ce mishi, ko kuma don kunyar kai din dan fari ne ba'? lyayenmu ai masu kunya ne, yayi shiru ya bar maganar. Muna isa Jaji na sha mamaki gidan da aka tsaida motar da muka yi tafiyar a ciki gida ne ginin kasa ko ince block din kasa ginin mutanen karkara sai dai babba ne so sai cikin zaure gidan muka shiga muka fada tsakar gidan mai matukar girma, Isiyaku ne yake jagoranta ta den daga hirar da nayi ma sai nags kamar yafi yallabai din yawan zuwa garin a'a ahah kar dai amarye ce yau a gidan namu? Na daga ido a yanayi na girmamawa ina sauraron kalamanta cikin zuciyata na tabbatarwa kaina da cewar itace dattijuwar da ban gane ba a Gaidan ashe daga nan taje can din. A'a wuce mansa wuce ki karasa ina uan shigowa, na bi umarmin da ta bani naci gaba da bin bayan Isiyaku ban karasa inda zanin ba naji tana cewa sannu da zuwa Alhaji kun zo ba? To hannurkn da zuwa hannunku da zuwa. Wata kofa na shiga wacce na dade ina hange saboda nisanta wani tabkeken gida na gani a cikin wata kanmalalliyar katanga ginin block, sannunku da zuwa ta yi min sannu da zuwa cikin matsananciyar fra'ar da ta baiyanarda jajayen hakoran makkanta guda biyu dan kamannin da ke tsakainta da shi kacna ne sai dai kuma hakan ba zai hanaka sheda cewar ita din mahaifiyarsa ce ba shi dogo ne ita. kuwa bata da tsayi shi ingarma ne ita mai dan jiki, ita fara shi wankan tarwada a bakcan kuma 130 su na da dan wani abinda ya hadasu da ya danyi shigenta kadan sai dai ban gane menene ba? Har kun fito? Cikin ladabi na ce mata, ah to sannu da Zuwa shiga mana na shiga falon na ta na samu daya daga cikin luntsuma-luntsumarn kujerun da ke wurin na zauna a cikin ina mamakin wurin nata yafi kama da na sabbin amare saboda irin kawatuwar da akayi mishi, sannu da Zuwa ta sake fadi daidai ta zauna a kan kofar shiga daya dakin nima ra sauko kasa na zauna muna gaisawa tana tambayata yaya gida? Yaya manyan duka? Ina amsa m ata da na ji ta danyi shiru sai na tambayeta Inna ina Izzatu, tayi dariyar jin dadin tambayar yar autar ta ta da na yi ta ce, ai kuwa dai yanzu na aiketa wurin yayarta dake nan bayanmu. Mubarak ya yi sallama ya shigo ya koma can gefe sannu Inna daga yanayin maganar tasu na kara gane gaskiyar abinda ya gaya min, baba baya nan ne? Ya yi tambayar bayan surn gaisa ta ce eh ya zaga baya can kasan sunf ara sharar gona saboda ana ganin kamar damuna tana gab da zata fara zube ya ce haka ne. Isiyaku ya yi ta shigo da tsaraba yana jibgewa a wani daki na daban wanda yawanci kayan amfani ne ya gama ya miko min jakunkunan guda biyu na dauki daya na mika mishi daya na ce a amyar min da ita ta ce a'a haba jaka tayi ta zama a cikin mota a sa miki su a dak mana. Mubarak ya ce ai ba dadewa ma zamu yi ba Inna Kaduna zamu uce gidan abokina, ta ce a'a ai dai ku ku wuce amma ita wannan ai nan ta zo za ta zauna ta ga yan uwanka su ganta ta sansu su santa in ya so in kuka juyo sai ku biyo ku dauketa. 131 Shiru yayi ni kuwa naji dadin hakan da ta fada tunda ni kam asalin niyyata dama ai ta zuwa wurina ne ya ce sai mu karasa Kaduna na ce to. Ashe kuma baki sun zo ta amsa a yanayi na kunya, saboda hada jam'in maganar da akayi sai naji ta ce ni fa amarya ta fito na ce wannan tafiya mai nisa da tayi gashi ba ta gama hutawa ba ta sake yin wata ko da yake dai wannan tai bada ce muka gaisa da matar da na wuto a tsakar gida tajuya ta tafi cikin natsuwa na ce mata, Inna ban san da mutane a gidan ba ni su Izzátu kadai na yiwa