Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hajiya ke zaki fara kawo shawara" "Nikuma?" cewar Hajiya babba. "Ke wai Afrah yaushe zakiyi wayo, bazaki koyi yin Abu da kanki ba? Saidai ni in yi?". To bari kiji daga yau idan baki kirkiro Wani munafincin da za'ayi ba wallahi bazan kara sa bakina a lamarinki ba". " haba Hajiya gobe ma zan nemo" "Dayafi miki kam". "Minal taci kuka harta gode Allah, ita ba dukan ne ya dameta ba zarginta dayake ne yake bata haushe, wannan ai zargine" Wanka tayi, ko mai takasa shafawa a jikinta tsabar zafi, haka ta daure ta kwanta a kasa, cikin sanyin tiles, ta rufe jikinta da Hijabinta tana tunani, har bacci b'arawo ya saceta" "Bilal ne yashigo d'akin ya ganta kwance a k'asa, ta takure waje d'aya, Kawar da kanshi yayi gefe yanajin kamar yayi ball da ita ko zaije sauki a ranshi" "A zahiri mutuniyar kirki, Amma a bad'ini tafi kowa iskanci, maimakon taji da wannan nakasar Amma tana kara sab'awa Allah chewwww" Tsallakata yayi yaje ya kwanta yaja bargo. "Minal ce tafarka cikin dare da zazzab'i me zafi, jikinta har rawan sanyi yake, sanyin tiles d'in ne ya dameta har yakawo mata zazzab'i, tashi tayi cikin rawar sanyi tahau gadon tareda janye bargon Bilal ta lullub'a jikinta dashi" _Asuba tagari_ Bilal ne yafara bud'e idonshi jin sanyi yayi mishi yawa, sai ganin Minal yayi ta kwanta a kan gadon tana bacci jikinta lullub'e da bargonshi, "ke? Ke? Tashi Dan Ubanki, Ubanki ne yasiya gadon? Shiru yaji babu amsa, ke ba tambayarki nake ba? Shiru har yanzu ba Amsa, bubbugata yayi, yaji batayi magana ba, zuwa yanzu yad'an fara tsorata, hannunta ya d'aga yaga yafad'i, a tsorace yafara bubbugata yana kiran sunanta, Minal!!! Minal!!! Ke? Ke?, har yanzu shiru" Fita yayi da sauri yaje d'akin Daddy, Sallama yayi a rud'e. Yashiga yace "Daddy Minal ta mutu," what? Minal kuma ta mutu? Wani irin magana kake *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 By Jiddah S Mapi Page 19... *___________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation "Kayi hauka ne? Meya kasheta?" Bilal yace "Daddy ni na kasheta, dukanta nayi, da hannuna" Daddy yace "muje d'akin naku" "Dasauri suka nufi d'akin Bilal, wurin shiga d'akin ne Bilal tsabar rikicewa, yayi tuntub'e da k'ofa, saura kad'an ya fad'i, Daddy ne yayi saurin rikeshi, Bilal kabi a hankali mana, kasan ba gani kake ba, meyasa zakayi sauri? Bilal yace " ba komai muje kawai Daddy" "Suna shiga d'akin, Daddy ya karasa inda Minal take kwance, kallo d'aya yayi mata yagane cewa doguwar suma tayi, yad'an d'aga hannunta yakuma. Sakewa, a hankali ya furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un Bilal meyasa kayi kisan kai?" "Bilal ne ya zauna a kasa jin wani irin jiri dayake Neman kada shi, yace " Daddy tamutu ko?" Daddy ne ya girgiza kanshi tareda cewa "Kwarai kuwa, karo na farko da aka fara kisan kai a Family d'inmu, yanzu abinda za'ayi dolene mukira 'yan sanda su San abinda ake ciki, sabida tsaro, kafin akaita makwancinta" Bilal yace "Daddy 'yan Sanda kuma? Meya kawo kawo 'yan sanda cikin wannan