Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 11
ne tsakaninsu da Asabe ga shi nan kuma tana zaune tana ta haihuwa 'ya'yanta. Delu tayi murmushi ta ce, tana ta yawo dai wannan haihuwar tata ta ukun ina ce-a unguwa ta yi ta? Ko menene ba a sani ba? 18 Ita. kam Asabe ai abin tausayi ce ita don kuwa mugun abin ki ne ya shafeta, ni tausayinta nake ji tunda ko jiya tazo wurina." Bakin Baba Lantana ya dan rusuna a dalilin cewar da Delu tayi ko jiya Asabe taje wurin ta watakila taso 1ne yanda ta yanke ta share tsofaffin aminan nata, itama yar tata tayi haka. Delu tayi amfani da damar da ta samu na shirun da Baba Lantana tayi ta ce mata "Kinga ni fa ba fada ma ya kawo ni wurinki ba, zuwa nayi in ji dalilin da yasa hidima irin wannan ta taso miki, ba ki neme mu ba. Cikin natsuwa Baba Lantana ta tambaye ta hidimar me kuma nake yi yanzu in banda ta fama da tsohon mijin da bai iya hassala komai. Delu ta ce, Kai haba bai iya hassala komai aka daura mishi aure? Ko kuwa dai don ya yi aurenne yasa ki ke fadin haka akan shi don ki bata shi? "Aure?" Tayi tambayar a wani irin yanayi, "Wane aure kuma? Wace mata ce zata yarda ta auri Mallam a yanda yake din nan?" Baba Sumaye da ke cikin gidanta tana jiwo hirar tasu, kasancewar a tsakar gida suke, don ko dakinta bata kaita ba,s ai ta takarkare ta rangada wata irin matsiyaciyar guda mai ratsa kunne da jiki. Kafin ta ce "Ubangiji na gode maka, na kuma roke ka ka yi wa Hadiza albarka da ta raba ubanta da wannan musiba da ya dade yana rayuwa a ciki. 19 Kar dai dama da ni wannan matsiyaciyar matar take yi? Aure? Wane irin aure kuma. Mallam zai yi? Wace mata ce zata yarda ta aure shi? Ai kuwa da taci.." Baba Sumaye ta kwashe da dariya tare da fadin Yau fa za a ga hauka tunda an yi wa mahaukaciya kishiya, aiyururururii." Sai ta sake rangada guda.4 Gaba daya Baba Lantana ta birkice, Delu kuwa ta yi maza ta suri takalmanta ta kama hanyar fita, tana fadin Ke ni fa ban san ba ki ji ba da ban zo na gaya miki ba, alhalin maganar take yi fuskarta cike da murmushi alamar bukatarta ta biya. BoBaba Lantana ta kama fadin maganganu tamfar wata zararriya, "To Mallam ma har wani namiji ne da za a yi kishi a kanshi, sullutu a cikin maza, shi in ana kiran maza har zai buda baki ya amsa? Ai karyarsu ta kai karya, ace ya yi mata biyu bai isa ba, Baba Sumayc tayi maza ta ce to na náwa? Wai an tambayi tsuntsuwa sunanshi? Ya ce na nawa? Ta bar wannan ta koma durawa Baba Sumayen ashar, ita kuwa ba ta amsa ba. Tayi ta gaji ta koma kan Babana da ba ya nan zuwanta runfarshi biyu bata samun shi ta dawo tazo ta zauna ta zagi Innata ta hada da Yaya Dija da ni da makwabta ta gaji rushe da kuka ita kadai. Ana cikin haka sai ga Asabe ta shigo gidan, rabe- rabe da 'ya'yanta uku biyu suna biye da ita, daya tana 20 goye ganin uwar tata a yanayin da take ciki yasa ikinta yayi sanyi kiyi hakuri Mama. Tanfar tuna mata zaman nata tayi ta juya kanta da zagi da tsinuwa ba dai kin ce ke wurin makiyana za ki rinka zuwa ba? To ki daina zuwa wurina na yafe musu ke kije can ku karata na bar musu ke. Ta ufe mata ya'ya da duka gaba daya gida ya kaure da koke-koke. A A zuciyata na ce, "Kun gamu da