tsaraba na tura mata jakar da tsarabar ke ciki, wannan duka su Izzatu? Ai kuwa dai su suka kwashe kayan jakar taki, to Ubangiji ya yi mulu aibarka ya rufa m uku asiri ya zaunarmuku da wannar aure na lau lafiya ya kuma kareku daga sharrin mahassada. Mubarak dake can gefe ya ce anin ni kawa nayi shiru. Ta mike ta fi ta ta kallei, ni fa zan wuce na ce mishi a'a mu kwana tare, da sauri ya kalleni a ina? Na nuna mishi ga dakuna in ma ba zaka kwana anan ba ai ba za ka rasa dakin kwana a gidan ba duk yanda za su kai da jin dadin ganin ai bai kai su ganmu tare ba, ta daure fuska mai don kar in ga yana wasa nima nayi kamar ban ganshi ba na kau da kaina gefe ta sake shigowa zata wuce, cikin natsuwa ta ce min wai so nake in yi sauri don mijinki ya danci wani abu kafi ya tafi, ban kalleshi ba na ce mata ai kwana zai yi, da sauri ta ce au haba? Lalle yau da bak a gidan to a zo a gyara muku wancan daki mana, ta fita tana kiran Izzatu mai yawon nunawa kawaye tsarabar da aka kawo mata. 132 Amma ba kina shirin turani wancan dakn ne ke ki dawo nan ki kwana ba ko? Na yi maza nace mishi share dakin tasa aka yi ta canza labule ta fitar da katifar dake ciki ta sa aka kai wata akayi shimfida yana dawowa daga sallar magariba na ce mishi kO zamuje can ne in kai mana abinci? Bai yi musu ba daki ne har da bayan gida a ciki ya fita sallar isha'i ya dan tsaya wajen mai gadin suka gaisa wanda shima ya jid adin ganinshi don har nan ya biyoni wai mu gaisa Innan ce ta ce mishi ai nima zanzo in gaisheshi ya ce to ba yanzu ba a barni sai da safe saboda duhu. Nayi hira yar kadan wurin Inna saboda sanin da nayi mijina yana can shi daya a dakin, sai da safe Inna, ta ce min to sai da safe 'yar nan dauki wannan kwanon ki tafi muku da shi na ce mata to, a dakin kwanciyar namu Mubarak ya yi kwanciyarshi iritn ashi bako ne ni kuwa na mike na zauna kan shimfidar na soma zare kayan da ke jikina daidai da daidai ina yin wurgi da su ba tare da ina lura da inda suke faduwa. Da sauri ya dago kai ya kalleni a hankali cikin murya kasa-kasa da ke kare baiyanar da bakuntrshi a urin ya ce min, "Ke Maryam a gidan mutane kike irin wannan tubewar?" Ban kula shi ba, ya yi maza ya jawo gefen babbar rigarshi ya rufe fuska, wai ma ba zai bari ya ga abin da nake yi ba, ban daina ba bar na kai ga babu abinda ya saura min sai r brazier da ke jikina na mika hannu daya da nufin in karasata itama sai na ji caraf ya rike hannun nawa. 133 "Tun da dai abin da kike so kenan to barni kawai zan karasa wannan din." Ban sani ba ko bakuntar da yake ji a zuciyarshi ne ya hanashi makara duk da abubuwa masu dadi da suka kasance a daren wadanda suka hanashi samun baccinshi, kiran sallar farko naji ya tashi ya kammala abubuwan da zai ya yi nufin fita masallaci ina jinshi yana tashina ban ayrda na tashin ba. Mubarak da dole dole ce ta sanyashi kwana a gidan nan sai gashi shi da kanshi ya cewa Inna zai bar tafiyar sai gobe saboda ganin yanda yan uwa ke ta isowa suna fadin sun zo ganin babban yaya da amaryarshi, ita kuwa Inna duk wanda ya shigo mace ko namiji dan uwa ne ko abokan zama abokan mutunci sai ta dauko wani abu cikin tsarabar da mukazo mata da ita ta mika mishi a yi ta godiya ana sa albarka, shi ma Mubarak rannan ya yi kyauta har na rinka tsorn kar dai kudin nashi su kare sai dai kuma anyi sa'a basu karen ba, bai yiwuwa in tsaya cewa Ina tayi farin ciki sai dai kawai in ja bakina in yi shiru. Washegari da hantsi ina