Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamshi, b'angaren kayan sweet ya nufa ya d'ebo su Chocolate da oatmilk dasu candy sweet Sai Ice cream saya siya mata sabida yasan tanaso sosai, wani zobe da d'an kunne na gold ya d'auka mata, murmushi yayi azuciyarshi yace "nasan idan tasa wannan she will become like princess". A takaice zuwa wannan super market dayayi, yayishi ne sabida Minal Dan yanason ya faranta mata kamar yanda itama ta faranta mishi, Yana gama siyayyan yanufi wajen me kaza, yasiyo gasasshe guda biyu, mota ya kama ya nufi Hanyar Hotel Cikin zumud'in zaije yaga beautyn shi. "Yana zuwa ya wuce Room 120 Wanda shi suka kama, Murmushi yayi yace "nasan yanzu tana jirana" Sai de me? Yana zuwa yaga kofar d'akin Rubb da kwad'o, Cikin mamaki yace "kai waya rufe d'akin? Kodai namanta d'akin ne? No Room 120 muke kuma gashi shine wannan" Ajiye ledojin hannunshi yayi yatafi wajen reception, tambaya yayi, ina makullun Room 120? Mika mishi makullin akayi Cikin mamaki yace to ina Minal taje? Kai baridai na dubata Cikin d'akin, da sauri yaje wajen d'akin ya d'ebo ledojin yashiga, "Beauty? Beauty?" Shine abinda yake fad'a nemanta yake acikin d'akin har karkashin gado saida yaduba dasu toilet gaba d'aya Amma ko Alamunta babu, Cikin firgici yafita a d'akin ya nufi wajen reception Yana tambayarsu waya kawo makullin, wata mata ce tayi mishi bayani cewar ai wata yarinya ce takawo Hannunta d'auke da jakan kaya" Bilal Cikin tashin hankali yace "no no beauty baza kiyi hakaba nasani zaki dawo" Barin wajen yayi da sauri yanufi harabar hotel d'in da wuraren shakatawarsu amma bai ganta ba, Zama yayi a bakin get Yana jiran dawowarta. Minal bacci take Cikin kwanciyar hankali, wasu samari ne sukazo wucewa, Sai sukaga mutum kwance akasa rungume da jaka, zaro ido d'ayan yayi da turanci yace "kai kaga wata fine girl a can?" Da sauri d'ayan ya juya yaga yarinya kwance tana sharar bacci, juyawa sukayi gabas da yamma sukaga babu me kallonsu, wurin Minal suka nufa d'ayan ya wupce jakar ya bud'e, ganin kud'ad'e yasa yace "guy's yaufa mun fito da sa'a ga kud'i ga kaya" Tafawa sukayi suna jin dad'i, Minal ce taji hayaniya akanta da sauri ta mike tana laluben Jakarta, ganin samarai guda uku a kanta suna kallonta kuma da Alama 'yan kwayane yasa ta tsala ihu tace "kafa me naci ban Baka ba?" Gudu take tsakaninta da Allah Samaran suna bin bayanta, mutane suna kallonsu Amma babu Wanda ya kula, Minal ihu take tana cewa "a taimaka min" babu Wanda yakejin yaren Hausa a cikinsu, Sai samaran suce "Ku kama mana ita b'arauniya ce" Idan mutane sunji haka Sai su kyalesu, A halin yanzu ta gaji da gudun kafafuwanta sun mutu, daidai wani kwana ne wata mota tazo da gudu, itama Minal da gudu tazo Sai kawai motar ya d'auketa cakk, Minal fad'iwa tayi a kan motar a sume jini nabin fuskarta, Da sauri me motar ya taka birki, samaran kuma ganin haka suka juya aguje da Jakar kud'in. Wani sugar Daddy ne yafito daga motar shida wata kyakkyawar mata wacce bazata wuce shekara 40 ba, inda Minal take kwance suka nufa, d'aukanta sukayi suka