Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 11
wata manufa shi yasa na nemeki me akayi mata? To in an yi mata sai ta nemeka da fitina wane irin al'amari ne wannan? Me akayi miki? Nayi shiru kenan gobe ko ya ganki kina yina binda kika ga dama kar ya nemeni don ban isa ki gaya min damuwarki ba? Ya mike ya fita ya barmu ni da ita, tana ganin yaf itant a soma yi min fada mai tsanani ni kuma na soma yi mata kuka dont ayi shiru taki yarda ta yi shirun. Ke ba za ki gane abubuwan ba ne, a halin da ake ciki fa ni babu mai sona a gidan nan nice bare, su kansu a hade yake in banda kwarata babu abinda ake son gani. Me suke yi miki na kwarar? Nayi shiru na rasa ta inda zan bullo mata, to a soka a gidama ai halinka ke ja maka kuma yaushe kika zo gidan har kika soma wadannan maganganun? Kenan har kin fara samun mas'ala da mijinki Maryam in banda mummunan tarbiya da kika samu? To kin girma gaban mai cewa miji ya kunshe baki kamar masai ai ni dama gabana yana faduwa ina tunanin wane irin zaman aure za ki yi? Kuka sosai ta soma yi har tana fyace majina da zaninta, wace irin magana kike so kija mana? Yanzu a irin yanda akayi auren nan naku da irin dawainiyar da mutumin nan yayi babu abinda ba a fada ba babu wahalar da baiyi ba ga 6acin rai a kan aurenn ne fa mnatar tayi ta tsalle tana cewa gara mata kishiyoyi hudu da ke ke kadai bata sani ba ma ashe sakarya za a 139 kawo mata, kai ba a kyautar zuciya Maryam da na samo Wacce tafi dacewa dake na baki. Ganin 6acin ranta da ambaton matarshi da tayi ya sa ni ce mata, to ai yafi sonta da ni kinga bare-baren da yake yi ne... ban karasa ba ta katseni, ba dole yafi sonta dake ba ita sulhu take nema a tsakaninta da shi ke kuwa kina nemanshi da fitizaa, haba in banda namiji bai gajiya da abinda yake so wane dadi yaji ne a tare da ke kuma karya kike yi mishi wane bare-bare zai yi a kanta da ya wuce wanda ya rayu yanayi a kanki? Kurna sai me in ya yi ba matar shi ba ce, ba da ita kika sameshi ba, na kara tsaranta kukan da nakeyi saboda tsananin bacin ran da kalaman anta suka kara min gaba daya yaya Dija ba zata fahimceni ba ban san yanda akayi ba sai naji bakina yana ce mata kwacemin shi akayi aka bata, kwace min shi akayi saboda ita tana da gata ai ba nata bane ni ba mijinta na aura ba ia ta auran min. To yan ya ya za ki yi Maryau? Tambayar da ta yi ta fito a lafazi na baiyanar da canjin da zuciyarta ta samu, ki yi hakuri ai kaddarace ta yi miki hakan ba wani ba ne, itama matarshi ce rabon ta kuma yaî naki zafi baki ga ke har yanzu baki da komai ba? Ita wate tara babu kwana biyar tayi ta haihu a gidan nan ina lissafi ban yi magana bane kawai kina nufin da ya aureki a wancan ba zai aureta ba'? Zai aure ta domin 'ya'yan dake tare da itan nashi ne. Don haka ki yi hakuri, ina share hawayena da bakin gyalena na ce, to shi kenan ni na hakura ya daina taba ni bana so bana so na hakura da shi tunda rabon ta ma yafi 140 nawa karfi to na bar mata shi ni ya kyaleni kawai, na ci gaba da wani kukan. Mubarak ya sake shigowa bayan ta amsa sallamarshi bari muje in saukeki sai in wuce don za ni Bauci, to ko zakaje kawai in