harda ke Nabeelah? Yafad'a yana kallon Baby,
Mommy ce tarufe bakinshi tace " munyi hakane domin mu kub'utar da kanmu da kuma kai daga zalincin Yayan Mahaifinka, Alhaji Umar, Bamuyi don bama sonka ba"
Baby cikin kuka tace "Yaya bansan kana Raye ba, wallahi ban sani ba" taci gaba da kuka me tsuma zuciya,
"Ina Daddy?" Cewar Bilal.
Lokacin Daddy yashigo yana tsaye abakin kofa yace "gani nan, waye kai?"
Bilal cikin mamaki yake kallon Daddy juyawa yayi wurin mommy yana kallonta sai yaga ta kawar da kanta tana kuka sosai, "Daddy baka sanni ba?"
Daddy ne yace "ina zan sanka bawan Allah naganka dai a gidana"
Bilal cikin firgici yace "mommy kina jin abinda yake cewa"
Mommy batayi maganaba sai kuka, cikin kuka tace "Bilal yanzu ba lokacin magana bane kabari idan munje gida sai nayi maka bayani"
Minal tana jinsu Amma tayi likimo tana jin labarin kamar Almara, kara runtse idonta tayi tana numfashi kamar meyin bacci, Bilal ne yajuya yana kallon inda take idanunshi ne suka cika da hawayen farin ciki ga Minal ga Iyayenshi ga kanwarshi wacce yakesonta sosai, tashi yayi yanufi wurinta, A hankali yariko hannunta yana shafawa, Kwantar da kanshi yayi akan hannunta hawaye sunabin kumatunshi, cikin kuka yace.
"Lalle kin cancanci yabo Beauty, Had'uwata dake ya haifarmin da farin ciki mara d'orewa, Kin Makance ta dalilina, Wanda sanadiyyar haka ni na tsira da lafiyata, Kin had'ani da iyayena, Nagode miki Minal, insha Allah saina zama gatanki a duniyarnan, zan saki farin ciki Wanda bakiyi zato ba, zan maidaki tamkar sarauniya, Zaki fito daban acikin mata"
Minal tana jinshi, Amma tayi mishi shiru, janye hannunta tayi daga nashi, ta juya mishi baya kamar acikin bacci, Murmushi yayi yace "nasan dole kiyi fishin dani, Amma komai zakiyimin zan jure har lokacin da zaki sakko ki kulani"
Baby ce tazo inda suke ta dafashi tace "Yaya matar Aurece fa, kuma kake tab'ata bafa 'yar mommy bace"
Dariya yayi Wanda yafi kuka ciwo yace "Nabeela wannan matata ce"
Waro ido Baby tayi tace "matarka kuma?"
Bai karayi mata magana ba yaje wurin doctor ya tambaya musu sallama, sabida ya matsu yaji meyasa Daddy yanuna bai sanshi ba me yayi mishi, Doctor ne yarubuta musu takaddar sallama gaba d'ayansu, Daddy yabiya kud'in, Kowa ya tashi yana shiri banda Minal dataki bud'e idonta tin d'azu, Bilal ne yaje yana tattara hannun riganshi Alamar zai d'auketa, "dakata" cewar Mommy, cakk ya tsaya yana jinta, "karka sake kasa hannunka a jikinta, tayimin bayanij komai, duk abinda yafaru tsakaninta da Mijinta ta fad'amin, kuma a lokacin na nuna b'acin rai na, sabida haka baza'a toye mata hakki ba"
Tashi tayi taje gefe Minal ta zauna, hannunta ta riko tace "tashi daughter an sallamemu"
Minal ce ta mike don batason tana yiwa Mommy musu, Ido hud'u sukayi da Bilal, had'e face tayi ta kawar da kanta tana kallon Baby data tsaya kamar statu, Mikawa Baby hannu tayi Alamar ta d'agata, Baby karasowa tayi ta riko hannunta ta mikar da ita, suka fice a d'akin, Bilal yana tsaye yana kallon ikon Allah, Mommy ma ko kallonshi batayi ba tafara tattare takalmanta, domin Bilal yabata haushi da irin wulakancin da yayiwa Minal, dolema ta hukuntashi.
