Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 11
wannan. lokacin babu abin da zamuce musu sai dai addu'ar Ubangiji ya sakawa kowwa da alherinsa amin summa amin. Mun dawo gida da babani a dalilin saukin da ya samu kowa murna yake yi muna farin ciki musamman da yake a yanzu yana da mata mai kula da tattali da kokari ganin asirin gidanta ya rufu sai dai kuma hakan bai hana hankalina da zuciyata tafiya wajen tunanin abitda ya hana Mubarek zuwa yiwa babana muriar dawowa gida ba rabonshi da zuwa asibiti tun kwana biyu ko uku da yin aikin bai sake takawa ba to yanzu kuma mun dawo gida ga mu ga shi ba zai shigo ya gaisheshi ya karasa ladanshi ba bayan duk irin hidima, dawainiya da ya yi da rashin lafiyar tashi, to ko dai matarshi ce ta hanashi zuwa? Tanbayar da ta zo cikin zuciyata kenan, nayi kokarin in kawar da hakan ta hanyar tambayar kaina anya Mubarak yana yiwa matarshi irin wannan tsoron kuwa? To amma me akayi mishi? Da dai naga damun kaina kawai zanyi sai nayi maza na cire wannan tunanin daga cikin zuciyata na maida hankalina kawai wajen lura da halin dà babana ke ciki ina kuma rama bacci da gajiyar zaman asibiti tinda muka dawo matarshi ke kula da shi ga anti Safina ga baba Lantana ba a je ko ina cikii kulawar ba na soma jin maganarshi daga dakin baba Lantanar yäna cewa uh'uh ba fa zan iya irin wadannan abubuwan ba a yanzu in kin ga da matsawa kawai jeki ni bani da wata damuwa a yanzu. 65 Mamakin babana ya kamani cikin zuciyata nace kar dai ace babana zai fara yin magana ne. Ba a dauki wani lokaci ba baba Lantana ta fito da halayenta da akafi saninta da su na kin yin girki da sauransu saukin abin kawai anti Safana tana nan tana kuma tsaye kan al'amuran mijint adama ni kaina da take matukar ji da ni batama ko kiran sunana a yanzu wai sai maman baba wani irin ji da ni takeyi ban sani ba ko gani take tamkar don ita da abinda ke cikinta na yi jinyar baban nawa. Rannan da sassafe na idar da sallar asuba na shafa fatiha na shiga dakin anti Safara inda nasan ya kwanaa don in gaisheshi in kuma bashi magungunanshi da naki yarda wani ya bashi, yana shan magungunan muna yar hira magana kadan kadan. Baba kana cin zaitun din an kuwa? Magani ne fa ba kadanka. Kafin ya bani amsa sai kawai naji muryar yaya Ibrahim yana sallama tare da shigowa cikin gidan, shigo mana Ibrahim, baba ya yi mishi umarni don haka ya shiga har cikin falon. Kan maganar zuwan mutumin nan ne ikita na ce a kira min kai inji kayi binciken a kan nashi ne? Na mike na fita saboda ganewar da nayi maganar a kaina ne tunda na ji ana ambaton likita wato Dr. Bello wanda ya biyo mu gida da kai kawo da hidimomi iri-iri. Ni fa baba binciken da'nayi kan mutumin nan ba wani mai yawa banc saboda ga Alhaji Ahmad a kusa da mu wanda aka dade ana tare yaushe za a je ana bincike kan wani sabo kuma? Gabana ya fadi jin da nayi ya ambaci sunan Mubarak, babana yayi maza ya ce, 66 Mubarak kuma? Cikin zuciya na ce, a to ai gara dai da ko tambayeshi. Cikin natsuwa va ce mishi, eh baba i ni a wurina banga wani wanda ya fishi ba, babu ma wanda ya kaishi cancanta in dai har za a bada auren ne bisa cancanta da dacewa babu wanda ye fishi dadewa a cikin nemankullurn kuna a