sata a mota se babban Asibiti. Bilal yana zaune a harabar hotel har dare Minal bata dawo ba, Da karfi yace "why? Why Beauty meyasa zakiyi haka, ina kikaje? Dana sani daban fita ba, Jin ana kiran Sallah ne yasashi tashi yaje yayi Alwala taredayin Sallah yayi Addu'a Allah yasa Tadawo, zama yayi akan sallayar yakasa yin komai, wasa wasa har Isha yayi bata dawo ba, ba karamin tashin hankali Bilal yake Ciki ba, ledan daya siyo su kazane yayi ball dashi, zuciyarshi kamar zai fasa kirjinshi yafito. "ina kika shigane Minal?". Minal an kaita Asibiti likitoci ne suka taru akanta ganin yanda Take zubar da jini a kanta, da kyar aka samu aka tsayar da jinin wani farin kyalle aka d'aura mata akanta, Matar da suka bugeta ne taketa zirga zirga a asibitin, Sai bayan isha kafin tafara motsa hannunta alokacin mutumin yafita Sallah matar ce kad'ai a d'akin ganin Hannun Minal yana motsi yasa tafice da gudu takira doctor, lokacin da suka karaso Minal ta farfad'o sai kiran " kud'ina, kud'ina kawai take". Matar ce tarike hannunta tace "kiyi hakuri 'yata zan baki kud'inki kinga yanzu da ciwo akanki idan kikaci gaba da kuka kanki ne zaiyi ciwo" Minal tace "to Amma zaki taimaka ki mayar dani kasar mu?" Matar tace "wani kasa ne?" Minal tace "Nigeria" Matar tace "dama me kikazo yi anan?". Cikin kuka Minal tace " Wanine ya satoni daga Nigeria sabida ni makauniya ce, shine yasa aka warkar dani, bayan na warke shine yamin Fyad'e yace kuma zai kaini wurin yankan kai yayi kud'i dani shiyasa kikaga na gudu". Cikin tausayawa Matar tace "oh Wannan duniyar ta lalace babu Wanda zai taimaka maka Dan Allah sai Dan wani Buri nashi, Allah dai ya kyauta". Lallab'a Minal tayi tace " kiyi hakuri in Allah ya yadda zan taimaka miki, Muma dama Next week xamu koma Nigeria kinga kafin lokacin zaki d'an samu sauki, saimu tafi gaba d'aya". _✔ote & comments_ _Jiddah S Mapi_ *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 By Jiddah S Mapi Page 33... "Minal murmushi tayi Wanda ya bayyana dimple nata tace "nagode Hajiya Allah yabiyaki" Matar tace "No kidaina godemin kuma banason ki kara cemin Hajiya, Ki kirani da Mommy, sabida inada yarinya wacce kuke yanayi da ita sosai, saidai ita tanada yawan surutu ba kamar keba shiru shiru". Murmushi Minal tayi tace "to Mommy" Matar ce ta kwantar da Minal a cinyarta tana shafa mata kanta a hankali har tayi bacci, Lokaci d'aya taji Minal tashiga ranta sosai, Suna Cikin haka saiga mutumin ya shigo, "ya jikin nata?" Matar tace "da sauki Ammafa Alhaji ina ganin yarinyar nan tana Cikin matsala, a hankali ta fad'a mishi duk abinda Minal tafad'a mata, ta d'aura dacewa, Alhaji ya kamata mu taimakawa yarinyar sabida tana Neman taimako". Alhaji ne yace "to ai Hajiya basai kin fad'amin ba, idan ka taimakawa mutum ai kanka kayiwa, Yanzu dai muyi Addu'an Allah yabata lafiya, Kinga idan tanada lafiya komai zaizo da sauki". Da sauri matar tace " Ameen" Bilal kwanciya yayi akan tyles zuciyarshi a cakud'e ji yake kamar ya tashi yayita ihu kozai samu saukin abinda yake damunshi, Waya ya d'auko yakira 'yan sanda