Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 11
nan zuwa, na ce mishi to na dawo na cewa bakon gashi nan zuwa na Wuce ciki bayan ya amsa min ta yanayin gyada kai saboda ya riga ya shagala da mu'amalar da yakeyi da carbinshi. 80 Ina daga cikin dacina a zaune na ji isowar babana ssboda kaurewa da yayi da wani irin barbarci na sha jin shi yana furta lcalmomi har da hira cikin harshen nasu idan yaga abolkan harshen nashi amma ba irin na yau ba aa hankali na sake fiitowa daga dakin nawa cikin sanda na leka zauren don in ga melke faruwea mutumin na ganii a tsaye ya saba gorarshi ta ruwa da tun sanda na kai mishi buts ya sake cikata da ruwa alamar tafiya zai yi yayin da shi kuma babana ya bajea kasa yasa hannu biyu yana rike da kafafuwanshi cikin yanayi na bada hakuri. s A Ka yi hakuri Abba Gana ka yi hakuri kar kace zaka tafi nasan nayi maka laifi amma tunda har ka iya nemana to layi halkuri ka zauna. To tayi hakuri ta zauna tayi menene? Ba ta riga ta ganta ba ba shi kenan magana ta kare ba, ai ta ganta taji dadi ta gofe tasan tana raye itace kawai bata je wajenta ba. Gabana ya fadi kar dai dan uwanka ne wannan ga zatona a zuci nake yin maganar ashe ban sani ba ta fito sai kawai naji babana ya ce min, eh Yacuwuna babanki ne wana ne uwarmu daya ubanmu daya, ban san sanda na kama ihu ina buga tsalle tamkar wata zararriya da sauri anti Safara ta fito tana tambayata menene? Ban iya bata amsa ba kartawa kawai nayi da gudu na nufi gidan yaya Dija don in kai mata labarin, gaba daya muka dawo har da yaya Ibrahim da yaran ya kwaso mu a motarshi saboda na sameshi a gidan. Tuni har zaurenmu ya fara cika da jama'a makwabta baba Bairu da baba Hodijo da ma wasu makwabtan sun hadu sai taya babana bashi hakurin ya zauna suke yi, shi 81 kuwa yaja ya tsaya sai nanata kalmominshi yake yi ta riga ta ganta ai ta gode ta ganta da ranta da lafiyarta to inta zauna me zata mata? Ka yi hakuri malam ka yi hakuri ka zauna na rokeka ka yi hakuri, cikin yanayi na natsuwa da girmamawa yaya Ibrahim yake bashi hakurin baba Baidu ya kaelshi ya ce mishi, kayi mana malam wannan mai rokon naka ai surukinka ne shi ne mijin babbar yar taka? Abba Gana yana jin haka jikinshi ya yi sanyi alamar surukuta tana da karfi da muhimmanci a wurinshi, a hankali ya koma kan tabarmar ya zauna sai dai kuma yana zaman sai ya daso ido ya kali mutanen da ke wurin cikin wani irin yanayi ya tambayesu to da da saa ta zauna ta hanata tafiyan nan kam me zata yiwa Bukar ne bayan ta tafi ta barta shekara talatin da daya? Yana fadin hakan ya soma shisshikar kuka shima baban nawa haka, nayi maza na karasa cikin gida da gudu ban tsaya gurin ganin abinda ya ci gaba da faruwa ba. Kafin magariba dai har makwabtas unf ara zirga- zirga a gidanmu kowa ya ji dan uwan malam Habu mai timatir ya zo sai yazo wai ya zo gaisheshi, kowa ya zo ya fita kuma da abinda zakaji ya zo fadi, wanshi aka ce ne ko kaninshi? Abokin magana ya ce a'a wanshi dai sai ace a'a to ai ma yafi malam Habun karfi da kuruciya, a'a ba zai fishi ba barijn gida da dangi wasa ne? Sannan shi malam. Habu wannan ja'irar mata da ya gamu da ita ai sa'a ma akayi da aka sam eshi a haka kasan ba karamin amfani auren nan yayi mishi ba don ma yayi jinya kanan nan ai duk sanadin ta ne duk masifar ta ce ta jawa mutumin nan wannan Wahalar. 