hannu yayiwa Bilal Alamar me kakeso?
Cikin fishi Bilal yace "kayimin magana mana inji Latif, kayi hakuri da abinda mayi maka, nayi hakan ne sabida in San wani Abu kuma gashi nasani"
Hawayene yafara sauka a idon Latif da hannu yakuma yiwa Bilal alamar me yake cewa?
Bilal ne yayi zuciya ya koma cikin Office na DPO tareda tambayarshi "meya samu Latif baya min magana kodai baka sanar dashi komai ba?"
DPO ne ya mik'e yace "Latif ya samu matsalar ji da kuma magana"
Bilal yace "ban gane ba,me kake Nufi?"
DPO yace "ina nufin Latif yazama kurma tun lokacin da aka kawoshi nan da kwana biyu, muna zaune sai kawai mukaji ihu daganan bai kara magana ba kuma bayajin komai sai anyi mishi nuni da hannu"
"Okay" Bilal yace yajuya ya tafi.
Yana fita ya nemi Latif sama da k'asa bai Ganshi ba, Motarshi yashiga, yajata zuwa gida su Latif.
Yana zuwa ya tarar da Abba yasa Latif a gaba yana ta kuka, sallama yayi, kafin yashiga d'akin jiki a mace.
Abba ne yace "meya sameshi Bilal? Tunda yadawo baiyi magana ba me sukayi mishi?"
Cikin wata irin murya Wanda take d'auke da bak'in ciki yace "Abba nima basu fad'amin ba, sukace wai kawai suma sunji baya magana"
Abba cikin tsawa yacewa Bilal "Tashi kafitar min a d'aki, banason ko k'ara ganin fuskarka"
Bilal ne yafara bashi hakuri Amma ina wannan karon Abba yaki sauraronshi , Bilal ya tashi ya fice jiki a sanyaye.
Motarshi ya shige ya kwantar da kanshi jikin kujerar, yana tunani, "Allah kafitar dani a cikin wannan k'uncin, ya Allah kabani ikon jure duk wani Abu dayake faruwa dani"
Kunna motar yayi yafara tuk'i a hankali, waya naga ya d'auko yakira Sabir yace "Sabir Dan Allah ko kasan gidansu Minal?"
Sabir yace "Eh a bayan kasuwa yake".
Katse wayar yayi tareda nufan gidansu Minal, yana zuwa ya tambayi wasu mutane, suka nuna mishi, Godiya yayi yabasu dubu dubu, daidai kofan gidansu Minal yayi parking tareda kiran wani yaro, yace " kai shiga gidannan kace wai ana yiwa Minal magana"
Yaron ne yashiga bai jima ba yafito yace "wai wayene?"
Shiru yad'anyi kafin daga baya yace "kace wai doctor ne yakawo mata maganinta"
Ba jimawa saiga Minal tafito sanye da wani pink na hijabi, fuskarta babu kwalliya Amma tayi kyau sosai, bakinta ne kad'ai ta shafawa lips, tsayawa tayi tana cewa ina kake?
Bilal dayake cikin Mota ne ya sauk'e ajiyar zuciya me nauyi, ya rasa me yake daminshi a 'yan kwanakinnan idan yaga fuskarta said yaji wani sanyi a zuciyarshi, tana cikin tambaya ne taji an rik'o hannunta da Saudi tace "waye ne?"
Bilal ne yace mata "shiiii muje mota nabaki maganin ki".
Cikin mamaki tace " yaya Bilal kasakar min hannu kafin Umma ta tafito"
Baiyi magana ba hannunta kawai yake ja,
Suna zuwa Ya bud'e motar face "shiga"
Cikin tsiwa Minal tace "bazan shiga ba gida zan koma"
Bilal yace "okay so kike in d'auke ki ko?"
Minal tace "Ai ni ba 'yar iska bace"
Bilal yace "OK ni kuma d'an iskane, idan baki shiga ba zan nuna miki halin 'yan iska"
Turo baki tayi tace "ai dama kun saba iskanci da Afrah"
_✔ote & comment_
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
Jiddah S Mapi
Page 23...
