Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 A hankali ya ce" *NAJEEBA*? idannuwanta ta saka cikin nasa ta ce" Na'am yaya dayabu, na rantse maka karya yake sarkin ba na gaskiya bane suka saka, Aba ya fi karfinka kennan a kasar nan? Hannunsa ya dago ransa bace ya dafe gaban goshinsa Bai kuma yi mata magana ba ya juya ya ringa kama kannen nasa masu motarsu yana saka kowa cikin motarsa, baya yi maka magana sai dai ya nuna maka hanya kan ka tafi sha'anin gabanka Sauran biyun da basu da mota ya janyo hannayensu ya kawo su ya buda bayan motar NAJEEBA ya tura su kafin ya maido hankalinsa kanta Sai da ya kuma kallonta kafin ya ce" rigarki ta cire, kina kaisu ki tabatar kin koma gida kin saka sutura Kai ta gyada masa tana kara cije lebenta masu mugun kyau da haske tamkar fatarta bata da wani duhu Juyawa ta yi ta shiga motarta Da gangan ta ringa yin kamar motar ta ki tashi har sai da ta ga fitowar mahaifinta ta bi shi da kallo kafin ta yatsina bakinta ta turo bakin ta tada motar gannin yayansu ya karasa kusa da motar mahaifin nasu ta gyada kai ta tabata idan ya gane gaskiya ne ba zai yarda ba sai dai du abinda za'a yi a yi Gudu take falfalawa da su a baya a zaune sanye da kayan makaranta har ta karasa babar makarantar school mai hade da islamiya Budewa ta yi suka fito ta buda jakarta ta basu kudin kari suka juya suka tafi cikin makarantar Motar ta koma ta yiwa kys ta tayar ta kama tafia Tana tafe tana kara cije lebenta a haka har ta zo wajen danja Sojan dake cikin motarsa wanda tun ficewarta dazu polisai na tsayar da ita ta ki tsayawa ne ya fito ya zagaya wajen motar nata Fuskarsa a hade take, sam ba annuri, yana daya daga cikin mutanen da akaiwa sunna dan tsaurinsu da iko da mugun taurinsu a kan aikinsu, sunna kama mai laifi koma waye, sunna da haye basa yarda da raini Sai dai kamar yanda kowani dan adam yake da point faible hakama na Mala'ila wato sunnan da akai masa shine shagwababiyar mace Da sauri ta saka hannayenta ta buda gaban motarta Kayan kwaliya ta janyo da mugun sauri ta buda madubi ta dan duka dan kar a hangota daga gaba ta gyagyara kwalin idannuwanta, ta saka dan jan baki mai tafiya da kalar lebenta ya hadu sosai Rigarta ta ja ta gyara ya kasance wajen da aka cira matan ya fito hakan ya sa ana gannin dan saman mamanta kadan ba da yawa ba Zuge gilashin ta yi bayan ta yiwa fuskarta takwaf takwaf Da wata irin yanga ta dago dara daran idannuwanta ta sauke a kan fuskarsa, lokaci daya kamaninta na salihar mace mai fuzga ya bayanna a tare da ita Gaban goshinta kuwa kwonce yake da wani irin ni'imtacen gashi wanda ya yi luf luf da shi Sai da ta kara yin luuuuu da idannuwanta tamkar wace zata sume sannan ta dauki tissu ta ringa goge idannuwanta nan da nan kuma sai kwallah ta taru Tana kallonsa ta kara rage muryarta, dama mace ce mai karamar murya zazaga hakan ya sa sai da ya kara matsowa ya kashe kunne yana jin abinda take fadi" muryarta a sanyaye, sai dai yannayinta a hargitse ta ce" Allah ya huci zuciyarka sir, hatsari na yi ne cen baya hankalina tashe banma ga sunna tsayar da ni ba, ka gafarceni mai laifi ce ni, idan kuwa na sauka na bada motar bani da ja domin ba wanda ya isa ya ja da ikon da kansa Wani fadi ya ji kansa ya kara, gilashin idannuwansa ya dan yi kasa da shi hakan ya bayannar da idannuwansa masu jan gaske , Murmushi ya yi mata wanda ya bayanar da hakoransa masu