Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 11
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels HALIN RAYUWA 4 HAFSAT G. SODANGI Mr. Yunus Abdullahi Dabai 1 Hakkin Mallaka (m) Sodangi Copyright O Sodangi GODIYA Godiyata har kullum ga Allah take, Masanin yau da gobe, mai kowa mai komai, Gwani mai hikima wanda yayi halitta tasa duka bibiyu, ya kuma halicci mutum da Aljan don su bautata mishi, Tsira da Aminci su tabbata ga cikamakin Anabawa shugaban Manzanni, Annabin Karshe Muhammad (SAW) da Alayensa da Sahabbansa da wadinda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zauwa ranar Altiyama, amin. Godiya mai yawa gare ku makaramta litattafaina, m kusa da na nesa, Ubangiji ya saka da alheri ys kuma Rara karfafa zumuncin da ke tsakani, na gode. SADAUKARWA Sadaukarwar littafin ta lyayena ce, Ahaji Chindo Muhammad Sodangi da Hajiya Fevime Musa Sodangi, Ubangiji ya saka muku da alheri ya kums fara muku lafiya amin. TUKUICI Tukuicin littafin naki ne: KHADIJA CHINDO SODANGI (Mrs Nasiru ldris) 2 JINJINA Jinjinar littafin taki ce Amarya ba kya laifi (Manc Umar) Zuhuriyya lbrahim (Mrs LAwal Chindo Sodangi), Ubangiji ya raya Umar da imani. FATAN ALHERI GARE KU Fatima Abdulkadir Kazaure Hafsat Iliyasu Unguwar Rimi Khadija Usman Nasarawa Nafisatu Ibrahim Muhammad Fatima Ahmad Shehu Kaduna Maryam Muhammad Gusau, Zamfara Umaima Abubakar Umar Maijidda Uba Magaji Na gode, Ubangiji ya saka da alheri, amin. KUNA RAINA Hajiya Maryam (Mami) Dan Hassarn Hajiya Jamila Ibrahim Na Bature Hajiya A 'isha Balarabe (Jazan) Ubangiji ya bar zumunci amin. 3 LITTATTAFAN SODANGI: 1. Uwar miji 2. Naga ta kaina 3. Rabon kwado.. 16. Wacece ni? 17.Wata fuskar.. 18. Mijin ta ce 19. Garin banza... 20. Ga ni gare ka 21.Biyan Bukatar rai 22. Shamaki 23. Hattara 4. Cikar alkawari 5. Wayyo duniya 6. Yi wa wani.. 7. Abu naka... 8. Mata ma su duniya 9, Nufin Allah 10. Kifin na ganinka... 11. Daga kin gaskiya... 12. Da kamar wuya... 13. Mai uwa... 14. Duk daya... 15. Mata da kicin dinsu 24. Kyautata 25. Ayi dai mu gani... 26. Tabbataccen al'amari 27. In kunne ya ji.. 28. Halin Rayuwa 29. Mai Daki... Littattafan ba sa nufin yi da wani ko habaici ga kowa, sai dai an rubuta su ne don fadakarwa da nishadantarwa, ana neman afirwa ga duk wanda yaga wani abu yayi kamar abinda ya shafe shi, ba da shi ake ba dace ne kawai. 4 HALIN RAYUWA4 A wannan lokacin ba zai yiwu in iya kwatanta halin da nake ciki, ba na tsoro, abu guda daya dai da zuciyata ta kasa yarda da shi, shi ne a in bar Rauhani ya yi min abin da yake son yi min, da in har shi ya yi min hakan sai na gwammace ma kawai gara duk abin da zai faru da ni ya faru koda kuwa wani abu ne da ya fi hauka muni. Tsayarwa kaina wannan hukunci da zuciyata ta yi, sai ya zama dalilin da na samu kuzarin takarkarcwa na kurmawa Rauhani ihu da iyakacin karfina. A bar ni bana son aikin, a bar ni kawai na ce a bar ni. Abinda nake ta fadi kenan. Iskar da ke kadawa a dakin ta tsaya nan take kuma haske ya bayyana a dakin, sai ga Mallan a zaune a wurin zamanshi, hularshi zaune daram a ken shi, nimaa nayi maza na mike na zauna muka fuslkanci juna ni da shi. Maryam kin 6ata aikinki,kin yi duk abinda aka ce miki kar kiyi, kin yi musu, kin yi gardama, kin yi jayayya har da kokawa. Ya tafí yana fushi yanzu ya ya kenan? Ban iya buda bakina nayi magana ba, balle in iya amsa mishi tambayar tashi, saboda har lokacin