Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 11
ai ba sai an sayi hakinta ba. Ana cikin haka aka soma rade-radin ango ya dawo ango ya dawo kan kace meye wannan har labarin ya bazu ko ina ango ya dawo, ai kuwa dai dama na san da kyar ace bai dawo ba yau, kai wannan ango da zumudi yake, maganganun mutnae daban-daban ne wannan. 110 Kan kace meye wannan sai na jiwo muryar tsiyaku a falo yana gaida jama'a, wani abu kake so ne suna tambayarshi ya ce a'a yalla6ai ne ya ce in shigo in gani in mutane sun danyi sauki ya shigo, ata mai iya shege ta ce mishi, jeka ka gaya mishi bamu yi sauki ba muna nan cike a wurin. Gaba daya suka kwashe da dariya suna fadin, ke dai baki da dama, ita kuwa tana dariyar tana fadin, a'a to haka kawai da rana tsaka ba zai jira abokai su kawoshi ba? Ba fa saurayi bane ta ce, eh ko ba saurayi bane ba zai shigo yanzu ba. Wajen karfe hudu da rabi aka soma walimar maza a masalacin unguwarmu wanda dama yafi kusa da gidan Alhaji Muhammadun don shi ya gina shi walima sosai aka shirya don saniya sukutum aka yanka dominta banda ciye-ciye da abubuwan sha iri-iri malamai kuma daga wurare daban-daban aka gaiyatosu. e Ana cikin haka Isiyaku ya sake shigowa falon, wai ina anti Asiya, tayi maza ta ce mishi gani nan, wai ince miki in babu matsala yana so ya shigo. Ta ce, to to kaje ka ce mishi ya danyi min hakuri kadan, Isiyaku yana fita ta mkie tace, kai jama'a surukuta fa ba wasa bane bikin nan ai munyi shi mu dan ragu mu koa gidan Hadiza, wasu suka ce ka nufi gidanka ma kai ai yamma ta riga tayi, a can gefe kuma wasu suna Rorafin wane irin rashin hakuri ne wannan ko bai yi hakan ba ai za a tafi a bashi wuri. Isiyaku ya sake shigowa, anti wai gashi duk wacce zata tafi a bata atamfofi ne wadanda akayi don bakin, hoton ango da anmarya ne a jiki da hakan ya kashe bakin mitar da suka soma yi mishi nan da nan aka shiga rabo, 111 bayar kowacce ta karba sai ta wuce ta tafi tana murna da godiya da fatan karin budi haka a dawo suna ana facin amin amin, kafin karfe shidan yamam sai ya zama babu kowa daga ni sai Hasiya Jibrin sai ko ita anti Asiyan saboda suna kokarin ganin komai yayi tsaf, a haka kuwa Mubarak ya shigo ina jin gaisuwar da ya tsaya yi da su nayi maza na jawo gyalena na lullube kaina, yana shigowa bai tsaya yin komai ba ya durkusa a gabana ya sa hannu biyu ya yaye lullubin gyalen nawa ya sake sa hannunshi na dama ya ture dankwalin dake kaina kafin ya sake sa hannun nashi ya damki gashin da ke gaban goshina ya iike amma ba damka mai karfi ba, addu'o'i yayi ta karartawa sai da ya gama ya tofa min a fuskata sannan ya mike ya fita, yana fita anti Asiya ta shigo tayi min sallam ta tafi sai muka zama dagı ni sai Hasiya Jibrin mai ji an mijinta ya zo daukarta ita ce ta kara gara min komai ko ina ya zama sai kamshi yake yi kasancewar ilama ta samu wata a gida su ma kuma suna fafatawa ya a iayi te hapi shawarwarin da take ganin tamkar za su yi min amtsni na ce kai ai dai Hasiya nafi son zaman lafiya a kan rikicin nan ni yanzu ba na son bacin rai na ri za na gaji da shi, ta ce to ai bashi da dadi ni su din ne gadara ne da su sai su rinka fadin