*___________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
"Nine nake iskancin?"
Shiru tayi batayi magana ba,
Yace "ok shiga ciki"
Shiga tayi tanata gunguni.
Shima zagayawa yayi yashiga,
Yana shiga ya rufe kofar da key, daganan bai sake cewa komai ba.
Minal ce taji shirun yayi yawa tace "yaya Bilal kayi magana don Umma tana jirana kuma idan na dad'e zata min fad'a"
Bai ce komai ba, sai kawai ya rik'o hannunta, ya d'aura a kirjinshi, tareda cewa "Minal kiji yanda zuciyata take bugawa a duk lokacin dana zauna kusa dake, jiya nayi Missing naki sosai, nakasa bacci sabida banji numfashinki ba, Minal abinda baki sani ba shine duk dare saina rungumeki kafin na iya bacci, Amma jiya na wahala sosai, Minal nasan bakya gani Amma kina ji, ina son koda bazaki gani ba to ki kalli idona yanzu"
Minal taji yanda zuciyarshi take bugawa sosai, abin harya bata tsoro, to Amma abinda yake d'aure mata kai shine irin maganganun dayake mata, Lumshe manyan idanunta tayi, nan gashin idonta yabi ya lafe, lips nata tad'an tab'e kad'an.
Bilal ido yazuba mata yana kallon irin baiwar kyau da Allah ya bata, shi a duniya babu abinda yake birgeshi kamar yaga ta tab'e baki cikin shagwab'a, hannun shi yasa akan lips nata yana zagayawa a hankali.
Da sauri ta juya kanta gefe tareda cewa "yaya Bilal niba 'yar iska bace, ka daina tab'amin jiki"
Bilal yace "Minal nima bad'an iska bane, ni mijinki ne kuma inada ikon tab'a ko ina a jikinki"
Da sauri ta janye hannunta daga kirjinshi tace "dama kasan ni matarka ce kuma kake zargina da fasik'anci? Kuma kake barina na kwana a k'asa? Yaya Bilal ka cuceni, ka wulak'antawa ni, yanzu kuma kazo ka yaudareni? to Allah yafika"
Tafad'a cikin hawaye.
Bilal ne ya juyo da fuskarta ya rike, handkerchief ya d'auko yafara goge mata hawayen, janye kanta tayi tace "bud'emin k'ofa in tafi Umma tana jirana"
yace "Minal ki taimaka muje gida yau ki kwana a gefena ko zan samu nayi bacci"
Cikin k'uluwa da b'acin rai Minal tace "yaya Bilal ka bud'emin k'ofa nace"
"Minal wallahi bazan iya bacci ba idan bakya d'akin"
Hawayene yafara fita a idanunta babu kakkautawa tace "wato inje in kwanta a d'akinka kai kasamu kayi bacci, nikuma ko oho ko? Wai meyasa Ku masu kud'i kuka fiye son kai ne? Meyasa Baku damu da damuwar wani ba? Nasan yaudarata kazo yi, sabida inje gidanku Ku samu abin wulak'antawa? To bazan je ba, nida gidanku har a bada..."
Bilal saurin had'a bakinshi yayi da nata Dan bayason yaji sauran maganar nata da baya mishi dad'i a cikin kunnuwanshi.
Waro ido tayi, tanajin yanda yake shan bakinta kamar yasamu sweet, (kuyi hakuri haka yanayin labarin yake)
mintsininshi tafara, tana dukan bayanshi, Amma me? Bilal yatafi wata duniyar, bayama jinta, Karo na farko daya fara kissing na mace kenan a rayuwarshi.
Saida yaga tayi shiru jikinta ya mutu kafin ya saketa yana mayar da numfashi a hankali, lumshe ido yayi yanajin wani irin kasala daya saukko misshi.
Minal a halin yanzu tsoro ma yake bata, cikin dak'ewa tace
"dama abinda ya kawoka kenan? Kazo kaci mutunci na? Ka nunamin cewar ban kaiba, Bilal mu talakawa ne bamuda wadata Amma kasani munada wadatar zuci Allah ya isa tsakanina dakai...."
