Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
laluben inda zatabi, dakyar tasamu kofa tana tafiya tana lalube, dab kofar falo taji karar tafiyar mutum, tsayawa tayi tana tambaya Dan Allah inane kitchen? Kitchen kikeso kisani Makauniya? Bataji dad'in sunan da ake fad'a mata ba tace eh, okay kibi hannun damanki zakiga wata kofa saiki shige ciki kinji?. Minal tace "to nagode" No need cewar Afrah wacce take murmushin muginta. Hanya Minal tad'auka har inda akayi mata kwatance, tana zuwa tabud'e kofar tashige, shiganta keda wuya taji kare yafarayi mata haushi, rud'ewa tayi jikinta yafara rawa har sandarta yafad'i, jin Karen yana shunshunarta yasa tafara ihu tana bubbuga k'ofar amma taji an rufe kofar daga waje, Afrah ce tarufe kofar tanata dariya yau bazan barki ba harsai karennan ya cinyeki mayya kawai, Suna cikin haka motar Daddy tayi horn jin Daddy zai shigo yasa Afrah sake kofar tashige falo dagudu, Minal kuwa ganin kofar yaki bud'uwa yasa tafara tsalle acikin d'akin tana ihu tsakaninta da Allah, Daddy ne yaji ihun yayi yawa sai kawai yabud'e kofar Jin anbud'e kofa yasa Minal fita dagudu mamakine yakama Daddy meya kawota d'akin kare? Cheww wannan wawiya ce wallahi ke...ke ubanme kikeyi ad'akin kare? Minal ko jinshi batayi tsabar tsorata. Tsawa yakuma daka mata keba tambayarki nake ba? Ubanme kike ad'akin kare? Ki..kitchen nake nema, kitchen d'in anfad'a miki nan gidanku ne? Mayya wayasan ko nama kikazo nema. Wallahi ba nama nake nemaba Hajiya babbace tace min in dafa mata shayi....la'ila ha illallahu ke Aljana bakya tsoron Allah, nida nake d'aki tin d'azu ina bacci taya zance miki kibani shayi cewar Hajiya babba, wacce take tsaye abayan kofa tin shigar Daddy. Minal ce tafara rantse rantse wallahi tallahi Daddy itace ta aikeni...ke wayake karya kenan? Uwatace take karyan? Aa gaskiyafa nake fad'a maka...Tass Daddy yawanketa da mari har saida tafad'i akasa, daga yau karki kara rainamin uwa kinaji? Gyad'a kanta tayi cikin hawaye tace to. Bilal ne yaji hayaniyar tayi yawa yana zuwa yaga fuskar Minal tayi jaa ta b'angare d'aya, Ke meya sameki kike kuka? Daddy yayi caraf yace babu abinda yasameta wai karene yabita shine kaji tana kuka, tashi kutafi d'aki yarinya sannu kinji? Cikin mamaki Minal tace Aa dama... Daddy yayi saurin zuwa gefenta ahankali yace "idan kika sake koda wasa Bilal yasan abinda yake faruwa wallahi saina fasa fitar dake kasar India" Jin ance kasar India yasa Minal saurin share idonta tace "eh Bilal karene yabini shine nafad'i, Duk abinda akeyi akan idon Bilal saide yakasa jiyo abinda Daddy yake fad'awa Minal" To Bilal ga hannun matarka riketa kutafi d'aki, hannun Minal yakamo yahad'a Dana Bilal. Jan hannunta Bilal yayi zuwa d'akinshi, suna shiga yakulle kofar da sakata yaja hannunta zuwa kan gado, ajeta yayi tareda cewa "ke zanyi miki wata tambaya idan kika sake kikamin karya saina kwakwule idonki da wuka" Firgita Minal tayi tace wallahi bazanyi maka karyaba Karka kwakwule idona Daddynku zai kaini kasar India agyaramin Dan Allah kayi hakuri.... Naji me Daddy yake fad'a miki d'azu? Babu komai, ke wato karyan zakiyi ko bayan naga duk abinda yafad'a