Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
akan kujera tace zauna anan nahad'a miki ruwan zafi kiyi wanka kozakiji sauki, dakyar ta amsa da to, bayan Umma tagama had'a ruwan tazo tarike hanun Minal ta kaita band'aki cike da tausayi, yawwa Minal tawa yi wankarki ko, har Umma ta juya zata fita taji Minal tace "Umma kitaimaka kimin wankar idanuna basa gani kuma kinsan ina period bansan yanda zan gyara jikina ba, nasan awannan lokacin ke kad'aice zaki iya kula dani yanda yakamata, jin haka yasa Umma taji wasu hawaye masu d'umi suna sauka a idanunta, juyawa tayi takoma cikin toilet d'in tareda rungume Minal suna kuka, ahankali tafarayi mata wankar harta gama ta kintsa mata jikinta suka fito, magani Umma tabata bata dad'eba bacci yad'auketa, Wasu hawaye Umma ta goge cikin sanyin jiki tafice a d'akin". " Latif ne zaune a office nashi shida wani manager d'inshi suna tattaunawa akan wasu kwangila dazasu d'auka, tura kofan office d'in akayi batare da excuse ba! police? Cewar latif yes police what happened, are you scared? Cewar wani police yana zazzare idanu, Meyafaru zaku shigomin office ko excuse babu? Idan mukaje station zakaji meyafaru amma yanzu ba abunda zance maka sai you are under Arrested!!! Menayi daza'a kamani? Arasa inda za'a kamani sai a office nawa ai mutane zasuyi zaton sata nayi koba hakaba manager? No..no..no Mr Latif basai katambayi manager naka ba abunda kayi ai gara Wanda yayi sata, Enough!! Kada ka kara dangantani da b'arawo intact ba inda zanje, baka isaba Mr Latif hasalima bazaka ja da hukuma ba komai taurin kanka, Haka aka kama Latif mutane sai binsu da kallo suke". Bilal kanshi yakulle kuma yaji labarin an kama Latif amma babu yanda zaiyi, haka yahakura kullum yana kan bincike amma har yanzu be gano komaiba, Zaune yake a garden yauma kamar kullum sanye yake dawani Kaya me launin ja da fari bakin glass yasawa fuskarshi Wanda ake kirada half face sandarshi yad'aura akan cinyarshi yana d'an wasa dashi, abun duniya yataru yamishi yawa, yana cikin tunani yaji an rike mishi fuska da Alama hannun mace he kuma yasan baze wuce Afrah bace, cikin wani Bakin ciki dabai tab'aji ba yace Afrah banason rainin wayo ki kiyayeni niba sa'anki bane, shake murya tayi ita adole ta iya yanga tace "yayana ya akayi kasan nice kodai kafara sona ne?" Ranshi ne yayi mugun b'aci, afusace yace ba dole naganeki ba kullum turare d'aya kike anfami da ita tin yana kamshi harya fara wari, Aduniya babu abinda Afrah ta tsana sama da ace mata tana wari wannan Kalmar tana matukar b'ata mata rai, itama Afusace tace "ai garani ansan turarene kuma Ina ganin komai kai kumafa? Makaho Wanda ze kare a makanta....karki sake kib'ata min rai Afrah idan raina ya b'aci kinsan banida kyau...sai me? Idan rannaka yab'aci adane nake tsoron b'acin ranka amma yanzu uban kuturuma yayi kad'an, ni kike zagi Afrah? Kai kuturu ne? Ai uban kuturu nace ba uban makaho ba. Okay tinda ke mayya Ce ai makaho sai makauniya Dan haka yau zancewa Daddy yanema min mata makauniya daidai ni kafin wani jumma'a zan nuna miki halin makafai. Idan kafasa ba'a yanka ragon sunanka ba Bilal. Kayi Aure gobe zan San kacika Bilal Umar Me Gold, Alokacin