Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ambaci sunanta Kamun ta sake magana mutumen ya wuce. Shiru tayi tana tunani, waye zai bata gift har haka, kaman ance ta juya taga wani mutum Dan nesa da ita yana kallonta. Sanye da rigar sanyi fara haka wandonsa ma haka, facing cap dinsa fara itama , gashin kansa ya sauko masa har baya, sai face mask dinsa baqi Qato ne sosai ๐Ÿ˜‚ fah. Shiru tayi tana tunani, kamar an tsikareta da sauri ta fara tafiya gurinsa, Ganin tana matso sa yasa ya fara tafiya irin ta zaratan mazan nan, ita kuwa tana biye dashi. Yana shiga kwana ya bacewa ganinta, ta nemesa har ta gaji, sannan tazo tana jiran bala yazo ya maida ta Bata jima ba kuwa saiga bala yazo daukarta. Toh yobe muke xuwa mu karasa jin mi suka je yi ko kuma katsina mukeyi?๐Ÿ˜‚ Katsina Baffan ammar ne cikin kasuwar katsina, kayansa yake kasawa, kunsan Monday anfi ciniki musamman kayan miya, toshi baffa su yake sayarwa Zaune yake ya kasa kayansa, kasan cewar babu ruwansa da kowa, shidai rayuwarsa kawai yake Wata matace tazo gurinsa tare da furta kabani kayan miya na dubu biya 5k ta fada tare da ciro kudin. Koda take miqo masa kudin ya juya yana hada mata kayan miyar. Yana gama hadawa ya miqo mata ta qarba, Duk cinikin ga da baffa keyi bai daga ido ya kalli matar nan ba, itace dai ta quresa da ido. Ganin baโ€™a basa kudin ba yasa ya dago da idonsa , caraf idonsa ya fada cikin nata. Da sauri taja da baya tare da furta Rashid kaine???? Da sauri ta saki kayan miyan ta arta da gudu . Ni kuwa Ameeratouh dariya ma taban wlh๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” Ganin abunda ya faru yasa baffa ya tattara kayansa ya wuce gida , jikinsa har karkarwa yake ๐Ÿ˜‚ Kuyi hakuri naso nayi typing da yawa amma wlh abubuwa sun mun yawa๐Ÿ™๐Ÿ˜ญ Yanxu wasan ya fara ku cigaba da bina fans din LIYANA โค๏ธ๐Ÿ˜Š [7/25, 10:50 PM] +234 810 666 6520: LIYANA Ep 14 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://whatsapp.com/channel/0029VadH6ZwADTOMRzzDVg1F/101 โ€ŽุงูŽู„ู„ู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุตูŽู„ูู‘ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ูŽู‘ูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑููƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ. โ€Ž"ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ ู‡ุฐุง ุงู„ุนุงู… ุนุงู…ู‹ุง ู…ุจุงุฑูƒู‹ุง ู…ู„ูŠุฆู‹ุง ุจุงู„ุฎูŠุฑุงุช ูˆุงู„ู†ุนู…. ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ู‡ ุนุงู…ู‹ุง ุชุฒุฏุงุฏ ููŠู‡ ู‚ุฑุจุชู†ุง ุฅู„ูŠูƒ ูˆุนุงู…ู‹ุง ุชุชุญู‚ู‚ ููŠู‡ ุขู…ุงู„ู†ุง ูˆุฃุญู„ุงู…ู†ุง. ุขู…ูŠู†." BISMILLAHI 28/72024 ABUJA Koda ta Mln Bala ya sauketa dakinta ta shiga ta ajiye box din sannan ta shiga bath room tayi wanta. Koda ta fito bata nemi papi ba saboda bataga car dinsa da securities dinsa da yake fita dasu ba. Wani jeans ta dauka blue ta saka wanda yayi matuqar fitowa da hips dinta, wanda suka qara girma. Wata T-shirt ta mata ta saka wadda akayi zanen heart gareta ta, daga saman rigan ya matseta saboda tula tulan na shanunta Daga wurin cikinta kuwa ya lafe kamar baโ€™a saka abinci a ciki, haka ya qara fito da shape dinta sosae. Wani ribon ta dauka ta daure gashinta daya saukar mata harga mazaunanta. Koni dake baku labarin nan saida na furta masha allah ta barakallah ๐Ÿ˜‚โค๏ธ Zaunawa tayi saman bed nata ta dauko box din da aka bata dazu tare da fara budewa. Wani box din ta qara gani acikin box din , red ne box din , yanada girma shima wata takarda