Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gidan nan inba damuwa Murmushi papi yayi tare da furta your wish is my command baby. Kuyi hakuri yau ba yawa na gaji wlh ๐Ÿฅบ๐Ÿ’” [9/18, 12:01 AM] +234 810 666 6520: LIYANA EP 34 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://chat.whatsapp.com/EQwrrqEY58RIB7ou8jEmJN โ€ŽุงูŽู„ู„ู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุตูŽู„ูู‘ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ูŽู‘ูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑููƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ. โ€Ž"ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ ู‡ุฐุง ุงู„ุนุงู… ุนุงู…ู‹ุง ู…ุจุงุฑูƒู‹ุง ู…ู„ูŠุฆู‹ุง ุจุงู„ุฎูŠุฑุงุช ูˆุงู„ู†ุนู…. ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ู‡ ุนุงู…ู‹ุง ุชุฒุฏุงุฏ ููŠู‡ ู‚ุฑุจุชู†ุง ุฅู„ูŠูƒ ูˆุนุงู…ู‹ุง ุชุชุญู‚ู‚ ููŠู‡ ุขู…ุงู„ู†ุง ูˆุฃุญู„ุงู…ู†ุง. ุขู…ูŠู†." Bismillahi 17/9/9/2024 ... murmushi ta sakar wa papi tare ta kama hannunsa, ahankali ta furta Muje ciki kamun tausa AMIR nagaji ta fada tana wani lumshe ido. Papi kuwa kamar jira yake, ya dauke abarsa sukayi ciki. A bangaren liyana kuwa koda ta koma dakinta da gudu tana shaqar kuka, saida ta jima tanayin kukan, kamun ta goge hawayenta ta sauko qasa ta fara aikace aikacen da zata yi. Tanayi tana sharar kwallah, lokaci daya tana tunanin miya canja papi har haka, zata iya cewa bata taba ji yayi mata tsawa ba, ko laifi ta masa saidai ya horata ta hanyar shareta ya daina mata magana gabaki daya. Nikuma ameeratouh nace baki san bunda farha ta shirya ba, wannan abun ba aikin papi bane na farha ne ta rigada ta juyesa๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ AMMAR Zaune suke da ARHAM suna dan fira tsakaninsu, saboda yanxu ARHAM din tausayin ammar din yakeji saboda yace masa bashida kowa, baffansa ya rasu baisan gurin wa zaije ba, kawai dai yawo yakeyi, to wurin ne kuma akayi kidnapping nashi, kuma acan gurin ya hadu da NOOR . Juyo da kallonsa ARHAM yayi zuwaga Noor dake shaqar shinkafa jallof, ci take kamar wadda zaโ€™a kwacewa plate. Dagowa tayi jin kamar idanu akanta. Karaff suka hada ido da ARHAM, turo baki tayi tareda murguda masa baki, cikin qunquni da takeyi wanda baโ€™ajin mi take cewa ta furta, kurwata kurr wallahi maye mai kallon haramun. Nikuma nace kun jini da yarinya๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” Ahankali ta ajiye plate din tare da tasowa ta haye gadon da ammar ke kwance, hannunsa ta kama tare da sarkewa da nata. Mikewa ARHAM yayi tare da fita sakamakon kiransa da akayi a waya. Ammar kuwa da idonsa ke rufe kamar mai bacci yadan bude kadan ta yadda zai ganta da kyau batare da ita noor ta gane idonsa biyu ba , dan tun dazu duk abunda take yana kallonta pretending kawai yake Ahankali takai hannunta kan sumar kansa da tayi yawa ta sauko masa har baya , sakamakon rashin rageta da bayayi. Cikin sumar kan nasa ta tura hannunta tare da furta, dama mace ne kai wallahi , sai nayita maka kitso, ta fada tana kara cakuda kan nasa. Ammar kuwa, tunda tasaka hannunta a kansa ya daina ganewa , ji yake kamar ya kamota ya rungumeta, wani yarr yarrrrr yake ji tundaga kafarsa har zuwa tsakar kansa, sakamakon qara cusa hannunta duka biyu a kansa. Ita kuma noor ahankali takai hannunta kan lips nasa da suke pink colour sharrr. Ahankali ta furta. Kai kam matarka ta bani komi na mata, qilan ma kafita kyau allah,nikam wallahi bazan auri mijin daya fini kyau ba