Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fi maimaitawa hankalinta ba a kwonce ba Ashe shine dalilin tarewar wadincen yan iskan yan uwan nasa a bangaren uwarsa ko? Shine dalilin zuwan mutane a yau din nan sosai gidan ko? Har ta fita tana takama ta bi ta gabansu ashe su daria suke mata sunna kallonta ne kawai??????? ?.................. Tana zuwa ta samu ta yi kiran mahaifiyarta tana kuka ta fada mata labarin da ya zama mumuna a wajensu Ranta bace ta daki gefen bed dinta ta ce" ke, ki nutsu, ki saki ranki a yi komai da ke Aman yanda na hakura mijina ya rabi wata y'ayana na haramta masu *ZINARIYA na rantse maki ba dai shi ya rabi wata ba in dai ina raye!* Da wadinnan kalaman ta samu jin dan sanyi a ranta sai dai cikin bacinta ta ringa jin mararta na kulewa, tana farkawa ta ganta cikin jinni, wanda dama an daure mahaifar ne dan kar ya zube tunda Aliyu ya rasu ta ringa dan zubar da jinnin nan Washe gari Abin da akai a kuraran lokaci sannan mai auren ya nuna ba zai yi taro ba aman bai hana cikar fada ba Sosai ake shagulgula an yanke sa dankara dankara wasu an shiga gashinsu wasu an yi madafa wajen masu aikin abinci aun dora su sai yi suke Masu busa na yi kamar ba da bakinsu suke busar ba, hakama masu doka gangar kidan barebari da makadan larabawa Kidan barebarin ya kasance kidan gado ne na mafi uawancin mutanen dake cikin garin damagaram *DAMAGRAM* Ko sunnan Damagram ya samo asali ne daga yaren bare bari wato barbarci hakama zinder dake nufin zindir Wajen ya dauke su, dangin mahaifinsa sun halarta du mata ne sai baza kamshin turaren wuta suke da takama da mulki...dama an san babarbare da dan karen isa koda kuwa ba jinnin sarauta bane Fararen barebari ne da suka samun farin a wajen mahaifiyarsu Allah ya jikan rai, mahaifinsu kuwa tsabar baki har wani shuni shuni yake Maakadan bare barin na yi ne da busa inda manyan mata masu ji da kansu ke dan takawa kadan su yiwa jinnnin sarautar kara Bangaren Anmy kuwa itama daga waje ne masu harkar larabawan ke yi wata mata ce ke wakar da makadanta sunna karkada wani abu yana yin cas cas cas Tun dazu a nan Najeeba ta fi auki, idan ta mike dan ta amsa kira ne da sauri ta dawo tana kallon dukan yanda suke yi Sai da ta gama fahimtar takun rawar nasu da irin yanda suke juya kugunsu da wani karfe a kugun nasu mai dauke da yan kannanun karafuna farare tass sunna kara yas yas yas ta mike ta zagaya wajen daya daga cikin marayan Da murna ta cire abin ta daura mata saman watsetsiyar shadarta da akaiwa wani irin zubi tun daga sama har kasa Na kafar ta amsa shima ta daura da kanta sannan ta kunce irin daurin dan kwalin da ta nada ta samu ta dora shi sama kadan ta dan soke shi ya bada kalar ture ka ga tsiya Ana gama dayar wakar aka saka wata, A hankali ta shiga karasowa wajen rawar tana kada iya kugunta banda saman jikinta tana dan juyi a hankali a hankali sannan na kafar natama tana kadashi da dabara hannanenta su duka biyu tana wasa da su ta hanyar juya su tamkar na macijiya tana wasa da su sak irin rawar kwararun larabawan nan Gaba daya wajen ya hautsine da buda da daria , Ido Zahrau ta zaro cike da mamaki tana kallonta, Bilkissu kuwa ta shige da gudu itama tama biye da yayarta sunna yi tare abin dai ba'a cewa komai Da sauri Anmy ta mike da alkyabar jikinta ta shiga takowa cikin nutsuwarta ta fito dan gannin da gaske ne abinda abinda Rukayya ta fada cewar ai ga Najeeba ta shige filin rawar Ai kuwa itama sai da ta zaro ido dan rawar da take din bata san a ina yar ta koya ba, uwa uba ita din kanwar sarki ce, gashi sarkin yana