maganar da wuri haka?. Daddy yace " Aa Bilal kiran 'yan sanda shine mafi muhimmanci" dasauri yasa hannu a Aljihu ya kira DPO tareda sanar dashi abinda yafaru, DPO yace "Alhj Ku kaita Asibiti kafin muzo muyi bincike" "Bilal ne ya d'auketa yasata a mota, suka nufi Asibiti, suna isa likitoci sukayi Emergency Room da ita, gwaje gwaje aka fara har suka gano tanada rai, Dogon suma ne tayi sakamakon zazzab'i daya damera" Ruwa aka d'aura mata tareda yi mata Allura" Bilal yakasa zaune yakasa tsaye, zagaye cikin Asibitin yake yi. Azuciyar shi yace "yanzu idan ta mutu ni nakasheta? Ni Bilal nayi kisan kai? Allah kasa ba mutuwa tayi ba" "Yana cikin haka sai ga likitoci sun fito, da gudu Bilal yakarasa wajensu yana tambaya, " doctor ta mutu ko?" Doctor ne yace "no bata mutu ba, Amma tana dab da mutuwa, kai mijinta ne?" Bilal yace "eh ni mijinta ne" Doctor yace "okay biyoni office akwai wata magana da zamuyi" Da sauri suka nufi Office na doctor. Doctor ne yacewa Bilal "zauna mana malam Bilal ka kwantar da hankalinka zata samu lafiya" Bilal yace "doctor ya kake ganin zan samu kwanciyar hankali bayan baka da tabbacin zata Rayu?" Doctor yace "magana nake son muyi dakai, magana kuma me muhimmanci" Bilal ne yasamu waje ya zauna, fuskarshi duk zufa. Doctor yace "Malam Bilal ko zaka iya fad'a mana me matarka taci last kafin faruwar hakan?" Bilal yace "Doctor me ya kawo maganar abunda taci, nidai nasan munyi fad'a da ita kuma na daketa da Belt shine kad'ai abinda nasani" Doctor yace "To a zahirin gaskiya munyi iya gwaje gwajenmu mun gano cewa matarka guba taci, hakan yakawo mata muguwar zazzab'i, anyi amfani da gubar da baza'a gane ba sai likitoci, sabida haka muna buk'atar abinda taci last, zamuyi gwaje gwaje akai" Bilal ne ya mik'e a tsorace yace "GUBA kuma doctor? Okay ina zuwa" Da sauri yafita yabar office d'in yanufi wajen daddy yace "Daddy Inason muje gida yanzu" Daddy yace "komai dai lafiya kam Bilal?" Bilal yace "kaidai muje kawai Daddy" Driver suka d'au hanya" Suna isa gida Bilal yatara duk ma'aikatan gidan da kuma mutanen gidan A babban Falo. Bayan kowa ya zauna ne Bilal yayi gyaran murya yace. "Waye yasawa matata guba cikin Abinci?" Falo yayi tsit babu Wanda yayi magana. Bilal yace "ba tambayarku nake ba? To wallahi idan Baku fad'amin gaskiya ba gaba d'aya yau saina koreku a aiki". " ma'aikatan ne suka fara baiwa Bilal hakuri, dacewa su basu San waya bata abinci da guba ba" Hajiya babbace ta mik'e tace "Kai baka isa ka kori ma'aikatan gidannan ba, sabida ba gidan Ubanka bane" Bilal yamike yace "Hajiya babba ki tsaya a iya matsayinki kada ki kuskura ki kara samin Baki a magana na, kina ji" Daddy ne ya mik'e yace "haba Bilal ya zaka tsaya kana yiwa mahaifiyata tsawa? Okay sabida ba ita ta haifi Babanka ba?" Wa kake tunanin zai baiwa matarka guba? Kasani fa ita makauniya ce zata iya cin komai ba tareda ta sani ba.....Bilal ne ya katseshi da cewa "Daddy Dan ita Makauniya ce sai a cuceta? A iya sanina babu guba a d'akinmu, dolene akwai Wanda yakai mata tasha, kuma saina samo meshi" Bilal