Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Alhaji Nura tare muka fara kuma tare zamu gama" "Dakata, Alhaji Ba tare muka fara ba ko ka manta ne in tuna maka?" Daddy yace "OK Dan Abu yana so yablalce shine zaka barmin ko? To muzuba mugani nida kai shege kafasa" Alhaji Nura yace "muzuba mana sai me" kitt ya kashe wayarshi.   Daddy ne yafara juye juye acikin gida yakasa tsaye yakasa zaune, Hajiya Babbace ta leko ta side na parking space sai taga Daddy yana zirga zirga, da sauri ta karasa wurinshi tace "Umaru Lafiya kake kuwa?" Daddy ne yajuya idanunshi sunyi jaa yace "Mama? Yanzune ya kamata nad'au hukunci me zafi akan dukiyar Dana dad'e ina sa rai, Bilal yagano cewa ina mishi mugunta kuma inason dukiyarshi, Alhaji Nura ya juyamin baya har yana ikirarin cewa muzuba mugani, idan har na sake na kyale Alhaji Nura to hakika zaiyi b'arna sosai ta wajen b'atamin plan Dana dad'e inayi, kinsan me zanyi?" Hajiya babba tace "ina zan sani" Wata muguwar dariya Daddy yayi yace.   "Kashe Bilal zanyi da hannuna sannan in d'aurawa Alhaji Nura hakkin kisan akanshi, daganan sai in kwashe dukiyar inyi yanda naso, Mama nasan bakisan wani Abu ba ko? To yau zan fad'a miki wata sirri, Mahaifin Bilal da Mahaifiyashi da kanwarshi nine nayi sanadiyyar mutuwarsu a lokacin da sukazo gaisuwan rasuwar maman Sabir, nine na kwance birkin motarsu ta yanda idan sukayi tafiya me nisa dole zasuyi Accident, kinsan dad'in danaji lokacin dana ga gawarsu kwance akasa?" "Amma Umaru Ka samu tab'in hankali ko? Domin na tabbata kanka ba d'aya ba kake wannan maganar, dolene anjima muje Asibiti a dubaka" Dariyar rainin hankali Daddy yayi yace "idan kin yadda kaina ba d'aya ba to hakan yake, kirike wannan maganar domin koda wani tsautsayi ya gibta aka gano nine nayi kisan to duk Wanda yaji kaina ba d'aya ba dolene ya kyaleni koda ko Alkali ne" Yana fad'an haka ya juya yabar wurin yana dariya.   "Da sauri Latif ya danna stop akan wayarshi dayake d'aukan videon Daddy, jikinshi har rawa yake tsabar tsorata, da sauri ya karasa wurin motarshi. Daddy ne yayi dariya yace "sannu da d'aukan video Latif, yaro bakasan zafin wutaba sai ranar daka taka" Yana fad'an haka yaciro wayarshi yakira wata nomba, yace "Ku tsaya akofar gidana akwai wata bakar motar dazata fita yanzu, inaso kubishi har inda zaije idan yafito Ku nuna mishi bindiga yabaku wayarshi inaso Ku fasa wayar kuyi kaca kaca da ita kada kutab'ashi wayar kawai zaku fasa" Yana kashe wayar ya kwashe da dry.   Latif dad'i yaji daya samu yad'au videon "Allah yakawo karshenka Alhaji Umar" Yana zuwa kofar gida yaga wasu gardawa tsaye da bindiga a hannu, da sauri ya koma mota yana kokarin gudu, suma da gudu suka karasa wurinshi d'ayanne ya nunawa Latif bindiga yace "bringam your phone" Latif yace "me zakuyi da wayata?" "Ok tambayarmu ma kake? Zaka kawo ko saina tarwatsa maka kai da wannan piston d'in?"   "Latif ganin mutanen ba imani ne dasuba yasashi Ciro wayarshi yamika musu, yanaji yana gani suka had'a wayar da kasa, saida wayar yayi kaca kaca ba'a ganin komai kafin suka bar wurin, bakin cikine ya lullub'e latif shikenan sun b'ata mishi plan".    "Minal da Baby had'a kayansu suke domin da karfe 9Am zasu d'au hanya, Minal ce tayi baya baya ta fad'a akan gado tace "wash Allah na gaji Baby bayana har ciwo yake" tafad'a cikin shagwab'arta, Baby ce yayi dariya yace "Dama ai ke raguwace ba kad'an ba" Dariya Minal yayi yace "nice raguwar?"   "Eh mana ke ai mijinki yana tare da wahala ba kad'anba" Minal ma tayi dariya tace "shifa yanada shagwab'a sosai, kinga ai Nima zai barni nayi nawa" Baby tace "wato kinada saurayi kike b'oye min ko? To maza kibani labarinshi"   Minal dariya tayi tace "hmm zandai baki kad'an daga labarinshi, shi dogone fari yanada yawan sumar kai, yanada dogon hanci sannan bakinshi karami ne, idanunshi manya ne yana d'auke da gashin ido dogo dogo, yana yawan yamutsa gashin kanshi Wanda hakan ba karamin kyau yake kara mishi ba, yana d'auke da pink lips, idan yayi dariya kumatunshi lotsawa suke" Pillow ta janyo ta rungume sosai, lumshe kyawawan idonta tayi a hankali ta bud'e bakinta kamar batason yin magana tace "yanason kamshi sosai, yanada sexy eyes, ke idan nace zan baki labarinshi tofa zamu kwana mu tashi ban gama ba, sannan kinsan me?"   "Aa sai kin fad'a" Baby duk lissafin danake miki ni kad'ai nake kid'ana kuma ni kad'ai nake rawana, shi baisan ma inayi ba, kinga mubar maganar nan domin b'ata lokacine, shikuma lokaci abune me muhimmanci, sabida Allah ma yayi rantsuwa da Lokaci inda yake cewa acikin suratul Asr (wal asr) Allah yace nayi rantsuwa da lokaci, (innal insana lafi khusur) lalle mutane suna cikin Asara (illallazina Amanu wa amilussalihati watawa saubil hakki watawa saubissabr) saidai wad'anda sukayi Imani sukayi tawassali da gaskiya kuma sukayi tawassali da hakuri".   Baby tace "lalle Minal kinada ilimin addini inama ace nice ke, sabida iyaye yanzu sunfi baiwa ilimin boko muhimmanci akan ilimin addini, sun manta cewa shine zai Amfanemu a Lahira"   "Shiyasa nace miki lokaci yanada muhimmanci Baby, yanzu ma lokacin be kure miki ba zaki iya koya idan kikasa kai". ✔ote & comment   *Wattpad* _@Jiddah S Mapi_ *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Page 39... By Jiddah S Mapi *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociatio ~ ajiyar zuciya Baby ta sauke tace "kedai bari kawai sister" Minal tab'e baki tayi batace komai ba. _washe gari_ Su Baby sun sa kayansu a mota Hamma yarda ne yake tayasu yanajin ba dad'i Minal zatayi nesa dashi, kowa yashiga mota Minal ce kusa da window sun gama sallama da kowa, knocking na glass d'in akayi, Minal ce ta sauke glass tanason ganin ko waye, Hamma Yarda tagani tsaye ya zuba mata manyan idanunshi, ganin kallon yana nema yayi yawa yasa tace "lafiya Hamma yarda?" Kawar da kanshi yayi gefe, hannunshi yasa a Aljihu ya Ciro wata farar paper ya mika mata, bai jira ta bud'e ba ya juya yashhiga gida, Duk abinda suke yi akan idon Daddy, Murmushi yayi ya kawar da kanshi. Baby tace. "Irinsu ba'ason rabuwan nan" Mommy ce ta harareta, kama bakinta tayi tana dariya kasa kasa, Driver ne yaja mota suka d'au hanyar Abuja. "Bilal ya kwana da mugun zazzab'i, manyan idanunshi har sun kankance, lips nashi sunyi jaa alamar yanajin jiki, daidai da sallah a zaune yakeyi shima da kyar, yana cikin wannan halin Latif ya shigo shima fuskarshi da alamar Damuwa Sam baiji dad'in fasa mishi waya da akayi ba, yana shiga yayi sallama Amma ba'a amsa ba, karasawa yayi cikin bedroom Bilal ya hango kwance akan gado ya kudundune jikinshi da bargo jikinshi yanata rawar sanyi, Da gudu ya karasa yana tambayarshi "Bilal meya sameka?" "Bilal baya iya bud'e bakinshi, sai lumshe idonshi kawai yake, Latif ne