Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
leqa Jordan 🇯🇴 JORDAN 🇯🇴 Wata matashiyar yarinya ce akalla zata Kai shekara 16 koh 17 , fara ce amma ba kwarai ba tanada kyau daidai misali sanye take da riga da wando rigar ta matseta sosai, qirjinta ya bayyana , sai wandon daya bude cingom ne Ke bakin tana ci kamar wata kilaki 😂 ta hakimce a saman kujera 3 sitter , ga hadimai nata hidima Bude qofar falorn akayi wata mata ce ta shigo ta mai Dan qiba fara ce itama ba sosae ba kuma tana kama da yarinyar dake zaune a falorn, sanye take da wata alkabba irinta matan sarakuna, ga jikinta ta mashi ado da zinari irin namu na mata, tafiya take cikin taku irin na isa , irin na matan sarakuna. Gaba daya hadiman dake dakin zubewa sukayi a qasa suna kwasar gaisuwa, BARKA DAI UWAR TALAKAWA, TAKAWARKI LAFIYA UWAR MARAYU , GIMBIYA FATEEMA KIYI LOKACINKI KUMA KIYI NA WASU. Haka wata hadima Keta mata kirari . Murmushin gefen baki tayi da alma akwaita da son girma. D’aga masu hannu tayi , alamun su cigaba da abunda suke . Kutsa Kai tayi cikin falorn. Sannu da xuwa momma na sameki lafiya? Yarinyar ta fada. Shiru wadda aka kira da momma tayi tare da zama saman kujera. saida takai minti biyar kafin ta furta HAFSAT “what’s wrong with you” mi kk so ki zama ne? Mi kk so NANA tace idan ta ganki da wannan dressing din? Turo baki wacce aka kira da Hafsat tayi tare da furta . Momma my dressing? Mi dressing din nawa yayi ? And NANA ma bazata ganni ba yanxu ma fita zanyi, sai dai idan kuma wani munafikin ne zaije ya fada mata irinsu BINTOU , tsohuwar da ko gani ba sosae take ba ai koh hango ni tayi daga nesa bazata ganeni Ba mutum ya tsufa yabar mutane su huta taqi duk ita dai ke wannan zancen har takai aya sannan ta mike tare da furta momma ni na fita tunda takuramun zakiyi. Bari mu leqa can wani yanki na katsina kATSINA Wani yaro ne ke tafiya hannunsa dauke da bucket din ruwa, fari ne sosae duk da kamar wahala ne ya maidasa yayi duhu , gashin kansa baki ne sosae har ya kusan kafada Dan ma baffansa na rage masa gashin kan nasa, bakinsa dan qarami ne kamar cokali bazai shiga ba , idonsa brown color ne, A kalla zai kai shekara 18 or 19. Yayi tafiya mai nisa kamun ya kawo wani Dan qaramun gida ya shiga. Sallama yayi cikin gidan Duk da yanada tabbacin babu kowa a cikin gidan Dan a tunaninsa baffa bai dawo daga kasuwar ba.gidan a share yake ko ina tsaff tsaff tsaff da alama masu gidan bandai tsafta ba. Ruwan ya ajiye tare da dauko buta zaiyi arwala Dan an fara kiran sallar magrib. Karo suka ci da wani dattijo akalla zai Kai shekara 65 a duniya saidai shi baqi ne kuma baya kama da yaron. Zaro ido yayi alamun mamaki 👀. Baffa yaushe ka dawo ? Yau ka dawo da wuri . AMMAR yanxu dai alwala zakayi koh tsayawa tambaya tah? Tsohon ya fada , murmushi wanda aka kira ammar din yayi tare da daukar butan yayi alwala suka fita da baffan xuwa masallaci. Na yau kenan Wlh na gaji😭😭🙏 Written by Ameeratouh [7/12, 9:44 PM] +234 810 666 6520: LIYANA EP 7 (SOFTNESS ) WRITTEN BY Ameeratouh (QUEEN 👑) Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://whatsapp.com/channel/0029VadH6ZwADTOMRzzDVg1F/101 BISMILLAHI DATE : 11/7/2024 ...... koda suka dawo masallacin, abun zama Ammar din shimfida baffa ya zauna, shiga daki ammar yayi tare da dauko wani kULA ya ajiyewa baffa a gabansa , Kulan duk ya tsufa amma duk da hk baisa kulan yayi baqi ba da alamu suna da tsafta sosae, budewa baffa yayi , shinkafa da wake ne wato ( GARAUGARAU), Kai kaci abincin ammar baffa ya fada , ataiqaice ya bashi amsa da EH , Kaje makarantar taku yau , Eh baffa yau lecture daya mukayi shiyasa na dawo na daura girki ammar din ya fada. Kadai ringa kula mutane ba abun yarda bane inji baffa. UHM kawai ya furtawa baffa kamar maganar ya ishesa.Toh allah maka albarka baffa ya fada . Amin ya amsa dashi tare da mikewa ya shiga ciki . Kwance yayi saman wata yar katifa , kallon cilin dakin yake tunani yake mai yasa baffa bai son suna mu’amala da mutane? Tambayata ana shine Su ahaka suke rayuwa suka dai? Idan kuma ba haka bane to meyasa suke su kadai? Su waye su? Waye ammar shi bayada mahaifiya ne? Ku cigaba da bibiyar wannan littafi mai suna LIYANA ABUJA Kwance take saman bed dinta, idonta arufe yake kamar mai bacci , tinanin mutumen daya taimaketa takeyi wanda bashida maraba da boyayyen mutum tunda bataga face nashi ba, k”ara gyara kwanciyarta tayi tana tuna yanda yake tafiya kamar wani namijin zaki har lokacin da idonta ya rufe ta daina ganinsa, tashi zaune tayi tare da furta “ why did he left “ ba tare da ya tsaya na masa godiya ba? Waye shi? Anyway allah biyasa ta furta tare da miqewa ta shiga toilet . Acan kuwa bangaren papin Liyana, zaune yake a bedroom nasa yayi tagumi yana tunani . Dafasa akayi , juyowa yayi tare da furta SOOMA . Papin YANA miyake damunka? kodai har yanxu tinani kake waya turo a kasheka? Papin LIYANA babu wanda za’ace bashida maqiya, papin LIYANA ko yanxu mutum ya fado duniya sai yasamu wanda bai sonsa, ballantana kai da allah ya daukaka kake tunanin bakada mahassada ? Koh Manzon allah SAW da akayi duniya dominsa akayi kuma lafira dominsa yanada maqiya Papin YANA. Duk wannan zancen mami Ke yinsa Shiru ne yabiyo ba kafun yace ‘’ MASOOMA “ ina godewa allah daya bani ke a matsayin mata kuma uwar Y’ata , ina alfahari dake, ya fada tare da sumbatar ta a forehead dinta. Fuska ta rufe tana murmushi. Wai SOOMA sai yaushe ne zaki daina jin wannan kunyar tawa Uhm? Ya fada tare da jawo matar sa ya rungume abarsa . SOOMAAA ya fada tare da Jan sunan. Na’am ta furta tare da qara shigewa cikin jikinsa . Kinsan tunanin da nake? Girgiza masa Kai tayi . UHMM..... tinani nake taya zan rayu bayan babu ke Sooma ya fada cikin sanyin murya. Sooma miyasa bazaki yarda a nema miki magani Ba? Sooma kinsan da cewa bayan ciwon QODA hadda CIWON hanta ke damunki? “Whyy SOOMA?” Kinsan da cewa kece komi nawa sai LIYANA amma... kukanta ne ya katse sa da sauri ya dagota . Haba sooma daga magana sai kuka Dan allah kiyi hkr na daina papin yana ya fada yana mai share mata hawaye. Papin LIYANA Dan allah karka bari YANA tasan wannan maganar kaji? Ni inaji a jikina bazan dau wani lokacin ba , And ko bayan raina karka bari yana tayi maraici Dan allah, ga FARHA nan ta jima tana sonka idan nabar duniya ka aureta Dan allah, ta fada tana kallon fuskar Mijin nata tana hawaye,nasan zata kulamun da ita. Ta furta tana mai rushewa da kuka. SOOMA ba kowa ke iya riqe amana ba sooma, bazan iya miki wannan alqawarin ba ya fada yana mai kamo hannunta. A hankali ta furta toh zaka iya mun wani alqawarin? Shima cikin sanyin murya ya furta EHh Zan miki SOOMA indai zan iya. Ko bayan raina Ka kai LIYANA gurin danginka koda kai bazaka je ba AMIR . Kallonta yake cike da mamaki zai iya cewa wannan shine karo na biyu da yaji ta taba fadin sunansa , ji yake kamar tana basa wasiya ne kamar bazata Kai gobe ba.bude baki papi yayi da niyar yayi magana aka fara knocking kofar bedroom din. Wannan kenan Bari mu leqa JORDAN 🇯🇴 Kwance take cikin shiga ta alfarma ta jinkira da kujera bayi na mata tausa a qafa, tsohuwa ce sosae a qallah zata Kai 85 years ko tafi haka, fara ce