na gama sai in tafi? Ya ce a'a uje kawai ai babu damuwa. Ta tashi suka tafi amma dai ranta a bacei watakila saboda ganin kamar zuwan nata bai samar da wata mafita ba. Ina zaune a falon ni kadai ina tunanin haushina takeji saboda bata san kishi bà saboda tayi sa'a ita kadai ce a gun mijinta ba zata iya fahimta ta ba saboda bata taba jin irin zafi da ciwon da nake ji a cikin zuciyata ba. Da kyar na iya tashi nayi wanka nayi salla na hau gado na kwanta ko nemarwa abin da zanci ban yi ba ina jin Rumasa'u tana ta kyakyacewa da dariya na kuma san dadi ne ya kamata Mubarak ya yi tafiya a ranar da zan karbi girki. Nayi duk abinda na sabayi na al'adata na sa makulli na kulle kofata na hau gadona na kwanta nufina wai in yi bacci da wuri sai dai baccin bai daukeni ba wajen karfe tara da rabi na dare na ji ana kwankwasa kofar tawa, na tso nazo na bude shi na gani a tsaye fuskarshi a daure alamar ranshi ya baci da kulle kofar da nayi, ban ma tsaya a falon ba balle in yi tunanin yi mishi wani abu ina jin shi ya. yi kaikawon da zaiyi ya gama maimakon ya shiga dakin da yake kwanciya ya kwanta sai naji shi ya shigo wurina nayi maza na gyara rufata. Tashi muje wancan dakin, nayi maza na ce mishi a'a ni a nan zan kwana.... wani irin cafka ya yi nmin mara 141 dadi kan kace meye wannan sai gani a inda yake nufin ganin nawa, yi hakuri ki sa hannu ki rage kayan jikin naki, na sake cwa uh'uh ba zan yi ba bana so kar kuma.. nayi maza na canza maganar saboda ganin abinda ya soma yi to ai kai kace baka tilasta mace ko sanda kake da guda daya ma baka yi hakan ba balle yanzu ya ce eh ita kadai zan rinka yiwa wannan adalcin banda ke tundakin bari na ganc ki na riga na gane ita daba ke daban, ni kuma zan iya zama da ku dukanku bisa tsarin da ko wacce take so banda haka kuma daga yau ba zan sake kai kararki ba tunda na gane baki da mutunci mara kunya kawai sokuwa sakarya wacce gata yia hanata fahimtar abinda take ciki, zagin da ya yi min din zagi ne na wulakaci bai kuma hanashi yin duk abinda ya shirya yi ba. Ance miki tsoro ne ya sa ni, kai traganarki wurinia? Tana da girma ne a wurina da kika barta har ta fita baki bata hakuri kan bacin ran da ta gmu da shi ba a dalilinki, sannan duk maganar da kikayin naji wani abin da baku i. himta b ke da Rumasıi'u shi ne ni din babu wacce za 1a sa ni n yi abinda banyi niyya ba, sannan baa zan saki wata a cikinku wani kato yaje ya auran min mata ba, ba kuma zan yarda in karkata karkatar da zata cutar da ri ba, dukkanku ing ennku ina kuma son dorewar zamana da ku don haka zan zauna da kowacce ne a bisa tsarin da ta nemi mu yi zaman ni da ita wacce ta nemi zaman lafiya mu yi wacce ta nemi sabanin haka ma ina shirye in wani zai yi min laifi in kyaleshi kuma ina tabbatar miki in kikayi min ba zan kyaleki ba, ba zan yarda ki bata min rai ki ga kamar kin ci bulus ba za ki 142 rinka tuna wane da kikayi min kaza nima nayi miki kaza ba kalau kik kwashe ba, don haka admision din da na saman miki na karanta Is!amic law a jami'a na janye shi na fasa ba za ki yi karatun ba. Na soma kuka ina bashi hakuri ya ce ai sai ki yi ai ba hauka nake yi