yace "daga yanzu na sallami duk wasu ma'aikatan gidannan" Da sauri inna wacce take dafa abinci a gidan ta tashi tace "inada magana" Bilal yace "muna jinki" Inna tace "wallahi yallab'ai gaskiya zan fad'a maka, sabida idan narasa aikin nan ban San ina zan samu wani ba, kuma Babar 'ya'yana da yunwa a can gida kauye" Bilal ne yace "kiyi maganarki muna ji" Inna tace "d'azu ne ina zaune a kitchen shine Hajiya Babba da Afrah suka shigo, suka mik'amin wani Abu acikin farar Leda, suka ce in sawa Minal a cikin abincinta na rana sabida tasa damuwa a ranta bata iya bacci, nikuma ban kawo komai a raina ba saina sa mata, na zata ko maganin bacci ne, saida ta cinye kafin naji Hajiya babba tana cewa yau karshen Makauniya yazo, daganan sai na fara zargin ko dai maganin mutuwa ne, yallab'ai shine iya gaskiyar abinda nasani" "Gaba d'aya Falon aka d'au salati kowa yana Allah wadaran da wannan halin, banda Hajiya babba da Afrah da Daddy da suketa kallon kallo a tsakaninsu" Bilal ne yace "dama ina zargin wani Abu, Amma tunda gaskiya yafito, Hajiya babba da Afrah sunyi yunk'urin kashe matata, to ina me Sanar da mutanen gidannan, nafasa Auren Afrah kuma bazan Auri Afrah ba har abada, m Ke kuma inna zan sallameki da makudan kud'ad'e Wanda zasu isheki keda yaranki, na sallameki a gidannan" Inna ce tafara kuka tana rok'an gafara, "Bilal baiyi magana ba yatashi yafita, daidai bak'in kofa yaji karan motar 'yan Sanda Wanda Daddy yakira su" Juyawa yayi wajen Daddy yace "sai kasan yanda zakuyi da 'yan Sandan da ka kira". _"ina kara Baku hakuri a 'yan kwanakin nan bazan iya typing dayawa ba sabida wasu dalilai nawa"_ _✔ote & Comment_ Jiddah S Mapi *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 By Jiddah S Mapi Page 20... *___________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation "Yana fad'in haka yajuya yabar gidan gaba d'aya, zuciyarshi a cunkushe yarasa me zaiyi yanzu, Asibiti ya nufa wajen Minal" Daddy da duk haushi yake ji yasa ya tashi a tsawace yace "haba Hajiya meyasa zaku baiwa wannan dak'ik'iyar matar guba tasawa Minal a abinci, yanzu baga irinta ba, nasan halin Bilal idan yace zaiyi Abu to babu Wanda ya isa ya sashi, gashi kun jawo yafasa Auren Afrah, wannan ai bala'i ne" Hajiya babbace tace "dakata Umar, karka sake kace zaka d'aura mana dukkan laifi, kai me ze hana ka zuba mata, sai mune zaka baiwa, kuma yanzu kana mana tsawa, ai idan yasan wata to besan wata ba, Dan yaga nayi shiru? To wallahi be isa ba saiya Auri Afrah koda boka koda Malam" Tana gama fad'an haka taja hannun Afrah fuuuuu wacce take ta kuka sai d'aki. Sun bar Daddy tsaye baki bud'e yarasa me yake ciki, sallamar 'yan sanda ne ya katseshi daga tunani, DPO ne yace "Alh munzo muyi bincike akan kisan kan da akayi" Azuciye Daddy yajuya yace "get out from my Room!!!" DPO ne yace "kamar yaya? Akan me zamu Fita? Ai sai munyi binciken da aka turamu" Daddy ne yace "to bata mutu ba, kuyi abinda zakuyi, idan kunga dama Ku bincika har cikin kwalban drinks" Yana fad'in haka yabar musu wajen, cikin jin haushin su Hajiya Babba