Bin bayansu shima yayi suka shiga mota driver yajasu sai gida, suna zuwa gida Minal ta bud'e motar ta fice batayiwa kowa magana ba, Bilal yabita da ido harta shige cikin gida, "yarinyar nan ne tadawo haka? Tayi fresh kamar ba itaba, ga wani class datake dashi yanzu, lalle akwai aiki a gabana"
Mommy tana kula da yanda yake kallon Minal Amma saita mazge, Baby ce tariko hannun Bilal tace "Yaya mushiga ko"
Gid'a kai kawai yayi ya bud'e mota suka fice, wani Room ne me kyaun gaske Baby takai Bilal, tace "yaya kaje kayin wanka"
Rungumeta yayi sosai kamar zai mayar da ita ciki, yace "yau ranar farin cikine a rayuwata Nabeela, na dad'e banyi farin ciki irin na yau ba, Saidai bakin cikina d'ayane shine Minal tana tsananin fishi dani ina tsoron kada ta gudu tabarni kamar baya, bazan iya jurewa ba, mutuwa zanyi"
Riko hannunshi tayi tace "gaskiya Yaya Minal bata sonka amma zanyi iya bakin kokarina domin naga ta soka fiyeda yanda kake sonta"
Murmushi kawai yayi yace "Allah yasa"
"Ameen"
"Minal tana shiga d'aki ta wuce toilet ruwa ta kunnawa kanta yana jikata ko cire kayan jikinta batayi ba, wani irin abune ya tokare kirjinta, tarasa mema yake mata dad'i, Sallama Baby tayi taga ba kowa d'akin karan ruwa taji a toilet hakan yabata tabbacin Minal rana wanka, zama tayi a gefen katifa tana jiran fitowarta,
Minal saida ta gaji Dan kanta kafin ta cire kayan jikinta tayi wanka, towel ta d'aura ta fito fuskarta a had'e kamar bata tab'ayin dariya ba, Baby tana kallonta saida gabanta ya fad'i domin bata tab'a ganin Minal a wannan yanayin ba, ita har tsoro ma take bata, Minal ganin Baby zaune yasa ta kara had'e rai taci gaba da sabgoginta, Baby ma ganin haka yasata share al'amarinta itama taci gaba da harkokinta.
Mommy ce ta leko tace "kufito duka muci Abinci"
Dafari Minal taso tayi gardama Amma saita tuna matsayin Mommy a wurinta, tashi tayi jikinta sanye da Bakin dogon Riga da gyallenshi 'yar karama ayi rolling na kanta, wayarta ce Babba a hannunta tana wasa dashi, fuskarnan kamar bata taba'a dariya ba, suna zuwa wurin dining Lokacin Bilal yafito daga site nashi, jikinshi sanye da Bakin Riga da wando iya gwiwa baki, zubawa Minal ido yayi, Amma ganin yanayinta yasa baiyi gigin yimata magana ba, Minal satar kallon shi tayi taganashi da bakin kaya, juyawa tayi ta koma d'aki kowa yana kallonta, canja Riga tayi daga baki zuwa fari, lokacin data fito kowa saida yayi mamaki saidai babu Wanda ya tambayeta dalili, Bilal dariya yayi, ya zauna akan kujera, Kowama ya zauna aka fara cin abinci, tsakuran abincin kawai Bilal yake, idan yaci cokali d'aya saiya kalli Minal, ita Minal ko d'ago kanta batayi ba, tana jin ta koshi ta mike tace "Alhamdulillah"
Daddy ne yace "tsaya munada magana idan mun gama cin Abinci kinji"
Minal saida taji zuciyar ta ta bata sauti kafin tace "to Daddy bari na zauna a can" tayi nuni da kujeran cikin falo, zuwa tayi ta zauna, tana sake sake acikin zuciyar ta, "yanzu idan sukace nakomawa Bilal ya zanyi? Gashi banason yin musu dasu sabida iyaye na d'aukesu koba komai sunyi min halacci" tunani kala kala take har suka gama cin abinci kowa ya dawo falo, Daddy ne yayi gyaran murya yace "Minal lokacin da kika bani labarin mijinki nayi wani tunani Wanda ban fad'awa kowa ba sai zuciyata, Babu makiyinka dazai so ka samu lafiya, kince mijinki shine yakaiki India aka gyara miki ido, to idan baya sonki kina ganin zai fita dake ayi miki gyara?"
Shiru Minal babu magana.
