Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 11
mishi murya shi kuma sai zirga-zirga yake yi yana kaiwa da kawowa don ya gane abinda take nufi. Amiru ya ja tsaki kafin ya saki wani lallausan murmushi ya ce, ban ga komai ba Alhaji kai ne kaga hakan ni dai na san a halin da Maryam take ciki a yanzu in ma kaga tayi wani abu makamancin hakan to sai dai tayi don ya zama dabi'arta amma ba don ta burge wani ba don haka kayi hakuri ka rage sa mata ido ku fuskanci juna kai dai ta don ku f jin dadin mu'amala a tsakaninku. Kai kam ai dama baka son laifinta ban taba kawo maka zancenta kan abinda take yi min ka goyi bayana ba sai ka ce wai sa ido nane ya yi yawa. Bai sake tanka mishi ba sai ya juyo gareni, ke rabu da shi kin ji Maryam daina kuka ki share hawayenki kin ji? Ni zan tafi. Nayi naza ma share hawayen nawa kamar 50 yanda ya bani umarni na kuma yi mishi godiya, Mubarak yabi bayanshi nayi maza na koma wurin babana. ai n sBa a wani dade da yin hakan ba sai na hango shi yana dawowa alamar rakyar ba mai yawa ya yi mishi ba don haka na yi maza na sake fitowa daga dakin na tare shi a dan dogon falon da kofofin dakunan ke ciki a hankali cikin natuswa ta yanda babu mai jin abinda nake fada na ce mishi, ko zaka daina zuwa ne don kar mu zo muna batawa juna rai? A yanayin da nayi mishi maganar a irin shi ya bani amsa, ranki ya zo yana baci dai amma ni me zai 6ata min rai? Aiina ganin so mi somin hakan na daga wurinki zan yi maza in yi maganin abin don gaba daya zan hanalki zuwa asibitin kamar yanda kika hana matan gidanku zuwa. Gabana ya yi mummunan faduwa na yi amza na daga ido don in kalleshi saboda mamakin maganar tashi in ga irin karfin halin da ke gareshi da zai yi min irin wannan hukuncin alhalin ni da mahaifina ne, wani irin lalataccen kallo naga yana yi min, kina nufin kinfi kowa kusa da shi ne ko kinfi kowa sonshi ne? Ki yarda in ga wani abinda bai yi min ba ki gani? In gani in zan hanaki zuwan ki zo ki ga wulakancin da zan yi miki baki iya rashin kunya ba? Kar ki dauka kuma wai kishinki nake yi kamar yanda Amiru yake fada ko daya. Rasa abinda zance mishi nayi na soma yi mishi kuka saboda sanin da nayi cewar zai iya aikata abinda ya ce din. Sakarya kawai sokuwa wacce ko ciwon kanta bata sani ba sai rashin kunyar tsiya. 51 Ya wuceni zai tafi nayi maza na ce mishi, to bana son aikin da kake son sawa a yi msihi. Maimakon ya ce min to kamar yanda nayi zaton ji daga gareshi sai naji ya ce min to ai bake ke da shi ba yana kuma da bakinshi dona cikin hankalinshi yake. Ya wuceni ya shiga ciki na share hawayena nabi bayanshi a kan kujerar da nake zama na sameshi yana tashe da babana da ke kwance yana fama da kanshi. Sannu baba ya soma yi mishi gaisuwar cikin natsuwa da yardar Ubangiji zaka samu saukin wahalar numfashin nan nan ba da dadewa ba tunda likitoci sun gano kan al'amarin sun kuma yi bayani da cewar dan karamin abu ne ya sameka don haka za su yi aiki su gyarashi in aka gano kan ciwo baba to ai shi kenan magana ta kare sai kawai a yi addu'a Ubangiji yasa a dace da abinda za a yi don haka nake so in rokeka ka yi hakuri ka kuma kwantar da hankalinka kar ka ce zaka sanyawa ranka wani