sosae idan nace sosae ina nufin sosae, glass ne a idonta alamu kamar bata gani sosai.. Written by Ameeratouh LIYANA EP 8&9 (SOFTNESS) WRITTEN BY Ameeratouh (QUEEN 👑) Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah Wannan littafi kirkirarren labari ne banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba https://whatsapp.com/channel/0029VadH6ZwADTOMRzzDVg1F/101 BISMILLAHI 17/7/2024 Kwance take cikin shiga ta alfarma ta jinkira da kujera bayi na mata tausa a qafa, tsohuwa ce sosae a qallah zata Kai 85 years ko tafi haka, fara ce sosae idan nace sosae ina nufin sosae, glass ne a idonta alamu kamar bata gani sosai.. Idon nata ASH color ne. Duk da ta tsufa bai hana kyaunta fitowa ba. Wata hadima ce ta kawo mata kula gabanta ta ajiye mata tare da furta gashi ranki ya dade. Meye acikin kulan? Ya fada . Chicken Pepe da kika ce in kawo miki ranke dade. Lalala yanxu abun naku ya koma qazafi? So kuke ku maidani sakarya marar hankali Rabi?ta fada tare da fashewa da kuka. Kuma Dan kinga da’na yana kwance rai hannun allah da bazaki laqa mun shairi ba. Wadda aka kira da rabi shiru tayi tare da zuba mata ido 👀, inda sabo ya saba da rigimar tsohuwar , kukan ta ne ya dawo da rabi cikin hankalinta, yi hakuri ranki ya dade miyayi zafi? Wani cool and soft voice ne ya tatso ta babba dakin yana fadin ,Ke kam NANA bazaki canza hali ba, tsohuwa kullum cikin fitina da tada hankali idan aka ce kin tsufa kin kusa mutuwa kice A’a . Wacce aka kira da NANA ce tace , Ni nasan babu mai shiga harka na sai ALHAMU , gimtse fuskarsa yayi tare da fadin A’a fah tsohuwa Sunana ARHAM (kind), kidena cemun ALHANU koh ALHAMU kk cewa ma “I don’t know” ya fada tare da zama kan kujera 2 sitter . Kyakkyawa ne sosae idan nace sosae Ina nufin kwarai , chocolate color ne yanada hanci bakinsa very small, ya tara qasumba ba sosae ba ,yanada lulu eyes masu kyau yanada tsayi , gashin kansa har baya , sanye yake da qananan kaya da talkami qirar guchii wannan kenan. Juyo da kallonsa yayi kan rabi , da ido yayi mata alamar ta dauke culan dake dauke da kazar. Ai kuwa kamar jira take ta dauki culan zata fice. Keee ina zaki tafi da abun naga zaki fice da culan NANA ta fada. Zan kaishi ciki ne naji kince bake kika ce a kawo miki ba. Yoo ko bani nace a kawo mun ba yana iya dole inci, miqomun abuna tunda bada kudinki aka saya ba ta fada tana turo baki kamar yarinya 😂 Kunjini da tsohuwa tana so tana kaiwa kasuwa 😂💔 Arham dai qumshe dariyar sa yayi tare da miqewa yayi hanyar qofa yana fadin tsohuwa ni nayi gaba watarana kwadayinki saiya kashe ki😂. Toh yayi alhamu saika dawo ka biyo mun da wannan abun da kuke sha mai qanqara din nan ta fada tana kai kaza baki Rabi kuwa baki ta saki tana kallon ikon allah yanxu fah tace bazata ci ba kuma gashi tana ci , hadda kiran ba qudinta bane. Muryan NANA ne ya katseta tana fadin meye kk tasani gaba kina kallo kamar manya Rabi? Anya 😂💔 Rabi dai taga ta kanta 😂💔 bari mu koma Nigeria NIGERIA 🇳🇬 .... papina yana ganku kamar baku lafiya and mamina kamar kinyi kuka LIYANA ta fada tana nufar mahaifiyar tata. Da sauri mami ta goge fuskarta tare da sakin murmushi tana fadin my princess babu komi Fah , kaina ne kawai ke ciwo, papi ne ya karbi zancen tare da fadin Eh headache ne kawai ke damunta yanxu ma nake son kiranki ki kawo mata magani. B’ata face tayi tare da furta Ayyah “word best mom “ babu lpy ta fada a shagwabe , nan take idonta ya cika da hawaye. Da sauri mami ta girgiza mata kai tare da kamo hannunta ta zaunar da ita saman bed din , haba my baby meye na kuka kuma? Ai naji sauki Are