miki, Bama wannan ba tin jiya wannan kayanne ajikinki har wari yake tsabar dattin jikinki, kalli yanda janbaki yab'ata miki fuska, ke wace irin k'azama ce? Ya akayi kasan kayan jiyane ajikina bayan idonka baya gani, kodai karya kake kaiba makaho bane? Eh niba makaho bane pretending nake, mezakiyi? Kuma idan kika sake kika fad'awa mutum cewar niba makaho bane wallahi saina hana akaiki kasar India, Dan Allah kayi hakuri wallahi bazan fad'awa kowa ba, dayafi miki alkhairi, tashi kije kiyi wanka karki cikamin d'aki da tsami, shiru Minal tayi, yasake cewa nace kije kiyi wanka. To ai Ummace takemin wanka, what? Ke wannan katuwar ce ake yiwa wanka? Kinga idan baki tashi kikayi wankarnanba saina saki aruwan daya tafasa. Hawaye Minal tafara zanyi Amma kanunamin toilet d'in, Jan hannunta yayi zuwa toilet d'in ya d'auko towel yawurga mata yace "saura kib'atamin toilet" bai Jira me zatace ba yafita tareda tura mata kofar. Minal tsayawa tayi kamar gunki tana tunanin ta ina zata fara wankan, Zama tayi akan tyles na toilet d'in tafara rusa kuka, nashiga uku Umma bazan iya rayuwa babu keba, Umma kece gatana aduniyarnan, Umma nayi Alkawarin idan aka kaini India idona yabud'u bazan zauna da kowaba sai ke....tana cikin kukan taji muryanshi ke soson da sabulu yana cikin bathtub idan kin gama ki aje awajenki Dan banason datti, Oh ni Minal tinda Allah yahalicceni ban tab'ajin Abu wai bathtub ba ta ina zan fara nema? Tashi tayi tacire kayanta tareda d'aura towel d'in lalube lalule tafara a toilet d'in cikin ikon Allah ta tab'o soso acikin wani k'aton Abu, azuciyarta tace yawwa nasamu badroom d'in (to kuji wai badroom ni turanci irin nasu Walidation s Mapi da Hafsat Ibrahim Khalil d'innan ba ganewa nakeba, lols) kan pompom ta tab'o batayi wani jira ba ta kunna taredasa hannunta taji ko ruwane, ihu ta sake tana tsalle jin ruwa tafasasshe ahannunta bata daina ihunba kuma bata kashe pompom d'inba cikin zuciyarta tace (hande min boni) yau nashiga Uku. Saurin shiga toilet d'in yayi yana tambayarta ke meye haka kikewa mutane ihu? Nalura bayan Makanta harda hauka ke daminki, yanzu me akayi miki? Cikin kuka tace (wala kod'ume) babu komai. Ke gashi kina kuka kuma kicemin (wala kod'ume). Zaki fad'a kosai na tattakaki? Na..na kone ahannuna tafad'a tana murza hannunta. Meya konaki? Ruwan zafine na kunna a badroom shine yakonani, dariya yaso yayi Amma saiya fuske, yace chewww idan baki iya abuba kitambaya mana akoya miki, girman kai da jiji dakai basa tab'a Barin mutum yakoyi abu, Akwai Wanda yakaika girman Kaine mugu kawai duk cikin zuciyarta take maganar, saida yahad'a mata ruwan wanka yad'auketa yajefata a bathtub d'in kafin yafita. Wanka tafara cikin jin dad'in ruwan harta gama tayi ta Neman hanya kafin tafita. Tana zuwa tayita neman man dazata shafa Bata samuba, dahaka tahakura ta kwanta akan gado, tana kwanciya tajita akan wani abu, data tab'a sai taga mai da kaya d'auka tayi tasa kayan tashafa mai tayi kwanciyarta. Duk abinda takeyi akan idon Bilal lumshe idonshi yayi azuciyarshi yace Ashe dagaske MAKAUNIYA CE ai nazata pretending takeyi yanzu inyi mata dukan tsiya, to Amma meya sameta? Ya akayi ta