Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yanzu Sai tarin messages din da suka cika wajen ajiyar message suma sun cicika wajen wanda ta ringa bi da gagawa tana karantawa Tsaf ta ga na yanzu an bude shi, kuma ta ga sakonsa Zahrau ne ta ce" mu je mana meye wai kuka tsaya a nan bayan kun ga da mutun a bayanmu? NAJEEBA ta waiwaya ta ga Dogarin nan ne Karasawa ta yi wajensa shi kuwa ya sada kansa yana gaisheta Murmushi ta yi ta ce" baba dan Allah daga kanka, ku kam bakwa gajiya da wannan gaishe gaishen? Kawo sakon ka koma abinka ka ji? Da mamaki ya dago yana dubanta jin ta kireshi da baba Tabas shi din datijo ne, aman kasancewarsa a karkashin gidan sarakan bai taba ji ab kireshi da sunna baba ba Ko baki akayi in dai sun samu shiga ciki shikenan suma sun samu hanyar wulakanta mutane a bayan idannuwan manyan Sam sarkin bashi da hayaniya baya anfani da sarautarsa dan wulakanta mutane, aman na kasa da shi sunna anfani da damar nan Kwarai ya ji mamakin gannin kanwarsa ce, aman ta kiraye shi da baba Sai ya ji darajar yarinyar ta shiga idannuwansa nan take harma ya sakar mata murmushi yana kokarin risinawa dan godewa Kanta ta girgiza tana dubansa ta ce" ba dai zaku daina dukawar ba baba sai an jima Gaba ta yi ta karasa kusa da yan uwanta Tafia suka shiga yi suka nufi bangaren Anmy Hat sauran sun samu shiga ta tsaya Hannun Ummulkhair ta kamo ta saka mata sakon a hankali ta ce" eyah auntyna zan je na dawo wollah bako gareni Ummulkhair ta yi murmushi jin yanzu kuma ta zama aunty bayan dazu ta gama cewa zata wanka mata mari, Itama a hankalin ta ce" aman ai kin san ba'a zance a gidannan ko? Najeeba ta ce" ai nima ba a gidan zan yi zancen ba Kanta ta gyada har zata juya ta damko hannunta Tana juyowa ta sanyaya muryarta ta ce" kar ki manta abinda Ya ke fada mana, mutuncinmu darajarmu kin ji? NAJEEBA ta yi murmushi ta shafi gefen fuskarta sannan ta juya tana kalle kalle kamar munafuka ta kama hanyar fita Ta jina tana leke har sai da sahun mutane ya fara daukewa sannan ta samu dam dam ta bi ta daya daga cikin kananun kofofin gidan ta fice da sauri Tana fita ta cire alkyabar nan ta haska da hasken karamar wayarta ta samu waje ta ajiyeta sannan ta gyara lulubin lafayarta ta shiga takawa a hankali tana tafia Idannuwanta take tafe tana lumshewa dan jin wata sansanyar iska na busawa ta ko'ina Irin yanda wajen gidan yake da fadi da shukoki abin gwannin sha'awa, nan ne ake gudun dawakai Tun da ta tunkaro babar kofar fita gabanta ya fara dari dari ta fara tunanin yanda za'a yi su barta ta fita Wasu irin dafka dafkan mutane ne tsaitsaye a kofar fuskarsu harhada kamar basu san yaren fara.a ko sakin fuska ba Me zan ce masu dan su barni fita? Ta tambayi kanta tana mai dan ja ta tsaya tana hangensu Idannuwanta ta kuma lumshewa gannin bafa dare ya cika sosai ba ita kuwa niyarta ta je har saloon dan ko kiransu batai ba ta ga shin idan bata nan zasu iya kulawa da wajen yanda ya dace? Rufar jikinta ta kara gyarawa kafin ta hade ranta Tana zuwa ta ratsa tsakanin na faro, ta ratsa na biyu, ta zo na uku ne wata gabjejiyar murya ta dakatar da ita ta hanyar tambayar inda zata je a irin wannan lokacin? Sai da ta juyo ta kalli mutumen, sarai ta san ya santa ya kuma ganeta dan haka ta masa karyar ba yar cikin gidan bane bama bai taso ba Dubansa ta yi da kyau ta ce" sako zan karbo wajen Abih da suka fita dan rakiyar sarki Sannin cewa sarki ya tafi kuma ta tabata mahaifinta na cikin yan rakiya ta samu wannan amsar duda tana da shakun idan har zai yarda Ga mamakinta sai ya