you sure mami? LIYANA ta fada. D’aga mata kai mami tayi tare da furta“ NOW STOP crying “ kinji princess? Uhmm kawai ta furta . Papi yana gefen mirror yana share kwallah .kallon irin wannan soyayyar dake tsakanin Uwa da ya’rta yake yaya YANA zataji idan idan aka fada mata halin da mahaifiyarta take ciki? Tashi tayi tana fadin gud night mami and papi cikin sanyi is like kaman bata son barin mamin nata. Tare suka hada baki gurin fadin “gud night princess “ Fita tayi ta koma bedroom nata tana xuwa ta haye bed nata dama already har 9:00 dama tanada lecture gobe kuma bataso ta makara Bacci take son yi but ta kasa sai tunani take miyasa idan taga mami kwana biyun nan gabanta ke faduwa? Badai kamar yau , na yau yafi na kullum yawa. Haka taketa juyi har kusan 12:00 na dare. Mikewa tayi ta shiga toilet ta dauri alwala tare da kabbarta sallah tayi nafila , data gama bata tashi zaune tayi tana roqon allah yasa komi zai faru dasu ya kasance alkhairi. Tana cikin shafa addu’a aka bude qofar bedroom nata . Mamaki ne zallah a face nata waye zai shigo mata bedroom da dare haka, bata gama tinani ba taga mami , cikeda mamaki tace mami? ? Kece a dare haka Eh princess nice “ I can’t sleep “ shiyasa nazo koh in koma? Mami ta fada. Lokaci daya tana rike kanta da cikinta tana furta YANA “ come here come and help ur mother. Da sauri LIYANA tazo tana kama hannunta tana fadin are you okay mami? Har yanxu kankin bai daina ba? Ina papi yake? Tana maganar tana taimaka mata ta zauna akan bed din. Yana bedroom nasa mana mami ta fada cikin dashewar murya da kaji maganar ta kasan she’s in pain 💔 , shiya ce nazo na zauna dake my princess , ina son inji zafin jikinki YANA . Koda yanxu shine zai zama na karshe ta fada tana shafa kan yar tata wadda tuni ta fara kwallah. “ But mami you promised me bazaki qara fadan haka Ba right?” LIYANA ta fada cikin muryar kuka Mami ce tace Sorry princess na daina but promise me one thing Meye shi mami zan miki koda shine last breath ina. Okay inaso ki kasance mai daukar kaddara mai kyau koh marar kyau, a duk inda kike ki kasance mai biyayyah duk da nasan kinada but ki kara, ki kare mutuncinki LIYANA kinji koh? Mami takai karshen zancen tana shafa kan yar tata Gyada mata kai tayi tare da furta insha allah mami Oya let’s sleep sweetheart inji mami. Hayewa bed din tayi tare da mami ta kwanta tare da mahaifiyar ta tah wadda jikinta yayi zafi sosae duk da yana taso ta fadawa papi but mami ta hana. 3:00 na dare Cikin baccin daya dauketa mai mugun dadi ta farka saboda sanyi sanyi asuba daya fara gaba towa, zana ta jawo zata rufe jikinta. Ganin mami ma bata rufa ba yasa ta jawo bedsheet din zata rufeta taji jikinta yayi mugun , bata kawo komi ga ranta ba ta rufe mami tare da rungumeta ta koma bacci. 5:00 am na asuba Tashi tayi domin gabatar da sallah asuba , kallon mami tayi taga tun kwanciyar da tayi dazu data rufeta kamar bata motsa ba, and tana mamakin miyasa mami yau bata tashi prayer ba? Maybe saboda bata samu bacci bane ta fada a ranta Direct wurin mami ta nufa tana fadin mamina is time for prayer hadda dan bubbugata amma koh gizau bata motsa ba. Mu hadu a gobe pls na gaji😂💔 Kuyi sharing Dan allah 🙏😭❤️ Written by Ameeratouh 🙏 [7/19, 6:15 PM] +234 810 666 6520: Rumanah sa’ad kaura Ina godiya sosae 🙏 [7/19, 6:16 PM] +234 810 666 6520: LIYANA EP 10 (SOFTNESS) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://whatsapp.com/channel/0029VadH6ZwADTOMRzzDVg1F/101 BISMILLAHI 16/7/2024 .... jijjigata take yi tana kiran mami ki tashi baccin ya isah haka , ga hawaye duk a face