Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 11
Duk da katse min baccin da tayi ta kuma hana ni sake runtsawa saboda buga min kofar da taki dainawa ban motsa ba, balle in yi yunkurin saukówa daga gadon nawa in fito. Ban saniba ko ta gane ba zan fito ba ne yasa ta bar tawa kofar ta koma buga tasu, a zuciyata na ce dama tuntuni hakan kikayi da yafi miki. Girki nane fa Mallam, yau a wurina fa kake, nan take ta soma kuka tana fadin "Ban yafe maka ba Mallam. Bazan yafe maka satan kwanan da kayi min kaje wurinta ba. Ban taba ji ko ganin Baba Lantana tana kuka ba a zaman da nayi da ita ba sai rannan, kuka kuma bana wasa ba, ko da yake babu wata kyakkyawar alaka ko wata kauna sa ke tsakanina da Baba Lantana. Amma kuma hakan bai sa naji dadin yansa Baban nawa yayi ba duk da dai itama bata taba yiwa wani adalci ba, a lokacin da ta samu damarta. Gari na wayewa nayi maza na gama abinda zan yi na suri jakata na saba a kafada na fita gidan na bar Baba Lantana a tsakar gida a tsaye rike da shirgegiyar tabarya 35 a hannunta, tana rantsuwar sai dai in ba za su fito ba, amma sai ta rafke su da tabaryar hannun nata. Na wuce na tati makarantar da nake zuwa TP, wato (Teaching Practice) saboda gab nake da kammala karatuna a Makarantar addini mai zurfi. A hanyata ta dawowa gida zuciyata tunani take yi kan yanda ta kare tsakanin Baba Lantana da su Babana. Ina isa gida ban san yanda aka yi ba sai kuma naga Baba Lantana da na bari da tabarya a hannu da kulu a goshi, ban tambayi Safara yanda aka yi ba, to balle kuma Baba Lantana da ban ma iya yin wata magana da ita ba. "Kin dawo ne?" Na ce mata "Eh." "To ga fura nan da nama Babanki ya aike da shi, na diban mii, nace to sannu. A zuciyata nace ko ba komai dai yanzu ina da kaso a abinda Babana yake kawowa. Na gama cin naman ina shan furar sai ga Baba Lantana ta fado cikin dakin nawa, nayi maza na mike tsaye saboda tsoratar da nayi, tunda ban taba ganin ta shigo dakin nawa ba. Ban sani ba ko itama ta gane tsoratar da nayi da itan ne yasa ta fara yi min bayanin avinda ya kawo tan cikin sauri kinga kulun goshin nan nawa ko?" Na daga ido na kalli kulun goshin nata da take tabawa da hannunta, kan in ce mata na gani sai kawai naji ta ce min, To Mallam ne yayi min shi. Nayi maza na sake kallon kulun saboda razanar da nayi da jin bayanin nata, kulun ya amsa sunan kulun ban san yanda aka yi ba naji bakina ya ce mata sannu, tayi maza ta ce yauwa. 36 A tsakanin wannan lokacin ba sai an gaya min ba, ni da kaina nasan Baba Lantana tara cikin wani halinba tsananin bacin rai kowane lokaci a cikin kuka take. Ashe haka Mallam yake? Tafdijam! Ashe shiru- shirun nan na shi ba na kalau ba ne? dama fa nasha jin ana cewa ka ji tsoron mai shiru-shiru, ban taba yarda ba sai a wannan lokacin, yanzu ne na gane lale Mallam munafuki ne. Ko kadan bana jin tausayin Baba Lantana, saboda azabtarwar da tayi mana ni da Bbana, ta wulakantamu ta tozarta mu, gara ma ni komai tayi min da sauki tunda a kuruciyata tayi min, amma shi Babana ta same shi ae da girmanshi da mutuncin shi a tsakanin mutanen unguwa. Kowa ya 1a girmnamasbi saboda ya kame kanshi bai shiga