tsaye yake a kan al'amarinta ga zaman tare da makwabtakar dake tsakani, don haka in har ba shi ne ya ce bai da bukatar auren ba to babu wani dalili da zaisa mu je muna binciken shi ikita, to yaushe ma muka sanshi? Cikin natsuwa da yanayi na rage murya naji babana ya ce mishi, to ai banga kamar har yanzu yana kan naganar nan ba tun yaushe rabon da ka ji sun turo kan maganar? Sannan tunda akayi aikin nan da kwana biyu har zuwa yanzu ban sake ganinshi ba. To in baya cikin neman saboda wa yake hidimar da yakeyin'? In ana tunanin ko makwabtaka ne shi yafi kowa sanin hakkin makwabtaka baba? Ai ya gaji da turowar ne yasa ya hakura ya zuba ido yaga iya kar al'amarin. To tunda ya nuna ya gaji yanzu sai a yi yaya da shi Tbrahim? Ba shi kenan ba sai a yi da wanda bai gaji ba yake ta kai kawo. Cikin zuciyata na sake cewa a to. A'a baba a basu hakkinsu tukunna sai in sunce basa so shi kenan sai a yi da wannan din, a ra'ayina ina ganin a yi musu aike a gaya musu in suna so su zo in suka ce basa so shi kenan. Hannu biyu na saka na dafe kirjina saboda tsananin harbawar da yake yi cikin tsananin karfi saboda tsoratar 67 da nayi da maganar tashi, ban taba jin muguwar shawara ba irin wacce ya baiwa babana a yau. A tambayi Mubarak da iyayenshi sai in sunce basa so na ne za a aurar da ni ga wani wannan wane irin zace ne? Tambayar da nake yiwa kaina kenan sai naji ya ci gaba da bayani yin hakan ba komai ba ne baba ba kuma wulakanta kai bane aure ne shi kuma auren darajarshi ta wuce duk yanda ake zato, in wasu sunyi mana mummunar fassara ma to mu kam ai babu ruwanmu tunda mun san alheri muke nufi ba kuma don wani abin hannunsu ba. Bayani sosai ya yiwa babana har dai ya gamsar da shi ya yarda da shawarar tashi. Cikin zuciyata na ce, na shiga uku yanzu bayan duk abinda na wuce a baya kuma bai isa bah er sai an sake jawo min wani wulakancin mai salo na dabna. Yaya Ibrahim yana barin gidan naje.na samu anti Safara wai in yi mata magana ko zanyi sa'a ta yarda ta yiwa babana magana kan rashin dacewar abinda suke shiryawa sai kawai naga ta kalleni cikin natsuwa ta ce min, to ai yana jin maganarki kema ki sameshi mana kawai ki gaya mishi. Yanayin da íayi mnaganar a ciki yasa na gane abinda take nufi don ahka na wuceta nayi tafiyata. Ina jin baba Lantana daga dakinta tana fadin ina ma dai in anje su koro wanda yaje din kwadayi mabudin wahala, in da kwadayi da wulakanci, kuda wajen kwadayi yake mutuwa, yaron nan da iyayenshi ba tun yau ba sunce basa so basa so ba sa so amma kun ki yarda ku hakura kun manne sai dole sun kar6i kai tir. 68 Duk da irin wadannan kalamai da baba Lantana ta wuni tana yi basu sa babana ya canza daga abinda suka shirya ba. Washegati da safe naji yana cewa anti Safara, yau fa za ni sallar juma'a da wuri kuma zan tati don sai naje gidan Alhaji Muhammadu nayi mishi maganar nan kafin in wuce masalllacin. Da kanka kenan zaka? Ya yi maza ya ce, ei ai gara inje kawai da kan nawa babu komai ai 1aganar aure ne ya yi magana da dan shi ne in suna so shi kenan su zo in kuma basa so shi kenan mun fita hakkinsu sai a yi da wannan da yake tsayen, ta ce haka ne Ubangiji ya zaba mana mafi alleri, ya ce to amin. Hankaline ya yi matukar