zansan ba'ayi asarar haihuwarka ba, Bilal Idan bakayi Aure gobe ba babu zuciya a kirjinka, matsowa tayi dab da kunnenshi tace Bilal gobene zaka zab'i sunan dazan kiraka dashi d'an Halak ko d'an Haram Am waiting for your decision". โœ”ote & comment Jiddah S Mapiโœ๐Ÿป *ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…* ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ *MAKAUNIYA CE* ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ By Jiddah S Mapi *___________________________________* *๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 10 Tana gama fad'in haka tajuya tayi tafiyarta, Bilal kuwa jiyake kamar yabita ya lakad'a mata dukan tsiya, Amma idan yayi haka Asirinshi ze tauno, gyara zama yayi azuciyarshi yace "Afrah ce take fad'a min magana son ranta? Yaushe aka haifeta lalle saina nuna mata ni d'an halak ne bad'an haram ba da wannan tunanin yatashi yabar wajen" Da dare kowa ya hallara ana cin abinci Bilal yace Daddy ina Neman wata Alfarma awajanka, Fad'i duk abinda kakeso nayi maka alkawarin zanyi maka, Daddy dama inason gobe ad'auramin Aure! Baki Hajiya babba tabud'e cikeda shinkafa tace Bilal yaushe kazama d'an iska? Aure kake roka ayi maka Gobe? Shikenan Bilal ka gama damu Kazama d'an iska, Wani irin bakin ciki Bilal yaji Hakika badan Hajiya babba tana matsayin kakarshi ba babu abinda ze hana yau ya sauke mata mari, Daddy ne yakatse mishi tunani tareda cewa "Bilal meyasa kakeson kayi Aure gobe kanada wata matsala ne? Shiru Bilal yayi daga bisani yace Aa Daddy kawai makauniya nakeson na Aura kuma gobe nakeson anemota, Makauniya? Bakada hankaline Kana makaho ka Auri makauniya? Da sauri Hajiya babba ta Karb'i zancen dacewa yanason yamayar mana gida gidan makafai shiyasa kaga shi makaho matarshi makauniya 'ya'yansu makafai shikenan gidan yazama na makafai....Ya isa, Hajiya babba kidaina min shishigi a lamurana ni nace inason in Auri makauniya toke ina ruwanki? Meye had'inki dani wai? To Wallahi idan ba'a nemamin makauniya gobe na Aura ba to zan bar gidannan." Da sauri Daddy yakatsar dashi no...no...no ba maganar Barin gida insha Allahu gobe za'a nema maka, Hajiya babbace tafara bala'i ta inda take shiga batanan take fitaba, ace za'ayi Aure a waje bayan ga yarinya agida meye laifin Afrah yarinya kyakkyawa ga tsayi ga jiki kamar matan samudawa ga hanci kamar indiawa ga zakin murya kamar larabawa ga ilimin boko kamar turawa. Haka takarashe surutunta babu Wanda ya tanka ta saima Daddy dayake kashe mata ido taki koda kallonshi, Afrah Kuwa tarike cokali cikeda shinkafa takasa ajiyewa takasa sawa abaki sai bin Bilal take da kallo kamar wata zararriya, Bilal ne yad'an saci kallonta yanason ganin abinda Hajiya babba ta lissafo cewa tanada shi amma baiga komai ba. Sai Jikin datake dashi kamar biredi,dariya yayi azuciyarshi yace Allah yakyauta. Minal tad'anji sauki Amma har yanzu bata mike yanda take ada ba saima kara yauki da take, Ummace tace "Minal ki rinka yin Abu da karfi mana meyasa kika cika raki da yauki ne haba, dama gaki kamar sandar sunuka kuma kina kara lalata kanki da kasala" Minal Ce tad'an ciji leb'enta nakasa kad'an tace to Umma ai Allah ne yahalicceni tsiririya haka