Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 11
shi da Amiru wani sati biyun mns beym nan ya sake dawowa a lokacin nan kawa baifi kwanaki biyar sulkz saura a fara bikin ba. A Ciki wadannan kwanakin kuwa babu abin da Yalkubudi bata yi min ba wanda suke yi wa amarensu ko da yake ma kamar karasawa ne don tafi kwanaki talatin tana min jike-jike, hayake-hayake, tsime-tsimw, gogo goge, gyare gyare, kuilum kuma ta kan yi ne tare da yi min bayami wannan uban zirga-zirga da wamuiea yro yake yi ai gara a kara gyara mishi ke ya sameki.. kin san ance wai ko kana da kyau to ka kara da wanka kar ki yarda ki zauna bakya gyaran jikinki don shi namiji da kike kallonshi.... ta danyi shiru kada katin ta ce, uhuyy ke yanzu yarinya ce ba za ki gane yanda alamarin yake ba tukunna. Ana cikin haka kwanakin biki suka iso jama'a suka yi ta haduwa fiye da duk yanda ake ko daga gida mutanan da sulka zo bikin ko kadan banyi zaton ganinsu haka ba Umman Mubarak, Yakumbo Halima, baba Sumaye, baba Lami, manyan dattawa wannan yan matasa yaran mata kuwa akwai anti Asiya aminiyar yaya Dija da malamata malama Basma akwai yar anti Safara 96 ga wasu mata su uku da suka gabatar min da kansu a matsayinsu ne angwaye alamar ko dai kanne ko kuma abokan wasan Mubarak sai dai ban san ta ina ba maza kam babu adadi don kuwa naji ana ta maganar yawan nasu abokan Mubarak da yawa sun zo daurin auren ga samarin unguwa irin Isiyaku su ma ba a barsu a baya ba don kuwa shi mai mu'amala da na kasa da shi ne abokan babana irinsu baba Baidu da baba Hodijo kasuwar timatir su ma ance mota guda suka zo abin dai gwanin dadi gwanin sha'awa. Ina kwance a dakin da nake zaman lalle ina lullube da kaina na ji an shigo an zo an durkusa a jikina a hankali na bude ido don ganin waye hakan? Inna na gani da sauri na saki wani lallausan murmushi yaya Dija ta zo ne? Ta ce a'a babanmu ne ya zo da mu ni da Abba, sannunku da zuwa na mike na zauna ina nunam ata kwanukan da na san akwai abinci a ciki don taci ta girgiza kai nuna alamar ta koshi. Buki baba Abba Gana ya yi irin wanda yake yiwa ya'yan da ya haifa a cikin shi kona ince fiye da haka dno kuwa yayi hidima ya ciyar da jarna'a abin ba a magana, bayan san kowa daga jama'a ne aka yi daurin auren bai yarda an dauki amarya kamar yanda abokan Mubarak suka so su yi ba sai ya ce tafiyar tayi nisa baza a dibi mutane masu yawaa yi irin wanan tafiyar da su ba a cikin dare. Don haka aka bari sai washegari a waunan lokacin ango baya zuwa wurin daurin aurenshi don haka Mubarak bai zo Gaidan ba yana Kaduna wurin harkokinshi. 97 Washe gari ana gama karyawa akayi ta shiri ana fita don shiga motocinda zasu dibi jama'a ganin da Baba Abba yayi kaiyade masu zuwan zai iya kawo bacin rai yasa shi yin shiru yace su angwayen su debi adadin abinda suka ga zasu iya diba su kuwa su Amiru da Abdulhamid suka ce duk wacce take son tafiya kawai ta fito, mata kuwa sukace me za su yi ba tafiyar ba. An fito da ni aka kaini wurin Abba Gana a lokacin nan kuwa yana tare da dan uwanshi Baba Goni alamar da tafiya ta zo ke nan kuka nakeyi sosai daga kuma cikin zuciyata kukan ke fitowa saboda tausayin abubuwa a yanzu kuma sa naga zaa tafi sai naji bana son tafiyar