saki abin karewar ya bata damar fita kennan Hakan ya sakata dan kure shi da ido tana mamaki, sai dai gannin ya hade rai shima yama daina kallon nata ya sakata daga kafadunta har tana ayanna lale gidannan sun fara sasauta tsaro Shi kuwa tana fita ya juya ya danna kira ya shaidawa mai bayar da tsaron fada cewa eh ta fita A hankali take takawa tana gannin yanda garin ke walwali idan dare ya yi Manyan fitilun bakin hanya masu bada jan haske sun gama ko'ina sun haske garin Motoci da mashin da keke da masu tafiar kafa kowa na kai kawonsa tamkar ba dare ba Shagunna du a bubude Shagunnan atampopi ne, na dogayen rigunna ne, na jakunkunna ne abin dai ba'a cewa komai garin nada yannayi mai dadi da tsaro koda dare ya yi Bata da fito da ko sisi ba, dan haka ta yi niyar takawa a kafarta duda wajen sa dan nisa ta tabata ba zata rasa mai rage mata hanya ba Wayarta kuwa ta kunna ba zata kiraye shi ba sai ya kuma kira idan yana nan sai ta fada masa inda take idan kuwa baya nan ya yiwa kansa Har ta gifta tankamemen shagon da ake siyar da kayan kwaliya da su atash da turaruka na yan gayu masu jiji da kansu ta dawo Da wayo ta ringa hangen ciki Gannin yau Elhajin ne da kansa ba yaron nasa ba ya sakata hawa yar matatakalar kofar shagon ta tura baban madubin kofar dake kofa ta shiga Irin sanyi da kamshin yannayin shagon ne ya buso mata baki daya jikinta hakan ya sa ta lumshe idannuwanta sannan ta kuma budewa tana kallon shagon Bata yiwa kowa magana ba kamar yanda kowa ke sha'anin gabansa yana siye siyensa A hankali ta ringa bin wajajen tana dudubawa Abin turawa ta dauka ta shiga bi waje waje tana zabar manyan hodoji da su turaruka masu kyan gaske da tsada tana sakawa Sai da ta ga an rarage mutanen cikin shagon sosai sannan ta nufo wajen Elhajin tana tura keken daukan kayan Tana zuwa ta sakar masa murmushi cikin sansanyar muryar nan tata ta ce" barka da warhaka Elhaj Elhaji dake zaune da katon tumbinsa a gaba shima ya sakar mata murmushin yana fadin" barka dai yar budurwa sannunki da zuwa Bata amsa ba sai dauka da ta shiga yi da daidaya tana dora masa a saman table din bayan ba nan ake kaiwa ba akoy masu amsa su irga komai su fada maka nawa ne ka biya a zuba maka a leda a raka ka har wajen abin hawanka Daya daga cikin yaran ne ya taso da sauri yana fadin" Hajia ba nan ake kai kayan ba cen ake kaiwa Da sauri ta ce" eyah, ban sani ba ai Hannayensa ya saka zai kwashe kayan sai ya ji muryar Elhajin na fadin" aa kai bubakar barsu a nan nima ai ba wani abu nake ba zan irga mata Bari yaron ya yo ya koma suka ci gaba da kulawa da mutannen Sai da ta gama ajiye masa komai sannan ta dan taka karfen jikin kujerar dake gaban table din ta hau tana lumshe idannuwanta Ajiyar zuciya ta sauke tana yarfe hannunta ta saci kallon Elhaj ta ga ita yake kallo dan haka ta dube shi ta dan yatsina fuskarta ta rage muryarta sosai a hankali ta ce" na gaji sosai Kamar wani wawa ko yaro karami haka Elhaji ya saki daria yana fadin" sannu hajia ai da kin sakani dauko maki da kainama sai na yi aikin gashi kin sha wahala bayan kin fi karfin shan wahala Murmushi ta yi tana kara sauke ajiyar zuciya Muryarsa ya dan daga ya ce" kai dahiru dauko faro maza Da sauri saurayin da aka kira da Dahiru ya juya ya dauko ruwan faro ya ajiye har biyu a gabanta Kayan Elhajin ya shiga warewa yana sakawa cikin manyan ledojin kampanin yana yi yana kallon Najeeba wace ta kawar da dubanta tana danna wayarta Kiran gangan ta kara a kunnayenta ta shagwabe fuskarta sosai ta turo dan lebenta na kasa sannan ta lumshe