82 Wasu kuma suka ce oh ka ji wani abin mamaki wai yana da 'yan uwan shi har da shakikai amma shekara talatin da daya bai nemesu ba ko me suka yi mishi haka oho? Kai koma me suka yi mishi bai kyautawa kanshi ba ko da yake dai ance wai in ka ga bera ya rugo da gudu ya fada wuta to binda ya koro shin ya fi wutar zafi. Daya mutumin ya ce uhun ai gara da kai da kanka ka fadi hakan don ni yanzu babu abinda ke kadani ya razanani in tsorata irin inga yanda mutnae suke wasa ko suke cin mutuncin zumuncinsu sai ince oh oh anya a irin wannan hali da muke zumunci dake kan siratsi kuwa da akace zai rinka fisgo mutanen da suka tozartar da shi a rayuwarsu ta duniya ya rinka jefasu cikin wuta a ranar alkiyama? Rabbi sallim sallim gaba dayansu suka ce amin amin nima nayi maza ciki zamu tsallake makatan na tayasu fadin amin din. Ban taba ganin babana a yanayi na farin ciki kwatankwacin wanda na ganshi a ciki ba rannan cikin zuciyata na ce oh ashe dai yana son 'yan uwan nashi in da suke ne kawai bai son zuwa, ita kuwa baba Lantana wacce itace mai abincin gidan nan nan taki ta tsaya ta yi wani abin arziki sai tsaki takeyi tana fadin, uhun malam wai shi ma nan yana da wayo yaga ya samu zai cusa yarshi gidan masu kudi yaje ya nemo dattijon babarbare wai shi ne wanshi don ya wanketa daga gorin rashin dangi da asalin da kishiya zata rinka yi mata to dadin abin shi ne babu abinda ban sani ba. Dadin abin shi ne babu ta inda abinci bai yi ta shigowa ba daga gidansu Mubarak ma katuwar kula aka kawo cike da farfesun kayan ciki ga kuma tuwo miyar 83 kuka nima a cikin gidanmu nayi mishi burabuskon gero da miyar kuka da naman kaji a ciki na kuma zubawa kowa har da baba Lantana da ta k tsayawa ta yi girkin, Anyi sallari sha'i sanda naji zuwan Alhaji Muhammadu ya zo yiwa wan babana barka da zuwa va kuma dade a wurin suna hira kafin ya yi musu sallama ya tafi. Gaba daya 'yan hira suka watse aka bar babana da dan uwanshi saboda kafafuwa sun fara daukewa alamar dare ya fara nisa gashi kuma lokaci ne na sanyi amma duk da haka baba Abba Gana ya shiga gida ya ki shiga wai shi zauren ma ya isheshi don haka a nan sukaci gaba da zamansu nima nayi maza na hura wuta cikin kasko na kai musu. A haka suka kwana suna hira ba na zaton sun samu runtsawa don sau biyu ina farkawa cikin dare ina jin zancensu sai dai bana gane me suke fadi saboda barbarcinsu suke yi. Washegari da safe daga gidan yaya Dija aka kawo lafiyayyen abin karyawa wanda basu da cikin gidanmu ba kawai har gidan su baba Sumaye sai da aka kai musu. Ina zaune a gefe sai taya babana murmushin da yakeyi nakeyi saboda jin dadin ganin dan uwa da yayi a zuciyata kuma ina tunanin yanda muke ni da yaya Dija haka su ma suke uwa daya uba daya sai dai kawai su maza ne mu kuma mata, ina wannan tunanin ina kuma kwatanta girman al'amarin da ke tsakaninsu sai na ji yaya Ibrahim yana ce mishi, baba ai sai kawai ka tsaya a yi daurin aure kafin ka tafi tunda ita Yacuwunan ai kwanan