Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
driver yace yi hakuri yallabai wallahi na manta da zamu fito ban duba ko akwai mai ba, yanxu kuma ya kare , kuma gashi babu gidan mai saidai in tara abun hawa inje in sayo tunda mun danyi nisa da gurin ba halin in koma a qafa. Okay babu damuwa ammar ya fada yana mai bude motar ya koma gidan baya inda noor take zaune. Kallonta ammar yake gani ta kafe guri daya da ido kaman wacce ke ganin wani. Inda take kallo ammar yabi da kallo. Wata matace riqe da hannun yarta yar qarama akallah zata kai shekara biyu ,Sai kuma wani farin dattijo dake murmushi a gefensu da alamu shine mijin matar . Dawo da kallonsa ammar yayi kan noor dake hawaye harda majina. Cikin dan damuwa ya furta “Minene noor “? Shiru ta masa batace masa ko cikanka ba. Bata dauke idonta a mutanen nan ba har saida taga bacewarsu daga gurin. Ahankali ta goge hawayenta tare da furta. “ nasan kanaso ka tambayeni wa’yancan mutanen ko “? Ta fada tana kallonsa. Ahankali ammar ya furta eh Shiru tayi kamun a hankali ta qara furta “Kuma nasan kana son sanin wacece ni tun ba yau ba kawai nice banbaka fuskan tambaya ba kuma danaga zaka tambaya zanyi saurin kauda zancen “ Hamma ammar kasan wanene wancan mutumen da kaganshi da yarinya? Ta fada tana kallon ammar Gyada mata kai ammar yayi Alamun bai saniba “Shidin mahaifina ne hamma ammar “ Ta fada cikin wane karye zuciya sai kuma ta fashe da kuka. Janyota yayi a jikinsa ya rumgumeta tare da furta “ SHIII banason kuka “ Ya fada yana dan buga bayanta Ya fahimci yarinyar kaman abunda ke damunta wanda sai an bita a sannu domin jin cikakken labarinta, amma yafiso sai hankalinta ya kwanta, saboda cikin idonta yana ganin cewa akwai damuwa shifide can cikin xuciyarta. Haka ammar yayita lallashinta har tayi shiru Haka kowa acikin car din yayi shiru baka jin komi sai ajiyar xuciya da noor keyi Ganin driver din bai dawo ba shine yasa ammar cewa bari su dan taka kar kafarsu tayi tsami, kuma koba komi sai yayi cigiyar wannan mutanen dake hotan nan tunda akwai mutane a gurin . Ahankali yacewa Noor taso mudan motsa kafafun. ABUJA MISALIN KARFE 5:00 AM Ahankali sanyi sanyi dake fitowa na alfijir ke ratsata, har cikin qashinta take jin wannan sanyi. Ahankali tafara bude idonta da suka mata nauyi, da qyar ta samu ta budesu duka. Ahankali tafara bin falon dakin da cat eyes nata “Mamaki takeyi cikin ranta waya kawota falon nan? Tunda ita tasan tun erish da taci tayi bacci a dakinta miya fito da ita kuma” Wani zare ido tayi tare da furta “ kardai da gaske ne abunda nayi mafarki yau “ Ganin tunani bazai kaita ko’ina yasa ta miqe dakyar ta koma dakinta. Dakyar ta samu ta lallaba tayi alwala tafara sallah jin cewa an fara kiran sallah a unguwar tasu. [10/11, 2:36 PM] BABY 😍🥳: LIYANA EP 42 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://chat.whatsapp.com/EQwrrqEY58RIB7ou8jEmJN ‎اَللّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ. ‎"اللهم اجعل هذا العام عامًا مباركًا مليئًا بالخيرات والنعم. اللهم اجعله عامًا تزداد فيه قربتنا إليك وعامًا تتحقق فيه آمالنا وأحلامنا. آمين." Bismillahii 11/10/2024 Akwana atashi babu wuya gurin ubangi gashi abubuwa da yawa sun faru a gidan papi da kuma gurinsu