harkar kowa, bai sa ido kan abinda wani yake yi, balle ya yi gaba ya bada labari. Bai sa ido kan abin wani ya gamsu da abinda yake da shi amma zuwan Baba Lantana gidanmu sai da ta maida shi abin kwatancen mutane. Komai aka yi sai ka ji sun co kai haba, kar ka maida mu Mallam Habu mai anatir Mana, to amma duk da haka ba na jir dadin ganin yanda yake yi na hanata kwananta da yake yi yana barinta tana kwana ihu tunda a karatun da ake yi mana Malamai suna yin bayani kan rabon kwana a tsakanin mata wajibi ne abinda kayi a can ne bai zamo lalle sai kayi shi a nan ba. Amma akaiwa mace kwanan wannen dole ne, to shi Babana baya kaiwa. Da dai ace ina cikin masu baiwa Babana shawara, to da nace mishi cikin biyu ya zabi daya. 37 Ya yi ko dai ya rinka shiga dalkin Baba Lantana yana kwana tunda dai zaman aurenshi take yi ko kuma ya ce mata ta tafi. Ya sake ta don ya sauwakewa kanshi al amura. Sanin da nayi hakan da ake yi bai yi ba, ya sa ni tafiya gidan Yaya Dijah nayi mata bayani, a yatsine ta kalle ni to ke ina ruwanki? Inta ji babu dadi ta tafi mana. Na ce, A'a Yaya Dijah, ai ba don ita nake maganar ba, nayi mata gwargwadon bayanin da zan yi mata, ta ce to naji in na zo gidan zan yi magana da ma ina so in zo wurin Baban na ce mata ko na kama hanya na dawo gida. Yaya Dijah ba ta zo gida ba sai a ranar Laraba da safe, muna zaune a falon Anti Safara inda nan ne wurin zaman Babana a kowane lokaci. Hira muke yi cikin yanayi na jin dadi ni da shi da Yaya Dijah, yayin da Anti Safara ke kicin tana shirya abincin rana, ita kuwa Baba Lantana da yanzu ko tsakar gida bata cika fitowa ba take dakinta. "Oh Baba, yanzu har a irin alherin nan da yake shirin samunmu na Mero ma zata samu kani a bayanta zamu sake samun dan uwa ke 'yar uwa, maimakon mu biyu ko mu koma mu uku ba za ka yi hakuri ka gaya.mana inda danginka suke ba? Ba don mu kadai ba Baba ba ma don mu ba tunda mu kam ni da Mairo ai mun riga mun mallaki hankulanmu, mun fuskanci rayuwa mun kuma fara gane yanda take ba, komai dan Adam yake so yake samu ba. Don wadannan da za su zo daga baya Baba gaya mana inda danginka da garinmu yake in wani laifi suka 38 yi maka i Hadiza yarica na roke ka ka yafe musu ta kai menene? Ai ya wuce Baba kayi hakuri ka... Tayi maza tayi dib taja balkinta tayi shiru ta bar Karasa maganar watakila sai lokacinne ta daga ido ta kalli yanayin da ke fuskarshi wanda ni tunda ta fara maganar nasa na gani shi yasa nayi ta taba ta bata gane abinda nake nufi ba. Ta tashi ta bar dakin saboda daurewar fiaskar tashi, ta kai matuka nima na tashi na biyo ta muka dawo dakina muka zauna tayi kuka har a gaji tnyi shir ta iar hawayenta. Kwana biyu bayan nan Anti Safara take bani abarin cewar Babana ba lafsya te da shi ba, kartin hali ne kawa yake yi yasa ake ganinshi yana yawo. Na ce, To. A zuciyata dai fatana da addu'ata bai wuce ya zamo ba maganar da Yaya Dijah tayi mishi ba ne yake nema ya tayar mishi da jikin. Na rasa yanda zaa yi in fuskance shi da maganar rashin lafiyar tashi, saboda tun daga. ranar da na raka Yaya Dijah tayi mishi wannan maganar fuskarshi daure take. A zuciyata na kudurawa Kaina ba zan