ba saboda kishi sai ki hanani taba jikinki tsawon wata guda? Kina so ne ki rinka tirsasani da hakan? Ai itama ban barta ta ci nasara a kaina da hakan ba balel ke, zuciyata ta kara kutata zafin da ke cikinta ya kara karuwa kwoacce magana zai yi sai ya hadani da ita kowacce magana zai yi sai ya nuna min ta fini, za ki rinka tuna sanda kika hanani kanki na hanaki, karatu saboda na gane wanda kakayi a baya bai yi miki amfani ba don bakya aiki da shi nan gabe in kika koyi sanya iliminki a cikin aya kanki sai mu san abin da muke ciki. Babana a shirya zuwa Gaidan wurin danginshi karo na farko cikin shekaru talatin dabiyu shi da anti Safara da jaririnta da su yaya Dija yaya Ibrahim nema zai kaisu a cikin sabewar motar da tace min Mubarak din ya bashi banje musu sallama ba banje musu sannu da zuwa ba saboda bai ga dama ba, na rame na zube haskena ya ragu saboda abubuwan da na samu kaina a ciki, a hakan kuma na soma girkin gidan gaba daya saboda yace in karba ko dama can kuwa tund awowar da' mukayi daga Jaji na soma yiwa baba abincinshi na safe da na dare saboda kasancewarshi mai lalurar suga. Banje ko ina da fara yin girkin ba naji hirar Rumas'au da kawarta tana gaya mata cewar a'a abubuwan sunyi sauki sun kuma lafa daman ashe doki ne kawai ya firgitata har ya nemi sata ta gudu ta bar ladanta 143 ai yanzu wayar gari take yi tana kwance tana hutawarta a dakinta nike tashi da sassafe in yiwa yara wanka in shiryasu in basu abinci su ci su tafi makaranta dole kuma in yi ko don in zauna da shi lafiya tunda shi a kan ya'yanshi babu abinda ba zai yi ba ko ita da ta haifesu lallabashi take yi in dai a kansu ne. Raina ya baci na samu kaina cikin wani al'amari nayi kamar in daure in ci gaba kawai da abinda nakeyi sai kuma naga ba zan iya in dai hidimar yuran zai iya zama sanadin zarnana to ina ganin gara kawai ya zama ko na samu in huta da 6acin ran da nake gamuwa da shi gashi ko bacci bana iyawa matukar yana dakinta to ni kuma bana iya bacci da daddare gashi tsakanina da shi abin ya ki dadi. Na kar6i girki ina cikin dakina a wkance da safe ban fito ba balle in yi abincin karyawa ball in yiwa yaran wanka, Ummulkairi ta shigo falon ina jinta ana gaya mishi baba wai inji mamauau wai zamuyi lattin makarant, to menene? Wai anti tazo tayi mana wanka ta shiryamu. Ina jira i ji kiraná zaiyi ko me zai yi Sai naji ya ce mata ke tafi bani wuri ba a dade ba naji isowar uwartata na ce Ummu tazo ta gaya maka za su yi lattin makaranta, ya ce to menene? Ta danvi shiru kafin ta ce, nace. wai wankan ba zata fito ba ne? Wacece mai wankan? Ke kuturwa ce da ba za ki yiwa 'ya'yanki wanka ki shiryasu ba, sai wata tayi musu? Ta ce ahh hakama zaka ce? To su bar zuwa makarnatar mana ya' ya na ne? Ai dama na sani tunda ka samu kwana biyu...: ya yi maza ya katseta, in kika 144 gayamin magana a gaban yara, bata tsaya ba ta juya ta fita, ban san yanda akayi ba sai naji an tafi kaisu makarantar bai kuma dai fita ba balle ince ko shi ya yi musu girki biyu a jere ban yi ba. Rannan ya zaunar da ni yana tambayata, kina da mas'ala da shirya yara da safe ne Maryam? Na ce mishi ch, menene