"Bama wannan ba, akwai wata muhimmiyar magana da Hajiya tace zatayi, Hajiya muna sauraronki"
Mommy tayi shiri d'akin ma yayi shiru, sai Bilal daya zubawa Minal ido kamar zai had'iyeta, saidai ita ko kallo bai isheta ba,
Mommy tace "Bilal banyi tsammanin kana Raye ba, lokacin da mukayi hatsari doctor yakiramu a d'aki yace mana idan har munason rayuwarmu to dolene muyi pretending akan mun mutu, sabida yaya Babanka daya sameshi yace koda bamu mutu ba to yanaso ya kashemu zai bashi makudan kud'ade, lokacin da aka kiraka awaya muna sane, sai daga baya akayi mana Alluran suma, nasan zakayi mamaki yanda mahaifinka yakasa ganeka, bai sanka ba, To lokacin da mukayi hatsari yasamu tab'in hankali a dalilin haka ya manta komai, hatta nida Nabeela kanwarka saida ya manta mu, da kyar muka Gina sabon rayuwa dashi inda yake kiran Nabeela da Baby, lokacin da muka buge Minal a India to munje checkup na Mahaifinkane ana bashi magani yana d'an samun sauki a hankali, har Likita yace zai iya dawowa hankalinshi, muna zuwa India bayan wata uku uku, yanzu mahaifinka yatara company da Dama acikin Abuja, munyi nesa dakaine sabida gudun kar Yayan Babanka ya gane muna Raye, sai gashi ta sanadiyyar Yarinyar daka wulakanta Allah ya had'amu, Minal yarinya me hankali Kabiyewa Yayan Mahaifinka kuka wulakanta ta, naji haushi sosai daya kasance Bilal d'ina shine ya wulakanta baiwar Allah me hakuri"
"Bilal dukar da kanshi yayi kasa, kamar yanda Minal ma tayi"
Mommy tace "idan har kun sasanta tsakaninku to mubaahirye muke da Baku gudumawa, idan kuma Minal taki tofa babu Wanda zaiyi mata dole saika hakura ka bata takaddar saki" A firgice Bilal ya d'ago kai yana kallon Mommy, cikin in ina yace "Mom....mom..mommy saki kuma?"
"Eh mana saki ai itama tanada 'yanci"
Daddy ne yace "haba Hajiya ya kike urta Kalmar da Allahma bayaso, itafa saki idan an ambaceta al'arshin Allah girgiza take, keda zakiyi Fatah Allah ya sasanta tsakaninsu"
Mommy tace "idanfa bataso baza ayi mata dole ba"
Daddy yace "to Amma ai kinsan ba'a saki da ciki ko? Koda zasu rabu sai bayan ta haihu"
Bilal ne ya d'ago kanshi yace "ciki kuma Daddy?"
Mommy tayi wup tace "eh ko bakaine kayi mata fyad'e ba?"
Minal wani irin kunya ne ya lullub'eta, Baby dariya maganar ta bata, shikuma uban gayyar sai kallon Minal yake kamar ya had'iyeta Dan farin ciki, Mommy tace "tashi kutafi my daughter's"
Tashi sukayi Minal duk ta kasa had'a ido da mommy.
Bilal ma mikewa yayi yawuce site nashi yanajin farin ciki,
Baby tana dariya kasa kasa tace "gaskiya maganar fyad'ennan ta dami Mommy, kuma batasan d'anta ne yayi ba"
Minal turo baki tayi tafara Marin Baby, Dariya kawai baby takeyi.
_bayan kwana biyu_
~Bilal ne kwance akan gadonshi yayi rub da ciki, abun duniya sun taru sunyi mishi yawa, yayi farin cikin had'uwa da iyayenshi yayi farin cikin had'uwa da Minal ga uwa Uba cikin datake d'auke dashi shiyafi komai sashi farin ciki, to Amma abinda yafi daminshi shine yanda Minal ta d'auke mishi wuta, ko kallon arziki batayi mishi, idan tsautsayi yasa suka had'a ido to da Sauri zata d'auke kanta, batason zuwa inda yakema, Tin yana ganin abin kamar wasa gashi har yana daminshi, yanason yaji d'umin jikinta, yayi missing nata sosai, pillow ya jawo ya rungume a jikinshi kanshi yana kallon silin, tunanin mafita yake Amma yakasa samu, sai da yayi wata tunani kafin ya saki murmushi Wanda shi kad'ai yasan ma'anarshi.