sake yarda Yaya Dijah ta ce min za ta yi mishi irin wanan maganar in bar ta ba, tunda baya so, shi kenan a kyale shi, yan uwanshi shi yasan abinda ke tsakaninsu. Abunda ya fi komai muhimmanci wurin da uba ne, tunda shi ne asali to mun gode tunda muna da shi kowa yasan muna da shi mun kuma san shi, mun rayu tare da shi, babu wanda zai yi mana gorin rashin uba, sai na rashin 'yan uwan uba. 39 Wasu suna nan su ba su ma san ubannin nasu ba balle suyi maganar danginshi suna nan kila a dadin su ma kuma suna rayuwarsu don haka na hakura itama zan gaya mata ta hakura suma yan bayan in sun hakura kamar yanda suka same mu mu ma akan hakurin. Rannan da daddare Anti Safara ta buga min kofa gabana yayi mummunan yankewa don kuwa na tabbatar jikin Babana ne yayi tsanani yasa aka tashe ni tunda tun da rana ina kallon iin wahalar da yake yi akan lai kawon numfashinshi da bai karasawa ya sauka cikn ciki sai dai a Kirji. Babu yanda Yaya Dijah da naje na kirawo a dalilin jikin nashi bata yi da shi ba akan muje asibiti ya ki yarda. Da sauri na 6alle kofar na fito na ufi dakin Anti Safara da ke bude a kasa, na samu Babana na zaune a cikin yanayin rauni mai yawa. Ko zama da kyau bai iyawa saboda ya riga ya rasa karfi a tare da shi, numfashi sai kaiwa da kawowa yake yi a tsakanin kirjinshi da makogoronshi. "Sannu Mallam, Ubangiji ya baka lafiya." Tana sannun tana share mishi hawayen da ke diga daga goshinshi, tana kuma kuka. Jikina ya dauki bari saboda yanda al'amarin ya tuna min da yanda naga Innata a daren da zata bar duniya. Da gudu na juya na bude kofa na bar gida. Nufina wai in je gidan Yaya Dijah in kirata tazo ta taya ni ganin abinda Babana yake yi, sai kawai muka yi kicibis da Isiyaku. Ban san daga ina yake ba,a wannan tsohon d aren ina za ki haka Anti? Me ya same ki ki ke kuka haka? Ban 40 iya ba shi amsa ba jikin Baba ne ya tashi? Nayi maza nace mishi "Eh" To ina zaki yanzu sha biyu saura kwata ne fa na dare. In asibiti kike so a kai shi ga makwabta." Lolkacin nena tuna ashe ma Baba Baidu ya kamata in fara gayawa ba wani ba, balle Yaya Dijah da ba ma kusa muke ba, tunda ance makwabcinka na kusa shi ne mutum na farko da ya Kamata ya taimake ka, in har ka shiga halin bukatar taimako. Tare da shi muka je na fara buga kofar gidan Baba Baidu, sai da ya ji ya bude kofar dakinshi zai fito sannan ya ce min, Bari in nemo mana motar da za ta kai mu. Na ce mishi "To, Isyaku na gode." Tamfar dai ba shi ne Isiyaku da na share ba na ko amsa gaisuwarshi ba. Ina tsaye a tsakar gida bayan na shiga dakina nayi shiru na debo duk kudin da nake da su, kuka mai yawa nake yi saboda yanda nake jin Babana yana magana cikin jarumtaka da kyar da kyar. Amanata yake baiwa Baba Baidu da matarshi, ni Mero sa shiga uku zan rasa uba mahaifi kamar yanda na rasa mehaifiyata yau ya ya zan yi? Gare ka nake bauta Allah, gare ka nake neman taimako ya Ubangiji, abinda kawai nake ta nanatawa kenan. Ana cikin hakan naji zuciyata tana zargina da cewar ni da Yaya Dijah muka fara haddasa mishi ciwon nashi da muka tasa shi a gaba muka yi mishi maganar da baya so. Ina yin wannan tunanin na sake rushewa da wani sabon kukan na nadama da bakin ciki. Isyaku ya shigo da sauri. 