mahaukaciyar Kaka, säi ga Yaya Dijah ta shigo ita da Aminanta, Anti Kubra da Anti Asiya. Nayi zaton zata rufe Yaya Dijah da duka, sai naga ba haka ba, sai da Yaya Dijan ma ta mika mata 'yan kayan da tazo mata da su a matsayin kayan fadin kishiya, shi ne naji ta ce mata je ki ki k2iwa Ramatu kin ji ko ba ki ji ba? Munafukai ke da yar uwarki." Ta ci gaba da zage-zagenta tana watsi da kayan. Ba su ce mata komai ba, sai lekowan da Anti Asiya tayi dakina ta ce min "Ke je ki ki karbo mana kayan cefane a wurin Baba, aiki muka zo yi don yanzu 'yan jere za su iso, na ce mata to. Ban dawo na samu Baba Lantana ba, kofarta a kulle itama Asabe ta tasa 'ya'yanta sun yi gaba sai kawai muka sake a gida muka yi ta hidimarmu, 'yan jere suka iso suka yi ta jerensu, makwabta ma suka yi ta shigowa suna yiwa Yaya Dijah murnar auren da ta yi wa Babanmu, sai hira ake yi ana aikin ana bada labarin haukar Baba Lantana ana kwashewa da dariya. 21 Da yamma yan biki suka tafi, bayan sun gama kintsa komai a kan sai da daddare masu kawo. Amarya za su kawo ta. Suna barin gidan sai kawai naga Baba Lantana ta balle kofar dakinta, ta fito, ashe wai duk abin nan da ake yi tana ciki ta kulle kanta, tana jin duk abinda ake fada. Muna hada ido da ita, ita ce ta ce min "Dukkanku kuma za ku ci ubanku, har da shi uban naku zan ga yanda za a yi ya yi mata biyu a cikin gidannan da ni ku ke yi." Tun kafin Baba Lantana tayi min wannan bayanin a tsorace nake da ita, balle kuma da ta gaya min hakan, ko dama can kuwa mafi girman tsoron nawa ya ii tafiya ne ga tunanin yanda za a yi Babana ya shigo dakin wata mata a gabanta, tana kallonshi, to halle kuma yanzu da tayi maganar da bakinta. Magriba kawai aka idar sai kawai jama'ar amarya suka dawo wai har sun kawo ta, nan da nan gida ya gauraya da kamshi, ba su wani dade ba kuma sai süka watse suka yi tafiyarsu. A ka bar amarya ita kadai a dakinta, nima ina nawaa dakin, ina fama da faduwar gaba saboda tsoron abinda zai faru tsakanin Babana da Baba Lantana in ya shigo gidan nan yau, tunda ta ji maganar ba u yi ido hudu ba. Kan turmi ta fito ta zo ta zauna da damara a kugunta, tana fadin "To duk wani iya shegen mutum ni kam ai kallonshi kawai nake yi, ni kam ai iyaka ce ai ni nafi tsumma lalacewa, yau zanga yanda za a yi 22 Mallam ya zo ya ce min yayi aure a gidannan zai shiga, wani daki, ai sai dai kowacce ta aura mishi ke din taz tayi gadinshi, in har ta matsu sai yayi abinda take so yayin da ke, munafukan banza munafukan wofi." Tana cikin wannan sambatun sai ga shi ya shigo da gyaran muryarshi da ya saba, da kuma sallama. Da sauri ta taso ta tare shi tana fadin Munafuki, na ce maka munafuki. Ina lekensu ta jikin kofa, na ganshi a tsaye yana kallonta, ai babu inda za ka je zan ga yanda za a yi ka ahiga wani wuri ba nawa ba, kai nan ma har wani namiji ne? nayi kamar in tashi in fita in taya Babana, sai kuma naga kai bari dai kawai in zuba ido in yi ta kallo, in har ta bana shi shiga dakin amaryar tashi shi kenan in gari ya waye in taga zata zauna ta zauna, in taga zata tafi ta tafi. Wane dadi ne ya kwaso Baba Lantana? Oho. Sai kawai na ganta tasa hannu biyu ta cukume wuyan rigar Bahana tana fadin "Kai din me? Me kuma aka yi..." Bata gama ba sai kawai naga tanfar an dagata sama ne kafin aka yi firo da ita ta tafi can nesa ta fadi. Mamaki yayi matukar kama ni, na ganin abinda yayin, nan take kuma sai na tuna ai duk iya shegen da Baba Lantanan ta rinka tsulawa a gidanmu bata taba gwada sa hannu ta shake wuyan Babana ba sai yau. Kafin ta taso tuni har ya gyara zaman rigarshi ta daidaita a jikinshi, yayi sallama kofar dakin Amarya ta amsa, ya shige ciki. 23 Ka fito Malam tun muna shaida juna da kai, tun tun muna girma da arziki da kai tun ban shigo nan din na same ka ba. Ta zabura wai zata shiga dakin Amarya, ban san yanda aka yi ba na dai ji Amaryar tana cewa. A'a haba wannan kuma ai neman wuce iyaka ne, koma dai daga can wurin zaman naki kawai in yana son ganin naki zai zo inda ki ke ya same ki." Ke har wata iyaka ce da ke? Ta soma zage-zage sai dai kuma ta kasa shiga dakin ta same shin, ana cikin haka naji an turo kofa an rufe girif an kuma sa sakata an kulle ta ciki. Buga kofar yayi matukar razana Baba Lantana, nan take ta kurma ihu mai karfi, ni kuwa nayi maza nima na sawa tawa kofar sakata, don kar ta fado min dakina, na hau gadona nayi kwanciyata aka barta a tsakar gida ita kadai tana ta faman sambatunta. Washegari kuwa farkawa nayi a dalilin an kwankwasa min kofa saboda makarar da nayi, saboda Baba Lantana bata bar ni na samu natsuwar da nayi bacci da wuri ba, shiga da fita ta rinka yi tana buga kofa kamar zata ballata, ban sani ba ko ni kadai ce kai kawon nata ya hana bacci. Ina bude kofar dakin nawa naga Amarya tsaye da murmushinta ga kamshinta na amarci a tare da ita, kai Yaya Dijah ba karamin ladan Babanmu ta samu ba, abinda zuciyata ta fada kenan sanda na karewa amaryar kallo. 24 Gajiye ce ta saki makara ko? Na tayata 1nurmushin da take yi nin, to in kin idar da sallar sai ki zo, na ce mate to. Ina shaia fatiha na shige dakin nata don kuwa dama na kosa inga Babana in ga yanayin da yake ciki. Yana zaune kan wata shimfidaddiyar darduma, kai da ka ganshi ka san yana cikin farin cikı, an tasa mishi abin karyawa a gabanshi. Na tsuguna na gaishe shi, farin cikinshi a bayyane yake, me ki ke so ki karya da shi? Tayi min tambayar bayan ta gana anmsa gaisuwar da nayi mata. Akwai tea skwai kunu, ge kuma farfesun kayan ciki. Na zuba musu ido ina kallo, can cikin zuciyata kuwa nasan da abinta tazo, ga kuma kayan tsarabar bikinki zan. Na ce, Na gode, a bar min & nan sai Za ni makaranta zan karba in kaiwa 'yar ajinmu. Babana ya ce, "A'a kar6i kici abinli in za ki je makeranta ki diba a nawe." Na ce, To. Hu'un, lalle namiji sai a bar shi, na kuma yarda lalle Mallam ba karamin algungumi ba ac, ashe duk halin naza shima ya iya, ina kallonshi sumu-sumu abin tausayi, ashe ba abin tausayin ba ne, ai inda nasan haka ne da ba karamin gasa shi nayi ba. Ashe dama lafiyarshi kalau? A zuciyata na ce da kin kashe shi dai ba gasawa ba in dai gasewa ne kawai ai dukanmu mun gasu. Ni da kain ba karemin mamakin Babana nayi ba, gaba daya kwanaki ukun nan na dakin Amarya ko rumfarshi ba ye budewa, yana nan a gida a kuma cikin dakinta, 25 yana kishingide akan darduma duk lekawan da zan yi kuma zan hango