tashi ben taba ganin yariyar da aka yiwa irin wannan tallan ba sai ni dama dai inyi sa'a suce basa so shima Dr. Bellon ya ji labari ya ce baya so na ya fasa in ga yanda babana da yaya Ibrahim za su yi da ni tun da dai na lura gajiyar da sukayi da ni ne ya sa suka yanke hukuncin yi min irin wannan wulakancin. Ban san abinda ya faru tsakanin babana da Alhaji Muhammadu mahaifin Mubarak ba illa iyaka dai da daddare Isiyaku yayi sallama a zanren gidanmu da anti Safara ta amsa mishi kuma ya slhigo har dakina ya sameni cikin fara'a ya soma gaisheni ina amsawa a natse sai da muka gama gaisuwar sai ya kalleni cikin murmushi yana susar eyarshi ni da yaliaba: ranki ya dai ya dade ne yana zaure yana son ganinki, nace to madalla. Ya dan saurara ko zaiji na sake yin wata magana bai ji ba ya gaji ya sake tambayata, me zance mishi? Ban 69 kalleshi ba na ce mishi abinda kaga ya N maka, ya gaji da tsugunno ya tashi ya tafi ban san yaya saka, kare ba. Kwana biyu a jere ko leken kofar gida bapyi ba saboda bakin ciki da takaicin yanda yaya lbrahim da babana suka hadu suka zubar min da 'yancina, ban salke jin wani motsi ko wata magana. daga wurin kwoab a sai kawai na gane Mubarak da iyayenshi sun karbi tallan aurena da su babana suka kai musu a daliin wasu yan al'amura da na lura da su shiryawa nayi da, safe cikin. kwalliya mai sauki mai kuma ban sha'awa riga da-siket din atanfa ce a jikina ni'na yiwa kaina dinkin don haka ba sai na tsaya cewa sun dace da jikin nawa ba pa sanya. takalmi silifas dan Italy tare da 'yar faramar jaka ta pos a hannuna, maimakon in yi tafiyaa-a haka- ko, in yi damara kamar yanda 'yan mata a loacin sukeyi sai ya jawo wani dan madaidaicin gyale na yane jilkin, pawa sai dai bai hana kwalliyar tawa baiyana ba'ta fto.tsalcar gida ina gayawa anti Safara zanje wajen yaya Dija yanza zan dawo. Ta tsaya tana kallona nuna alamar bata gamsu, da yanda nayi mata bayanin ba, sanarwa kenan ba neman izini ba, na yi maza na ce mata yi hakuri anti ba sanarwa ba ne neman izini ba zan dade ba. Ta yi murmushi ta ce, to ki gaisheta, nace mata to za ta ji, na kamo hanya na fitod aga gida ina jin baba Lantana tana fadin, anyi jiran anyi jirani abin ya gagara har an koma yin talla, ban kulata ba çikin zuciyata dai na shirya zuwa wurin yaya Dija ne don in san menene ake ciki, in kuma gaya mata ra'ayina kan hakan da aka shirya don ta sani. 70 Yar tafiya 'yar kankanuwa na fara nir tina in kara ba bakin hanya inda zan samu abin hawa sai kawai ga Isiyaku ya biyoni da sauri har yana haki, wai lki dawo in ji shi. Na ja na tsaya ina kallon Isiyaku cikin takaici, kai Isiyaku kafin in gaya mishi abinda nake nufin gaya mishi sai naga ya saki wani lallausan murmushi, ai ba dagani bane ya hacla da rantsuwa kafin ya ce shi yallabai ranka ya dade din ne ya ce in zo in gaya miki kar ki tafi ko ina gashi can suna tsaye shi de bakinshi. Ban san dlaili ba bana iya karya dokar Mubarak ko da dai a lolkacin zuciyata tana raya min ne wai zanbi umanin nashi in komá gidan ne in bar tafiyar saboda kar in kunyatasbi a gaban bakin nashi amma can cikin raina ni da kaina na sani ba haka bane ba don su ba ne maganar guca daya ce a duk hali ko yanayin da