damuwa don kar jininka ya zo ya hau aikin da za a yin ba wani mai wahala bane. Ya zubawa babana ido tare da saurarona binda zai ce, yayin da nima na yi hakan tare da fatan in ji ya ce baya son aikin tunda mu kam ni da yaya Dija ba ma so gashi kuma ba shawara da mu ya yi ba kafin ya zartar da hukuncin sai kawai na ji babana ya ce mishi na gode Ubangiji ya yi maka albarka. Ya ce amin, ya mike ya fita ba tare da ya nuna alamar ya san da tsayuwata a wurin ba. Wulakanci irin na Mubarak yawa ne da shi ga dukkan alamu kuma watakila shima ya san shi din gwani ne tunda shi da kanshi ma yana barazanar zai yi shi don haka sai nà kudurawa raina in ma za a yiwa babana aikin 52 to ba shi ne zai dauki nauyin abinda za a kashe ba kamar yanda na lura yake nufin yi yan kadarorina zan sayar da na samu na tara da kudin da nake samu a sana'ata ta dinki zan sayar in baiwa yaya Dija kudin ta hada da abinda ke hannunta ta mikawa mijinta ya hada tunda naga alamar aikin zai ci kudi masu yawa. Yaya Dija ta iso na bata labarin duka binda ake ciki da wanda ya faru tsakanina da Mubarak, fada ta rufeni da shi a kan wai ai ni nake jawoshi ta hanyar sakar mishi fuskar da nakeyi mishi amma in ba haka ina ruwanshi da mu da har zaizo yana yi mana irin wannan shisshigin? Aje ya ji da harkokinshi ya barmu mu ma mu yi namu sannan ta riga ta gaya min bata son aikin ba za a yi ba ban ce mata komai ba har ta yi ta gama har ma ta tafi iyaka dai kawai addu'a nake yi da kara gayawa Ubangiji halin da mahaifina yake ciki wanda kuma nasan ya fini sani. Ana idar da sallar magariba sai ga Amir ya sake zuwa dubamu na ji, dadin ganinshi saboda ganin shi kadai ne ya zo ya duba babana ya juya zai fita nayi amfani da baccin da ya tarar baban nawa yana yi na biyoshi waje muka tsaya a dan tsaye a wajen da muka tsaya da Mubarak. Cikin natsuwa na soma yi mishi magana wanda roko ne na ya taimakeni ya gayawa Mubarak cewar ya fita hanyar jinyar da babana yakeyi ya daina zuwa asibitin bana kuma son duk wani taimako nashi. Wani dan siririn murmushi ya yi mai hade da ajiyar ciya a hankali cikin natsuwa ya tambayeni, wai ni in sani mana me Alhaji Ahmad yake yi miki ne? Ni dai 53 basan tunkina yar kankanuwarki yake tare da ke tun baki isa komai ba tun baki ma san ke wacece ba, amma har zuwa yau din nan bai samu matsayin da ya dace dashi ba a wurinki. Nayi maza na kalli Amiru cikin ntusuwa saboda jin kalaman nashi kan in san abinda zan budi baki in gaya mishi sai naji ya ci gaba da cewa, saboda kawai kin san yana sonki saboda kin gane ba zai iya fita harkar ki baa duk motsin da za ki yi idonshi yana kanki iyayenshi sun bashi aure amma kin hanashi natsuwa da zai zauna lafiya da iyalinshi lafiya ya iya jaruntaka kan komai amman in akan ki ne sokancinshi yawa ne da shi, ni da kaina na sha bashi shawara kamar yanda nasha yi mishi gori a kan ki wai dan ya yi zuciya ya kawar da kai daga gareki amma ya kasa ya yi aike gidanku ace an hanashi yafi a kirga kullum kuma ya zo kusa da ke sai kin san abinda kika yi kika 6ata mishi rai amma yana biye ba zan ce mishi ya fita harkarku ya daina zuwa ba don ko na gaya mishi ba ji zaiyi ba don haka in ya zo ke da kanki ki kara