bansan ta inda zan soma ba.
Ba Bakura ne ya ɗaura mun aure wai da Yahanasu, shine suka kawota, kayanta ne a motar" Ajjiyar zuchiya na sauke, na dafe kaina tare da runtse idanuna, ina jin wani ciwo a zuchiyata, tare da jiran abunda Zubaina zata ce." Murmusawa naji Zubaina tayi, abun mamaki, dan ba abunda na zata daga gareta ba kenan, wallahi na ɗauka ƙaramar hauka zata yi mun. Hannuna ta zame mun zuwa ƙasa, tana hawaye, ga murmushi a fuskarta. Gabaki ɗaya ta rikirkitani.
Ki dena asarar hawayenki, babu wata mace da zata samu irin kwatan so da kulawar da nake baki, Bulama naki ne Zubaina. Akan waccan kucakar yarinyar kike kuka, ta isa ta haɗa kanta da ke ne?" Murmushi tayi, ta sa hannu ta share hawayenta tace.
Bulama wannan hawayen daka ga ina zubarwa bana komai bane, face tausayinka. Yau na kuma tabbatarwa lallai iyayenka da ƴan uwanka ba sonka suke yi ba, kuma suna adawa da aurenmu ne sabida ni ba Kanuri bace. Amman kayi haƙuri ka rungumi ƙaddarar data tunkaroka. Ta ɓangarena baka da wata matsala, Allah ya bamu zaman lafiya, kuma kar wannan yasa ka damu kan ka ma sam. Damuwar shine, a ina to zata zauna tunda dai ni na cinye nan?" Ajjiyar zuchiya na sauke, dan dama babban damuwata shine, bansan da wacce siga Zubaina zata fassara lamarin ba. Amman naga bata ɗauka da zafi ba. Lallai Zubaina ta cika matar rufin asiri, mace ta gari, mai son farin cikin mijinta da ƴaƴanta.
A BQ Mama Gana tace zasu yi mata jeren. Zubaina me kike so inyi miki dan in faranta miki rai a matsayin dannar ƙirji? Ki sanar dani duk abinda kike so, ni kuma zan mallaka miki" Dariya tayi tace.
"Wannan ka bari sai ka dawo sai mu tattauna. Ka ɗauki yarannan ku tafi, ni kuma zanje ƙauye bincike dangane da case ɗinnan, bansan ƙarfe nawa zan dawo ba, gashi inason zuwa in ga Mama." Key ɗin babbar motata na miƙa mata, ta harareni cikin soyayya tace
"Wannan na meye to kake bani?" Rungumeta nayi tsam a jikina ina sauke ajjiyar zuchiya. Cikin raɗa nace mata.
Na baki motar kyauta, ni zan riƙe taki. Zubaina duk abunda na mallaka naki ne, ke da su Mama, abinda kike son ayi a gidannan shi za'ayi Zubaina. ki ɗebi kayan abinci a store ki tafinma da su Mama dashi" Sakinta nayi, na ajjiye mata key ɗin motata na ɗauki tata, na fice a ɗakin, ina share zubar data tsattsafomun. A dai dai wannan lokacin da za'a auna ni, haƙiƙa jinina ya hau, tsabaragen rudanin da nake ciki"
*MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!*
Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online
Gakayanmu kamarhaka
Tafi budurwa duniyane
Tsumin lahaula
Gombar bujenki jagab
Shu Umar zumarmu
Mumuna da,aeki
Makalemata
Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara
Dahuwar kaza cicibin kala kala
Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata
Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari.
Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma
AMARYA
MAI JEGO
WACCE ZATAYI KOME
Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji.
Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure.
Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo.
MRS BUKHARI CE
[26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI ( B4B)
7
SAKON GODIYA.