kawai sai ayita cemin sandar sunuku? Takarashe maganar cikin tura baki da rirrintse idanu, ita adole an zageta. Shikenan to Minal d'ita kinsan fa banason kiyi fishi, kid'anyi dariya kad'an to ko hankalina zai kwanta, kara mak'e fuska tayi tana fuffura hanci ita aduniya ba abinda ta tsana Kamar ace ita tsiririya abun yana b'ata ranta matuka, Kumafa idan kaganta kamar abarwa iska tsabar rashin Auki, da kyar Umma tasamu tafara dariya haka sukayita hiransu, cikin hiran nasune Umma take cewa "nikam Minal bakida saurayine?" Shiru Minal tayi nad'an wasu lokuta Kafin tace Umma nibanida saurayi Madina tacemin inada kyau kar in kula kananan samarai, kumani wad'anda suke cewa suna sona daga Isa me rake sai wani me siyarda Dankali abakin kasuwa, kumafa Umma dankalin ba d'anye ba dafaffe mamanshi take mishi yake kaiwa Bakin kasuwa kato dashi. Haba Minal ina laifin me sayar da Dankali? Ko Dankalin ba sana'a bane ba? To banason buri banason araina mutum duk Wanda yazo miki kirikeshi hannu bibbiyu kina Jina? Tura Baki Minal tayi kafin tace "To" mikewa tayi tana surutu azuciyarta duk iya kwalliyanta ace me Dankaline yake sonta dame rake? Dankalinma ba d'anye ba dafaffe. Idan suka karamin magana saina had'asu da Almajirai suyi musu dukan tsiya, idan yaso naraba musu Alale ladan duka. Daddy duk ya rud'e ina za'a samu makauniya Kafin gobe? 'Dauko wayarshi yayi yakira Alhaji Nura, kana inane? 'Dayan b'angaren aka amsa da ina office, OK muhad'u A Farm house nawa, ok. Bayan wasu lokuta Alhaji Nura da Daddy suka had'u a Farm house, Bayan sun gaisa Alhaji Nura yake cewa lafiya kuwa naganka acikin damuwa? Gyaran murya Daddy yayi Kafin yace "wato Alhaji Nura lamarin Bilal yana d'auremin kai, yau kawai yazomin da zancen yanason gobe gobe ad'aura mishi Aure da makauniya idan bahakaba zai bar gidan" Wani irin dariya me sauri Alhaji Nura yayi Kafin yace "shine Dama maganar? Ai fad'uwa tazo daidai dazama, idan ya Auri makauniya ai bakuda matsala, ita bagani takeba balle idan taga anyi Abu babu kyau tafad'a mishi, kaga zaka kama tsuntsu biyu da tarko d'aya, nafarko dolene yakara Aure idan matarshi tahaihu sabida kula da yara kaga saika Aura mishi Afrah, nabiyu zega kamar kanasonshi tinda har kayi mishi abinda yakeso kaga ze mallaka maka komai nashi" Dariya Daddy yayi tsabar farin ciki shiyasa nakeson shawara dakai Alhaji Nura, kana saurin gane abu to Amma samun makauniyar shine matsala ni ina zan samu makauniya? Wannan ba damuwa bane Akwai wata yarinya datake sayar da Alale a company da tanada ido amma yanzu ta makance zanyi magana da mamanta, Nagode Alhaji Nura Allah yabar zumunci, Allah yakara had'a kanmu, Ameen cewa Alhaji Nura nan sukayi sallama kowa yatafi gida. "Latif yana cell babu abinda ake gana mishi sai Azaba, kuka yake yana rokansu sufad'a mishi abinda yayi Amma sunki fad'a, tin yana rokansu harya fara gajiya yayi shiru yana kallonsu, Wani babban police ne yashigo yana tambayansu ya Amsa laifin shine? No yallab'ai wannan yanada taurin kai yaki fad'an komai cewar wani police me katon tumbi da gashin Baki, OK kubarni dashi kuje kuyi aikinku zanyi mishi wasu tambayoyi, Fita sukayi akabar Latif da DPO sannu Malam Latif