NAJEEBA
NAJEEBA ta tabe baki tana sauko da kafarta ta fara fita
Du an tataro sauran sun layi kamar yanda suke yi idan sun san sun yi laifi ko sun ga iyayen nasu a hargitse
Anmy ranta bace ta ce" NAJEEBA shine wani dan iska ya dake ki a ciki ba'a fada min ba? Cikin mace fa nan ne yaro ke kwonciya, idan ya jiwa yarinyar nan ciwo walahi Yaya sai na daure ubansa!
Najeeba ta shiga sakin murmushi tana gyada kanta tana kallon Anmyn nasu, sai a lokacin ta tuna da ciwonta ta sada kai gannin Aba na hararanta
Ta kai dubanta wajen ZAHRAU ta ce" ke kau an yi wata irin y'a, shine kika tsaya yana zaginki baki dauke min fuskar shege da mari ba?
Aba ya sauke ajiyar zuciya ya ce" ya ilahi BILKISSU ke da zaki hane su fada ke ke fadan sun ki duka? Yanzu zaki gindaya sharudan abinda ya kawo mu ko sai kin sa sun kara raina mutane?
Bakinta ta dan zumburo tana kallonsa ta ce" aman ai kaima kana da wani laifi ko yaya? Ina matarka ne da bata zo gidannan ta zauna da mu ba ko kyankyaminmu take?
Ummulkhair ta yi carab ta ce" Anmy, uhum nan kuwa da kanwarta ta haihu har aka yi sunna tana gidansu aman da yake ta raina mu mu.......
Shiru ta yi sakamakon juyowa da Anmy ta yi ta ce" na koya maki? Tambayarki na yi? Ni na kiya maki tsegumi? Yi min shiru a nan my daughter!
Kansu suka sada su duka jin ta fara hawa da gasken
Tsayawa ta yi kansu tana dubansu murya a kausashe ta ce" *MUTALAB ND BILKISSU FAMILLY*!
su duka suka shiga dago kansu a hankali sunna kallonsa,
Sai da ta dago d a n y a t s a r t a m a n u n i y a t a n u n a s u t a c e "
[ 1 / 2 0 , 9 : 5 0 A M ] U m m u S u h a n =?
?: >?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????
* M A G E *
_ ( M a i k w a n c i y a r d ' a u k a r r a i ) _
>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????
* N a *
* S A J I D A *
=ث?(' * T A U R A R I N M A R U B U T A N N I G E R ( A S S O . ) * ?
_ ( T s i n t s i y a m a d ' a u r i n k i d ' a y a ) _ >??
& * [ T . M . N . A ] * & =???=؊??
h t t p s : / / w w w . f a c e b o o k . c o m / T a u r a r i - m a r u b u t a n - n i g e r - 1 1 1 7 7 3 5 6 0 6 7 7 0 0 3 /
_ B i s m i l l a h i r r a h a m a n i r r a h i m _
10
Ku kiyaye ni, na fada maku ku kiyaye ni! Shin ku manya idan baku baiwa kannenku abin koyi mai kyau ba so kuke tun kafin mu mutu a ringa cicira maganar tarbiyar da muka yi maku?
Zahra ke ce baba fa, me ya kaiki ke mace budar baki ki yiwa mutun gorin tabon rayuwa bayan ke bakima fara taki rayuwar ba?
To ku sani, duniyar nan ba matabata bace, kar na ji kar na gani ko bayan raina na soke maganar yiwa mutun gori a rayuwarku idan kuwa aka yi ban yafe ba
Kai suka ringa gyadawa,
Hannunta ta saka ta dauki yar karamarsu dake son bare chocolate tana dubansu ta ce" da zai yarje min da a hannuna kuke, da zai iya da ya barmin ku dan na tabata tarbiyar y'aya a hannun mace take
Numfashi ta sauke ta ce" sai dai hakan ba zai yiwu ba domin yana da shakuwa da ku mai tsanani
Nan saman cafet din da suke zaune ta nemi waje ta zauna gabansu tana dubansu sunna dubanta
Murmushi ta yi masu ta ce" ina son ku sosai, kun san da haka?