zauze a gabanta yayin da Mubarak yake waje wajen mai gidan don yin sallama da shi saboda tafiya za mu yi sai ta kalleni ta ce min "Ubangiji ya yi miki albarka ya rufa miki asiri ya baki zuriya mai albarka, ya jikan mahaifiyarki da rahamarsa, in kunje gida kuma ki sa hannu ki kar6i girkin gidan mijinki da yace min baki soma ba ki rinka girki kina baiwa uban mijinki yana cin abincinki, itama matar gidan uwar taku kar ki yarda ki samu mas'ala da ita don tana da tasiri mai karfi a kan al'amarin mijinki sannan 134 ya'yanshi ki sa hannu biyu ki rikeiSu babu ruwanki da uwarsu kin ji ko baki ji ba ko? Na ce "Naji Inna na gode Ubangiji ya kara girma. Izzatu ta shigo dakin kuka takeyi wai zata bini na ce "To Inna inje da ita mana ai itama 'yar yata da na goya haka take kamarta. Ta yi maza ta ce "A'a ba yanzu ba in kin haihu dai za ta zo ta tayaki jego." Shiru nayi ban amsa ba. Inna ta ban tsaraba kashi biyu tace daya namu daya kuwa na yaya Dija, muna barin Jaji Kaduna muka karasa gidan Abdulhamid muka sauka shima mata biyu ne da shi sai dai shi amaryarshi har ta haihu nan din ma fafatak ishi mai zafi akeyi a tsakaninsu. Mun dawo da kwana uku anti Safara ta haifi da namiji zuwa ginin yaron da nayi shi ne shigata gidanmu na farko tun taifiyata Gaidan shi ma barka kawai naje bai yarda naje sunan ba wai ban kai zuwa suna ba don haka Rumas'au ya tura taje a madadina duk da ba wani shiri muke yi ba. A wannan lokacin ne akayi gagarunin zama tsakanin Rumasau da Mubarak da kuma iyayensu gaba daye ashe duk wani iya shege da takeyi da nunannin ita da miji kut da kut suke a mane dajuna ita kishi ne kawai ya sa take yin hakan tsakanin nasu ba mai dadi bane. Wurin yan tsegumi masu kai kawo tsakanin jama'a na samu labari don a bakin Mubarak dai ba zan ji ba saboda baya yin maganar wata a wurin wata musamman ace ba ta nan. Ashe wai tun sanda babana ya zo ya yiwa Alhaji Muhammadu maganar nan cewar in har Mubarak yana 135 da muradin aurena bai fasa ba to su zo su karbi auren ya basu, ya ce eh basu fasa ba, da ta ji maganar ta rokeshi va yi mata alfarnmar neman wata ya aura in yaso ma kar ya auri guda daya ta yarda za kuma ta zauna da su lafiya in har ni zai hakura da ni ya ce mata a'a wannan bai shafe ta ba in tana da wani abin dai ta fada, ta ce ita kadai ce ya ce to a'a ba huruminta bane don ba itace zata zabar mishi matar da zai aura ba, tund aga nan in yazo gareta da bukatarshi bata sauraronshi ba ta yarda da shi, haka suka yi ta zama har akayi bikina watanni uku don haka da na zo gidan shi kuma sai bai salke komawa ta kanta ba shiga dakin yake yi ya yi baccnishi in gari ay waye ya tashi ya fita, ba ki ga yande ta kare ba, na cewaa mai bani albarin ai bana kallonta, ta ci gaba da bayani, ai yanzu ba ta fi rabin da ba don irin wannan wulakancin ciwo ne da shi to yanzu shi ne ta gayswa kakar ta ta irin zaman da sukeyi shi ne akayi zaman to yanzu wai an sasantaus shi aayi mishi fada an gaya mishi laifinshi ya ce a yi hakuri zai gyara itama anyi mata na ta fadan ta rokeshi gafara ya ce ya yafe. Hausawa suka ce wai kishi kumallon mata gashi dai dama can ban san irin zamand a sukeyi a tsakaninsu ba amma da akayi min wannan bayanin sai na dan ji nauyi a zuciyata nan take kuma sai ta fara tunano min to wato abinda ya faru kenan shi yasa jiya na ganshi ya makara a dakinta bai kuma iya fitowa mun karya da safe ba har na gaji na karya a wurina ni da Inna wai yana bacci kan