cikin gidan yana falonsa , falon da yana iya hangen du abinda yake wakana ta nan ta droon din dake yawo yana daukan dukan rahoton wajen ko ta windows dinsa wanda tana fitowa droon din kuwa na daidai ita Ajiyar zuciya ta sauke gannin gaba daya mawakiyar ta nufota tana ta kodata da larabci hakan ya saka har wani yam yam take ji Abin fa ya karkato da hankula dan harta kannen mahaifinsa sun maido hankalinsu, wasu daria suke sunna tafi wasu kuwa cike sa takama sula cire kai sunna dan tabe baki irin abin ya basu haushin nan Yarinyar baiwar dake bin Anmy da jakarta ne ta bi bayanta a lokacin da ta nufi wajen kidan Ido ya kura a hankali daga kwoncen da yake yana biye da droon din daidai anmynsa dan shi har ga Allah baima ga abinda ke faruwa ba ya dai ga fitowarta ne Gannin tana nufar wajen kidan nan ya dan lumshe idannuwansa a ransa ya furta" anmy, me zaki je yi wajen nan ne? Bai karasa tunaninsa ba idannuwansa suka sauka a kanta Irin yanda take kada kugunta tana yiwa anmy murmushi gefenta kanwarta ce itama tana kokarin yin irin na yayar wato mai sunnan gimbiya Aubahannalah Shine abinda ya furta a fili a hankali Fuskarsa ne ya shiga hadewa yana mai bin abin da wani kakausan kallo kamar a gabansa take Tunaninsa Anmy zata janyota ne ta fitar da ita, sai ya ga ta yi mata magana a kunnenta kafin ta kalli yarinyar dake rike da jakarta Buda jakar yarinyar ta yi ta duka sosai gaban Anmy Anmy ta saka hannunta ta dibo wani irin damin kudi dami har hudu masu aku ta dora saman kan NAJEEBA mai dauke da dan kwalin nan Bata gama hautsina wajen ba sai da ta ciro sarkar zinari ta dora sama Ai kuwa mawakiyar nan me zata yi banda kara kwarin muryarta da rangada guda sannan suka duka Najeeba ta sauke masu karinsu Hannunta Anmy ta riko suka fice a hankali suka fita baki daya Sunna fita ya kuma binsu da droon din Anmy ta juyo ta kalli abin Yar karamar yatsarta ta nuna ta ce" kin kyauta Najeeba, kin san sarai yayanku ya tsani rawa ko? Shine yau kika cashe a gabansa domin wannan abin da kike ganni yana nufin a hannunsa abin sarafashi yake Wani mukut ta yi da yawun bakinta ta matsa kusa da Anmy ta rage muryarta ta ce" Anmy ai kina nan ba zaki bari a min komai ba, kuma anmy alkawari ne na yi idan zai kara aure sai na yi rawa ni so na yi fa na kirawo Annabo Gaba daya ya zaro ido domin baki daya wani motsi da magana idan kana son ji zaka iya dannawa ka ji hakan ya saka shi dannawar dan jin da me zara kare kanta sai ya ji ashe ita so ta yi ta dauko makadin nan dake kade kade a cikin garin ta kawo shi wannan gida na alfarma ya kada mata me? Sai kawai ya ji yana sakin wani kakausan murmushi yana girgiza kansa Shi kadai ya san da abinda zai yi masu daga ita har makadan sai kamaninsu sun sauya Anmy ta ringa gyada kanta tana kallon yar tata A hankali ta ce" Najeeba, maza zo cenza kayan nan ku je tare da yan uwanki ku yiwa amaryar kwaliya domin daga an shiga salar magariba za'a shigo da ita ta baya Kanta ta gyada ta yi gaba abinta Sai da sukai salar la'asar suka fito su hudu reras cikin wani irin danyen lesh kowace da kalar da ta dauki fatarta Wasu tsadadun alkyaba ne suka dora sama wanda dole ka kale su ka kuma kallo sannan ka yaba koda baka shirya hakan ba Bayan wata dankareriyar mota fara kar suka shiga su dukansu Direba ne gaba da wani bajimin dogari zaune fuskar nan tasa uwa an zagi mamansa sam ba fara'a Da wani irin gudu yake ratsa manyan titunnan garin fit fit fit Kasancewar motar da number gidan sarki ne ya saka sojojin dake hanya da polisai sam basa gigin tsayar da ita duda ba sarkin