ta fada tana turo baki kamar wadda akayiwa laifi. Nikuma Ameeratouh nace ina ruwanki da matar sa, kuma mu ina ruwan mu๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” Shikuma ammar dariyarsa yake dannewa dan harga allah dariya noor ke basa, yanason ya hanata abunda take masa but ya kasa , bayason ya katse mata nishadi. Da sauri ammar ya bude idonsa da suka canza colour suka qanqance da jaraba sakamakon abunda yaji noor na masa. Kallonta yakeyi cikin mamaki da kuma yarinta, janye hannunsa dake bakinta tana tsutsa kamar mai shan alawa yayi tare da dan hararar ta ya furta manya kawai tare da juya mata baya. Turo baki tayi tare da miqewa ta koma saman kujera( gurin zaman masu jinya) Nikuma nace jinya take dama ๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” MADINA 7:00AM Ahankali yake bude idonsa, sakamakon hasken dake shigowa dakin. Kallon dakin yayi wanda ya bata a Daren jiya, tsaki yayi tare da mikewa direct bathing room ya shiga. Ya dauki kusan 1 hour kamun ya fito qugunsa daure da towel, shafe shafensa yayi tare da shiga inda yake adana kayansa. Sanye ya fito cikin shigarsa ta uniform dinsa na army (sojoji) ya fito sakk FIELD MARSHAL dinsa wato MUHMD Q JALAL Ahankali ya fito har falorn gidan karo yaci da Auntie mimi dake qoqarin jera abinci. Kallonsa tayi cikin fuskar damuwa ganin yanayinsa kamar wanda baisan akwai rahama ba, gashi face nashi ya nuna alamun damuwa. Kallonsa take tun daga sama har qasa, kamun idonta ya sauka zuwa ga ciwon hannunsa daya jiwa kansa ciwo jiya. Da sauri ta dauko first aid box tare da kamo hannunsa, jansa tayi har saman kujera tare da fara masa treatment, tanayi tana hawaye. Dago habarta yayi tare da girgiza mata kai alamun ta daina kuka, ahankali ta saka hannunta tare da goge face nata. Murmushi ya sakar mata tare da furta Auntie mimina zanyi tafiya yau but bazan jima ba zan dawo ya fada tare da miqewa ya nufi hanyar fita. Girgiza kanta kawai tayi tare da kallon daya daga cikin masu aikin ta furta, kaje ka gyara masa room dinsa nasan ya lalata shi. Karku rude masu karatu Auntie mami dae mimi duk daya ne a gurina kar kuji nace ku rude ๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” Nigeria Abuja Tunda asuba liyana ta tashi daga barci ta fara aikin da zatayi 6:30 daidai ta kammala. Wanka tayi tare da yin dressing nata na zuwa school, abincin ma bata tsaya ciba tadai saka ga lunch box, saboda ganin take idan ta tsaya anti farha zata tsayar da ita Ni abun yama ban dariya ๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” 7:00 daidai tabar gidan tare da malan bala, basu tsaya ko ina ba sai Nile university, suna isa ta saki wata ajiyar xuciya ๐Ÿ˜‚ Acan gida kuwa. Koda su farha suka tashi bataga liyana ba, ba qaramun takaici farha taji ba saboda liyana ta bata mata shiri. Haka ta zauna ta zuga papi, wai yarsa bata daukesa da daraja ba tunda zata iya fita bata fada masa ba , idan ita bata ganin mutuncinta tunda bata dauketa uwa ba to shifa miyasa bazata fada masa ba. Ai kuwa papi ya dauka ya cika yayi fam Nagaji ๐Ÿ˜‚ [10/11, 2:36 PM] BABY ๐Ÿ˜๐Ÿฅณ: LIYANA EP 35 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://chat.whatsapp.com/EQwrrqEY58RIB7ou8jEmJN โ€ŽุงูŽู„ู„ู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุตูŽู„ูู‘ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ูŽู‘ูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑููƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ. โ€Ž"ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ ู‡ุฐุง ุงู„ุนุงู… ุนุงู…ู‹ุง ู…ุจุงุฑูƒู‹ุง ู…ู„ูŠุฆู‹ุง ุจุงู„ุฎูŠุฑุงุช ูˆุงู„ู†ุนู…. ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ู‡ ุนุงู…ู‹ุง ุชุฒุฏุงุฏ ููŠู‡ ู‚ุฑุจุชู†ุง ุฅู„ูŠูƒ ูˆุนุงู…ู‹ุง ุชุชุญู‚ู‚ ููŠู‡ ุขู…ุงู„ู†ุง ูˆุฃุญู„ุงู…ู†ุง. ุขู…ูŠู†." Bismillahi 18/9/2024 Tsaye yake sai safa da marwa yake ( zagayen daki). Fuskarsa har wani sheqin ja takeyi saboda fushi abunka da farin mutum. Farha kuwa ko damuwa dashi batayi ba, dan zaunen ta take, ta aza kafa daya kan daya tana TikTok kamar wata ya 18/20 years idan tayi wani abu. Ahankali liyana ta sanyo qafarta acikin falorn, bakinta na furta , ASSALAMU ALAIKUM. Cikin sanyinta a koda yaushe ta furta ina wuni papi ina wuni autie ta fada tana sakin murmushi. Shikuma papi kallonta yake yi cikin takaici, sai famam hararta yakeyi. Ita kuma liyana bata lura da yadda face din papin nata ya canza ba ta saka kai zata wuce . Wata uwar tsawa papi ya dakawa liyana, wadda tayi sanadiyar sakin littafanta dake cikin jaka tana kamewa guri daya saboda tsoro. Wani tsawan ya sake daka mata tare da furta. Bada ke nake ba liyana daga gidan ubanwa kika fito?. Ya fada yana kauda kansa daga kallonta, saboda duk ya kalleta gabansa keyin mummunan faduwa, ga wani tausayinta da yakeji, but idan ya tuna da farharsa sai yaji yafison ya rasa kowa daya rasata. Pappp pappi, da..ga ma... makaranta nake, liyana ta fada tana karkarwa, saboda bata taba ganinsa cikin wannan fushin ba. Ahankali papi ya furta Toh uwar wa ta baki izinin fita daga gidan nan? Ya fada cikin nuna halin ko in kula Idonta ne ya cika da kwallah, badan komi ba saboda abunda ya fada nacewa uwar wa ya bata izini. Babu kowa papi . ta fada hawaye na saukowa daga idonta sharrrrr. Cikin fushi da kuma abunda farha tasashi ya furta. Daga yau bazaki sake zuwa school din ba, saboda banyarda da cewa can kawai kike zuwa ba papi ya furta. Da gudu liyana ta ruga ta shiga dakinta tana kuka, batasan mike damun papinta ba ya canza mata sosae, ita bama school din dayace ta daina xuwa bane ya bata mata, abunda yafi daga mata hankali da kuma saka xuciyarta zafi shine, dayace ba school dai take xuwa, kenan akwai inda take xuwa? Ta dauki lokaci tana kuka , kamun daga bisani ta daina, ahankali take ajiyar xuciya, ta dauki kusan 10 minutes a haka , kamun ta miqe ta shiga toilet duk da tana ganin dishi dishi. A bangaren farha kuwa. Lokacin da papi ya gama yiwa liyana fada, murmushi farha ta saki tare da daukowa papi ruwa ta basa. Saida ta tabbatar da hankslinsa ya kwanta kamun ta furta. Yauwa Amir batun yazeed ne dama, ya kamo hanyar dawowa yau, kaga kenan gobe zai iso tunda safe cox zasu kwana a hanya. Murmushi mai tsafta papi ya saki tare da furta allah kawosa lafiya baby, sannan zan tura miki 3 million ki shirya masa tarba, ina fatan zasu isheki. Murmushi farha tayi lokaci daya tana gyada masa kai AMMAR Zaune suke cikin mota, ARHAM na gaban car din , yayinda Ammar ke mazaunin baya shida noor data aza kanta saman kafarsa tana barci. Sunyi tafiya mai dan nisa kamun su iso qofar wani babban gida wanda aka qawa tashi da flowers masu kyau. Kutsa kai yayi sukayi cikin gidan sakamakon gate din da aka bude na gidan. Sosae gidan ya kawatu da shuke shuke, sosai gidan ya burge ammar amma ko kadan bai nuna qauyanci ba, kasan cewarsa ya taso gidan talakawa masu wadatar xuci. Ahankali car din ta tsaya daidai wani part acikin gidan, part din