ta gani aciki an rubuta . This is for you LINA, ajiye takardar tayi tare da fara bude box din , wani agogo tagani golden , agogon yayi kyau sosae, anyisa ne da zallar zinari, a tsakiyar watch din anyi harafin Q aciki Watch din yayi kyau fah yan saurare๐Ÿ˜‚ Wata takardar ta sake gani, saidai wannan yafi wancan girma and wannan hadda flowers pink color. Rubutu ne akan takaddar da akayi shi da yaren turamci wani kuma da wani yare da bansaniba AMMOURA (my darling) โ€œI believe there are some things in life you canโ€™t deny or rationalize, and love is one of them. I know youโ€™ve a lot to ask but Iโ€™m not able to be fully exposed yet. When Iโ€™m comfortable, you will see a different person. Love you Ammoura โค๏ธ Na kusa fara sakin new novel dina (AMMOURA) Ina fatan shima zaku tarbesa? YOBE STATE Suna cikin tafiya sukaga wani bukka, hayaqi na tashi a kai, suwaiba ce tace Farrha zamu cire kayan mu ne a can gurin mu saka jajaye can Gyada mata kai farha tayi tare da tafiya inda suwaiba ta nuna mata Babu kunya babu tsoron allah suka cire kayan su suka saka wani riguna daya fito da siffofin jikinsu. Saida suka gama sannan suka nufe bukkar. Zaune yake cikin bukkar tsirara haihuwar uwarsa , baqi ne tilin kamar bakin gawayi, bakinsa kamar duburar jaki, idonsa jajir dasu Suna shigowa suka samu wuri suka zauna. Kallonsu yayi tare da sakin wata mahaukaciya dariya kamar kukan jaki koh dadi babu Saida yagama dariyarsa kamun ya kalli farha Ya dau lokaci yana kallonta kamun ya furta Nasan mike tafe dake , akan Amir ne koh? Gyada masa kai tayi tare da furta ehhh ehh malan. Tsawa ya daka mata da yayi sanadiyar sawa farha ta dashi zata ruga suwaiba ta rike ta Nikuma Ameeratouh nace tsawar mutum ta firgitata balle kuma azabar allah , toh allah kasa mu cika da imani, allah ka tsaremu da aikata shirka amin๐Ÿ™ Zaunar da ita suwaiba tayi tare da furta mi kike yi haka farha? Farha bata bayar da amsar ba boka yace Ke suwaiba kinsan tsarin gurin nan miyasa baki fada mata ba ? Suwaiba zatayi magana ya daga mata hannu tare da furta Bana buqatar jin komi ya isah . Yana gama fada ya jiyo zuwa ga farha yace Kinaso ya aureki nan da sati biyu koh? Gyada masa kai tayi a tsorace tace eh. Kallonta ya qara yi sama da qasa kamun yace Buqatar ki zata biya amma kuma, daga karshe wasu aguguwa zasu biyo baya ta sanadiyar yar shi Kuma inada sharadi baโ€™a biyan mu aiki sai komi ya kammala , kuma duk abunda muka buqata zaโ€™a bamu shi ba jayayyah Da sauri tace boka indai zan samu AMIR komi zan iya bayarwa Kallonta boka yayi tare da sheqewa da dariya, dariya yake son ransa sai can kuma ya bace batt Suwaiba ce ta kalli farha data firgice tace kinga tashi mubar gurin nan Wannan kenan JORDAN ๐Ÿ‡ฏ๐Ÿ‡ด GIMBIYA AYAANA ce zaune ta aza kafa daya akan daya Wani guri take kallo da alama ta lula duniyar tunani, ta jima a haka kamun jakadiya ta katse mata tunani Sannun dai ranki ya dade jakadiya ta fada . Kallonta Gimbiya tayi tare da furta yauwa jakadiya, Barham din ya iso ne jakadiya? Eh ranki shi dade ya qaraso tun daxu yazo yana daqin sirri yana jiranki . Jakadiya ta furta Da sauri GIMBIYA AYYANA ta mike tare da furta muje koh? Da sauri jakadiya ta miqe tare da bin uwar gijiyar tata. Sunyi tafiya mai nisa kamun sukai wani Dan corido. Saida jakadiya ta leqa ko ina bataga mutum ba kamun tace ranki ya dade muje daga ciki babu kowa. Da sauri suka shige gurin, nan ma saida sukayi tafiya mai nisa kamun sukai wata qofa da akayita da karafuna naji da qarfi. Wasu Numbers ta saka qofar ta bude kamun ta shiga daga ciki . Wani mutum na hango sanye da kaya baqaqe fuskarsa a rufe koh idonsa baka gani . Suna isa garesa ta furta barham........ Mu hadu daku a gobe pls Kuyi hkr jiya banyi posting ba, kunsan harkar karasu hardai a jamiโ€™a 8:00 to 6:00 muke shiyasa kuke jina shiru amma kuyi hakuri๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™ [7/25, 10:50 PM] +234 810 666 6520: Plz sorry ba'a yi muku posting ba aiki ne ya mata yawa but xuwa anjima za'ayi plz๐Ÿ™๐Ÿ™ [7/25, 10:50 PM] +234 810 666 6520: Dan allah kuyi sharing kuma kuyi like Dan soyayyar ku da ubangijin mu๐Ÿ™โค๏ธ [7/25, 10:50 PM] +234 810 666 6520: Masoyanmu Dan Allah Ku dinga yi muna like shi ze bata dama da qarfin yi muku typing din wani plz [8/7, 6:36 PM] +234 810 666 6520: Makaranta baya barina yimuku posting kuyi hkr pls [8/7, 6:36 PM] +234 810 666 6520: LIYANA EP 15 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://whatsapp.com/channel/0029VadH6ZwADTOMRzzDVg1F/101 โ€ŽุงูŽู„ู„ู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุตูŽู„ูู‘ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ูŽู‘ูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑููƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ. โ€Ž"ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ ู‡ุฐุง ุงู„ุนุงู… ุนุงู…ู‹ุง ู…ุจุงุฑูƒู‹ุง ู…ู„ูŠุฆู‹ุง ุจุงู„ุฎูŠุฑุงุช ูˆุงู„ู†ุนู…. ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ู‡ ุนุงู…ู‹ุง ุชุฒุฏุงุฏ ููŠู‡ ู‚ุฑุจุชู†ุง ุฅู„ูŠูƒ ูˆุนุงู…ู‹ุง ุชุชุญู‚ู‚ ููŠู‡ ุขู…ุงู„ู†ุง ูˆุฃุญู„ุงู…ู†ุง. ุขู…ูŠู†." BISMILLAHI 2/8/2024 .....juyowa wanda aka da barham yayi tare da sadda kanshi qasa alamar girmamawa tare da furta . Ranki ya dade komi na neman jagule mana, wani ya gan mu amma bamu samu nasarar kamasa ba. Dago fuskarta tayi a furgice, nan take idonta ya janza launi zuwa launin ja, gumi ta fara lokaci daya ta zauna a qasa dabas , saida ta dauki lokaci kamun ta furta. Mi hakan ke nufi barham? Asirin da muka dade muna boyewa ne yake son bayyana wai mike faruwa damu ne ta fada lokaci daya kuma tana miqewa tsaye. Wanda ta kira da barham din ne ya bude baki da niyar yin magana ta katse sa tare da furta. Kwana daya na baka barham ka nemo ko waye, idan kuwa ba haka ba kasan sauran, Gimbiya AYAANA bata magana biyu. Tana gama fadin haka ta fara tafiya cikin isah irinta jinin sarauta , da sauri jakadiya ta mara mata baya wannan kenan. Wai mi Gimbiya AYAANA ke boyewa, kodai tanada alaqa da YUMNA dake rufe a kurkuku, Yaya GIMBIYA fateema zata ji idan taji yarta tana bin maza, yaya nana zata dauki abun? Ku biyoni nida alqalamina ๐Ÿ™โค๏ธ MADINA Airport Wasu jerin motoci ne kirar ROLLS-ROYCE masu masifar kyau , wanda idanu bazai iya misalta kyau irin nasu Nayi kokarin ganin na kirga maku yawan cars din amma na kasa , saboda yawan su bazai qirgu ba a idona Motocin sunanan a tsaye kamar akwai wanda suke jira ya sauko daga jirgin amma har yanxu bai fito ba. Ahankali naga ya sako kafarsa wadda take fara soll a matakalan jirgin ahankali yake saukowa cikin taku irin na jaruman maza Wayace a kunnen sa da alamu wayar mai mahimmanci ce Dan qaramin bakinsa ne Ke matsi alamun magana yakeyi Dubo nayi zuwa cycle face nasa, fari ne sosae kaman balarabe, yanada manyan ido , kwayar idon nasa arsh color ne. Yanada kyau sosae irin sosae din nan wanda bazan iya misilta muku ba. Fuskar tasa a daure take tamau