'Bangaren Minal kwance take ta d'aura kanta akan pillow, tunani take sosai yanda take jinshi aduk lokacin da suka had'a ido wani irin abune yake bin jikinta, tarasa menene saidai ta ajiye a matsayin tsanar datayi mishi ne.
Da dare bayan kowa yaci abinci, su Minal suka koma d'aki saida sukayi hira sosai kafin kowa ya tofa Addu'a suka kwanta, sunyi Nisa a bacci sai Baby taji ana buga musu kofa, "wayene?" Taji shiru mike tayi taje tayi bismillah kafin ta bud'e, Bilal tagani tsaye yana mata murmushi "yaya Bilal..." Shiiiii yafad'a ya janyota waje yace "karki fad'awa kowa fa, nasan ke kad'aice zaki taimaka min, wallahi Nabila ina cikin matsala yau idan banji ta kusa daniba zan iya samun matsala, kiyi hakuri ki koma d'akina pls ki kwana a can da ssassafe kizo sai in koma na tabbata bazata ganeba"
Baby ya bata tausayi sosai abinka da d'an Uwa tace "to yaya Amma fa karya gane"
"Bazata ganeba Nabila ki kwantar da hankalinki kinji?"
"To yaya"
Peck yayi mata a kumatu yace "gud nyt", murmushi tayi tace "karfa kayi mata komai" tana fad'a ta gudu, Bilal tsayawa yayi yana mamakinta yaushe ta palle haka?"
Shiga d'akin yayi yanajin farin cikin zaiga beautynshi,
Yana zuwa ya
Ganta kwance tana bacci cikin kwanciyar hankali, ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe idonshi yanajin dad'i, hawa gadon yayi ya janyota jikinshi, lumshe idonshi yayi yana shakan kamshin turarenta me sanyashi nishad'i, hulan kanta ya zame yana shafa gashin kanta me laushi da kamshi, hannunshi yafarayin kasa dashi yana shafa wuyarta in a romantic way, Minal cikin bacci taji kamar ana shafa mata jiki tayi kamar zata tashi, Bilal ganin haka yasashi komar da ita ya kwantar iska yafara hura mata a kunne yana shafa duk jikinta a hankali yanda zataji dad'in bacci, Minal Dad'in yanayin takeji hakan yasa ta rungumeshi sosai tana bacci cikin jin dad'i, Bilal ganin haka shima ya rungumeta kamar zai mayar da ita ciki, cikin bacci ta d'aura hannunta a kanshi tana yamutsa gashin kanshi, Bilal da bacci yafara d'aukanshi yaji hannunta a jikinshi, a take yafara Neman natsuwarshi ya rasa, "Ruwaaaa" shine abinda tafad'a cikin muryan bacci da shagwab'a, Bilal saida tsikar jikinshi ya tashi jin yanda tayi maganar, daurewa yayi ya tashi cikin sand'a ya bud'e bedroom freezer ya d'auko Goran swan yadaqo inda take, d'agata yayi ya fara bata, A hankali take sipping harta kawar da kai Alamar ya isheta, komawa tayi ta kwanta shima aje Goran yayi ya janyota jikinshi ya lullub'esu da bargo me laushi, yana shafa hannunta har bacci b'arawo ya saceshi.
*Asuba tagari*
~Minal ce tafara bud'e idonta a hankali, juyawa tayi gefe tana kallon yanda Baby ta rufe fuskarta da bargo, hannu takai zata tasheta sai tayi wani tunani kawai ta kyaleta, Bilal kuma yanajin lokacin data farka Hakan yasa ya rufe fuskarshi da bargo, saida yaji tashiga toiletkafin ya dirka akan gadon ya fice,
Yana zuwa wurin corridor yaga Mommy tsaye tana waya, cak ya tsaya yana kallonta , lokacin Baby ta fito daga site nashi.
✔ote & comment
*Wattpad*
_@jiddah S Mapi_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Page 42...
By
Jiddah S Mapi
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociatio
~tsayawa sukayi cakk ganin mommy awurin, Mommy tad'an juya baya kenan taga Baby tsaye tana wawware ido, "ke zonan" jikin Baby ne yafara rawa cikin tafiyan marasa gaskiya ta karasa wurinta "meya faru kike waremin ido?" Baby shiru tayi mommy cikin tsawa tace "ba tambayarki nake ba?"