yanada girma sosai. ARHAM ne yafara fita sannan yayiwa AMMAR alamun ya fito shima. Juyowa ammar yayi tare da kallon noor dake bacci amma sai faman turo baki take, kaman mai jiran a tabata ayi dambe. Ahankali yadan bubbuga face nata tare da furta, kasa sarkin bacci tashi a haka. Ammar ya furta Zumbur ta tashi tana murza idonta, kamun ta gama iya shegen tah ammar har ya fita daga car din. Fitowa tayi itama tare da yin sauri ta isa gurinsa. Hannunsa ta kama tare da furta , shine zaka tsere kabarni koh tohm allah ba azzalumin bawa bane ta fada tana dannawa ARHAM harara dake kallonsu. Murmushi ammar ya saki dashi da ARHAM Ahankali suka kutsa kai cikin part din . Wani sanyi da kamshi mai saka kwanciyar hankali ne ke ratsa su sakamakon shiga falor da sukayi. Wata matace akalla zata kai shekara 49 ko sama da haka, ruwan tarwada ce mai tsananin kama da NANA , saidai ita nana farace wannan kuma tarwada, sai kuma nana da tafita tsufa sosai, ta wani bangaren kuma tana kama da ARHAM but ba sosae ba. Da murmushi ARHAM ya isa gurinta tare da rungumeta lokaci daya yana furta . Sannu da gida mommy nah ya fada ya zaunawa kusa gareta tare da daura kansa saman cinyar ta. Murmushi wadda aka kira da mommy tayi tare da shafa kansa tana furta son har yanxu qaqi girma kai dai. Noor kuwa baki ta bude tana kallonsu, sai kuma ta maida kallonta ga ammar dake kallonsu ARHAM cikin shaโ€™awa. Ahankali ta furta kai hamma AMMAR dan allah karkace mun matar sa ce waccan tab ta fada tana kallonsu. Buge mata baki ammar yayi, wanda yasa tadan saki qarar dayasa ARHAM da mommy juyowa garesu. Ahankali mommy ta saki murmushi tare da kallon arham ta furta, sune koh? Gyada mata kai ARHAM yayi. Ahankali ta qara kallon noor da AMMAR waโ€™yanda suka yimata kaman ceceniya da wasu na kusa da ita. Cikin sakin face mommy tace ku qaraso mana kuka tsaya a can. Riqe hannun ammar noor tayi kamun ta furta, Muje tare wallahi dan naga kana tsayawa gwara mu mutu tare a tsira tare Kai jamaโ€™a allah yima noor sauqi ๐Ÿ’”๐Ÿ˜‚ Sosai mommy ta sake dasu, inda ta jawo noor ajikinta wadda keta faman cin magani ๐Ÿ˜‚ ABUJA Sosae ake gyaran gidan da aikace aikace kaman wani gidan biki. Su Auntie farha anci wanka kaman baza,a mutu ba, cikin sauri ta iske malan bala tare da furta, yi sauri bala jirginsu ya kusa qarasowa ta fada tana shigewa car din. Shima malan bala shiga yayi tare da kama hanyar airport [10/11, 2:36 PM] BABY ๐Ÿ˜๐Ÿฅณ: LIYANA EP 36 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://chat.whatsapp.com/EQwrrqEY58RIB7ou8jEmJN โ€ŽุงูŽู„ู„ู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุตูŽู„ูู‘ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ูŽู‘ูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑููƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ. โ€Ž"ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ ู‡ุฐุง ุงู„ุนุงู… ุนุงู…ู‹ุง ู…ุจุงุฑูƒู‹ุง ู…ู„ูŠุฆู‹ุง ุจุงู„ุฎูŠุฑุงุช ูˆุงู„ู†ุนู…. ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ู‡ ุนุงู…ู‹ุง ุชุฒุฏุงุฏ ููŠู‡ ู‚ุฑุจุชู†ุง ุฅู„ูŠูƒ ูˆุนุงู…ู‹ุง ุชุชุญู‚ู‚ ููŠู‡ ุขู…ุงู„ู†ุง ูˆุฃุญู„ุงู…ู†ุง. ุขู…ูŠู†." Bismillahii 19/9/2024 Tsaye farha take tana sakin wani cool murmushi saboda shauqin son ganin gudan jininta. Ahankali jirgin ke saukowa daga sararin samaniya har ya sauko duka ya tsaya cakk. Baโ€™afi 30 minutes ba saiga wani matashin saurayi ,aqallah zai kai 27 years ,yanada dan haske but ba sosae ba, yana dan da kyau but sosae ba Wani tarin uban suma ne akanshi wanda akayiwa wani kafurin aski irin na manyan arna, Idonsa kaman na mujiya, dan zagayen bakinsa ya rine daga kalan pink ya koma baki. Sanye yake cikin wata T shirt baqa, sai wani dan short wando da bai wuce cinya ba, ga wasu uban sarqoqi daya saka a wuyansa. Cikin tafiya irinta yan jagaliya, ko nace yara marasa ji yake tafowa da dan saurin sa. Hannu ya bude yana fadin oyoyo momcy. Ai kuwa da dan sauri farha ta rungume sa tare da furta , welcome back son. Ta fada tana sakin murmushi tare da kama hannunsa suka shiga car din da tazo ita da malan bala. Ahankali motar tasu ta kutsa cikin gidan papi, kallon gidan yazeed yake cikin zuciyarsa yana fadin, lallai momcy ansamu duniya shiyasa naga har wani fresh takeyi, nima a gaskiya zan huta tunda babu banbanci da can inda na baro har nan ma ya fishi, wani cool murmushi ya qara saki lokacin da yake qara qarewa gidan kallo yana ayyanah wani abu a ransa. Farha ce ta katse masa tunani tare da furta, fito son mun kawo ta fada tana jawo hannunsa a motar. Jansa tayi har cikin gidan tare da furta kaje kayi wanka son zan shirya maka lunch, farha ta fada tare da nuna masa dakin dake sama. Cikin sauri da kuma gajiya ya nufi dakin, murda handle din qofar yayi tare da fadawa ciki. Tsaye yayi a bakin door din yana qarewa abun mamakin daya gani kallo. Kwance take saman bed dinta tana bacci, duk surar jikinta a bayyane take, sakamakon shigar dake jikinta, wani gajeren wando ne wanda da qadan ya rufe mata mazaunanta, sai kuma wata yar T shirt da tasaka wadda ta tattare ta koma saman cikinta. Abunda ya faru shine liyana koda ta tashi da zazzabi ta tashi sakamakon kukan data kwana tanayi, dakyar ta mike tayi wanka, data fito kuma bata tsaya zabar kaya ba kawai ta saka wannan domin a ganinta ba mai shigowa dakinta, kuma bata saka ran akwai wanda zai shigo ba har bacci yayi awon gaba da ita wannan kenan. Kallonta yake tundaga kan qafarta har zuwa kan santala santalan cinyoyinta . Ahankali ya taka har bakin bed din tare da duqo da kansa a face nata yana karewa face nata kallo. Liyana kuwa acikin barci taji kamar mutum a kanta, ga kuma wani zafi dake dan feso mata. Ahankali tadan fara bude idonta kadan kadan ,tun tana budewa tana ganin dishi dishi har ta bude su duka ta sauke idonta a kansa. Qara zare ido liyana tayi tana kallon abun mamaki, kulle ido tayi tare da qara budewa, domin ganin dagaske ne wai qato ne a dakinta, ganin ya sakar mata murmushi yasa ta daka uban tsalle tare da sakin qara ta fito dakin da gudu. Fadi take papi papppi papiiiii kana ina, wayyo umminah ta fito falorn tana kuwa da kuma hawaye. Shikuma yazeed ganin ta fito da gudu ya biyota yana tambayarta miya faru. Farha kuwa da gudu ta fito dakinta, jin kuwa a gidan, kuma ita duk zamanta a gidan bata taba jin haka ba, daure take da daurin qirji dan ta dauka barayi ne suka shigo gidan da rana tsaka. Karo taci da liyana ji kake gabb sun buge, da sauri liyana ta koma bayan farha tana furta Auntie qato a dakina wallahi ta fada daidai lokacin yazeed na qarasowa gurin. Wani qululun bakin ciki ya tasowa farha ga wani takaici na cewa ta kira danta da qato to mi take nufi Jawo liyana tayi tare zabga mata wani wawan mari wanda yasa liyana saida taga taurari ji kake puuuu pauuuu qarar mari. Dafe kunci liyana tayi, saboda a rayuwarta baโ€™a taba marinta ba sai yau saida jinta ya dauke na wani lokaci. Cikin fusata farha ta furta dan ubanki dan nawa