kaman bai taba dariya ba . Yanada jiki irin na masu karfin nan. Sanye yake da jallabiya baqa wadda ta qara fito da kyau nasa , takunsa yake irin na karfafan maza da kuma irin wanda sarauta ta ratsa. Da sauri wasu qartin larabawa maza suka nufe sa. Nan take suka zagayesa alamun maybe masu basa Tsaro ne. Kara gimtse fuska yayi cikin xuciyar sa yana ji kamar ya rufe su da duka. Yana kaiwa gurin wata mota wadda tafisu kyau aciki ya dakata ya tsaya. Da sauri daya daga cikin su ya bude masa car din ya shiga. Basu bata lokaci ba suma saura suka shiga tasu suka fara tafiya ahankali har suka bacewa ganina Nikam Ameeratouh da gulma nace ko waye a wannan kasar lallai yanada mahimmanci ๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” Bari mu leka gurin su HAJIYA FARHA mu dawo ๐Ÿ˜‚ KADUNA STATE Zaune take saman kujera ta aza kafa daya kan daya, sanye take da wani danqareren less , ta saka wani uban attach a kanta, kamar ba musulma ba Waya take dannawa alamun wani abu take nema , ta dauki kusan minti 3 uku kamun naga ta kara wayar a kunne Baโ€™afi second 4 ba mai wadda aka kira ta dauka, banji mi akce daga cikin wayar ba naji FARHA ta furta Suwaiba na matsu gobe tayi saboda naji ance amir zai dawo aiki kinga kuwa gobe aikina zai cika kaman yadda boka ya fadamun Daga cikin wayar naji wadda aka kira da suwaiba ta furta. Chass qawata sai kinyi wallahi, nifa na matsu azo ayi abun nan In huta kema ki futa cox mun wahala da yawa. But Taya kika san gobe zai dawo farha? Suwaiba ta fada. Wani murmushi farha tayi kamun ta furta Kin manta boka yace zai karkato da hankalinsa gareni? Ko jiya saida ya kirani amma kuma ya kasa cemun komi sai nice Ke masa surutu tohm anan ne yake fadamun zai dawo aiki gobe . Banji mi suwaiba ta fada ba Sallama farha tayi mata tare da kashe wayar ta miqe ta shiga daki. Ni kuma nace allah sa kar papin liyana ya dawo aiki gobe๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ ABUJA A bangaren papin liyana kuwa abun duniya yasha masa kai ya rasa ina zai saka kansa kwana biyun nan. Liyana kuwa ta damu da halin da mahaifinta ke cika ta kasa hakuri saida ta masa magna . Anan ne yake cemata yana tunanin maminta ne da kuma tafiyar da zaiyi gobe Nan take ta kwantar masa da hakali take fada masa ai kwana daya zaiyi zata iya zama ita kadai. Murmushi papi yayi tare da furta ai nasani YANATA . Turo baki tayi tare da furta papi yau kuma babu princess?? Dariya yayi mata tare da furta qatuwa dake zan cemiki princess yanxu kin girma yarinya. Bata rai liyana tayi tare da yin narai narai da ido alamun kuka Ganin haka yasa papi ya daina dariyar tare da furta sorry princess bazan sake ba kinji my baby? Autar papinta yakai karshen maganar tare da tsokanarta ๐Ÿ˜‚ Zatayi magana papi ya katseta tare da furta gobe kinada school fah tashi kije ki kwanta. Kaman jira take papi yayi magana ta mike da sauri tare da furta gud night papi ta fada tare da hayewa step tayi daki Tana shiga daki papi shima ya tashi ya wuce dakinsa Allah sarki liyana bata san ba gaskiya papi ya fada mata ba kawai dai ya fada mata ne Dan hanklainta ya kwanta Papi ya hadu da shairin boka dana farha ๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” [8/7, 6:36 PM] +234 810 666 6520: Inason in buda WhatsApp group na comment toh fans ina mi kuka ce In buda koh kar in buda? Wanda keson In buda danna mun emoji kaman haka โค๏ธ [8/7, 6:36 PM] +234 810 666 6520: LIYANA EP 16 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://whatsapp.com/channel/0029VadH6ZwADTOMRzzDVg1F/101 โ€ŽุงูŽู„ู„ู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุตูŽู„ูู‘ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ูŽู‘ูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑููƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ. โ€Ž"ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ ู‡ุฐุง ุงู„ุนุงู… ุนุงู…ู‹ุง ู…ุจุงุฑูƒู‹ุง ู…ู„ูŠุฆู‹ุง ุจุงู„ุฎูŠุฑุงุช ูˆุงู„ู†ุนู…. ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ู‡ ุนุงู…ู‹ุง ุชุฒุฏุงุฏ ููŠู‡ ู‚ุฑุจุชู†ุง ุฅู„ูŠูƒ ูˆุนุงู…ู‹ุง ุชุชุญู‚ู‚ ููŠู‡ ุขู…ุงู„ู†ุง ูˆุฃุญู„ุงู…ู†ุง. ุขู…ูŠู†." BISMILLAHI 4/8/2024 Abuja Yau takasance monday, ranar da yan makaranta suke zuwa makaranta, masu aiki suma suje gu aikinsu. Kuma yau takasance ranar da papi zaije kaduna gurin dubo aikinsa ya dawo. Masu aikin gidan ne keta hidima, yayinda papi ya zauna ya zubawa guri daya ido alamun hankalinsa ba anan duniya yake ba. Ni kuwa Queen Ameeratouh nace komi yake tunani oho. Ahankali take saukowa daga step din , sauri takeyi amma hakan bai hanata fita cikin natsuwarta ba. Sanye take da atamfa blue color da akayiwa dinkin A-SHAPE . Face nata koh powder babu, lips gloss ne kawai ta saka a dan qaramun bakinta da yayi pink abunsa kamar ta saka Jan lebe. Papinah na shirya LIYANA ta fada tana qoqarin aza Dan siririn blue din mayafinta akan daurin da tayi da hausawa ke kira ture kaga tsiya. Jin shiru baโ€™a amsata ba yasaka ta dago kanta tana kallon direction din inda papi yake zaune. Masha allah gaskiya tayi kyau ba kadan ba fah fans๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” Papi ta qara furtawa , ganin yayi shiru still yana kallon guri daya yasa ta karasa kusa garesa tareda dan bugun kafadunsa lokaci daya kuma ta furta papi.. Da sauri ya dago face nasa lokaci daya kuma yana zare ido. Da sauri ta furta papi โ€œ whatโ€™s wrong with you โ€œ ? Kana lafiya? Ta jefo masa tambaya lokaci daya. Da sauri papi ya furta babu komi my princess , kawai inajin babu dadi In tafi nabarki daga ke sai maids ( masu aiki). Murmushi tayi har saida dimples inta ya lotsa, kamun tace. Papinah donโ€™t worry kaji , kaga ko maids in ai mutane ne and tomorrow zaka dawo koh? Gyada mata kai yayi. Sannan ahankali ya furta tohm princess tashi muje na sauke ki school sai nima na wuce koh? Da sauri ta miqe tayi hanyar barin falor tana fadin papi time is going. Wannan kenan Bari mu leqa wurin baffa ๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” KATSINA Ammar ne zaune akan wata kujera yar tsugunno. Kallon baffa yake dake lullube da wani Dan bargo daya tsufa. Sannu baffa ammar ya furta. Yauwa ammar. Baka fita ? Baffa ya fada. Shiru ammar din yayi kamun can ya furta. Taya zan fita baffa? Bayan bakada lafiya, kuma kaqi fadamun mike damunka . Baffa tun lokacin da ya hadu da wannan matar a kasuwa ya kwanta ciwo inda ammar yayi yayi ya fada masa matsalarsa yace bazai fada ba, shi ba abunda ke damunsa. Toh fans kodai akwai abunda baffa Ke boyewa ammar? Muje zuwa๐Ÿ˜Š Zaune baffa ya tashi tare da yaye bargon da yayi lullubi dashi. Ya jima a haka kamun ahankali ya furta. Ammar.. da sauri ammar din ya dago face nasa saboda jin yadda baffa ya kira sunansa. Ammar nasan tunda ta ganni nasan komi ya kusa zuwa karshe, banso hakan ta faru ba har saina nuna maka kai asalin wanene kai. Baffa ya fada tare da ruqo hannun ammar din. Da sauri ammar ya furta . Wacece