"Am..am mommy dama naje tambayar yaya ne me za'a dafa mishi"
Kallonta mommy tayi daga sama har kasa tace "banason karya kifad'amin gaskiya"
"Wallahi gaskiya nafad'a miki mommy, yayan yana bani tausayi naga ya rame dayawa yana bukatar kulawa"
"Ok jeki ai shiya jawa kanshi, yayi wasa da dmarshi"
Wucewa Baby tayi batace komai ba Dan tasan halin Mommy yanzu zata bubbugeta, ajiyar zuciya Bilal ya sauke yanajin dad'i mommy bata kamashi ba.
_bayan kwana biyu_
"Bilal ya gaji da halin ko in kula da Minal take mishi, hakan ya kudiri aniyar yau ko ana ha maza sai sun shirya, tashi yayi yaje d'akinsu Da Baby, yana zuwa yayi knocking bai jira an amsa ba yashige lokacin Minal ta d'aura kanta akan cinyar Baby tana tsife mata kitso, d'ago Kansu sukayi suna kallon wanda yashigo, Bilal ne tsaye ya jingina da jinkin kofa idonshi akan Minal, Minal ganin irin kallon dayake mata yasa ta dukar da kanta, a hankali yafara takawa har ya iso wajen dasuke, kneel down yayi yasa hannunshi a kunnenshi yace " Minal na tuba, wallahi bazan karayi miki abinda bakya soba, nasan Mommy tayi farin cikin kasancewarki surukarta, ta baki wannan damar ne sabida bataso ta tauye hakkinki, Minal wallahi ina sonki, ina sonki har cikin zuciyata, nasha wahala lokacin da kika gujeni" hawayene yafara fita a idonshi, Cikin muryar kuka yace "Dan Allah ki dawo gareni na horu iya horuwa pleaaasss"
Minal yabata tausayi to amma batada tabbacin wannan maganar dayake har cikin zuciyarshi ne, juyawa tayi daniyar ta gasa masa magana sai taga Baby tana share hawaye, jikinta yayi mugun sanyi ganin yaya da kanwa suna kuka a lokaci d'aya, tunawa tayi da irin taimakon da iyayenshi sukayi mata dakuma kanwarshi data sota kamar 'yar uwa, itama hawayene suka fara bin kumatunta, cikin kuka ta tashi ta itama tayi kneel down kamar yanda Bilal yayi ta rungume shi sosai tanajin Wani irin tausayinshi yanabin duk jikinta, Baby tana hawaye tana dariyar farin ciki, Bilal gani yake kamar a mafarki, shima rungumeta yayi tsab a jikinshi yana sauke numfashi, Baby ganin sun manta tana wurin yasata tashi taje wurin Minal a kunne ta rad'a mata "nagode sister kibashi kulawa na daban, kinsan an dad'e ba'a had'u ba"
Tureta Minal tayi, dariya Baby tayi ta gudu.
"I love you Minal
Bazan iya rayuwa babu keba, acikin jinina kike, I love you so much"
Minal lumshe idonta tayi tana sauraronshi, d'agata yayi ya d'aurata akan gado, rigar jikinta yafara d'agawa a hankali, saurin rike hannunshi tayi tace "me zakayi?"
Kallon cikin idonta yayi yace "babyna zan duba"
Minal janye hannunshi tayi tace "katafi site naka kada mommy tazo ta ganka anan"
"To ai kota ganni tasan wurin matata Nazo ko?"
Da kyar Minal tasamu yabar site d'in,
Baby ce tayi sallama tana dariya kasa kasa, "dariyar me kikeyi?"
Baby shiru tayi batace komai ba, Minal ta kuma cewa "ke yarinyarnan na kula Aure kikeso shiyasa kike maganar banza"
Dariya Baby tayi tace "ni ai gaskiya nake fad'a".
"Minal, Baby, Mommy, Daddy da Bilal sun had'u a dining suna cin abinci, kujerar Bilal tana kallon na Minal, kowa ya maida hankalinshi yana cin abinci, Bilal ne ya d'auko cokalinshi ya cire nama akan plate na Minal, d'ago kanta tayi tana kallonshi, signal yayi mata ya kashe mata ido d'aya, juyawa tayi tana kallon su mommy ganin basa kallonta yasa ta murgud'a mishi baki tayi farfar da idonta kamar wata yarinya, kallonta kawai yakeyi yana dariya, duk abinda suke akan idon mommy idan taga zasu kalleta saita kawar da kanta, saita kafarshi yayi daidai na Minal ya takata da d'an karfi "washh" shine abinda tafad'a, Daddy da Baby ne suka d'ago suna tambayarta "lafiya?"