ina cikin tsananin tsoro, jikina ma bai daina 6arin da yake yi ba. Ban sani ba ko ya gane hakanne yasa shi kawo shawarar cewa ya sake kiran Rauhanin ya ba shi 5 hakuri, ya yi aikin da ya zo yin don kar haukan da ya yi alkawari ya same ni. Nayi maza na ce mishi "Aa, a bar ni kawai." "A bar ki hauka ta same ki? nayi shiru ban amsa ba, "Kin gwammace kiyi hauka ko?" Na sake yin shiru, "To shi kenan tunda abinda ki ka zaba kenan, dulk abinda ya faru da ke dai ba za a sake kawo mana ke nan mu karbe ki ba, tunda kina cikin bijirarrun mutane masu taurin kai. Sakamakon taurin kai kuma nadama ne. Ina kuma yi miki albishir da hauka kafin fitarki cikin wannan dajin." Yana fadin hakan naji an daka min wata irin tsawa, wanda saboda tsananin tsoro na kasa fahimtar daga in da tsawar ta fito Tashi ki ba mu wuri." Abinda naji an fadi kenan da karfi. Ina jin hakan nayi maza nayi waje, yankawa kawai nayi da gudu ba tare da na tsaya neman takalmina ko tunanin ta ina na fito ina kuma ya kamata in dosa? Gudu kawai nake yi a cikin jejin nan, bana ko waiwaye ban kuma san inda na dosa ba. Gaba daya fatana da addu'ata bai wuce in isa gaban mahaifina kafin haukar ta same ni ba. Ina gudun ina kokarin jaddadawa kaina har yanzu dai da hankalina, hauka bata fara samuna ba tukuna, tunda duk abinda nake gani ina ganewa, ina kuma iya tuna komai nawa sai in yi maza in ci gaba da karanta addu'ar da damna nake ta karantawa Hasbunallahu wani' imal wakil." 6 Ina cikin haka na hango wani mutum a gabanta, tsoro ya kara kama ni, ina tunanin ko Mallam ne ya turo shi ya zo ya mayar mishi da ni, Nayi kamar in juya da baya saboda tsananin tsoratar da nayi, sai kuma naga to ai in shi dinne ma zan iya juyawar ya sake tare ni a inda na koma din, don haka na dake zuciyata na ci gaba da taiyata har naje kusa da shi zan wuce naga ashe manomi ne yake aii a gonarshi, sai dai ban iya buda baki na tambaye shi hanya ba, saboda kar ya gane ni din bakuwar jejin ce. Nayi tafiya rannan har na raina kaina, amma zuciyata bata gaji ba, ko tsayawa in huta bana yi, kokarina kawai in fita bakin hanya ne in ga gari in ga ta inda na bulla don na riga nasan na kauce banya. Ina cikin haka na sake hango wani mutum da sauri na nufi wurinsli daga nesa kadan na tsaya na gaishe shi nayi mishi tambaya kan hanyar da zan bi in shiga gari Barin abinda yake yi ya yi ya taya yana lallona, ke kuwa ya ya aka yi ki ka kawo yanzu cikin dajin nan? Ban iya ce mishi komai ba, don haka ya gaji ya ce min Kina kusa da gari sai dai akwai tabkeken rafi a tsakaninki da shi, in kin iya ruwa ze ki iya bin nan ki fada raf ki tsallaka, in kuwa kin san ba ki iya ruwan sosai ba, sai ki bi nari don rafin yana da zurfi, in an yi ruwa ya kawo ba karamin ta'adi yake yi ba. 7 Na ce, Na gode. Har na fara tafiya ta nan din da ya ce, sai naji ya daga murya ya ce min kiyi ta tafiya har sai kin ga yar gada sai ki hauta ki tsallaka za ki ga kauye a nan za ki samü abin hawa zuwa cikin gari." Na sake cewa "To na gode. Wannan hanyar da ya nuna min din ita nabi nayi.ta tafiya har na kai inda ya ce zan ga gada, gadar ta langa-langa ne, wanda mutancn wurin suka hadu suka yi don su rinka samu suna tsallakawa zuwa inda gonakinsu suke in ban da gudun ceton rai nake yi babu abinda zai sa in iya hawanta. Na isa kauyen, a lokacin da duhun dare ya riga ya sauka ya mamaye ko ina, ga shi babu haske ko kadan, don kuwa babu. wutar lantarki