Bilal shi yama fita a hayyacinshi, jikinshi ya mutu sosai, bud'e kofar yayi, cikin wata irin murya dashi kanshi baisan yana da ita ba yace "fita"
Minal tace "dole ka koreni tunda kagama abinda kakeso"
Bilal yakara cewa "ki fita nace"
Dama ai ba zama zanyi ba, kuma Allah ya isana....
yace "idan baki fita ba komai zai iya faruwa Minal, karki kara magana a Motarnan, muryarki tana d'agamin hankali"
Minal fita tayi a motar tace "Allah ya isana ban yafe ba"
Rufe kofar yayi, yaja motar da mugun speed yabar unguwar, shi kad'ai yasan me yakeji a jikinshi, idan yakara minti biyu tareda ita komai zai iya faruwa, shiyasa yabar mata Unguwar gaba d'aya.
tsayawa tayi tanajin karar tafiyarshi, hawaye ta goge da bakin hijabinta, tace "yanzu ya zata ni 'yar iska ce, shiyasa yayi min haka, Amma insha Allahu bazan kara fita ba idan yazo".
Bilal yana zuwa gida yawuce d'akinshi cikin wani irin yanayi, Hajiya babba ce taga yanda yake tafiya kamar zai fad'i, da sauri takira Afrah tace mata.
"Afrah kinsan me? Yanzu naga Bilal naki yazo ya wuce ko sallama baiyi ba, da Alama wannan Makauniyar Ce ta b'ata mishi rai a Asibiti, yanzu abinda za'ayi kije ki ki jiyo meya sameshi"
Afrah tayi farfar da ido tace "da gaske kike Hajiya babba ta?"
Hajiya babba tace "yo dama karya zan miki?"
Da sauri Afrah tace "bari inje d'akin Mommy Nasa Abayarta tukun, don bayason kananan kaya"
Hajiya babba tace "oya jeki"
Afrah d'akin Mommy ta nufa, tana zuwa tace "Mommy Dan Allah kibani Abayarki d'aya mana zanje wajen yaya Bilal nawa ne kuma bayason kananan kaya"
Mommy ce tace "d'auka mana Auta abayar ma saikin tambaya?"
Cikin jin dad'i tace "yawwa nagode my Mom"
'Daukar Abayar tayi tanufi d'akinta tareda yin kwalliya, tasa Abayar babu laifi tayi kyau
Ta nufi d'akin Hajiya babba tana kwarkwasa, tace "Hajiyata Nayi kyau?"
Hajiya babba tace "iye su takwarata anyi kyau, kin ganki kuwa? kamar sarauniya, yau idan Bilal yaganki saiya rud'e, Amma matsalata dake d'ayane, shine wannan jikin naki kamar buhun shinkafa"
Cikin fushi Afrah tace "ai Allah ne ya halicceni haka"
Tana fad'a ta nufi d'akin Bilal knocking tayi.
Bilal a daidai lokacin yagama cire kayanshi ya d'aura towel zai shiga toilet kenan yaji ana knocking.
Cikin b'acin rai yace "waye?"
Ba'ayi magana ba har yanzu kuma ba'a daina knocking ba,
Zuwa yayi ya bud'e kofar, sai kawai yayi arba da Afrah, tsaki yaja yace "what do you want"
Afrah tace "dama yaya naga kashigo ranka a b'ace shine nace ko zan iya taimaka maka?"
Dame zaki taimaka min?
Afrah tace "koma menene yaya, ai shi namiji baya rasa buk'ata"
yace "okay nagode Amma banaso ki kai kasuwa sabida ni jikina a tsarkake yake, kuma bazan b'ata ba, na kiyayeshi ne wa mutum d'aya a duniya, ba kowa bace kuma sai Matata,
Keda kika saba rabarwa maza a titi, kije nabar musu, Nidai bana buk'ata,
Kuma kibi a hankali sabida cutar zamani tayi yawa sosai".