mas'alar? Na ce a canzamin wani aikin kawai ba wannan ba, bai ja ba ya ce, to ki rinka yi m usu lesson, na ce to, za ki yi? Na ce eh zan yi, ay ce to shi kenan na tashi nayi tafiyata ba tare dan a tsaya gaya mishi wani dalili ba balle aje ana kace nace, da na samu zarafin gaya mata magana kuma sai na gaya mata cewar ni din zama kaina nake yi a wurin mijina ba zamanw ani ba duk wata kunatawa da zan yiwa wani to zan yi ne don in kara gyara auren nawa amma ba don ina tsoron kar ya zamo mishi wani sanadi ba. Rannan ya dawo daga tafiya ya shigo dakina ya sameni Inna da Izzatu suna gaisheki da sauri na tambayeshi kaje ne? Ya ce min eh, na ce amma baka gaya min zaka ba'? Ya ce e ban yi niyyar cewa najen ba sakon da ta bani in baki ne ya sa na gaya miki, tana ta tambayata wani har yanzu haka kike babu komai? Nace mata eh shi ne ta bani wani ita ce tace ni kawo miki wannan amma na gaya mata cewar ke din maganin hana haihuwa kike sha, ban yi mamakin jin maganar a akinshi ba don naji irinta ko makamanciyarta a bakin Umam bance mishi komai ba na sa hannu biyu kawai na karbi Itacen na ce mishi na gode na kai daki na adana. To a haka abin yake jifa-jifa zan danji wasu kalamai Suna fitowa daga bakinshi wanda nasan ba ganin abin yayi ba gaya mishi aka yi kamar in tambayeshi ta inda 145 maganganun suke zuwa msihi sai na fasa na ja bakina kawai na yi shiru. Ni da Rumasa'u kuma a wannan lokacin wani irin zama m ukeyi na kai da gindi iyaka dai naki yarda mu yi zaman gaba zaman da babu wata mu'amala a tsakaninmu ko bata kulani ba gaisheta nakeyi sai dai hakan ba yana ufin zata yi min in kyaleta ba ne ina kuma mu'amala da yara in musu lesson in yi musu alheri gawargwadon iyawata in kuma sukayi min ba daidai ba in hukuntasu tun ina yi m usu hukuncin a ce su jira babansu in ya zo Su gaya mishi har abin ya zama rikici tsakanina da ita ban daina ba shima ukam ban taba ji ya yi min magana ba. Rannan Mubarak yana dakin ban san yanda akayi ba dasawamukeyi tuns afe dai nasan yake tattalina yake tarairayata watakila saboda yana bukatar daren ya zamo mai cike da kwanciyar hankali, to dansa hannu ki rage kayan jikin nan naki mana Maryam yaushe rabon da ki yi min irin wannan mututnawar? Ba fa najin dadin irin wadannan abubuwan na tashi zaune na soma cire kayan jikin nawa saboda nima ba jin dadin karfin da yake gwada min nake yi ba, dadi ya kamashi, yanzu in duniya tana da gaskiya Maryam ni ace tsakanina da ke zaki iya hanani jikinki? Wannan jikin dai to na wane ne? Ban kalelshi ba nace naka ne, to me nayi miki ya sa kike gayawa mutane ba za ki yi a zama da ni ba? Wa ya gaya maka? Ya ce uh'uh kar ki tabmayen wanda ya gaya min kin fada ko baki fada ba? Cikin natsuwa na ce mishi, na taba gayawa yaya Dija banda ita ban taba gayawa wani ba itama kuma nasan ba zata fada ba, ya yi maza ya ce 146 haka ne me nayi miki? Bance mishi komai ba sai naji ya ce min, kishi ne ya yi miki yawa Maryam ni kuma bakya barina inji tausayinki sai kice zaki tirsasani, ba zan iya ba ba zan iya yarda da hakan ba saboda ina gani na cancanci abubuwa guda uku daga wurinki saboda dalili guda daya, na