makance? Tab'e baki yayi yace (d'okam damuwa mako) wannan damuwanta ne.yafad'a da yarensu na asali wato fulatanci. "Waya yad'auko tareda kira hello DPO? d'ayan b'angaren akace yes dawa nake magana? Sunana Yusuf d'an kanin baban Latif Wanda kuka rikeshi sabida sharri da akayi mishi, okay meyafaru? DOP zan baka miliyan Biyar karike Latif ko ciwon kai banason yasameshi, idan kuma nasa akayi bincike Nagano kana hukuntashi zan kai karanka koto dasunan ka karb'i cin hanci, sannan banason kowa yasan wannan zancen, idan ka yadda katuromin account numbarka yanzu, miliyan Biyar? Cewar DPO, kana tantama ne? Bilal yafad'a, Aa nayadda zan turo maka insha Allahu yanzu za'a cireshi a cell a office nawama zai rink'a zama...okay Bilal ne ya katse wayarshi tareda cewa zanyi maganinkane kwad'ayayye" โœ”ote comeent & share ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ *MAKAUNIYA CE* ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ By Jiddah S Mapi Page 13... "Tashi yayi yashiga toilet domin yayi wanka, saida yawanke cikin bathtub d'in sosai kafin ya iya wanka aciki, towel ya d'aura babba tareda sa karami akanshi yana gogewa, fitowa yayi yaje gaban mirror yashafa manshi me kamshi tareda taje gashin kanshi Wanda yake bak'i wuluk, agogonshi yad'auka yasa a hannunshi na dama, kafin yajuya zuwa wajen wardrobe, wani dark blue na polo yad'auko da farin wando dogo, jikin aljihun wandon dark blue ne, sawa yayi a hankali, nan asalin kyaunshi na cikakken Fulani ya bayyana, jikin rigan an rubuta Mad Over You da manyan harufa. zuwa wajen mirror yayi yana kallon kanshi a madubi, a zuciyanshi yace " Alhamdulillah ko ba'a fad'amin ba nasan inada kyau, to meyasa zan cuci kaina in Auri Makauniya? Dolene in nemo wacce takeda lafiyan idanu, wacce zataga cikin k'wayan idanuna tafurtamin kalaman soyayya, wacce zansan tana cikin farin ciki ko bak'in ciki, Amma wannan Makauniyar ai bazata iya wad'annan abun ba, Anyway zansan abunyi" yana fad'in haka yad'auko eye glass nashi bak'i babba yamak'a afuskarshi, sandarshi yad'auko tareda Fita a d'akin" Har ya iso bakin kofa yatuna cewa yafad'awa Minal shiba makaho bane "to idan tafad'awa Daddy fa? Kai anya banyi kuskure ba? Wannan yarinyan da karamin bakintan nasan magana baya mata wuya, kai dolene naja mata kunne yafad'a tareda komawa cikin d'akin" Minal kuma bacci yayi mata dad'i cikin baccin take mafarkin an kaita India an gyara mata idonta yayi sauk'i, murmushi tafara najin dad'i. "Wato ta kwanta akan gadona tana bacci harda murmushi ko? Zakici Ubanki yarinya, sandar hannunshi yad'auko yakwala mata a bayanta, afirgice Minal tafarka tana salati, ke? Harkin samu damar yin murmushi akan gadona? Wato baccin dad'i yake miki ko? To bari kiji daga yau idan kika kara kwanciya akan gadona saina kwakule idonki d'aya" Da sauri Minal ta dirko akan gadon, Ash tafad'a cikin Azaba Dan ta bugu da jikin gadon ba wasa. "Kad'an kika gani, nan gaba wuta zan aje akasa kifad'o akai mayya, kuma idan kika sake Daddy yasan cewa niba makaho bane saina kwakule idonki da daddare kina jina?" Cikin rawan jiki Minal tace "eh" "Kitashi ki gyara d'akinnan sannan kicanja bedsheet d'in akwai