mai mazansu aka aura, nayi daríya kawai bance mata komai ba. to Kafin a yi sallar magariba shigowar ango biyu shi ne ma ya bada mtoar da ta maida Hasiyan gida tare kuma da yi mata alheri. Yana idar da salar magariba ya sake shigowa, kin yi salla ne? Yana daga tsaye ya yi mint ambayar na ce 112 mishi eh, ya ce to bari in koma wajen wa'azin nan kar su Abdulhamid su sani a gaba don ba wani kirki ne da su ba ga sa ido, na yi murmushi na ce mishi to, amma ai kin san in anyi sallar ish'ai zamu shigo tare da su ko, zasu rakoni sayen bakin amarya, ban ce mishi komai ba ya sake juyawa ya fita, ni da kaina tunani nake yi cikin zuciyata ina tambayar kaina kot a ina yake biyowa yake wannan zirga-zirgar oho? Ko da yake Mubarak bai bar kawaen da na zo da su daga Gaidan sunz auna ba sai ya ce aje da su in gari ya waye zaije ya yi sallama da bakin gaba daya zai hada har da su ni kadai din sai nayi shiri na tunda ashekaru baya can na taba yin kawancen su Jumare su Hasiya Jibrin, na kara gyara kaina ko da dai dama akwai kwalliya mai kyau nake wacce kuma ban dade da yinta ba ga kuma kanshi mai dadi a tare da ni. Ina jin sanda suka shigo falon saboda sallamar da suka yi sai dai ban yi musu amsawar da zasu ji ba daga falon suka zauna a kan kujerun dake wurin, to ina amaryar take? Kai Alhaji Ahmad to ka kori 'yan matan amarya yaya za a yi a sayi bakin amaryar? Maimakon ka barsu in munzo mu maidasu? Ai sai ka fito mana da ita. Mubarak ya leko dakin da nake a takure cikin lullu6i zo ki basu ko ruwa ne Maryam in kuma da wani abu ki hado musu, ban yi musu ba na tashi na shiga kicin na shirya musu 'ya'yan itace a plate daya sai da na cikasu da nau'o'insu kala daban-daban sannan na cika wani plate din da kayan tsarabar amarya na zuba soyayyan naman rago da yaya Dija ta sa a kawomin a wani plate din na hadasu kan wani madaidaicin tirem ai kyau na 113 kawo musu, maimakon in yi shiru kawai in ajiye musu sai na manta na kara gaishesu, Mubarak ya ce, shi kenan ta hutar da ku sayen baki, Abdulhamid ya ce, a'a a'a kai kayi mata wayo ka korar mata kawaye ka kuma sanyata aikin da yayi dalilin da ta yi magana don haka ga kayan sayen balkinta nan turarurruka ne akwati guda muka kawo mata ta yi ta fesawa tana yin kanshi. Sunkuyar da kaina kasa nayi nayi shiru tare da kasa rufe fuskata da gyalen dake hannuna saboda kunya, Ubangiji ya zaunar da wannan aure naku lafiya Maryam ya kuma sanya albarka mai yawa a rayuwarku, gaba dayan maganar Amiru kenan yayin da Abdulhamid ke fadin, amin amin. Kawo ledoji in akwai ki juye musu kayan su je da shi can, ban yi magana ba na tashi naje na kawo ya juye musu suka yi min addu'a suka tafi, shima ya bi bayansu don rakiya da kuma zama wurin wa'azin da akeyi, ina jin duk karatunad akeyi har aka kai ga gamawa malamai suka yi addu'o'i ga kasa, jama'ar kasar, al'umarm usulmi da kuma ango da amarya, ina jin hakan na tabbatar ya kusa shigowa don haka nayi maza na jawo gyalena na kudundune a kasa na rufu da shi na daddanne ko ina ina jinshi ya shigo yanakiran sunana Maryam, Maryam, to wai-ke ya ce miki amarya tana yin bacci ne tun kafin angonta ya shigo, ban motsa