"No ba komai abincinne da yaji"
Dariya Bilal yayi yace "to amma nawa babu yajifa"
Ko magana batayi mishi ba, ganin haka yasa ya faki idonsu ya janye plate nata ya tura mata nashi, harara ta zabga mishi ta janye nashi tahad'a duka biyu, tashi mommy tayi tabar wurin ganin abun Nasu bana karewa bane zuciyarta fal da farin cikin.
"Haka sukaci gaba da rayuwa Bilal yana nunawa Minal soyayya itama Minal ba'a barta abaya ba tana kula dashi daidai gwargwado, saidai idan taga Mommy sai tayi kamar ba ita ba, kamar koda yaushe Minal da Baby ne suke shirya breakfast a kitchen, Bilal ne yashigo cikin sand'a ya zagaye hannunshi ya d'aura akan cikin Minal kwantar da kanshi yayi a bayanta a hankali yace "meyasa kike gajiyarmin da kanki da kuma Babyna?"
Minal ture hannunshi tafara ganin Baby tana kallonsu, shikuma sai dad'a kankameta yayi, mommy ce ta shigo kitchen d'in daniyar karb'ar flask na tea, ganin Bilal ya rungume 'yar mutane yasata waro ido tace "kai bakada kunyane? A gaban kanwarka kake wannan abin?"
Langwab'ar da kanshi yayi ya kashe murya kamar wata mace yace "Mommy Babyna fa nake dubawa"
Minal ji tayi kamar ta nutse a kasa Dan kunya, takasa d'ago kanta ma, Mommy tace "Gaskiya abinnan naku ya isheni dama Daddynku yagina maka gida a can GRA ka tattara matarka Ku koma can, ke Minal!!! Minal shiru tayi, mommy tace "maza jeki had'a kayanki kafin yaronnan ya aikata abin kunya, kuma jiya naji kince kinason kije kiga mahaifiyarki to in Allah ya yadda gobe dukkanmu zamuje mu gaisheta"
Minal ta manta dawani zancen kunya d'ago kanta tayi da Sauri tana dariya tace "nagode Mommy"
Mommy tafiya tayi tabasu wuri.
~Da yammacin ranar Hamma Yarda da Inna ne suka sauka a garin Abuja, gidansu Baby sukaje, suna zuwa Akayi musu tarba me kyau, Hamma Yarda sai dube dube yake yanason ganin Minal, amma baiganta ba har yaso ya tambaya sai kawai ya dake, b'angaren Minal kuma tana kwance akan gado ta had'a rai wai Ita tayi fishi Dan Bilal yace yanajin kunyar Umma, Bilal ne yashigo d'akin ya kwanta a bayanta, hannunshi ya zagaya dashi ta cikinta, cikin kunnenta yafara yi mata wakar kauye irin na soyayya, tin Tana dakewa harta ware tafara dariya, d'agota yayi yace "tibda kin sakko ki tashi ki shirya zan kaiki shopping kinji?"
Dad'i Minal taji ta tashi da Sauri ta Shiga toilet tayi wanka tana fitowa tashafa mai da hoda jambaki ja tashafa a 'yar karamar bakinta, dogon Riga na atamfa tasa da gyalle ja ta d'aura d'an kwali daidai goshi, jaka ta rataya tasa flat shoe, tareda feshe jikinta da Wani turare me kamshin gaske, Bilal ido ya kura mata yana ganin irin kyaun da Allah ya bata, juyawa tayi ta kashe mishi ido d'aya tace "nayi kyau?"
Lumshe idonshi yayi ya bud'e mata hannunshi alamar ta rungume shi, Turo baki tayi tace "pls mutafi kar muyi latti"
Kin bud'e idonashi yayi kuma bai sauke hannunshi ba, dataga da gaske yake yasa zuwa Inda yake, cikin Sauri ta rungume shi tace "shikenan ai saimu tafi"
Kemkem ya riketa yana sauke numfashi, cikin kunnenta yarad'a mata "kinyi kyau"
Murmushi tayi tace "na gode"
Mikewa yayi da ita a jikinshi yad'au makullin mota suka fara tafiya, suna ahiga falo Minal tafara janye jikinta daga nashi, shikuma yace ai baki isaba, Hamma Yarda ne ya d'ago kanshi sai ganin Minal a jikin Wani namijin waro ido yayi yace "mommy waye wancan?"