yabada cigiyarta agidan TV da gidan redio, acikin Daren ya tashi yayita Addu'a Allah ya bayyana mishi ita cikin gaggawa. _washe gari_ Bilal ne yatashi da sassafe yatafi police station wata kila yasamu information akanta, yana zuwa akace babu wani labari, Idonshi ne ya cika da hawaye yarasa ina zaije ya ganta, zama yayi akan wani dutse dake cikin station d'in, yayi kusan Rabin Awa yana zaune baisan abunyi ba, yaga polisawa sun shigo da wasu samarai su Uku kallonsu kawai yakeyi, a hannun wani police ya hango wata jaka ta mata, idan ba gizo idonshi yake mishi ba, yana ganin kamar jakar Minal ce, da gudu ya nufi wajen 'yan sandan yace "yallab'ai waye me jakar nan?" Police d'inne ya nuna samaran yace "wannan ne sukayi fashi, mun kamasu suna raba kud'in awani lungu na 'yan shaye shaye". Da sauri Bilal yariko d'ayan yace " Dan Allah ina me jakar nan, wallahi idan kuka fad'amin zan Baku kud'in daya ninka wannan kuma baza'a kulleku ba". 'Dayanne yace "matar da muka karb'a a hannunta ta gudu kuma mota ya bugeta". Kukan kura Bilal yayi ya shake wuyanshi yace "a ina?" 'Yan sandane suka fara kokarin kwace saurayin da idanunshi suka firfito tsabar Azaba. Sauran da suka ga yanda d'an uwansu yasha matsa sai sukace zasu nuna inda suka ganta, motar 'yan sanda suka shiga dukansu harda Bilal dayake ta huci kamar zaki, daidai karkashin bishiyar da Minal ta kwanta suka nuna mishi, Bilal ne ya dirka akan motar yanufi wajen, saidai baiga kowaba, cikin sanyin jiki sukaje inda tayi accident d'in ma babu wata Alamarta, Zuwa wannan lokacin Bilal yakasa controlling na hawayenshi kuka yake kamar karamin yaro, daidai wajen da Minal ta fad'i ne yaga wata zube, d'agawa yayi yana kallo, yasan wannan tabbas zoben Minal ne, sa zuben yayi a hannunshi yana kuka. Police ne suke bashi hakuri, har suka koma office, an kulle samaran shikuma Bilal sunyi mishi Alkawarin zasuci gaba da bincika mishi ita. Da haka ya koma Hotel d'in cikin sanyin jiki. Minal tad'an samu sauki sabida kulawar da matarnan da mijinta suke bata, kamar kullum yauma Minal ce ta kwantar da kanta a cinyar Mommy, cikin muryanta na shagwab'a tace "Mommy yaushe zamu tafi a Asibitin nan? Nifa nagaji dashan magani da karb'an Allura" Dariya mommy tayi tace "haba mana sai kace keba jaruma ba, babyna fa bata tsoron Allura" Minal ce tayi murmushi tace "Mommy inason inga babyn naki nima tashiga raina tin ban ganta ba" Mijin matar ne yashigo d'akin yace "to Daughter ai gobema za'a sallamemu itama ta dameni tanason ganinki, nace mata saidai gobe, kinga sai jibi mu tattara mu koma kasarmu Nigeria ko?" Cikin jin dad'i Minal tace "to Daddy". Washe gari Doctor ya basu takaddan sallama, Minal sai murna take zataje taga Babyn Mommy, tariga kowa shiga motar cikin zumud'i tace " Daddy ayi sauri mana mutafi" Daddy ne yayi dariya yace "to daughter" A wani babban gida me kyau sukayi horn me gadi ya bud'e musu, Minal ce ta bud'e motar tafita, wata kyakkyawar yarinyace 'yar shekara 17 tazo da gudu ta rungume Minal, Minal tana ganinta tagane cewa itace Baby, cikin jin dad'i itama ta