ba shima bai tsananta ba sai ya juya ya fita, motsin ruwan da naji ya saa na gane wanka yake yi, ya sake shigowa dakin Maryam, sau daya kawai ya kira sunan nawa sai kawai ya sunkuya ya sa hannu biyu ya sureni ya nufi falo da ni, ke ance miki amarya irin ki tana da wani lokaci ne na yin bacci a 114 darenta na farko? Muje ki biyamin karatunki in ji, doguwar kujera ya nufa ya zauna ya mike kafarshi guda daya a kanta ya zunar da ni a kan cinyarshi ya sake dauko daya kafar tashi ya dora a jikina nayi matukar takura da hakan da ya yi min saboda kunya da rashin sabo bana zaton a tsawon dadewar da nayi da shi ya taba taba jikina da nufin shi in dai ba a kan wani dalili mai karfi ba shima a wancan lokacin ne nan baya ba a wannan karon ba, a yau din kuma da ya dorani a hakan rigar baccin da ke jikinshi mai igiyoyi ce ko tsayawa daureta bai yi ba sai dan gajeran wando kirjinshi gaba daya a bude yake har zuwa kan cibiyarshi hannu biyu na saka na rufe fuskata yayin da jikina ke ta faman bari. sWai ina kike kokarin zuwa ne? Da kike mutsu mutsun kwacewa, ya sa hannayenshi duka biyu ya cire nawa da na rufe fuskata da su ban yarda na bude ido ba balle in ga yanayin da yake ciki sai kawai naji ya dora bakinshi a kan nawa, gaba daya ya kidimani ya sanyani na shiga wani hali da ban ma san yanda zanyi in kwatantashi ba sai dai kuma nasan babu mamaki ya samu kanshi a yanayin da ya wuce wannan don sau biyu zuwa uku yana cewa me za ki ci Maryam, ga abubuwanci na kawo mkiki kin san bai kamataki kwanta baki ci komai ba, sai dai ya kasa sakina balle in iya ganin abin da yake cewa ya zo da shi din bale har in iya samun zarafin da na iya kai wani abin bakina, yanda ya fito da ni falon adauke haka ya mike ya sake maidani dakin a dauke ya dorani a kan shimfidar,a jiyar da na bari wurinki za ki bani, kyautarda kika dade da yi min nake so in karba a yau, a kankame nake a jikinshi yake wadannan kalaman 115 ina jinshi ban tanka ba ban kuma motsa daga yanayin da nake ciki ba sai na ji shi ya soma cewa. Yi min wani alheri guda daya mana Maryao so nake ki martaba min irin martabawar da kika yi min a wancan ranar da wancan lokacin tashi ki sa hannuki rage min wadannan kayan na jikinki da kanki karki barni ki ce sai dai ni inyi yi min wannan alfarmar don in kara jind adi in kara farinciki zuciyata ta kara gamsuwa kuzarina kuma ya karu saboda na san zan karbi ajiyar tawa ne in. karbi kyautar tawa cikin yarda da gamsuwa da amincewarki ba tilastaki zanyi ba. Yana gama fadin hakan na mike na zauna na sa hannu na soma cire kayan da ke jikina da kaina yana karbar su yana yin jifa da su ba tare da yana lura da inda suke tafiya ba, sannu a hankali har na cire duk wani abin da nake sanye da shi saura rigar nono na maida hannayena baya da nufin in balleta itama kowa ya huta, sai naji ya ce min uh'uh Maryam bar min wannan in karasata da kaina, ai ko a wancan ban barki kin cire ta ba, yana daga kwancen ya miko hannayenshi ya balleta itama ya yi wurgi da ita komai naki yana nan tsaf Maryam kamar yanda na fara ganinshi sai dai ma kyau da kwarjini da suka kara. Zai yi wuya rannan in har akwai wani wuri a jikina rannan da Mubarak bai yi mishi irin abinda yake ganin shi ne ya kamaceshi ba saboda wani irin yanayi da ya samu kanshi a ciki na kidima tamkar dai ace bai taba sanin wata mace a tube a gabanshi ba tsawon rayuwarshi sai a wannan ranar. 