wani a cikin wardrobe ki shinfid'a, Minal tace "to" Saura nadawo bakiyi ba saikin gane kuranki Miskiniya kawai. "Yana fita Minal takwanta akasa tana kuka, nashiga Uku ni Minal wannan wani irin bak'ar kaddara ne? Dana sani baya maganin komai, ya Ubangiji ina rokanka daka fitar dani a wannan rayuwar, ya Allah ka d'auki raina, awannan lokacin..kukane yakubce mata tasa hannunta ta toshe bakinta dashi, hawayene yakebin hannunta har zuwa wuyanta. kitashi kiyi aikin daya saki Minal karki jawa kanki matsifa cikin zuciyarta take magana, tashi tayi tafara laluben gadon, cikin ikon Allah tasamu tacire bedsheet d'in, d'aukan bedsheet tayi tafara share cikin d'akin dashi, dakyar tagama sharan, tafara Neman inda wardrobe yake, ahankali takeyin komai cikin nutsuwa Har Allah yasa taga bedsheet d'in d'aukowa tayi ta shimfid'a dakyar, Haka tagama gyaran d'akin cikin zuciyarta tace Alhamdulillah nahuta dawannan matsifaffen, koba komai zai barni da idanuna koda bana ganin komai" Kwanciya tayi akasa tana d'an hutawa, muryan Hajiya babba taji afalo tana cewa "ina Makauniyar takene? Yarinya bazaki fito ki zauna a cikin 'yan uwanki ba? Wannan wani irin bakin haline? Zaki fito ko saina zo?" Dasauri Minal tamike tana Cewa "gani Hajiya babba kiyi hakuri gyara nake" Gyaran Ubankine? Akwai gyaran dayafi sada zumunci ne? Fita Minal tayi tana lalub'en kofan falo, ahaka harta iso cikin falon tazauna akasa tana baiwa Hajiya babba hakuri, Ke dallah kimin shiru, tashi zakiyi kishare cikin falon nan sannan ki goge ko ina, kina jina? Minal ce tace "to" Hajiya zanyi....kada kiyima kiga ikon Allah mayya kawai Mara gata kwad'ayayya, tashi kifara maza" "Mikewa Minal tayi tana Neman tsintsiya bata ganiba, Hajiya a taimakamin da tsintsiya, Wani irin tsintsiya? Kiyi da d'an kwalinki, sa'arki ce ni dazakice in nema miki tsintsiya? Mara tarbiyyar banza, Minal cire d'an kwalinta tayi tafara goge cikin d'akin, gashin kanta ne ya bazu yazo mata har fuska, idan ta d'aure gashin saiya kara kuncewa,ga falon yayi mata girma harta gaji tabarshi haka, laluben inda take jin karan TV tafara don ta goge, dakyar tasamu ta goge TV da receiver, Bilal ne yayi sallama a falon tsayawa yayi yana kallon yanda take kokarin gyara gashinta daya zubo mata afuska, azuciyarshi yace " me kuma takeyi afalo? Wannan yarin yan mahaukaciya ce, nida nace tagyara d'akina kuma tazo tana gyaran Babban falo?" Karasawa inda take yayi, yana zuwa yarike gashinta yana ja, "wato ke bakyajin magana ko? Ince ki gyara d'akina kizo kina gyaran falo? Kuma ba d'an kwali akanki? Ko bakisan maza suna shiga falon bane?.....kayi hakuri yaya Bilal Hajiya babba ce tasani gyaran Falon, Shine me? Bata kai tasaki gyaran bane? To barima kiji kina gama gyaran nan kije kibawa flower ruwa kina jina? Tace eh, cikin azaba Dan ita kad'ai tasan irin rik'on da yayiwa gashinta, saketa yayi tayi tangal-tangal tafad'i akasa, Tashi tayi dakyar tafara Neman hanyar Fita, tana fita taci karo da Hafeez Wanda yake tsaye abakin kofa yanajin duk abinda sukayi da Bilal, hannunta yarike tareda janta, tsorata Minal tayi tafara tambaya wayene? Ina zaka kaini? Shiiiii kidaina magana wajen