Yana fad'an haka yaja kofar yarufe Gibb, yabar Afrah tsaye.
"Shiga toilet yayi ya kunna shower, ruwa yanabin duk jikinshi, idanunshi a rufe, babu abinda yake tunawa sai moment nashi da ita, yarinyar ta rud'ashi yanda baiyi zato ba, ada idan abokanshi sukace mace zata iya rud'ashi sai yaga kamar karya suke, sai gashi yau yarinya karama wacce bazata wuce 17-18 ba tana Neman hanashi sukuni."
A hankali ya bud'e idanunshi Wanda sukayi jaa, ya sauk'esu akan towel nashi datake d'aurawa idan tayi wanka, tunawa yayi da lokacin da tace badroom, murmushi yayi a hankali ya furta "Badroom"
'Daukan towel d'in yayi ya rungume a jikinshi cikin kasala yace.
"I Miss You"
_✔ote & comment_
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
Jiddah S Mapi
Page 24...
*___________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Saurin buge bakinshi yayi yace "why? Meyasa nakamu tun yanzu, wata zuciyar tace mishi, kai Bilal kadaina yaudarar kanka, akan wannan yarinyar"
'Daura towel d'in yayi tareda sa karamin akanshi, yana gogewa, gaban dressing mirror yaje, ya shafa lotion tareda taje suman kanshi, wardrobe yaje ya d'auko kayan baccin shi, yasa turare me k'amshi ya feshe jikinshi dasu, sallaya ya shimfid'a yayi sallar nafila raka'a biyu, nink'e sallayar yayi, ya hau gado ya kwanta tareda rufa bargo a jikinshi, bacci yakeji sosai sakamakon jiya bai samu yayi ba, idonshi ya lumshe yanason bacci ya d'aukeshi, Amma ina? Duk satar bacci yau yaki satar Bilal, dazaran ya lumshe ido sai ya tuno lokacin da yake kissing nata, hannun shi yasa a sumar kanshi yana yamutsawa, da karfi yace "meyasa yarinyarnan take nema ta hanani sakewa? Me nayi ne? Meyasa nayi kissing nata?, Bilal ka jawa kanka matsifa"
Duk yanda yayi bacci ya d'aukeshi a daren, ya gagara,
Daga karshe ma sauk'a yayi akan gadon ya nufi wardrobe nashi, ya d'auko wani jins da Amless yasa, makullin motarshi ya d'auko yafice a d'akin,
Yana zuwa parking space ya d'au motar yafice a gidan da gudun bala'i, unguwar su Minal kawai ya nufa, yana zuwa ya tsaya a bakin k'ofa yarasa me zai farayi,
Can yaga wani yaro yazo wucewa, yakirashi yace "kashiga gidannan kace mijin Minal yana mata magana"
Yaro yace "to"
Jimm kad'an saiga yaron yace "wai bazata zo ba, idan ka gaji ka tafi"
Shiru Bilal yayi yace "ita tafad'a maka haka?"
Yace "eh"
Bilal yace "kace mata magani ne doctor yabani nakawo mata"
Tafiya yaron yayi bai dad'eba yadawo yace "wai kasahanye maganin tabar maka kuma idan nakara dawowa zata fasamin kai"
Dubu d'aya yaciro yabawa yaron yace "gashi nagode"
Yaron murna yayi yace "nagode"
Bilal kwantar da kanshi yayi jikin sitiyarin motar, zuciyarshi tana mishi ciwo, Yakai Awa biyu ahaka, Saida ya gaji Dan kanshi kafin yaja motar jikinshi duk a mace.
Minal kuma babu abinda takeyi sai tsaki, tace "lalle yaya Bilal ya rainani dayawa, ban tab'a sanin shi jarababbe bane sai yau, wato Dan nabarshi d'azu shine yanzu yadawo ko?"
Umma ce taji Minal tana surutu tace "lafiyarki kuwa Minal ke kad'ai kina surutu"
Minal tace "ba komai Umma Alwala nake".