116 Gyara ki ji dan tsaya ki ji abinda zan gaya mia taimakeni ki karantamin wannan addu'ar don mu karantata tare da ke.... ya soma karantota ni kuma nayi maza na sake maida tafukan hannuna a kan fuskata na rufe saboda tsananin kunya da nauyin da ambatonta a bakina ya yi min, sai dai nayi dabara na karantata cikin zuciyata... Waiyo Maryam, waiyo Maryamu, Wayyo Mairona, bani da nake wahala da hakuri da juriya a dalilin shi ce nake furta kalmomin ba shi da yake yin yanda yake so ne kuma yake furta kalmomin da yake so ban iya ce mishi komai ba... Nace in sonki Maryam nace ina sonki kin ji abinda na fada ko ba ki ji ba? Ba dai ke burinki ince ina sonki ba? To sau nawa yau kike jina ina furta miki wannan kalmar? Maganar yake yi cikin yanayi na jaruntaka saboda gajiyar da ke tare da' shi da dai ace so shi ne samu da shiru ya yi ya yi baccinshi don jikinshi ya samu hutund a yake bukata, ni kuwa ina jinshi bance mishi yi shiru ka huta ba saboda gani nake nima tamkar bai yiwa nawa jikin irin adalcin da ya dace ya yi mishi ba. Washegari da safe ni kan farkawa nayi a makare saboda bude ido nayi na kalli agogo hannunshi dana gani kusa da ni na ga karfe shida ne har da mintoci guda biyar na mike na shiga bandaki nayi wanka sosai na yiwa jikina duk wani abinda nake ganin zai taimake shi nayi alwala na fito ina cikin yin salla ne na ganshi ya shigo dakin ya koma gefen gado ya zauna sai da na idar na shafa addu'ar da nayi sannan ya mika hannu ya sake kamoni ya dorani a kan cinyarshi kamar yanda yayi min 117 Jita, saukin abin kawai babu irin mas'alolin jiyaa tare da shi banda haka kuma a yanzu yana sanye da sabuwar jallabiya ne da ta saukar mishi har idon sawunshi. Kin yi min addu'a kuwa? Na gyada kai a hankali nuna alamar eh, don kuwa ban tashi a wurin ba sai da na yi mishi, ya ji dadin amsar da na bashin, cikin natsuwa ya ce min addu'o'i masu yawa nayi miki Maryam na kuma yiwa Inna. Muka dan yi shiru kafin ya kawar da shirunda tambayata me kike so ki ci yanzu nasan kina jin yunwa musamman ma da yake kin kwanta ba ki ci komai ba, ban yarda mun hada ido ba na ce mishi nafi so in yi bacci. Ya yi maza ya mike na kwanta ya tayani gyara kwanciyar sai da na ce mishi ya yi sannan ya fita ya ja kofar dakin wai don in kara samun nutsuwa. Na farka ne ina tunanin lalle nayi bacci saboda yanda naji yanayin jikina ya canza ban dade da farkawa ba na soma jiwo muryar Mubarak a falo yana magana da wata da nake zaton Umminshi ce. To ko Maryam ce kadai a gidan yau kam ai ab za ta yi girk ba, 8in ta ga dama tayi in bata gani ba ta bari duk abinda take ganin kamar in tayi ita ta yiwa ta bari ba ita na yiwa aurena ba. Ban ji maganar Umman ba saboda muryarta ba mai karfi ba ce kamar tashi sai na ji shi yana cewa, eh Umma dukansu nawa ne na kuma yi alkawarin yin adalci a tsakaninsu, to amma yana daga cikin adalcin ne ace don na kwana a dakina marya jiya