ya Ciro waya da sauri yakira doctor, cikin minti goma sha biyar saiga doctor yashigo, duba Bilal yafara yana mishi gwaje gwaje, ruwa ya d'aura mishi tareda yi mishi Allura, a lokacin Bilal ya samu bacci, Doctor ne yacewa Latif "tin yaushe yafara rashin lafiya? Kun barshi saida ciwo yaci jikinshi kafin Ku kira doctor? Yanzu Abinda nakeso dakai ka rika kula da lafiyarshi kada kabarshi yana yawan tunani domin zai kawo mishi babban illa" Latif ne ya gid'a kanshi cikin jin tausayin Abokin nashi, magunguna Doctor yabashi yace "ga wannan ya rikasha akan lokaci" godiya Latif yayi ya biyashi kud'inshi, 6:30Pm daidai Bilal ya bud'e manyan idanunshi yana kallon silin, a hankali ya maida kanshi zuwa ruwan da yake hannunshi, tashi yayi da Sauri ya zame ruwan yana kallon Latif, Latif ne ya mike yace "Bilal lafiyarka kuwa? Kana gani fa ruwa aka sa maka kuma ka cire, bakason lafiyarka ne?" "Dama kun damu da lafiyata ne?" Latif cikin mamaki yace "wani irin maganane wannan Bilal? Lafiyarka ai abun Damuwa ne" Bilal ne ya tab'e baki ya mike zuwa toilet Dan ya watsa ruwa, Latif ma bece komai ba Dan yasan Halin Bilal tsab idan yace bazaiba to babu Wanda ya isa ya hanashi, Gashi Bilal tausayi yake bashi sosai ganin yanda ya rame ya kara haske kamar ba jini a jikinshi, Bilal ne yafito daga toilet d'in ya zauna a gefen gado yana shafa lotion nashi me kamshi ko kallon inda Latif yake baiyi ba, latif ne ya matso inda yake ya dafa kafad'arshi yace. "Bilal gaskiya kana bani tausayi, ada nayi niyan sai kasan darajar Minal kafin nafad'a maka inda take, Amma gaskiya lamarinka sai karuwa yake, kana ramewa sosai" Bilal ne ya zame hannun Latif cikin fushi yace "basai kafad'a min ba na hakura kawai" Latif yace "nasan bazaka iya hakura ba kana fad'a ne kawai, Amma dolene nafad'a maka, ranar Dana sameka a airport to aranar naga passport na Minal kuma na duba information akai sai naga an rubuta Abuja Maitama" Bilal ne yariko hannunshi idonshi ya cika da hawaye yace "Dan Allah Latif kar kayimin karya don samun lafiyana pls" Latif yace "ba karya nake ba gaskiya nake fad'a maka" Bilal ne ya mike yanufi wardrobe passport nashi yafara nema, zauje yayi visa. "Baby tayiwa Daddy maganar makarantar Minal, Daddy yaji dad'i sosai washe gari akayi mata register a makarantar su Baby, Minal tafara zuwa school rana ta farko harta fara gane Abu, 'yan mata sai zuwa wurinta suke wai sunaso suzama kawaye, Minal sai dariya kawai takeyi musu. "Bilal yayi visa gobe da sassafe zai tafi Abuja, Latif ne yace "Bilal yakamata fa kabi komai a hankali kada kayi gaggawa" Harara Bilal ya banka mishi baice komai ba yaci gaba da shirya kayanshi. _Guy's am seriously busy am trying my best to write in return just expects ur moment. .well if you won't comments I will not give update...silent readers pls comment....next Update when can't promise am vary busy, Thanks you All_ ✔ote and Comments *Wattpad* @jiddah S Mapi *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Page 40... By Jiddah S Mapi *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociatio ~had'a kayanshi yayi ko kallon inda Latif yake bai kara ba, yana gamawa ya Ciro waya ya sanarwa manager cewa kwana biyu bazai zo company ba, Latif da kallo yake kawai yake binshi, shi abun har mamaki yake bashi wai ace Bilal ne ya rud'e akan soyayya haka? "To Allah dai ya kyauta" "Amma Baby