sun b'ata mishi plan" "Bilal yana zuwa Asibiti, yawuce d'akin da aka kwantar da Minal, yana shiga yaga ansa mata uniform na patients, blue, kanta babu d'ankwali, hakan yasa gashinta ya bazu, akan gadon, fuskarta tayi fayau, idanunta a rufe, karasawa yayi kan gadon da take, d'ankwalinta ya d'auko ya d'ago kanta a hankali, yad'aura mata, a hankali yakara maidata, kura mata ido yayi, yanajin tausayinta a kasan zuciyarshi, doctor ne ya turo kofar yashigo" Doctor yace "Bilal ka samo ruwan sanyi da towel ka goge mata jikinta" Bilal yayi shiru daga baya yace "doctor babu mata ne wad'an da zasuyi mata hakan?" Doctor yace "malam Bilal ita fa matarka ce, me zai hanaka yimata hakan?" Bilal ne yace "okay doctor zanyi mata" "Fita doctor yayi" "Bilal ne yamik'e tareda d'ibo ruwan sanyi acikin wata 'yar roba da farin towel, zuwa inda take yayi, ya zauna, ya rasa ta ina ma zai fara, saida yad'an ja lokaci kafin ya d'agata ya fara cire mata uniform d'in, bayan yacire mata ne yasa towel d'in a ruwa ya fara goge mata jikinta a hankali, yana gamawa ya shafa mata wani lotion me dad'in kamshi, ya mayar mata da kayanta ya kara kwantar da ita, tareda rufeta da bargo" "Mayar da robar yayi da towel d'in, yazo ya zauna kusa da ita yariko hannunta yana murzawa a hankali, tausayinta yakeji har cikin zuciyarshi, cire bargon yayi tareda hawa gadon shima ya kwanta a gefenta, yaja bargon ya rufa musu, a haka har bacci ya d'auke shi" "Doctor ne yashigo d'akin da niyan yimata wasu Allurori, ganin Bilal yayi kwance a kan gadon, dariya yayi, a fili yafurta " Allah ya shiryeka Bilal" "Daddy yau yana cikin bak'in ciki, wayarshi ma ya kashe, Dan bayason damuwa, Yarasa wani shawara zai bawa kanshi, tunawa yayi da Alhaji Nura, da sauri ya d'auko wayarshi ya kunna tareda neman numbar Alhaji Nura" Yace "Hello Alhaji Nura kana inane?" Ta d'ayan b'angaren akace "ina Company ne Alhaji lafiya?" Daddy yace "okay ina son ganinka yanzu a Farm house, katse wayar yayi ya nufi parking space, driver ne yaganshi yace " Alhaji tafiya ne? " Daddy ne yaja tsaki yace "Aa ba tafiya bane gudu ne" "Shiga motar yayi yafice da mugun speed". "Yana zuwa farm house, yad'an zauna yana jiran Alhaji Nura, ranshi ne yafara b'aci sosai, wayanshi ya d'auko tareda lalub'o numbar Alhaji Nura cikin fad'a, yace "zakazo ne ko bazakazo ba?" Alhaji Nura yace "gani dab da k'ofa ranka shi dad'e" Motarshi ne yadanno kai, cikin farm house, da sauri ya karasa inda Daddy yake yanata kai kawo. "Lafiya Alhaji?" Daddy yace "ina kaga lafiya, Asirinmu ya Tonu awajen Bilal, ji nake kamar in kashe Hajiya babba, wallahi yau da ace Hajiya ba ita ta haifeni ba da saina kasheta da hannun" Alhaji Nura yace "me ya faru Alhaji kamin bayani yanda zan game" Daddy yace "ina gubar danace maka yau zan baiwa Hajiya babba tasawa Minal a abinci?, shinefa taje takaiwa wata dak'ik'iyar mata, gashi matar ta tona mana Asiri, kuma Bilal ya sallameta da mak'udan kud'ad'e" Alhaji Nura yace "shine kake tada hankalinka? Inda kayi kuskure shine, daka nuna gaskiyar Hajiya a idonshi, yanzu