SAKON GODIYA TA A GAREKU MEMBERS NA CIKIN ( MAI IDO A TSAKAR KA DUNIYA PAID GROUP) KUN BIYA KUƊINKU, KUMA KUNA GWANGWAJENI DA COMMENTS INA GODIYA, NACE KU HUTA DA WANNAN PAGE ƊIN, NA SADAUKAR A GAREKU KUYI YADDA KUKE SO DASHI.
GAWURTATTU UKU FANS GROUP KUMA INA MIƘA SAƘON GAISUWATA A GAREKU.
BAN FA MANCE DA HAUSA NOVEL WWW. BATI. COM GROUP BA. IN DAI SHARHI NE KUN IYA. YA KAMATA MARUBUTA SU SAN DA ZAMAN WANNAN GIDA NAKU MAI ALBARKA.
ZUBAINA:
Yana fita na sulale a ƙasa, zaman ƴan bori nayi ji kake tim, na ɗaura hannuna aka na zunduma wani irin ihu. hawaye ya gama wanke fuskata, zuchiyata sai tsalle take yi mun. Ba ƙaramin dagewa nayi, na daure zuchiyata, ban rufe Bulama da duka ba tsabar ruɗani. Na danne ne dan gudun abunda kaje kazo, duk a cikin kissa da kisisina ne namu na mata. Duk da nasan Bulama a mallake yake, amman ance in kana da kyau ka ƙara da wanka. Yanzu duk irin shige da ficen da nayi dan in raba Bulama da iyayenshi, da danginshi, amman sai da iyayen Bulama su kai mun kishiya? Sabida neman mallaka babu irin surƙuƙun da ban shiga ba babu inda kafata bata taka ba, mune har shagamu, dukiya kuwa na narkar da ita sosai, ina kan narkarwa ma, sabida Bulama mutum ne shi mai yawan ibada, baya wasa da sallah. Asirin baya wani dogon zango a jikinshi, shi yasa akai akai nake gurfana a gaban malamai daban daban dan a sabunta mun asirin. Amman gashi daga ƙarshe mun zama mu biyu a wajan Bulama. Wallahi idan tsirara zanyi yawo sai nayi, amman wannan yarinyar sai dai ta zame mun ƴar aiki, ƴar reno da jiran gida, amman bata isa taji dai_ dai da ɗumin Bulama ba, da hakan ta faru gara Bulaman ya bar duniyar" Dariya nasa, ga kuka sharɓe sharɓe a idanuna na zama tamkar mahaukaciya, iyayen Bulama sun mugun sammaceni, amman zasu sha mamaki suma." Miƙewa nayi na faɗa ban ɗaki da hanzari a gaggauce na yi wanka na shirya tsab cikin riga da zani na Atampar koddibuwa, jakata na zara na fice a ɗakin Bulama, uniform ya kamata ace nasa domun zuwa office, dan akwai fitar da zamu yi zuwa kaciya bincike akan case ɗin dake gabanmu, amman sawun giwa ya take na raƙumi. Key nasa na kulle ɗakin Bulama da nawa ɗakin na fice. A tsakar gida na tadda gayyar tsiyar, zasu shiga mota, da halama wani wajen zasu, idanu na zuba ma Yahanasu, mummuna da'ita wai da ita aka haɗa ni kishi, iyayen Bulama sunyi kuskuren da zasu jima suna nadamar hakan a fili, nafita takota ina, ni banga da abinda zata ja hankalin ɗa namiji ba ma. Kafin in ƙarasa garesu, suka ja motarsu fuu, me gadi ya wangale musu get, Mama Gana ta leƙo ta tsittar mun da miyau har suka fice ina tsaye a wajan, nannauyar ajjiyar zuchiya na sauke, na shiga mota nima na fice. Kai tsaye gida na wuce, dan in sanar da mahaifiyata halin da ake ciki.