tsawarya sannan iskar sigarin da ya zuga ta daki hancinta hakan ya sa da sauri ta kai tissu din nan wajen hancinta ta rufe tana kokarin danne tarin dake son taso mata Wayarsa ya miko mata yana kallonta da idannuwansa tamkar wanda yake daga maye ya ce" dora min numberki a nan yan mata, zan yi kiranki na fada maki yanda muka yi da su domin na fada masu su barni da ke ne, kin san akoy yan cikan dake son lalata mana gari Murmushin yake ta saki tana jin cikinta na neman hautsinewa sakamakon shakar warin nan dake fitowa daga bakinsa yana dukan hancinta, a duniya idan akoy abinda ke sakata gudawa to warin baki ne, bata san wani irin rashin lafia ne haka ba wanda idan ta shaki warin baki nan da nan cikinta ke murdawa ta nemi rikicewa harda juwa Tana faman lumshe ido ta dora masa numbobin da bata san ko na waye bama tana masa dan murmushi ta mika masa wayar Amsa ya yi ya kashe mata ido daya sannan ya bata hanya ta tayar da motarta ta halba bakin titi Tana yin nisa ta sauke ajiyar zuciya a fili ta furta" *Wawa kawai!* Maimakun ta je gidan kamar yanda yayanta ya mata kashedin cenza rigar jikinta, haka ta yi kwana ta je clinik, wato asibiti mai zaman kanta Tana zuwa bata yiwa kowa magana ba da yar farar jakarta da kuma farin dogon takalminta ta karasa bangaren likitan dake duba mararsa lafia Gannin yannayinta a wanke ya saka ba wanda ya tsayar da ita, ita kuwa kai tsaye ta karasa ta dan yi knocking Yana kokarin saka farar rigarsa ta likitoci ya bata damar shigowa domin a tunaninsa nurse din da zata kawo masa liste din mutanen da zai duba ne yau Kamshin turaranta ya saka shi juyowa da sauri Lokaci daya fuslarsa ta fadada murmushi yana kallonta Gannin fuskarta ba murmushi da alamun baci bacin rai ya saka shi saurin kara juyowa yana kallonta ya ce" oh angel, waye ya taba min ke da safe haka na ga fuskar ki a hade kamar wace aka batawa ko baki da lafia ne? Jakar hannunta ta ajiye saman fararan takardun table din tana kara yatsina fuskarta ta ja dan kwalinta baya gashinta ya kara bayana ta sauke ajiyar zuciya ta kale shi Sai da ta ja wata yar shasheka sai kawai hawaye ya shiga bin kuncinta Lokaci daya ya rikice, ya bi ya daburce, ya kai hannunsa da niyar kama hannunta sau uku yana fasawa sannin da ya yi cewa a duniya ta tsani a taba jikinta, du irin yanda take da iya wankar samari kana yin wannan kokarin na kwatanta zaka tabata zaku bata , batawa kuwa wace ba zaku shirya ba Kansa ya dafe yana jin zuciyarsa na bugawa, a duniya yana son yarinyar nan, idan kuwa ya ga ranta bace yakan fita a hayacinsa, bai san wani irin so ne yake mata mai tsanani haka ba, dalilinta ya sa ya daina fade fade a garin domin tana da kawaye kai bama maganar kawaye ba saloon dinta du wata mai ji da kanta a cen take gyaran kai ne, gyaran jiki ne, ko kunshi, ko mak up shi yasa ya nemi biye biyen matan da yake ya ajiye gefe, matarsa kanta yana kiyayewa kar ta san yanada aure domin shifa a kanta yana iya sakin matar tasa, Baban burinsa ya sameta, ya cin mata ta aure ko ba aure, sai yana gannin abu ne mai wuya ba auren domin har yanzu baban abinda ya fi bashi mamaki a kanta du irin wayewarta da tarin shagwabarta ko soyayar shan minti ba'a yi da ita, mutane da yawa na mata muguwar fasara, shi dake tare da ita shi ya san wacece ita Agogon hannunta ta dan kunce tana kallonsa ta ce" kudin jakana sun kare shine hankalina ya tashi domin yau