nan ne za a daura auren nata. 84 Da sauri ya ce a'a a'a a'a ba za ta tsaya a nan ta daura aurenta ba zata kai ta can gida dangi ma ta ganta mijinta tana sonta ta bita can gida ma zata bata in bata Sonta ta zauna ta bata miji a cen shi kenan miji kam tana karewa ne? Duk da irin yanayin da yayi maganar a ciki kowa ya gane abinda yake nuff gaba daya sukayi tsuru tsuru ana kallonshi an rasa mai karfin halin da zai musu maganar tashi ni kuwa ko a jikina ban damu ba don ya ce zai tafi da ni tunda dai babana ya yarda wanshi ne uwa daya uba daya kowa ya gansu tare kuma sai ya yi magana a kan kamanninsu dan uwan babana ne ban damu ba duk yanda yaga dama ya yi dani musamman ma kuma da yace zai kaiwa dangi ni don su kara yarda da cewar shi din ya ga Abubakar yana nan a raye har ga sheda nan ya zo da ita na yarda mai kama da shi karo na farko da na ji wani ya ce wai ina kama da babana. Yaya Ibrahim ya shiga yi mishi kalamai da bayanai na nuna mishi wai ai tunda ya riga ya zo sun ganshi sunji bayanin komai to yana tafiya za su je don haka ba sai ya tafi da ni ba daga zarar an gama bikin zai gayawa angno ya kawo musu ni ko ma mu taho tare dukanmu ai kaga uban angon baba shi baya nan ne ya yi tafiya. Baba Abba Gana ya kalli yaya Ibrahim cikin natsuwa ya tambayeshi, a'a Ibrahimu zata hanata tafiya da abinta ne? Yayi maza ya ce a'a baba ba haka bane. Ya gyada kai tare da fadin, to insha Allahu zata je da 'yan uwana. Ya sake bude baki cikin natsuwa ya ce mishi, to ko zaka daga tafiyar daga gobe ka kai jibi don mu yi shiri mu maida kai gidan. 85 Haka nan ba yanda nayi zaton ganin Gaidan din na ganta ba gari ne babba da ya ci gaba a kan al'amura da yawa musamman ma masarautarsu haka nan zamantaaekwar garin akwai sha'awa a ciki mutane ne masu kula da lamuran addini. Babana yan uwa ne da shi sosai abin har abin mamaki yanda ya iya tsallake yan uwa da dangi masu yawa haka yayi tafiyarshi ba tare da ya taba waiwayarsu ba. Sai dai banfi kwana uku da zuwa garin ba na soma jin labarai iri iri na abinda ya yi dalilin da ya sa babana ya tsallakesu ya yi tafiyarsu, labaran dai iri-iri ne kowa kuma da irin abinda yake fada sai dai wanda nafi kamawa shine wanda matar baba Abba Gana ta bani da kanta wato Kabudi sunan da na ji suna kiranta kenan ita ce ta shedamin cewar su su babana su biyu ne wurin uwarsu daga shi sai Abba Gana saboda ita uwar tasu ta rasu da wuri hasalima bayan haihuwar baban nawa da kadna ne ta rasu, sun fara maraicin mahaifiyarsu baa wani dade ba sai na uba ma ya samesu don haka sai rikon nasu ya koma hannun kanin mahaifinsu wanda ko kadan bai kula ya tsare zumuncin dake tsakaninshi da dan uwanshi da ya rasa ba banda gadonsu da ya cinye tun basu isa komai ba sai kuma suka taso a hannun nashi cikin wahala mai yawa shekara da shekaru dai su ne masu noma mishi gonakinshi da suka taso kuma yaga sun isa munalin aure har wani tsohon aminin babansu da ya rike zumunci ya baiwa Baba Abba Gana auren 'yarshi shi sai ya nuna yarshi da ta soma tasowa yace in ta isa aure ta babana ne tana isa auren kuma sai dan mai kudin 87 garin ya zo ya ce yana sonta sai kawai ya dauketa ya