a kauyen, babu kuma hasken farin wata saboda watan ya kusa karewa. A haka na wuce kauyen nan nayi tafiya har inda na samu wani mai mashin da ya yarda ya fidda i bakin hanya a dalilin tsananin gajiyar da ya gani a tare da ni. A kofar gida na samu Babana a tsugune yana tashe da fitilar kwai, daga ganin ikuma nasan ya yi wahala ya neme ni har ya gaji. Ina isa gabanshi na fadi a kasa ina kuka tare da fadin "Ka yafe min Baba." Ban wani tsaya bata lokaci ba nayi maza na attaba mishi bayanin komai, tunda nayi saa nazo gabanshi da hankalina, shi yasa nayi maza na gaya mishi don ya sani saboda kar haukar ta Same ni yayi tunanin zai yi ta wahalar neman min magani tunda ba hauka ce da zata warke ba, ka 8 taimake ni Baba ka tsare ni wuri daya kar ka bar ni in yi ta yawo a tube irin yanda nake ganin yan uwan mahaukata suna barinsu suna yi." "Ke Yahcuwuna. Ya kira sunan nawa cikin wani irin yanayi na damuwa, "Ki daina yin haka bari fadin irin wannan maganar, ya ya ki ke yi wa kanki mummunan fata irin wannan? Nayi maza na ce, "Baba mai Rauhani ne ya gaya min ai har kokawa da Rauhanin ma nayi. Ya mika hannu ya kama nawa "Zo mu shiga gidan, na godewa Ubangiji da ya dawo min da ke lafiya." Baba Lantana ta galla mishi harara ta ce, "Uhun, ai kai kam ka shiga uku, yarinya ta tafi taje ta gama barikinta ta dawo tana dingishin ta samu wadanda suka fi karfinta, amma kana bari kana fadin wai ka gode Ubangiji saboda ta maida kai sakarai." Isyaku ya yi sallama daga tsakar gida ya tsaya yayi tambaya, "Baba wai Anti Meron ta dawo?" Da sauri Babana ya ce, "Eh, ta dawo." Ba tare da ya tsaya tambayar in ji waye ba, ta sake fadin "Ka ji wani irin rainin hankali ma Malam, sai ka ce ba tare suke ba, sai ka ce ba shi ya kawota ya ajiye ya wuce gidanshi.." tayi maza tayi kasake ta bar maganganun da take yi ta koma sauraron bayanin da Baba yake yi min. Ai ba za ki yi hauka ba, ai karya yayi miki ba Rauhani ba ne, shi mutumin ne da kanshi yayi miki wannan abin don ya samu ya tsoratar da ke, ki yarda yayi lalata da ke. Ba mutumin kirki ba ne, Boka ne. Ko 9 Malamin tsubbu. Ba da Rauhani ki ka yi kokawa ba, bai yi nasara ba ne a kanki saboda ke din mutuniyár kirki ce, uwarki ma haka, Ramatu mutuniyar kirki ce sannan bata da tsoro. Baba Lantana taja mummunan tsaki "Wannan Ramatu ai bata kyauia ba da bata jaka ku ka tafi tare ba.". Tuni sai ta bar maganar da take yi ta ni da Mubarak muka fita yawo, ta koma ta Rauhani da hauka don tafi yi mata dadi. "Hauka kam ai sai kin yi tunda Rauhani ya ce sai kin yi, to shi yana karya ne ma da za'ka ce mata ba za ta yi ba? Ba dai har nan dama Dijan take kai ba? Ai kuwa dai kun tsokano tsuliyar Dodo." Sallau yayi sallama ya shigo tare da fadin "Baba ashe ta davo?" Ai ta dawo Sallau ya sake fita ya sayo min shayi da biredi in banda yayi wannan dabarar watakila da haka na kwana ni da Babana ba muyi wannan tunanin ba, balle Baba Lantana. Kwana muka yi Babana yana rike da allon Karfenshi yana rubutu yana wankewa yana bani ina sha, saboda na kasa ko da runtsawa ne in yi saboda tsananin tsoron da nake ciki. Washegari da sassafe sai ga Yakumbo Halima da Yaya Dijah sun iso, ita kam Yakumbo taje wajen Yaya Dijah ne wai ta ji taje na karbo sakon ko ban je ba naki Zuwa? Yaya Dijah ta ce, "AI ma wunin jiya ba a ganni ba ana ta nemana kan haka suka rankayo gida don Su 10 gani na dawo ko ban dawo ba? In ban dawo ba a nufi