cewar DPO dakyar Latif ya Amsa da yawwa, Malam Latif inason kafad'amin gaskiya domin gaskiyarka shi zai fitar dakai anan, sabida ni bana d'aurewa karya gindi kaji? Kai Latif ya gyad'a mishi cikin Azaba da fitan hayyaci, Yawwa shin Malam Latif Kaine ka aikata abinda ake zarginka dashi? Bansan me nayiba, Ok bazaka fad'i gaskiyanba kenan?Alright may be haka shirya barin nan dawuri ba, Wallahi bansan menayi ba, enough! kana nufin kace bakai katura akashe Bilal abokinka ba? What!!! Bilal natura akashe? Bakai kad'aiba harda Ubanka shima yau anan ze kwana saikun gane kuskurenku, Latif mamaki yahanashi magana sai kawai yazubawa DPO na mujiya yakasa koda kwakkwaran motsi tsabar girgizan dayayi, DPO yakira sauran ma'aikatan yace kuci gaba da dukanshi har sai yafad'i bakinshi, haka suka fara dukan Latif Baji bagani, DPO yana fita aka kirashi awaya yana d'auka yace Allah yataimaki Alhaji, yanzu fitowana daga wajenshi bakaga yanda yayi laushi ba, d'ayan b'angaren akace ka kara bashi wahala sosai yanda zebar duniya cikin sauki, Dariya DPO yayi yace kaga Musa afili Fir'auna azuci wato kai Alhaji har yanzu baka daina mugunta ba? Cikin dariya Daddy yace zan daina ranar daka daina aikin d'an sanda, kace sai karshen rayuwarka? Dariya suka kwashe dashi Kafin DPO yace bari muje muci gaba da biwa jama'a hakkinsu, Daddy ne yace ko kuma kubawa Aljihunku hakkinsu ba, Kashe wayar sukayi suna dariyar mugunta" _Washe gari_ Alhaji Nura ne yaje gidansu Minal bayan sun gaisa da Ummane yace am dama wata alfarma nazo nema awajenki, Ummace tace wani irin Alfarma Alhaji? Alhaji Nura ne yayi dariya tareda cewa "nasan kinason 'yarki Minal ko?" Alhaji wazai haifi 'ya yaki? Hakane to inason kibani Minal gobe ad'aura mata Aure dawani d'an gidan uban gidana, nayi miki Alkawarin zan fitar da ita kasar India agyara mata idanunta, sannan shima yaron makahone ammashi bamuda tabbacin warkewarshi sabida shi Acid aka watsa mishi idanun sun tarwatse, Shiru Umma tayi tanajin abinda yake cewa, ita harga Allah tanason taga Minal tafara ganin Abu kamar kowa to Amma..idan tayarda daga baya suka karya Alkawari fa? Alhaji Nura ne yace hajiya nayi miki Alkawarin bazan bari ta cutuba believed me, dasauri Minal tafito wacce take rakub'e ajikin kofa tana shafe shafen inda zatabi, Ummace ta tashi tariketa, rike hannun Umma tayi tareda cewa "Umma kitaimaka ki yadda ad'aura Auren yau wallahi ni nayadda indai za'a kaini Aduba idona, Dan Allah Umma nasan kina sona kuma zakiso kiga ina rayuwa kamar kowa takarashe maganar tana kuka sosai. Jikin Umma duk yamutu tana tausayawa 'yar tata sosai, kallon Alhaji Nura tayi tareda cewa na Amince Amma sai Baban yaron yazo dakanshi Kafin ad'aura Auren yau, Cikin farin ciki Alhaji Nura yace to...to..to insha Allahu yanzuma kuwa, nan yaciro bandir na 'yan dubu dubu ya ajiyewa Umma dafarko taki karb'a Amma yace kememe saita karb'a, godiya tayi shima yace ya gode nan yajuya yayi tafiyarsa yana me farin ciki, Umma Ce tacewa Minal 'yata bakya ganin kamar munason mu tafka kuskure? Da mahaifinki yana raye kina ganin zai yadda da wannan Auren? Minal tace Umma zai yadda tunda yanason farin cikina, to Allah yasa hakan yafi