muka samu kanmu a ciki ni da shi bana iya sabawa ko bijirewa umarninshi. Na juyo da baya na korna na nui gida a makogarona ina fadin don dai kana da baki ne kawai a zuciyata nasan ya zama min tilas in koyi jaruntakar da zan koyi bijirewa irin wadannar dokokin nashi ba komai ya ce min shi kenan ba. Ina tsaye a kofar dakina ina kokarin bude kofar tare da yiwa anti Safara bayanin sai an jina za ni sai na jiyo sallamarshi a cikin zauren gidanmu da kanshi ya yi sallama alamar bai zo da dan aike ba nayi kamar kar inje sai kuma naga to ai baba Lantana tana kallona ni kuma bana so ta sheda wani al'amari a tsakanina da shi don haka na juya na koma zauren tuni har kanshinshi ya 71 mamaye ko ina a wurin kwalliyar kananan lkaya ya yi, sun kuma yi matukar karbarshi. Ina zaki da safen nan kikayi wanna kwalliyar haka? Ban san yanda akayi ba naji bakina ya bashi amsa, gidan yaya Dija, to yaya za ki fita baki gaya min ba? Ba ki ji maganar da babu yaje ya gayawa baba bane? Nace ban ji ba na fadi hakan a daidai lokacin da zuciyata ke nanata maganar tashi, ba ki ji maganar da baba ya je ya gayawa baba ba ne? Wato babana ne ya je ya gayawa babanshi cewar da nayi banjin ba da yanayin da nayi maganar a ciki ya sashi zuba min ido yana kallona, ba ki ji bane ko kina da wata magana ne, tsakanina da ke ai babu wani 6oye-6oye ko kin yi nufin 6uyan ma ba zai yiwu ba don babu wani al'amarinki da ban sani ba, don haka fadi gaskiyarki kawai in kina da wata magana ne kuma kiyi. Na daure fuska sosai kafin nace, ina da ita, da sauri cikin natsuwa ya ce, ai kinga hakan yafi fadeta inji. To ni gaskiya ba da yàrdata aka yi miin hakan ba a ma. shawaceni ba don haka bana so karma ka dauki hakan da wani muhimmanci da har zaisa ka rinka neman ka shiga harkokin rayuwata bana so. Ya dan gyara tsayuwarshi kadan kafin ya tambayeni bakya son me? Na yi shiru bakya so kamar yaya? Ai magana za k yi don in gane abinda lkike mufi. Na sunkuyar da kaina don kaucewa kallon da yake yi min in kuma ji dadin gaya mishi abinda nake son gaya mishi. Nace bana son auren da ake shiryawar saboda bakai nake son aura ba ina son auren saurayi ne dan uwana kamar yanda nake budurwa ba inje ina auren mijin wata ba. 72 Hankalinshi a kwance ya tambayeni, to yanzu yaya kike so a yi? Na ce rokonka zanyi ka fita hanyata ka daina kulani ka daina shiga harkokin da suka shafi gidanmu. Wani irin lalataccen kallo ya yi min kafin ya tmabayeni, kenan har kina da wata harka taki da ake shiga, yaushe rabon da kika ga daga ido na kalleki. Kirana aka yi kirjina ya bada wani irin sauti na dum, a dalilin jin kirana aka yi nan da ya ambata na shiga uku ni yasu tawa ta sameni, yaya Ibrahim ne ya yi min sanadin wanman wulakancin gashi tun ba a je ko ina ba an soma gorantamin ban iya daurewa na soma kuka ban iya tsayawa ba na juya da nufin in shiga gida sai ya yi maza ya tura kofar zauren dake wurin ya rufe ya hanani shiga ban daina kukan da nake yi ba. Kin shiga ulu ke 'yasu taki ta samehi yaya Ibrahim ne ya yi miki sanadin wulakanci gashi tun ba a je ko ina ba an soma goranta miki, to da akayi miki me? Kina so ki gaggantsaramin maganganu ina kallonki inja bakina in yi shiru? Ya soma yin magana kamar yana nufin yin rarrashi, nayi naza na bijire mishi gaba daya tunda gori ay shiga cikin maganar ai kuma shi kenan magana ta kare ban shiga ba ma kenan ina kuma ga na shiga gaskiya ba zan iya ba da wanne zan rinka ji da gorin da zaka rinka yi min ko da wnada matarka da 'yan... Kinga Maryam kinga, nayi maza na bar maganar saboda jin kinga-kingan da ya fara ambatawa don haka na koma yin kukan kawai ina fyace majinata da bakin gyalena. 