Yannayin farin ciki ne ke wanzuwa a fuskokinsu
Itama da tausayi take dubansu duba da ba wanda ya girma da iyayensa, wasun laifin iyayen nasu ne wasun kuwa laifin mahaifin nasu ne, hakan ya sa take matukar tausaya masu take kuma jinsu a ranta
A hankali ta ce" Allah ya shiryar min da ku
ABIH ya dubi DAYABU, DAYABU ya sakar masa murmushi domin kafin su shigoma kamar zata kama da wuta ta tanadi sai ta mari wani yau a cikinsu, dama DAYABU ya san tana samun kanta gabansu zata kasa tabuka komai, saidai ta dawo rarashi da adu'a
Abih ya girgiza kansa yana ciro wayarsa yana duba whatsup dinsa domin ya jima rabonsa da ya duba tun zaman makokin da suke
Sannu fa, Allah ya masa rahama.....mesage din da ta iya aiko masa kennan
Ba salama ba wani doguwar magana, rasuwa akai masa ta masa gaisuwa fakat
Dubansa ya kai wajen NAJEEBA dake kallon Anmy
Wani sa'in wasu abubuwan yarinyar sak mahaifiyarta ta kwaso
Irin jan ajin mahaifiyarta da sauransu idan ya ga ta yi yakan tuna da, sai kuma haushin maman nata ya lulubeshi harma ya tabe bakinsa ya kawar da kai yana furtawa a kasan zuciyarsa cewa kudi ko? Ki kara neman kudi , ki yi ta neman kudi, idan kin mutu a nadeki da rigar kudin a kaiki!
Sarkin Garin Agadez ne ya zo da maganar cewa yana son auren Zahrau
Gaba daya yan matan da aka bari ne suka kara dubanta sunna masu firfitar da idannuwa
Itama kuresu ta yi da kallon bale Zahrau da ta dafe kirjinta tana kallonta baki bude
NAJEEBA kuwa sai kawai daria mai dan sauti ta kufce mata, dariar ta fara saki sai ta karasheta da tari tana tari kamar tari ne ya taso mata
Zahrau ta ce" na shiga uku Anmy, sarkin garin Agadez fa? Anmy matansa nawa? Anmy jajayen buzaye? Anmy sirikin yaya fa?
Ta sada kanta ta ce" kuma ma tsoho ne
Murmushi Anmy ta yi ta ce" matansa biyu, zai yi ta uku da ke
Maganar sirikin yayanku sai me? Kin ga kema kin zama sarakuwarsa
Maganar tsufa kuwa ajiyeta gefe ba tsoho bane
Ido ta ringa kikiftawa ta rarafa ta je jikin Anmy ta dora kanta ta ce" Anmy, ni kuma? Anmy kin san inada tsoro fa, ba zan uya rigimar gidan sarauta ba kar ki kai ni kin ji?
Murmushi Anmy ta yi tana gannin yanda Abih ke hararanta , karshema sai ya yi kwafa ya mike ya fita
Ai kuwa kamar jira NAJEEBA take ta mike ta kwaso shoki ta jefawa ZAHRA wace kanta ke saman jikin Anmy tana shafa kanta
Daria take kasa kasa ta juya ta nufi dakin Anmy, au kuwa suka rakata da kallo
Anmy ta yi murmushi tana girgiza kai,
Tsakiya suka sakata sunna ta rarashinta tare da fada mata dadadan kalamai da fada mata cewa idan tana so za'a mata idan kuwa bata so ba za'a yi mata dole ba
Najeeba kuwa na shiga daki ta bar dariarta ta fito tana juyi har ta ka r a s a g a b a n m a d u b i
I d a n n u w a n t a t a l u m s h e a f i l i t a c e " A n m y m a t a c e k e m a k i n z a m a s a r a k u w a r s a
W a y o d a d i m u n z a m a s i r i k a n s a ( t a z a m a d a i h a j i a >?#?)