ace yau ta fito ta yiwa mutanen gida girki? Banji abinda tace ba na sake jinshi ya ce, a'a Umma ku yi hakuri kar ku roketa na gaji da 118 rokon da ake yi mata in dai alfarmar yiwa Maryam girki ne kar ta yi bana so. Assalanmu alaikum, wata sassanyar murya ce na ji tayi sallama na kuma ji dadi saboda na gane mai ita, a'a Ramatu ce Umman ce ta fadi hakan ta amsa eh ta soma gaisheta kafin naji tana cewa Mubarak sannu kawu, ya amsa tare da amsa gaisuwar da take yi mishi, yaya su babanki da antin, tace sunce a gaisheku. Ban san me ya gani ba naji yana ce mata, ai tana bacci ne, cikin ladabi ta ce msihi ba dakin zan shiga ba zan shiga kicin ne in ajiye kayan da nazo da shi ya ce mata to. Tana shiga kicin din naji motsin ruwa ya fara zuba a fanfo na tabbatar zata gyara wurin ne tayi wanke wanke, Inna yarinya ce da yaya Dija ta yiwa tarbiya iyawar iyawarta aka kuma yi dace ita din mai daukar tarbiyya ce. Tashi nayi na shiga bandaki na sake watsa ruwa a jikina an fito na zauna nayi shafa nayi kwalliya da wani lallausan leshi na sanya 'yan kunne da sarka na zinarin da ake yayi loakcin me ludayi nayi matukar yin kyau ga kashi na fito na tsaya a bakin kicin din ta juyo ta kalleni saboda motsin da taji cikin natsuwa ta soma gaisheni mama ina kwana? Na ce mata lafiya Inna yaya su Abbati? Ai da wai zasu biyoni Mamanmu ce ta hanasu zuwa to a kan me? Na yi tambayar daidai na shiga kicin din na dauko kwalbar zaitun da cokali na dora kan dan karamin tire saboda hangen Mubarak da nayi a falo a mike kan doguwar kujera a hankali na ma tsa kusa da shi na durkusa cikin nutsuwa na tambayeshi, kana bacci ne? 119 Ya yi maza ya bude ido ya kallen, uh'uh ina jiran farkawarki ne, sai dai kuma idanuwan nashi sun canza launi watakila bacci gami da gajiyar hidimar da akayi watakila damuwa ko bacin rai. Ba ki karya ba, kai kaci wani abu ne? Uh'uh na fara mikam ishi robar ruwan swan, ya ce a'a na sha ruwa na ce to ungo zaitun magani ne bai yi musu ba ya karba ya ci kwaya uku, wai me za ki ci ne? Na danyi murmshi kafin nace mishi, me yasa ka damu da yawa, a daki na fa nake maganar tayi mishi dadi ko kina dakinki ai ke din bakuwa ce Maryam ban amsa ba na mike na shiga kicin don nasan ina da wasu abubuwan a ciki sai kawai na ci karo da kayan da Inna ke cewa zata ajiye sinasir ne da miyar taushe da ya ji kayan ciki a ciki da kashi na bude oven na sa kwanon farfesun kajin da tun jiya ta aikomin da shi ban samu naci ba ga kuma gasassun kajin da shi Mubarak din ya shigo da su bai barni na tabasu ba, nan da nan na kewayeshi da abubuwa iri-iri kasancewar kuma dama na riga na saba da cin abinci a gabanshi sai kawai na zauna muna ci tare, ga dukkan alamu kumna dadi ne ya kamashi watakila ya ga alamar in ma so ake a takurashi kan abinda zanci to zai iya samun sauki ta wurina tunda zan iya kula da kaina kina nufin duk da bakuntar dake tare da ke zaki iya hidimominki? Cikin natsuwa na ce mishi me zai hana? To yi min wani alkawari man Maryam, a hankali cikin natsuwa na tambayeshi kamar wanne fa? Tsareni yayi da idanuwanshi kafin ya ce min,n a zaki barni in zauna lafiya za ki barni in samu natsuwa a tare