rungumeta, Mommy ce tafito tana dariya tace "to baby saiki kaita d'akinki acan zaku zauna, yau dai gaki ga Minal" Baby ce tayi dariya tace "wallahi kuma mom gata kyakkyawa, ai nasamu sister". Hanun Minal tariko tace " sister muje kiga d'akinmu. ✔ote & comments _Jiddah S Mapi_ *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 By Jiddah S Mapi Page 34... "Murmushi kawai Minal tayi, suka nufi d'akin, wani d'akine mai kyau ta kaita ne d'auke da pink & white colour, gadone babba me kyau sai Teddy's dayawa, Baby ce tace " sister colour na d'akin yamiki?" Cikin murmushi Minal tace "wallahi yamin kyau inason pink colour da fari" Dariya baby tayi tace "wow kice munason Abu d'aya, shiyasa Allah yahad'amu, bakisan wani Abu ba, tunda naganki naji kin kara burgeni sabida shiru shirunki, Allah yasa dai zamuyi tazama dake" Minal tayi Dariya tace "Ameen, yanzu tashi muje muyi aiki karmu bar Umma ta gaji, sabida ta gaji a asibiti dayawa". Baby tace " Haba ke kuma ni ai bana aiki, da zaran nadawo daga school za'a kawomin Abinci inci, akawomin ruwan wanka inyi, sai nayi sallah sai bacci". Minal cikin mamaki tace "yanzu babba dake sai an kawo miki abinci? Kuma sai an kai miki ruwan wanka?" Cikin dariya Baby tace "eh mana Sister meye aciki" Minal shiru tayi. Baby tace "tashi kiyi wanka sai kici Abinci kisha maganinki kiyi bacci". Minal tamike tace " to". "Kwana biyu Bilal ya rame yayi haske sosai, tunani bibbiyu suka taru suka mishi yawa, ga tunanin Minal dayake hanashi bacci, ga kuma tunanin yanda Daddy yake son ya kasheshi, wannan wani irin bala'i ne?". Afili yafurta "anya yarinyarnan bata koma Nigeria ba? To Amma waye zai bata kud'in jirgi?" Tashi yayi da sauri yace "dolene nakoma Nigeria gobe, gashi batada waya, oh God help me out". Shirya kayanshi yafara da sauri yana tattara abubuwan dayake bukata, drawer yabud'e yaga babu kud'i, murmushi yayi yace "nasan za'a Rina ta tafi Nigeria". Minal tayi wanka taci Abinci sannan tasha magani, Suna cikin hira da baby ne mommy ta bud'e d'akin tace " sannunku yarana" Baby ce tace "yawwa mommyn mu" Minal dariya kawai tayi. Mommy tace "yanzunnan Daddynku yacemin gobe zamu tafi Nigeria sabida ana nemanshi a office, so abinda nakeso daku kuzo muje d'akina Ku kintsa min kayana kafin kuzo Ku kintsa naku, Minal kid'anyi aiki kad'an sabida zaki d'an samu saukin jikinki". " to mommy" shine abinda suka fad'a. Bayan wasu mintina kad'an suka kintsa kayansu Dana mommy. _Asuba tagari_ Bilal ne ya d'auko trolleyn shi da wayoyinshi yanata sauri ya iso airport. Taxi ya kama yatafi babban airport na kasar India, burinshi kawai ya iso Nigeria yaga Beutynshi, Suna zuwa yaje ya nuna musu visanshi yashige cikin jirgi yayi kwanciyarshi, tareda rufe fuskarshi da handkerchief, A hankli yace "I miss you beauty" kashe wayarshi yayi duka". Minal da Baby da Mommy sai kuma Daddy sun shirya kayansu a mota dukda mommy tahana minal yin komai hakan bai hanata shirya kayanba, suna gamawa driver yajasu sai babban airport. Da zuwansu airport suka tarar jirgi ya kusa tashi, da sauri suka shiga duk suka