flower zan kaiki, da Minal taji haka sai tayi shiru" "Bayan lambu yakaita yace " zauna" zama tayi shima yazauna agefenta har jikinsu yana gugan juna, d'an matsawa gefe tayi atsorace tace "lafiya kuwa" Haba baby meyasa kika cika tsoro ne?. dafarko dai sunana Hafeez, matsayin kanin Bilal nake agidannan, naji duk yanda kukayi dashi, nasan Bilal baya sonki kuma bazai tab'a sonki ba musamman yanda kike miskiniya, Bilal da mata manya yake harka, masu kud'i da aji ba irinki kamar tsinken tsire ba, bugu da kari gaki Makauniya" Nasani baya sona nima kuma na tsaneshi cewar Minal. idan harkin yadda da abinda zan fad'a miki kuma kika Amince, na rantse da Allah a cikin kwana Uku zan kaiki India agyara idonki tsaf kifara ganin duniya, idan kuma baki yadda ba to wallahi yanzu kika fara ganin wulak'anci a gidannan kai ba gidannan bama ako ina, Da sauri Minal tace menene kakeso kafad'amin Wallahi zanyi Inde zakasa akaini India infara gani" Numfashi Hafeez yaja tareda cewa "kiyimin Alkawarin bazaki fad'awa kowaba" dasauri tace "nayi maka Alkawari" "Okay to idan kin yadda zan rika biya miki bukatanki wanda nasan Bilal bai tab'a yimiki ba, nima kibiyamin nawa bukatan, Minal tace " menene bukatan naka?" Bawani Abu bane domin nasan mafi yawan 'yan mata yanzu Bazawaraye ne, kema inasa ran haka kike ko? Dasauri Minal tamike tareda cewa "kasan me kake fad'a kuwa Hafeez? Baka da hankali ne? Zinafa kake niyan muyi, hawayene yafara bin kumatunta, ina matsayin untynka kake min irin wannan maganar? Minal kin shiga uku, ina rayuwarnan zata kaimu, mutane ba tsoran Allah kowa yazo wajenka daniyan taimako saiya nemi yayi lalata fakai, Hafeez idan haka ka d'aukeni Allah ya isa tsakanina dakai, bazan yafe maka ba mugu azzalimi, don 'yan mata bazawaraye ne shine nima kakeson ka lalatamin rayuwa? Gara na zauna babu idanu da inyi zina".......ke ya isa dalla karki rainamin wayo, an fad'a miki bansan sirrinki bane? Inace ke kike ciyar da gidanku da sunan talle kije kina rabawa gayu jikinki a titi, shine yanzu Dan kina gidanmu kike nema kiyi pretending, to bari naja kunnenki, idan kika fad'awa mutane abunda yafaru tsakaninmu saina saceki insa acire idon naki gaba d'aya, yana fad'in haka yabar wajen, Minal zama tayi akasa tana kuka. Wannan wani irin k'azamin gida kika shigo ne Minal? Ya Allah katsareni ka kareni daga sharrin mutanen gidannan" Bilal saurin juyawa yayi don bayason Hafeez yaganshi azuciyarshi yace "wato soyayya sukeyi shine yajuya mata baya, shiyasa take kuka, nasan Hafeez nasan halinshi akan mata babu macen da zaiyi soyayya da ita wani Abu be shiga tsakaninsu ba, wannan ma Ashe mazinaciya ce, Karuwar gida wacce tafi na waje hatsari, dolene insan abunyi" โœ”ote & comment Jidah S Mapi *ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…* ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ *MAKAUNIYA CE* ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ By Jiddah S Mapi Page 14... *___________________________________* *๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation "Barin wajen yayi da sauri yana sake sake azuciyarshi, lalle yarinyannan tacika Karuwar gida, idan kaganta kamar bazata