41 Ga mota Anti na samo." Ya wuce cikin dakin ya gaya musu. Babana bai iya takowa da Rafafunshi ya fito ba saboda karfi ya tafi sai da aka rirriko shi aka fito da shi muna isa asibiti aka ba mu gado. Dama kuma shi kwastoman asibitin ne, fayil dinshi aka dauko aka dora bayani akan wanda yake ciki. Mun kwana muk wuni a asibiti babu alama na samun sauki a tare da Babana, hankalinmu ya kai matuka wajen tashi, bar gara nima akan Yaya Dija. In ban da kuka babu abinda take yi, ni na tayar mishi da ciwon. Na ce, A'a Yaya Dijah, dama bai da wata lafiya, ba ki ji bayanin da Anti Safara take fada ba, na cewar ya dade ba ya bacci da daddare. A'a amna ai bai tsananta ba sai bayan da nayi mishi maganar duk kalaman da nake gayawa Yaya Dijah bai sa ta samu na suwa a tare da ita ba. Likitoci ne suka yi ta zuwa duba jikin Babana, kusan duk wanda yazo duba shin kume ya kar tafi ne a yanayi na tausayawa da fadin kai lalle Mallara Habu yana jin jiki, Ubangiii yasa kaffara ne. Wai kuma a wannan lokacin ne da ake cikin wannan al'ama rin naji Baba Lantana tana yiwa wata mata da in banda a zuwanmu asibiti ban yi zaton ta taba ganinta ba tadin Baban da al'amarinsu. Ai ni don dai kar a ce ban zo ba ne kawai amma 1n ba haka ba ai ko mutuwa yayi bani da wata asara mutumin da yake daukan girkinka yana kaiwa kishiyarka kana ji kana gani ba ka da yanda za ka yi. Yaje yana yin abin nan da ita. Ni kam ai alhakina ne ya kama shi yanzu ba sai suje suyi ba in gani? Kin ga tun 42 kafin yayi auren nashi sai ya yi wata biyu wata ku ba kula ni ba, a hakan... Ganina da suka yi ya katse hirar tasu ganin da nayi in sallami Baba Lantana in ce ta koma gida ita kadai ba zai zamo mai sauki ba, zai kuma kara bayyanar da rashin adalcinmu mu da Babanmu da ke fama da kanshi. Wanda ita take kokarin baiyanawa koya ya zama sheda akai, bisa haka sai na hada ta ita da Anti Safara nayi musu magana akan su koma gida wanda da kyar suka yarda hakan. In na tsaya cewa mun shiga wani hali ni da Yaya Dijah dama duk wani, wanda yake tare da mu a tausayawa to na tsaya bata bakina kawai nake yi. Ina zaune kan kujerar roba ina tashe da Babana bayan tafiyar Yaya Dijah da mijinta, in banda kuka babu abinda nake yi na roke ka ka yafe min abinda nayi maka. Baba abinda kawai nake iya fadi kenan ban ji lokacin da ya shigo ba saboda shagalar da nayi da abinda ke gabana sai ganinshi kawai nayi a tsaya ta daya gefen kusa da Babana. A daga ido na kalle shi Mubarak ne yana cikin natsuwa mai yawa yanayin da ke fuskarshi ce ta kara bayyanar da hakan. "Ubangiji ya baka lafiya Baba, yasa kaffara ce. Shi ciwo ai rangwame ne, domin kaffara ce ga zunubai sannan jikin naka ma da sauki ba haka nayi zaton ganinka ba." Babana ya dan daga ido ya kalle shi saboda jin kalamin nashi, ya sake yi mishi sannu kafin ya sake 43 daidaita tsayuwarshi, ya karanto addu'ar da ake yi wa mara lafiya. Kafin yayi mishi sallama ya juya da nufin tafiya. To zo mana, ban iya yi mishi musu ba duk da mun dade kwarai ba mu ga juna ba ban da haka ma mun dade da fita hanyar juna. Tun bayan abind ya faru a