Anguwar Dankwata:
Dankwata, anguwar shege da shegiya, in kaga ɗan halak baƙone. Wannan shine kirarin wannan anguwa, wacce ta cika ta batse da ƴaƴan talakawa marasa ɗa'a da kunya, unguwar da tayi ƙaurin sune a garin kaduna kenan, duk da akwai jerin sunayen unguwannin da sunansu yai shura wajan lalacewar tarbiyya, irin su Layin dutse, kabalan doki, kabala costine, da unguwar sarki, da sauransu dai, Dankwata itama tana ɗaya daga cikin irin wadannan unguwannin, amman hakan baya nufin babu masu tarbiyya irinta islama fa, a kwaisu sosai, sai dai ɓatattun su suka rinjayi kintsattsun anguwar, dalilin da yasa akaima jama'ar anguwar kuɗin goro kenan. Hancin motarta ta kutso dashi cikin anguwar, matan aure da zawarawan unguwa sai kallon Zubaina akeyi, ana zunɗenta, ba wanda take kallo, dan bata cikin nutsuwarta. A ƙofar wani gidan talakawa ta tsaya, mai ƴar ƙaramar ƙofar shiga, da kuma kofar shago irinna cikin anguwarnan, ƙofar gidan akwai dakali wanda yaji sumunti sumul sumul.
Zubaina:
Da hanzari na fito a cikin motar, na faɗa cikin gida. Ko bi takan munafukan matan layin banbi ba, nayi shigewata cikin gida. Mama tana zaune a gaban wanke_wanke tana yi, ga ƙosai da kununta akan tabirmar dake shinfiɗe a kusa da ƙofar shiga ɗakin nata. Sagir kuma ƙanina, yana zaune a turmi yana karyawa. Mama ta ɗago ta kalleni, kuka nake yi sosai, dan hankalina a mugun tashe yake matuƙa. Da sauri Mama ta miƙe har tana yarda kwanon da take wankewa.
"Yau me zan gani ni Jummai ɗuwawu ya mutu ya bar zani Zubaina kece da kuka, ince dai ba asirin bane ya karye ya sako ki ba ko?" Gabaki ɗaya Mama ta ruɗe, dan Bulama shine, cinsu, shansu, sututarsu. Hatta gidan da suke ciki shi ya siya musu, a gidan haya mahaifinmu ya rasu ya barmu, bai bar mana gadon komai ba, sai gadon talauci.
"Kiyi magana mana kin kaɗamun hanjin cikina, Sagir kana ganin ƴar uwarka a cikin damuwa amman kaƙi kazo kaji me ke damunta" Sagir yace.
"Inji meke damunta in mata maganin me? Matar data ɗauka rayuwar ɗa namiji tamkar a hannunta take. Kowa ya ɗebo da zafi bakinshi, Mama ku dena sani a cikin irin wannan sabgar taku, ta ƙin Allah, duk iskancina tsoro kuke bani, dan muma ƴaƴanki Mama ba ƙyalemu kika yi ba, kullum cikin bamu rubutu kike mtwsss" Yana gama rashin kunyarshi ya fice yana fito. Ni bambi ta kanshi ba, Mama ce ta shiga ƙunduma mishi manyan zagi, tana kwashema rayuwarshi albarka.
"Ki jini da yaro fa, da haka yake so, ai sai ya dena cin komai na cikin gidan tunda mijinki ne yake kawowa, wa ya siya mana gidan? gidan haya ubanku ya mutu ya barmu a wulaƙance a ɗaki ɗaya, ɗakin da in damina ta sauka, bamu da banbanci da na titi, dan duk ruwan daminannan a kanmu yake ƙarewa. Da ba dan ƴan uwana sun tsaya mana ba, karatun zamanin ma wa zai samu. Zauna ki faɗamun damuwarki, ni kuma in share miki hawayenki" Sulalewa nayi na zauna a kan taburma, itama zaman tayi a gefe na.