ba zan bude saloon ba kai kuwa ka san inada kashin kudi shine na zo Kabsa ya dafe cike da kulawa ya ce" Angel, kuma shine sai kin taso? Haba baby idan kika yi kirana ko ina ne sai na zo na kawo maki aman shine zaki taso har ki zubar min da tsadadun hawayenki? Mikewa ya yi yana maganar ya dauko jakarsa ta laptop ya buda bayanta ya ciro kudi masu kauron gaske ya buda jakarta ya zuba mata Catin Airtel ya ciro ya buda jakar nata ya kuma saka mata sannan ya dubeta ya ce" kin karya? Idannuwanta ta juya masa cikin yannayi na lumshe su kafin ta dan cije lebenta na kasa ta kuma sake shi Jin an kuma buga office din ya saka ta tashi ta dauki jakar nata ta sakar masa murmushin da ya saka saman kuncinta cen sama kamar kusan idannuwanta lotsawa kadan wanda hakan ke kashe masu begenta, ta kara yi masa wani warwar da idannuwanta sannan ta kuma gyara tsayuwarta ta ce" jarumina, ka kula da kanka, sai mun hadu Bai iya amsawa ba sai wani irin sakai da ya yi da bakinsa ya rakata da kallo tamkar ya janyota ya maidota ya rukunkumeta a jikinsa yake ji har ta fice a office din Wata wawuyar ajiyar zuciya ya saki a fili ya furta" dole na malaki babyn nan, tawa ce ta ni kadai! Ita kuwa daga nanma direct shagonta ta nufa, wato saloon dinta Motarta ta parker ta sauka bayan ta ciro gilas dinta pink coler mai yannayin heart ta dora ta dauki jakarta ta nufi cikin wajen da tun daga kofar take hangen da alama sunna da mutane sosai yau bayan ta hana a dauki mutane da yawa yau sakamakon amaryar da zata shirya Tana shiga wajen ya dauki ihu, domin kawarta ce bahija da kuma Ramlat suka kawo mata ziyara, kai ziyarar tafe take da son jin abinda ake cicirawa a gari wai sun kai mahaifinsu kara gidan sarki Itama da murna ta karasa wajensu ta zauna tana kallonsu Sai da suka gaisa, masu aikinta suka kawo mata jus da ruwa, da sauri dayar ta je ciki dan gyara mata abin kari ita kuwa ta sakarwa Bahija murmushi ta ce" bahija ina zuwa bara na cenza kaya Bahijarma murmushin ta sakar mata sannan ta dauki Iphone dinta ta danna kira Shiga ciki ta yi ta cire abayar nata ta dauko wata doguwar riga marar nauyi ta saka mai dan gajeran hannu Gashin kanta ta hade ta yi sama da shi ta saka masa dan karamin ribom ta daure shi hakan ya sa yake ta reto da cikarsa da kuma tsayinsa ga bakinsa Tana fitowa gaban madubi ta je ta shiga bin aiyukan da akaiwa mutanen, Biyu ne atach din da aka saka masu bai yi mata ba domin ya yi tudu da yawa dan haka ta sa a kunce ta shiga hada zare a jikin katuwar allura ta harhada da yawa su kuwa suka shiga sauke masu sai da aka gama na fari ta kama cike da kwarewa da kaunar aikinta ta gyara masu ya yi tsaf tsaf da shi ya kwonta kafin ta caje masu ta masu yanda suke so da shi Sai da suka gama suka biya kudin da aka yanke masu na aikinsu cike da farin cikin samun biyan bukata suka tafi Sai da saloon ya rage mace daya ta maida hankali ta saka mata gashin ido ta gyara mata girarta sannan ta saka mata akaifun nan da ake kira natural masu tsadar nan ta gyara mata su sukai wani iri kamar nata domin an rage tsayinsu sosai da sosai sun bada kala Itama biya ta yi ta tafi cike da farin cikin sakin fuskar NAJEEBA Sai da suka gama tafia ta je jikin madubin ta juya takardar dake nuna a bude suke zuwa a rufe suke ta dawo wajen ma'aikatan nata Fuska tamke ta ce" Nadia yaushe kika zama uwar gidana? Nadia da ta san ta yi laifi ta ce" aunty