gidan Malami." Sai suka zo sulka same ni, Babana ya kwashe bayani yayi musu, suka yi wa juna barka saboda ban yarda na ambaci sunan Yakumbo Halima cikin bayanin da nayi mishi ba, da ban san yanda suka kwashe ba. Bayan fitanshi ne Yakumbo ta rinka rantsuwa wai tana so in yarda bata san haka yake.ba, don bai taba nuna mata ba. Yaya Dijah ta ce mata "Haba Yakumbo, bari wannan rantsuwa da ki ke yi, za ki kai ta in da za a cuce ta ne da saninki." Wai a wannan dan zuwan da suka yi sai da Baba Lantana ta sossoka musu maganganun da Yakümbo ta tanka mata suka yi fada kaca-kaca. Ba karamin rashin lafiya nayi ba saboda wahala da kuma ciwon da kafafuwana suke yi, tayi a dalilin raunukan da suka samu ta hanyar taka kayoyin da ke watse kan hanyoyin jeji da kananan itatuwa. Duk da halin da nake ciki na kusan kullum sai Babana yasa allura ya cire min wata kaya a kafa, ba wannan ne abinda yafi damuna da tsaya min rai ba, irin tabbatar min da Babana yayi cewar shi wannan mutumin da muka je wurinshi ba kowa ba ne illa Boka' saboda ni da kaina na ta6a kamanta wani hadisi da ya ce, "Wanda duk yaje gun Boka ya kuma yarda da abinda Boka ya gaya mishi, to ya kafurta da abinda Manzon Rahama (S.A.W) yazo da shi, in kuwa yaje 11 wurin Boka bai yarda da abinda Boka ya gaya mishi ba, to zai yi kwana arba'in yana Ibadar da ba za a karba ba." To wannene mai sauki a ciki? Sai na samu kaina cikin wani irin yanayi ma tsananin rashin lafiya a dalilin tsananin tsoro da tasin hankali, babu abinda nake tsoro iris mutuwa a tsakanin wadannan ban samu yar nutsuwar zuciyaia ba sai da Babana yayi min bayani dalla-dalla, lokacin ne na dan samu natsuwar zuciya ta na koma yin Istigifari da kyautata zato wurin Ubangiji tare da kudurawa raina ba zan sake ba. Ba zan sake zuwa wurin wani ba da sunan neman taimako akan aurena ko a kan wani dalili na daban, dama can ban taba ba, in ban da warinan lokacin to ba zan sake ba gaba daya lamurrana dama ga Ubangiji suke, ga. t shin kuma zan kara maida su, in kara dogara in har da rabon zan yi aure an ubuta cikin kaddarar rayuwata, to zan yi. Dor nayi Imani da kaddatsare mai kyau da mara kyau. Sanna rashin auren in har an kame kai ba zai zamo munnaunan kaddara ba in har ba a rinka watsewa ba, nan take nä shiga tunano manyan mata da suka gama rayuwarsu ba tare da sun yi auren ba, ko suka bar shi a shekarunsu naa kuruciya suka maida hankulansu kawai wajen yin Ibadarsu, da auren da baa san ka'idarshi ba, ba a tsare mutunci da sharuddodinshi ba, ai gara barin shi yafi. 12 Nan take sai naji zuciyata tana kara raya min tsare budurcina da yin komai wajen ganin budurcin nawa yaci gaba da kasancewa a tare da ni, matukar ina cikin hayyacina saboda in zamo daga cikin 'yanmata masu mutunci da ke kaiwa mazajensu 'yanmatancinsu, ko kuma suke gama rayuwarsu su koma ga Mahaliccinsu da abinsu a tare da su. Kan haka sai na kara kudurawa raina cewar zan Kara kyautata sana'ata in kara riketa hannu bibbiyu don ta zamo min abinda zan rike wajen ganin nayi ta karatuna, ban zamo mai dora nauyina ga kowa ba. Kusan satina biyu a gida ban fita ko'ina ba, ina jinyar kafafuna a kwanakin nan duka babu wata rana da gari ya waye har yamma tazo ba tare da Baba Lantana ta jaddada min haukan da Rauhani ya ambata min zai same ni ba, don kuwa in ita muna yi mata rashin mutunci muna kwana lafiya, don kawai Faddarar wahala ta kawo ta gidanmu, ta auri tsohon ubanmu, to ai shi Rauhani ba zamu yi mishi iya shege ya kyale mu ba, tunda ba tsoron ubanmu ya ke yi ba. Ko kallonta bana yi, maganar tata kuma ba ta damuna saboda a yanzu, na ragë damuwa da al'amarinta, ban da haka kuma nafi yarda dá maganar Babana a kan tata, don haka ina cikin kwanciyar hankalina, ga kuma neman auren da nasan Yaya Dijah tana yi wa Babana, wanda nasan ba da dadewa zai tabbata, tunda na shaida abubuwa da dama da ta gabatar. 