kina ganin karatu da cikin nan zaiyi kuwa?" Minal tafad'a cikin hawaye azuciyarta kuma tanajin Bakin cikin abinda Bilal yayi mata, Baby ce ta share mata hawayen tace "mata nawa suke karatu da ciki? Mata sunfi dubu, meyasa zaki tada hankalinki? Kowa da nashi kaddarar ki godewa Allah daya kawo miki naki ahaka" Minal rungume Baby tayi tana kuka, Baby bubbuga bayanta take alamar rarrashi, suna cikin haka mommy tayi sallama, ganin yanayinsu ba karamin tausayin Minal taji ba, itama karasawa tayi ta rungumesu duka tana rarrashinsu, saida taga Minal ta daina kuka kafin ta saketa, tace "Daddynku ne yace nakiraku" Mikewa sukayi dukansu sukabi bayan Mommy, suna zuwa babban falo Minal da Baby suka zauna a kasa inda Mommy kuma ta zauna agefen Daddy, gyaran murya yayi yace. "Am Minal? Naji sakon da kika tura Baby tafad'amin kuma naji dad'i da kikace kinason karatu, to Amma raina yayi matukar b'aci da ke bakizo da kanki kika fad'amin ba, daidai da rana d'aya ban tab'a d'aukanki bare agidannan ba, dake da Baby duk 'ya'yan cikina na d'aukeku bakuda bambanci awajena, daga yau idan kina bukatar Abu kizo da kanki ki tambayeni karkiji tsoro, nima Uba nake awajenki kinji?" "Insha Allah Daddy zanyi yadda kace nagode da kulawan da kuka bani, Allah ya biyaku da gidan Aljanna" Tafad'a tana goge hawayenta da gefen d'ankwalinta. Daddy yace "Ameen, to kuma akwai wata Alfarma danakeso awajenki, inason kifad'amin gaskiya idan kinaso ko bakya so, inason in had'aku Aure da Hamma Yarda, Wanda asalin sunanshi Abubakar, jikan Innace wacce mukaje wurinta a yola, mahaifinshi ya rasu sanadiyyar cutar Hanta data dameshi, an kaishi kasashe da Dama Amma ba'a dace ba daga baya sai mutuwa da yayi, Abubakar takwaran Mijin Inna ce, anace mishi Hamma Yarda ne sabida takwaran baban babanshine, yayi karatu secondary anan gida Nigeria, sannan yayi University a kasar England, kasancewar yayi karatu a kasar turai hakan bai hanashi riko da addininshi kem kem ba, na yadda da tarbiyyarki sannan na yadda da tarbiyyar Hamma Yarda, na tabbata idan kika Aureshi zakiji dad'i, Za'a bar Auren saikin haihu tukun" Wasu hawaye masu d'umi ne suka fara bin kuncin Minal, zuciyarta sai dukan Tara Tara take, tarasa ta ina zata fara yiwa Daddy bayanin tanada Aure, gashi sun nuna mata so bana wasa ba, Mommy ce ta katseta tace "Minal idan har bakya son Hamma Yarda kifito ki fad'a mana mu bazamuyi doleba" Minal dukar da kanta tayi cikin jin kunyar karyar datayi musu abaya, cikin kuka me tsuma zuciya ta bud'e bani da kyar tana har hard'e zance tace "Ku gafarceni Mommy da Daddy da Baby nayi muku karya tin rana ta farko da kuka bugeni da mota, banyi Dan ra'ayina ba, nayine don in tsere daga sharrin Mijina.....kukane ya kubce mata, tashiga yi ba tsayawa. Mommy ce ta taso daga kan kujera ta riko Minal tace "me kikeyi haka Daughter? Idan bakya sonshi ai babu dole" Minal juyawa tayi tana fuskantar Bedroom sabida batason had'a ido dasu, sakamakon karyar datayi musu, tana kuka tace "Mommy inada Aure, kuma ba soyayya mukeyi da Hamma Yarda ba, soyayyan da mukeyi ta 'yan uwantaka ne a matsayinmu na musulmai, kuma na d'auki Hamma Yarda kamar yayana ne yanda Baby ta d'aukeshi, ya zan Baku labarin Mugun Mijin Dana Aura Wanda yayi sanadiyyar makancewata daga baya ya wulakanta ni, babu abinda yake b'atamin rai kamar idan na tuna ranar Aurena da aka kaini gidan