aikata ba, Lalle saita fad'amin meye a tsakaninsu? Kuma yaushe tafara karuwanci? (Niko nace ina ruwanka malam Bilal tinda ba sonta kake ba)" Minal zuciyarta har bugawa yake tsabar yanda maganar Hafeez ya tsaya mata arai, sandarta tad'auko tafara neman inda flower yake, cikin ikon Allah tasamu tabawa flower ruwa da taimakon mai gadi, godiya tayi mishi takoma cikin gidan d'akin Bilal tanufa danufin ta canja kaya domin na jikinta ya jik'e" "Bilal ne tsaye cikin d'aki sai kai kawo yake yarasa meya hanashi nutsuwa, Sallama Minal tayi Cikin tsawa yace "ke daga ina kike?" Ta tsorata da yanayin maganar A hankali tace "Yaya Bilal kaifa kasani aiki awaje kuma kake tambayana daga ina nake" Okay wato zaki fake da aikin Dana saki ko? Kinje kina karuwancinki kicemin Aiki kike. Niba wannan bama tin yaushe kuka fara harka da Hafeez? Idan kikayimin karya zan cire idonki d'aya yau" Wallahi yaya Bilal yauma tsautsayi ne yahad'ani dashi, babu abinda yake tsakanina dashi.. Karasowa wajenta yayi "zaki fad'amin gaskiya ko kuma" Jada baya tafara don tayi matuk'ar tsorata, "Okay guduma zakiyi ko? Kinsan baki da gaskiya ai dole ki gudu, zaki fad'amin yaushe kika fara karuwanci ko sai nayi abinda nace" "Wallahi yaya Bilal niba karuwa bace d'an uwanka shine yake nemana da iskanci, kuma ban yadda ba" "Zaki fad'i gaskiya ne idan jikinki yagaya miki, cire wannan rigan me kamada tolotolon" yaya Bilal me zakamin wallahi niba 'yar iska bace ka yadda dani. "Zan yadda dakene idan kika fad'amin gaskiya, d'iba da gudu tayi tanason tabar wajen, cikin rashin sa'a taci karo da k'ofar toilet, kanta ne yabugu sosai, baya baya tayi zata fad'i Bilal yana kallonta harta kai kasa, ko motsi bata karayi ba, Tsallakata yayi yaje wajen frij yabud'e, Goran faro me sanyi ya d'auko, yana daga tsaye yafara kwarara mata ruwa, afirgice ta farfad'o daga suman datayi, wallahi yaya Bilal niba karuwa bace.....hannunshi yasa a bakinshi yace shiiii karki kara bud'e bakinki anan, Tashi yayi ya cire belt na wandonshi sannan yace " zaki fad'i gaskiya ko kuma?" "Wallahi yaya Bilal gaskiya nake fad'a maka" Belt d'in yad'auko yafara watsa mata kota ina ajikinta, ihu takeyi tsakaninta da Allah. "Afrah wacce suke zaune a falo itada Hajiya babba tafara jin ihu a d'akin Bilal, da sauri ta mike tana cewa " hajiya ihu fa nakeji a d'akin yaya Bilal " Shine me zakiyi? Cewar hajiya babba, "Zanje naduba meyake faruwa kar wani Abu yasameshi". Amma wallahi Afrah bakida wayo, waya fad'a miki idan anji ihu a d'akin ma'aurata ana zuwa lek'awa? To kul kada ki kuskura koda watarana ki lek'a su, don dazaran kin lek'a to hawan jini ne zai kamaki," Wannan yaron bashida kunya ko kad'an, da ace idonshi abud'e da anyi jarababbe wallahi, cewar hajiya babba" "Afrah jin haka yasa ta koma ta zauna tana kuka, Hajiya babba wallahi yaya Bilal yana cin Amana na agidannan wannan ai cin fuska ne, gaskiya na gaji, kawai asa Daddy yad'aura mana Aure koda bayaso, bazan jira sai wannan Makauniyar ta haihu ba" Kiyi hakuri Afrah ta insha Allahu ke kad'ai zaki zauna da Bilal kinji? To hajiya har yaushe? Kawo kunnenki kiji cewar hajiya babba, Da sauri Afrah ta matso da