13 eNa soma zuwa Makaranta, wai ashe dan wannan neman nawa da Babana yayi a gidajen makwabta da ke kusa ma wai abin magana ne, ya madidi ake tayi da ni da shi ana fadin wai ai gashi nan ya ki aurar da ni yana jira sai ya samu' dan mai kudi irin Mubarak. To ga shi nan na gaji da zaman gidan na fara gudu ina tafiya abinda kake yi a boye zan fara fito da shi fili. Ko kula zancen ban yi ba, balle in samu wata matsala, tunda an yi wadanda suka fi ta, na kuma ga wucewarsu lafiya. Abu guda daya da yafi bani mamaki shi ne, kowa ko kuma in ce ko wadanne mutane a gidansu sukan yi al'amarinsu shiru. Babu mai cewa konai, amma ni da Babana kemai muka yi sai an ce mun yi. Da ana tsayawa á iyakacin abinda muka yin ma to da sai in ce da sauki, amma ina sai an kara. Ta gidin Yaya Dijah na bi da muka tashi don tasan naji sauki har na fara zuwa Makaranta. Na same ta cikin farin ciki an kawo mata adashenta da tayi wanda dama tàci alwashin kashe kudin gaba daya a hidimar auren da za'a yi wa Babana. Dadi ya kama ni, amma ko kusa ban kai Yaya Dijah murna da dokin auren ba, duk da kudinta take kashewa. Ina dawowa naje na samu Babana a runfarshi, na zauna ina shan timatir din da na dauka saboda sha'awar da ya ba ni, muna 'yar hira ina ba shi labarin irin kąratun da aka yi a kwanakin da ban je ba. 14 Ya ce min "Eh, ai shi karatu haka yake, in dai har kullum kana zuwa ana yi da kai, to ba ka gane yawan abinda ake yin ya dame ka ba, sai in ka yi fashin zuwa. Na ce, Eh Baba." A hankali sai na shigar da bayanin abinda na tarar Yaya Dijan tana shirin yi, shi ne hada kayan aure don maganar tana kara karfi tana kuma kara matsowa. Wani irin shiru Babana yayi, ya kafawa kwandon alayyahun da ke gabanshi ido ba ya ko kiftawa. Har tsoro ya fara kama ni, kar dai ya ce ba ya so. Cikin natsuwa 8ai na tambaye shi "Me ya faru kayi shiru haka Baba? Ya ci gaba da aikin shirya alayyahun nashi yana daurewa saboda mna su zuwa saye yana yi min bayani, Wato ba wai bana son auren ba ne, fitina nake tsoro. Ta zo ta kashe kudinta da tayi ta tattalawa bata yi wa kanta ko ya'yanta wani abu sun ji dadi ba, in zo ni kuma ban ji dadin abin ba, wannan ta gidan må ya ya aka kare da ita kullum tana raina abinda ake kai mata, balle kuma a ce an je an dauko yarinya an kawo, alhalin ba wani abu nake da shi ba." "Kai ai ina ganin kama wannan ba za ta yi wata fitina ba Baba. Tare muka je gidansu dazu cikin maganganun da naji Yaya Dijan tayi mata, har da na daki ta ce mata guda daya ne kuma bai da wani girma. Sai naji ta ce, "Ai babu komai, shi aure in aka yi shi zaman lafiya ake bukata ba wani abu ba. 15 Babana ya ji dadin kalamin nata da na gaya mishi, nan take ya ce "To babu laifi, sai lkuyi." Ya mike yaje ya dauko wani tsohon bankinshi na karfe ya kwakulo makullin a inda yake boyewa ya bani ya ce min bude ki dibi abinda yake ciki na dai san babu yawa, amma je ki ki kai mata ko sabulu sai ta saya." Na ce mishi, "To Baba." Na louma yi mishi godiya cikin farin ciki, don kuwa bakan alama ne na shima yana son auren. A natse kwarai na yi wa Sallau bayani, ko ban gaya mishi abinda za ayi da dakin bá, amma nayi kokari na fahimtar da shi ya gane cewar bukatar dakinne ya taso, ba son korarshi nake yi ba. Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min "To, tunda haka ne Mero, in rinka kwana a zauren gidan nan mana kawai, ai shima wani babban dalki ne, in na rufe kofar waje na rufe ta ciki ba shi kenan ba?" Nayi maza na ce "Kwarai kuwa Sallau, to ai ma shi kenan tunda ka samarwa kenka wata dabara. " A haka al'amura suka ci gaba har na kai ga fita daga dakina na koma na Sallau na kira mai gyara ya y wa dakin gyaran da ya dace kafin mai fenti ya zo ya yi. Ita bata yi tunanin ba dom a ranar da ake aikin ma wuni tayi tana fadin, To tunda babu tsayayyen da zai tsaya ya kwasa ya kai gidanshi, can inda ake ta harin kuma uwar yarinya taja tayi damara ba dai a shiga ba, sai dai a kare a titi. 16 Ai sai kiyi ta gyara kina fenti don ki ji dadin zama tunda ba ki da ranar tashi." Ban kalleta ba ma balle tasan naji abinda take fadi. Da daddare ma da Babana ya dawo naji shi yana tambayarta ni ina butar nan ne? Sai naji ta ce mishi, Ni fa Mallam na wanke butocina na tura su a Rarkashin gado, don na fara gajiya da wannan auren na zuba ruwa a buta. Kai baka da wani aiki sai na a baka ruwa a buta, don haka rinka yi da na roba kawai ga su nan a bakin famfo suma a wanke suke nayi maza na tashi na fito na ba shi butar da nake amfani da ita, na koma dakina can ciki na zauna. Ina jin ta tana cewa, To, ni in ban da na san in ta kasance a kanka dolensu su bani ciki da falon da nake ciki zan yi wannan susutaccen zaman ne? To dadin abin duk tsiyarsu su din mata ne, mata kuma ba wani Rarfi ne da su ba da dai suna da namiji a cikinsu ne ai da anga tsiya to babu shi." Ranar Laraba da sassafe bayan an idar da sallar Asuba aka daura auren Babana da amaryarshi Safara a Masallacin unguwar su Baba Baidu ne yaje ya karbar mishi auren. Yana dawowa daga daurin auren Baba Sumaye ta rinka rangada guda tana fadin, "Kai, wannan ya da jaruntaka take, to ashe ma tana da irin wannan kokarin ta bar ubanta yayi ta rayuwa a cikin wannan fitinar? Ubangiji ka yi wa Hadiza albarka." 17 Da yake Baba Lantana bata tunanin koma1 game da Babana musamman kuma da yake tasan mu'amalah tayi matukar ja baya tsakaninshi da Baba Baidu balle iyalinshi, bata kawowa ranta komai ba sai kawai ta rinka jan tsaki tana fadin "Munafukan unguwa, ko ina ta samo wata Hadiza kuma oho." Sai tayi maza ta sake jan wani tsakin don ta tsani Baba Sumaye, ta tsani kuma ta jiwo muryarta tana wata magana sai tayi tsaki tayi ashar ko ta ce munafukan unguwa. Tsohuwar aminiyar aminiyarta Delu, ita ce tayi sallama ta shigo gidan, rabon da in ganta kuwa an dan kwana da yawa, ina jin tun lokacin da ta shirya aurena da surukinta Alhaji Muhammadu Nalami, ta gaiyaci tsofaffin abokai don su tayata sheda isowar ta da mallakarta shekaru hudu kenan da suka wuce. Delu ce yau a gidan? Tayi mata tambayar cikin wani irin yanayi na wulakanci da shirin tozartawa, "Kun gama zagaye-zagayen gulmarmakun naku ne kuma ki ka gaji ki ka zo wurina? To ai babu abinda bana ji, duk maganganun da ku ke fada suna dawo min, musamman ma ke. Tunda ke kam ai butuluci ne yake sa ki fadar magana a kaina, ko ma menene a tsakanina da Nalami ai aure

Chapter 1 of 11