mijina, a kasan tyles cikin sanyin AC muka kwanta nida kawata" share hawayenta tayi taci gaba da basu labarin irin wahalar datasha sanadiyyar Mijinta, Abu biyune ta b'oye musu shine Sunan Bilal da kuma sunan Daddyn Bilal. "Amma wannan Mijin naki yacika mugu Mara imani, Da ace nasanshi to wallahi babu abinda zai hanani kaishi koto, sabida gani nake kamar wa Baby akayi wannan abun" cewar Mommy wacce tun kafin taga Mijin Minal taji ta tsaneshi, da ace zata Ganshi yanzu dasai ta zabga mini duka don ba karamin haushi ya bata ba. Shiru Daddy yayi yarasa mema zai fara fad'a awannan lamarin, ajiyar zuciya ya sauke yace "shikenan tashi Ku tafi d'aki babu komai Allah yana tare da mai hakuri, sannan shima sai yaga sakayya insha Allah" Baby ce ta riko hannunta suka tafi d'aki, Minal sai kuka take, Baby cikin muryar rarrashi tace "to miye anfanin kukan? Ni wallahi har naji maza sun ficemin arai, Ai garake ma baya miki maganar Banza, nida Yaya Mujahid kullum daga yace nayi mishi kiss, sai yace nayi hugging nashi, saifa nayi da gaske na had'e rai kafin ya daina, nafad'awa kawayena na makaranta sukace wai duk maza yanzu shine aikinsu koda Aurenki zasuyi sai sunyi miki maganar banza" "Haba Baby, ai idan kinga namiji yana yi mini maganar banza tofa must of them ba Aure ya kawosu ba iyeyine kawai, sai suce Aurenki zasuyi daganan idan sun samu abinda sukeso sai kiga sun fara sauya miki, idan kuma suka gano keba 'yar iska bace sai kiji sunce gwadaki suke, babu wani gwaji, a lokacin da suke gwadakin da kin yarda wallahi bazasuce gwadaki suke ba, mazan ne yanzu sai an had'a da Addu'a, *Note* _('Yammata yakamata mukula sosai da samarin zamaninnan zakiga wani yazo wurinki da niyar Aure sai kiga yafara bijiro miki da maganar banza, idan kika nuna kefa ba 'yar iska bace sai kiga yace wai Dama wallahi gwadaki yakeyi yanason yasan ke 'yar iskace ko mutuniyar kwarai, idan ke wawiyace kuma saiki yadda, sai kiji suna cewa 'yammatan yanzu duk bazawaraye ne, baby bari nafad'a miki they know what they are doing, sunsan me sukeyi, mu kula sosai muyi taka tsantsan, wani Dan cin fuska idan yagama dake sai kiga ya koma wurin kawarki, wanima sai kiga ya Aureta an barki a zero zero, ga rashin mutuncinki ga bakin cikin ya Auri kawarki, maganin karta faru tofa kada a fara)_ _back to business_ Baby ajiyar zuciya ta sauke tace "to ai ina sonshi sosai Minal bari dai nayi istikhara" Dariya Minal tayi tace "istikhara ana yinshi ne a lokacin da Abu bai shiga zuciya ba, shi istikhara ai Neman zab'in Allah ne, to idan yariga yashiga zuciyarki kinga koda Allah ya nuna mini ga Wanda yafi Alkhairi ke kuma Wanda yake ranki dabanne, bama wannan ba Baby nida tin d'azu gabana sai fad'uwa yake narasa meyasa" "Wallahi nima hakane Minal saidai kawai muyita Addu'a Allah yasa Alkhairi ne" Minal tace "Ameen". _washe gari_ Bilal da Asuba ya d'au jakar kayanshi ya ya nufi airport, saida yashiga office ya kara duba information akan anguwarsu Minal kafin yaje yashiga jirgi, sai Addu'a yake Allah yasa yaga Beauty cikin sauki, sai 8:30Am kafin jirgi ya tashi, cikin minti 30 suka sauka cikin garin Abuja, Bilal fita yayi yashiga restaurant yaci abinci kafin ya kama taxi yanufi maitama unguwar da Minal take, zoben hannunshi yashafa a hankali yace "am coming to you beauty" yayi wani murmushin daya bayyana dimple nashi, fararen hakorinshi ma suka