S a i d a t a g a m a d a r i a r t a t a n e m i w a j e t a k w o n t a t a n e m i b a c i d a n t a y i n i y a y a u f a s a i t a t a r i b a k o k o d a y a n e
Bacinta ta sha isashe har kusan salar la'asar sannan ta farka
Bayi ta shiga ta yi wanda da brosh ta fito ta zauna tana shafa man ta
Tana gamawa ta dauki wando da riga cikin kayanta duda wandon a dan sake yake rigar ce ta dan dameta ta saka abinta ta yi lamo tana kallon faratunanta da kunshin jikinsu ke son fita
Kusan magariba Anmy ta shigo da wayarta a hannunta ta mika mata tana hararanta ta ce" anmatana, sai na gwada amshe wayarki na wata guda na ga yaya zaki yi?
Murmushi ta yiwa Anmy tana sada kanta dan ta san idan ta yarda da gatse sai ta amshe din, ita kuwa babar damuwarta ace an rabata da waya
Kallon Anmy ta yi gannin bata bata karamar ba
Anmy ta buda bangaren kayanta ta ciro mata sahari dinta ta wurga mata shi sabo ne sannan ta ciro alkhaba sabuwa fara kal mai yan duwatsu a gaba ta ajiye mata gefenta ta rage muryarta ta ce" ku shirya bayan salar magariba ku je ku yiwa sarki salama
Najeeba, ki kula, yayanku zai kasance a wajen nan ni kuwa bana nan ki kula na fada maki
Gabanta ne ya fadi jin wai zasu je su yiwa sarki salama, to ita yanzu tsakani da Allah ina ita ina zuwa yiwa sarki salama? Taga dai Zahrau yake so, me zai hana a turata da jakadiyoyi? Walahi tana tsoron haduwarsu da wannan bawan Allahn da ta dasawa sunnan dunkum!
Sai da ta kusan fita ta juyi ta ce" karamar wayarki tana wajen SHAHEED
Wani irin kululu cikinta ya yi kamar wace ta sha abinda zai sakar mata ciki daga jin cewa karamar wayarta na wajen SHAHEED
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une
Ta fada a fili tana mikewa da gudu ta yi bayi
Bata zane ko'ina ba sai saman WC tana rike cikinta dake juya mata
Bil haki ta shiga gudawa tsabar faduwa da gabanta ya yi da kuma irin yanda cikinta ya juya daga jin wayarta na hannun SHAHEED
Me hadinsa da wayata? Me ya kai wayata wajensa? Na shiga uku Anmy kin kashe ni kin kare, da ya amshi wayar nan gwara ya amshi babar ya rotsara da kas, Anmy kin san neman shari yake a kaina shine kika bashi hanya, wannan tsanata da nake hangowa a idannuwansa shine kika bashi abinda zai idasa tsanar tawa?
Sai da ta gama gudawar zufa na karyo mata ta tsaftace jikinta ta wanke ta fito ta zauna kasa ta kunna babar wayar nata
Wayar na kunnuwa kamar jira ake network ya hau sai ga message rututu
Bata tsaya dubawa ba ta shige wajen Call
Da sauri ta ringa tura message cewar kar a nemeta a numberta airtel ta yarda wayar ne a kirayeta a numberta MOOV
Da sauri take ta tura message din sai da ta gama ta fara sauke ajiyar zuciya a tunaninta ta toshe hanyar kiranta
Wajen message din ta shiga, nan ta fara cin karo da message din samarinta kala daban daban
Ciki kuwa harda masu shaida kata sun kasa hakura sun je gidan ake shaida masu rasuwar yarima ashe dan yayanta ne
Wasu sun tsaya iya gaisuwa
Wasun kuwa cikin ikon Allah ta ringa bin message dinsu tana zaro ido jin sun je har fadar gaisuwa
Bata san lokacin da ta furta" uban wa ya aike ku? Da sunnan wa? Kuka ce wajen wa kuka zo?