ne a ciki ba A hankali NAJEEBA ta ce" *kudi* masu gidan rana kuna gannin mutannen mu da su sai kallo basa tsayar da motar dan tambayar takarda Ummulkhair ta yi murmushi ta ce" aa Najeeba, sarauta dai Kudi ai kowama yana iya yinsa Sarauta kuwa gado ce Ko baran gidan sarki wani ne a cikin garin sarki bale ka shiga wannan mota? Inaga ko kwaya ka dauko zaka samu hanyar shiga da ita je ba tare da an san ko meye a motar ba Najeeba ta lumshe idannuwanta ta furta" *Sarauta* wani sa'in sai ma ga sarauta ta cika izgili Kun ga cewa a fada aka daura auren nan? Maimakun gidan su budurwar tasa? Zahrau ta yi murmushi tana kallonta ta ce" baba da karamin kennan Najeeba ta yatsina fuskarta ta ce" ai shi girma ko wani iri ne hawa yake yana sauka Akoy wajen da zaki ga girman zai samu yaya wanda dole zai sada Idan har sarki nada zuciya a cikin kirjinsa.......to tabas zai saurari kidan wace ke motsa masa ita Ummukulsum dake kallon wajen da suka tsaya ne ta yi murmushi duba da irin wajen da sarki ya dauko mace Tabas ta yarda a yanzu cewa sarkinsu baya mu'amalantarka dan kana mai kudi ko talaka Yana mu'amalantar kowa ne bisa tsarin da ya zo masa Ashe da wata motar a bayansu wace ke dauke da wasu yan matan bayi su su shida Irin kayan gidan sarautar ne a jikinsu sun yi kwaliya daidai misali Hannayensu dauke da sako du suka layu a bayan su NAJEEBA A hankali suka ringa takawa inda Dogarin nan ke ta fama wajen ture yaren dake son taba su Najeeba, wajen kaiwa du wani wanda ya janyo waya dan yi masu hoto ba tare da sun amince da hakan ba Gannin gidan cike da jama'a ya saka dogarin sada kansa da neman alfarmar su koma mota ya fitar da mutanen ciki Da sauri Zahrau ta girgiza masa kai a fili ta furta" zamu cudu da su dan bama kyamatarsu Murmushi Najeeba ta sakar mata da ido ta jinjina mata Duda hakan sai da ya fara shiga ya shela cewa a bada hanya kannen mai martaba na tafe Sannan ya dawo da sauri ya koma gefensu da zabgegoyar bulaliyarsa a hannunsa yana kuma sama masu hanya sunna ratsawa a hankali a hankali Kallo fa ana binsu da shi gaba daya sun mimike sunna faman yi masu sannu Wani daki aka nufa da su wanda suke tunanin a ciki amaryar take Zaune take da zumbulelen hijab dinta da kawayenta su hudu Ba kujeru a dakin sai tabarma su kansu sunna zazaune ne saman wata yar katifa wace take ta kanninta domin dakin kanninta ne Kanta a sade yake tana jin gabanta na faduwa cike da tsoron dago da kanta dan gannin kannen mijin nata Har yanzu ta kasa gaskata cewa ita Bintu itace ta zama matar mai damagaram Zata iya rantsewa cewa bata taba gannin fuskarsa ba ko a hoto, haka kuma idan dai ta hange shi to sun fita kallon hawan sarki ne da yake yi ana gobe sallah wanda ke shaidawa al'umar garin cewa sallah ta kama a washe gari ne Takan hangi hannunsa daya tak dake rike da igiyar dokinsa dayan kuwa a cikin alkyabarsa Farin hannun wanda ke dauke da wasu irin jijiyoyin sai idannuwansa dake dauke da kwali wa'inda idan ya juyo yana mai bin jama'ar garinsa da kallo sannan yana dan amsa gaisuwarsu da ihun kiran sarkin da suke sunna biye da tawagar Wai yau ita Bintu yar gidan malan sulaiman itane Allah ya yi zata tare a gidan sarki? Ko a baiwa bata taba hasaso kanta ba Hakan ya hadasa mata rawar jiki cike da tsoron kannensama kafin a kai kansa Tana cike da zulumi da tsoron matarsa da aka yi tataki a jiya aka zo aka baiwa iyayenta labarin wacece Zinaria Ta san cewa ita tana kasa da ita ne, ita talakarta ce, dan haka zata nemi masalaha da ita tun kafin ta gagari zama a damagram Daburcewa yan matan suka yi wata