bayyana, rabon da Bilal yayi murmushi tun ranar da Minal ta gujeshi, wayarshi ya Ciro yanda kallon sreen d'in, hoton Minal ne Wanda ya d'auketa ranar a India tana bacci, gashin kanta duk a hargitse ta turo baki kamar wacce zatayi magana, Lokacin tayi mishi kyau bana wasaba shiyasa ya d'auketa photo, manna wayar yayi a kirjinshi ya lumshe idonshi a hankali yace "I miss you" Saidai wani ikon Allah yana shiga cikin Maitama yaji gabanshi yana fad'uwa har wata zuciyar tace "kodai zuwanka ba alkhairi bane" wata zuciyar kuma tace mishi "fad'uwar gaba asarar namiji" Dakewa yayi yanata Fad'in innalillahi, har suka iso kofar gidan dayakeda tabbacin shine gidansu domin har numbar gidan saida ya d'auka, Yabiya me Taxi kud'inshi ko canji bai tsaya ya karb'a ba ya juya ya tafi, yana zuwa kofar gidan Me gadi ya tsayar dashi yana mishi tambayoyi, Bilal ganin an rainashi yasashi kutsa kai yana kokarin shiga ciki, Rigimane ya b'arke tsakaninshi da me gadi. "Minal Baby Mommy da Daddy suna zaune a dining sunacin abinci, kowa yayi shiru sai karan cokala kawai akeji, Minal sanye take da Riga da wando, rigar top ce me ado ajikin pitch color, sai wando daga wait an d'ame sai kasan aka bud'eshi (palazo) ta ta d'aura kanta da bakin d'an kwali Wanda ta taje gashinta ta bazashi a bayanta, ba karamin kyau dressing d'in yayi mataba, musamman yanda ta d'aura black d'an kwali, sai farantakanta ya kara bayyana, Baby kuma tasa wando jins blue da t shirt fari, sai farin picap datasa akanta itama tayi kyau, sai mommy datasa Black abaya da gyallenshi, Daddy kuma shadda yasa da Alama office zaije idan ya gama, kowa yanacin abincine Amma Sam yau gidan yayi shiru dayawa jikinsu duk a mace musamnan Minal datin jiya gabanta yake fad'uwa, Daddy ne ya katse shirun dacewa "Minal da Baby yau zakuje super market kuyi sayayya, nabawa mommynku 50 thousand tabaku, sannan akula banason yawuce yawucen banza, musamman ke Baby nasanki dason yawo kamar kinci kafar kwad'o" Minal ce ta toshe bakinta rana dariya kasa kasa, Baby sai hararanta take ta kasa tana hura hanci, Daddy yace "yi dariyanki Da Karfi My daughter, yarinyarnan yawonta yayi......kafin Daddy yakarasa sukaji hayaniya abakin gate, Gaba d'ayansu suka mike suka fice don ganin me yake faruwa, me gadi suka gani yana kokarin ture wani matashi, Daddy ne yace "kai kai meke faruwane?" Cakk jinin jikin Bilal ya tsaya da aiki, jin wani murya da bazai tab'a mantawa a rayuwarshi ba, bayanshi a juye, yakasa juyawa yakalli me maganar tsabar yanda wani shock ya d'ibeshi, Me gadi ne yafara yiwa Daddy bayani "wai yace dole sai an barshi yashigo sai kace gidanshi" Daddy yace "barshi mana yashigo malam Yusu, kasan dame yazo?" Me gadi yace "Alhaji mutanen yanzu ba abun yadda bane" Daddy yace "kabarshi Wanda ya cuci wani ai kanshi ya cuta bawan Allah shigo". "Duk maganar dasukeyi Bilal yana jinsu Amma shi yanzu da za'a yanka jikinshi tofa jini bazai fito ba, bai karasa tunani ba yakarajin Muryan daya firgitashi, "Bawan Allah kayi hakuri kashigo, kada ranka a b'aci" cewar Mommy, Baby ce takarasa don tabashi hakuri tana zuwa ta bubbuga bayanshi tace "Dan Allah kayi hakuri d'an uwa ba wulakanci akayi makaba, me gadi aikinshi na lura da wanda zai shigo kawai yayi" Ganin baiyi maganaba yasata d'an turashi kad'an, Sai gani kawai tayi yafad'i a wurin a sume, ihu tafara tana kokarin d'agashi su Daddy