abinda zakayi Asibiti zakaje ka samu Bilal, ka nuna mishi cewar Hajiya babba da Afrah sunyi kuskure, kaga daganan saika rab'e dashi ka kwashi dukiya nima a d'anmin nawa rabon" Daddy ne yace "Shiyasa nake son inyi shawara dakai, sabida kanada basira d Sosai, yana fad'in haka yashige mota sai Asibiti" Alhaji Nura ne yayi dariya yace "ita rake dama bata zubar da ruwa Dan kanta, sai an matseta tukun, zakasan kana Neman shawara a wajen Alhaji Nura" "Daddy yana zuwa Asibiti yaga Bilal kwance a gado d'aya da wannan Makauniyar, abin ya matukar b'ata mishi rai, da sauri ya karasa inda suke kwance, lek'awa yayi yaga duk suna bacci, a hankali cikin sand'a yaje wajen ruwan da aka d'aura mata, tareda kara gudun ruwan sosai tsabar mugunta, sand'a yake yanason yabar d'akin, daidai bakin kofa ya tsinto muryar Bilal yana cewa. "Daddy me kazoyi a nan?" Jikin Daddy ne yafara Rawa cikin in ina yace "Am...am dama nazo naduba jikkn nata ne kuma naga duk nuna bacci shine nace bari in d'an....Bilal ne ya katseshi dacewa "ai jikin natama da sauk'i, saura kawai ta farfad'o" Daddy yace "to..to Allah yakara mana sauki gaba d'aya" Bilal yace "Ameen" Daddy ne yafita a d'akin. Bilal yajuya yana kallon Minal, shafa fuskarta yayi a hankali yafurta "sleeping Beauty" Sauka yayi akan gadon tareda rufa mata bargon" _washe gari_ "Umma ce da Madina sukazo Asibitin, idanun Umma duk sun kumbura tsabar kuka, sakamakon Fad'a musu da akayi cewar Bilal ne yayiwa Minal duka har Asibiti" Suna shiga Bilal yaga Umma, kallo d'aya yayi mata yagano akwai alak'a tsakaninta da Minal, Dan akwai kama sosai, d'an duk'awa yayi yace "sannu da zuwa Umma" Umma ce tace "dakata!!! da gani nasan Kaine Bilal, meyasa zakayiwa 'yata wannan dukar? Kaika haifeta ne? Baka ganin rauni datake d'auke dashi? Minal fa Makauniya ce, bakada tausayi ne? Allah ya isa tsakanina dakai tunda kake cutar da 'yata, ai an fad'amin komai, an fad'amin duk abinda kakeyi mata" "Duk'ar dakai Bilal yayi yana bata hakuri" Ko sauraronshi Umma batayi ba, Ranta ya b'aci sosai, sai matsifa take. Zama tayi a gefen Minal tana kuka sosai. Madina ce take lallab'ata. "Bilal fita yayi a d'akin, yaje cikin Asibiti, yazauna, tagumi yayi yana tunanin yanda rayuwarshi take tafiya, kwata kwata babu jin d'adi babu kwanciyar hankali, ita Minal da a 'yan kwanakin nan idan yaga fuskarta yana samun nutsuwa da farin ciki ga mahaifiyarta tazo dawata maganar" Hajiya babba ce da Afrah a d'aki Afrah tana ta kuka wai Bilal ya fasa Aurenta, Hajiya babba ce taketa lallab'ata Amma taki tayi shiru, ran Hajiya babba ne ya b'aci. Tace "Zakiyi shirune ko saina koreki a d'akin nan? Haba Afrah ya zaki kaskantar da kanji awajen namiji kiyita rusa uban kuka? Koda shike bazan hanaki kuka ba, wata kilama idan kina kukan zaki d'an rame, ko kyayi fasali kila ya yadda ya Aureki, Amma kin aje jiki kamar drom, wazai yadda ya Aureki?" Afrah ce tace "haba Hajiya babba, ya zakice haka? Kina ganin yanda yake nuna yafison wancan blind girl d'in a kaina" Hajiya tace "Afrah basai kin zageni da turanci zansan