Kafafuwanta ta mike ta mayar da kanta baya, gashin kanta du ya bazu saman bed din tana kikifta ido
Cen ta yi tsai da ranta, a hankali ta ce" NAJEEBA shin ubankine da zaki ringa rikicewa dan kawai ya amsar maki waya ko dan kawai ya samu ribar an zo an masa gaisuwa?
Nan Abih ya san kinada samari, Dayabuma haka sun yanka ki ne?
Dago kanta ta yi da irin duban nan na basawa ta juya kwayar idannuwanta masu girman gaske kafin ta furta" ke allura kike cikin ruwa, dole sai kin yi samari zaki iya fitar da gwaninki, bai huce yace ya hada kananun wayoyinmu zai yi bibcike kamar yanda ya saba lokaci zuwa lokaci
Ko kuma dan sirikinsa na son aunty Zahrau zai hada dan ya goge du wata alakarta da wani?
Huci ta furzar ta ce" ke koma menene bashi da hurumi da tarin samarinki! Idan kuwa yauma zai bi ki da kallon kyama da tsanar ne halas kema ai kina da idannuwan!
Haka ta yi ta zama har kusan magarib
Lokacin ne Zahrau ta shigo ta karsa inda take zaune itama ta zauna jikinta a sanyaye
Dubanta ta yi, sai ta ji itama jikin nata ya yi sanyi
A hankali ta dora hannunta saman hannunta na dama ta kara sanyaya muryarta ta ce" idan har kin san bakya so, idan har kin ji bai maki ba, idan har bakya ra'ayin aure ki zauna a gidan sarauta, idan har maganar yanada mata biyu ke kayar maki da gaba har ya kai kina jin ba zaki iya jurewa ba
Dan shiru ta yi kafin ta tsareta da ido ta ce" *Kar ki amince*
Ajiyar zuciya Zahrau ta sauke ta ce" aman sai na ga su Abih sunna murna da hakan, idan na tashi kai tsaye na nuna bana so yaya kike gannin zasu ji a ransu?
NAJEEBA ta yi kara fuskantarta ta ce" kwarai ba zasu ji dadi ba duba da yanzu abinda suka sako gaba burinsu su yi mana aure da daidaya
Hannunta dayan ta riko tana dan murzawa ta ce" to aman ina anfanin ki je ki kasa zama ki dawo? Koda hakuri kikai kika zauna kina shan wahala kina tunanin zasu ci gaba da jin dadin hadin nasu ne?
Hannunta ta kai wajen habarta ta dan dago ta ce" Aunty, baki dayanmu ina mana fatan mu auri mazan da muke so kuma suke son mu
Na tabata su ne zasu fi gannin darajarmu, zasu ji tsoron rasa mu, zasu kula da lamarinmu
Mu kuma na tabata tare da su ne zamu yi hakuri mai inganci, zamu yi biyaya ke aunty mu bautu ba tare da mu kanmu mun ankara cewa vautuwar muke ba cike da farin ciki da nutsuwar zuciya
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" abin ne akiy gigita
Kin ga zinaria yanda take a hakama ta tsane mu ina da na auri ubanta? Kin dai taba gannin mahaifiyarta matar kyankyamin bakin mutun take ita kanta ta cenza daga buzuwa ta koma balaraba dan ta tsanu jinsin baki
Murmushi NAJEEBA ta yi tana lakatar mata hanci ta ce" wannan du bana so su zamo damuwar da zasu hanna ki auren Mai martaba sarkin Agadez
ZULAIHAT da kike magana a gaban idannuwanki idan ubanta na magana tana iya daga kanta ne? To da izinin Allah idan kika auri ubanta ta nuna ba zaku yi zaman lafiya ba dolenta zata yiwa uwarta biyaya dan ba ke ba ko ni nan na zama auntynta
Ta karashe tana dage mata gira guda hakan ya saka Zahrau sakin yar daria tana jan kuncin Najeeba