cikin dangin ubana. Yakumbo Halima ta shigo dakin ga alama kuma kiranta akayi suka gaisa da baba Abba a cikin yanayi na mutunci da girmamawa, kece uwartasu? Tace eh Mallam suka dan yi hira kadan a cikin hirar tasu ta sake jaddada mishi ita da inna mu uwa da uba daya suke ita ta sha nono ta bar mata, to Ubangiji ya jikansu da Rahamarsa in tamu tazo kuma yasa mu cika da imani aka amsa amin amin, to mun gode fa mun gode mun gode yayi ta nanata godiyar tamkar dai wani abin akayi mishi sai da suka soma yi mishi sallama zasu tafi sai ya ce, to ungo ana Kabudi mika musu wannan sadakin da uban mijinta ya zo dashi ne wannan kuwa ni na bayar in kunje ku sai mata abinda kuka ga ya dace Yakumbo tasa hannu biyu ta karba tare sa yi mishi godiya me yawa. Motar amarya itace motar da ta tashi a karshe kenan duk sauran motocin sunyi gaba kafin ita daga ni sai 98 Yakabudi ne kuma a bayan motar yiuyin da Amini da wani wanda ban sani ba suke gaba. Kafceciyar wayar cellular da ke hannun Amiru tayi kara ya dauka tare da anmsewa, ran ango ya dade ban ji abinda Mubarak ke gaya mishi ba na dai ji shi Amirun ayna ce mishi, gabn daya jama'a dai sun taso suna ka hanya amma mu garu nan a kofar gida ba ma taso ba saboda shi warnan baban na ta da kake bani labari ya ki bada ita. s Mutumin dake tukin ya yi murmushi, kai Ahlaji Amiru kar ka se ango ya shide kai in banda Allaji Adbulhamid ya dage ai da cewa ya yi wai shi ma zai biyo mu in yaso ko a Goabe ya tsaya shi nc ya ce sai dai ya taho mu mu zauna. Kai dai muna hanya amma mn biyo bayansu ne, ban san abinda yace ba naji Amirun ya sake ce mishi to amin. Muna zaune a bayan motar ni da Yakabudi bacci takeyi saboda gajiyar hidima da kuma sanyin AC da ya ratsaya, ni kuwa tunanin al'amura da yawa nake yi Innata na fara tunswa 'yar rayuwar da mukayi tare dan sanin da nayi mata mu'analar da nakeyi tunawa a tsakanina da ita, rasuwarta da yanda hakan ya zama sanadi na la'amura masu yawa, zamana da babana, mu'amalar da ta gudana tsakanina da shi, na tausayawva da kulawa har kawo zuwan baba Lantana gidanmu al'amuran da aba Lantanat ayi mana sanadinsu a Zuwanta gidanmu tausayin babana ya kama ko ncc ya kara kamani musamnan da na tuna yanda ya bar gida ya bar danginshi ya fito ya soma rayuwa tare da lanaia rayuwar da da kunnena, na ji shi yana tabbatar mata da 99 cewar ita ce banagre mafi dadi da rayuwarshi ta dandana yazo ya rasata a lokacin da bai zata ba ya yi bakin ciki irin wanda bai misaltuwa bai gama wattsakewaa daga rashinta ba da kewarta ya zo ya fada hannun baba Lantana, alamuran da sukayi ta faruwa har kawo wannan lokacin da muke ciki, wata rana sai labari ai babu wani abinda yazo ya tabbata in dai ba kudurar Ubangiji ba ne, wannan jimlar jimlace da mutane daban-daban suka yi ta furtamin ita a lokuta daban-daban bisa faruwar al'amura edaban-daban sai dai ban taba kawo tsammanin wucewar tasu za ta zo min a haka ba saboda tsananin daci da ciwon abubuwan da sukayi ta faruwar sai na rinka ganin tamkar ba zai wuce ba na rinka ganin tamkar ba zai wuce ba na rinka ganin tamkar nawa mas'aloli da damuwowin ba masu wucewa ba ne masu dawwama ne don haka şai na zamo a duk lokacin da wani babba ya tabbatar