Alkhairi, Ameen Umma" Kuyi hakuri jiya nasa page 8 amaikon page 9 โœ”ote & comment Jiddah S Mapiโœ๐Ÿป *ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…* ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ *MAKAUNIYA CE* ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ By Jiddah S Mapi *___________________________________* *๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 11 Alhaji Nura yayi matukar farin ciki da Umma suka amince mishi, yana fita yakira Daddy awaya yafad'a mishi duk yanda sukayi tareda cewa saidai fa Alhaji sunce sai kazo dakanka, haba Dan Allah ni meze kaini bayan kasuwa anguwanda ko mai gadina bazai zauna acan ba bale inje wai Neman Aure kaidai kawai kugama Idan yasoma kace musu Kaine Uban yaron dukba matsalana bane, Aa Alhaji dolenefa saika sauke girman kai kafin kasamu abinda kakeso Awajen yaronnan ai Idan kazo dakanka darajarka zai karu a idonshi, dakyar Daddy ya yadda akan zaizo, to naji bani adreshin su, ai wannan babu wani adreshi bayan kasuwa kawai senta har kofar gidansu, cikin kosawa Daddy yace baga irinta ba, ace yaro bayajin magana, gashi zaiyi aure agidanda ko adreshi babu kuma Makauniya, kai Allah yawadaran. Kashe wayar yayi yatafi d'akin Bilal tareda yin excuse, yana shiga yaga Sabir zaune agefen Bilal yana duba wasu takaddu, Direct b'angaren Sabir yawuce, Sabir me kakeyi da takaddu batareda sanina ba? Am Daddy ai nina sashi yamin sign Takaddun wasu company ne dasuka kawo mana kwangila....haba Bilal meyasa bazaka aikamin ni nayi sign d'inba? Daddy ai sign bawani matsala bace Sabir ma zai iya, shiru Daddy yayi daga bisani yace "dama maganar Aurenkane yakawoni an samo yarinyar dazaka Aura yanzu ahakama gidansu zani muje ad'aura Auren Idan yaso daga baya saita tare koba hakaba? Aa Daddy ba maganar tarewa daga baya kawai Idan an d'aura yau to akawota yau...Bilal meyasa kafiye taurin kaine? Daddy kayi hakuri idana Dalili, bakada Dalili Bilal illa ka kuntatawa Afrah, bara nafad'a maka babu wacce tafi Afrah awajenka sabida ita 'yar uwarkace ta jini, yana gama fad'in haka yafice ad'akin azuciye, Sabir ne yajuyo yana fuskantar Bilal yace haba Bilal meyasa bazaka bishi yanda yakeso ba, Sabir babu ruwanka tsakanina da Daddy sai Allah yanzu zakaga mun shirya mun dawo normal, dariya Sabir yayi yace hakanefa kuma kunfi Kusa, yawwa gara daka sani" Minal yau tana cikin farin ciki, azuciyarta tace nakusa warkewa? Idona yakusa fara gani? Wayyo Allah na dad'i kasheni, ai Idan nayi Auren nan nadaina Fad'a nadaina Neman tsokana insha Allahu duk abinda akacemin inyi bazan tab'ayin delay ba tinda zasu warkar min da idona, ganin irin farin cikin datake cikine yasa Umma Amincewa da ayi Auren yau, Madina ce tashigo gidan da gudu tashige d'akin Minal, tana shiga tace "Minal wai dagaske kina Aure kuma yau?" Murmushi Minal tayi Wanda yabayyana dimples nata tace Eh Madina yanzuma an tafi d'aurawa waya fad'a miki? Daga wajen Isa me rake nake yace wai tinda an yaudareshi to mubiya mishi reken dayayi tabamu koya kai kara.. Idan yafasa kai karan ba'a yanka mishi ragon suna ba, Ke kinsan Isa da fad'a fa, Aa karene shi. Kinga abar maganar nan yanzu wa kike Aura? Nima ban sanshi