"Menene yake faruwa Zubaina kike kuka, ince dai munafukan anguwa basu ganki kina hawaye ba ko? Dan yanzu sai kiji sunanki a majalisar matan aure da zawarawa"
Hmmm Mama iyayen Bulama ne suka taɓoni, kinsan munafukan tsofaffinnan aure suka yi mishi da ƙanwarshi da suka taso gida ɗaya, sai ga baƙi jiya har mota uku sun kawo wata mummunar baƙar yarinya da sunan Amaryar Bulama, duk rabashi da danginshi da nayi, sai da suka ci galabar cusgunamun" Sallallami Mama ta soma yi tana tafa hannayenta tana faɗin.
"Ni jummai naga ta kaina kishiya tara rana ɗaya, ta goma na ƙofar gida. Aure fa kikace Zubaina. Lallai da badan mun tashi tsaye da bin malamai akan Bulama ma da yanzu iyayenshi sun sa ya sakoki, sun toni asirinmu a unguwa. Ke Kanuri fa basu da mutunci, kuma da yawansu mayu ne, gasu da ƙabilanci, basason nasu ya fita ya auro bare. Muna zaman mu lafiya suna shirin tagayyaramu. Amman ke wanne hulunci kika ɗauka dan nasanki da zafin kishi, duk cikin yaranma ke kika biyoni. Nifa ranar da Babanku yace yana neman aure, a gadon asibiti na kwana. Gari na wayewa kuwa na shiga bin ƙauyuka ina yima bokaye da ƴan tsubbu biyayya, har sai da naji zancan auren ya watse sannan na soma iya bacci."
"Mama ni da kwantar da kaina naso inyi in ɓullowa abun ta bayan gida. Dan yanzu haka Bulaman ya kuma gigicewa a kaina, baya son yaga kukana. Motarshi fa da safennan ya bar mun, yace ma in ɗebo muku kayan abinci a store. Amman ban ɗiboba sabida ƴan uwanshi kar su gani. Gashi yace in faɗi duk abinda nake so zai yi mun. Amman mama ni ƙona gidan zanyi cikin dare duk mu zama ganda" Mama ta buge mun baki tace.
"Baki da hankali ne, kin ɗauko hanya me kyau kina son ɓata rawarki da tsalle. Ai yanda kika kwantar da kanki shine dai_dai, yaƙi ɗan zamba ne Zubaina. Zanje wajan boka duk yanda muka yi ni da kaina zan zo in kawo miki magunguna, kinsan dai aikinshi ba wasa, tunda shi ya juyar miki da hankalin Bulama. Ke dai zube kuɗi kawai, ki tashi karma kiji komai da ƙafafuwanta zata bar gidan, shima kuma bazai taɓa iya zama da'ita ba. Ke sai dai bayan raina ne zaku yi kuka Amman ba yanzu da rayuwata ba. Ke dai kafin ya sallameta ki samu ki kabci rabo mai mugun tsoka ki samu ki ƙarashe gininki, a zuba miki haya." Kuɗi masu kauri na ajjiyema Mama.
Gasu Mama in basu isaba kice ya bamu maganin za'a kawo mishi ciko tunda an saba. Ni zan tafi" Baki Mama ta washe bayan ta dafi kuɗin tace.
"Muje in ga motar mana." Tare muka fita da Mama. Matan unguwarmu muka gani, sun haɗa gungu guda na gulma, dama kullum a cikinta suke. Suna ganinmu suka soma dariya.
"Ahh Maman Kofur Zubaina, Zubaina Amaryar mota ta samu ne? Kai Masha Allah."
"Eh Jamila kinga, da safennan mijinta ya bar mata ita kyauta, albarkar aure" Da biyu Mama ta faɗama Jamila hakan, dan ita taƙi zaman aure fur, da an kaita data fito. Tsaki nayi na shige motata, mama na ɗaga mun hannu na wuce. Ban zame ko ina ba sai gidan ƙawata Mabaruka. Da sallama na shiga cikin gidan. Kishiyarta na tsakar gida, ta haɗe kan yaran gidan tanai musu wanka, ga tulin wanke_wanke a gefe, ga kayan wankin yaran duk a gefe guda. Da fara'a ta gaisheni cike da girmamawa, a yatsine na amsa mata nayi shigewata ɗakin Mabaruka. Tana zaune a ƙasan ledar ɗakinta tana kallon tashar Arewa 24 Tana ganina tayi dariya.