da ke, na zaki 120 barni in yi hukunci da duk wani abinda kika san nawa ne, Za ki taimakeni in fita daga mas'aloli in har ina cikin su. Ban kalleshi ba na ce mishi in har kayi min bayanin yanda zanyi in yi maka hakan ina ganin kamar zanyi amma yanda kayi min maganar a haka ai ba zan gane abinda zanyi ya zama D8 1ya yi maka wadannan abubuwan ba. Yana kallona ya ce min, ki taimakeni ki yarda in na saki iki yi in na hanslki ki cikin sauki na ce mishi zanyi saboda ba tare da na tsaya yin wani tunani ba saboda yaya Dija da sauran mutanen da suke ganin sun isa su gaya min inji sunyi ta gayamin cewar in ya hanaki ki bari in ya sa ki i yi shi aure da kike gani ba komai bane face ladabi da biyayya sai ko mututnawa na ce musu to don haka hankalina a kwance na ce mishi to kamar yanda Suma na gaya musu. Wanka yayi ya tsalo wata irin kwalliya da zan iya cewa ban taba ganin yayi kyau irin na rannan ba ya wuce can cikin daki, zo mana, na tashi na bishi ina tunanin ya yi kiran ne don ina tare da Inna. Wannan hular da wannan wacce ya fi kamata in saka? Na reba kallo tsakanin hulunan duka biyu kafin ance mishi, wannan bai sake dubava ba ya sanya wacce nace din. Me da me kike so a kawo miki? Na gane abinda yaken ufi na ce ni fa nafi so in yi girki da kaina, kina amarci kina girki? Ba a yin haka abubuwa sai su yi miki yawa, ki kwanta ki yi bacci ki huta, nace uh amma ai Inna tana nan za ta yi min aiki bai sake magana ba kudi ya cire ya ajiye a gefen madubi, zan turo Isiyaku ki yi 121 mishi lissafin abinda kike so a kawo miki, nace mishi to a dawi lafiya, ya ce Ubangiji yasa ya fita. Kudin da ya ajiye din masu yawa ne sosai har Zuciyata tana tunanin me zan saya da su haka? Ina zaune ina jiran zuwan Isiyaku cikin tunanin ko dai bai ganshi bane ko kuma ya manta ya yi tafiyarshi? Sai ga Isiyakun ya shigo da manya manyan ledoji a hannunshi kicin ya wuce ya ajiyesu na ce mishi, kai Isiyaku ba nice mai girkin gidan ba kai musu can, ya ce a'a nan ya ce in kawo wadannan ga nasu can a waje na ajiye musu, Inna nasa ta duba kaji ne da koda, sai kayan ciki da kuma sauran abubuwan da zan nema ba tare da na tambaya a gidan ba na dawo na zauna ina tunanin a yanda zanyi da aiki irin wannan na sani da bance mishi zanyi ba saboda dai karfin hali kawai na ke yi nake daure amma gaba daya jikina ciwo yakeyi sai ga anti Kubra ta yi saliama ta shigo bayan na ji ta tana gaisawa da Rumasa'u a tsskar gida ina ganinta naji dadi ya kamat sannu a zuws anti, sannu 'yar albarka ke dai ai daga gidan Hadiza nake ina can sai ga mijinki yaje kunyar ambatonshi a matsayin mijina ya kamani saboda yanayin da take magana a cilcin nashi yaje ya kai mata fan hamsin ya ce ta sailami duk wasu baki da suke nan daga wurinta har zuwa gidan baba ya kuma sake bada jakar guda ya ce a sai miki abinda aka san zai yi miki amfani don ya tambayeki kin ce ba kya son komai. Kunyar anti Kubra ta sake kamani na sunkuyar da kaina kasa har na kasa dagowa, ato ina masu cewa ita tana aiki ne kawai ke kina waje yanzu ai tun a wajen ana 122 tare ne kawai ba komai ake yi ba? Shiru nayi ban iya ce mata komai ba. Itace ta sarrafa duka