shi an tasa mishi wani dan abin motsa baki a gaba. In kuma ya fito don yin alwala zuwa Masallaci, sai kaga tana biye da shi tana rike mishi da butar tanfar dai ace gadinshi take yi. A wannan lokacin ba ka iya kwatanta yanayin da Baba Lantana take ciki, in ban da uhun maza? Babu abinda za ka ji ta tana fadi. Namiji? Kai lalle sei a bar su, ashe dai babu wani dan kankani a cikinsu. A haka aka koma dakin Baba Lantana ina daga dakina ina jiwota, "Oh, Mallam ashe lafiyarka kalau ka ke yi min irin wannan abin? Gaba daya ikwanan nan uku ba ka yi fahsi ba ko daya, ina kallonka yau din me ba za ka yi wani motsi ba ne ina yi maka magara kayi shiru ka lullube kai de bergo. Ko kana nufin a kaina ne ba ka da lafiy, amma in a can ne lafiyarka kalau? To i ba zai taba yiwuwa ba, nayi maza nasa yan yatsuna shabbaba na toshe kunnuwana da su don in samu in daina jin maganganun nasu, ko zan samu in yi bacci. Komai na Safara a tsare yake, kullum girkinta yazo zata ba mu lafiyayyan abinci da irin kudin da ake baiwa Baba Lantana tana rainawa, tana kin yin girkin. Ga ta gwanar iya abincin gargajiya ce iri-iri. Su burabusko, su gwate, su dan wake su danbu su gauda su gurasa, su sunasir su wasa-wasa, balle ayi 26 maganar tuwo, sai tayi sati biyu tana girki bata maimaita abinda ta girka ba. Haka nan abin karyawa tuni muka daina sanmakon fito nemanshi, ganin da tayi inä ita nemo mane ranar girkin Baba Lantana, yasa ta kirani ta ce min rinka zuwa nan kullum da safe muna karyawa kin ji, shi dai da ya ajiyeta ranar girkin nata su san wanda suke ciki, na ce mata to. Baba Lantana ta tsunduma. cikin wani irin abu.da bata taba zaton zata tsunduma cikinshi ba, a zamanta da Babara, ga kishiya te kwatsam wacce kuma ta haife ta ga shi tasa hannu ta kalallame shi, in ban da Beban nawa ba dan gayu ba ne, don su wanka da shafa man nan da duk sai tayi mishi, to ba zai yaria ba. Ga ehi tana ganin wadansı irin al'amura a wurinshi wadsnda bata taba tsammanin yana da su ba, sai ta zama kemar wata zareriya, babu abinda take so irin ta samu abokin hirar da zata yi zance da shi don ta rage damuvarta babu. Saboda babu mai zuwa wur inta duk ta kore su sanda ta samu daular gidan miji ita kuwa Amarya sai kai-kawo take yi da 'yan uwa da abokan zama, dan muguntan da take yi mana na kin yin girki muyi takai kawon neman abinda zamu ci yanzu duk ta kau. Ko kadan Safara bata kallon abincinta in ta gama ta ce su zo su ci ta ce to, tunda tare suke ci in bata gama ba ma oho. Za ta ci wani abu nima zata ba ni. 27 Bakin ciki ne ya ishi Baba Lantana, taga kamar in ta tayar da wuta zata iya korar Amaryar nan saboda taga komai take yi ba ta ce mata komai. Ta karbi kudin cefane ta ki yin. girki, ko taga shanyarta a igiya ta zube. Rannan an tashi da safe naji Anti Safaran na cewa Yaya ina kwana? Ko dama a lalace take amsa raata gaisuwar, amma bata daina ba. Yaya ina kwana? Ta sake maimaitawa, sai naji ta ce mata, ke raba ni da wani yaya, yayan mnunafurci, ki kira ni yaya a bayan idona kina yi min munafurci, rike yayarki bana so tunda ai ni ban ma ga wani abinda na girme ki da shi ba. Ta ce, To kiyi hakuri. Taja bakinta tayi sbiru bata. kiranta Yayan oa ta