ne qato? Iyye saidai idan uwarki dake cikin qabari itace qatuwa ta fada tana nunen liyana Yazeed dake tsaye yana kallon mahaifiyar shi data wanke wannan kyakkyawar halittar da mari yake kallo, duk da yasan halin mahaifiyar sa garesa wallahi saida yaji tausanta. Cikin fada farha ta sake fadin Daga yau kuma ba nan ne dakinki kiba, ki koma down stairs kisamu daki kishiga, nasa a kwashe miki kayanki daxu kina kwanan asara naso tadaki to inada abunyi shiyasa, ta kare fada tare da kallon yazeed ta furta kai kuma wuce kayi wankan da zakayi ta fada tana watsa masa harara Kai farha ikon allah ๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” Badan yazeed yaso ba yabi hanyar dakinsa, itama farha wucewa tayi aka bar liyana dake durkushe a gurin tana kuka. Koda ya koma dakin kwanciya yayi a bed din liyana tare da furta ohhh god sheโ€™s damn cute and sexyy zatayi dadin harka yazeed ya fada yana lashe lips nasa na qasa AMMAR Sosae mommy ta karbesu kamar yayanta, inda ammar aka bashi room a dakin ARHAM saboda ARHAM din yace yana son zama dashi a room din Ita kuma noor aka kaita dakin qanwar ARHAM sunanta hauwaโ€™u amma suna kiranta da AUTA, saidai koda su ammar suka zo bata na, ta tafi gidan yayarta weekend but a yau zata dawo kasan cewar sunada school monday. Kayan auta mommy ta bawa noor inda suka amsheta dass kaman nata abunka da sabuwar budurwa yanxu take cikin tashen girma. Ahankali take saukowa cikin riga doguwa, wadda ta matseta daga sama, qasa kuma ya bude. Direct part dinsu ARHAM ta nufa, babu sallama ko notice ta murda handle din qofar, daidai kuma lokacin ammar ya fito daga wanda daure da towel, kasancewar ARHAM baya nan ya fita shiyasa ya fito a haka saboda ammar badai kunya ba. Tsura masa cat eyes nata tayi tana kallon qarfaffan jikinsa, duk da shekarunsa ba wasu da yawa bane iya ka sukai 23/24 yanxu, amma hakan bai hana mazantakar surar jikinsa bayyana ba. Ahankali ammar ya juyo karaff suka hada ido da noor wadda ta dade anan tsaye, dan allah ya taimakesa bai cire towel din ba๐Ÿ˜‚ Da gudu ammar ya koma toilet tare da dan leqo kansa ya furta . Ke anya noor kedai ce kuwa, taya zaki shigoma mutane daki babu ko sallama. Tabe baki tayi tare da furta, kai kasan wannan hamma ammar yo ni ina ruwana da wata sallama dan ma kasamu nazo ganinka dan nayi kewarka ta fada tana turo baki. Tsaki ammar yayi tare da qoqarin rufe bayen yaji noor na fadin Hamma ammar bazaka fito daganka ba, koh nazo in fito dakai ta fada tana qoqarin zuwa bakin toilet din Ai da sauri ammar ya kulle toilet din yana furta inke bakida hankali ni inada shi. Turo baki tayi tare da bude qofar dakin tana kunkuni qasa qasa. Daidai zata fita taci karo da wata budurwa saโ€™arta, kamarta sakk da ARHAM saidai ita fara ce sosae, sakamakon ARHAM da yake chocolate color. Yamutsa fuska noor tayi tare da rabata zata wuce, ahankali yarinyar cikin cool voice nata ta furta, did I know you please ko baki mukayi a gidan ? Mtswwww noor taja tsaki tare da fadin idonki ya fada miki tasa kai ta fice tayi dakin mommy. Niko ameeratouh nace mutum da gidansu๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” [10/11, 2:36 PM] BABY ๐Ÿ˜๐Ÿฅณ: LIYANA EP 37 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://chat.whatsapp.com/EQwrrqEY58RIB7ou8jEmJN โ€ŽุงูŽู„ู„ู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุตูŽู„ูู‘ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ูŽู‘ูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑููƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ. โ€Ž"ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ ู‡ุฐุง ุงู„ุนุงู… ุนุงู…ู‹ุง ู…ุจุงุฑูƒู‹ุง ู…ู„ูŠุฆู‹ุง ุจุงู„ุฎูŠุฑุงุช ูˆุงู„ู†ุนู…. ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ู‡ ุนุงู…ู‹ุง ุชุฒุฏุงุฏ ููŠู‡ ู‚ุฑุจุชู†ุง ุฅู„ูŠูƒ ูˆุนุงู…ู‹ุง ุชุชุญู‚ู‚ ููŠู‡ ุขู…ุงู„ู†ุง ูˆุฃุญู„ุงู…ู†ุง. ุขู…ูŠู†." Bismillahii 25/9/2024 ..bin bayanta auta tayi har dakin mommy, daidai noor zata shiga dakin auta tasha gabanta tare da furta. Ke halan yar uban wace dazan miki magana kina wani sharewa kuma acikin gidan, gidan mun ma sanye da kayana . Auta ta furta tana sakin huci. Kallonta Noor take irin kallon nan da ake cewa up and down, sai kuma ta yamutsa fuska , alamun yan miskilancin sun hau kan nata. Gefe tabi zata wuce auta dake huci, da sauri auta ta riqo ta tare da dawowa da gabanta tana furta, badake nake ba. Wani qululun baqin ciki ne ya tokare maqogwaron noor, cikin haushi ta furta tabayata kike ni yar ubanwa ce koh? Toh kije ki tambaye tsohonki ko gyatumar ki zata fadamiki, noor ta fada tana turo dan qaramun bakinta. Cikin takaici auta ta daga hannu zata kaiwa noor Mari, kamun takai noor ta riqe hannu tare da falla mata mari har biyu ji kake pauuuuuu puuuuuuu. Ai kuwa nan aka fara dambe dan auta tace saita rama, dambe sukeyi kamar ba gobe. Allah sarki auta babu karfi amma ta dage sai tayi fada da noor daketa nada naushi tana makawa Auta. Mommy da tazo fitowa daga daki taga noor ta haye cikin auta tana kwasar garabasa ๐Ÿ˜‚ Da sauri ta janye noor da kyar, sannan ta daga Auta itama, jansu tayi har falorn qasa tare da fara tambayarsu miya faru Daidai nan kuma Ammar ya fito bedroom nasu, sanye yake cikin qananan kaya da suka masa masifar kyau, sumar kansa daya gyara har baya. Gaida mommy yayi ta amsa masa a sake. Zaunawa yayi yana kallonsu noor da akewa shariโ€™a. Mommy ce ta katse shirun nasu da fadin inajinki noor. Mommy itace daga ganina tace mun wai yar gidan uban wace , shine na shareta banyi magana ba kawai tazo zata mareni ni kuma na riqe hannun tare da mata marin maimakon wanda zata mun. Noor ta fada tana dan turo baki. Ahankali mommy ta juya dace nata da auta tare da furta. Hauwaโ€™u bansan yaushe ne zaki canxa halin nan naki ba, daga ganin mutum kin kamasa da rigima haka akeyi ne? Koh kuma haka na koya miki? Mommy ta fada tana tsare auta da ido. Mommy bafa haka akayi ba itace ta fara tsokana nah auta ta fada tana sakin kuka na dukan da taci. Mommy zata sake magana ammar ya rigata da fadin. Mommy baki san halin yarinyar nan ba, nasan noor bataji maybe itace ta fara tsokanarta, ammar ya fada ya tsuke fuskarsa. Cikin tsiwa noor ta bude baki zatayi magana ammar ya katseta da fadin. Will shut up your mouth out there... dake nake magana ne ko akwai warinki a nan. Ganin dagaske ammar fada yake mata ga face nashi kaman wani tiger yasa idonta ya cika da hawaye dan bata taba ganinsa a haka ba. Ahankali ammar ya kalli auta dake hawaye ya furta, come here sister, ai kuwa kamar jira auta keyi ta taso tare da riqe hannun daya miqo mata Zaunar da ita kusa garesa yayi tare da fara share mata hawaye, yana furta Sorry kinji ki kyale mai idanun aljannun can kinji, ya fada yana ballawa noor harara duk da hawayen da take zubar wa ji yake kamar ana zuba masa wuta a zuciya . Noor kuwa kamar ta mutu haka taji dan bakin ciki, da gudu ta fita daga part din tana kuka

Chapter 9 of 13