zauna. Kowa yana jiran jirgi yatashi. Daidai lokacin da jirgi zai tashine Minal taji kafar mutum yana cokalin ta, da sauri ta juya tanason tayi bala'i, kawai taga trolley irin na Bilal, lek'awa tad'anyi a hankali taga Meshi ya rufe fuskarshi da handkerchief, Ido ta tsurawa meshi, hannunshi takalla saida zuciyarta tace dimm, ganin Bilal kwance sabida tasan wannan tabbas zobenta ne, Da sauri tajuyar da kanta gefe wajen Baby, Tace "sister kibani Nikab naki mana insa wallahi iska yamin yawa". Baby tayi dariya tace " to bari na Ciro miki kinsanni dason Nikab kuwa? Hmmm ai lokacin da Daddy zaije Saudiya tsarabar Nikab nace ya kawomin ai kuwa yakawomin dayawa zan baki sauran ma idan mukaje gida" Minal ganin surutun Baby yana b'ata mata lokaci yasa tace "bari naduba da kaina" Baby tarikota tace "no ai ke bakida lafiya, bari nad'auko miki" Minal komawa tayi ta zauna jikinta duk yana rawa tsoronta d'aya kada Bilal yamike ya ganta, Baby ce tazo da Nikab d'in tace "bari nad'aura miki, ke ai dama Nikab yafi dacewa dake, sabida kinada kyau" Murmushi kawai minal tayi. Saida baby tad'aura mata Nikab d'in kafin taji sauki a ranta, Biro da 'yar takadda tace "baby inason ki rubutamin wani Abu, sabida inason koyan karatu da rubutu". Baby ce tayi dariya tace " kawo takaddar na rubuta miki, amma kina fad'an abinda zan rubuta" Minal tace "to yanzu dai muyi misali da mutum d'aya acikin jirginnan, sai muyi akanshi" Baby tace "okay ta amma dawa zamuyi? Kodai muyi da daddy?" Minal tayi dariya tace "Aa muyi da wancan Wanda yarufe fuskarshi da handkerchief d'in". Baby tace " yawwa nima tin d'azu hankalina akanshi, da Alama tunani yake, Amma daga ganinshi fa handsome ne" Minal ce tayi dariya tace "hmmm wasu mutanen idan kin gansu handsome saikice inama da saurayinki ne, to Amma idan kin zauna dasu zakice inama da ban sanshi ba" Baby tace "kumafa hakane yanzu kina fad'amin abinda zan rubuta" Minal tace "ki rubuta, Assalamu Alaikum, bawan Allah meyasa ka rufe fuskarka? Shin akwai wacce kake tsoron ta ganka ne? Toni sunana Minal, kuma idan nakoma Nigeria bazaka kara ganina ba, na tsaneka, banason ganin fuskarka, ina rokon Allah har na fita a jirginnan kada ka bud'e fuskarka, hasalima ko sunanka aka kira yana sani bak'in ciki, gara ka koma Inda ka tashi domin bazan tab'a yadda kasan inda nakeba, daga Minal wacce aka lalatawa rayuwa sabida kai, ka taimaka mata sabida wani dalili naka, ka b'ata mata rayuwa, Allah ya isa tsakanina dakai. Baby ce ta d'ago tace "sister wani irin magana ne wannan?" Dariya Minal tayi tace "ai koyan rubutu zanyi, kede kawai kibani ai ba gani zaiyi ba kawai dai inason in karanta in b'oye sabida wata rana in gwadawa saurayina". Dariya Baby tayi tace "gashi to ai ba wannan sakon yakamata ki rubutawa saurayinki ba, sakon soyayya yafi dad'i koda Neman tsokana ne, kamar nida yaya Mujahid nawa". Minal bata kara magana ba, shiru kawai tayi ta karb'i takaddar. Lokacin da jirgi ya sauka Minal ce tayi sauri zata fita, Baby ce tariko hannunta tace " ya zaki fita ki barni mudai je mu biyu mubar su mommy". Minal