Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daga Yobe saita gundiri kowa a gidan da jarabarta. Sai dai tana da kirki, gata da son sada zumunci. Shi yasa ko aure ne ya taso a gidan, ita ke shigema matan ƙannen nata gaba. Gaggaisawa akayi, aka shiga jajantawa juna. "Ohh Innana dare ɗaya harkin faɗa wallahi. Ki dinga sassauta ma kanki, adda'a zamu bita dashi, Allah ya toni asirin duk wanda ke da sa hannu a wannan lamari. Ƙannen nata ne suka yo sallama suka shigo. Da yara mazan gidan. Duk ɗaya bayan ɗaya tai ta tambayar yaran iyalansu. Daga baya matan ƴaƴan nata suka shigo su uku suka gaisheta. Su Dala basu yi aure ba tukunna. Amman an tsaida lokacin dama harda su Fanda, da Yahanasu a cikin waɗanda za aima auren, yara kusan goma za'a aurar. Ba Bakura yace. "Modu ai saimu hanzarta muje asibitin sha ɗayan rana tayi. Wakil yana can ya kai musu abinci." Shisshiryawa suka yi, mota uku suka nufi asibitin. A hakanma, sai da aka ba ƴan matan gidan Haƙuri kan cewa inta dawo gida sa ganta." ZURIYAR GIDAN BULAMA BUKAR BULAMA.......✍🏻 Sai mun haɗu zuwa bayan sallah in Allah ya kaimu cikin rayayyu. Ya kuka ji salon? Labarine mai ɗauke da ɗumbun darasin rayuwa. Ku kasance dani on 20 July in sha Allah. Zaku iya biyan kuɗin karatu tun yanzu masoyanmu. _GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 July 20 in sha Allah._ _1-NIHLATUL-KHAIR_ 👇🏽 *(Ummu Affan)* _2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_ 👇🏽 *Badi'at Mrs bukhari* _ZULFA_ 👇🏽 *Ummu maher(miss green)* _Littafi ɗaya;400_ _Littafi biyu;800_ _Littafi uku;1000_ Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽 07068606171 Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number. 08104335144 *GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa 10K ne kacal. Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 07068606171 08179523215 Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽 2K sati biyu 3k idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama 10k kacal Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼 [26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI ( B4B) 2 Wannan labarin ya faru a gaske. Babu wani abu dana ƙara, saima waɗanda na ɗan sakayesu, dan gudun ɗaga ma masoyana hankali. Sadaukarwa garuku iyaye mata. Duk wata uwa ta duniya wannan littafin sadaukarwa ne a gareta. Gargaɗi. Ban yarda a sarrafamun littafina ta ko wacce siga ba. Yin hakan take dokace, a kiyaye. Nasiha. ( Mu guji ta'amali da miyakun ƙwayoyi domun kare lafiyarmu. Wannan saƙone daga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi) Saƙon gaisuwata Zuwa gareku Maman Khairat Ummu Nabeela Maman Yasser Maman inteesar Jinjinar ban girma a gareki.(Ambassador)Rashida Adamu Abdullahi mai sa'a, kuma women lida ta ƙungiyar 13_13, bugu da ƙari ƴar gwagwarmayar ƙwato hakkin mata, ƴar siyasa, kuma ƴar kasuwa. Shugabar ƙungiyar Mata Jarumai Association of kannywood atis ZURIYYAR GIDAN MARIGAYI BULAMA BUKAR BULAMA. Shine mahaifinsu Ba Bakura. Shi cikakken Babarbarene ( Kanuri) Gaba da bayanshi, mazauna Damaturu. Auren zumunci suka yi shi da Matarshi mai suna Yahanasu. Kasancewar Baburawa akwaisu da ƙabilanci, aurensu kuma da tsauri, hakan yasa wasu yaruka basu fiye aurensu ba,.Su da Shuwa arab, banbancin al'adunsu