"Sabon kabari mai sa a tuna Allah, makara motar ƙarshe , tsatsa mai kashe ƙarfe, shegiyar gyaɗa da ƴaƴan kanya, shegiyar uwa sai bukka, ke ce da safiya haka kofur Zubaina? Yau aikin ya garara Bulama ya taro match kenan, ina kika baro dangin mijin naki?"
Ke baki san a cikin damuwa nake ba ko? Kefa na faɗama a waya cewar Iyayen Bulama sun mishi aure, danginshi matar suka zo kawowa ma dan rashin kunya" Ƙirji ta dafe tace.
"Nifa nayi tunanin wasane Zubaina, yanzu ina kika baro kishiyar kika tawo nan, bakya gudun su miki wani binne binnen su sabautaki?"
Basa gidan sun fita, duk da bansan inda suka je ba, amman basu isa su samu makarin asirina ba, nasha gabansu. Mabaruka wanne boka kika sani shege wanda baya tsoron komai? Ki haɗani dashi" Ajjiyar zuchiya tayi tace.
"Hmmm ni ko nake da arne na kan dutse ma, dan bama musulmi bane. Shi yaimun aiki akan waccan shegiyar yarinyar, ke baki ganta na sakar mata aiyukan gidan ita ke komai ba? Shekara huɗu kenan ina juya kowa a cikin gidan, har uwar mijin ni juyawa nake yi. Amman ko hantararta bana yi, dan har kwancen kaya bata nake yi, in ba ƴan uwanta ma, Yayarta da suke ciki ɗaya, in tazo gidannan a nan inda kike zaune take zamanta, yaƙi ɗan zambane Zubaina, in kika ce ihu da hargagi zaki yi, fallasa kanki zaki yi, aje aita miki baki. Kwanciyar mage nayi musu, amman a baɗini suna shan gashi. Ina zaune a nan da kika zo kika same ni, zan jiyo ihunta yana jibgarta, ni nake zuwa ƙwatanta a hannunshi, har in dafa mata ruwan ɗumi na gashi." Sallamar kishiyar Mabaruka ne ya katseta. Shigowa tayi da kofin tea da plate a rufe ta ajjiye a gabana.
"Ina wuni mu sake gaisawa, mun gaisa ɗazu a gurguje" Da Lafiya" Na amsa mata, sai fara'a take faman zabgawa, Kallon Mabaruka tayi tace.
"Yaya me za'a dafa ne da rana, inason dana kammala aikin inje inyo mana cefanenne?"
"Uhm Sagira ki dafa mana faten doya da wake, sai kisa bushasshen kifin da Adam ya kawo jiya yana nan a kitchen, da daddare kuma tuwon shinkafa miyar kuɓewa ɗanya, amman a siyo ɗanyen kifi Adam yafi so" Da "To Yaya" ta amsa ta miƙe ta fice. Bakina a buɗe na dubi Mabaruka nayi dariya, dan har naji ɗan dama dama a zuchiyata, kuma inajin nima hanyar da Mabaruka tabi ita zanbi, ko dan in yaudari dangin Bulama, dashi kanshi Bulaman, duk macen da bata iya kissa ba ansha da'ita.