Noor. Daga cikin Abunda ya faru gidan harda isko liyana da yayi yaci mata mutunci yadda baku zato daga karshe kuma yace ya bata kwana uku ta fito da miji, ko kuma wallahi saiya daura mata aure da malan musa . Hankalin liyana ya tashi matuqa inda ta rasa ina zata saka kanta, ta daina ci ta daina sha sai kuka duk ta rame ta zama abun tausayi, har tsirewa taso yi ta tafi gurin DADA ( kakarta) , amma sai farha ta kamata kuma ta fadawa papi shikuma ya qara security a gidan nasa. To mukoma cikin labarin mu. Kwance take saman bed dinta duk ta galabaita kamar wadda tayi sati tana jinya Ahankali take sauke numfashi dakyar kamar wadda keda cutar numfashi Hawayene ke zubowa ga idonta wa’yanda duk suka kunbure suka janxa launi zuwa launin ja. Tunani take yau kwanakin da papi ya bata saura kwana daya takk ya rage, ahankali cikin muryarta data dashe ta furta. “ mami... miyasa kika tafi kika barni? , miyasa kika tafi kika barni cikin kuncin ? Miyasa kika bawa papi amana mami? Ya kasa rike amanarki ? Miyasa bamu tafi dake ba mami? Mamina inason na tafi inda kika tafi saboda banda wani sauran amfani a duniya “ Ta fada tana sakin wani marayan kuka wanda ke fitowa daga can cikin zuciyarta. FARHA Tsaye take tana watsawa yazeed wani kallo na takaici kamar ta kifesa da mari saboda takaicin abunda yazo mata dashi “Nifa mummy bazan yarda fah ke kincika gurinki amma ni kin hanani nawa, wallahi dauke yarinyar nan zanyi in kaita wani guri can inta morar kayata” Yazeed ya fada cikin takaici. Wani killer smile ta sakar masa saboda ta gano yadda zata tafiya da dan nata. Ahankali ta furta “; kabari a daura auren nata tukunna son, kaga da zaran an daura saika je shi gurin malan musan mu ninka masa abunda Amir din ya bashi, kaga kenan dashi aka daura aure amma kai ke muriyar abunka “ Ta fada tana sakin murmushi ganin dan nata ma ya yarda da haka. Miqewa yayi tare da furta gaskiya mummy ke ko cikin mugaye keta daban ce ya fada yana barin farha a gurin Niko nace Innalillahi allah tsare liyana daga wannan zunubin. Zaune malan musa yake sai wasar baki yake yana fadawa malan bala daya bata rai labarin abunda suka tattauna kamar haka “Malan musa inaso ka auri diyata liyana saboda na lura kaine kawai zaka mun wannan taimakon “ Papi ya fada Zare ido malan musa yayi tare da fadin “Minake ji kana fada alhaji, kuma bayan haka ni ina naga kudin yimata hidima? A’a wallah abar wagga magana marar dadi “ Murmushi papi yayi tare da furta “Indai batun ciyarwa ne zana baka abincin da zai isheka shekara, sannan zan baka jarin miliyan bitar “ Wani Dariya malan musa yasaki tare da fadin ayi haka alaji. Murmushi papi yayi tare da juyawa ya koma ciki domin yaga malan musa ya amince. Toh kaji yadda mukayi da alajin malan bala Bata rai malan bala yayi tare da furta “Wallahi bakada kirki musa, kuma wallahi bakasan halacci ba wallahi, duba zaman da mukayi da mahaihiyar yarinyar ga kamun ta rasu shine zakaci amana? To wallahi barin gaya maka ko shi kansa alhajin ganin nakeyi baisan miyake ba, amma kajiraye lokacin da zai dawo normal gidan, inaji ajikina komi ya kusa zuwa daidai” Maln bala na kai karshen maganarsa ya mike yabar malan musa na fadin hassada dai tah ke damunka. Kaduna Kamar yadda