shanyayun idannuwanta ce" yaya Irin yanda ta fadi yayan dole ko ke mace ki kaleta harma da sakin baki, domin jan yayan da ta yi sannan ta idasa da wani dan gurnanin kukan shagwaba Yan kafafuwanta dake jikin table din ta shiga dan bubugawa ta ce" yaya ina kampanin fa, har na zo na zabi abubuwan da nake so ka yi ka zo ka kawo kudin mana...... Ta kasan ido ta saci kallon elhajin, irin yanda yake sakin murmushi baki daya hakoransa a waje hakan ya baiwa kumatunsa damar kara girma, micik micik din idannuwansa suka kara dan shigewa sai dai kamshi kam yana ta fitar da kamshin miski kansa kuwa sanye da huka Hular dake kansa ya kara turowa gaba yana kallon shagwababiyar yarinyar Tashin hankali ya furt a kasan zuciyarsa Yo wannan na sameta nima na koma danye sharaf, dan na tabata idan muka fara wasan yar tserenmu a cikin falo ta dora tabara tana bubuga kafa ta ce sai na goyata Murmushi ya kara saki ya shiga zube mata kayan a cikin ledar Gannin haka ya sakata dan zaro ido ta kara fadin" aman yaya kace na fito sai mu hadu kuma kace yanzu an kirayeka wajen aiki? Shikenan ba komai Yi ta yi kamar ta kashe kiran ta dubi Elhajin Hannayenta masu tsararun yatsotsi ta hade, bakinta ta kara zumburowa ta kyabe fuskarta ta ce" ka yi hakuri Elhaji ka ji? Ka ga dama a kafa na fito motana ta samu matsala na yi tunanin mu hadu da yayana ya maida ni gida idan ya biya kudin kayayakin nan , sai dai kash ka ji wai an kirayeshi aikin gagawa ka san likita bashi da lokacin kansama Dan Allah ka yi hakuri Elhaj na bata maka lokaci da tsarin kayan nan Har yana inda inda ya ce" aa aa, idan yayanmu bai siya ba ni kuwa aikin me nake? Idanma da karin wasu a kawo su nan Hajia ai ke din baba ce Kikifta idannuwanta ta yi ta ce" ban fahimta ba Elhaj Wayarsa ya dora saman table din yana dubanta yana murmushi ya ce" ki dora min numberki nake nufo yan mata sannan ki bar maganar wai kudin kaya bayan shagonku kika shigo Murmushi ta yi a kasan zuciyarta tana ayanna zaka fada ne Sai kuma ta dan zaro ido tana girgiza kai ta ce" aa aa, ka rufa min asiri idan na je da kayan nan na ce wa ya bani? Yayanmu baya bari bayan nan yaya daga shigowa dan fita da kaya haka? Aa ba zan iya amsar kayan nan ba gaskiya Elhaj Kamar da wasa sai ga Elhaj na lalabar Najeeba cewa ta amshi kayan nan ba wani yawa kuma ai ita mace ce tana iya adana kayanta a dakinta Da kyar ta yarda aman tana ta dafe gaban goshi irin ya takurata amsar nan Cike da kulawa ya kara turo mata wayarsa ya ce" wanenen yayan nan namu mai sa'a a duniya da ya zama yayan wannan kyakyawar shagwababiyar budurwar? Wayar tasa ta kala kirar samsung ce babar gaske sannan sabuwa ce dal sai walwalin sabunta take aman bata dauka ba ta lumshe idannuwanta tana masa murmushi ta ce" sunnansa Ibrahim Adam , likita ne a baban asibiti na kashi Kansa ya ringa gyadawa cike da murnar jin hakan, nan take ya kuma tambayarta mahaifinmu fa? Dubansa ta yi duba irin ja wai Allah? Ta tabata wannan mutumen ya girmi Abih, aman da yake irin abihn ne gashi sai kira yake mahaifinsu sannan Yaya DAYABU yayansu ko me? Oh duniya yanzu du wace ta dan yi masa shagwaba kennan sai ya fada ya karba da gudu gudu shi kuwa? Sauka ta yi daga saman kujerar tana ganni yaronsa na jidar kayan yana fitarwa sannan tana gani ya saka kudi a leda guda irin kar ta gannin nan ta ki amsa Byron dake ajiye ta dauka ta duka ta rubuta masa number kanninta Najeeb ta ajiye masa tana murmushi ta ce" na gode Elhaj Shima murmushin ya yi da sauri ya saka takardar a aljihunsa har ya fara tunanin sauka da wuri