Najeeba ta yi murmushi ta ce" matarsa kuwa meye hadinki da ita? Idan ita tana kyankyaminki, mijinta kuwa ya ga abin so kuma sai ta yi mamakin bakar fatar nan jinnin shuwa arab ta firgitata a lokacin da mijinta ya zama baya iya yi sai da yar duma dumar Abih
Ta karashe tana mai shigar Zahraun da cakulkuli
Ai kuwa nan suka cakule sunna cakulkuli sunna kyakyata daria kamar ba su ba
Sai da sukai sallah suka ringa shiga wanka
Kayan mak up ta baje saman cafet din dakin Anmy
Cikin nutsuwa ta ringa gyarawa yayun nata fuskokinsa cikin simple mak up mai tafe da tsarin kalar fatarsu daidai da kowace
Nan da nan sirrin tsarin kyansu ya fito
Baki dayansu Lafayar ce suka nanada wace ta sha turaran wuta mai balakin kanshi
Wajen saka alkyabar kuwa NAJEEBA ta yi tsaki ya fi a irga sannan ta dora nata
Yan matan fitowa sukai reras su hudu da su kamar ka sace su ka gudu
Tsayinsu ya kasance da kadan kadan suka fi junna,
Yannayin jikinsu ne ya bambanta da kalar fatarsu dan wata ta fi wata haske, bakin wata ya fi na wata fizga aman fuskarsu kamarsu daya ciki kuwa har irin lebunnansu daya
Jeruwa sukai NAJEEBA ta kashe masu hoto da Iphone dinta suka fito das da su a hoton kamar wasu amaren sarakuna wato gimbiyoyi
Zahrau jinta take cikin nutsuwa cikin alkyabar, dadinta take ji sosai
A haka suka firfito sukaiwa Anmy salama
Message din Ambassador din Niger wanda ke zaune a kani ne ya shigo wayarta cewa ya zo fadar yana zaune da mutane ita kawai yake jura yau ba zai iya baci ba sai sun hadu
Murmushi ta yi bayan ta karanta bata bashi amsa ba, sannan sam ta sha'afa shi din bata masa kashedin kar ya kirayi numberta na Airtel ba, hasalima saka wayar ta yi a jirgi dan bata so a gaban manya ta yi ta samun kira dan ta tabata tana dagawa abin zai zama magana
Sunna tsakar FADA ne, wajen ya dauki hasken fitilu ne ga kuma hasken sarakunnan dake walwali
Wajen a zagaye yake su kuwa su biyu sun tsaya dan nesa sunna zantawa
Tun daga nesa dogarai ke sanar da zuwansu da kirari da komai tamkat su dinma y'ayan sarautar
A hankali ya juyo dubansa wajensu dan gannin shin sun saka alkyabar yanzu ko basu saka din ba?
Gannin sun saka ya saka shi maida dubansa wajen mai martaba
Ga mamakinsa sai ya ga ya fi shi bada hankali kansu
Murmushi ya yi a ransa yana furta ikon Allah
A dazu karara Abih ya nuna masa irin rigimar da ta faru tsakanin Zahraun da tsoron manemin aurenta
Cikin ikon Allah yana buda baki sai ya yi murmushi ya ce" dama ba mijinta babe shi yasa Allah ya kawar da shi daga rayuwarta kafin mai wajen ya iso
Kuma dubansu ya yo kadan gannin sun dakata , sai da ya sha iska ya dan dago hannayensa ya yafito su
NAJEEBA ta tabe baminta a ranta fadi take" irin ga yan gidansan nan, ahi ba zai yi mana magana ba mai dunkum kawai!
Irin yanda suka nemi zubewa kasa dan gaishe da su ya kara birge sarkin garin Agadez
Sai dai sam bai barsu ba ya hanna hakan
Irin yanda du suka layu suka sada kansu daga tsayen da suke ya saka SHAHEED lumshe idannuwansa yana murmushi fadi yake" yanzu mutun yanzu ba mutun ba, dan ya tabata a wajen nan aka jata fada walahi zata kwabe alkyabar nan ne ta nuna hali , shi dai mutun marar kamun kai me ake da shi?
Itama baki take yatsinawa daga kasa tana fadin" na tsani raini, na tsani Raini!