Afrah kuwa Bilal yana barinta awajen, tayi fuuu sai d'akin Hajiya Babba, da gudu tafad'a akan gadon ta cire gyallen,
Hajiya babba bud'e baki tayi tace " wai Ku wasu irin marar kunyar yarane? Wasan soyayyar zakuyi shine har cikin d'akina zaki shigo da gudu?
Koda shike ai 'yan India ma basa kunyar kakarsu, to ina shi Uban gayyan? Nasan dole mana ya rud'e idan ya ganki, gaki da jiki kuma ai maza sunfi son mace me jiki......Afrah ce ta katseta tace "dallah can Malama kiyiwa mutane shiru, wani India kike magana anan, mutumin daya tsaneni, duk kyaun danayi Saida ya kushe daga karshema yake cemin karuwa me rabawa maza jikinta a titi?
Ai koda wasar soyayyan zaiyi to saidai da wannan makauniyar, kuma nayi rantsuwa babu shi babu zaman lafiya da wannan Makauniyar me kama da jinnu, indai har ina Raye...
_kuyi hakuri yau bazaku samu dayawa ba sabida wani uzuri dayake gabana, ina yinku 'yan makauniya ce fans group, wannan shafin na sadaukar muku shi gaba d'ayanta, musamman masu yimin comment, gaskiya inajin dad'in hakan_
_✔ote & comment_
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
Jiddah S Mapi
Page 25...
*___________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Hajiya babba tace "yanzu nasan inada jika, bari nabaki wani kissa, kinga shi namiji? Idan yace miki bayason irin dressing dakikeyi to wallahi karyane, yana fad'an hakane sabida bayason yabada kanshi awajenki, Amma kinsan me? Kiyi dressing naki da kananan kaya, tananne zakija hankalinshi, musamman idan yana ganin surarki, kin gane?"
Dariya Afrah tayi tace "nagane Hajiya babba ta, kina nufin inyi tasa kananan kaya babu wata matsala kenan?"
Hajiya babba tace "hakan take jikata"
"To hajiya babba yauma zanyi hakan"
Bilal kuma yana zuwa gida ya kwanta a k'asa kan tyles ya lumshe idonshi yana tunanin rayuwa.
Knocking na kofar akayi, cikin kasala yace waye? Ba'ai magana ba yaja tsaki yaci gaba da tunaninshi, knocking aka karayi,
Tashi yayi idon shi har yana rufewa, yaje ya bud'e kofar.
Afrah yayi karo da ita tasha wani Wando daidai gwiwa, rigar jikinta da akwai gara babu,
Duk jikinta ana gani,
Bilal juyawa yayi yace "Auzubillahi minashaid'anirrajim"
Afrah ce tace "yaya akwai Abinda kake b'ukata ne?"
"No bana buk'atar komai"
Shiga cikin d'akin tayi tareda dafa kafad'arshi, tace "yaya awannan lokacin kowani namiji yana tareda matarshi kai meyasa bazakaso kazauna da mace ba?"
Bilal yace "wannan ba abinda ya shafeki bane ba, hasalima ni idan mace tasa kayan da suka fito da surarta bata tab'a birgeni"
"Yaya Bilal nasan kana buk'ata ta sosai, kawai nok'ewa kake"
Cikin tsawa yace "Afrah bana buk'atarki ko kad'an, hasalima 'yar uwata na d'aukeki, inajin bak'in cikin yanda kike rayuwa kamar dabba, koba komai ai ke musulma ce, sannan ina gargad'anki da kifita a d'akin nan"
Cikin tsiwa da rashin kunya Afrah tace "bazan fita ba yaya saidai kayi abinda zakayi"
"Okay bazaki fita ba?"
Afrah tace "Eh"
Bilal bulalar daya siya ya d'auko ya nuna mata k'ofa yace "get out of this Room"
Cikin tsiwa tace "bazan fita ba"
Bulalar ya watsa mata, ihu tayi tace "bazan fita ba ko zaka kasheni"
Dukanta yafarayi kota ina da Bulalar, tana ihu.