yau dan ya je gida ya loda number ya yi kiranta Gasgi bata fada masa sunnan mahaifinta ba, aman ba komai koma yar gidan waye zai sani kuma shi ba da wasa ya zo ba da girmansa ba zai tsaya bin layi da kannanun yara ba dan ya san wannan samarin na zamani sunna yiwa wannan yar cakwai din layi Tana fitowa ta harhada kayan ta tsayar da dan adaidaita Yaron ne ya ce" an ce a kaiki fa Ta juya ta kalli wanda zai kaitan Kanta ta girgiza masa kawai ta shiga adaidaita sahun nan Direct sunnan shagonta ta fada masa sannan ta shiga lalubawa ta zaro kudin nan Murmushi ya saki tana gannin masu aku biyu wato jaka ashirin cif sababi Kanta ta gyada tana ayanna" yanzu haka baya fitar da zakah! Dan sahu na ajiyeta ta bashi kudin nan , nan ya shiga neman cenji dan haka ta amsa ta shige ciki ta saka a kawo masa Saloon din a cike take , sai aiki ake kuma a tsaftace take dan haka ta ji dadin hakan sosai Kayan aikin ta bude ta shiga lolodawa abinta wajen kayan siyarwarta, a hankali ta furta" halal na ci Zuwa ta yi ta zauna lokacin kuma karfe tara ta yi kuma a lokacin kiran ambasador ya shigo wayarta Bata daga a kira na fari ba sai a na biyu Zuwa lokacin ta amshi takardar tana duba wa'inda ke son kwaliya Byro ta amsa ta shiga dangwala ok a kan wa'inda zata iya yiwa a cikin satin nan sannan tana dora lokaci Sauraronsa take yana ta surutun dan me take bashi wahala ne Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce" ka san dai na yi missing dinka a lot ko? Shima ajiyar zuciyar ya sauke yana jinta Ta ce" ina saloon ka zo na ganka ka ji? Tana gama fada ta kashe kiran ta kara fefesa turare ta kara duban kanta a madubi sannan ta ci gaba da kimtsa abinda ba lalene su kimtsa shi yanda take so ba Bai dauki wani lokaci ba sai gashi ya tsaya a kofar shagon Mikewa ta yi ta fita Bude motar ta yi ta shiga, sai dai tana shiga wata ta fito tana kallon numbobin bayan motar Kanta ta gyada ta koma da sauri ta dauki wayarta tana neman number kawarta Da gagawa ta ce" kin kade kawata, kin kade, kin san da ambasador ne ya fita daga shagon NAJEE? Kawar nata ce ta zabura daga zaunen da take tana ciye ciyen naman da aka gasa mata rusheshiyar mata da ita bata da aiki sai ciye ciye, itane matar ambasador kuma uwar y'ayansa uku ta ce" wace najee din? Saloo? Amsa ta bata cewa" kwarai yanda na gansu haka Allah datar da ni gannin annabi kiri kiri Ji ta yi zuciyarta ta shiga bugawa da sauri ta shiga neman abinda zata yafawa kanta tana fadin" gani nan zuwa Su kuwa tafia suka yi mai dan tsayi ya tsaya wajen masu gashin kaji Siya ya yi ya shigo motar da su ya tayar ya karasa wajen stade, wajen da yawanci samari ke zuwa su kebe da yan matansu su yi hira cikin aminci Sannan wajen akiy duhu hasken bashi da yawa sosai Kashe motar ya yi ya dauki wayarsa ya haska yana duban fuskarta A hankali ya ce" ina son ki Najeeba, ke kuwa kina wahalar da tsufana Murmushi ta masa ta ce" ka daina kiran min kanka da tsoho, ka fi yaro karami a wajena kai din jarumina ne na yarda da hakan Kansa ne ya ji na huruwa ya kawo hannunsa a hankali ya shafi gefen fuskarta wanda hakan ya saka ta dauki hannunta ta bige hannunsa har wayar nasa ta fadi Ranta ne kuma ta bata ta ce" meye haka? Ka san dai ba kyau ko? Kansa ya dafe yana kallonta ya ce" wai wani irin ba kyau? Yaya kike son ringa cutata ne a rayuwa? Ni bance zan je cen ba, na adana zuwa cen har mu yi aure aman kuma dan taba jikinki ba zaki barni ba sai ki ringa hanna min ko dan ba ni ake yiwa son auren ba? Idannuwanta ta lumshe cike da rakaicin soyayar zamani, Soyayar