gaya mishi in ya ji shi kenan in kuma bai ji ba sai ya yi tayi na dai san har da alhakin abubuwan da yake yiwa matarshi uwar 'ya'yanshid a take matukar sonshi cikin wadannana bubuwan da kike yi mishi. Ya wuceni ya yi tafiyarhi ba tare da ya tsaya ko da don yi min sallama ne ba. Na koma dakin da babana yake kwance na jawo kujerar robar da na saba zama a kanta cikin natsuwa na zauna zuciyata cike da tunanin kalaman da Amiru ya yi min nice mai yawan batawa Mubarak ko shi ne mai yawan bata min a sanina kullum a cikin kaffa-kaffa da shi nake matukar yana wuri bana sakewa in yi abinda na 54 ke so kai ko baya nan bana iya saba dokarshi saboda tsoro ko gudun bacin ranshi da nake yi amma a hakan bana tsira sai ya san abinda ya ce na yi wanda ya yi min wani abinda zan raina kaina ko in zubar da hawaye a dalilinshi amma ka ji irin kalaman da baokinshi yakeyi min to babu laifi. Har dare har washegari Mubarak bai dawo ba maimakon in sake in ji dadin rashin ganin nashi sai na zama ko iya amsa gaisuwar likitan nan bana yi saboda tsoron kar mu na cikin gaisawar ya shigo ya ganmu ya ce ba a yanayin da nake amsa gaisuwar sauran mutane nake amsa mishi ba. Wunin ranar nan har dare bai shigo ba sai wajen karfe goman dare a lokacin nan kuwa babana yana cikin wani hali da ya yi dalilin da sai da naje na kirawo likitoi saboda kei kawo mai tsananin da numfashin nashi kc y1, a-hankali ya turo kofar ya shigo bai nufi wajensu don gani ko jin abinda ke faruwa ba wurina ya zo ya tsaya bai yi wata magana ba har sukayi abinda za su yi suka gama suka tafi, da sauri muka isa inda baban yaku wance don ganin halin da yake ciki gaba daya ya jike da gumi cikin Zuciyata na ce ya wahala, hawaye suka sake zuba daga idanuwa na sharr, bance mishi komai ba haka nan shima Mubarak din ya juya ya fita ya barmu a dakin, na kai guiwowina kasa na durkusa yayin da na kwantar da kama a gefen gadon nashi hawaye suna ta zubo min, jimawa kadan na sake dagowa na kalleshi saboda yanayin numfashin nashi da naji ya sauya bacci ne ya daukeshi na dan ji dadi kadan saboda tunanin yanayin da zai sake farkawa a ciki. 55 A hankali naji an turo kofar an shigo na waiwaya don ganin wanda ya shigo Mubarak na gani cikin zuciyata na ce, ashe ba tafiya yayi ba, to dawo daga nan mana tunda ya samu ya runtsa. Ban yi musu ba na koma daga nan din da yace na zauna, a hankali ya mikomin ledar da ya shigo da ita, bude ki cinye abinda ke ciki ba hilkima bane don kana jinyar mara lafiya ka yi ta zama da yunwa in ka yanke jiki ka fadi sai jinyar ta zama ta mutum biyu maimakon da ana yin na mutum daya. Na sa hannu na karba ina ci shi kuma yana yi min nasiha shi mutum hakuri yakeyi ya koyi jaruntalka idan al'amari irin wannan ya sameshi ba ya yi ta kuka yena kin cin abinci ba kinga irinr amar da kikayi kuwa? Na maida ledar na ajiye saboda koshin da nayi na bude robar ruwa ina sha, sai da yaga itama na maida ita na ajiye sannan ya tambayeni, amma yanzu ai kin gane ya zama dole mu tsaya wajen ganin an yiwa baba aikin nan ko? Na yi maza na daga ido na kalleshi saboda jin dolen da ya ambata sai naji ya ce min, to zai yiwu ne mu barshi a cikin wannan halin? Kin ga haka