min da cewar zasu wuce wata zai wuce har ki ganki kina bayar da labari sai in samu kaina da tambayar kaina to yaushe ne? Yaushe ne wata ranar da zai wuce? To gani a yau sai na samu kaina da yarda da cewar tabbas mutum mai gaggawa ne mai sauri ne a kank al'amuranshi, saboda ganin da nayi tamkar daurin aurena da Mubarak da akayi kawai ya kawo karshen al'amuran duka zamana da baba Lantana da ma shi baban nawa a gida daya ya kare, lissafin da ake tayi min na dadewar da nayi babu aure a ce nan kusa babu sauran sa'a ta shima ya kare a yau ni din matar aure ce, matar ma kuma ta Ahmad Mubarak wanda duk kwaramniyar a kanshi aka yi ta yi haka na zurfafa cikin tunani mai tsawo nayi nazári mai zurti kan al'amuran rayuwa da kai 100 kawon al'amuranta abubuwan da na shiga da wadandA idona ya gane min sai na kara tabbatarwa kaina da cewar rayuwar gaba daya wata rana zata kai ga kaaewa, tausayi ya yi matukar kamani har na kasa hana idanuwana zubar da hawaye. Sannu a hankali sai gashi ahr mun iso garinmu har gamu muna shiga unguwarmu, bude ido ki gani Maryan nisan tafiyar da kika sanyamu ta kare gamu mun iso gida, Amiru ne ya ke yi min wannan magana,r ban tanka mishi ba. Babana na hanga a kofar gida cikin kwalliyar da ban taba ganin yai irin ta ba, habbar riga da 'yar ciki da wando ga kafceciyar hularshi ta zanna a kanshi, bakin da ke fita daga cikin motocin dake tsayawa yake yiwa sannud az uwa wadanda yan uwanshi ne da suka biyo motocin amarya sai dai nasan 'yan daidaiku ne kawai zai iya shaidawa a ciki sauran duk sai anyi mishi bayaninsu, tunanin babana ya sake dawomin ban taba yin kwana bakwai ban ganshi ba don ban taba zuwa wani wurin da na bar shi na abr unguwaru da aka haifeni da gidanmu naje na kwana bakwai ban dawo ba, to inama nake zuwa? Gidan yaya Dija ne sai ko Yakumbo Halima da sauran dangin Inna nan din kuwa bana iya zaman da zanyi kwana bakwai nake gudowa in dawo gida sai wannan karon de nayi tafiyar dana kwana sittin da daya. Ganin da nayi za a wuce kofar gidanmy bayan nayi zaton nima a nan za'a saukeni yasa nayi maza na cewa Amiru, a'a a'a ba a nan za a saukeni ba? Gaba daya shi da mai tukin suka hada baki wajen tambaya ta gidanku? Ai furta kalmar na bayar na karar mishi da baba sukayi 101 tare da baba Abba Gana ya rabaki da shiga gidanku ba tare da izinin angon ba yarinya shi kuwa tuntuni aikina jin wayoyin da yake tayi jaddadawa yake yi lalle ne a wuce da ke gida kar a ce za a tsaidake a ko ina, ban san dalili ba ina jin bayanin na Amiru na soma yin kulka hawaye suna ta gudu a kan fuskata, a hakan aka shigar da ni gidansu Mubarak sashin Umman shi aka fara kaini itace ma ta jagorance mu ta wuce gaba muna biye da ita a baya zuwa inda tace can din ne wurina muna tafiyar ina tunanin shekaru biyar ne cif har da wasu watanni ban shiga gidan ba da nake shiga irin shi tafiyar da mukeyi kafin mu isa inda zata kaimin ya sani fahimtari rin canjin da gidan ya samu a shekarun da nayi ban shiga ba. To ga nata wurin nan bismilla ina jin ta fadi hakan na soma karanto addu'o'i iri-iri ko dama can kuwa tun isowata kofar gidan nake addu'ar ban fasa ba man tarar da su anti Kubra, anti Hindu, Hasiya Jibrin da mutane da yawa wadanda