73 Nace in kina da magana mai ma'ana ki yi ina jin ki na tsaida kukan da nakeyi cikin natsuwa na ce mishi a fita hanyata kawai, ban sake yin wata magana ba ya juya ya fita yayi tafiyarshi na dawo cikin gida na zauna ina tunanin al'amurana úa Mubarak babu wani alherinshi ko taimakonshi a kaina da ban tuna ba ko ince na manta a'a komai irin sa ne dashi sai dai yanda zuciyata take rike da wannan lissafin hakakuma take rike da abubuwan da suka faru tsakaninmu da gidansu, da baubuwan da mutanen unguwas uka yi ta fadi tuni dama mutane da yawa suke fadin wai babana yaki aurar da i ne yana jiran Mubara din saboda kwadayin dukiyar gidansu ba wannan ne abinda yafi komai damuna ba irin dauke kafar da ya yi fun muna asibiti har kawo dawowarmu gida bai zo ya gaida babana ba yana ganina ina ganinshi sai ya yi kamar bani yake kallo ba sannan a hakan wai an bisu har gida ance in suna so su zo bayan ga wani yana takai kawo a kaina an san za a bashi ni me yasa ba a bashi din ba tuntuni tun sanda suke zirga-zirgar aike shi da mahaifinshi sai a yanzu da suka tattara nmutane suka yi watsi da su? Ina alwalar sallar azahar a tsakar gida Rukaiya ta yi Sallama ta shigo, ran amaryarmu ya dade, ban wani kulata ba don ana jin kamar ina son wasan nata, anti Safara tayi ma'a sannu da zuwa ta kuma jagoranceta Zuwa dakinta hakan ya kara tabbatar min da cewar ba wurina tazo ba, a cikin zuciyata dai na kasa tunano yaushe rabonta da shigowa gidanmu? Dakina na wuce na soma gabatar da nafila kafin in yi farillar har ta bar gidan kuwa ban san yanda na tashi daga kan salalyar ba don 74 amin amin, dakina ta sbigo ta samen, ke kuma menene haka kika shige daki kika hau gado kika zauna ba za li bar gidan ba sai masu kawo kayan sun zo sun sameki? Na tashi na zauna ina kallont,a kayan me za a kawo? Harara da dakuwa ta hadamun gaba daya, ba fa na son rashin kunya, na ce to yaya dija ni ina sanin abinda ake ciki ne? Kin san irin bakaken maganganun da ya zo ya dankaramin kuwa? Ni gaskya, ta ce to ba yanzu ne lokacin fadin gaskiyar taki ba mai gaskiya tashi ki shiga gidan baba Sumaye don kar su zo su sameki a nan a ce kin yi rashin kunya tunda ina ganin kamar za su zo da yawa saboda ya ce min zai hada komai a azo da shi kayan na gani ina so kayan sa rana, kayan aure da kuma na sakun lalle don baya so a saka mishi lokaci mai nisa. Ban iya ce mata komai ba saboda hayaniyar da akeyi a cikin gidan alamar mutane suna kara shigowa, anti Safara kuma sai kai kawo take yi tana kokarin ganin kowa ya sarou abinda zai kai bakinshi. Duk da kokarin da yaya Dija tayi na ganin na fita gidan ba tare da an ganni ba sai da wasu suka gannin basu kuma ja bakunansu sun yi shiru ba sai da suka yi tambaya, ai dama amaryar tana gidan ne? Sai dai