tsakaninmu, sai muka shiga kiyayyar juna, ai ba nisa za ki yi ba, ya gaya min hakan don kara karfafa min in zo din. Ke haka ake yin jinya ne? Nayi maza na kalle shi don in ji ta inda kuskuren nawa yake in gyara, kin tasa shi a gaba sai kuka ki ke yi, kina rokonshi gafara? To a kan me ki ke yin hakan, ki, Rara kashe mishi jiki ko ki kara-tsoratar da shi, ki karya mishi zuciya? Shi majinyaci karafa shi ake yi da kalamai na karfafa zuciya, ba yi tayi mishi kuka ba, shi ciwo ma da ki ke ganinshi be shi ne mutuwa ba fa. An yi yafi a kirga mai laifiya ya mutu ya bar mara lafiya a kwance, kin gane? Nayi maza nace mishi eh. Yanzu ke menene damuwarki da ki ke wannan kukan? Ban iya boye mishi ba ko in ce zanja mishi aji saboda halin da nake ciki, sai kawai na gaya mishi Babana bai da lafiya. Gashi an kawo mu wurin da kowa ya zo ya ganmu sai ya ce uh' uh hh lalle Mallam Habu yana jin jikı, a dakin da yake din ma na gobe da nisa ne kusan kullum sai an yi mutuwa a dakin dazu ma an yi wata mutuwar. A hankali ya ce min, to kiyi hakuri ba ni in yi magana a canza muku dakin a kaiku inda za ki dan samu natsuwa shima Baban ya samu kulawa ta musanmman. 44 Koma wajen shi ina zuwa, ban ce mishi komai ba na tashi na tafi na dawo na samu Babana a yanayi na canji. Nan take na tuna da addu'ar da Mubarak yayi mishi wacce na taba ganin bayanin da Manzon rahama yayi a kanta cewar duk sanda mai duba mara lafiya ya karantawa mara lafiya ita, Ubangiji zai saukar mishi da wani rangwame a halin da yake ciki, ko da kuwa cutar ta ajali ce. Nayi maza na matsa kusa da shi. "Sannu Baba." Ya amsa a hankali "Sannu Yachuwuna, kina ta wahala da ni, Ubangiji ya yi muku albarka." Na dauko kofi na tsiyayo kunun gyada na zauna kusa da shi ina gauraya kunun da cokali don ya yi sanyi. "Bari in kurkure maka baki ka dan sha kunu Baba, ka dade ba ka ci komai ba." Ya dan sha kunun kadan kafin ya daina kar6a nima na kyale shi ban matsa ba tunda dai ya dan sha Na gyara zama a kan kujerar da nake zama tare da jingina a jikin gadon nashi ban san yanda aka yi ba, sai ji kawai nayi ana ta shina. Nayi maza na bude idona da gaske ashe bacci nayi, ga dukkan alamu kuma yayi nauyi, don na dan ji canji a tare da ni. Na kalli Nos din da ta tashenin bisa zaton ko lokacin shan maganinshi ne yazo, sai naji ta ce min "Bari mu canza muku dakin ko?" Nayi maza na kalleta duk da bayanin da Mubarak yayi min akan canjin dakin ban dauka da sauri ne haka ba. 45 Yayanki ya ce a maida sBaba privater ward. " Na ce mata To. Aka dauke mu aka maida mu private ward. Mu kadai nea wurinbga tsafta ga kulawai ta musamman sai dai maimakon saukin das Babana ya dan samu ya dore sai kuma jikinya: kara táshi, kasancewar likitoci baba tsinkewa a wurin sai sukal yi ta: kai kawo suna bincike kan oalanarine nashi, ina daga gefe ina kallonsu cikin natsuwa yayin da zuciyata take ta faman karanto addu'o'i iri-iri, kafin gari yawaye har an canza mishi magungunan da yake sha gaba daya. Ganin haka ne ya sani matsawa kusa da shi sosai lokacin da wani lokaci ya sake shigowa don duba yanayin jikin nashi da safe, sanmu da aiki doctor. Ya juyo ya kalleni, yauwa