na fada abaya abubuwa dayawa sun daga cikin abubuwan hadda rashin dawowarsu noor da ammar kidansu ARHAM , driver kawai ne ya dawo inda yake fadin anan ya barsu yaje ya shawo mai koda ya yagansu wasu sun bisu da gudu, kuma koda ya bisu baiga ko dayansu ba. Ba karamun tashin hankali arham yashiga shida mommy saboda koba komi an zama daya, gashi baida hoton ko dayansu balle ya bada cigar su Auta ma ba’a barta a baya ta damu sosai musamman ammar saboda tafi shiri dashi akan noor ABUJA Wani babban gida ne mai girman gaske sosae, zagaye gidan yake da wasu manya sojoji Sojojin sunkasu kashi uku wasu sanye da uniform din kasar saudia, wasu na Nigeria 🇳🇬, dayan bansan na wace kasa bane. Kutsa kaina cikin gidan nayi har can cikin bedrooms in gidan Sanye yake cikin shigarsa riga da wando qananan kaya, gashin kansa daya sha gyara ya saki har baya , juyo face nashi daya qara haske yayi. Nikam nace miya kawo MUHAMMAD nan Nigeria 😂 fans kunji fah Ahankali ya sauko zuwa qasan falon yana magana da yar hausarsa wadda bai iyaba sosai “Uhmm ku ajiyesa a gurinku sai randa nake buqatarsa “ya furta cikin wata cool voice nasa. Katse wayar yayi tare da zauna saman wata kukera one sitter maybe akwai wanda yake jira. Kamar minutes 5 saiga wani qaton mutum yana nufo inda yake tare da wasu mutum biyu Morning sir jibgegen mutum din ya fada Batare daya kallesa ba yayi masa nuni da kujera Zaunawa mutumen yayi kamun ya daga kai ya kalli wanda yazo dasu AMMAR ne da NOOR tsaye suna kallon qaton mutumen, shikuma ammar ya kafe MUHAMMAD da ido ganin kamar ya taba ganin face din Itama noor juyowa tayi tana kallon MUHAMMAD din, ganin tayi ya mata kama da ammar din, saidai wannan tsoro ma yake bata ganin fuskarsa babu rahama duk da shima ammar din ba dariya yake sosae va amma gwara ammar da wannan. Nasan fans zaku tambayeni ya akayi ammar da noor suka zo nan to nima bansaniba 😂 MUHAMMAD kuwa duk da yaji idanu akansa bai saka ya dago kansa ba yaciga da abunda suke. Kuzo ku zauna waton mutumen ya fada cikin hausarsa ta koyo Zaunawa sukayi a qasa, hannunsu sarke dana juna Noor ji takea kamar ta kwasa da gudu dan tsoro. “What’s your name?” Katon mutumen ya fada. Ahankali ammar ya furta AMMAR A JALAL Da sauri jibgegen ya kalli ammar bama shikadai ba harda MUHAMMAD saida ya kalli ammar Kallon da yahaddasa masa faduwar gaba da mamaki ganin fuskar mahaifinsa sak da wannan yaron. Kallon ammar yakeyi tun daga sama har qasa. Ahankali idonsa ya sauka ga hannun ammar mai dauke da zobe. Wani irin miqewa yayi tsaye har saida yaronsa ya furta “Everything okay sir “ Ko tankasa baiyi ba ya nufi gurin ammar ya durqusa, hannun ammar wanda keda zobe ya kama tare da karo nasa shima zoven, irinsu daya sak. Mamaki yakeyi wannan zuben su biyu ne kawai masu irinsa daga shi sai brother insa daya bata yana jariri kuma baya tunanin yana raye . Ahakali wata zuciyar tace masa ai bakuga gawarsa ba koh sacesa akayi. Shikuma ammar kallonsa yake da mamaki ganin zobensu yazo iri daya. MUHAMMAD kuwa domin tabbatar da zarginsa sai yace masa bakada wani suna sai wannan? Shiru ammar yayi tare da furta babu gaskiya saidai watarana baffana na kirana da UKAIL amma idan na tambayesa waye mai wannan suna saiya