ba su yi sa'a sun sami mai basu amsa ba muka wuce kofar baba Lantana a kulle kamar bata nan nayi maza na kalli yaya Dija na ce mata, tana ciki fa ta kulle kofar ne kawai irin yanda tayi ranar da aka je jeran anti Safara, bata amsa min ba. A gidan baba Sumaye dakin da muka saba zama sanda muke yara na shiga na hau dan gadon bonon da ke wurin na kwanta, maimakon zuciyata ta tsaya wajen 76 tunanin alamarin dake faruwa a kaina a halin dan ake cii sai ta koma tunanin da rayuwar kuruciyata tun sanda nake yar karamata sosai mu'amalata da su Jumare har kawo ranar da na wayi gari a wannan dakin ina baccin da ake kira baccin hasara na rasa Innata ban sani ba, hasken rana ta tashi na fito waje idanuwana suka sheda dimbin jama'ar dake sallatar wata gawa dake shimfide cikin makara a ka kuma lullubeta da zanin Innar tawa amma ban gane itace a kwance a ciki ba, hawaye suka soma zuba min ganin babu kowa a gidan sai ni kadai ya sa ni na sake nayi kuka har sai da na gaji nayi shiru don kaina ban kuma wani dade ba bacci mai nauyi ya daukeni wanda ban tashi ba sai da naji ana taba ni na bude ido naga baba Sumaye a firgice na ce mata, magariba har tayi baba? Ta ce eh, nayi maza na ce ban fa yi la'asar ba, ta ce to ai sai ki tashi ki yi, na idar da sallar magariba ina addu'a ita kuwa baba Sumaye sai fadi take yi, kai uh-uh uhhh, ta gyada kai jimawa kadan ta sake nisawa ta ce, mu mata muna da aiki shi namiji a kan matar da yake so ai maganin shi hakuri ne kawai in kayi hakuri komai sai ya wuce amma in ba haka ba ai abin da wahala wannan irin kaya da Alhaji Mubarak ya yi miki dame sukayi kama ni Sumaye? Ta kama baki ta rike tana fadin, kinga ni ko Kayan auren ban gama gani ba na tashi balle kuma sauran komai fa a ciki sha biyu ne dozin sai bayani baba Sumaye take yi min tamkar dai ta mance ni ce amaryar a wancan lokacin namu kuma ba a hirar aure ko kayan aure da wacce za a yiwa aure. 77 Ban samu ganin kayan auren da baba Sumaye ta bani labari ba saboda gaba daya kayan babana ya ce yaya Dija ta tafi da su can gidanta ta adanasu. Kwana uku da kawo kayan auren Mubarak ya zo a zauren gidanmu na sameshi da ganinshi nasan zuciyarshi a soshe take saboda yanayin da na gani a tare da shi, daga wurin yaya D:ja nake naje wajenta ne don ina so in yi muku adalci dake har ita da na so da sai kawai in samu malam Ibrahim in nemi alfarimar lokacin da nake so a sanya main na biki to banyi hakan ba sai naje na sameta don in baku damar ku me kika gaya mata da yasa ta ce min wai zaia shiga wannan maganar ne kawai in mun warware mas'alar da ke tsakaninmu? Menene a tsakanina da ke? Me bayi miki? Me yasa ke baki da sassauci kan abinda ya sihafeni? Daga shekaru biyar zuwa yau za ki iya tunaw da wani abin da kika yi min guda daya da niyyar ki i in ji dadi? Kina tsammanin in banda wani al'amarin 1e na daban a tsakaninmu da ke zan lamunci irin wadar nan abubuwan ne? Ai bana son 6acin rai Mero abinda ya kenan ya tsare mutum ya yi ta gaya mishi maganganu in banda hzka bai iya komai ba gaba daya samarin da nayi ban taba ganin wanda baya zama ya gaya min irin son da yake yi min ba sai shi tsawon rayuwata da shi bai san ya vabi kwalliyata ba sai dai ya saya min