ba! What? Baki sanshi ba? Kinada hankali kuwa? Kwarai kuwa inada shi hasalima nafiki hankali zasu kaini kasar wajefa agyara idona...Minal bakida hankali wallahi Amma Umma tasani? Madina kidaina cewa banida hankali hasalima Idan kika kara nuna bakya son Auren nan kece babbar makiyata, Minal karki tafka Kuskure arayuwarki, Madina zaki iya tafiya Idan shine abinda yakawoki Idan kuma kud'in Isa me rakene ya ajiyeki kije kice mishi bazan bada ba, yanda take maganan zakace wata jarumace, Allah yahuci zuciyarki, Ameen Cewar Minal" Bayan sallar Azahar aka d'aura Auren Minal da Bilal akan sadaki dubu d'ari, Da mangariba su Afrah ne da hajiya Salamatu sukazo d'aukan Amarya da gayya Afrah tace zata bisu domin tinda safe taketa ruzgan kuka, suna zuwa lokacin Umma tagama yiwa Minal fad'a da nasiha, Minal kinga halin damuke ciki kuma nasan halinki, inason kimin alkawarin zakibi dangin mijinki da mijinki sahu da k'afa duk abinda zasuyi miki karki rama kuma karki rike azuciyarki kinga da ace Ina rike abinda dangin mahaifinki sukayimin da yanzu bana raye da bakin ciki yakasheni......ina Makauniya takene? Tin d'azufa muke jiran afito da ita, muryan Hajiya Babba ne yake magana, Umma atake taji zuciyarta ta tsinka, Amaikon suce mata Amarya sai suce makauniya? To Allah dai yakyauta, Tashi muje Minal, to Umma Minal tafad'a tana kukan rabuwa da mahaifiyarta itama Umma dauriyane kawai Idan bahakaba tafi Minal shiga damuwa. Suna Fita cikin gida suka hango Afrah tayi kitson Attach har baya, tasa wani dogon Riga d'amamme kanta ba d'ankwali tana taunar cingom sai kallon mutane sama da kasa take, Hajiya babba kuma an rike kwankwaso kamar afilin dambe suke, Ummace takarasa da Minal tace sannunku dazuwa Hajiya..dakata bashi yakawomu ba, Ina Makauniyar? Shiru Umma tayi Kafun tanuna musu Minal gatanan, kinga malama ba Aljana mukace kinuna manaba makauniya mukace kibamu cewar Afrah, Itace makauniyar bakiga sanda ahanunta ba? Da sauri Afrah taja da baya ganin wata kyakkyawar yarinya rik'e da sandar makafai Idan kaganta zaka rantse ba makauniya bace, Murmushi Minal tayi cikin siririyar muryanta me sanyi tace ina wuninku? Dabamu wuniba Aida bakiji zuwanmu ba kiwuce mutafi malama cewar Hajiya Babba, Allah yakiyaye hanya Minal Umma tafad'a tana kuka, Hawaye Minal tashare tace to Umma kikula da kanki, Dama kunsan kuna sonta kuka sayar da ita kwad'ayayyun banza, Minal kuka kawai takeyi na rabuwa da Ummanta, ke kirufe mana baki kinsan kinason gidanku kikace zaki Auri d'anmu? Madina ce tazo dasauri tace Minal Ummace tace narakaki gobe sai indawo, To waya hanaki binmu gidanmu ai akwai abinci cewar Afrah, Shiru Madina tayi tana tunanin wani irin rayuwa Minal zatayi tareda wad'annan mutanen? Allah dai yakyauta. Sai bayan mangariba suka shigo G.R.A Madina sai ware idanu take tana kallon manyan gidaje, Daidai wani Babban gida Madina taga anyi parking sai lek'awa take tajikin window, Horn driver yayi megadi yazo ya bud'e musu suka kutsa cikin gidan. Madina sai kallon cikin gidan take azuciyarta tace "Minal Allah yasa nan gidan zamanki ne" Shiga cikin gidan sukayi har zuwa wani babban falo me d'auke da Kayan Alatu, kujerun d'akin kamar na sarauta