dan Allah ki yi hakuri, walahi tun jiya suka tambayeni yau zasu zo a masu aiki, kuma ke baki ce min kar na bude ba sai dazu a lokacin tuni sun zo na yi na yi na ce da su su tafi suka kiya, clients dinmu ne aunty ke ke hana mu wulakanta clients dinmu Wani huci ta sauke ta ce" to maza maza a gyara wajen a tatare komai a tsaftace, minister ya yi amarya nan za'a kawota nan da awa biyu, ku tanadi komai domin tun daga kurkun zamu silleta dan uban mama zata gani ba tace ba za'ai mata kishiya ba? Daria kawarta ta fashe da shi tana kallonta ta ce" NAJEEBA, wai waye ya taba ki yau du kike hawa uwa fulawa? Murmushi ta sakar mata kafin ta gyara zama kusa da ita ta dauko gashin idon da zata sakawa kanta bayan natama masu tsayin gaske ne da baki, aman da yake tana da bako yau za'q kara firgita shi Abin sakawar ta dauka bayan ta saka masa col ta shiga dan hura shi tana kallon yanda Ramlat ta huda hancinta Murmushi ta yi ta ce" Ramlat idan na kale ki hanci a huje kamar saniya Ramlat ta hade fuska ta harareta ta ce" bana son wulakanci NAJEEBA ke dake son a huda maki gwfen lebenki fa, nan har cewa kika yi a huda maki harshenki kina tsoron kanwar dad ne ya sa kika fasa wancen aman ai jira kike a kawo maki dan kunnen zinarin da kika saka a maki a huda maki lebe uwa wata yar hannu Idannuwanta ta jujuya tana dan rawa da kanta ta kalli madubin ta dago shi sosai a hannunta tana kallo ta kasa kasa ta daidaita ta dora na gefen dama Dayan ta dago shima ta shiga dan matsa masa kadan a sama ta shiga yarfe shi dan ya sha iska kafin ta dora, kunnayenta ne suka jiyo mata muryar bahija na cewa" wai me kuka je yi fada yau ne? NAJEEBA ta dan saci kallonta ta daga kafadunta ta ce" matsalar cikin gida ne Baki ta tabe ta ce" ku dai cikin gidanku kulun matsala, to Allah ya sawaka, aman yaya kuka kwashe da mai damagaram yau? Sai da ta kuma gyarawa ta dora ta daidaita da kyau, tana dago idannuwan nata sun kara wani irin girma da fuzga ta sauke su samanta ta ce" yau na ji jaraba wai ke ina ruwanki da son sannin abinda ke tafe a gidanmu? Kar ki manta kowa da sirrinsa wanda yake gannin sirri ne haba! Da sauri ta ce" aa, Allah ya baki hakuri, ni ba wani abin ya sa nake tambayarki ba gani na yi ke ke zaginsa kice ya damu mutane a kasa ya hanna mana rawar gaban hantsi ya tsane ki Allurar da ta dauko tana kara daidaita kashin idon dan ya yo das kar a ga col din da ta saka da shi ta shiga aiki da shi cikin kwarewa ta ce" ba zaki gane ba, ni ina iya zagin ahalina! Aman ke ya haramta a gareki Ramlat ce ta yi gagawar cenza zancen ta hanyar sako wani, daidai lokacin kuma yayanta ya yi kiranta cewa gimbiya na nemansu bayan salar isha'i Sai da gabanta ya fadi, lokaci daya ta shiga aiki cikin rashin kuzari gashi aiki ne jajir a gabanta shirya matar minister guda amarya wace kuma ta yiwa kanta alkawarin sai ta mata kwaliyar da zata firgita uwar gidan domin uwar gidan ce abokiyar gabanta wace suke fada da ita Ba ita ta bar saloon ba sai da magariba ta shige sosai, bayan ta yi sallah ta kama hanyar gidansu da wani irin gudu Tana zuwa a kofa ta bar motarta ta yi bangarensu da gudu tana lalubar kys din dakinta Budewa ta yi ta afka bayi ta shiga wanka da wani irin sauri Tana fitowa sallah ta yi domin tun tana hanya akai isha Sai da ta gama ta shiga ciro kayan sif dinta tana ta zubarwa a nan da kyar ta iya daukan wata jar abaya irin na dubai