kace meye wannan sai zuciyata ta soma nunawa idanuwana irin bare-bare. da zumudin da Mubarak din 136 yake yi a kan daidaitawar tasu nan da nan sai naji na kullace shi a cikin raina. Kusan sati biyu ay kasa gane al'amarina tun yana kallon abin a wani irin yanayi har dai ya gaji ya tambayem Kina da damuwa ne? Na ce babu, to meke faruwa ne? Na ce ba komai, a'a yaya za ki ce min babu komai, na mike na tafi na barshi wuri bai sake ce min komai ba muka ci gaba a haka. Rannan mun kai sati hudu a wannan lokacin ko yarda mu hau gado daya da shi bana yi cikin dare ya taso ya zo ya sameni a kan katifar da nake kwance na yi zumbur na tashi na zauna, wani irin lalataccen kallo ya yi min, ke kar ki maidani sakarai mana kina ganin kamar wai zan tilastaki ne? To a kan me? Ai ba haka nake ba ko sanda nake da mace daya bana wannan shirmen bale yanzu. Maganar tashi ta soki zuciyata naji zafin ta ba kadan a raina na ce ai kuwa dai sai dai mu yi ta zama a halka in don ka ga ana kai kararka ne, ya katsemin tunanin nawa a dalilin maganar da ya yi, so nake in tambaye ki wane laifi nayi miki? Na tabe baki tare da girgiza kai don in nuna mishi bai yi min komai ba, ya zubamin ido yana kallona haka kawai kike nishadin ki ka ga bari ki yi min wulakanci? A zuciyata nayi nufin ce mishi eh sai dai ina dagowa da nufin yin maganar idanuwanmu suka hadu sai naji ba zan iya ba nayi maza na sunkuyar da kaina kasa, ba kya ganin kamar in na gaji da hakurin da nakeyi zan iya ramawa don kema ki ji inda dadi? Cikin natsuwa na ce mishi ai gara ka raman, ya ce to shi kenan ya mike ya koma in dai ya fito ya yi kwanciyarshi. 137 Washegari da muka tashi ko gaisheshi ban yi ba na ci gaba da harkokina na kuma zuba ido cikin sauraronta ina ramakon nashi zai faro. Ina cikin dakina a kwance sai kawai naji sallamar yaya Dija da sauri na taso ina rike da dankwalina a hannuna kai yaya Dija bakya ko jin tausayina, sai ki ki zuwa in yi ta jin marmarinki har in gaji in hakura, bata amsa ba ta nemi wuri ta zauna na wuce naje na kawo mata abubuwanci citrus wrapes, perrz da arapers ciko farantin nayi nazo na ajiye mata na sake komawa naje na kawo mata soyaiyan naman rago na sake komawa na kawo niata kindirmo na sake juyawa na dauko wani kwanon tayi maza ta dago ido ta lkalleni, ke bana soon rashin bankali ina zan kai wadannan abubuwan da kike taramin? Zo ki kwashe su duka 'ya'yan itace kawai nake bukata yanzu nace mata to. Wani abu ya faru ne? Tayi min tabmayar bayan mun gama gaisawa a hankali na tambayeta me kika gani? Idonta yana kaina ta soma yi min magana cikin natsuwa, Alhaji Amadu ne ya aika a gayawa babansu wai in babu damuwa yana son ganina yanzu, na taba baki tare da girgiza kai, fuskarta tayi saurin canzawa alamar ba ta ji dadin yanayin amsar da na bata ba kan atce min komai sai gashi ya shigo adonshi yayi kyau gashi sai kanshi yake yi. Ki yi hakuri na tasoki, ta ce a'a babu mas'ala ina fata dai babu damuwa, ya ce eh babu a hankali ya soma magana, ba ina nufin kawo kararta ba ne don gaskiya ba dabi' ata ba ce ma yin hakan amma ina so in rokeki a yi mata magana saboda bana son fitina a tsakanina da 1ta, 138 na tambayeta in wani abu akayi mata ta fada ko ba ni ba in wani ya yi mata tana da yancin gaya min domin zamana take yi taki ta yi magana nace zAn rama abinda take yin don itama tai in da dadi ta ce wai gara inr ama, kinga kenan tana sane da abinda take yi tana yi ne kuma da

Chapter 9 of 11