suna shiga ciki Hajiya Babba tajuya takalli Madina tareda cewa saiki kaita d'akinshi tabaya yake, Idan kun b'ata Allah yasa ku gane hanya mukam munada abinyi ko Afrah ta? Haba Hajiya Babba yazakice suje d'akin yaya kinsan fa ni kad'ai yakeso kuma Idan sunje Koran kare zeyi musu kigan jikinsu mana very dirty, Aa Afrah barsu suje ai ba ganinsu zaiyi ba, Ke Aljana kitsaya a iya matsayinki karki wuce gona da iri acikin gidannan don gidan masu kud'ine Idan bakya gani kawarki tana gani zata fad'a miki, kazaman banza matsiyata, tana matsifa taja hannun Afrah sukayi d'akinsu. "Minal wannan wani irin rayuwane? Anya zaki iya zaman gidannan? Tabd'i wallahi saina fad'awa Umma yanda sukayi mana...Aa Madina Dan Allah karki fad'a mata mutanennan zasu kaini kasar turawa agyara idona kiyi hakuri madina kinji? Shikenan tinda kin zab'i wulak'anci akan Gata Allah yasa hakan yafi Alkhairi, Ameen Madina, Yanzu ina zamu farabi Minal bansan ko inaba gidan yayi girma dayawa, kibari kawai muzauna anan Allah zai kawo Wanda ze nuna mana," Haka suka zauna cikin falon har bayan isha babu Wanda ya tanka musu ga yunwa ga ishi Minal harta fara gyangyad'i saiga Hafeez yashigo falon Madina ce ta tashi ta sunkuya har kasa Ina wuni? Harara Hafeez ya bank'a mata meye hakan 'yanmata? Am.. Am Dama d'akin Wanda yayi Auren mukeson kanuna mana, Chewww Idan kunbi senta karku tsiya zakuga d'akin, yana fad'in haka yabar wajen yana dariya. Madina ranta yafara b'aci wannan wani irin wulak'anci ne? Minal nifa zan tafi gida bazan iya jure wulak'anci ba. Kiyi hakuri madina Idan kin tafi dawa zan zauna? Kiyi hakuri kawata. Suna zaune harsun fara bacci Sabir yashigo yaga mutane kwance akasa ga sanyin tyles bubbuga Jikin bango yayi yana tashinsu, Da Saudi suka mike atare yace "lafiya 'yanmata kukayi kwanciyarku akasa, Minal ce Wanda fuskarta ya kwab'e da janbaki tafara kuka tace, Nice Amaryan da akamin Aure da d'an gidannan, Cikin mamaki yake kallonta to amma meyasa suka barku anan? Kuma ai shi makauniya ya Aura, Nima MAKAUNIYA CE bakaga sandata ba? Shiru Sabir yayi yana kallonta gata kyakkyawa kamar India kuma idonta babu alamar ciwo, to Untyna muje nakaiku kidaina kuka kinji untyna? Share hawayenta tayi tace to mungode, D'akin Bilal yakaisu ya Ajesu afalo kuzauna anan bari nakawo muku Abinci ko Untyna? Minal tace to mungode, Aa kidaina godiya kefa untynace kinji Amaryan yayana? Rufe fuskarta tayi tana dariya" Wai hayaniyar me nakejine Sabir? Muryan Bilal ne sukajiyo acikin falon, da sauri Minal tamike jin muryan Wanda tafi kowa tsanarsa aduniya Wanda sanadiyyarshi tazama makauniya Mara galihu, Shima tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, wannan yarinyan me kamada Aljanun kuma me takeyi agidannan? Yakuma naganta da Sanda? kaddai itace Daddy ya Auromin? To ai idanunta lafiya suke, shikenan na d'ibo ruwan dafa kaina, yana cikin tunanin yaji tace "kamar muryan Bilal nakeji? Saura kad'an yace "mata eh saime?....amma bayason asirinshi yatonu, Madina ce tace eh Minal shi kika Aura shima naganshi da Sanda, Minal tace Allah shikara ai daba makaho yazama ba da gurgu ne mugu kawai, Bilal ranshi yab'aci yace " ke karkimin rashin kunya zanci