ma tariko hannunta daidai wurin da Bilal yake kwance, tad'an duka kad'an ta cusa Takaddan datayi rubutun acikin Aljihun rigarshi, Da sauri suka fita. Bayan su mommy sun fito driver yazo d'aukansu, Hanyar Abuja suka d'auka. ✔ote & comment _Jiddah S Mapi_ Watpadd @Jiddah S Mapi *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 By Jiddah S Mapi Page 35... *___________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation "Abuja zone 2 shine unguwar su baby, wani Babban gida me kyaun gaske aka driver ya tsaya yayi horn, me gadi ne yazo da gudu ya bud'e musu yana d'aga hannu yace " barkanku da dawowa" Suma d'aga mishi hannu sukayi kowanne fuskarshi d'auke da murmushi, parking yayi a parking space, duk suka fito kowa yanajin dad'in yadawo kasarshi, Baby ce tariko hannun Minal tace "muje mu huta a d'akinmu ko" Minal batace komaiba tafara binta, Minal dataga kyaun gidan a zuciyarta tace "tabd'i Ina ganin gidansu Afrah kamar Aljanna, Amma na tabbata idan Afrah tazo gidannan saita raina kanta" Wani babban falo ne me d'auke da lemon green and White colour suka shiga, cikin show glass d'in akwai wani Abu me yalk'i Wanda ya k'awata d'akin, da kwalaben turare kalala, gefe kuma wani zungureren TV ne a kunne, mutanen cikin TV d'in kamar zasu fito tsabar girman Tivin, Chinese carpet lemon green da fari ne a shimfid'e a kasa, sai wasu luntsuma luntsuman kujeru set, (tsaya a lissafa kayan falon da kyaun gidan b'ata lokacine)". Baby ganin Minal tana bin ko ina da ido yasa taja hannunta tace "muje d'akinmu muyi wanka Dan nifa na gaji sosai" Minal tayi murmushi tace "raguwa kawai" Jan hannunta kawai tayi zuwa d'akinta, Minal ganin d'akin Baby yasa ta saki baki tana kallon ikon Allah, wani gado pink and white colour ne acikin d'akin, Teddy's kamar na siyarwa, sai wardrobe bango to bango, da wasu manya manyan kujeru guda biyu gefen gadon, sai bedroom freezer, Wanda aka cikashi da drinks da kayan d'anye irinsu Ayaba, Apple, lemo, kankana, babu Wanda babu. Minal a fili tace "ya Allah Kaine kayi masu kud'i, kayi talakawa, kayi wasu da lafiya wasu kuma babu lafiya, wani me kud'in ysnada lafiya wani kuma ga kud'i ba lafiya, wani talakan yanada lafiya amma bashida ko sisi, wani talakan bashida lafiya kuma bashida ko sisi, wani me kud'in yayi kyauta ya taimakawa mutane, wani me kud'in ya wulak'anta Wanda basu dashi, wani talakan kayishi da zuciya wani talakan kayishi babu zuciya, Ya Allah kada ka bamu kud'i Wanda zai hallakar damu, ya Allah kabamu kud'i Wanda zai amfanemu duniya da lahira, takarashe maganar tana kuka, tunawa datayi da mahaifinta Wanda sanadin dukiya aka kasheshi.....Baby ce ta katseta ta hanyar rungumarta itama tana kuka tace  " hakika kin fad'i gaskiya Minal, dazan baki labarinmu dasai kin tausaya mana, Amma Daddy ya hanani maimata abinta ya wuce, banason in tuna baya ko kad'an natsani dukiya Minal....." Da sauri tashare hawayenta tace "kije kiyi wanka, nikam sai nayi waya da Yaya Mujahid nawa, Dan har yanzu baisan na dawo ba, Minal toilet ta nufa bata kara magana ba. Bilal yana bacci