sannu ko? Ya ya jikin nashi? Na yi màza nace da sauki, yanayin da na gani a tare da shi ya karamin kumarin yi mishi tambayar da nake son yi mishi, Dr. An ganw wani abu ne a tare da shi da yasa aka canza mishi magu agunan nan? Sai dai ya daga ido ya kalleni kafin ya maida kallonshi ga aune-aunen da yake yi, mara lafiyan mene ne dinki? Na yi maza na ce mishi, babana ne mahaifi, to me za ki yi in kin sani? A hankali na ce babu komai, nayi shiru ban sake ce mishi komai ba, ya ci gaba da abinda yake yi har sai da ya gama zai fita sai ya sake kallona ya ce min, me sunanki, na ce mishi Maryam, har ya yi kamar zai juya ya tafi sai naji ya ce min, menene aikin zuciya a jiki? Cikin nutsuwa na ce mishi harba jini zuwa sassan jiki, to daya ko biyu daga cikin jijiyoyin da sukeyi mishi wannan aikin ne ya samu matsala. Jikina ya yi sanyi sosai da jin bayanin nashi amma da yace min kin gane? Sai na yi karfin halin ce 46 mishi eh kamar in sake yi mishi wata tambayar sai naga to kar ya ce na dameshi don halka na hakura nace mishi, na gode, ban san tunanin da ya yi ba wanda ya sashi ci gaba da yi min bayani, bangaren hagu na zuciyarshi ne ta samu matsala har ya dan kumbura kadan saboda jjiyoyin wurin basa aiki sosai shi yasa numfashi yake yi mishi wahala. Bayanin da ya yi min ya sani tambayar shi, to yanzzu menene abin yi Dr? Za mu yi mishi ailki nę mu gyara Jjiyoyin.... bai gama yi min bayanin ba sai ga Mubarak ya shigo duk da sanin likita. ne ko kallonshi ban yi ba balle ya ce bari ya gaisheshi na juyo da kallona gareshi da nufi gaisheshi saboda mutuncin da nalke ganin yayi min na kulawar da nake -ganin ya nuna a kan rashin lafiyar babana, wani irin lalataccen kallo naga ya yi min, jkina ya kara yin sanyi cikin zuciyata ina tunanin laifin me nayi mishi, sai kawai na ji ya ce min, shi. ma wannan din saurayinki ne? Gabana ya yi mummunan faduwa nan take kuma na ji mummunan bacin rai a zuciyata, wacce irin mummunan magana ce wannan, ina fama da jikin babana ya kalleni ya ce, wai ina samartakan, me ya maidani? Nayimaza na kawar da maganar tashi daga cikin zuciyata na dai kudunawa raina kamewa in daure mishi fuska sosai watakila don yaga na dan sakar mishi ne yasa yake so ya yi min wulakanci irin wanda ya saba. Yaya Ibrahim ya iso tare da yaya Dija kamar yanda suka saba yi kullum ta zo ta tayani mu yi mishi abinda ya dace sai su tafi sai lkuma ta gama abinda zatayi sai ta zo mana da abincin rana daga gida kuma Anti Safana take zuwa mana da kunun gyada da baba yake sha sai da 47 daddare Yakumbo Halima ta kawo mana abincin dare ita kam baba Lantana ko tazo da wani abu bana yarda ta baiwa babana saboda na riga na jita tana fadin alhakinta ne ya kamashi banda wannan ma na ji ta tana fadin' ko ya mutu bata da asara, ashe Alhajit Mubarak ya zo? Nayi shiru ban amsa mata ba to me ya sa kika yarda yad awo da mu nan? Ban tsaya yi mata wani bayani ba na ce mata ki yi hakuri mu ne zamu biya, bata sake yin maganar ba sai ta tambayeni, to yaya kuka kwana da jikin nashi? Ban boye mata ba sai nayi mata gaba daya bayanin da likita ya yi min, dama ana yin irin wannan aikin ne? Ta yi min tambayar