Tun da suka tsayan yake kallon Zahrau,
A hankali ta dago dubanta ta sauke saman fuskarsa
Irin murmushin da ya sakar mata a bayanne yake shi ya sakata dan saka idannuwanta cikin nasa kafin ta lumshe su ta kawar da su a hankali tana jin zuciyarta na dokawa
Ko ba komai ya iya kallo
Ta furta a kasan zuciyarta
Dogarin dake cen nesa rike da sakonsu ya yafito
Yana karasowa cike da bada umarni a tausashe ya furta" idan su gimbiya sun koma bangaren GIMBIYA uwa, ka bi su da sakon nan
A hankali ya yi maganar dogarin ne ya ringa takadi yana furta su Gimbiya sun gode da sauransu
Wayoyin dake cikin aljihunsa kasan babar rigarsa ne suke ta vibrate
Wayar wajen Zahrau ne da ta Najeeba da ta su ummu, ya amshe su ne a wannan karon bama dan bincike ba sai dan ya daidai du wani shigi da ficin da zai hada zahrau da wani, dan tuwon girma miyarsa nama
Sai dai tun da ya amsa yar karamar fara kar din samsung din ciki ake ta kira
Hannunsa ya saka ya lalubi wayar ya cirota
Yana kallon screen din sai ya ga sunnan kamar haka" Ambasador zumana
Wayoyin du farare ne, bai dai tantance wace marque dinsu ba hakan ya sa ya kasa gane ta waye
Sunnan sam bai masa, sunnan ya saka shi dubansu daya bayan daya dan sunnan nan ba sunnan mutunci bane, koda soyaya ne me ya kawo zumma a ciki?
Haka kawai ya tsayar da dubansa tsakannin ummulkhair da NAJEEBA, sun fi masa kama da wa'inda basu san meye jin magana ba
Jin an maido kiran ya saka shi dagawa sannan ya kara a kunnayensa
*haba baby, haba hearty, me yasa zaki ringa bani wahala haka ne? Kin san mutun nawa ke iya saka dukiyarsu dan su ganni? Kin san mace nawa ke faman na zama abokin gaisawarta? NAJEEBA na yi missing din ki, shi ya sa na taso na zo har masarautarku da alama baki ne da ku dan da kyar na iya gannin su liman babama, ki fito ina bakin zagayen kwanar gidan sarki dan Allah, idan ban ganki ba yau ba zan iya rintsawa ba*
Dukan ratabi maganar nan ya yishi ne ba tare da ya ji muryar wanda ya amsa kiransa ba, shi dai dama faman da yake ta daga tunda ta gadaga kuwa zai fada mata gaskiya ne ta zo, ta zo fa idan bata zo ba ba zai bar wajen nan ba
A hankali ya shiga cire wayar daga wajen kunnensa
Zuwa lokacin kuwa irin jin abin ana kallon kan nan ya saka NAJEEBA dago dubanta dan tabatar wa ke kallonta ne?
Da sauri da kuma tsoro ta mayar da kanta kasa ta sada sakamakon irin duban nan dake sakata jin babu dadi da ya tsareta da shi
Ne ya sa ya tsane ni ne?
Ta tambayi kanta
Yana kokarin mayar da wayar message ya shigo kamar haka" kin kuwa san irin tsarabar da na kawo maki? Na zo maki da iPhone 12, na siyo maki wata gown, na siyo maki wata sarkar zinari a dubai
*Baby ko nawa kike da bukata a yau zan baki in dai zan samu biyan bukata*
Biyan bukatar ne ya kasa karasa cewa na son ganninta, sai ya tsaya a iya biyan bukata
A dole yau ya gama yarda cewa yarinyar nan ta gama wulakanta su,
Karshen wulakantawa a yanzu har nan cikin gidan nan mai daraja take baiwa samarin nata zuwa, sannan har a zo har nan a yi kokarin yada lalatar da aka saba?
Bayan su ke hukunta wanda ya aikata lalata?