zamani na bada gudunmuwa sosai wajen kokarin tatsar mazan zamanin da take Dan me maza suke kokarin nunawa mace iskanci koda kuwa da nikaf suka ganta? Yanzu har fadi ake masu nikaf din sun fi masu yawo ba hijab munafurci shin laifin matan ne ko mazan? Hannunta ta saka zata bude motar da sauri ya ce" hala har kin yi fushi? Kin ga kar ki min fushi dan Allah dawo mu ci kazarmu ki amshi tsarabobinki kin ji? Najeeba ta juyo tana kara hade rai ta ce" bude min na fita Hannayensa ya saka gaba daya ya janyota jikinsa yana fadin" come on baby meye na fushi bayan ko dan shan mintin nan baki taba barina na yi ba Sosai ya riketa a jikinsa ita kuwa ta saka dukan karfinta ta hankade shi ta mika hannunta da sauri ta danna mabudin dake gefensa ta bude motar ta fito da wani irin karfi Wani kukan takaici ne ya zo mata lokaci daya lafayarta ta warware Bayanta ne ta ji ya daki wani abu Da sauri ta juyo jin an rike damtsen hannunta Kamshin turaran da ta shaka ne ya so halaka tunaninta da sauri ta saka hannunta da lalube ta lalubo jin jikin baya dauke da babar riga hakama fuskar ba nadi Wata mota ce ta hasko wajen Idannuwanta ne suka sauka a fuskar wanda ya riko hannunta Idan ana fadin an yi gamo takan dauka a wai ne sai yau da ta yi gamo da kanta Wannan mutumen aljani ne , aljanninma mai aljanin kyau Girarsa biyu a hade take kamar ransa a bace sai dai kyan fuskarsa ya batar da bacin ran Wani dogon hanci ne da shi da lebunna jajaye uwa na macen da ta san kanta take gyaran kanta Kamshi yake mai dadi da sanyi Kirjinsa wasu rikakun pecto biyu daka daka ne suka gaje wajen Damtsen hannunsa kuma tamjar zasu fasa rigar jikinsa baka wace ta dame shi Tsayinsa sosai ya yi mata tsayi hakan ya saka gaba daya kanta ke kallonsa sama sama Rigar jikinta ta kasan abayar fara ce mai dogon hannu aman ta dameta sosai Ya take dayan hannun lafayar nata hakan ya sa take kara karkacewa Bata taba jin mutun mai karfinsa ba, irin damkar da ya yiwa hannun nata ya sakata jinta ficik a hannunsa Gaba daya jikinta ne ya kara daukan rawa tana dubansa shima ita din yake kallo yana son gane shin abinda ya fitar da shi ya ganni ko ba haka ba? Takaici, haushi, tarin tsanarta ne yake ji a ransa hakan ya sa ya kara matse tatausan damtsen hannunta Bakinsa ya buda a kausashe ya ce" To fa, waye wannan? Ina sarki? Zai samu damar hukunta NAJEEBA kamar yanda yake fata? Najeeba gamo fa kikai mun shiga uku=?2?=?2?=?2?=?2?=?2?[1/20, 9:50 AM] Ummu Suhan=? ?: >?????????????????????????????????????????????????????????????? & *[ T.M.N.A]* & =???=؊?? https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 13 Kansa ya kara sadawa sosai kafin a hankali ya ce" Allah ya huci zuciyar Anmy Zamanta ta maida ta gyara tana mai girgiza kanta, kennan ta tabata wata yake ganni har kamshin turaranta ya zauna a jikinsa? Cikin nutsuwa ta ce" kar ka manta kai ne mai hukunta laifin da ya kai hukunci, shin aikata abin hukuntawa ka yi? Sai da ya kuma lumshe idannuwansa ya bude a hankali ya girgiza kansa Ajiyar zuciya ta sauke jin aa, dan haka cikin nutsuwa ta ce" bana gane gabanka bare batanka SHAHEED, bana fahimtar me kake boyewa a cikin zuciyarka Maganarka ta kasance kadan Wata ajiyar zuciyar ta sauke sannan ta ce" koda kai sarki ne, ni mahaifiyarka ce Ka yi kokarin yin shawara da ni idan bata girmi kwakwaluwana na mace ba ka ji? Kansa ya ringa gyadawa a hankali sannan ya dan dago ya dubi fuskarta Muryarsa dai cikin nutsuwa ya ce" ALLAH ya huci zuciyar mahaifiyata Murmushi ta yi tana lumshe idannuwanta ta ce" idanma wacece