ranki ya b'aci ba, kifad'a da Hausa ma yanda zanji me kikace da sauk'i" Afrah tace "Hajiya Blind girl fa nace, kuma yana nufin Makauniya" "To ai saiki fad'a da Hausa yanda zan gane, yanzu ki kwantar da hankalinki, ni Salamatu nace saikin Auri Bilal" "Bilal duban agogo yayi yaga lokaci yaja sosai, tashi yayi zuwa d'akin, yana zuwa yaga drip na Minal ya kare, a zuciyarshi yace. Yaushe akasa mata ruwan gashi harya kare" "Yana kashe drip d'in yayi tunanin Minal ta gaji da kwanciyar, zuwa yayi wajenta yana kokarin 'dagata" Da sauri Umma ta ajiye butar data fito dashi a band'aki, tace "idan ka tab'a jikin 'yata Allah ya isa ban yafeba" "Bilal ne ya tsaya cak ko motsi be kara ba". _✔ote & Comment_ Jiddah S Mapi *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 By Jiddah S Mapi Page 21... *___________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Umma ce ta karaso tace "dama kana sonta ne? Kuma kake wulak'anta ta? Yarinyar nan da kasan wahalar data sha a rayuwarta da bakayi mata haka ba, kun yaudareta, wai zaku kaita India a gyara mata ido, amma kuje kuna wulak'anta ta, to bari nafad'a maka, banason nakara ganinka a Asibitinnan, kuma kaida Minal har Abada, zan d'auketa awajenku, bazaku kara ganinta ba, balle kusamu damar wulak'anta ta, kaje mun gode da hidima" Bilal k'afafunshi sun kasa d'aukarshi, jin kalamun mahaifiyar Minal yake kamar Almara, cikin yanayi na nadama yace "Umma wallahi na tuba, Umma bazan iya kwana a d'aki d'aya banda Minal ba, nasaba da ita" "Ka saba da ita ko? Ai gara kacemin ka saba da dukanta zanfi ganewa" "Umma Dan Allah ki yi hakuri ki yafemin Wallahi na tuba" "Idan kaga na yafe maka to Minal ma tayafe maka". Suna cikin haka, Minal tad'an d'aga hanunta, a hankali tace "Yaya Bilal inajin fitsari" Da sauri Bilal yaje inda take ya d'agota yace "Kina lafiya Minal?" Minal kawar da kanta tayi tace "yaya Bilal nace maka inajin fitsari" 'Daukanta yayi ya kaita toilet, shiya cire mata wandon uniform d'in, datayi fitsarin yayi mata tsarki, kafin yariketa suka fito. Umma Ce ta k'araso wajen ta rungume Minal tana kuka, Minal tace "Umma yaushe kikazo?" Umma tace "Minal jiya nazo, ya jikin naki?" Minal tace "da sauk'i Umma" Doctor ne yashigo d'akin yana tsokanar Bilal "Malam Bilal d'azu na shigo ai naga kana wata yanayi shiyasa nafita" Bilal kawar da kanshi yayi Dan yanajin kunyar Umma sosai. Doctor ne yace "yawwa dama ba wata Matsala, jira kawai muke ta farfad'o gashi kuma Allah ya taimaka, zaku iya tafiya gida Amma saimunyi mata Allurori" Minal tace "Allura kuma? Meyasa za'amin Allura?" Doctor yace "kina tsoro ne Madam?" Minal tace "niba tsoro nake ba" Doctor yace "okay Bilal kabiyoni Office kaida ita akwai wasu magani da ya kamata a bata" Daganan yafice a d'akin. Bilal ne ta rik'o hannun Minal, yanufi office na doctor da ita. Suna zuwa doctor ya d'auko Allura yace "to madam tashi ki karb'i Alluranki" Idanun Minal ne yafara cika da hawaye, a hankali tace "Dan Allah kar kayimin da zafi" Doctor yace "kince ai bakya tsoro, to meye na kuka?" Bilal ne yafara