shareni. Shiru MUHAMMAD yayi domin zarginsa ya tabbata amma yanason tabbatar wa. Nagaji wallahi😂💔 [11/3, 7:51 PM] BABY 😍🥳: LIYANA EP 43 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://chat.whatsapp.com/EQwrrqEY58RIB7ou8jEmJN ‎اَللّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ. ‎"اللهم اجعل هذا العام عامًا مباركًا مليئًا بالخيرات والنعم. اللهم اجعله عامًا تزداد فيه قربتنا إليك وعامًا تتحقق فيه آمالنا وأحلامنا. آمين." Bismillahii 12/10/2024 .. shiru Muh’d yayi kamar mai nazarin wani abu. Ya dauki kamar 5 minutes kamun ahankali ya furta “Yanxu ina baffan yake?” Muh’d ya fada Shiru ammar yayi idonsa ya cika da kwallah Ahankali ya furta. “Sun kashe shi “ Zare ido Muh’d yayi cikin xuciyarsa yana furta “Shidin ma basu kyalesa ba? Har yanxu suna bibiyar rayuwar da basuda tabbaci shi din ne “ Ajiyar zuciya ya sauke tare da furta Bani labarin abunda ya faru . Ya fada a takaice Shiru ammar yayi yana nazarin , baisan saboda mi yake jin cewa ya yarda dashi ba, duk dashi ba maison tambayoyi bane amma baya gajiya dana Wannan Noor dake zaune kusa da ammar duk ta gaji, gashi wani irin tsoron Muh’d take ji take kamar Tayi fitsari a gurin. Ahankali ammar ya bude bakinsa tare da fara bawa Muh’d labarin rayuwarsu shida baffa har rabuwarsa da baffa da kuma kidnapping nashi da akayi, haduwarsa da noor da kuma kidansu Arham. Shiru MUHAMMAD yayi duk ilahirin jikinsa rawa yake, idonsa sun juye daga launin Arsh sun koma ja, jijiyoyin jikinsa duk sun bayyana, xuciyarsa wani tafasa take jin cewa irin rayuwar da dan uwansa yayi cikin qasqanci bayan shi yana rayuwa cikin daula. Ahankali ya furtamorning “ mi mukayi maku zaku rabamu cikin ahlinmu “? Ya fada cikin muryarsa irinta zakuna Kallon ammar yayi tare da fadin ina jakan da baffan naka ya Baka? “Nabarta acan gidan “ Ammar ya fada Mikewa MUHAMMAD yayi tare da furta “Tashi muje “ Miqewa ammar yayi da noor wacce ke rike da hannunsa suka bi bayansa. Wata mota aka bude masa fara ya shiga. Motar daya shiga ammar ya nufa shima yashiga tare da Noor. Kamar jira suke su shiga motar ta tashi tare da jerin guda biyu tare dasu suka bar gidan . KADUNA Gidansu ARHAM Acan gidansu ARHAM kuwa sun waye gari suka ga HAJIYA NANA A GIDANSU yadda kukasan daga sama ta fado tare da hadiman tah Gabadaya gidan ta tashi hankalin kowa harda mommy bata raga mawa ba wai ita ta hana ARHAM ya dawo Jordan, gabadaya ta hana kowa sukuni Zaune ARHAM yake yana kallon nana daketa masifa wai ba sonta yake ba Tsaki yasaki tare da furta “ wlh dai nana kin bani kibar mutum da abunda ya damesa kinqi “ Ya fada yana yamutse fuska saboda shi ba mai son surutu bane. Miqewa yayi tare da bin hanyar fita gidan saboda duk nana ta ishesa. Yana qoqarin bude car dinsa nana tafito tana fadin duk inda zashi saita bisa. Basu gama gardamar da suke ba sukaji horn na car a waje. Da sauri mai gadin gidan ya wangale gate din. Ahankali motocin su ammar ke shigowa gidan har suka qarasa shiga duka. Bin moticin da idanu Arham yayi saboda yasan cewa bana gidansu bane kuma dadynsu ba yau zai dawo daga tafiyarsa ba. Bai gama tunanin zuciyarsa ba saiga ammar ya fito yana sakar masa murmushi , bai gama mamaki ba saiga noor itama. Da sauri arham ya qaraso