kayan adon kawai dana kai munzali na 'yan matanci gaba daya burina ya yabi kwalliyata ne don inji dadi bai yi ba ko ince baya yi na kai wani matsayi na bukatar ace ana sona bai yi ba wasu suka yi ta furta min hakan na kasa jin dadin kalmar a bakunan su saboda ba a wurinsu nake son jinta ba, bai buda baki ya gaya min irin 78 son da yake yi min ba sai a loakcin da al'amura tsakanina da shi suka rikice ko ince suka lalace ya fadeta a sanda fadin nata bai amfanar mana da komai ba tunda wannan lokacin kuma bai sake gaya min wata magana makamanciyarta ba da zata sani in ji sanyi ko inji dan wani sassauci a zuciyata, ban san yanda aka yi ba naji nakina ya ce mishi, nifa nafi son auren mutumin da zai rinka furta min kalmomi masu dadi yana gaya min irin son da yake yi min. Maimakon da ya ji hakan ya gaya min wata magana mai dadi sai na ji ya ce min, to ya ya za ki yi da kaddarar rayuwarki Mero? Ko wace mace ai da irin kaddararta ke taki kaddarar ita ce ta ba za ki auri saurayi ba mijin wata za ki aura ba kuma za ki auri wanda zai zauna yana yi miki irin wadannan kalmomin ba don bai iya ba. Na 6ata rai na ce ko kuma a kaina ba? Eh to watakila a kankin ne kawai nake hakan da kuma za ki yarda da shawarar da zan baki da kin daina kawo zancen wata a tsakanina da ke. Na yi shirn shima ya tayani yin shirun na dan wami lokacin kafin ya kawar da shirun da tambayata, da ma damuwar kenan? Ban kula shi ba, sai na ji ya kara sassauta muryarshi a hankali, cikin nutsuwa a soma cewa, ban yarda na koyi irin wannan rayuwar ba ne Maryam saboda nafi so da sha'awar rayuwa irin wacce na samu iyaye da kakannina a kai ina irin rayuwa ta kunya da kawaici kan abindą kake so musamman mace kin gane? Shiru nayi ban ce mishi komai ba har ya yi min sallama ya tafi a kan gobe zai yi sammakon tafiya 79 Legos nace to Ubangiji ya kiyaye hanya, ya ce to amin na gode. Kwana hudu bayan tafiyar Mubarak aka yi bakon wani dattijo a gidanmu ganin shi da zanen barebari irin na babama da nayi da kuma sanin da nayi cewar babana yana mutunta duk wani mutumin da ya gani da irin wannan zanen a fuskarshi ya sa nima na mutunta wannan dattijon ta hanyar shinida mishi tabarma a cikin zaure na,kawo mishi ruwan sanyi tare da butar alwala da kuma abincin da aka girka wanda bai yarda ya taba komai a ciki ba in banda butar da ya dauka ya je ya taba ruwa ya sake daura alwalarshi da ta kárye a sanadin taba ruwan da ya yi sannan ya dawo kan tabariar ya sake zama ya zubamin ido yana kallona cikin natsuwa ya tambayeni a daidai lokacin da ya ci gaba da jan dogon carbinshi yana kos kos kos, to ina malam Bukar din da tace nan din gidanta ne tace babanta ne? Kai tsaye na fahimci inda yake nufi tunda shiua baban nawa shigen irin hausar da yake yi kenan na ce msihi e maiam shi ne babana, ya gyada kai ya ci gaba da abinda akeyi, ni kuma na mike na shiga gidi na dauko gyaiena bayan na shedawa anti Safara cewar zanje kiran babana saboda wani bako mai irin zanen shi ya zo wai yana son ganinshi ta ce to yi maza ki kira mishi shi nace mata to na fita. Bako da irin zanena ya zo nema? Ya yi min tambaya cikin yanayin murmushi na yi maza na ce mishi ci baba, ya ce to muje gani

Chapter 5 of 11