zai yíwu? Sannan ba zai yiwu a cireshi daga nan a kaishi wani wuri ba domin nan teaching hospital ne. Kalamai da mabayani masu yawa yayi min a natse har dai na bude baki na ce mishi, to ai yaya Dija ma ba ta son aikin. A hankali ya ce min to ai baban naki ne Maryam kin fita iko da shi ke lika fi kowa shan wahalarshi in yana cikin rashin lafiya kamar kina ciki ne dubi yanda kika zama a dan tsakankanin nan, kece kuma baki da kowa sai shi in aka rasa shi kinfi kowa rashi ita tana aure tana da mijinta da iyalinta ga ya'yanta ke ce baki da kowa sai 56 shi, Ina jin ha tadi hakan na soma kuka'saboda yarda da zuciyata tayi cewarni ce bani da kowa sai babana in aka Pasashi ni nafi kowa rashi. Kukan da nake yi bai hanashi ci gabs da yi min magana ba, ke madadin da namiji ce a wurin shi duk kuma abinda da namiji ke yiwa uban a laulawa da taimakawa shi kikeyi mishi ke kinfi wani da namijin ma jaruntaka don haka tsaya kawai a matsayin da ya dace da ke ki taimaki mahaifinki ya samu lafiya in kuma ailkin ya zo da akasi to kar ki ji zafin kanki ki dauka kawai kaddarar kenan kin kuma rasashi ne a kokarin da kikeyi na nema mishi lafiya. Kalaman Mubarak sukayi matukar shigata ta yanda har naji na yarda da magamar yin aikin nan take kuma sai naji zuciyata ta daina tsodo addu'a kawai nake yi a yi aikin a sa'a. Da safe yaya Dija tana isowa ita da mijinta a gabanshi nayi mata maganar ina ganin mu bar neman sallama don komawa wani wuri mu tsaya a nan a yi msihi aikin kawai don ba zai yiwu ya yi ta zama a cikin wahala irin wannan ba. Tayi maza ta ce min, a'a ba zai yiwu don ba zai yiwu mu yi abinda zaum sanyashi cikin hatsari ba ban taba ganin inda akayi irin wannan aikin ba ba kuma zai yiwu a fara a kanshi ba. Ai hatsari bai wuce ciwo ba yaya Dija gardama mai tsanani ta shiga tsakaninmu, saboda taja ta tsaya a kan bata son aikin tunda itace babba kuma itace zata fadi yanda za a yi, nace mata a'a ni ya kamata in facla saboda nice tare da shi a wuri faya ni nafi ki tsoron rasashi saboda nasan zan fiki maraicinshi ni ce ni kadai bani da 57 Uwa bani da... ban iya karasawa ba kuka na soma yi mata. Yaya Ibrahim ya kalleni cikin natsuwa ya ce min, kece mai fadin abinda za a yi mishi Maryam tunda kina so a yi mishi aikin za a yi ké Dija ki yi akan wannan ra'ayinta za a yi. Karo na farko a rayuwarmu ai da yaye Dija da jayaiya irin wannan ta shiga tsakaninamu bata taba cewe gAma yanda zaa yi nace mata a'a ba, hankelina ya yi matukar tashi da abinda ya farun musamman da na ganta tana ta kuka saboda ta riga taki aikin da za a yin sai karfinta kawai akayi bata yarda ta zauna ba ma a asibitin kamar yanda kullum take yi kama hanya tayi ta tafi, To in ailkin nan bai yi nasara ba me cewa yaya Dija? Tambayar da na yiwa Mubarak kenan a lokacinda ya zo don jin yanda mukayi da ita, bata fuska ya yi sosai kafin ya ce min, to in kama ska yi nasarar fa? Ke ba a i yi addu'ar yin nasara b sai ki zausa kina abrin zaciyarki tana raya miki mnanan abubuwa? Da wani wanda yake rike da rayuwar wani ne ko kuwa da wata hikima ne da za ta sa mutum ya tsallake wa'adinshi? Da irin wadannan kalaman na yarda na sanya hatmm a kan takerder ailkin da