dariya kasa kasa. Minal tasan Bilal yana nan sai kawai ta dak'e ta mike . Doctor ne yace "juya to Madam" Minal taki juyawa, Bilal ganin hakane yasa yatashi, ya iso wajenta, ya rungumeta yad'an ja wandon uniform d'in kad'an, kafin yayiwa doctor Alama da ayi mata. A hankali tafara cewa "kasakeni yaya Bilal, wallahi zan cijeka, banason Allura" Bilal ko kulata baiyi ba, Doctor ne ya d'auko Alluran yazo yayi mata. Lokacin da Alluran ya shigeta ihu tayi tareda kankame Bilal sosai, kamar zata mayar dashi ciki. Saida Aka gama Alluran kafin tafara jin kunya, taki sakin Bilal. Doctor ne yace "to sakeshi mana ai an gama ko bakiga na zauna ba?" Bilal ne yace "ai bata gani, idonta yasamu Matsala". Doctor yace " matsala kuma?" Meya kawo mata matsalar?" Bilal ne ya tambayi Minal wacce take rungume dashi har yanzu yace "Minal meya samu idonki kiyiwa doctor bayani" Ita kuma Minal gani take kamar ta kwafsa datayi kukan Allura, (abinka da fulani) hakan yasa taki sakin Bilal, cikin jin kunya, tace "munyi fad'ane da wasu mutane shine suka watsamin Acid" Doctor yace "subhanallah, dolene sai an fita da ita kasar waje kafin a gyara mata idon" Bilal yace "eh ana kan hanyar zuwa" Magani likita yabata, yace a kula sosai, Allah yakara mana sauki gaba d'aya" _✔ote & Comment_ Jiddah S Mapi *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 By Jiddah S Mapi Page 22... *___________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation "Ameen" Bilal yace. Doctor yace "to malama Minal a kula sosai, anji?" "Minal dataki sakin Bilal kin amsawa tayi, Bilal sai dariya yake" Saida suka fita a office d'in Bilal yace "to sakeni yanzu ai mun fito, karki jawo mutane suyita kallona" Minal saurin sakeshi tayi, ta turo baki tace "ai kai kace ayimin Allura" Kura mata ido yayi, yanajin wani irin Abu yana yawo a jikinshi, a 'yan kwanakinnan idan tana magana sai yaji kamar karta daina. Yace "to ai Alluran ne zai sama miki lafiya ko bakyason lafiyar?" Cikin shagwab'a tace "inaso mana yaya Bilal" Riko hannunta yayi yace "kin San me?" Minal girgiza kai tayi alamar Aa. Yace "bakinki yana min kyau" Wafce hannunta tayi tafara tafiya cikin jin kunyar maganar tashi. Riko hannunta yayi da sauri yace "kiyi hakuri" Batace komai itadai tafiya kawai take, Ummace ta hangosu daga nesa, ta karaso inda suke, tana hararan Bilal, wafce hannun Minal tayi daga nashi kafin taja ta suka tafi. "Bilal ya kasayin komai yana tsaye kawai, dayaga tsayuwan bazatayi mishi komai ba, yasa yafara binsu, gani yayi Umma takama Mashin mai K'afa Uku, tasa Minal Aciki itama tashiga sai tafiya" Cikin zuciyarshi yace "me take nufi kenan?" Minal ce tace "Umma ina yaya Bilal d'in?" Shiru Umma tayi mata, takara cewa Umma ina yaya Bilal? " Umma ce tace "Minal idan kinason kwanciyar hankali na to kada ki kara yimin maganar wannan yaron daya yaudareki, yasa kika Aureshi dasunan za'a gyara miki ido, Madina tafad'a min komai, naji duk irin wulak'anci da cin mutunci dasuke miki, ai Makanta ba hauka bane, kuma maraici ba kaskanta bane" Minal tasan ran Umma ya b'aci