Hajiya babba wacce ta sake kunnuwa ne taji ihun Afrah, da gudu tanufi d'akin, tana zuwa taga Bilal yana dukan Afrah kamar shiya haifeta.
Cewa tayi "kai bakada hankaline? Da zaka kama yarinya kayita duka haka?"
Bilal dama haushin Hajiya babba yakeji, yasan duk iya shegen Afrah to da bakin Hajiya babba,
Bulalar ya watsa mata abaya daidai lokacin data k'araso wajensu.
Ihu Hajiya babba tafara tana Sosa bayanta, Bilal cigaba yayi da zabga mata Bulalar.
"Hajiya Babba k'ofar fita ta nufa tana k'ok'arin bud'e kofa, Bilal yabita da gudu yakara zabga mata wani, Sosa bayanta take sosai.
Da karfi tace "Bilalu bani bace, gacan Afrah a bayanka"
Bilal zabga mata Bulalar yake tsakani da Allah, da kyar Hajiya babba ta kwaci kanta, tabud'e kofar, tana fita tafad'i akasa, da rarrafe ta isa d'akinta
Bilal Jan Afrah yayi Wanda duk jikinta yayi tsami, ya wullata waje yarufe kofarshi.
"Hajiya babba tana zuwa d'aki tasa sakata, toilet tanufa da kyar tasamu tayi fitsari, tana sauke nunfashi kamar wacce tayi wasan tsere.
Minal kwance take akan gadonta, tana tunanin Abinda yafaru tsakaninta da Bilal, tunawa tayi da yanda yake fitar da numfashi lokacin dayake kissing nata, yarrr taji ajikinta, " Auzubillahi" shine abinda tafurta.
Lumshe idonta tayi daganan bacci ya d'auketa.
_Asuba tagari_
Daddy ne ya lek'o d'akin Bilal yace "Bilal kasameni a falo"
Bilal yace "to Daddy"
Bayan Bilal yaje falon ne yaga Afrah da Hajiya babba, sai Mommy da Daddy,
Gaishe da Daddy yayi Amma Daddy yaki Amsawa saima tambayar daya bishi da ita na "Bilal meyasa ka daki mahaifiyata?"
Bilal yace "nifa daddy ban daki Hajiya babba ba, Afrah kawai na daka, itama Dan tayimin laifi ne"
"Wani irin laifi tayi maka da zakayi mata wannan dukar, kuma ai koba komai ita kanwarka ce"
Bilal yace "Daddy Afrah tana shigemin sosai, ya za'ayi ta shigomin d'aki da daddare, cikin k'ananan kaya? Kuma tasan matata bata nan, idan wani Abu yafaru laifin wa za'a gani?"
Daddy cikin Mamaki yace "Bilal? Ya akayi kasan tasa kananan kaya? Bacin kai ba gani kake ba"
Bilal jin tambayar da Daddy yamishi saida zuciyarshi tabuga, yarasa wace amsa zai bashi..
_✔ote & Comment_
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
Jiddah S Mapi
Page 26...
*___________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Shiru Bilal yayi dan baisan Amsar dazai bashi ba.
Daddy yakara cewa "Bilal tambayarka fa nake ya akayi kasan kananan kayane ajikinta?"
Bilal yace "Daddy jikina ne yabani, sabida nasan sune kayan datake sawa, maganar duka kuma nasan Afrah kawai nadaka Amma ban tab'a Hajiya babba ba, Daddy inada haukane zan daki Hajiya babba?"
Hajiya babba ce ta harzuk'a tace "yo hauka na nawa kuma? Kana mak'aho ina zaka sani? Yanda kayita zabga min bulala abayana kamar kasamu jaka, tin jiya Addu'a nake yanda kayita zabga min bulala, Allah yasa mala'iku suyita zabgawa Uwarka guduma"......Bilal da ranshi ya b'aci yace " Hajiya babba kada ki kara sa uwata a wannan lamarin, sabida tana kabari batasan meyake faruwa ba"
"Kabaro Bilalu ba Kabariba, ai nima Uwata tana kabari kuma ka zage kayita jibgana"
Bilal bai k'arayi mata magana ba, kawai yatashi yafice a d'akin.