ka aureta Wannan karon da idannuwansa ya bata amsa yana kara sada kansa a gabanta Murmushi ta yi ta furta" Allah ya yi maka albarka A hankali ya amsa da amen Bai tashi daga gabanta ba sai da ya cike lokacin da yake dauka a gabanta sannan ya mike ya yi mata salama ya koma bangarensa dan yau ba zai fita fada ba su waziri na cem sunna gabatar da shara'ar garinsa mai mutane masu rigima da saurin kawo kara Kamar wace ta jima bata zo dakin nata ba irin ta shekaran nan Da murna da komai ta shiga tana ta kara kallon dakin Jingina ta yi da jikin garun dakin nata, kai a duniya fa tana ji da dakin nan nata domin rabin tanadinta a cikinsa ya kare Bata tunanin ko dakin wata mai kudin mai auren zai nuna mata wani abu shi yasa take gannin idan ta tashi aure za'a kwashe komai a kai mata gidan mijinta ne Kalmar miji ta sakata buda idannuwanta *Mijina* ta furta a hankali Ina ka buya? Ina kake ? Yaushe zaka zo? Ko a ina kake na san baka da aure, Idanma kana biya yan mata kana da budurwa ka yi gagawar salamarta Zama ta yi saman kujerar dakin nata wace take da yannayin takalmi mai tsini ta dan talafe kuncinta A hankali ta ce" bana so ka zama farin mutun, dan rike NAJEEBA sai tsayayen namiji Farin mutun kuwa ya cika son jiki da sanyi sanyi Murmushi ta kuma saki ta dora kafa daya kan daya ta daga kanta kadan tana dan wasa da habarta ta ce" sannan ina so ka kasance mai lebe pink iya na kasan na saman ya zama baki....bai dameni ba idan an ce dan shaye shaye mai baki ja aman fa bana so ka zama dan shaye shaye ka ji? Hannunta ta dora wajen kirjinta tana kara dora kafa daya kan daya ta ce" kirji fafada, askin yan tasha........murya irin ta zaki, damtse mai taurin gaske Idannuwanta ta rufe da hannayenta irin ta ji kunyar nan ta ce" fafadan kirjin da zan iya kwonci na yi isashen baci da juyi Wani murmushi ta saki tana fadin" na san sai ka so mata, ....na san sai an so ramawa a so min kai abinda na fi sani shine ba zan yarda a karya min kara a ido ba! Ke NAJEEBA! Muryar zahrau ta sakata zabura tana kallonta , a rikice ta ce" meye? Zahrau ta ce" kin haukace ne kina zaune kina magana kasa kasa kina ta murmushi kina wani irin abu a saman kujera lafiarki kalau kuwa? Yanzu da nace kowace maza ta gyara dakinta ke ko kakaba baki fara ba bale shara bale guga kina zaune kina uban meye? Da sauri ta mike tana hararan Zahraun ta shiga yaye zannin saman gadonta ta ce" yaya ake so mutun ya yi kiba idan akoy irinku a waje? Shikenan ba zan zauna na hasaso yanda nake son gannin mafarkina ba sai an samu mai dirowa ciki ya katse ta hanyar sako nasa maganar? Yaya ake so mutun ya iya labewa ya samu lokacin kansa idan ba wada bashi da kys din dakin wani? Ni gaskiya ana takura min Zahrau ta tabe baki ta ajiye wayarta ta shiga tayata gyaran dakin tana fadin" yaya ake so a yiwa gandamemiyar budurwa aure a kaita dakin miji ta aikata abin kirki idan gyaran dakinta kawai na daukan mata awa biyu? A yi mata a ga ikon Allah, aunty ta yayama zan ringa aiki a cikin gidan ni daya bayan na gama tsara zan rayu da mijina tamkar abokan junna? Zamu raba aiyukanmu ne, mu rufe dakinmu mu saka kida muna yi muna casu abinmu, aunty ba zan iya auren namijin da bai iya rawa ba, ba zan iya auren namijin da bai iya sakani daria koda bana so ba, ba zan iya auren namiji mai tsare gida ba....Najeeba ta fada tana cilowa auntyn nata babyn nunus na zaki Cafewa ta yi utama ta jefa mata tana daria ta ce" gidan aure zaku gina ko gidan shedanu? Mace ai ita zata yi aikace aikacen gida , ta tsaftace ko'ina ta

Chapter 8 of 58