da Minal da Mommy suka karaso, d'agashi sukayi suna son ganin ko wayene, Baby ce ta fad'i ajikin Minal, Minal d'agata tafarayi Amma sai taji tayi Nauyi, Alamar itama ta suma, Ihu Minal ta sake tana cewa Mommy!!! Mommy!!! Juyawan dazatayi sai taga Daddy yana bubbuga Mommy Alamar ta tashi, Minal da me gadi sun rud'e, Ko kallon inda bakon yake basuyi ba, suna takan Mommy da Baby, Daddy zufane yafara keto mishi kota ina, meyake faruwane? Me hakan yake nufi? Daga mutum d'aya ya suma sai biyu subi bayanshi? Minal ce garin d'aga Baby taji ta taka hannun mutum, juyawa tayi tana kallon meshi, a gigice takai idonta kan fuskarshi, jada baya tafara tana girgiza kai, Daddy be ankaraba yaga Minal ta fad'i akan mommy asume, babban rigan jikinshi ya cire, yaciro hulan kanshi yana fifita jikinshi, wuri yasamu ya zauna tsabar tashin hankali yarasa mema zai farayi, Baba me gadi sai zagayesu yake, idan yabi takan wannan yadawo kan wannan, shima yarasa me yake faruwa ". ✔ote & comments *Wattpad* _@Jiddah S Mapi_ *بسم الله الرحمن الرحيم* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *MAKAUNIYA CE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Page 41... By Jiddah S Mapi *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociatio ~me gadi yagaji da zirga zirga gashi ba Dama ya d'agasu sabida matane, cikin hanzari ya d'aga Bilal yasashi a gaban mota, Daddy ma yatashi yasa su Baby da Mommy da Minal a mota, suka nufi hanyar asibiti, suna zuwa aka karb'esu hannu bibbiyu, likitoci suka rarrabu akansu suna basu kulawa, Daddy da me gadi ne suka d'an fita domin subasu wuri, Zagaye cikin Asibiti Daddy yafara yana tunanin menene yasa dukkansu suka suma a lokaci d'aya? Share zufan daya fito mishi a goshi yayi, Megadi ne yace "Alhaji zamanin yanzu mutanefa ba abun yadda bane, zakaga mutum simi simi kamar mutumin kirki saika zauna dashi kafin kasan Halinshi, ni Dama tun zuwan yaron bai shiga raina ba, bakaga gashin kanshi ba kamar rumfa" Daddy cikin dakewa yace "malam Yusuf Addu'a shine babban abinda yakamata muyi yanzu ba wai surutu ba" Malam Yusuf shiru yayi bai kara cewa komai ba, Sai bayan Isha kafin su Baby suka farfard'o Abin Mamaki Baby da sunan Yaya Bilal ta tashi, Mommy ma Bilal taketa Ambata, Sai Minal data tashi Tana Hawaye wani nabin wani, ta b'angaren Bilal yana farfad'owa yaganshi a d'aki kwance, a hankali yagmfara bin d'akin da Kallo, murya a toshe yace "Ashema Mafarki nakeyi, to amma inane nan?" Wani doctor ne yashigo yayiwa Bilal murmushi tareda mika mishi hannu suka gaisa, yace "Sannu Kaine Bilal ko?" Bilal gid'a kanshi yayi alamar eh "ok wad'anda aka kawoku tare suna nemanka, Akwai wacce takeson ganinka acikinsu" Bilal sai a lokacin ya tuna abinda yafaru sauka yayi akan gadon yace "ka kaini wurinsu" Doctor yace "kabi a hankali fa" 'Dakin dasu Minal suke Doctor yakaishi, suna zuwa Doctor yayi sallama Bilal ma cikin sanyin murya yayi sallama, Minal ce kwance ta rufe idonta kamar me bacci, Zuciyarta tana mata sake sake da Dama, Jin sallamar Bilal yasata kara runtse idonta, Bilal yana shiga d'akin yaga Mommy tanata kuka, karasawa wurinta yayi da gudu ya rungumeta, itama rungumeshi tayi sosai tana kuka, Baby ma tashi tayi akan gadon da aka kwantar da ita ta rungume Bilal ta baya tana kuka, cikin sheshekar kuka Bilal yace. "Mommy kuna Raye Dama? Shine kuka gujeni,

Chapter 12 of 14