Gidan ma gaba d'aya yafita mishi arai.
Yana shiga d'aki yafad'a akan gado, cikin zuciyarshi yace "yanzu da Minal tana nan koba komai zan kalli fuskarta inji dad'i, to Amma meyasa takemin haka? Wata zuciyar tace mishi "kodai Dan kaki ka kaita India aduba mata idonta ne take wannan fushin?"
Wani tinani yayi kafin yatashi da sauri yanufi wardrobe ya d'auko Riga da wando yasa, makullin motarshi ya d'auka, tareda barin gidan gaba d'aya.
Gudu yake shararawa akan kwalta, bai tsayaba saida ya iso kofarsu Minal, yana zuwa dab yaji jikinshi yayi sanyi, duk zafin daya d'auka.
Yana zaune kusan minti talatin, harya cire ran zata fito, sai kawai yaga Madina tazo wucewa harta shiga gidan, "Alhmdllh" yace sabida yasan dolene tafito yanzu tinda ga kawarta.
Saida yakara kusan minti talatin akalla yayi Awa d'aya zaune awajen, kafin ya hangosu sun fito daga gidan, Madinace agaba sai Minal dake bin bayanta, tana kokarin sa hijabi.
Saida yabari suka wuce motarshi kafin yabud'e yafito.
A hankali yafara bin bayansu, cikin sand'a yasa hannu ya d'auke Minal,
Minal kuma jin an d'agata sama yasa tafara kiran "Madi....kafin tak'ara ya rufe bakinta da hannunshi, saida yakaita motar kafin yasake mata baki.
Minal da duk ta tsorata tace "wayene? Dan Allah kuyi hak'uri ni makauniya ce"
Shiiiiii Bilal yafad'a, "karki sake magana anan idan bahaka ba saina kwakule idonki nakaiwa kare ya cinye"
Minal takara mugun firgita muryar Bilal, tasan zai iya tunda ya tsaneta, jikinta ne yafara Rawa,tace "Dan Allah yaya Bilal kayi hakuri wallahi bazan kara aika maka bak'ar magana ba na tuba, nabi Allah"
Bilal kunna mota yayi yad'au hanya da mugun speed, kamar zai tashi sama.
Minal Addu'a tafara afili tace "Subhanaka inni kuntu minazzalimeen".
_✔ote & comments_
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
Jiddah S Mapi
Page 27...
*___________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Banda Addu'a babu abinda Minal takeyi,
A b'angaren Bilal kuma dariya ma take bashi, bai wuce ko Ina ba sai Airport, parking na motarshi yayi kafin yaja hannunta suka fito, Minal tana ta rok'anshi Dan Allah kar yayi mata komai, ticket ya yanka musu kafin yawuce da ita wajen jirgi, yana zuwa yace kitsaya anan kar kiyi kuskuren fita sabida nan ba gidanku bane kinaji?
Gyad'a kai tayi tace "Dan Allah yaya Bilal karka cutar dani"
Bilal ko kallonta baiyi ba, yawuce yaje ya siyo abinci da drinks.
"Oya kici"
Minal kuka tafara tace "banajin yunwa ka maidani gida kawai"
Bilal yace "ok karki ci kizauna da yunwa, nidai nafita a hakki"
Kuka Minal tafara, kamar anyi mata mutuwa.
Daidai lokacin aka fara announcing cewa jirgi yakusa tashi kowa ya shirya.
Minal kukanta ne ya tsananta jin hardasu jirgi,
Bilal zama yayi a gefenta yana kallon yanda take kuka kamar anyi mata mutuwa, dariya ma abun yabashi, saida yayi daidai son ranshi kafin yariko hannunta yace "haba mana beauty meyasa kike kuka haka? Nifa gidan yankan kai kawai zan kaiki a kasar waje, kinga ai addu'a zakiyi ko?"
Ihu Minal tafara tana bubbuga kafarta a kasa, tace "nashiga Uku na lalace nahad'u da d'an yankan kai, shikenan nawa yakare, Umma ki yafeni na saci kud'inki na siya awara a makaranta"
Bilal dariya yake harda rike ciki, wayarshi yad'auko yafarayi mata video.