cancanci kulawa tausayawa da kuma rangwame, ki kula da ni ki kyautatamin saboda kasancewata a tsakaninku a tsakanin naku kuma ina cikin zargi, dole kuma in yi adalci saboda shari'a bata barni in yi abinda naga dama ba ta kewayeni da dokoki in nayi miki kuskure kuma ki yi min rangwame saboda kin san kuskure nayi kin sani sarai ba zan 6ata miki da gangan ba ai ina gudun 6acin ran naki bakya ganewa na wadannan abubuwan kuma don kin yi min su ba komai bane saboda ina sonki ba dabi'ata bace fadin hakan amman kin sani na koya karfi da yaji a hakan kuma ban tsira ba. A hankali na ce mishi, to ka yi hakuri, ya ji dadi sosai, a hankali ya sake ce min, to yi min wani alkawari bayan hakurin da kika bani don in kara samun natsuwa a raina, ba zan sake hanaka jikina ba, ya sa hannu juyar da ni ta yanda muka fuskanci juna, ba za ki sake ganin bacin raina ba kenan ai ko laifi kikayi nasiha kawai zan rinka yi miki ba fada ba, ai da wata ce tayi min yanda kika yin sai in bata wata shida to amma ke da yake kin san ba zan... na katseshi ta hanyar tambayarshi, ya cem aka ina hana kaina haihuwa? Ya ce uh'uh ai nace kar ki tambayen amma ba ga magani nan Inna ta ce ta kawo miki ba ki sha ba me yasa? Yaya Dija ce ta ce in ajiyeshi tukunna, ya danyi shiru kadan kafin jimawa ya 147 sake tambayata, da ma ita antint asan da wani abu ne? Nayi shiru to shi nę ni ba za ki gaya min in sani ba, Inna ma in gaya mata hankalinta ya kwanta, kinga yanda ta kosa taji kina da wani abu kuwa sai kace bata taba ganin jika ba. Tun daga ranar muka koma zama mai dadi tsakanina da shi sai dan abinda ba za a rasa ba ban sake yarda wani abu ya faru tsakanina da shi da ya zama dalilin da nayi mishi rowar kaina ba, hakan kuma sai ya zama sanadin raguwar bacin rai a tsakaninmu. Ana cikin hakanc ikina ya kai watanni bakwai yaya Dija ta soma yi min aiken magugunan zaki da saukin nakuda sai dai bana sha don basa yi min dadi rannan ta zo dubani muna hira sai ta ce min bakya shan magungunan saboda bakinki ya saba da zaki bari zan Rara tambayar baba Lami inji rake ne yake maganin zaki ko zuma ne? Wadannan kam ai za ki sha ko? Nayi maza na ce garama dai ace raken ne, to ki dai bari in kara bincike tukunna nace to. Tun daga washegarin ranar na soma shan rake a matsayin maganin zaki da kuma saukin nakuda, sai in wuni ina sha ina gyatsarshi ina karawa in naga ya kusa ya kare mi ince Isiyaku a kawo min rake ya ce to ya kawoshi cikin wheelbarrow, ke Maryam kin tabbatar raken nan da kike sha haka maganin zakin ne ko? Ince mishi eh baba Lamin gidan su yaya Dija ce fa ta fada ita kuwa ka san babba ce haihuwarta goma sha hudu sai Mubarak ya ce min to babu laifi. Rannan na wayi gari bani da lafiya nayi maza na yiwa baba abincinshi na safe da na dare na aike mishi da 148 shi saboda tun daga jin cabkar farko da nakudar nan ta fara yi min na gane uh lalle da magana ba karamin artabu za a yi da ita ba. Kafin hantsi har na fara gundura da ita na fara gurnani ina mita tafdijan yanzu duk uban raken nan da nayi ta sha dama haka zamuyi da nakudar nan? Mubarak ya kalleni ya kawar da kai, to rake da kika yi ta sha ba