ba zai yiwu in yi ta lissafinsu ba, aikin jere suke ta yi daga ganin jama'ar dake wurin dai kai ka san ba karamar gaiyata yaya Dijat ayi ba. Mun kuma shigo. ne muka sama su Yakumbo Halima da su baba Sumaye da suka rigamu isowa suna fadni, kai masha Allahu tubarakallahu Ubangiji ya yiwa Hadiza albarka mafi yavwancin mutanen dake wurin sukayi a amin, amin, ita kam ai uwa ce ba ya ba. Wani daki da babu komai a ciki daga labule sai katifar da aka yiwa shinfida mai kyau aka kaimu ni da Yakubudi ina shiga anti Kubra ta biyomu ta yiwa Yakubudi sannu da zuwa ni kuwa kallona tayi ta tsuke fuska kafin ta ce min, maza share hawaye ki hadiye 102 kukan da kikeyi ya ishen haka na gani a wurin Hadiza jiya tun da akayi waya akace an daura auren ki da Alhaji Ahmad take kuka tun ina rarrashinta ina bata hakuri har sai da ta kureni nayi mata kaca kaca nace ina dalilin da za ki tara jama'a irin wannan ki yi t skuka a cikin su, to maza kema sharesu ni ma ina nan kika tuna in na naki kukan na dadin ganin burinki ya cika ne kin auri mijin da kike so duk daya kar in sake ganin hawaye a idonki Ban tankawa anti Kubra ba iyaka dai dama nasana halinta na kuma san tana cilkin mutanen da suke sen yaya Dija. Hasiyan Jibrin ta shigo na lama ji dadin shigowar tata, kin gani abokan tasowarki har sunyi salla suna cin abinci ke kina zaune wanan doguwar tafiya ai ko mura kike ya rage ga ruwan zafi na zube miki ki yi wanka si ki yi alwala ki yi salla ki dan ji dadi, nace mata to kafin in idar har ta tanadar min abubuwa masu saukin ci wadanda ba za su gunduren da sauri ba irinsu strawberry grabus citrus da apple masu ban sha'awa wadanda ko don kyansu zaka iya 6ata lokaci mai tsawo kana cinsu basu gundureka ba, itama Yakabudi ta kai mata tare da abincinta tana ci ita kuma ta dawo wurina muna hira, ai naso in zo her Gaidan din nayi maza nacem ata gara daa bakije ba Hasiya da Walid yasha wahela tafiyar tayi tsanani da yawa, ta yi murmushi ta Ce, to ba biki uwarshi akeyi ba, na yi murmushi a karo na farko tun bayan da bikin ya fara na ce, ai kuwa da uwar tashi bata kyauta mishi ba don da ta wahalar da shi. Hira kadan aukayi sai naji ta soma tambayata ina ata dai kin shigo ne da shirinki shiri kamar yaya Asiya? A 103 hankali cikin muryar rada ta soma yi min bayani, shirin rike mijinki a hannunki mana ko kin san yau kwana hudu kenan da dawowar uwargidanki daga yaji, gabana ya yi mummunan fadiuwa saboda a anzu zaman lafiya nafi so ba fitina ba, duk da ta gane faduwar gaban da na samu bata yi shiru ba sai ta ci gaba da bani labarin da take son bani alamar dai ta matsu sai ta gaya min, ai rikici mai yawa akayi bayan tafkiyari ta ja ta tsaya kan in dai Alhaji Ahmad zai aureki to ita ya sauwake mata saboda wai kina waje ma baki bar aurenta ya zauna latiya ba balle kuma a ce kin shigo gida gaba daya kuna daga ita har yan uwanta sun mara mata baya.suna fadin ai da aurenki gara a ce wasu kishiyoyin ya kawo mata su zama hudu, wajen kwana talatin ta yi bata nan shi da abokanshi suka yi ta zuwa biko ana yi musu wuiakanci wasu abokanshi har suka fusata suka ce ya saketa ya ce a'a ashi ba zai yi aure don ya rabu da ita ba ne dukanku yana sonku ya kuma yi alkawarin