sosai, kuma itama a nata b'angaren hakane, sabida daurewa take tana yiwa Bilal magana, don kar Umma ta fahimci wani Abu. Sun isa gida lafiya, Umma ce tacewa Minal "muje in miki wanka ko?" Gyad'a kai tayi tace "to Umma" Umma ce tahad'a ruwan zafi takai band'aki, zuwa wajen Minal tayi tarik'o hannunta, had'i da kaita band'aki, cire mata kayan tayi, wani irin firgita Umma tayi ganin bayan Minal da shatin Bulala kamar na jaki, Kuka tafara tace "Minal meya sameki a baya haka? Dame suke dukanki? Wannan wani irin zalinci ne?" Kuka take tsakaninta da Allah Minal tana bata hakuri, da kyar ta lallab'ata har tayi shiru. Bilal ganin tsayuwa bazai karb'eshi ba yasa yakama Napep shima yatafi gida jikinshi duk a mace. Yana shiga yaga Hajiya babba a cikin gida ta d'aura d'ankwalin shadda har goshi tana harare harare ita a dole gidan d'anta. Tana ganin Bilal tafara Tambayarshi "ina mayyar matar taka datayi mana sharrin mun bata guba"? Had'a rai Bilal yayi ko kala baice mata ba yayi hanyar d'akinshi. Alwala yayi tareda yin sallar Isha, sannan yayi Nafila raka'a biyu tareda yin Addu'o'i, zuwa kan gado yayi ya kwanta, yarufe idonshi daniyyan yayi bacci Amma me? Sai bacci ya kauracewa idanunshi, tunaninta yafara lokacin da akeyi mata Allura, yanda ta rungumeshi ne ya tsaya mishi arai, filo n daya d'aura kanshi ne akai ya d'auko ya rungume sosai ajikinshi, a hankali ya yace "I miss you". " Minal ji take kamar wata sabuwar halitta yau gata ga Ummanta zasuyi bacci tare, ji take ko za'a kasheta bazata kara zuwa gidansu Bilal ba, gidansu Bilal ya zame mata kamar kurkuku, bata ganin haske agidan sai duhu" Kwanciya tayi akan katifar Umma tace "Umma Dama inason tambayarki wani Abu" Umma tace "Minal zaki iya tambayana komai Amma banason ki kawomin maganar wannan yaron" Minal tace "Umma yadda kika tsani Bilal be kai kwatankwacin yanda na tsaneshi ba, Amma akanshi nakeson nayi miki tambayar" Umma tace "ina jinki" Minal tace "Umma ranar danazo wajenki, kikace Mijina yana zuwa gidannan, to ya akayi da kikaje Asibiti baki ganeshi ba?" Umma tace "Minal Nagane cewa wani yake turawa don ayi mishi bincike, domin wancan yanada hankali, kuma sunanshi Sabir" Da sauri Minal tace "Sabir kuma?" Umma tace "Eh kin sanshi ne?" Minal tace "Aa Umma ban sanshi ba gaskiya" (tayi hakane sabida Umma takara tsanar Bilal). _Washe gari_ Bilal ne yaje Police station tareda cewa DPO a saki Latif sabida bashida laifi, DPO yace "an gama ranka shi dad'e, Kud'i Bilal yaciro a Aljihunshi tareda ajewa a gaban DPO. DPO yace " an code ranka shi dad'e, (Abinda DPO bai saniba shine Bilal yana videon shi ta kasan Tebir, daga lokacin daya karb'i cin hanci har zuwa yanzu). Bayan an saki Latif ne Bilal yazo wajenshi yamika mishi hannu tareda cewa "Congratulations Abokina" Kawar dakai Latif yayi ko kara kallon Bilal baiyi ba yabar wajen. Cikin k'uluwa Bilal yabishi yace "haba Latif ina maka magana kuma kayi tafiyarka? Sai kace baka sanni ba? Ai koma menene saika tsaya ka saurareni" Latif shiru yayi Amma ya kurawa Bilal ido, da

Chapter 7 of 14