tare da rungume ammar tare da furta “WHERE HAVE YOU BEEN BROH? Ya fada da muryarsa dake nuna tsantsar farin ciki. “UHMM” Kawai ammar ya furta tare da kallon inda nana take. Itama nana ammar din take kallon ganin kamarsa sakk da danta data baro can gidan kwance, in banda tasan baida yaro mai qananan shekaru zata ce dansa ne. Ahankali ta furta ikon allah. ARHAM ne ya katse shirun ta hanyar furta “Muje ciki broh hankalin mommy duk ya tashi saboda ku, ko ina anduba ba’a ganku ba “ Har sun fara tafiya ammar ya tsaya tare da furta hamma ARHAM muna tare da bako ne fah wanda ya cece mu. “Okay jeka ce ya shigo “; Arham ya fada yana watsawa nana harara tare da furta. Nidai muje ciki kin tsurawa dan mutane ido to kurwarsa kurr Tsaki nana tayi tare da furta kanka akeji, ta fada tare da shegewarta. Tsaye Arham yayi yana jiran ammar. Ammar kuwa cikin dan saurinsa ya isa da motar ya bude Zaune yake ya jingina da kujerar motar, idonsa rufe kamar mai barci. Kallo daya ammar ya masa ya gane idonsa biyu. Ahankali ya furta kashigo mana ka zauna anan. Bude idonsa MUHAMMAD yayi face nashi ya juya gurin face din ammar, ya dauki 3 minutes yana kallon qanen nasa tare da furta muje koh. Ahankali ya fito daga cikin car din ya jero tare da ammar duk da yafi ammar din tsayi, da kagansu kaga jini daya Kunsan jini yadda yake ko baku kama da mutum wallahi da anganku za’a gane, to kamar hakane ta faru da muh’d qaid zance koh ammar ( ukail)😂 Ahankali suka shigo cikin falon wanda ke dauke da mutanen gidan Sallama ammar yayi tare da isa gurin mommy dake washe masa haqora ARHAM ne ya tsurawa MUHAMMAD ido kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa Ahankali ya furta “Zauna pls” Arham ya fada Ahankali Muh’d ya zauna Ya dauki kusan 3 minutes kamun ya dago idonsa ya saukesu kan ammar Aikuwa karaf suka hada ido Lumshe idonsa yayi ya bude ahankali Da alamu ammar yakewa magana Da sauri ammar ya kama hanyar bedroom nasa da aka basa a gidan Ya jima a dakin kamun ahankali ya fito da jakar da baffa ya basa Ahankali idon kowa ya koma kan ammar dake rike da jaka, bai tsaya ko ina ba sai gaban Muh’d. Miqa masa jakar yayi tare da furta gashi Karba MUHAMMAD yayi tare da zazzage jakar a qasa, gabadaya pictures din suka watse a gurin Wani picture ne daya matsa kusa da mommy gurin qafarta. Ahankali ta saka hannunta ta dauki picture din. Wani irin faduwa gabanta yayi ganin fuskar yar uwarta ( NANA) a jikin pictures din ta riqo wani yaro babba dayan kuma jinjiri ne riqe da hannunta . Wani irin miqewa tayi tsaye tare da fara qwalawa nana kira wadda tayi shigewarta bedroom nata wai tayi fushi Kira take yiwa nana bana wasaa ba. ADDAH!! ADDAH!! Haka take fada Cikin wani irin haushi nana ta fito tana fadin “Dan allah Rumaysa ki fita a harkata wai ni warinki ce dazaki rinqa kirana a haka, kindai sanwas ko dana nafarko ya girmeki koh tau, mutum daga zuwansa sai masifa ba’a bari ya huta “ Nana ta fada tana qarasowa gurin kanwar tata. Miqa mata photon mummy tayi tare da furta “Duba ki gani “ Karba nana tayi tare da gyara mazauni glass nata a idonta , saboda dama ba lafiyar ido ya dameta ba. Wani irin zaro ido tayi tana kallon hoton tare da ina kika samu wanga hoto haka Rumaysa? MUHAMMAD