kuma kian sunanta, ana cikia haka ta sake cewa kicin nata ne a ranar girkitita bata yarda wani ya shiga ba. Nan ma ta ce, To sai ta fito de risho dinta in zata dan yi wani abu ta tura a baya kofarta tayi. Ba a gama da wannan ba sai kuma ta fito da wani salon in Safara ta gama abinci ta kawo ta kira ta ba za ta ce ba za ta ci ba, sai ta dauko kujerarta tazo ta zauna tasa hannu ta gutsuri lomar tuwon ta kai bakinta, sai ta fara tauna shi. Sai tayi wuf ta dawo da shi ta tofar tare da fadin, kai tir, wannan tuwon ai danye ne ke ba ki iya komai ba ne a tayuwarki sai jarabar bin miji? Ba ta ce mata. komai ba, rannan dai sai ta gaji ta ce mata da dai kin 28 daina irin wannan abin, tunda kema kin san baida amfani, shi hatsi ai be a yi mishi haka. Sai kuwa Baba Lantana ta zabura ta sake gutsurar weci lcmen te ka: bakinte, tayi mishi tauna daya te maido shi kan asalin tuwon da ke cikin kwanon wanda ite take ci, anyi din an yi wa hatsin rama mishi. Haka kawai sai ki rinka yiwa mutane danyen abinci kice sai an ci dole? To an yi an kuma karawa. Ta sake gutsura ta kai baki ta sake mayarwa cikin kwanon, ina daga dakina ina jin su ban san yanda aka yi ba sai kawai naji an kaure da dambe. Dambe kuwa ra gaske, tunda dukkansu karfafa ne, ko motsi ban yi ba balle in yi tunanin raba su, sai kawai raga an daga Baba Lantana an nanata da kasa, Safara ta haye kan ruwan cikinta tayi ta kirbar bakinta da duka, da ta ga hakan ma bai yi mata ba, sai ta shaketa her sai da wuya ta sa ia bude baki tayi maza ta kwaso gwajaljelon tuwon da ta tauna ta mayar te warba mata shi a baki ta matse bakin sai da ta hadiyo shi. Sannan ta saketa ta mike tayi tafiyarta tare da fadin "Haba, ina amfanin babban da bai san ciwon kansi ba? Ina kyale ki ba ki san kyale ki nake yi ba, to mu zuba shege ka fasa ni da ke." Da daddare Babana ya dawo, ta zaunar da shi ta rattaba mishi bayani, kala bai ce mata ba. Ta sake tunzura zata tasa shi a gaba da masifa, ya fito yazo yayi shimfida a tsakar gida yayi kwanciyarshi, duk da 29 sanyin da ake yi bai tashi ba sai da lokacin zuwa Masallacin shi yayi. Wannan zaman ai' ba dole ba ne, kai Mallam ai dama ba mijin mata biyu ba ne, muturmin da baya iya buda baki yayi magana yaya za ayi ya iya ajiye mata biyu? Kullum balki a rufe kamar na mai ciwon bubu. Gara kawai ka sauwake min ka sake ni ka ji ui ko ba ka ji ni ba? Bai kulata ba, ta gaji da fadan ita kadai ta shiga dakinta ta kama fitar da kaya, ai na ce na daina wannan matsiyacin auren, yau na daina shi ko ka bani takarda ko kar ka ba ni tafiyata zan yi. ina ganin ta gama kwashe kayanta ta tafi na shiga dakin na share yana, na share dattin dakiu tas na ce wa Anti Safara bari in taya ki ki kwashe kayanki ki koma can, da sauri ta ce min au haba? Na ce mata eh. Nan da nan muka bar komai muka koma aikin jidan kayanta muka maida su dakin Innata, dakin da nake ganin kamar babu vani daki da zan so kamar shi, muka gyara komai yayi tsaf gwanin kyau. Gidanmu yayi matukar yin dadi, Anti Safara tayi ta tattalinmu ni da Babana, har ma da Sallau. Sai dai sh1 kam bai iya zama ba, yana ganin Baba Lantana ta kwana biyu bata dawo ba, sai yayi wa Babana sallama. ya tafi sai dai bai fadi inda za shin ba. 