Lokacin da jirgi ya tashi, wani irin runguma Minal tayiwa Bilal tsabar tsorata, jingina jikinshi yayi da kujerar shima ya rungumeta sosai ajikinshi.
Minal baccine ya d'auketa.
Bilal tausayi yarinyar take bashi, ganin da tana ganin komai amma yanzu bata ganin komai sai duhu, yanason ya tambayeta meya sameta har idonta ya makance Amma yana ganin kamar bazataji dad'i ba.
6:30Pm daidai suka sauka a kasar India.
Hotel Bilal ya kaisu a kwalkwata.
"Inane nan yaya Bilal?"
"Wajen yankan kai ne, Akwai matsala ne beauty?"
Bata kara magana ba.
Bilal hannunta yaja har zuwa d'akin daya kama musu.
Suna shiga yace "oya cire kayanki kiyi wanka"
"Ni bazanyi wanka ba a wanke nake"
Cikin tsawa Bilal yace "tashi kiyi wanka nace, umarni nabaki ba ra'ayinki na tambaya ba"
Ta tsorata da maganar tashi, dama gata gwanar tsoro, ka kaini toilet d'in tafad'a cikin cikin tsoro.
_✔ote & comments_
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
Jiddah S Mapi
Page 28...
"Janyota jikinshi yayi ganin yanda ta tsorata"
Yace "beauty kidaina janyo ina miki tsawa wallahi banason wani yaji tsorona ko kad'an"
Jikinta rawa yake sosai tunawa datayi, akwai watarana da Madina tace mata idan mutum yana binka a hankali to akwai abinda yake bukata,
Azuciyarta tace "nashiga uku yau na lalace, Ashe da gaske yankani zaiyi? Subhanaka inni kuntu minazzalimin"
Bilal janta yayi zuwa cikin toilet yahad'a mata ruwa me zafi, yace "shiga kiyi wanka ina zuwa"
A tsorace takeyin komai harta gama wankar, Bilal ne yashigo da towel babba da karami, d'aura mata yayi kafin yariko hannunta yakaita cikin d'akin, mai yashafa mata tareda sa mata sleeping dress yace "ki kwanta kihuta kafin gobe muje Mumbai Dan acan me yankan kai yake zama"
Firgita tayi zata tashi Bilal yayi saurin maidata yace "haba beauty ina zaki? Kefa bakya tsoro kin manta lokacin da kike min rashin kunya a Company? Ai dama barinki nayi sai yanzu zan rama"
Minal sai kikkifta idanu take, jin yace zai rama abinda tayi mishi, cikin murya me sanyi tace "yaya Bilal na rantse da Allah Madina ce take zugani Amma bazan kara maka rashin kunya ba Dan Allah kayi hakuri"
Kiyi kwanciyarki nidai bazan hakura ba, yana fad'an haka yashiga toilet d'in shima yayi wanka daganan yayi Alwala yazo yayi sallah raka'a biyu kafin yashafa lotion nashi mai kamshi, taje suman kanshi yayi, shima yasa rigan bacci yahau gadon tareda rungumeta, Minal tanajin ya rungumeta tafara mutsu mutsu Amma yaki sakinta saida ta hakura Dan wuya.
_Asuba tagari_
"Acan gidansu Bilal kuma hankalin Sabir ya tashi sosai ganin Bilal bai kwana agida ba, zuwa d'akin Daddy yayi yace " Daddy banga yaya Bilal ba bai kwana agida ba, ko kasan inda yaje? Hankalina duk ya tashi"
Daddy yaji maganar kamar Almara, "badai Bilal yayi zuciya bane yabar gidan? Nashiga uku ina yakai takaddun gidajenshi da company nashi?"
Cikin firgici yacewa Sabir "kadubashi a garden?"
Sabir yace "babu inda ban dubashi ba Daddy"
Daddy yace "OK kacewa duk mutanen
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 14