cikin wani irin yanayi, na ce nima ban sani ba tana jinnace ban sani ba ta soma kuka, ban iya bata hakuri ba kukan nima na shiga yí muka hadu muka yi sai da muka gaji muka yi shiru don kanmu. A sallameshi kawai, nayi maza na kalleta a sallameshi" yaya Dija mu yi yaya da shi da wannan numfashi nashi? Ai ba gida zamu maidashi ba wani asibitin zamu sake mishi in da za a bashi magani ya ji sauki ba tare da an yi mishi aiki ba, kin taba ganin wanda aka yiwa irii wannan aikin dą sukace za su yi mishi ná gyara jijiyoyin zuciya? Nayi miaza maca mata uh-uh ta ce to. Gaba daya muka sake tsundurma cikin wani hali na kunci da danuwa. Mubarak ya sake dawowa shi da abokinshi Amiru kulawarshi da tsayawarshi kan al'amarin babana abin sha'awa ne don kuwa gaba däya ma'aikatan wurin sun dauka shima dan babana ne komái yake yi baya sauraron kowa duk abinda aka ce za a yi sai ya ce a yi sau biyu ina zuwa wajen sayen maganin da aka 48 rubuta sai su ce kudinku da kuka ajiye bai kare ba na luma san shi ne ya ajiye kudin amma a kame kwarai nake da shi in ba shi ne ya tambayeni wani abu ba bana tanka mishi, shima kuma ba sosai yake shiga harkar tawa ba sai ta kama ina dai kaffa-kafia da sh saboda na riga na sanshi na kuma kara ganeshi shi mutum ne mai iya wulakanci a ko ina kuma a kuma ko da yaushe a shiryc yake ya yi min in ba haka ba banga dalilin da zaisa ya kalleni a halin da nake ciki na rashin lafiyar babana ya ce wai a asibitin ma samari nakeyi. Cikin natsuwa da girmamawa na gaida Amiru, yaya mai jikin? Na ce mishi da sauki, ashe aiki za a yi mishi ko? Na dean yi jim kadan cikin tunani kafin na ce mishi, anya? Anya wane iri? Ya yi min tambayar cikin wani irin yanayi na tsatsuwa mai yawa, na sunkuyar da kainaa saboda yanayin da yake kallcna a ciki sai naji ya ci gaba da yin magana, ba yanzu muka fito daga wurin likitocin da za su yi aikin ba ni da Alhaji Ahmad? Ai ya riga ya gama maganar da su har ya yi setting din bill din da suka bayar baki san komai bane a kai? Ban iya cewa komai in banda sa hannun da nayi na soma share hawayen da suka Soma zubo min. Ban sani ba ko ganin hawayen nawa ne ya sashi saurin juyawa wajen Mubarak din, kai baka yi mata bayanin komai ne? Ya ya za ka tsaya kan yiwa mahaifinta aiki irin wannan ba tare da ka yi shawara da ita ba? Kuma. mcke tsakaninka da ita tunda dai ka hadiycshi ka zo ai sai ka bar komai ka fuskanci maganar rashin lafiyar kawai in ya koma gida sai ku dora daga inda kuka tsaya. 49 Har a mu'amalar da takeyi da samari sai in yi hakan dai ta? Gabana ya fadi saboda jin mu'amala da samarin da ya ke ikirari, ba sha'anin gabanta take yi ba ba sai in kyaleta nima in yi nawa ba? Wani irin mummunan tsaki Amiru ya ja kafin ya ce mishi, kaif halinka kenan a ko ina a ko wane hali a kuma kowane irin yanayi wai kana iya yin kishi. Ran Mubarak ya soma baci da jin maganar tashi a fusaceya soma ce mishi, a'a kai Amru kar kaja ta raina ni fa wane irin magana ne wannan? Ni kishi nakeyi a kanta? Yanzu kai baka ga irim abinda suke yi ita da wannan likitan da muka samu a nan ba tana yi msihi magana una wani yauki tana wani kakkashe

Chapter 3 of 11