dadi kika sha ba? Na soma kuka, yayi maza ya dakatar da ni, ke Maryam tsaya in gaya milki mata fa basa kuka in zasu haihu har ki yarda ki yi abinda Rumasa'u za ta zo tana yi miki gori don ita ba ta kukan haihuwa. Hankalina a tashe na ce to kar tayi din mana ni ina ruwana? Ya mike ya kama hanyar fita tare da fadin, bari in kira su Umma su zo su kaiki asibiti da wuri tun baki jawa kanki wani abin magana ba a gidan. Sy Ynna syja sgugi daudau uba cewa uh uh uhh tafi can lalle yau za a yi ta, ba za a yi komai ba, lafiya yau za ki haihu ai duk wanda kika gani da danshi abinda ya ji kenan kafin dan ya kai ga zuwa hannu. Waiyo waiyo kwankwasona ai yau kam ina jin gaba daya zai ratattake ya zube a kasa da dai ace na san haka ne da ban bata lokaci ba ma wajen shan raken nan. Rumasa'u ta kyalkyale da dariya har tana neman wurin zama a dalilin dariyar ta tsananta lalel yau mata zasu haihu tafdijan. Takaici ya kama Mubarak ya rasa yanda zaiyi dani to wai ke babu dama ki rufe bakinki ki yi shiru ne? Umma ta ce a'a to wai kai ina ruwanka da ita ne? Nace uhun kyaleshi kawai bai san yanda abin yake ba ne waiyo waiyo kwankwasona. 149 Sannu Maryam, Umma ce mai yi min sannun sai in ce mata yauwa Umma na gode. A haka mukaje asibiti muka samu yaya Dija don an gaya mata za a kaini asibiti, ita kam saboda takaici ji ta rinka yi tamkar tayi amai don bakin ciki, to wai ke ba dama ki yi shiru ne? Sai ince uh uh yaya Dija ba ki fa san abinda nake ji ba kin san ke naki masu saukin kikeyi da rakin da magana, ganin da kukan da ihun kiran likitan gaba daya basu sa haihuwar tazo ba sai da lokacinta yayi wajen karfe goma da rabi na dare gabjejen yaro kato ga girma ga nauyi tubarkalla gashi mai kyau sai raba idanuwa yake yit amkar dai ace kallon mutane yake yi. Suna Mubarak ya yi irin wanda Rumasa'u da yan uwanta sukace wai bai taba yi ba ya kuma sanyawa yaron suna Muhammad ya kara yiwa babanshi takwara bayan da ya yi mishi da danshi na biyu wanda yake namiji 'yan uwan Mubarak na Jaji sunzo sunan ba kadan ba sun kuma zo min da alheri mai yawa, Inna ma ta cika alkawarin da ta yi na turo min Izzatu ita da Inna ne da kuma tsohuwar da aka daukar mun suke tayani hidimar jegon. Duk kokarin Mubarak na ya boye ya barwa zuciyarshi al'amuranshi don ya samu tsaida adalci tsakanin iyalinshi ya kasa kawar da kai a kan al'amarinshi yana ganinshi yake sakin lallausan murmshi na kuma san da wuya in har ya san sanda yake yin hakan. Wani irin lafiyayyan jego nayi ni da yaron muka zama tubarkalla in banda ina aka saka damu babu abinda Mubarak yake yi da mu. 150 Rannan ya shiga dakina ya fito a lokacin nan kuwa satina uku ne da haihuwa na tsala wata irin kwalliya da in ka ganni sai kayi zaton ranar ne zan karbi hidimar mai gidan, biyosyi nayi tsakar gida ina rungume da yaron a kafadata, karbeshi mana to ba ka ce wurin baba zaka ba? Kaje mishi da shi mana, maganata nakeyi ba tare da na damu da zaman Rumasa'u a tsakar gidan ba. Mubarak ya juyo ya karbeshi yana kara lillibeshi atre da fadin, ki fa rinkayin hankali da shi girman jiki ne kawai... bai karasa ba sai kawai muka jiwo Rumasa'u ta kwallara