'Yan kwanaki kadan da auran Babana, kwanakin da ko talatin ba su cika ba, sai ga Babana har ya yi kyau, yayi fes da shi in muna zaune mu biyu kuwa zai 30 dar rage murya ya ce min, "Oh, ashe lafiyayyar yarinya ku ka samar min? Ubangiji dai ya jikan Ramatu da rahamarse. In ce mishi amin. Randa Baba Lantana ta cika sati biyu da tafiya, raear Yaya Dijah tazo mana wuni da ita da ya'yanta duka, dama dan da Anti Safaran ta yaye Nasiru, rabon Yaya Dijah da yin irin wannan zuwan ni dai na manta. Babana ya wuni cikin farin ciki yana ta ina yaka saka da jikokinshi, itama Anti Safaran haka. Sai wajen. yamma ta shirya zata tafi, ya yi tayi mata addu'a yana sa maia albarka, ita zuciyarta gaba daya ko daga ji kuma kasan har da jin dadin abinda tayi mishi. Da zata tafi sai naji ta ce min ga dan hira nan na kawo miki, ya taya ki zama nayi maza na ce mata to na kama hannunshi na riks nayi mata rakiya muka dawo tarc da shi. Mu'amalla ce sosai tsakanina da Safara, duk da ta same ni a shekaruna na budurci sosai wanda a lokacinmu ma ba a cika samun 'yanmata masu shekaru irin nawan ba in dai ba a gidajen da 'ya'yansu ke karatu sosai ba. Amma hakan bai sa tayi wasa da kulawa da al'emurana dan kankanin canji in ta gani a tare da ni zata tsaya taga ta warware min shi. Haka nan sai aiki ya mana keza gyara abu kaza kar kiyi kaza, kaza da ki ke yi ki daina babu kyau. Abinda na tabbatar shi ne da ita ce ta zauna da ni a shekaruna na kuruciya, to da tarbiya sosai tayi min, n kuma zan fita to bai zamo meta komai ba in ce mata za ni 31 wuri kaza ta ce min kai a'a kina yawan fita ba dab1' ar budurwa mai mutunci ba ne yin hakan. Sai dai in makaranta za ni, in kuwa za ni Makarantar to ko ina da kudina tunda ina sana'ata tana gani zata kawo kudi ta ce min ungo ki kara, in yi mata godiya. A haka sai gidan namu ya sake zama wani wuri mai cike da ni'ima zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali ga kuma girmama na gaba, tana girmama Babana nima ina girmamata, tan kyautata min nima ina kula mata da danta. Gaba daya sai muka zamo muna son junanmu sosai. Rannan aka wayi gari Safara tana yin mashasshara da mura, ban kai gane kan kornei ba saboda ban taba kawowa raina cewar wani abu zai iya faruwa ba, na dai ga Babana yana ta kaiwa da kawowa cikin wani iri yaneyi na tsananin farin ciki, bai isya zama a runfarshi ya wuni kamar yanda ya saba, sai ya dawo gida dubata. Wani lokaci sau daya wani ma ahr sau biyu in zai shigo kuma bai shigowa hannu haka sai yazo oa wasi abinda zai miko min ya ce "Karbi ki wanke muku." in ce mishi To. In wanke in kawo mata ita kuma sai ta ce mun to dibi naki mana, in ce mata to in diba ta ce min kara in naga zan kara in Kara in kuwa ya ishe ni in ce ya ishe ni. Anti Safara da kanta ne ta gaji ta ce min ciki ne da ita saboda Iuran da tayi ta gane ban gane ba, mamaki gami da farin ciki suka taran mun, har ta gane abinda nake ciki. Mamakin me ki ke yi haka? Kin yi zaton ba zai kara haihuwa ba ne? Na ce, "Eh, to ai na gane kamar ya girma." 