baffa, kuma bayan wannan asalin nawa inada wani asali ne? Ya jefawa baffa tambayar a jejjere. Kallonsa baffa yayi kamun ya saki wani cool murmushi. Ahankali ya furta Ammar ka ajiye tambayarka lokaci zai bayyana maka kai ko wanene. Shiru ammar yayi cikin xuciyarsa yana furta, miyasa baffa ke masa haka? Wani lokacin shi zaiyi magana amma kuma idan ya tambayesa saiya share? Anya ma baffa ba gamo yayi? Ya jefawa kansa tambayar. Katse masa tunani baffa yayi tare da furta lokacin sallah yayi fah ammar tashi ka dauro alwala nima ka taimaka mun nayi. Ahankali ya tashi duk jikinsa yayi sanyi. Wannan kenan muje birnin MADINAโค๏ธ MADINA Babban bedroom ne, mai dauke da qatoton bed wanda aka sakawa bedsheet light blue, komi na dakin light blue ne. Da alama mai dakin yafison color light blue Qarar ruwa ne ke tashi a kusa da bathroom alamun kaman mutum ne aciki. An dauki kusan 30 minutes kamun a kashe ruwan. Bude qofar bathroom din akayi. Sanye yake da towel light blue iya qugunsa, jikinsa sai tsiyaya yake da ruwa alamun yanxu yafito wanka. Jikinsa a murde yake kaman wani Dan dambe, ga wani six packs a cikinsa, ga wasu muscles da yake dashi alamun wannan mutumen qarfi yayi masa yawa Gashin kirjinsa daya jiqe ya kwanta luff gwanin ban shaโ€™awa Babu macen da zata gansa a haka hankalinta bai tashi ba Wani Dan qaramun towel ne a hannunsa yana goge sumar kansa daya jiqe da ruwa. Ya dauki lokaci a haka kamun yaje gaban mirror dankin nasa da yake cike da lotion, da turaruka kaman wata mace . Wani cream ya dauko mai suna BABOR seaCreation wannan lotion din yana daya daga cikin lotion din da sukafi kowane tsada a duniya. Ahankali yake shafa lotion din har ya kammala. Wani body spray ya dauka ya fesawa jikinsa Ahankali ya taka yayi hanyar wani corido, yana kaiwa bakin gurin yaja ya tsaya Hannunsa yakai gurin wani Dan qaramun abu dake maqale da ginin wurin. Nan take qofa ya bude a gurin , Kai tsaye ya shiga cikin gurin . Ya jima a cikin gurin kamun ya fito sanye da wani jallabiya light blue daya karbi jikinsa masha allah Agogonsa yake qoqarin gyarawa karar waya ya fara tashi, baiyi qoqarin barin abunda yakeyi ba har saida wayan ya katse, kamun a sake kiransa Saida aka jira masa masa kira har 3 kamun yaje dauki wayar A hankali ya furta ASSALAMU ALAIKUM cikin wani cool and soft voice Banji mi akace daga cikin wayar ba . Ahankali ya qara furta tohm ABBIH insha allah zanzo . Yana gama fadar haka ya kashe wayar tare da qoqarin barin bedroom din Wannan kenan [8/7, 6:36 PM] +234 810 666 6520: Ga masu so shiga group na comment din novel din gashi sai kuyi joining [8/7, 6:36 PM] +234 810 666 6520: https://chat.whatsapp.com/HsA605rUcncAI9UkmbjocD [8/7, 6:36 PM] +234 810 666 6520: Kuzo gashi nayi maku posting din duk da banyi niya ba๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” [8/7, 6:36 PM] +234 810 666 6520: LIYANA EP 17 (SOFTNESS ) ( LOVE AND ROMANTIC STORY) Written by princess meera Banyarda wani ko wata sun juyamun littafi ba duk wadda tayi haka ita da allah https://whatsapp.com/channel/0029VadH6ZwADTOMRzzDVg1F/101 โ€ŽุงูŽู„ู„ู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุตูŽู„ูู‘ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ูŽู‘ูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑููƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ูŽู‘ูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ. โ€Ž"ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ ู‡ุฐุง ุงู„ุนุงู… ุนุงู…ู‹ุง ู…ุจุงุฑูƒู‹ุง ู…ู„ูŠุฆู‹ุง ุจุงู„ุฎูŠุฑุงุช ูˆุงู„ู†ุนู…. ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ู‡ ุนุงู…ู‹ุง ุชุฒุฏุงุฏ ููŠู‡ ู‚ุฑุจุชู†ุง ุฅู„ูŠูƒ ูˆุนุงู…ู‹ุง ุชุชุญู‚ู‚ ููŠู‡ ุขู…ุงู„ู†ุง ูˆุฃุญู„ุงู…ู†ุง. ุขู…ูŠู†." BISMILLAHI 5/8/2024 ..Ahankali yake taka step din saukowa daga dakin nasa kaman bayaso . Tafiya ce irinta wani bijimin zaki , tafiya yake ahankali amma idan mutum na binsa abaya zaiyi taku biyu kamun yakai garesa duk da mutum idan yagansa zaiga tsantsar izzah da kasaita dake tattare dashi . Ahankali ya ratso cikin babban falorn wanda tsayawa gayin tsaruwarsa bata lokaci ne. Wasu qartin maโ€™aikata ne maza keta aikace aikace, wasu a bakin fita part din , wasu kuma suna goge goge Masu mopping suna sanye ne da uniform farare tass Sukuma na bakin qofar sanye suke da uniform black color Jin kaman motsin mai gidan nasu kuma ga kamshin perfume (turare) dinsa yasa gaba daya suka jera layi , suka tsaya kaman wasu duwatsu Yana sauko qafarsa daga step din yayi daidai da lokacin da duk suka furta. Good morning sir. Suka sake sara masa again alamun girmamawa ga mai gidan nasu. Ko kallon inda suke baiyi ba , bai kuma nuna alamun akwai mutane a gurin ba , ko kuma yaji abunda suka fada Bode masa qofar falorn akayi ya fita daga falorn. Da sauri masu cigaba da aikin suka cigaba alamun basu damu da abunda yayi musu ba alamun sun saba da halinsa. Koda ya fita daga falorn bai zarce koh ina ba sai waje inda motocin da zai fita dasu suke. Babban fili ne sosai dan hadda titi (kwanta) a gidan, da kuma qananan part alamun na masu masa hidima ne Oho nidai bansaniba atoh๐Ÿ˜‚๐Ÿ’” Cars ne masu masifar kyau da aka jera akalla zasu kai guda five. Bude masa daya akayi ya shiga ciki . Kallon driver nasa yayi kamun ahankali ya furta king palace ๐Ÿ‘‘ Wannan kenan ABUJA NILE UNIVERSITY Zaune take tana jiran malan bala yazo daukarta Yau gaba daya bata jin dadi batasan mike damunta ba , tun tafiyar papinta gabanta ke faduwa kaman wani abu zai faru dashi. Ta jima tana tunani a gurin kamun ahankali ta furta Allah ya tsare mun kai papinah, ya dawo dakai gobe lafiya nayi kewarka Bata gama rufe baki ba saiga malan bala ya tsaya domin daukarta Mikewa tayi cikin sanyin jiki ta shiga gidan baya ta zauna. Malan bala ne ya furta, yar babanta kiyi hakuri wallahi uzuri ne ya riqe ni kinji koh? UHMM kawai ta furta bata sake cemasa komi. Sunyi Dan nisa cikin tafiya, Kamar ance liyana ta dubi mirror dinsu taga car nabin bayansu. Kallon car din take cikin mamaki aranta tana furta wannan motan ??? Da sauri tacewa malam bala ya dakata da motar kaman ana bibiyarsu abaya. Aikuwa malan bala ya tsaya domin ganin motar bayansu zata tsaya ko kuwa? Tsayawarsu keda wuya motar dake bibiyarsu ta tsaya . Sun dauki tsawon 5 minutes kamun Bala ya furta Yar babanta ki tsaya In dubo su waye suke bibiyarmu. LIYANA tanaso tace masa ya dakata kar ya fita, amma ina malan bala harya fice. Malam bala kuwa babu tsoro ya nufi motar domin ganin su waye . Bai qarasa ba car din tayi ribos ta fice a guje. Baki malan Bala ya riqe alamun mamaki ๐Ÿค” Saida yayi minti daya kamun ya kama hanya ya koma cikin motar su, hanyar gida yabi direct Abunda ya faru shine koda su LIYANA suka tashi a school taga motar a bakin school din nasu, kuma abunda ya bata mamaki shine Bala driver na zuwa motar ta tashi, and kuma sai gashi taga motar ta biyosu Wannan kenan KATSINA Misalin qarfe

Chapter 4 of 13