matukar ba ita ta tsoma kanta cikin abinda bai shafeta ba zai yi iyakacin kokarinshi wajen ganin yayi adalcin da zai tsarevwa kowa hakkinshi. Na yi ajiyar zuciya mai karfi ba tare da na ce mata komai ba baya ga Ubangiji ya bashi ikon yin hakan saboda iyakacin gaskiyata nake nufi nafi son zaman lafiya a kan gutsiri tsoma. Sau biyu anti Kubra ta kawo min kan wayar telephone din dake dakin wai in kar6a zai yi magana da ni ban kara ba saboda sai nafi son ya kyaleni kawai in zauna shiru ko zan samu natsuwar da nake bukata a tare da ni, tunda na soma gane cewar nan gidan nashi dana zo ma zai yi wuya in har zan samu zancan shirun da nake 104 Dukata don ina daga kwance na jiwo baba Sumaye tana cewa, kun ga dangin uwargidan nan babu abinda suke nema in banda a yi rikicin da za a yi kaca-kaca a bikin nan to na rokeku kar in ji wani cikinku ya kulasu. Tana fagfin hakan na ji mutanen dake wurin su na ta bayaninai mu ma kaza mu ma kaza tun jiya suke yi. mana wulakanci abu kaza da kaza har suna gori wai.. Yakumbo Halima ta katse masu kokarin yin bayanin kan irin gorin da suke yin tare da fadni, abin dai bai yi dadi ba da kwabar yarsu suka yi suka nuna mata muhimmancin zaman lafiya da yafi musamman ma da yake akwai sanaiya mai karfi a tsakanin mu da su, haduwarsu karkashin miji daya kuma wannan kaddara ce su dukansu biyun matan shi ne in banda haka ai da Mero ya fara aura da ya aureta a wancan lokacin kuma da ba ma zaton zai koma auren 'yoarsu to kaddara don haka mu ba ma fada da ita sai dai mu yi mata addu'a, yanzu ita wacce tayi sanadin abin ina take? Itama ba ance shekaranjiya ta tafi ba itama ta yiwa kanta sanadin nata auren saboda sharrinta, shi mutum duk yanda ka kai da kinshi ai baka iya hana shi samun abinda kaddararshi ta rubuta mishi in da hakan yana yiwuwa ai da auren Mero da Alhaji Mubarak bai yiwu ba. Na zaro ido ina kallon Hasiya Jibrin don son jin karin bayani kan maganar da na ji Yakumbo Halima ta fada na wacce tayi sanadin da aurena da Mubarak bai yiwa ba a wancan lokacin itama ta yiwa kanta sanadin nata auren na kuma san da baba Lantana take nufi, sai Hasiya Jibrin ta gyara zama ta ce min, ei ai ranar da ake shirin tafiya daurin aure baba yasa a yiwa 'yan kasuwar timatir dinsu 105 abinci na musamman ya ce su ci a kuma zuba nmusu a kula a sa musu a motar da suka yiwo shata saboda nisan tafiyar sai baba Lantana ta ce zata yi wannan tana kai kawo tana hidimar girki ana raha ana barkwanci da ita har muna cewa a'a kaga baba Lantana abin mamaki ta sake sai hidima ake ta yi da ita, ashe ashe baba Lantana da abinda ta shirya, kamar baba ya sani ya ki fita daga cikin gidan nan har muna ganin kamar ya daan takura mana ashe ashe in bali labari sai kawai idonshi ya kai kan baba Lantana tana zuba wani abu a cikin abincin nan bayan an gama shi ai kuwa dai nan da nan ya isa wurinta ya tambayeta me take zubawa a çikin abincin? Ta ce bata zuba komai ba ya yi yayi ta ki yarda da cewar ta zuba wani abu ya ce to ta diba tayi nan ma ta ki. Hannu biyu na saka na dafe kaina saboda sarawar da yakeyi a dlai in tsoratar da nayi ban iya barinta ta kai karshen baya iin ba na tambayeta me take zubawa a ciki Hasiya? Sai ca ta kuramin ido