kunnenta, rad'a hajiya tayi mata, nan suna tafa Afrah tana jin dad'i, tace "hakan za'ay Hajiya babba ta" "Bilal bayan ya gama lakad'awa Minal duka, yashiga toilet yayi Alwala, eye glass nashi yasa, kafin yad'au sandarshi yafita da niyan zuwa masallaci, A falo yatarar dasu Hajiya babba suna hira, Hajiya tana ganinshi tafara habaici, oo ni Salamatu yara yanzu ba kunya ne dasu ba, ace yaro yanzu kagama tunkushe 'yar mutane har tana ihu, kuma babu kunya ka kara yawo acikin gida, wannan jarabar dame tayi kama? Bilal bai gane maganarta ba, shidai ya fahimci taji ihun Minal, to ina ruwanta Dan na duki matata? Allah dai yashirya Matar nan" fita yayi ko kara kallonta baiyi ba, Afrah ce tace "Hajiya babba kidaina surutun nan kinga fa ko kallo baki isheshi ba" idan bai kalleni ba ai yajini ko?". "Daddy da Hafeez ne zaune a cikin d'aki, Hafeez ne yace " Daddy nayi duk abinda kace inyi, kuma naji d'azu har duka yayi mata, yanzu hakama tana kwance a d'aki bata da lafiya" Daddy ne yayi gyaran murya yace "yawwa my son kasan meyasa nake sonka? Sabida basirarka da iya munafinci, na tabbata yanzu zargi ze shiga tsakaninsu, shi zaiyi zargin tana karuwanci ita kuma zatayi zargin yana iskanci, to yanzu abinda za'ayi ni zanje in kaita asibiti, idan ta warke saimu cusa mata k'in Bilal azuciyarta, daganan saimu Nuna mata buk'atarmu, tayi kokari ta sato mana takaddun shi gaba d'aya, daga nan sai kuma me? Sai akashesu gaba d'aya Daddy" dariya Daddy yayi yace "Allah yamaka Albarka my son" Ameen daddy". "Minal tinda uwarta ta haifeta bata tab'a shan wahala irin ta yau ba, jikinta duk yayi tsami, tsanar Bilal ne yashiga zuciyarta bana wasa ba, da kyar tanemo inda sandarta take, da rarrafe ta iso band'aki, ahankali tafara Neman inda bathtub yake, ruwan zafi Dana sanyi ta bud'e, da kyar ta iya shiga cikin bathtub tayi wanka, towel ta lalubo ta d'aura ajikinta tana mejin bak'in cikin Amfani da kayanshi, sallama taji anayi a falo da sauri ta nemi hanyar fita, taje tasa hijabi kafin tanemi hanyar falo, Daddy ne yace " aa sannu Minal, meya faru naga fuskarki a kumbure bakinki kamar ya fashe?" Shiru Minal tayi Dan dazaran tace zatayi magana to kuka ne zai kubce mata, Kinyi shiru Nazo in gaidaku kuma saina ga jikinki a farfashe waya dakeki? Yaya Bilal ne, tafad'a tana kuka, Me kikayi mishi? Dazaiyi miki irin wannan dukan dako agidan yari ba'ayiwa mutum? Banyi mishi komai ba, haba wannan ai mugunta ne shi baya duba nakasar dakike d'auke dashi ne? Wannan ai mugunta ne, kinga jeki shirya yanzu mutafi Asibiti kinji? Minal tace "to nagode Daddy, azuciyarta tace Allah yasa ya shiryu ne ya canja hali" "Da sauri tanemo kayanta tasa ta lalub'o sandarta tayi hanyar falo, a hankali take tafiyarta jikinta duk ba dad'i" daddy ne yaje yarike sandarta yace "ganinan muje ko?" Gyad'a kanta tayi, suka yi hanyar parking space, Hajiya babba ce tafara tafi tana salati, la'ila ha illallahu muhammadarrasulullahi sallallahu alaihi wasallam, oh ni salamatu me nake gani haka? Umaru Kaine kake yiwa wannan k'azamar yarinyar jagora yau? Allah meyasa kanunamin wannan rana? Allah da raina ka d'auka kafin yamma, tafad'a tana kuka, Daddy ne yaje