Za a yiwa babana. Cikin tsananin tsoro da fargaba ina gama sanya hannun na koma gefe ina kuka yana rarrashina. Yanda babana ya wuni karfashin dokar lilkita na bar ya ci komai ko da kuwa ruwa ne baka nima na wuni ban iya sanya komai a bakin nawa ba gashi babu yaya Dija sai Inma yarta babban da dama take zuwa tayani zama in ita bata zo ba saboda aiki ko wani aikin sai dare suka 58 zo ita da yaya Ibrahim idanuwanta a kumbure alamar tayi kuka har ta gaji ban iya ce mata komai ba na daga hannu ko bayanin likita na cewar za a shigar da shi Dtiyata da misalin karfe goma da rabi na dare ba. HASBUNALLAHU WA NI'IMAR WAKL' abinda kawai nake karantowa kenan a bakina da kuma zuciyata suka gama abinda sukeyi suka tas. Wajen Rarfe taran dare Mubarak ya iso babu abinda bai zo min da shi ba wanda ya san ina so amma ban iya cin komai ba saboda tashin hankali sai kaduwa nakeyi tamkar awcce sanyin hunturu ke kadata. Ana cikin haka har lokacin ya iso gadon likita naga an fara kawowa cikina ya bada sautin kulululu ban iya daurewa ba sai da na ruga da gudu na shiga bandaki kafin in fito na samu har an canza mishi kayan jikinshi da rigar likiten na raca yaada zenyi da raina na rinka jin tamkar ince na fasa abar yi mishi aikin kawai, shi da kanshi babana za gane ya shiga wani hali saboda jinshi da nayi yana cewa, Mubarak na gode Ubangiji ya yi muku albarka in har ban fito ba kuma to ka rike min uwata amana. Maimakon Mubarak ya ce misbi to ko ya gaya mishi wata magana da zata yi mishi dadi sai kawai naji ya ce mishi, a'a baba ni kar kace ka bar min amanar Mero don ba zan karba ba in zaka bani aurenta kawai ka bani ga mutane can a wancan dakin inka yarda in yi hanazrin kiran mutum biyu kawai ko uku don su tayan shedawa. Haushin Mubarak da takaicinshi suka kamani har a halin da babana yake ciki yana iya yi msihi musu da sauri na ce mishi, a'a baba daina cewa ka baiwa wani 59 amanata ai lafiya zaka shiga ciki ka kuma fito lafiya babu abinda zai sameka sai alheri, kai në zaka fito ka ci gaba da kula da ni mu ci gaba da zamanmu babu abinda zai sameka sai alheri, babu abin da zai sameka sai alheri, nayi ta nanate fadin hakan tamkar dai shi ne abidna zai sa hakan ya zamo ya yiwu. Ni da shi muka bi bayan gadon da ake tura habana, babana yana ta salati ni kuma sai kuka nakeyi shi kanshi Mubarak ya shiga wani hali, watakila don ganin babu kowa a wurin daga ni sai shi saboda batta su anti safara da na tuntubesu kan aikin basu bani goyo baya ba balle inji daiin gaya inusu cewar vau da daddare za a a yi, don haka babu wani wanda yake: da cikakkiyar masaniya na abinda ake ciki. Suna tafiya muna biye da su har muka kai inda aka tsaidamu shi kurna aka wuce da shi ciki. Kwanciya nayi a kasa ina kuka, tashi-tashi ki gani? Tashi ki zauna, kin taba ganin inda kuka ya yiwa wani amfani ko ya zama sanadin samun biyan bukatarshi? Addu'a ai itace ta kamace mu tashi ki zauna. Da irin wadannan kalaman nashi ne na mike na zauna kan daya daga cikin kujerund a ke wurin shi, kuma ya fita ban san inda ya je ba jifa jif dai yakan shigo ya zo ya sameni ya gaya min kalmomi na karfafa zuciya da kara tuna min muhimmancin tsayawata kan addu'a maimakon