bashi ya ce babana ya yi hakuri ga kanwarta nan in ta isa auren zai bashi itama da ta isa auren sai ya dauketa ya sake baiwa wani da ya zo daga waje ya bashi kudi bai lura da cewar shekara da shekaru babana ke nomoe mishi gonakinshi ba, ana cikin haka ne ya sake cewa an satar mishi kudinshi da yake binnewa a gonarshi a gindin bishiya babu kuma wanda zai yi mishi wannan satar in banda babana don yafi kowa sanin gonar a dalilin haka ne ya yi mishi wulakanci a bainar jama'a, tare da fadin wai tuni dama shi ya gane duk sace-sacen da ake yi a nan gidan dama makwabta ba kowa ba ne ila shi kam haka ya kwace mishi 'yan kadarorin shi da ya yi aikin kodago ya dan adana kwanaki biyu ne kawai da faruwar hakan da safe ya dauki garmarshi ya fi ta kamar yanda ya sabayi kullum sai aka ga shiru bai dawo ba aka bishi gonar ba a sameshi ba sai garmar tashi aka gani a ajiye a kan daukota aka dawo da ita gidan tund aga ranar babu wanda ya sake sa Bukar a idonshi sai ko wannan ganinn da dan uwanshi yaje ya yi mishi, sunyi nema sun yi nema har suka gaji 'yan kwanaki kadan da tafiyar tashi sai ya baiyana kowa ya gane ba shi ne mai yin dauke dauken nan ba dan kanin baban nasu ne da suke kai daya da shi don ko da ya bar gidan ba a daina ba banda haka ma sai kawai aka kama shi da akuyar mutane ya yanka ta ya durata a buhu, hankalin babban nasa bai yi mummunar tashi ba sai da ya ga damuna tazo ya rasa mai nome mishi gonarshi ga kuma dan nashi da surkayen nashi suna kallo lokacin ne ya yi nadama mai tsanani ya yi kuka har ya gaji ya nemi Bukar har ya zama abin 88 tausayi a kan neman nashi ko zuwa akayi aka bashi labarin cewar anga wani mai kama da shi a wuri kaza sai ya debo kudin mota ya ce a tafi a gani ko shi ne sai aje a dawo a ce mishi ba shi bane, sula yi nema har suka debe tsammani, suka hakura sai a 'yan shekarun nan da yan uwan Malam suka yi ta rasuwa sai hankalinshi ya sake tashi ya sake yin niyayr zai sake neman Bukar ko zaiyi dace in har yana raye su ga juna kafin rai ya yi halinsa shekaru biyar kenan yanzu tunda ya koma bai da wani aiki sai na rokon Ubangiji ya sadashi da dan uwanshi in har yana raye in kuwa baya raye to ya nuna mishi wata alama da zai gane hakan don ya samu natsuwar da zai hakura to a cikin hakan ne ya samu labarin anga wani mai kama da shi a can kasar kudu ya shirya ya tafi ya yi iyakar neman da zai yi har ya gaji ya dawo bai sameshi ba wannan fitar da ya yi dai na wannan karon shi ne fita ta uku ko hudu da ya yi sai kuma gashi ya dawo cikin nasara. Cikin natsuwa nace mata, shi kanin baban nasu ya dade da rasuwar ne ya kabidi? Bana shekararshi tara kenan, cikin shekaru taran nan kuwa ba karamin zuba akayi ba a gidan kin ga wancan dakin da wanene da wance a ciki wannan ma da su wanene in takaice miki dai a yanzu daga babanki ne sai dan uwanshi goni su ne manya a gidan shi kuwa goni shi ne dan karami baban nasu kanin wancan da suka taso tare da Bukar. Tausayin al'amarin ya kamani can cikin zuciyata na yi tunanin duk yanda abu ya kai da zai tsakaninka da dan uwanka to yafiya ituce maganin al'amarin tunda in ma baka yi hakan ba watarana sai a wayi agri ba