Tabas a yau sai ya kamata turmi da tabarya da kansa ta yanda zai yi mata hukunci baki daya garinsa ya sani dan akan baiwa gawa kashi ne dan mai rai ya ji tsoro
Ya san bai isa ya hukuntasu ba tare da huja ba
Zai nuna mata yaro yaro ne, zai bi ta da kansa idan ta kama! Zai yi mata kamun da ba zata musa ba, zai yi mata bulalar nan a tsakiyar gari sannan shi kuwa katon banzan zai haka rami a cikin gari a jefe shi! Baya son zina! Baya son mazinaci
A hankali ya fara jin tashin zuciya yana jin wani masifafen haushinta
Tir da ke! Ke kuwa bayan rashin jin magana sai kika auri aikin da zai rarake ki ya tsufantar da ke a wulakance ya hada ki da cuta ko ya hada ki da tabo? Mace da zata ji, da ta kilace kanta a dakinta komai muninsa dan samun sakamako mai kyau zuwa gaba
Dubansa ya kai kan Ummulkhair
Da hannunsa ya yafitota
Tun da ta ga haka a hankali ta tako ta dan tsaya dan nesa da shi kanta a kasa
Wayoyin saura ya hada ya mika mata yana mai nuna mata ta koma
Da murnar samun wayoyinsu ta juya ta koma kusa da yan uwanta, Najeeba fa nan da nan tsayuwar ta isheta, tun da ta ga wayarta a hannun Ummulkhair sai kafafuwanta suka fara yi mata kaikayi harma ta ringa jin kamar wace take jin fitsari
Ta gaji da tsayuwar iskancin nan da irin duban da su Zagra ke aikawa junnansu da mai martaba da kuma irin kausasashen kallon da mai garinsu ke aika mata na kiyaya wanda ya kara fitar mata da tsayuwar kallon kallon a rai ya sakata a hanakali ta ringa dan matsowa kusa da Ummulkhair
Raf ta kai hannunta saman nata ta damki mai wayoyin wanda tsaf a kan idannuwansa harma ya yi murmushin samun nasar a d o m i n d a m a b u r i n s a t a k a r b i w a y a r d a n y a a i w a t a r d a a i k i n s a a y a u b a s a i g o b e b a !
. . . . . . . . . . . . . . m o r e c o m m e n t a m i n a n a r z i k i =??=??=??=??=??=؞?=؞?=؞?=؞?=؞?=؞?=ؓ?=ؓ?=ؓ?=ؓ?=ؓ?=ؓ?=ؓ?=ؓ?
[ 1 / 2 0 , 9 : 5 0 A M ] U m m u S u h a n =?
?: >?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????
* M A G E *
_ ( M a i k w a n c i y a r d ' a u k a r r a i ) _
>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????>?????
* N a *
* S A J I D A *
=ث?(' * T A U R A R I N M A R U B U T A N N I G E R ( A S S O . ) * ?
_ ( T s i n t s i y a m a d ' a u r i n k i d ' a y a ) _ >??
& * [ T . M . N . A ] * & =???=؊??
h t t p s : / / w ww.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
11
Sakar mata wayoyin ta yi baki daya ita kuwa ta koma wajenta tana mai ci gaba da tsayuwa irin na yan uwanta
Sai da suka kuma yin magana wace iya su ke jin abinda suke fada tsakaninsu sirikan kafin SHAHEED ya kai dubansa wajen su ZAHRAU
Muryarsa kasa kasan nan ya buda bakinsa a hankali ya ce" ku koma ciki, sarki na godiya
Kamar jira take a salamesu, ita ta fara daga kafarta tama manta da sai sun risina sun kara godiya ta yi gaba a hankali ta shige ciki
Suma bayanta suka biyo sai dogarin dake tafe da wata katuwar ambulope dauke da sako dan nesa da su
A nan tsakiyar gidan suka tsaya NAJEEBA na ta dadana wayarta tana duba sakwonnin da ta bari, irin kirate kirayen da ta samu wa'inda du ba'a daga ba aman an daga na yau na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 58