kuka ko yawaita damuwa ba zan iya tuna irin addu'o'in da nayi a ranar ba, fatana da burina da a yi nasara ne a fito da shi yana raye don in aka samu akashi kan hakan to ban san abinda zan cewa yaya Dija da 60 sauran wadanda suke da hakka kan rayuwar tashi ba gaba daya Saboda tsananin kidima da damuwa bana iya tantance dadewar da sukayi a ciki gaba daya in banda duk abinda ake yi a cikin duhun dare ne guda daya da Dayi zaton anyi adadin kwanakin da basu kidayuwa saboda dadewarsu da na gani. Mubarak ya sake shigowa ya sameni a inda ya barni a zaune. Sannu Maryam, da kyar na iya buda bakina na ce mishi, yauwa saboda jin da nakeyi tamkar la66an bakin nawa a manne suke, cikin yardar Ubangiji za a yi nasarar aikin da ake yiwa baba Ubangiji kuma zai yi miki sakaiya kan al'amuran rayuwarki gaba daya bance mishi komai ba ya nemiw uri ya zauna yana kallon agogo in dai komai ya tafi daidai ai sun kusa fito da shi. Cikina ya sake bada wani sautin na kuluulu saboda jin da nayi ya ce in komai ya tafi daidai kenan in bai tafi daidai ba ma an kusa sanin abinda ake ciki kenan. A haka muka ci gaba da zama a wurin babu mai cewa wani komai, idona yana kan agogo in banda tafiyar lokaci babu abinda nake dubawa, zuciyata kuwa tana ta karanto addu'o'i haka, a haka a irin wannan yanayin da awowi suka zama tamkar kwanaki a hakan kuma dai har muka kai lokacin da suka ambata na kammala aikin da za 8u yiwa baban nawa sai kuma gashi an fito da shi kwance a kan gadon babu wata alama ta motsi a tare da shi, muka Sake biyo bayansu zuwa dakin da dama muka bari aka dorashi a kan gadonshi aka kwantar da shi, abu guda daya kawai da ya dan kwantar min da hankali shine 61 tabbacin da naji suna ta baiwa Mubarak ina anyi nasarar aikin da aka yi mishin. Amma ban samu natsuwa a tare da ni ba har sai kwanaki biyu bayan nan da naga babana ya soma wattsakewa daga mummunar wahalar da ya sha har kuma gashi numfashin nashi ya daidaita saura ya samu karfin jikine kawai. Mutane sukayi ta zuwa duba babana saboda jin labarin aikin da aka yi mishi kai kace ahi kadai ne mara lafiya a asibitin nan, ina jin wani daga cikin yan kasuwar tumatirin nasu yana gayawa abokin tafiyar tashi, kaga ja'irar yarinyar nan yar gidan Malam Habu mai tumatir, kai wannan yarinya da jarumtaka take bata gajiya da hidimar mahaifinta kullum a cikin kai kawo da dawainiyarshi take shi yasa duk iya shegenta sonta yake yi. A to ba dole ya sota ba Malam ko da na mijine ya ke irin hidimar da yarinyar nan take yi akan mahaifinta ai yaci a yaba mishi balle ita yara irin wadannan ai haka suke sunada halin tsiya da na arziki, kai ba duka ba inji wani da bansan ko waye ba ita dai wannan anyi dacentane Ubangiji kuma zai saka mata ya shiryar da ita ya bata mijin da zai sota ya riketa duk da iya shegen nata. Babana bai cika kwana biyar da yin aiki ba sai da kowa ya gamsu da aikin da ak yin ya kuma ce gwara da akayi hakan ciki kuwa harda yaya Dija. Tun kwana biyu da aikin babana sanda ya soma dawowa cikin hayyacinshi Mubarak ya dauke kafa ya daina zuwa asibitin baya zuwa da daddare balle kuma da rana, ko dama can kuwa mafi yawancin zuwan nashi kan 62 zamo cikin dare ne lokacin