Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 11
in mata gwalo, rannan ina falona a kan kujera shirya Muhammad nakeyi sai ga Mubarak ya shigo zuwa ya yi ya zauna kusa da ni ko ince manne de i tamkar dai a ce maida mu cikinshi zai yi dagan i har yaron, rike yake da kafarshi yayin da shi kuma yake ta faman modar nono. Ban taba ganin mai son da ba irinki gyara dai gyara dai kowane lokaci balkya gajiya da gyarashi ke duk kokarinki wai ki nunamin kin fini sonshi ne ko? Da sauri na ce mishi wace ni yallabai? Baba ne ya ce alkai mishi shi shi ne nake kara kintsashi. Ya kara baiyanar da jin dadinshi ya ce min, kin san abinda yasa baba yake son yaron nan, nayi maza nace mishi uh'uh, to tunawa yake yi da irin wahaloli da kai kawon bacin ran da nayi ta gamuwa da su a kanki Maryam domin shi din shi ne takuici na duk wani abinda kika sani a tsakanina da ke na bada yaron aka fita da shi ya knkameni a jikinshi na tsawon lokacin da yaga hakan ya isheshi sai da ya sake ni don kanshi sai kuma ya kalleni ya ce min, na ganki kina 153 yiwa Rumasa'u gwalo dazu kar ki sake don ba zai zamo min komai ba inje in sameshi in gaya mishi cewar ba ita kadai ce fitinanniyar ba ku dukanku biyun mutane ne daa baku da kirki don baku damu da son zaman lafiya ba, too kawai nace mishi na ja bakina nayi shiru ban dai sake ba. Rannan sai ga Asabe ta zo wurina a wan1 irin yanayi da ba zai kwatantu ba na rashin kyan gani ga kazanta na tuna tsabta da kwalliya irin ta Asabe wai ta zama kazamar da karnintama kawai ya isa ga 'ya ya uku su ne biye da ita daya kuma a bayanta hudu gaba dayansu callo duya zaka yi musu ka kawar da kai, aka ce min kin haihu shi ae nace bari inzo in ga yaron daga nan in yi miki barka, na ce ai na gode bari in kawo miki shi ki ganshi, ne shiga daki don dauko mata shi. Mubarak dake wurin ya kalleni, ke kada ki rinka yi min rashin hankali kin ji ko? Na ce mishi to na dawo na sameta muka dan soma hira har ta kaima na tambayeta ina baba Lantana'? Ta tabe baki ta ce tana can Enugu tana jin dadinta mu tayi banza da mu a nan ta barmu tamkar ba itace tayi mana sanadin wannan wahalar ba, ai ko rannan da naje wajen yaya Salau da sauri na ce a'a Sallau yana ina ne Asabe, ta ce yana can wani gari nan baya yana ta sana'arshi ta gwari, na c kai madalla kowa Ubangiji ya bashi yanda zai yi, maimakon tace amin sai ta ce uhun kai kam ai uwa ta riga ta lalata maka komai sai dai sakaiyar Ubangiji kawai don ta ciceka, zuba mata ido nayi ina kallonta cikin zuciyata na ce, me wannan haihuwar ta amfanar? Iyayen da akace mu yi musu addu'a ita sakaiya take nema a kanta uwar uba kuwa dama ba a maganarshi na sake yin wani tunanin na tuna 154 rayuwar dá baba Lantana ta so inyi kenan a gidan Nalami sai kuma reshe ya juye da mujiya da hannunta ta kai yarta. Kinga baya bamu sabulun wanka bare na wanki balle man shafawa balle zani abincima na dare kawai yake bayarwa in nayi magana ya ce wai shi yana ganin kokarin kanshi in nace zan yi sana'a matarshi ta hana in wasu sukayi tausayina suka bani abu tace satar mata nayi shi kuma yana kallo bai cewa komai don tsoronta yake ji tafi karfinshi. Mama ga kudin cizo a jikinki tayi maza ta kai wa yarinyar duka wannam ne kudin cizo? Kyankyaso ne, na mike na shiga daki na debo turare guda biyu na kawowa Asabe tare da kudi masu dan aiki don na Mubarak ne na gani a ajiye tayi ta godiya ta tafi ta bani ina tunanin rayuwa tare da tambayar kaina ko me baba Lantana taje yi a Enugu? A wannan shekarar ne dai babana ya tafi aikin haji Alhaji Muhammadu mahaifin Mubarak ne ya biya mishi amma sai ya ce wai Muhammad dan jariri ne ya biya mishi. Shekaru biyar bayan wannan lokacin na sake jin wani jegon