na faman bara ta samo kujeru, wara na kallon abin shansu da cinsu da baki daya suka kare saura kadan kadan dan sun yi taro kamar me duda a kure lokacin ya zo ko anko basu samu sun yi ba Da sauro dayar ta ce" bara na je shagon kalamu na samo jus Da kallo Najeeba ta bita har ta fita Kujeru ne dogarin nan ya ja daga kofa ya yi salama yana rike da su Bashi da hurumin shiga wajen da matar sarki take kai tsaye hakan ya saka shi tsayawa daga kofa da kujerun da ya fita da gudu ya sauke mutane ya dauko Najeeba ta bi hannunsa da kallo Kujerun da alama zasu yi nauyi gashi itane karama a cikinsu Matsalar bata daukan abu mai nauyi gaskiya dan haka ta juya ta koma cikin dakin da du suka bubude windows din dakunnan ta kakabe tabarmar nan ta dube su da murmushi a fuskarta ta furta" bismillah Ba tare da wani damuwa ba yayun nata suka zazauna baki dayansu NAJEEBA kuwa ta kai dubanta wajen amaryar A hankali ta shiga takawa ta karasa kusa da bed din Baki baki ta zauna cikin nutsuwa ta saka hannunta ta dago habarta wanda hakan ya saka baki dayansu jin gabansu ya fadi Ita Najeeba gabanta ya fadi ne a kan dalilin da bata sani ba Ita kuwa gabanta ya fadi ne jin wani irin lalausan hannu ya taba fuskarta wanda zata iya rantsewa hannun nan ya fi fuskarta laushi Da sauri ta sada kanta, yar karamar muryarta na rawa rawa ta ce" Barkanku da isowa Subahannalah Najeeba ta furta a kasan zuciyarta Bata so haka ba! Sam bata so haka ba! Ta yaya za'ayi wannan ta iya kwatar kanta a wajen Zinaria? Yarinyar kamaninta sam basu nuna yannayi na wada ta iya fada ko ta san tsatsaya a rayuwarta ba Yarinyar gaba dayanta yannayi na wata irin saliha ne a tatare da ita Haka kawai ta ji ranta na bacewa domin ita ba haka ta so ba, ta so ace wada ya auran nan ta ci ubam Zinariya a iya iskanci sai su ga ta iskanci Muryarta a sanyaye ta ce" yaya sunnan ki? Bintu ta kara sada kanta ta ce" sunna na Bintu Najeeba ta gyada kanta ta kai dubanta wajen kawayen nata Su kansu basa yannayi da yan iska Aman a kan me zai tashi ya wani dauko saliha haka? Wannan ai wulakanci ne salon banzar matarsa ta wulakanta yar mutane? Cikin nutsuwa Najeeba ta ce" ku dakata daga kofa, lokaci na tafia zamu kimtsa gimbiya Gaba daya suka yi waje bayan sun risina sun kara gaishe su Tabatarwar da suka yi cewa ta yi wanka mahaifiyarta na zaune tana kallo Najeeba ta buda akwatinta na kayan mak up Cikin nutsuwa ta shiga gabatar da aikinta cikin wata irin kwarewa wace a dan kankannin lokaci yar budurwar ta kara wani irin fresh da ita ta kara wani irin kyau hancinta ya fito zuwat sa shi yana wani irin sheki Gaba daya yarinyar kanta ce mai kyau, wani irin nutsatsen kyau mai birgewa Turaran wuta suka shiga yi mata ita kanta kafin su dora kayan da suka zo da su suka shiga turare mata su baki daya Mahaifiyarta na rike da turaren ruwan da suka bata concentrer mai wani irin dadi tana shafa mata lungu lungu na jikinta Daidai da pant dinta sai da suka turara mata sannan suka bata baya ta saka sabuwar bra din da pant din Taimaka mata suka yi wajen suturta mata jikinta da suturar da aka zo mata da ita wani farin lesh ne mai wani irin laushi Dinkin ya karbi Bintu sosai Nan Najeeba ta kuma zaunawa da agraf dinta tana kashe mata daurin dan kwali tana dantse shi yanda zai zauna Dole yarnan ta birgeka Saima da suka rufa mata alkyabarta mai dauke da wani irin ado tamkar dawisu da ta kalli kanta a madubi sai kawai ta fashe da kuka ta fada jikin mahaifiyarta tana jin gaban kirjinta na dokawa Ashe zata ga irin wannan daukaka daga Allah kafin ta mutu? Mahaifiyarta