acikin jirgi, Saida akayi Kusan 30mins da sauka su kuma pilot d'in babu Wanda ya tasheshi, Saida ya farka dan kanshi kafin yasan sun iso, da sauri ya tashi yad'auki kayanshi, motar Gombe ya kama yasa kayanshi aciki, Sun d'au hanya ne yasa hannu a aljihu zai d'au wayarshi yaci karo da wata takadda, baiyi gigin bud'ewa ba sabida yanayin dayake ciki, ganin takaddar karamace ba wata babba ba yasan babu wani Amfani, can gefe ya wurga takaddar, bai kara ko kallo ba, 4:30 na yamma suka iso Gombe, da sauri ya fita a motar burinshi kawai ya iso gidansu Minal, har ya fita a motar yaga wata mata data zauna a gefenshi tad'au takaddar da yasar tana karantawa, ranshi a b'ace ya warce takaddar ya mayar Aljihunshi, "wannan ai rainin wayone ya zan yasar da takadda ta d'auka ta karanta?". Unguwar su Minal direct ya nufa yanata Addu'an Allah yasa ta dawo, daidai kofar gidansu yaji zuciyarshi tana tsinkewa, tsayawa yayi yakasa shiga gidan, wata zuciyar tace mishi " yanzu idan ka shiga bata dawo bafa ya zakayi?" Wata zuciyar kuma tace "to idan baka shigaba ya zakasan ta dawo ko bata dawo ba?" "Runtse idonshi yayi, ya daure yayi sallama" Cikin gida kuma Umma tana zaune ta rabka tagumi kamar kullum tana tunani, taji sallama a kofar gida, da sauri ta Amsa ta d'auko hijabinta tasa a zuciyarta tace "Allah yasa an samu Minal ne". Tana lek'awa tace " wayene?" Bilal ne yayi shiru, Umma tad'an fita kad'an lokacin Bilal ya d'ago fuskarshi, Ummace ta zabga mishi wata muguwar harara cikin b'acin rai tace "lafiya? Me kazoyi? Bawan Allah tun kafin na kira maka yara suyi maka duka ka b'acemin dagani, banason ganinka na tsaneka, sanadiyyarka 'Yaya ta makance, kuma sanadiyyarka rayuwarmu ta lalace babu ita babu dalilinta, Allah ya isa tsakanina dakai" Bilal kasa ya durkusa yace "Umma ki yafeni na Tuba nabi Allah, wallahi inason Minal, tsakani da Allah....."dakata malam ka tashi kabar kofarnan, kafin natara maka yara". Cikin sanyin jiki ya tashi yana kuka yatafi, shikam duk wulak'ancin da matar zatayi mishi tausayi take bashi, dayasan idan idon Minal ya bud'e zai jawo musu matsala daya barta da makanta, yaci gaba da kula da ita, karkashin bishiya yaje ya zauna ya aje kayanshi idonshi yana fitar da hawaye, A hankali yace " where are You beauty? Karki gujeni a wannan lokacin danake cike da buk'atarki, Saida kika lasamin zumarki kafin zaki gujeni? Kitaimaka ki dawo beauty" Shi kad'ai yaketa surutunshi, Saida mangariba ya gabato kafin ya tashi ya nufi gida jikinshi duk a mace. Yana zuwa gida lokacin Afrah tana zaune tayi tagumi, tana tunanin Bilal, Sallama yayi muryanshi a toshe, da sauri Afrah ta d'ago kanta tana kallin kofa, ganin Bilal ne d'auke da jaka yasata tashi da gudu taje ta rungumeshi, shima runtse idonshi yayi ya rungumeta sosai domin a wannan lokacin yanada buk'atar haka. "Afrah jin bai hantareta ba yasa taji jikinta duk ya mutu da ganin yanayinshi, ya rame sosai saiya kara haske fuskarshi tayi fayau, 'Dago kanta tayi tace " Yaya meya sameka haka duk kabi ka rame?" Idonshi ne yacika da hawaye a wannan lokacin idan