"Ƙawata ya kika ga aikin na kan dutse? Ai shiyasa kika ganni hankalina akwance, rabon kwana yake yi mana, amman wallahi har makara nake yi salla tsabar kwanciyar hankali. Ai namiji, da kishiya basu isa sun ɗagamun hankaliba, in ke baki yi musu hakan ba, kece zaki kwashi takaici da ciwon zuchiya a hannunki, daga ƙarshe in baki yi wasa ba ki jiki a kabari. Ai na taimaketa ma tunda na barta take zaman auren, bansa yayi waje da'ita ba. Gashi dama ba gata bane dasu, basu da wanda ya tsaya musu a family, dangin Baban nasu suna ƙauye, dangin mahaifiyarsu kuma, suma takansu suke yi"
Mabaruka tashi muje ki kaini gun wannan boka nima yai mun irin wannan aikin da yayi miki, ko zanji salama. Da dana shigo cikin gidannan zuchiyata baƙa, amman yanzu zuchiyata kamar auduga dan haske." Dafani tayi tace.
"Zan kai ki ƙawata, amman sai fa kin shirya dan aikinshi akwai mugun tsada, ya iya aiki amman fa saiya mugun talautaki, dan manyan kuɗi yake karɓa. Ki duba ɗakina sai da fa na siyar da komai nawa, ke hatta zanen ɗaurawa a shekaru biyu baya neman gagarata yayi. Gashi kina gani har yanzu ɗakina bai dawo kamar da ba. Akazo kuma cinikin su Adam yaja baya. Kinsan sana'ar saida motoci haka take, zuwa take yi. Yanzu abun yaja baya sosai, ni kuma aikina na asibiti ba wani aiki bane, ga ƙannena da mahaifana da nake kulawa dasu. Amman dai ina ganin biyan buƙata. Ke lokacin da aka kawota fa, bacci wannan bana iyayi, daga baya ma cikin dare sai inji kamar ana kiran sunana, so tayi ta fitar dani a gidan a haukace. Alhalin dani aka tara arzikin Adam, ni nasha wahalarshi lokacin da yake matsayin malamin makaranta mai ɗaukar nera dubu takwas a wata a matsayin albashi. Hannu ta bani muka tafa, nace mata.
Kuɗi ba zasu zama matsala ba Mabaruka, yanzu haka sai da na ba Mama wasu kuɗaɗen, zata je mun wajan bokanta, shima yankan wuƙane. Babu kuɗi masu yawa a hannuna, amman dai ina da kadarori na zinarai a gida, sai in kaɗar dasu, ranar biyan buƙata rai ba'a bakin komai yake ba ai ƙawata, a wanne anguwar yake ne?" Dariya tayi mun, ta buɗe plate ɗin da Sagira ta ajjiye a gabana, wainar ƙwai da biredi mai yanka yanka ne a ciki, ta dubeni tace.
"Ba lallai in kin karya ba, maza ki karya sai muje, amman fa a garin Jos bokan yake, kin taki sa'a ma da safe kika zo, zamu iya zuwa a yau harma mu juyo, sai dai zamu yi dare, ni dama night nake dashi a asibiti, ba dai wata matsala dai ko?"
Koma akwai babu Mabaruka, ni kam banga ta cin abinci ba, taso kawai mu kama hanya, sai naje gida na ɗakko zinaran nawa, sai mu je senteral in siyar dasu a layin ƴan gwal." Cikin ƙanƙanin lokaci Mabaruka ta shirya cikin leshi na goduwar riga, fuskarnan tata taci bilicin tayi ɗoɗar, hannunta kuwa duk dabbara dabbara kamar an babbaka Adaga ( plantain). A wajan kishiyarta ta bar yaran nata, muka wuce gida na kwashe setin gwal ɗina wanda Bulama ya sai mun, da ɗan kunne da sarƙan da na saima kaina, ƙarƙaf nayi, muka je kasuwa na kaɗar, muka nufi hanyar Jos. Wayata ce ta shiga ruri Bulama ke kirana, gefe guda na samu na kashe motar, sannan na ɗauki wayar.
Ango mijin Amarya ranka shi daɗe ango da girman kujerarka" Dogon tsaki ya ja, yace.