da zirga-zirgar dubiya tayi sauki in dai ba wani dalii mai karfi ne ya kame na yazo da ranar ba. Rannan da safe ni da yaya Dija ne kawai a tara da shi bayan mun goggoge mishi jiki mun gyarashi mun tsabtace komai na dakin sai kamshi yake yi yaya Dija ce a kusa da shi tana bashi ruwan tataccen kabeji da karas yana sha a hankali yayin da ni kuma na gama tattara kayan wanke-wanken mu na mikawa Inna nace taje ta wanke sai kawai mukaji an turo kofar dakin a hankali tare da yin sallama, gaba daya muke amsa sallamar tare da maida hankalinmu wajen kofar. Gabana yayi mummunar faduwa saboda ganin mai sallamar, Umma ce ko ince Umman Mubarak tare da Rumasa'u da Rukaiya, kadan ya rage in dibibice in rude saboda rabon da muyi gaba da gaba da su haka an dade ko ince tun daga ranar da abinda ya faru tsakanina da Mubarak na samuna da akayi a dakinshi da al'amuran da suka biyo baya wa ta mu'amala bata sake hadani da wani daga cikin mutanen gidan ba, wacce tayi dalilin haduwarmu a wuri daya kamar hakan ba dan gara-gara Rukaiya in ta kure mana a makaranta mukan gaisa saboda munyi karatu tare. Sannu da zuwa Umma yaya Dija ce ta fara yin gaisuwar daidai tana mikawa Umman kujerar zama, na mika hannu don karbar yarinyar da take hannun Rumasa'u duk da yanayin dake fuskarta tamkar dai ace mu din ba wasa tare muke yi ba, gaba daya aurenta da Mubarak ya canza al'amuran dake tsakaninmu ni da ita kowa ya fi jin zafin wani oho?. Ko da yake dai nikam can 63 cikin zuciyata na sani bana jin zafin Rumasa'u kamar yanda nake jin zafin Mubarak da wadanda suka sashi aurenta. Gaba dayansu na bisu na gaishesu kamar yanda naga yaya Dija tayi, yaya jikin na malam? Yaya Dija ta sake amsawa Umma zancensu ni kuma na dawo da hankalina wajen sauraron abinda Rukaiya ke gaya min naga Hasiya jibirin shekaran jiya ta tabaye ni ke na gaya mata tace in gaisheki itama zata zo, nayi murmushi na ce mata ai jiya tazo nan ta kusa wuni muna zancenmu ban sake Juyawa na kaili Rumasa'u ba saboda bata bani fuskar da zan iya fuskantarta in kakalo wata naganar da zanyi da ita don haka na ci gaba da wasa da 'yarta da kuma hira da Rukaiya, kc kadan dai banji dadin sammakon da sukayi mana ba an saukin abiıma sun zo sun samu babana da kuma dakin da muke ciki cikin tsabta. Bayan tafiyarsu yaya Dija ta kalleni tayi murmusbi ta ce, kai kishi babu kyau mata suna kokari, ban tanka mata ba balle zancen ya yi nisa na kalli knna na ce mata, jeki ki yi mana wanke-wanke kin ji? Ta ce to ta tashi ta fita ba fa zuwansu bane ina jin Alhaji Mubarak ne ya turosu. Na sake kin amsawa don kuwa ban san dalili ba sai naji bani da ra'ayi a kan zancen nasu. Sati biyu da aikin babana aka sallatmo mu muka dawo gida bisa dokoki da aka jaddada mana binsu. Ranar wuni nayi ina aiken Inna gidajen mutanen da sukayi ta zirga- zirga suna ta dawainiya da mu irinsu Jumare gidan baba Hodije Yakubo Halina, Hasiya Jibrin, malamaina ua Markas irin su Malama Basma da Hindu abokan karatuna na makarantar mu ta ilimi addini mai zurfi 64 musamman wadanda mukayi aji daya da su wadanda har karo-karon kui suka yi suka kawo min don taimakawa Zumunci irin wanda mutane suka nuna mana a

Chapter 4 of 11