kaíin ta ce, guba su ci su mutu ko ince duk wanda ya ci ya mutu, salati na rinka yi ina karawa kr fin daga bisani na shiga yin hamdala ina godiya ga Ub.ngijin da ya yiwa babana wannan rufin as rin bai barta ta ja mana wannan abin akin cikin ba ko me muka yiwa baba Lantana ni da babana ta ki mu irin wannan kiyaiyar? Akmar in tsaya yin wannan tunanin sai kawai ma na kavwar da shi na kalli Hasiya na ce, to sai aka kare a ya ya? Ta ci gaba da takaicin abinci ta kama kuka da zage- zage wai zai kulla mata sharrin da ya saba kulal mata, ya ce a'a ai babu sauran sharri je ki na sauwake miki auren ya isa haka, za ta yi rashin mutunci su Anti Kubra suka 106 fitar da ita daga gidan aka dauki abincin aka je aka tona rami aka juyeshi aka rufe don kar wani abu mai rai ya ci, na ce hodijan na kame bakina nayi shiru. Rannan dai da daddare bacci ya gagara ta yayi gaba daya mutanen dake dakin sunyi bacci amma ni idona biyu. A baya a duk lokacin da na kan zauna in yi tunani a kan yin aure na kan ga kamar yin auren hutu ne amma tunda auren ya gabato ni na samu kaina cikin wani irin yanayi da yanzu da wadannan al'amuran suke ta faruwa sai na gane lalle akwai wani babban al'amari a cikin don haka maimakon in yi ta juyi idona biyu ni kadai saboda bacci ya gagareni sai na koma karanta kalmar Lahaula wala kuwwata illa billa kalmar da Manzon rahama ya tabbatar mana da cewar tana maganin musibu kala daban-daban har guda dari daya babu wato casa'in da tara mafi kankantar musibun nan kuwa shi ne bakni ciki har gari ya waye ban daina ba da na idar da sallar asuba ma komawa nayi na kwanta na ci gaba da karantawa. Ina cikin haka sai ga anti Safara ta shigo dakin da nake nayi maza na mike na zauna na tare ta da murmushi cikinta ya fito ta kuma kyau ba kadan ba. Amarya ta ango, anya da wata amaryar dá ta fiki morewa kuwa Yahcuwuna? Nayi maza na katse murmushin da nake yi kafin na tambayeta, wacce irin morewa kuma anti bayan duk wannan kwararmniyar? Ta ce kin auri mijin da yake sonki ban taba ganin so irin wanda Alhaji Amadu yake yi miki ba kwaramniya kuwa ina ruwanki da ita tunda dai kinyi sa'a Ubangijin mu ya 107 rufa muku asiri ke da babanki duk abinda akayi nufin ya same kun bai sameku ba. Nayi maza na ce haka ne anti, to zuwa nayi yanzu don in ganki in gaya miki kisa hannu biyu ku karbi al'amarin mijinki kar ki yarda ki tsaya sakarci ko tunanin wai ko ke amarya ce a'a yi hidimar aurenki kawai ke ko iya shegen nan amare a yi ta tsiya ana wani iface-iface ban yarda ki yi mishi ba kin ji na gaya miki, hannu biyu na saka na rufe idona tare da fadin ki yi min irin tuwon da kike yi min jiya anti. Zanyi miki ma yafi na jiya dadi ki ci tare da angonki don nasan ba wuya ace ya wuce yau din nan bai dawo ba, kisa hannu biyu ki karbe shi in yaso babu kuma ruwanki da kwaramniyar da take cikin gidanshi kar ki daga ido ki kallesu balle su ganekin san abinda suke ciki, ita mace da kike gani ko wace da halinta tak Zama, nace to na gode anti, tayi min sallama ta tafi har cikin zuciyata sai naji dadin iin kalaman da ta yi min. To haka akayi wunin bikin ranar cikin wani irin cikar da ba zai ki atantu ba ta wurin mu ma dai muna da yawa ga yan uwn babana da suka