Ubanki Idan kika rainani danasan ke za'a Auramin da saidai inmutu ba Aure k'azamar banza....haba yaya? Aina Kasansu dahar zaku fara fad'a kaida bagani kakeba? Cewar Sabir Wanda yashigo da Plates na Abinci guda biyu ahannunshi, Kame-kame Bilal yafara Am..Amm Dama naji suna hirane kuma ina bacci shiyasa nake musu fad'a, yaya ai dakasansu dako tsawa bazakayi musu ba kawar Amaryace da Amarya, yafad'a yana murmushi, Bilal ne yafara magana azuciyarshi shikenan nashiga uku na cuci kaina. Wannan me kamada Aljanarce mamata, wayyo Allah ya zanyi? Anya bazan janye Aurennan ba? (Nikuma nace waya fad'a maka ana janye Aure Bilal?) โœ”ote & Comment Jiddah S Mapiโœ๐Ÿป ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ *MAKAUNIYA CE* ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ By Jidda S Mapi Page 12... Yaya tunanin me kakeyi? Ai kamata ace kayi farin ciki tinda burinka yacika koba hakaba? Cewar Sabir, eh hakane Sabir ai yanzuma ina cikin farin cikin Kaine baka luraba, Sabir ne ya ajiyewa su Minal abincin Untyna kuci Abinci bismillah, zama sukayi suka fara cin abincin, kallonsu Bilal yayi tacikin glass d'inshi, azuciyarshi yace "wayaga Amarya da kawarta Allah yakyauta" Minal kuwa cikin ziciyarta tana tunanin yanda zatayi zaman Aure da wannan mugun mutumin, Idan nayi mishi rashin kunya nasan zasu fasa fitar dani kasar waje aduba idona, Idan nabishi ahankali kuma zai rainani dayawa ya zanyi? Madina taga cowslow dayaji bama da cocumber sai tura abincin take kamar ba gobe, Madina zafi nakeji kayan jikina sunyi nauyi wallahi bazan iya bacci ahakaba, to yaya kikeso muyi minal? Ina zan shiga in nemo miki kayan bacci? Idanun Minal ne yafara cika da hawaye tasan da tana gidansu da Umma ta canja mata kaya zuwa na bacci Amma yanzu haka zata kwana da kayan jikinta...kiyi hakuri Minal Idan yaso gobe saiki tambaya subaki ko? Gyad'a kai kawai Minal tayi, Suna gama cin Abinci Madina tafitar da plate d'in, suna hira kad'an kad'an har bacci ya d'aukesu awajen." Bilal kuma yana shiga d'aki ya kwanta agado yana tunani ya akayi yarinyannan ta makance? Wata kila garin Neman tsokana ta tsokano wanda yayi mata illah, tab'e baki yayi yace "Anyway matsalarta ce bata shafeni ba, kuma koda tana makauniya Idan tayimin raini sainaci ubanta" Shima ahaka bacci yad'aukeshi. Hajiya Babba kuwa aje Afrah tayi tana koya mata kissa da kisisina da munafinci kala kala saida ta tabbatar Afrah tahau layi kafin takyaketa sukayi bacci. _washe gari_ Minal ce zaune akasa tarike gyallen Madina kemkem tana kuka wallahi Madina babu inda zaki nasan Umma bazatayi fad'a ba, Minal wai bakida hankaline? Agidan mijinkifa kike ya za'ayi muzauna tare? Suna cikin haka Hajiya Babba tashigo d'akin wai ina Makauniyar take? Kinzo kin zauna ad"aki baki iya gaida mutane bane? Ko agidanku ba'a baki tarbiyya ba? Koda shike ina zaki samu tarbiyya awancan akurkin gidan, tashi Minal tayi tana cewa gani Hajiya kiyi hakuri, Bazanyi hakurin ba kifito kidafamin shayi me citta sabida nan gidan d'ana ne zanyi yanda naso. Madina haushi gidan yafara bata bata kara cewa komai ba ta d'auki jakarta sai tafiya, Minal batasan ta tafiba. Rike sandarta tayi tana

Chapter 4 of 14