jegona na uku sai dai a wannan lokacin ina yin jegon ne a wani sabon katafaren gida da Mubarak ya gina mana in da ni da Rumasa'u muka zama sai wacce taga dama ne take shiga wurin 'yar uwarta don bama ma jin motsin juna iyaka dai katanga ta hadamu a wannan lokacin kuma ina jegon nawa ne bayan na kammala karatuna na digiri a jami'ar garinmu banda wannan kuma wani karin jin dadin shi ne ina yin jegon ne a karkashin 155 kulawar uwar miji wacce bata taba zuwa gidan dan nata ba sai a dalilin haihuwar tawa ga kuma baba Sumaye da na riketa matsayin uwa saboda sanin da nayi taso uwartawa sanda take raye taso ta kuma bayan bata nan ta kuma ike amanar dake tsakaninsu yana kuma daga daga kuntatawar da da zai yiwa iyaye a bayansu ya mutunta wanda suke mutuntawa. Inna da Izzatu suka shigo su biyun a yanzu manyan ya mata ne in ka barni ma sai in ce shirin aurensu Mubarak yake yi ko da dai bai gaya min ba don su din a hannuna suke. Shirin mikewa nake yi inje wurinshi saboda dawowarshi da naji sai gashi ya shigo da murmushina na tareshi ina fadin, yallabai kaji wai ashe musakai da mabaratan nan da gwamnatin kudu ta tattara ta dawo arewa da su ashe wai har da baba Lantana a cikinsu ashe can Enugun da taje bara takeyi sannan wai bata barar hakan kawai sai ta lallankwaye ta maida kanta tamkar wacce aljanu suka taba yanzu kuma da aka daw0 ia su anyi juyin duniyá ta koma yanda take abu ya gagara komai ya makale tana can sai zuwa kalon ta akeyi tana ta kuka. Juyawa yayi zai fita ba tare da ya ce min kala ba, Inna tayi maza ta ce mishi haba kai kuwa wane irin miskilanci ne wannan? Yarinya tana ina taka saka da kai sai faman gwaleta kana shassharewa kakeyi me tayi maka ne? Ranshi a hade ya ce, haba Inna gajiya nayi da abin kunyar da yarinyar nan take jawa mutane, yanzu ace ita ba zata daure tayi hakuri da bainda sauran mata suke 156 hakuri da shi ba? Kullum in zata haihu ta rinka ihu kenan tana yi mana bankada a wuri ana kallona? Kuma wai har a gabanki ba zata fasa ba? Inna ta ce mishi kai tafi can da wannen maganar taka kai dai fitinannen mutum ne yanzu yanda wurin nan ya kacame da iface-ifacen mata har kana iya sheda ga muryar wata a ciki? Duk matan ma yanzu ba kukan haihuwar suke yi ba? Kai kasanta ne? Da sauri ya ce ba dukansu bane Inna ai Rumasa'u bata yi shiru take haihuwarta sai dai a ganta da danta kawai, haushi da takaici shi suka taru suka lullubeshi in har akwai wani abidna na tsana bai wuce misalin da yakeyi min da haihuwar Rumasa'u ba. Da sauri naji Innan tayi mishi tsawa, kai tafi can ka bani wuri wadannan 'yan mitsi mitsin 'yayau da take haifowa in tace za ta yi kukama ba sai a dake ta ba, dadi ya kamani shi kuma yayi murmushi, Inna ba ki son laifin Maryam to a dan bani yaron in kaiwa abokaina da suka zo min barka su ganshi. Yana barin dakin nayi kwafa na ce bari tunda abin nashi ya zama hakan nasan abinda Zanyi ba sai na yarda na kara baihuwar ba ne ma zai sake yi min irin wannan wulakancin? Ai yafi kowa son 'ya'ya tunda shi ne mai zirga-zirgar nunawa jama'a su to na daina ba zan kara ba. Ta harareni da gefen ido kafin tayi tsaki ta ce min kinji shirmenki kuma ni ina cewa wani abin za ki yi don ki kwato 'yancniki a wurinshi ya kame bakinshi ya daina wannan iya shegen? To in kin bar haihuwa wa kika yiwa? Danki ai arzikinki ne, yanzu ni baki ganni ba? 157 Haihuwarshi fa akayi aka kwace min shi na hakura na tafi da ya girma bai nemoni ba? Da sauri na ce mata ya nemeki Inna, to da wanda ya kai ni morarshi ne a yanzu? Da sauri nace babu. Ta gyada kai, to nemo wata mafitar amma ba wannan ba na ce to. Kwanakin jego sun kare har inna da baba Sumaye sun koma gidajensu daga ni sai iyalina ne a gida 'yayana