nata, kwasawa tayi da gudu tayi dakin papi, bude handle din da zatayi suka ci karo dashi saura kadan da bigesa LIYANA are you okay??? Papi bai karasa maganar da yake ba YANA ta katsesa tana fadin papi , papi , papi mami bata motsi ta fada lokaci daya tana nuna masa bedroom nata. Bai bari ta karasa ba ya wuce da dan gudunsa yayi dakin yana, da gudu ita ma ta mara masa baya. Bude kofar dakin yayi, yana zuwa kallo daya ya mata ya gane ta rasu amma zuciyarsa bata yarda ba, daukarta yayi tare da fita da ita da gudu yasata a mota , LIYANA ma sauri tayi ta shiga Dan kar ya tafi ya barta, securities din gidan tambayarsa suke alhaji miya faru amma babu wanda ya amsa mawa yaja motar ya fice daga gidan . Yana isa hospital din wasu manya manyan likitoci suka karbeta already nan ne suke duba lafiyarta. Wani room suka shiga da ita tare da fara dubata cikin gaggawa Liyana kam dakyar papi ya riqeta, tana kuka tana fadin dole abarta ta shiga Daqar papi ya samu ya lallasheta ta tsaya ta nutsu aljihunsa ya tab’a yaji ko yazo da phone insa, ai kuwa yazo da ita. Wata number ya shiga kira saida ya kira sau biyu sannan aka dauka. Ana daukar wayar ya fashe da mugun kuka, daga gani har cikin xuciyarsa yake fitowa, kuka ne yake wanda da alama ya jima yanason ya fito sai yanxu ya samu damar fita . Saida ya dauki 10 minutes a haka kamun ya furta ADDAH , ADDAH zaki iya biyo plane zuwa abuja yanxu ? Wata dattijuwar murya ce daga cikin wayar ta furta AMIR, zan iya jurewa ka fadamun allah yayiwa MASOOMA cikawa ne? Kar kayi tunanin komi Amir inada karfin imani, ka fadamun ya’ta ta rasu koh? Ta karashe cikin sanyin murya. ADDAH... I don’t know, I don’t know addah, I’m scare I’m scared to loose her addah, ADDAH MOSOOMA itace rayuwata ita ce dangina banida kowa sai ita she’s all I have papi ya fada lokaci daya yana rushewa da kuka, kuka yake bilhaqqi . Allah sarki💔🥺 nidai ameeetouh nayi tsaye da alqalami na . Rayuwa yanxu babu tabbas In kaine yau to gobe ba kai bane, wlh wlh komi kudinka komi dukiyarka allah na iya jarabtar ka ta wani abu, kodai rashin lafiyar da kudinka bazasu maka maganinta ba, koh kuma mutuwa, koh kuma Allah ya dora maka son abunda kudinka da kyauka bazasu samar maka ba. Allah sa muga ma da duniya lafiya. Ameeratouh ❤️ .... saida ya dauki minti 30 a gurin har saida addah ta tsinke wayar da kanta. Wata nurse ce tazo zata wuce ta gansa. Please sir are you the one that come with patient with liver/ kidney problem? Nurse din ta fada Gyada mata kai yayi tare da furta “ yes I am “. Okay sir doctor want to see u in his office nurse in ta fada. Da sauri ya miqe yana share hawaye wasu na qara fitowa lokaci daya yana furta la’ilaha illah anta-subhanaka inni kuntu minan zalimin , innalillahi wa’inna ilaihi raji’un , maimatawa yake har yakai office din doctor, murda handle din yayi lokaci daya kuma gabansa na faduwa. Assalamu alaikum ya furta murya a dashe, Ur welcome sir inji doctor Kunsan ba kowa ke amsa sallama ba especially wanda ba musulmai ba kai har muslmai ma sunayi, kuma hakan babu kyawo Dan haka a gyara dan allah. Wuri papi ya samu ya zauna yana kallon doctor tare da furta “ doctor I’m hearing you” Shiru doctor yayi na tsawon minti 3 kamanu ya bude baki ya furta, sir I don’t know how you will take ita but, katsesa papi yayi tare da furta Idan ta rasu doctor ka fadamun I can take it weather I like it or not lokacinta yayi. Shiru doctor yayi kamun ya furta I’m sorry to say sir matanka ya rasu. Rumtse ido yayi yanajin xuciyarsa na masa wani irin zafi, addu’a yata maimatawa a ransa har yaji