bubuwan da ta samu an kawo din ta adana na adanawa ta girka na girmawa irin kayan shan farfesu ki sha romo sosai saboda kula da jikinki bayanin take yi min bayam ta titsiyeni na ci na sha adadin da yake nema yafi karfin cikina, ai garama da tayi miki haka mu kishiya wacce iin yunwa ce bata gana mana ba ga abin nan a wadace amna bata sarrafa shi ba balle ta baka sai ita da 'ya'yanta ta san hikimar da tayi ki kula da kanki na gaya miki ki ci gasasshe nama ki sha farfesu ki kuma hora kanki ba yanda za ki citu ba kama hanya a tafi ta bar Inna tana gyaran wajen. An idar da sallar azahar Mubarak ya shigo baba da yaya Dija suna gaisheki naje na yi musu bangajiyar baki, nace ina amsawa ya ka barosu? Lafiya ni zan kwanta ko za ki zo mu je tare? Na ce uh'uh na nuna mishi Inna da ke kici bai yi magana ba ya wuce ya shiga daki sai wajen hudu ya fito. Rannan da daddare mnuna kwance a gadon mu gwanin dadi yana manne da ni a jikinshi hira yake yi min yana bani labari baki sani ba Maryam a hankali na tambayeshi menene, cikin nutsuwa ya ce min, sai in rinka ganin tamkar a mafarki nake sai na ganki a zahiri ko na jiki a jikina sai in gane ba mafarki bane, sai in tuna lokacin da baba yake lallashina yana gaya min cewar in matarka ce zaka aureta wani ai baya auren matar wan ashe ashe ashe kuwa haka din ne, a hankali cikin natsuwa na ce mishi baban? Ya ce eh mana ance miki ni na iya irin wannan noke noken ne irin naki? Kana son 123 abu kana kaiwa kasuwa? In banda na nuna mishi zahirin al'amarina zai yi ta wannan zirga zirga ne da ya rinka yi ke fa kina jin yanda nake ji ko na rinka ji, gaya min gaskiya sau nawa kika taba yin mafarkina? Ni bana Rarya maryam bana kaiwa kwana ashirin ban ganni tare da ke ba a taccina har na rinka sanmun mas ala na wankan da nakeyi ban san dalilinshi ba na yi kamar ince ishi ai nima ganin nake tamkar mafarkin nake yi sai na fasa neyi maza na ja bakina na tsuke, a hankali kuma sai na ce mishi to mu yi bacci mana yallabai ko zaka samu ka kara wattsake gajiyarka. Kwanaki uku a jere ni nake hidimomina ni nake yin girkina babu fashi kuma kullum yaya Dija zata aiko min da abin karyawa mai dadi da gamsarwa Inna zata zo tayi min duk aiyukan da suka dace ta kuma tayani hira sai lokacin makaranta ta yi shiri ta tafi in ta taso ma nan wurina zata sake dawowa haka shima Isiyaku kullum zai kawo min cefane.. Rannan na cika kwana hudu cikin daki ban ito ba saboda ajiyar Mubarak bai yarda munyi irin kwanciyar da muka yi a kwanak biyun da suka biyo bayan daren angwancinmu ba ina jin sanda Inna ta shigo ta gama abinda zatayi tazo ta tsaya daga bakia kofa ta gaisheni ta ce min zata je makarantar allo ta dawo na ce mata to kin karya ne? Ta ce eh nace to sai kin dawo, ina cikin hakan ne Mubarak ya sake shigowa dakin ko za ki zo muje can wajen Rumasa'u mu karya, kamar in ce mishi tuntuni bata kirani karyawa ko cin abinci ba sai yanzu da na riga na zama 'yar gar? Ban iya yin hakan ba na ja, bakina kawai na yi shiru. 124 Ya nemi wuri a balkin gadon ya zauna, bana so wata mas'ala ta taso ace ta wurinki ne Umma ta kirani ta ce min wai anyi mata fada taji

Chapter 8 of 11