Tambayar ta bawa mommy mamaki tace "mijin Minal ne shine d'ana danake Baku labari" a hankali ta labarta musu abinda yake faruwa, Jikin Hamma Yarda yayi sanyi sosai Sannan yaji zuciyarshi ta karye, lalle yayi hutun jaki da kaya yanda yasa rai zai
Auri Minal sai gashi Wani ya rigashi, Allah mai iko, Minal ce ta karaso wurinsu tana dariya da farin cikin ganinsu cikin murna tace "Hamma yarda yaushe kazo?"
Dakewa yayi yace "mun d'an jima anan, ya kike?"
"Lafiya lau ya Adamawa?"
Yace "Adamawa lafiya lau ya mijinki?"
Bataji dad'in tambayar dayayi mataba a hankali tace "gashi can lafiyarshi kalau"
'Dago kanshi yayi suka had'a ido da Bilal murmushi Bilal ya Sakar mishi, shima murmushin yayi ya Mika mishi hannu suka gaisa, Mommy tace "gobe ai tunda gakunan saimu tafi gaba d'aya ko?"
Inna tace "hakane zamuje duka"
_Washe gari_
Dukka Familyn suka Shiga Babban Mota sukaje Gombe wurin Mahaifiyar Minal, saidai Wani abin mamaki suna zuwa sukaga yanayin gidan ta canza daga gidan talakawa zuwa gidan masu kud'i, Minal ce ta zaro ido tace "kai gaskiya munyi b'atan hanya ba nan bane"
Bilal ma abin yabaahi mamaki, Sunyi parking domin tambayar gidan sai ganin wata mota sukayi yashigo layin, daidai kofar gidansu Minal motar ta tsaya, Latif ne yafito daga motar, jikinshi sanye da suited, yasa bakin glass, cikin Mamaki Bilal yace "kai nan nefa gidan mushiga dai mugani"
Dukka suka fito daga motar suka Shiga cikin gidan, Minal a bakin kofa ta tsaya tana tsoron had'a ido da Umma, saida Bilal yayi da gaske kafin ta yadda ta b'uya a bayanshi suka Shiga, suna shiga sukaga Umma zaune akan kujera tana shan Maltina gefe d'aya kuma Latif ne yake zaune yana danna waya, minal ce tafara sallama, Umma d'ago kanta tayi tace "aa minal 'yar Autan mata me miji sai yau kika tuna da uwarki? Koda shike ai kin samu gidan masu kud'i kina cin kaji da kayan sanyi, sannu da kokari, nima Allah bai barni hakaba Yabani d'a me hankali da kula dani kuma shine wanna tayi nuni da Latif.
"Minal ce ta zube akan gwiwowinta tace "Umma na tuba wallahi nayi hakane sabida wasu dalilai, nayi hakane sabida inason a kama Alhaji Umar ace ana sace matar d'anshi inason a kamashi da laifi a kullezhi ko za'a tsira daga zalunci da cin amana irin nashi, Cikin kuka ta fad'awa Umma duk abinda yake faruwa da Wanda yariga yafaru, Umma jin wannan bayani ba karamin rikita ta yayaiba , juyawa tayi gun Bilal tace " to amma meyasa bakayimin bayani da wuri ba?"
Bilal dukar da kanshi kasa yayi domin shi kunyar Umma yakeji sosai, Umma ce ta mike takawo ma su Hajiya da Daddy tabarma tanayi musu sannu da zuwa, Cikin fara'a suka Amsa, Baby waccetunda suka Shigo ta d'aura idonta akan Latif taji zuciyarta ta buga , Latif ma satar kallonta yake tayi tin d'azu lokaci d'aya yaji ta gudu da nutsuwarshi, Bilal ne ya bugeshi yace "da Allah ka daina ganemin kanwa wannanfa itace Nabeela"
A kid'imeLatif yatashi yana Kallon baby cikin mamaki yace "are you serious?"
Bilal ne yayi mishi bayanin komai, Latif yace "kai vary surprise to Amma meyasa tafi da kyau yanzu tazama fresh"
Bilal dariya yayi yace "saiba ka zuba mata ido shiyasa"
Dariya Latif yayi yace "to ai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 14