wani a 89 cikinku, sannu a hankali kuma sai dukkan ku ma ku kai ga karewa. Babana dangi ne da shi masu yawa ku san kullum sai baba Abba Gana ya bada umarnin a kaini wajen wasu da ya dace su ganni duk da na gane abu mai zati aka yiwa babana wanda ya yi dalilin barinshi gida babu ma dai irin satar da aka dala mishi don kuws na sah jm manya su na fadin wai ita satar dan halal ma baya yinta to amma duk da baka sai na rinka ganin tamkar da bai yi fushi mai tsanani ba haka da yayi ya tafin ya samu kamar wasu shekaru da basu tsananta ba da sai ya waiwayi dangi musamman ma da yake a can in da ya tafin shima ya samu rubonshi na aure. Baba Goni shima mutumin kirk ne amma da ganin tsarin zarman nasa da baba Abba Gana kasan ba karanmin hakuri yakeyi da shi ba. Wata irin kulawa baba Abba yake yi min amman duk da haka bai hana sanda na kwana bakwai a gari naji hankalina ya kona gida ba kewar mutacn da us baro ta fara damuna babana, yaya Dija da iyalanta sannn a hankali sai naji shima Mubarak ina som ganinshi ban kuma ji hankalina ya tashi na gane har a vanzu da kulım nake kin auren Mubarak ba kararmin son shi nake yi ba don kuwa a ranar da na ji kishin kishin wurin Yatakabudi cewar baba Abba Gana ya ce ba zai sake barina in koma gida ba zai rike ni ne kawai ya aurar da ni a nan don da hakan ne kawai yake ganin zai karfafa zumunci tsakaninmu da yan uwanmu da mu da su ba wan shakuwa muka yi ba tunda in ya aurar da ni a nan to ko Su basu raye zumunci zai dore a tsakaninsu yaya Dija 90 zasu rinka zuwa ko ba don kowa ba don ni su ma nasu ya'yan tunda gani a cikinsu zasu kula da zumuncin dake tsakaninmu da su yaya Dija, kasa bacci nayi kwana nayi rannan ina tunanin duk da tunanin nashi unari ne mai kyau ama anya zan iya zama da wani mijin kuwa matukar ba Mubarak ba ne? Duk wani mutumin da ya taba zuwa wurina kan maganar aurena na amince wani dalili yana hana auren nake mancewa da shi inji garama da ba a yi auren ba ya fiye min in gamu da shima ban yi komai ba saboda bani da wata danuwa gamne da game al'amarin shi amma banda Mubarak, Mubarak ne mutum daya da zuciyata ta kasa daina kishinshi na kasa daina jin zafinshi na kasa fita cikin harkokinshi in daina son jin abinda yake ciki, na kan dai daure in kawar da kai game da shi har in bude baki ince mishi ya fita harkata amma a zahiri ne kawai hakan yake faruwa yana gwada zai fita harkar tawa sai inji nayi matukar takura, dan sa'an da nayi ma shi ne shi din ba wani jarumi bane kan lamarin fita harkar tawa da ban san yanda na rinka ji ba a raina. Kwana biyu bayan maganar da Yakabudi tayi min naje dakin baba Abba Gana da safe don gaisheshi kamar yanda da ma kullum nake yi tun zuwana gidan sai ya zaunar da ni yana yi min bayani game da muhimnmancin yin auren zumunci a wurina ga dan Uwanki nan da na yiwa Bukar takwara da shi don shi ne dan da Kabudi ta fara haifa bayan barin shi gidan sai in hadaki da shi dan uwanki ne amma ba zan yi hakan ba sai na baiwa mutumin da aka gaya min cewar yana sonki lokaci na kwanaki ashirin da dayu in har ya biyoki kafin cikar wadannan kwanakin to shi kenan ke din rabon shi ce in 91 kuwa bai zo ba