na mata murmushi ta rasa inda zara ajiyeta domin sai ta ga katifar nan ba zata zaunu da alkyabar nan ba Zahrau ta kamata tana murmushi itama ta zaunar da ita suka sakata tsakiya suka kashe hoto nan suka fito reras da su tamkar ka sace su ka gudu Sakwanin aka ringa ajiyewa kala daban daban kafin su yi masu salama a lokacin har an shiga salar magariba suka fito Tuni kuma motoci sun fara layuwa dan daukan amaryar mota hudu ce kawai dan ba'a so a ga shigarta ta kofar baya idan ya so daga baya sai a kawo mutane Su dai daukansu ya yi ya maida su fada Sunna fita Najeeba ta tserewarta dan tana son zuwa ta shaki iskar duniya ta ji sanyi na ratsa mata jikinta Motar yaya Dayabu ta shiga ta tayar abinta ta tafi siyan ice cream Zuwa lokacin da ta nufi wajen hutunta wanda rabonta da wajen yau kwana hudu kennan tuni an kira isha Da piyawatanta a mota da kuma abin sallah Tana sauka daga motar ta dauki piyawatan Gefe ta koma ta daura alwalarta sannan ta dawo cikin motar ta dauko salayarsa ta dauko alkyabarta A nan ta shinfida cikin nutsuwa ta tayar da sallarta Sai da ta gama baki daya sannan ta mike ta mayar cikin motar ta cire alkyabar ta dauko ledar ice cream dinta da wayarta Tun da ta tinkaro wajen ta dan ja ta tsaya sakamakon gannin mutumen nan zaune kansa sade Yau kuma irin shigarsa sai ta sakata kara kallonsa da kyau Dan waigawa ta yi ko zata ga motar da ta kawo shi? Sai dai hata ga mota ba Adu'ar neman tsari ta ringa yi da miyagu Kasancewar ya saka shada marron sai gaba daya hasken fatarsa ta kara fitowa Daga sajensa zaka gane mai summa ne sosai sannan baka ce sidik summar Kwalin idannuwansa dake nuna kansu ko a cikin dare ne sun kuwa nuna kan nasu da taimakon fitilun dake kukune Karasawa ta yi ta zauna a wajen da take zama hakan ya sa suke facing din junna Shima bai yi tunaninta a wajen nan a irin wannan lokacin ba kasancewar ya san cewa ita din kirjin biki ce du inda ta ji da maganar biki ko ba na gidansu ba zuwa take bale yau nasu? Kura mata ido ya yi gannin ta kasa bude abinda ke ledar sai dan jujuya cokalin hannunta take Shin dama tana da kunyar cin abu a gaban bakon ido ko cikin salon yaudararta ne da neman janyo hankalin namiji a kanta? Basarwa ya yi ya ki yi mata magana a yau din ya daga kansa sama yana gannin yanda farin wata ke kara haske Kasancewar ta rasa nutsuwar hutawar ya sakata kallon wajensa Sai da ta yatsina bakinta a hankali ta ce" hi Dagowa ya yi daga kallon saman ya sauke a saman kanta Da sauri ya cire idannuwansa domin dinkin lesh din nata daga gaban kirjinta an yi kata wani heart ne an cire wajen an zagaye shi da kyalkyali aman kuma an baiwa mararabar kirjinta damar bayannuwa sosai Kai kam ina ne gidanku kake zama a nan koda yaushe? Ko a saman bishiya ne? Ta fada tana nuna masa bishiyar dake wajen Shima bishiyar ya kalla, sai ya ji murmushi na zo masa, wato da alama a tsoracema take da shi ko? Kafadunsa ya dan daga a hankali ya ce" daga wajen auren sarkin garinnan nake, na gaji shine na zo nan na huta Bakinta ta dan tabe ta daga kafadunta Muryarsa mai sanyi ta kuma jin ya ce" daga ina kike haka? Me kike zuwa yi nan? Ko kema daga wajen auren sarkin kike ne? Dago idannuwanta ta yi ta sauke saman kansa a hankali ta ce" ban san shi bama ni sarkin nan, sannan wajen nan wajena ne ban san dalilin da zaka tambayen me na zo yi ba Wajenta ne? To ka ji ya fada a ransa Mikewa ya yi cike da isa ya dawo kusa da ita ya zauna inda take binsa da kallo har zamansa A hankali ya ce" freind? Hannun nasa dai ya miko mata yauma, shi kam ko a inda ya fito haka