sauki, kamun ya mike tsaye ya kalli doctor ya furta, I wanted to see her Da sauri doctor yace okay let’s go. Fita sukayi tare da doctor din har suka kai room din da aka ajiyeta . A bakin room din yaga LIYANA idonta yayi ja tasha kuka harta gode allah , tana ganinsa ta taso tana fadin. Papi ka musu magana su bari in shiga inga mamina pls I don’t want anything to happen to her pls papi . Zuciyarsa yaji tana kara karyewa 💔, daurewa yayi ya ka’ka’ro murmushi tare da furta. Princess your mom is okay taji sauki yanxu ita ma zanje gani ki vari In shiga in fito. Shiru tayi kamun ta furta Papi toh miyasa bazamu je tare ba. Da sauri ya girgiza mata kai yace mata . NO princess mutum daya zai shiga and kinga idan muka je tare zamu takurata doctor yace karmu takura ta. Shiru tayi lokaci daya kuma tana kallon doctor. Da sauri doctor yace “ yes ma’am “ abunda daddynki ya fada gaskiya ne. Shiru tayi ta koma ta zauna tana tinani anya gaskiya papi ya fada but, tasan kuma papi baya mata karya. Numfashi taja kamun kuma ta furta allah baki lpy mami. PAPI Ya dade tsaye yana kallon gawar matarsa acikin room din lokacin daya aguguwa da yawa suka fado masa a cikin xuciya. Tunani yake lokacin da yazo kasar NIGERIA baisan kowa ba. Bari mu leka labarin papi koda kadan ne abunda kawai yasani shine ya gansa a Nigeria a garin ADAMAWA da wata jaka a hannunsa wadda takardunsa ne na karatu ke ciki sunansa kawai yasani bayan shi baisan komi gameda shi ba, baisan kowa ba haka yata yawo har yasamu wani bawan allah ya bashi guri ya zauna har ya fara fahimtar komi a hankali haka yasamu aiki, ya fara rufawa kansa asiri. Lokaci daya allah ya hadasa da MASOOMA itama yar adamawa ce kuma sunada Hali sosai. anan suke zaune suma,lokaci daya suka fara soyayya har abu yakai ga iyaye, farko iyayenta sunso a fasa saboda ba’a san asalinsa ba, sai daga baya mahaifinta da mahaifiyarta wato ADDAH , suka barsu ganin soyayyar tasu tayi qarfi. Bayan aurensu ne mahaifinta ya rasu ya rage daga ita sai addah , sai qanwarta guda daya, haka rayuwa taci gaba har ya koma abuja da aiki, lokacin kuma arziki ya bunqasa sosae Sunada shekara biyu da aure ya haifo yarta mace wato ( LIYANA) . Tunda ta haifeta bata sake haihuwa ba kuma shima bai damu ba MASOOMA kuma daga baya ta samu wannan ciwon. Mukoma cikin labarin mu .. Dafa kanta yayi tare ta fara yimata addu’a na neman rahama ga ubangiji. Ya dade yana mata addu’a kamun ya kalle face nata da yayi fari sosae, face din nata kaman tana murmushi. Lokaci daya kuma yana tuna maganar su ta jiya. Tace ita bazata kwana a dakin , ita wurin YANA dinta zata je, tanaji ajinta kaman bazata Kai gobe ba, tanaso taji zafin jikin yarta . Lokacin da zata fita a dakinsa saida ta masa kalllon karshe tare da furta ka riqe alqawari AMIR. Insha allah MASOOMA bazan bar amanar ki tayi kukan maraici ba zan kula da ita, allah maki rahama yasa can tafiye miki nan. Papi ya fada tare da kallon doctor yace ku shiryata sai mu wuce gida can ayi mata sutura . Ya fada lokaci daya yana fita Room din. Koda ya fita da LIYANA yaci karo , duk ta fada allah sarki baiwar allah. Murmushi ya kakalo kamun ya furta, Princess maminki ta samu sauki yanxu kije gida ki hado kayan da zata buqata anan kinji? Ba zata iya yin musu da papin nata ba ganin yanayinsa, amma bawai Dan ta yarda da maganar daya fada ba . Maganar papi ya dawo da ita a duniyar tunani . Karki damu na kira BALA yazo ya kaiki gyda masa Kai tayi tare da bin hanyar fita waje. Koda ta fita malan bala ya iso shiga motar tayi sukabi hanyar gida gabanta na

Chapter 2 of 13