"Bakya ji Zubaina, ai bani da wata amarya face ke, mai zanyi da wannan mummunar yarinyar. Bama wannan ba, kin ganni a shagon siyar da atampopi na mudassar and broda shine nace bari in kiraki, atampar wanne kamfani kike so? Far nayi da idanuna kamar yana ganina kana nace. Da yake duk atampopin da nake saye a hannun Hajiya Zulai nake siyansu, kuma nafi yarda da kayayyakinta, me zai hana ka bari in ka dawo ba sai mu je gida mu sameta ba?" Murmushi yayi mun yace.
"To shikenan bari in sai takalma da mayafai da jakunkuna tunda dai na shigo shagon, da girmana goɗai goɗai ai bana shiga in fito ban sai komai ba, sai munyi waya, kuma ina ƙara baki haƙuri a bisa ɗanyan hukuncin da su Ba Bakura suka yanke mana, kuma ina kan tunanin yanda zan ɓulloma da lamarin, Ahmad ma yana office ɗina yana jirana, ashe ya shigo gari bai ko kirani ba. Sallama mu kayi da juna, wayar nabi da harara, Mabaruka sai dariyar ƙeta take yi mun.
"Kai ƙawata a cikin wayar ma ba'a barshi ba harda uwar harara kuma? Ki dena ba kanki haushi, baki da wata matsala, wallahi in cewa zaki yi Bulama karya je aiki, zama zaiyi ya tusaki a gaba kuita soyayyarku. Ke dai ki daure zuchiyarki karki sake ki nuna mishi kishinki, itama haka kar ki bari tasan kina kishinta. In ma ya shiga wajan nata, bacci kawai zaita shantaka bashi da sauran kuzari, ballantana har yayi miki halin nasu na maza, dan ƙaramin aikin namijine yayi ruf da ciki akan yarinyar washe gari ki ganta da ciki. Kinga saiki tashi a tutar babu, kin aureshi tun bashi da wani abun hannu, kuna tare aka tara komai. Daga ƙarshe kina gani za'a raba gado ƙila ma kasonta yafi kasonki yawa, musamman in maza take haihuwa, tuminin takaba kuwa daidai za'a baku, kinga kuwa ai kwaɓarki tayi ruwa, shi asiri gaskiya ne, amman kissa da kisisina wani sa'in tafi asirin saurin aiki, duk macen da tayi watsi da kissa ai ta makaro wallahi" Wani ƙududun ƙwallon kishi na haɗiye, ya tafi tuƙuƙuƙuƙu har ya faɗa cikina.
Ki dena wannan lissafin, ai nice mace kaɗai da zan gaje dukiyar Bulama ko ƴan uwanshi sai dai suyi hange Mabaruka. Babu macen da Bulama har ya isa ya kwarara mata maniyyinshi a mararta ta samu cikin da zata samar mishi da ɗa. Wallahi babu ita, nifa gani nake yi gangancine wannan rabon kwanan, duk ranar da asiri ya karye, zasu sadu da juna fa kenan? In kuwa haka ta faru ina kike tunanin zan iya saka kaina Mabaruka, anya ba kuskure bane sallama miji ga kishiya dan gadarar an zargeshi da surkulle?"
"Babu ganganci a ciki. Ni dai shekara huɗu ina kan wannan tsarin kuma babu, saɓanin lamba da na taɓa cin karo dashi, ke nafa yadda da bokannan yana da muggan rauhanai baƙaƙe da yake aiki dasu, wallahi ko kashe yarinyar kikace yayi, ko shurawa bazata yi ba, sai dai mu koma gida mu samu gawarta anai mata wanka, ke munci dubu sai ceto fa. Ajjiyar zuchiya na sauke, har muka isa garin Jos Mabaruka tana bani labaran irin gumun da tayi a gidanta, ta kwaci ƴancin kanta. Munsha wuyar hanyar saminaka sosai, sabida