dake gefe yana duba wata takarda daya samu acikin kayan, gabadaya hankalinsa nakan takardar duk da muryar nana dayaji saida gabansa ya fadi, saboda ko mutuwa yayi ya dawo zai gane mai wannan muryar, amma haka ya dake ba tare daya dago kansa ba. Mommy ce ta nunawa nana ammar da hannu wanda ke gefen MUHAMMAD Nana juyawar da zatayi tayi ido biyu da MUHAMMAD daya dago idonsa shima Wani irin zabura nana tayi tare da furta “QAIDDDD!!!” Ta fada cikin wani sauti me nuna firgici Ji tayi falon na juya mata, Ahankali tayi luuuuuuu zata fadi Da sauri qaid ya tareta ta fada jikinsa. Kallonta yake ba tare daya furta komi ba ya azata saman 3 sitter dake gurin Ahankali ya furta “RUWA” [11/3, 7:51 PM] BABY 😍🥳: LIYANA EP 44 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://chat.whatsapp.com/EQwrrqEY58RIB7ou8jEmJN ‎اَللّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ. ‎"اللهم اجعل هذا العام عامًا مباركًا مليئًا بالخيرات والنعم. اللهم اجعله عامًا تزداد فيه قربتنا إليك وعامًا تتحقق فيه آمالنا وأحلامنا. آمين." Bismillahii 3/11/2024 Ina godewa allah daya bani dama na sake typing din wannan littafi bayan rashin lpy da nayi, bayan haka kuma wayana ya lalace sai shekaran jiya aka gyara Ina mai baku hakuri dan allah kuyi hukuri ba lafina bane 🤲 Cigaban labarin mu. Ahankali ya furta “Ruwa” Da sauri mommy tayi hanyar kitchen tare da dauko gorar ruwa ta kawowa Qaid. Karba yayi tare da bude gorar ruwan; ahankali ya zuba ruwan a lallausan hannunsa tare da zuba mata a face nata. Wani ajiyar xuciya nana ta saki tare . Ta dauki kusan minti 3 kamun ahankali ta fara bude idonta da take ganin dishi dasu ta saukesu kan qaid. Ahankali ta furta. Kaine dagaske???? Ta fada tana shafa fuskarsa. Ciza lebensa na kasa yayi tare da gyada mata yana dan sakin murmushi. Zaune nana ta tashi tare da kallon kowa cikin falon har idonta ya sauka kan ammar ( UKAIL) Muhmd ta kallah (QAID) tare da furta “Shikuma wancan mai kama da jalal dina fah?” Murmushi ya sakar mata tare da furta “Nana UKAIL dinki ne da suka so su kassara autan UMMI ne “ Ya fada cikin wata murya ta tausayi. Cikin wani irin mamaki nana take kallon ammar kamun ta furta. “ gaskiya allah shike rayawa sannan kuma shike kashewa tun yana jinjiri ya bata amma sai gashi ya bayyana garemu “ Ta fada hawaye na zubo mata a ido. Hannunta ta miqawa ammar tare da furta zonan kaji? Da sauri ammar ya qarasa gurinta domin yanxu koba a fadamasa ba ya gane cewa wa’yannan danginsa ne saidai akwai tamboyoyin dayake so yayi duk da ya fahimci ba shine kawai ya bata cikin dangi ba harda wanda yake tunani yayansa ne. Dago kai nana tayi tare da kallon ARHAM tare da furta. “ kai bakaga abokinka na yarinta ba koda yake ba ganesa zakayi ba “ Kallonta ARHAM yayi shima cikin yar tsokana ya furta “Yo koban ganesa ba ai idona qalau suke basai nasaka gilashi ba “ Bata fuska nana tayi tare da furta “Kaji dashi tunda nidai jikokina sun bayyana ka daina mun walaqanci allah kuma aure dani dakai babu yaxu nayi sabon ango amma dai duk da haka ina dan sonka “ Ta fada tana nuna UKAIL wai shine sabon angon Gabadaya falon dariya suka saki jin abunda nana tace. Nanace ta katse dariya ta hanyar tambayar qaid ya akayi ya bata. Shiru yayi tare