yasa Minal a mota, kafin yazo wajen Hajiya babba, yace "mama idan bakisan meyake faruwa ba kidaina saurin magana, ai nine nayi sanadiyyar dukan da Bilal yayi mata, sabida burinmu yakusan cika, ta hanyar yarinyannan zamu samu duk abinda mukeso, idan yaso daga baya sai insa asaceta ya Auri Afrah, koba hakaba?" Da sauri hajiya babba tace "eh hakane Allah yakiyaye muku hanya, Allah yasa tasamu sauk'i oh ni salamatu dama yarinyar gata kamar karkashi a ruwa, Allah dai yasa karta mutu maka a hanya Mushiga uku" Ameen Mama" "Driver yakira yace kaimu general hospital, Nan sukaje general hospital akayi mata duk abinda yakamata, aka had'a mata magunguna da Allurai, kafin sukaje gida, Bilal daya dawo tin d'azu bega Minal ba kuma hakan be dameshi ba, kwanciya yayi yakira wani a companynshi yake tambaya yaya company, ta d'ayan b'angaren akace "gaskiya yallab'ai company yana Neman b'aci, komai sai rugujewa yake, wannan managern bashida hankali, gashi Latif baya nan, bugu da kari kaima baka nan" Bilal ne yace "karka damu komai yakusa dawowa daidai nan yakashe wayar yana tinani" "Minal ce tayi sallama cikin d'akin, ta gaji sosai Dan haka tacire gyallen da d'an kwalinta tayi wurgi dasu, tareda sandarta, laluben inda gado yake tafara harta samu, tsalle tayi ta d'ale gadon tana cewa " wayyo Allah na nagaji" jitayi tafad'i akan Abu Amma batasan ko menene ba, tayi zaton ko garin sauri ne d'azu tabar wani Abu akan gadon, sharewa tayi kawai tayi kwanciyarta akan Abun, ahaka har baccin gajiya ya d'auketa" "Numfashi Bilal yaja da karfi, jin tayi bacci ajikinshi, ya tattaro sauran nutsuwan daya rage mishi, ya d'agata a hankali ya kwantar da ita agefe, ji yayi jikinta da zafi sosai, hakan yasa ya kara gudun Ac, yaja mata bargo iya kanta kafin yasauka akan gadon, hannunshi yaji ta riko tana cewa "Hafeez karka tafi kafad'a mishi gaskiya, kafad'a mishi abinda yake tsakaninmu, kaji Hafeez? Karufamin Asiri karya kasheni" Da Alama mafarki takeyi, Da karfi Bilal ya kwace hannunshi tunawa dayayi yagansu da Hafeez ga kuma irin maganan dayake Fitowa abakinta, yarufa mata Asiri? Zargina ya tabbata kenan, Afusace ya juya ya d'auketa akan gadon yayi wurgi da ita zuwa kasa, karuwar gida, Shine abinda yafito daga bakinshi" "Tashi tayi afirgice tace Wayyo Allah Aljanu, ke? nine Aljani? Aa kayi hakuri yaya Bilal bada kai nakeba, "Dawa kike idan bani ba? My nawane ad'akin?" Wallahi ba dakai nake ba, "Ke dalla kimin shiru kafin inci Ubanki karuwar banza kawai ballagaza" "Yaya Bilal kadaina fad'amin karuwa niba karuwa bace" "Nafad'a Ke Karuwace, Karuwar ma tagida, wacce take bin kanin mijinta suna lalata, mazan waje basu isheki ba saikin had'a Dana gida, kinyi Asara, dama nasan idonki yariga ya bud'e da kud'i tinda kullum kina wajen talla, barinki ba kud'i riks ne babba, nizan taimaka ina baki sabida karkizo kifara Neman Sabir yaro me hakuri" "Ya isa!!! Yaya Bilal ya isheka haka, niba karuwa bace kaninka shine babban d'an iska, kuma dakake cewa idona ya bushe ai ban kaika bushewan ido ba, Hafeez yafad'a min kana harka da manyan 'yan mata masu kud'i, an fad'a maka ban San sirrinka bane? Dakake cemin

Chapter 5 of 14