sai bayan cikarsu ko da da karin kwana biyu ne to ba zai saurareshi ba. Hankalina a kwance na ce mishi to baba saboda ni da kaina na gamsu da adalcin da ya yi na bada wa'adin kwanaki ashirin da daya duk da dai a lokacin ina da waje kwanaki tare ne a gidan. Yan uwan babana sun nuna min gata na zumunci sun martaba zamaa a cikinsu sun kamama bakuntata irin karramawar da har na rinka yin mamaki sai dai duk da haka zuciyata tafi son in koma gida kusa da babana da yar uwata yaya Dija da iyalinta in so kuma shi ne samu to zanso ace na wayi gari a gidan Mubarak a matsayin ni din matrshi don haka sai nayi ta addu'a ya iso Gaidan kafin cilar kwanakin da baba Abba Gana ya dibar mishi na kwanaki ashirin da daya. Ranar da na cika kwana goma sha hudu wato sati biyu cif da zuwB garin Gaidan sai ga Mugaram ya iso babu wanda ya yi zaton ganinshi a lokacin har nima farin ciki irin wanda nayi bai raisaltuwa sai dai ban bari an gane ba. Sub iyu ne suka zo abinda naji ana gayawa Yakabudi kenan sai nayi zaton ko shi da Amiru ne, sai da na shigga dakin da aka saukesu na gansu eai naga ashe ba Amiru bane, rana marya ya dade, inji abokin nashi. Mubarak ya harareshi, kai nan har wani kulata zakayi? Ya yi dariya to ba zan kulata ba me ya kawoni? lta amaryar ma ance maka ta na yin laifi ne? To ai shi kenan tunda a wurinku bata.yin laifi. Na gaida abokin nashi cikin mutunci da girmamawa a hankali Mubarak ya tambayeni, kin ganeshi kuwa? Na 92 gyada kai muna alamar eh, ya sake kallona a ina kika sanshi da kikace kin ganeshi, na yi murmushi kawai nayi shiru, gayamin sunanshi in har kin gane shin da gaske, ban fadi sunan ba saboda in girmamashi sai na ce mishi na taba ganinku tare da salla ka ce min daga Kaduna yake. Ya yi murmshi ya ce, a to ai tace maka ta ganeni kai Icafi so sai ta ambeci sunana ga tsal ita kuma mai kunya ce, to ni shikenan yi ta zugata. Na matsa kusa da kwanukan abincin da na samu an kai musu na soma budewa yallabai ai baku ci abincin ba, bai kalleni ba ya ce, to abinci muka z0 ci sunje sun dauko min mata ba da sanina ba sun kawo min ita nan ni banyi musu muzurai kan abin da suka yi min ba sai su ne kuma wai za su yi min? Cikin natsuwa na ce mishi, too kayi hakuri si kasan iyaye ne. A hankaii ya dago ya kalleni har da shi ma wannan gorin a cilkin iyayen ya kare? Jin yanda yayi maganar a kanshi ya sani yin maza na ce msihi, shima fa kanin babana ne. Ya yi kamar bai sani ba, au haba? Ai na dauka shima yana cikin maneman naki ne? Abdulhamid ya yi murmushi tare sdaa fadin, kai kam Ahamad Ubangiji ya shiryeka surikin naka kake cewa yama cilkin manema. Mubarak ya murtuke fuska ya ce, to menene don ya nema ba 'ya'ya maza suke da babanta ba ta haramta ne a wajenshi? Ai ni wannan mutumin ban yarda da shi ba don bai yi min kama da wanda zan yi surkuta da shi ba baka ga ko kadan bai yi murnar zuwan namu ba? 93 Na kau da kai daga zancen nashi saboda ganewar da nayi bai san komai maganganunshi ne dai kawai na'zato da kishi da ya saba da su na soma zuba abincin da aka kawo musun na mika mishi ya karba ya ajiye a gaban Abdulhamid kafin ya sake karbar wanda na sake zubawa ya ajiye