uku Muhammad, Khadija sai mai sunan babana Abubakar Siddik sai kuma 'yan mata na Inna da Izzatu da masu aikin gidan a yanzu ban cika lura ko neman sanin me Rumasa'u ke ciki ba balle ta dameni musamman da na gane irin roaganganun da yake yi min suke yi min ciwo na ita dabn ce ba halinku daya ba ita ai tana jin maganata, ashe itama yanayi mata dace nayi naji shari'ar da akayi musu inda take ta kuka tana fadin kusan kullum sai ya kirata da sunan Maryam banda haka kauma sai ya gaya mata ni din daban ce ni ina girmamashi ina jin maganrshi ina gudun bacin ranshi tun daga nan na tattara maganganun nashi na ajiye a gefe saboda na gane dabi'ar shi ne in za a yi fada da shi ya fadi mai zafi in kuma ana zaman lafiya kaga tamkar bai iya komai ba sai alheri. A yanzu kokarina yafi tafiya re wajen ganin ban bashi damar da ya sake shigo min da wata ba amma, Rumasa'u wata a tsakaninmu ya fada ya kara nanatawa wacce bata shigo ba za a iya hana shi kawota ya hakura amma wacce take ciki to babu mai rabashi da ita don shi din wani irin kishi ne da shi da ba zai iya lamuntar ganin wani kato ya aurar mishi matarshi ba don haka sai ya 158 gwammace in tayi mishi yayi mata in anji jiki a gyara amma ba saki ba. Ita kuwa Rumasa'u a yanzu babi abinda take so irin ganin ya kara aure ya dai kawo wata wai nima in ji irin abinda taji sanda aka kawoni. Mubarak ya shigo dakina bina yakeyi da kallo ban fa gane irin yangar da kike yi min ba na lura wani yanga kike yi min kin a wani shan kanshi kina jammin rai ko sanda zan karbi ajiyata a wurinki ai ba irin wannan jan ajin kika yi min ba, wuce shi naje zanyi yayi maza ya cafko kuguna ya rike zo ki gaya min me ya faru? Wata uku da haihuwarki amma har yanz ba ki yi min ban gajiya ba. Na daure fuska sosai don kar yaga alamar wasa na ce ai ni na daina irin wadannan abubuwan, wadanne? Nayi shiru ban amsa ba ia magana dai kenan ya jani zuwa inda yake nufin kainin ya shimfideni shima ya kwanta a gefena nayi maza na tashi na zauna, me kike yi ne haka? Na ce mishi a'a ai ba zanyi bane ba kuma zan yarda in sake ba da inje ina yin abinda zai zama sanadin da zan rinka ja maka abin kunya a cikin mutane suna kallonka ai gara ba a fara ba. To a ina kika ga ana yin hakan Maryam kicekin daina samun ladan mijinki kin daina faranta mishi rai, kin daina menene menene? Wai zna me yakawo wannan ma ganar ne kinji wani ya ce miki wani abu ne? Na bata rai na ce, ina ruwana da wani? Me wani zai yi nin ya dameni? Wulakancin ka ne kawai ya isheni na gorin da kake yi min a kan kukan hai... 159 Ban karasa ba ya yi maza ya ce, ni Maryam ai babu sharri a tsakanina da ke to ni yaushe nake iya sheda wata murya a wurin nan abinda Inna ma ta ce gaba daya duk matan zamanin yanzu kukan haihuwar sukeyi, ai in dai don ta wannan ne sha kuruminki gasa wannan bakin nawa' zanyi ba za ki sake jin wata kalma ta fito daga cikinshi in dai a kan ihun nan ne sai san barka da godiya, don haka sa bannayenki biyu kawaiki rage min kayan nan dake jikiniki don ki sa ni in ji dadi in samu farin ciki da natsuwa a zuciyata saboda sanin duk abinda nake yin yinshi nake bisa yarda da amincewarki, kina so ne nima ina so ba tilastawa ko fin karfi na nuna miki ba. Sannu a hankali cikin yanayi na natsuwa da jan rai irin na mace don dai in kara sashi ya kara matsuwa da abinda ya riga ya matsu, nasa hanu na soma zare kayan dake jikin nawa ina jifa da su daidai da daidai ba tare da na danu ko na lura da inda kayan suke faduwa ba. Wassalam Taku HAFSAT C. SODANGI Fatan alheri gareku dukanku, na gode Ubangiji ya saka muku da alheri bisa kulawar da kuke yi ma rubutuna na gode. 18/2/2015 160 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11