yake gaishe gaishe da mata? Duda yanzu abin ya zama ruwan dare dan gaisawa da mace ba wani abu bane da namijin da ba muharaminta ba bayan ba kyau Murmushi ta yi tana hararan hannun nasa a hankali itama ta ce" zan yi tunani Haka yauma ta bara masa hannun sakaye yana binta da kallo har ta shige motarta sannan yauma bata dauke abin cikin ledar nata ba nan ta bara masa su ta yi tafiarta Kansa ya gyada yana ayanna" du salonki, sai na ga ainahin wacece ke! Du iya tsare tsarenki na kwana da sannin ke din *MAGE CE MAI KWONCIYAR D'AUKAN RAI* da wani irin sauri amintacen dogarinsa ya karaso wajen da yake zaune ya zube kasa kansa kasa jikinsa na rawa ya ce" Allah ya ja da kwananka, Allah ya taimaki mai damagaram kiran gagawa ya samu daga wajen Gimbiya Allah ja da rai Da sauri ya kalle shi ya waiwaya baya ya ga har ta tafi Kira daga wajen gimbiya da gagawa? N Mikewa ya yi yana takawa ya nufi motar Bai shiga ba sai da ya mayar da rawanin kansa ya dora alkyabarsa ya cenza takalminsa ya rige sandar girmansa sannan ya shige baya ya lafe Jan motar yake gabansa na faduwa duba da irin abinda aka fara fada masa A haka suka samu shiga ta baya suka shige suka karasa wajen da Gimbiya ta umarci a kawo shi Du mutannen wajen dukawa suka yi a lokacin da aka shiga shelar shine Cikin taku irin na kasaita ya ringa daga kafarsa daya na korar daya har ya karasa wajen da GIMBIYA ke tsaye tare da y'ayan yan matanta Yannayin tashin hankalin da yake karanta a fuskarta shi ya saka shi kara rage hanzarin tafiarsa Motar da ya bada dan kawo amaryar nasa ce ya ganni a bubude Wasu mata ne ya ganni a duke nesa kadan aman kuma kuka suke A hankali ya kai dubansa wajen motar Idannuwansa ne suka sauka kan wasu fararan kafafuwa da aka fitar Irin yanda kafafuwan suke ajiye ne zai shaida maka mai su idan dai ba barci yake ba to yana cikin halin rashin lafiar da baya iya motsa su Da alama kuma mutumen dake ciki ahi daya ne Haka kawai ya ji zuciyarsa ta doka da wani irin duka mai tsanani A hankali ya karasa gaban mahaifiyarsa Kansa ya dula sosai ya ce" Allah ya ja da ran Anmy Anmy ta dago tana dubansa cike da fargabar abinda zata fada masa da tausayin yarinyar dama shi kansa da iyayen yarinyar Me zata ce masa ne? Ce masa zata yi su kansu yan rakiyar yarinyar basu san cewa ta rasu a cikin kotar ba har sai da aka zo aka kamo hannunta dan fitar da ita a sadar da ita da dakin mijinta? Ko kawai ta ce da shi SHAHEED ALLAH YA YIWA YARINYAR DA KA AURA YAU RASUWA? SAI TA RASA KALMAR DA ZATA IYA HADAWA DAN SAMUN WANNAN BAYANI BAKINTA NE YA SHIGA RAWA A LOKACIN DA TA BUDA TA CE" >?????????????????????????????????????????????????????????????? & *[ T.M.N.A]* & =???=؊?? https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 17 A hankali yan matan suka marmatsa bayan sunna dan dukawa sunna nan afuwa suka barshi tsaye gaban Anmy A hankali ya jinginar da sandar hannunsa ya saka hannayensa biyu ya dago fuskar mahaifiyarsa Irin yanda kwayar idannuwanta ke cikowa da kwallah ne idan wani abu mai rikitar da zuciya ya faru ya ganni Kwonce kwalar take a kurmin idannuwanta hakan ya sa fuskarta yin wani iri Sauran matan tsohon sarki biyun ne suka karaso suma da yannayin juyayi a fuskokinsu Fulani ce ta dora hannunta saman na sarkin dake gefen fuskar mahaifiyarsa A hankali ta girgiza masa kai wanda hakan ya saka shi saurin rintse idannuwansa domin wannan lamari shi ya faru a lokacin da ya rasa mahaifinsa Sun ringa dafa hannunsa ne sunna girgiza masa kai Da sauri ya maida dubansa wajen motar nan Kafarsa ya daga

Chapter 12 of 58