rakoni daga Gaidan ga dangin Inna ta wadanda su ma masu yawa ne babu laifi ga gaiyar yaya Dija na kawaye da dangin mijinta masu kara nan gidan su Mubarak ma ba a magana uwargida kuwa kai kace tamkar da gadara yan uwanta suka zo don su nuna su din masu yawa ne. A wancan lokacina marya 6oye kanta take yis aboda k unya da kawaici ba kamar yanzu ba da amarya ke kai kawo a tsakanin yan bikinta sai dai hakan abi hanani tsala ado, wuni nayi ina kwalliya ta burgewa kwalliya 108 kuma mai tsada da kowacce nayi sai kaga kamar kar in cireta saboda ina tare da gwanayen kwalliyar irinsu malama Hindu da malama Basma ga uma anti Asiya wacce ita dama babbar sana'arta kenan gyaran amare ciki da waje, in nace ciki da waje kema sai ki gane abinda nake nufi. A gaba daya sashinmu a wancan lokacin bakina ne bikin farko da mutanen mu suka sheda video coverage ana daukar su ana kuma yi musu tambayoyi, me zaku ce game da wannan aure na Alhaji Mubarak da amaryarshi Maryam? Wasu su yi magana wasu kuwa kunya da rashin sabo ya hanasu cewa komai in banda kyalkyalewa da dariya wasu kuwa da abin yayi matukar burgesu duk da sun kasa cewa komai fadi sukeyí yau ku zo ku gani bin mutnae akeyi ana yi musu tambayoyi da irin abin nan na masu rahoto. Malama Basma itace tayi magana ta ilimi har ta samu jan hankulan mutane gaba daya aka koma sauraron bayanin nata tayi magana ne a kan matsayin aure da kuma' menene kishi a musulunci, tayi magana sosai ta kuma karfafa magangnaun nata da ayoyi da hadisai tare da kawo misalai na manyan mata magabata yanda suka tafiyar da rayuwarsu tsakaninsu da mazajensu da kuma kishiyoyin nasu duk da ba wai basa kishin bane ya sa suka yi hakan a'a sai dai su fahimtarsu a kan kishin daban mu ma a yau tamu fahimtar daban. Da ta kawo karshen jawabin nata sai tace ya ku yan uwanam ata ina kira garemu da mu yi gyara a kan yandaa muke tafiyar da al'amuran da suka danganci kishinmu a yau mu daina kishi na jahilci kishi na rashin sanin ya 109 kamata mu koma yin kishi irin na shari'a wanda shi ne ibada. Wassalamu alaikum wa rahamatullah, gaba daya wuri ya kaure da kabbara malama Ubangiji ya saka miki da alheri abinda kowa ke fadi kenan. Ana gama wannan aka shiga yin hotuna wai duk ribibin da kaeyi nayin hotuna da amarya ita Rumasa'u da kyar ta yarda aka yi mana hoto guda daya ni da ita da aka kawoni dakinta kuwa kamar yanda aka saba bisa al'ada na kai amarya wurin iyayen miji da uwargidanta in har tana da ita yan uwanta basu ji kunyar fadin babu wata amana tsakanina da ita ba tundai ta din ba wan girmana tayi ba banda haka kuma ai banbancin dake tsakainta da ni kadan ne iyaka ita tana ciki ne ni ina waje ba manyan dattawan da suka kaini ba wadanda shekarunsu suka kai fassara musu al'ar ari ko da kuwa da kafa ka iadeshi ba da baki ba ko ni da nake lullube a gabansu na gane abinda suke uui, to balle kuma su a haka muka tashi muka fito aka dawo da ni dakina tunda dama sai d aka kaini wurin Umma kafin a kawo ni wurinsu mun dawo' daki nuka ci gaba da harkokinmu sai a wata yar uwarta ta shigo wai ga kudin sayen bakina marya an manta ba a bayar ba, anti Astya ta ce, aki haba a1 babu komai mayar masu kawai, ita wannan amaryar

Chapter 7 of 11