32 la sake wani murmushin tare da fadin "Don ya haifi Hadiza sai ya tsufa ko kuwa dai dun kin ji matarshi tana yi mishi sharin bai tabuka komai? Shira nayi ban yi magana ba, don kuwa naga kamar ta wuce sanina. sNa dai san kawai ba karamin farin ciki nayi ba, saboda ganin da nayi nima zan samu kani ko kanwa, in musu nima irin abinda Yaya Dijah take yi min na kulawa da tausayawa. Muna cikin wannan halin sai ga Baba Lantana tana shigowa da kayanta kwararam-kwararam tana ajiye su a tsakar gida, tana komawa tana shigowa da wasu. Ta rame tayi baki tanfar wacce ta tashi daga jinya mai tsanani. Yaya haka kuma naga an shigar min claki? Wannan wane irin neman magana ne? ba sakina aka yi ba, ba komai ba sai kuma kawai daga na fita da kayana ayi maza a shige nin daki? Ke Yachuwuna kina ganin irin wannan neman maganan ko? Nayi maza na kalleta a firgice na soma gaisheta cikin wani irin yanayi saboda rashin sabo da yin magana da ita. Babana ya fito daga dakin Safara ya wuce zai fita bai kulata ba ta bishi da kallo, Mallam kana gani na dawo ba za ka kula i ba? shiru yayi yana tafiyarshi, tayi maza ta sake ce mishi to kayi mata magana ta fita daga dakina ta bani wuri in sa kayana don kar hakan ya zama wata fitina a tsakaninmu. Bai tanka ba yayi ticewarshi ya tafi, bain ciki ya kama ta ta ce "Wannan shirnu na Mallam, wannan shiru na Mallam ashe ba zai daina ba?" Ta jinjina kai ta rasa abinda zata ce. A zuciyata na ee, da dai kin san abinda 33 zai faru kenan da ba ki yi mishi abinda ki ka yi mishin ba. Baba Lantana taja ta tsaya cikin wani irin yanayi na rashin sanin abin yi, da dai ba su taba gwada yar kashi da Safara ba, da tayi wani yunkuri. To babu hali, tana shakka gashi kuma Safara sai kai kawo take yi ko kallon inda take kuma bata yi ba, balle ta tanka mata. Ta gaji da tsayuwa tayi kamar ta kwashe kayan nata ta koma inda ta fito, ban san kuma me ta tuna ba. Sai naga ta bude wancan dakin tasa kayan nata a ciki. Ta gyara tayi zamanta. Tsoro yayi matukar kama ni, ko me yasa Baba Lantana tayi irin wannan canzawar? Mace ce mai fadin rai, nuna isa da ganin kowa ma bai isa ba, wani abu taje ta gano ya sa ta tayi wannan canzawar ko lkuwa dai wani abin take shiryawa? Na gama abincin daren' da nayi don tun zuwan Anti Safara mafi yawancin girkinta ni take sawa in yi, to balle kuma yanzu da take fama da laulayin cikinta. Ina gamawa na zubawa kowa har ds Babs Lantanan na kai mata nata na yiwa Babana shimfidar tabarma a tsakar gida inda ya saba zama, na ajiye mishi nashi a nan. Yana dawowa daga Masallaci ya shiga wurin Anti Safara yayi mata sannu da jiki, ya dawo ya hau kan tabarmarshi ya zauna ya soma cin abincinshi. Baba Lantana ta fito tazo daga bakin kofarta tana yi mishi magana, bai ce mata komai ba. To ka shiga daga ciki mana Mallam, wannan hirar da ka ke yi a waje ai ya wuce ka'ida." 34 Bai ce mata kala bá, har bacci ya dauke ni suna nan a wurin shi yana kan tabirma a zaune, ya jingina da jikin bango, ita kuma tana daga bakin kofarta. Ban san yanda aka yi ba, cikin dare ne kawai na farka a dalilin buga minkofar dakina da take yi da iyakacin karfintai tana gaya min wai in fito in ga abinda Babana yakeyi, girkinta ne amma gashi nan ya sake ta ya shige dakin wannan tsinanniyar matar yana yin abinda babu kyau.

Chapter 2 of 11