a gabanshi. Suna gama cina bincin Abdulhamid ya mike, kai nifa zan sha iska a waje daga nan inga yanayin wurin, bai jira amsar da Mubarak din zai bashi ba ya ficewarshi. cikin nutsuwa na kalli Mubarak na ce mishi, ashe ka dawo? Ya ji dadin irin karbar da nayi musu ha watakila bai zaci hakan don haka cikin murmushi ya ce min, na dawo na zo ban sameki ba na ce darma ana yin haka ne mace tayi tafiya mai tsawo irin wannan babu izinitn mijinta ba a gaya musu an riga an bani ke ba ne? Gashi anzo suna cewa wai ba za ki bini ba ni kuna na zo ne da niyyar tafiya da ke ban gane abinda suke ba fa ko kin san da wani abu ne? Na ce mishi a'a sai dai a'a da nace bai hanani gaya mishi bayanin da baba Abba Goni ya yi min na ce to amma ai kazo kafin cikar lokacin da ya diban. Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, ke dai kawai ki danyi gaban ki jiramu a kan hanayr can ta shigowa unguwar in muka fito sai kawai mu daukeki mu yi tatiyarmu don in ba haka ina ganin wadannan ba rabuwa da su lafiya zan yi ba. Na yi murmushi na ce, haba yallabai ranka ya dade ai kaima ba zaka so in yi irin wannan salamar da su ba in ka bisu a hankali sai ku daidaita shi baba Abba Gana ai al'amuranshi masu sauki ne gashi kuma mutumin kirki ne sosai. 94 Hira sosai mukayi da Mubarak irin wanda ko da bamu taba yin irinshi ba ko kuma mun dade har na mance rabon da mu yi irinshi, nayi mishi kalamai masu 8aua ya samu natsuwaa tare da shi. In dai sake komawa wuinshi kenan da maganar? Nace mishi eh, to babu laifi bari in kira Abdulhamid muje inda tuntuni haka kikeyi min Meor ai da babu dalilin da zaisa in yi ta sakin baki ina daddankara miki bakaken maganganu, to in nazo da damuwa sai kice sai kin karamin to in ban gaya miki bakin ki ji kema inda dadi ba yaya zanyi? Ban tanka mishi ba na wuce na tafi don su samu damar sake ganin baba Abba Gana. Sai bayan sallar la'asar ya sake aikowa a kirani a jikin motar da suka zo a ciki na sameshi, to mun daidaita da su Maryam duk da dai ba haka naso ba to amma tunda mun ajiye matsayar da muka yarda da ita shi kenan magana ta kare, ya ce a nan zan yi daurin aure a nan zai yi biki saboda ba zai yiwu a ce za a dibi jama'a a je can ba lokacin biki kuma da kyar ya yarda da kwanaki talatin da biyar nan gaba sati biyar kenan sannan wai a nan za a bariki. Na ce to ai kamar yanzu ne sai kaga lokacin yazo, ya ce to yi min wata magana komai kankantarta da zai sa in ji damuwar da ke zuciyata tayi min sauki don bana son tafiyar da zanyi in barki. Cikin natsuwa na sunkuyar da kaina kasa don in tabbatar bai taf ida wata damuwa ba sai na ce mishi, ai ko ka tafi ka barni a nan din ba wani abu bane babu wani abin da zai faru a bayan naka sai alheri, ya ce to babu laifi. 95 Sai bayan tafiyar su Mubarak din ne na gane banda dinbin tsarabar da ya kawo musu har da kyautar manyan kudi ya yi musu ga kuma lissafe-lissafen da Yakabudi tayi mishi nasu a wurinsu ans bada kudin yin lalle da kuma na turare ya tambayi yewan su ta fada suma ya bayar. Sallama mukayi da Mubarak ba tare da ya gaya min cewar zai dawo ba amma sati biya bayan tafiyar tasu sai gashi ya zo

Chapter 6 of 11