ihu da sauri muka juya don ganin abin da ya sameta kwankwaso naga ta rike da iyakacin karfinta gabana ya yi mummunan faduwa don tsoron abin da take shirin yi don kuwa damkar da naga ta yiwa kwankwason nata irin wanda na rinka yiwa nawa kwankwason ne a ranar da nayi gwagwarmaya da nakuda waiyo-waiyo kwankwasona, Umma ina jin dai yau din nan za a yi abinda ba a taba yi ba don gani nake tamkar kwankwason nan nawa zai tarwatse ne ya ratattake ya zube a kas,a me rake kai yara ku kira min mai rake. Mubarak dai tunda ya yi mata kallo guda daya bai sake ba balle ya nuna ya ji ko ya ga abinda take yi, hannu biyu kwai ya saka ya dauke danshi ya wuce ya yi tafiyarshi da shi ya barni nan wurin a tsaye ina kallon busasshen wulakancin da Rumasa'u take yi min, ni ba abin in sureta in fyadeta da kasa ba damben tsiya za mu yi kafin in kaita kasa don itama karfi ne da ita to balle a halin da nake ciki yanzu na jego danye. 151 Humhum hum waiyo waiyoo bayana in dai kuka raken yakema to ba zan sake shanshi ba, ta kwashe da dariya ai kuwa dai an bar dadi. Na shigeta nayi tafiyata na shiga daki na zauna ina jirani zuwan Mubarak don ya san da ni takeyi amma ya ja bakinshi yayi shiru. Yana shigowa na soma magana yanzu nan haka matar nan za ta yi tayi min irin wannan wulakancin a gidan nan ba za ka tsawatar mata ba? A fusace kwarai ya ce min an ki a tsawatar din sanda kikeyi ban yi miki kashedi ba? Bance miki za ki yi abin da za ta zo tana yi miki iya shege da shi ba don ita bata kukan haihuwa kikace tayi din, sai kuma yanzu da kika jawa kanki abin magana inje ina tare miki? Ba zanyi ba in taji kin yi shiru ba ki tanka mata ba za ta gaji ta bari ai babu abin da ya tabbata kar ki kulata kin ji? A kan dole na ce mishi to don na gane ba zai yi komai a kai ba. Ta tasoni a gaba abin har ba a magana, kyakkyawar dariya in taji nayi sai ta shiga kwalawa mai rake kira. Rannan kawai nayi sa'a tana cikin tsala tsiyarta a tsakar gida tana murde-murde da iface-ifacen a rike mata kwankwaso zai ratattake ya zube a kasa sai kawai na ji muryar baba yana kwalawa Ummana kira, ina Ummulkhairi ta ke? Da sauri Umman ta fito tana rike da dankwalinta a hannunta, gani Alhaji lafiya dai ko? Bai amsa mata ba ya soma jero mata tambayoyi, yanzun nan kina nan a gidan nan ake yin wannan iya shegen baki hana ba? Ko kina jira ne sai abin ya zama tashin hankali a tsakaninsu? A kidime Umma ta ce mishi, nayi magana Alhaji.. Da sauri ya sake tambayarta ba ta ji ba kenan 152 saboda kema ta raunaki? To ai kuma shi kenan na riga na gano kan al'amari na gane dalilin da ya sa fitina taki karewaa tsakaninsu shi ne na kina da bangaren da kike marawa da kinja kin tsaya a matsayiniki na uwar danki kawai wanda ya yi ba daidaiba ki tsawatar mishi da abin nasu bai yi tsanani haka ba don haka zanyi maganin abin in kuma na sake jin sunyi fada to na san mai laifin tunda na gane ita din fitinanniyar yerinya ce. Tu daga nan jikin Rumasa'u ya yi sanyi ta shiga tsoron kar wani abu ya hadani da ita baba ya ce itace mai laifin, ni kuwa sai nayi arnfani da wannan darmar nima muna hada ido da ita sai

Chapter 10 of 11