baiyi magana ba zuciyarshi zata iya bugawa, cikin muryan Kuka yace "Afrah soyayyace, soyayyace tasa nazama haka, ta gujeni" Kara rungumeta yayi yaci gaba da kuka kamar karamin yaro. Jikin Afrah ne yayi sanyi, ganin yanda yake kuka, a hankali tafara bubbuga bayanshi tana lallashinshi, Da kyar tasamu yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, Amma har yanzu yaki sakinta. Hajiya babba ce taga Afrah ta jima, d'ankwali ta d'aura tafito tana kiran "Afrah ina kika shigane.....turus ta tsaya ganin Afrah rungume da namiji, Salati tafara tana tafa hannu, tace " shikenan Afrah kin zauce, yanzu tsabar rashin kunya zaki gayyato kato cikin gidannan da rana tsaka ki rungume? Hawaye tafara sharewa da bakin zaninta tanata salati. Afrah ce ta saki Bilal, Hajiya babba tana ganin Bilal ta zaro ido, tace "La haula wala kuwwata illa billahi, Bilalu? Kaine ka rame ka fige kayi bak'i kamar d'an kasar Kenya?" Bilal bai kulata ba ya d'au jakarshi zai wuce, Afrah ce tayi saurin karb'a tace "kawo nakai maka d'aki Yaya". "Murmushi yayi ya mika mata suka Wuce Hajiya Babba data saki baki". ✔ote & Comment Wattpad  @Jiddah S Mapi *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 By Jiddah S Mapi Page 36... *___________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Har d'aki Afrah takaishi, tana zuwa ta ajiye mishi jakarshi, tashige cikin toilet d'in, ruwan wanka ta had'a mishi, tareda fesawa towel nashi turare, fita tayi taje wurin dayake zaune gefen gado ta dafa kafad'arshi tace. "Yaya kaje kayi wanka sai kayi sallah, sai kaci Abinci kafin ka huta" Murmushi yayi yace "nagode Afrah" Afrah ma cikin tausayinshi tace "ka daina godemin yaya" Tashi yayi yashiga toilet itama Afrah fita tayi da niyar dafa mishi indomie. Bayan Minti talatin Bilal yagama wankarshi, yana fitowa yaga Afrah zaune kan gado hannunta rikeda Plate, murmushi yayi mata Yawuce yaje ya shafa mai, wardrobe yaje ya d'auko kayan baccinshi, ya koma toilet yasa kafin ya fito, Afrah ce tace. "Yaya ga abincinka" Karb'a yayi ya bud'e yafara ci, gishiri yayi yawa a abincin amma ya zaiyi yarinyar ta damu dashi sosai, dahaka ya daure ya cinye indomie Tass, yace. "Yayi dad'i" Dariya Afrah tayi tace "nagode, yanzu ka kwanta ka huta" Bilal yace "sai nayi sallah" Afrah tace "oh hakane fa, kayi sallah saika kwanta" Tashi Bilal yayi, ya idar da sallah tareda yin nafila raka'a biyu, yana idarwa yahau gado ya kwanta zuciyarshi a cunkushe, bayajin dad'in komai, magana ma daurewa kawai yake yi, Afrah ce ta rufe shi da bargo, cikin sanyin murya tace. "Good Night" Juyawa tayi zata tafi taji ya riko hannunta, zuciyarta ne ta tsinke, da sauri ta juya Dan tabbatar da shine ya rike hannunta, Ganin Bilal yana hawaye abin ya matukar tada mata hankali, da sauri ta karasa wurinshi tana tambayarshi ko lafiya?. Hannunta ya damke yace "Afrah ki taimaka ki nema min ita, wallahi ina cikin matsala, bazan iya bacci ba sai naji muryanta, koda ba magana me dad'i zata fad'amin ba kitaimakeni...." Afrah jin dalilin kukanshi ba karamin haushi abun yabata ba,

Chapter 10 of 14