din nan ta zira Sai da ta zira ta dauki pant ta saka da sauri sauri ta caje gashin kanta ta warci turaranta tana gudu gudu tana fesawa da wayarta a hannunta da wata jakarta baka wace ta dauki takalminta baki a hannu Ba wanda ta nema dan ta san sun tsufa a gidan Gimbiya da gudu ta fada motarta ta tayar ta warceta ta nufi cikin gida (Gidan sarki) Ta kofar baya ta bi domin ta san idan ta bi ta gaba zasu kara tsayar da ita ne Bangare bangare ta ringa ratsawa, gidan dauke yake da gilas wani irin ginni mai haukata bawa Tana ratsawa har ta karaso bangaren da akan hada su a masu nasiha wanda a nan gimbiya ke hada su Sai da gabanta ya yanke ya fadi sakamakon hango takalma hakan ya shaida mata kowa na nan ita kadai ce bata zo a kan lokaci ba Sai da ta dafe zuciyarta a hankali ta furta" woyo Allahna na kara laifi Da sauri ta saisaita nutsuwarta ta karasa Hannayenta ta saka ta buda kofar madubin dake rufe mai nauyin gaske wace take goge kal kal duda dare ne kana gannin kanka tar a jiki Dan dakata ta yi ta ciro jan bakinta ta shafa tana kallon madubin ta saki murmushi, wanda baki daya hakan ya faru ne a kan idannuwanta kanwar mahaifin nasu wato Gimbiya da kuma yan uwanta, sai matar mai martaba da kuma yaronsa prince, dan kuwa madubin irin wanda idan kana gannin kanka daga waje ne kai kuwa ana ganninka daga ciki kuma baka gannin masu ganninka, ita kuwa rashin lafiar dake damunta idan ta ga madubi sai ta amsa tayinsa ta hanyar dan kara gyagyarawa Hannayenta ta kuma saka ta tura kofar ta shiga da salama kasa kasa Gabanta ne ya yi tsale ya yi luguden kidi ya fadi , hakan ya sa ta saki jakar hannun nata tana raraba ido jikinta na dan rawa rawa Yayanta da yayunta da kannenta ta ganni laye a layi daya kowane kansa a kasa kamar sun zo neman gafara Gefe data matar sarki ce ta sha wata mahaukaciyar kwaliya mai daukan hankali sai walwali take gata fara ce sai haskawa take Gimbiya ce tsaye a tsakiyar falon itama ta sha wata irin nitsatsiyar kwaliya jikinta sanye da alkyaba Da sauri ta kara kallon yan uwanta ta ga kowa da alkyaba a jikinsa, ita daya ce bata saka ba, hakan ya kara bata ran maman nasu Du bata kara firgicewa ba sai da ta sauke dubanta kan MAI DAMAGARAN, SARKI SARKIN SARAKUNA SARKI MAI MULKI CIKIN AMINCI, ZAKI BAYA DAUKAN WARGI, MAI GARI MAI KAUYUKA DAN *ABDUL MALIK ALI BUZU* *SHAHID* yake aban prince *ALI SHAHEED ABDUL MALIK ALI BUZU* miji a wajen *ZINARIYA ZULAIHAT* yar sarkin agadez, D'A daya kwalin kwal a wajen GIMBIYA *BILKISSU MAI GADON ZINARI* Kansa ya juyar daga kallon tsanar da ya gama jifanta da shi ya maida kan matarsa dake zaune tana ta sakin isa da takama da sarauta Yar yatsarsa ya daga ya yi mata nuni da ta fita Idannuwanta ta lumshe, dama ta san ba zai barta ta ji abinda ya faru ba, baya taba barinta jin ainahin sirrin da ya shafe su, bata san wani irin mutun ne shi mai shegen zurfin ciki da boye laifin yan uwansa Mikewa ta yi ta kara sakin shigar jikinta alkyabarta ta sauka sosai ta shiga takawa a hankali har ta karaso kusa da NAJEEBA dake tsaye baki daya jikinta ya yi wani kalau kamar ba ita ba Cikin murya kasa kasa sosai ta kara rabar NAJEEBAR ta ce" kauce min a hanyar yar talakawa! NAJEEBA ta dago da sauri sannan a hargitse ta sauke kakausan kallo a saman kanta, kafin ta ankara ta..................... >????????????????????????????????????????????????????????????

Chapter 3 of 58