da furta “Dogon labari ne nana sai an zauna yanxu akwai aikin da zanje amma ya idan na dawo zan fada miki, and zamanku babu tsaro a nan zan turo a dauke ku” Nana zatayi magana ya katseta ta hanyar furta “Nana kawai kiyi abunda nace kota ina neman rayuwar mu suke” Ya fada tare da miqewa yabi hanyar waje. ABUJA Rana bata karya saida uwar taji kunya Yau wa’adin da papi ya dibarwa liyana ya cika , gidan sai yan shirye shirye suke. Farha kuwa tana dakinta domin yau duniya sabuwa take a gurinta ji take kamar ta mutu da murna Abangaren papi kuwa Gabadaya hankalinsa ya tashi sakamakon rashin malan musa domin kuwa an nemesa sama da qasa ba’a gansa ba gashi limamin masallaci da mutane shi kawai ake jira, kuma babu waliyinsa ko guda. Cikin tashin hankali ya ciro wayarsa tare da kiran farha . Kira daya biyu ta daga wayar tare da furta “Baban Amarya” “Farha akwai matsala fah” papi ya fada Wane matsala kuma amir? Nan papi ya kwashe komi dangane da malan musa ya fadamata. Wani murmushi farha ta saki saboda wani mugunta da taji saboda bataso papi yama sake ganin yar tasa ta bazu duniya ita ina ruwanta. Ahankali ta furta “Kana jina amir?” “Ehhh ina jinki farha “ Papi ya fada “Idan kashiga masallacin yanxu ka miqe kace idan da maison yarka zaka bashi ita kyauta, sadaki ko nawa ne zaka karba kaji koh? Amasa papi ya bata tare da kashe wayar ya nufi masallacin. Kamar yadda farha ta bashi umurni haka yayi. “Gyaran murya ya fara yi tare da sallama ya fara kora masu bayani Gabadaya mutane gurin qus qus suka fara , wasu nacewa qilan ciki gareta ake son laqa masu toh inva ciki gareta ba taya wannnan mai kudin zai bada yarsa sadaka. Kowa dai gurin da abunda yake fada a gurin. Wani tsoho ne a gurin yayi wa liman magana aikuwa liman ya washe baki tare da jin dadi. Ahankali liman yayi gyaran murya kowa ya saurara. Ahankali ya furta “Ga wani bawan allah nan yace yana son nemawa dan auren yarinyar idan ba damuwa uban yarinyar saiya matso kusa “ Papi bai tsaya bin shawara ba ya hada babbar rigarsa ya zauna aka fara shirin aure . Naira duba ashirin 20 mutumen ya ciro ya bawa papi a matsayin sadaki tare da furta “ ina nemawa dana MUHMD QAID ABDUL JALAL yarka “ Saida gaban papi ya fadin jin wannan suna yana son ya tuna amma ya kasa Nan dai papi ya karba yace ya bashi Nan lima ya shaida daurin auren MUHMD QAID DA LIYANA AMIR AKAN SADIKI DUBU ASHIRIN aka shafa fatiha kowa ya watse . Papi aka bari tare da tsohon inda papi yake cemasa yaushe za’azo a dauko amarya. Murmushi dattijon yayi tare da furta “Duk ranar da kuka saka ai sai muzo mu tafi da ita” Dariya papi yayi tare da furta “ atoh ai indai hakane yau bama sai gobe ba sai kuza ku tafi da ita “ Girgiza kai dattijon yayi tare da furta shikenan allah kaimu anjima. Nan dai papi yayi masa kwatance gidansa suka exchanging number suka tsaida maganar cewa anjima zasu dauki amarya. Nikam nace haka ake lamarin dama 😂🤔 Papi kuwa kama hanyar gida yayi wani bangare na xuciyarsa yana farinciki ya cikawa farha burinta Wani bangare kuma sai yaji rashin kyautarwa haka Koda ya isa gida ya shaidawa farha abunda ya faru . Wani dadi taji tare da fadin “Papin liyana barin je in hada mata kayanta “ [11/11, 8:52 PM]

Chapter 11 of 13