kaɗanne, sunyi matuƙar kama a al'adance sosai.Bulama ɗan boko ne sosai, manajer ne a bankin first bank dake garin DamaturuYaranshi Biyar huɗu maza sai ɗaya mace. Bakura shine babban ɗan Bulama, wanda ake kira da Ba Bakura, Ba ko Bawa yana nufin ( Baba a yaren Kanuri. Matarshi ɗaya itace Hajja Gana. Mata mai sauƙin kai da son mutane. Itace suruka ta farko a cikin gidan Marigayi Bulama. Yaran Ba Bakura biyar. Bulama Babba shine ɗanshi na farko, Ma'aikacin banki ne shima, ya gado takwaran nashi. Yana zaune a garin Kaduna da matarshi mai suna kofur Zubaina, sai yaranshi biyu mace da namiji. Macen sunanta Maryam taci sunan mahaifiyar matarshi Zubaina. Namijin kuma sunanshi Bakura suna kiranshi da Bawa. Bulama Babba shine kaɗai yake auren bahaushiya, kuma shine kaɗai yabar garin Damaturu da zama, sai dai ya shigo ziyara. Daga baya ma ziyarar ta gagara, ko waya saiya shafe fin wata biyu bai ɗaga waya ya kira iyayenshi ba. Aike kuwa da duk wata sai yayo aiken kuɗi masu tsoka, duk iyayenshi sai an bibbisu da kuɗinnan, ba dan basu dashi ba, sai dan biɗar albarkar iyaye, kuma shike riƙe da gidan ada, kasancewarshi babban ɗa a gidan. Ya taso cike da soyayyar ƴan uwanshi sosai. Amman matarshi ta shiga ta fita ta raba shi da kab ƴan uwanshi, babu mai zuwa gidanshi, tunda baya neman mutane, kuma ko an kirashi sai yayi ra'ayi yake ɗauka. Ko da yaushe Hajja Gana a cikin damuwa da ƙunar zuchiya take, bata jin daɗi sam yanda mace ta rabata da ɗanta data reni cikinshi harna tsawon wata goma sha biyu, yaron da sai tiyata akayi mata aka cireshi a jikinta, ta kuma sha baƙar azabar jinya. Ko da yaushe a cikin hawaye take. Ba Bakura shi kuma ko da yaushe a cikin bata haƙuri da tausarta yake. Wannan kenan. Sai mai bi ma Bulama Gunsum, matarshi ɗaya mai suna Yalewa, sai ɗiyarsu ɗaya mai sunan mahaifiyarsu, suna kiranta da Ba gana. Lauyan gwamnati ne shi. Sai mai bin Gunsum. Bukar, Shi bashi da aure, yanzu ne dai ake shirin yin gagarumin bikinsu, shi ɗan kasuwane babba a babbar kasuwa, yana da shagunan suturu, yana da shagon kayan ƙwaliya da shafe shafe na mata, kasancewar fannin kasuwanci ya karanta. Sai bai binshi itace Fandau Babba, tana gidan mijinta tana aure a Yobe, ita kuma malamar makarantar sakandare ce. Sai ƴar Auta Aisa ita kuma a wani kamfani take aiki, itama kasuwancin ta karanta, tana aure a Damaturu, soja ne mijinta, suna zaune a barrak. Sai mai bin Ba Bakura itace Mama Gana. Tana aure a Yobe itama, yaranta Huɗu dukka maza. Yurom ne babba, sai Ya Ari, sai Mainam, sai Bulamanta. Principal ce a Babbar makarantar mata dake Yobe. Masifaffiyace ta bugawa a Jarida ( maman Yaseer kanta ta sara mata) Sai dai tana da kirki da son ƴan uwa sosai, kuma kasancewarta ita kaɗaice mace a cikin ƴan uwanta, sai suka ɗaurata take jan ragamar auren yaran gidan, itace haɗa akwatuna, itace gyaran Amare, da siyan kayan ɗakin amaren. Maza kuma ita ke haɗama matansu akwati, sannan da ita ake komai dai. Sai mai bi mata Ba Modu. Yaranshi Takwas, matanshi biyu Innana itace uwar gida. Yaranta biyar. Bulama Baƙi shine Babba a ɗakinta. Likitan ƙashine a wani asibiti mai zaman kanshi, sai Wakil, shi kuma nurse ne a wani asibitin shima mai zaman kanshi sai Yahanasu, ita kuma ƴar jarida ce, tana aiki a gidan talabijin dake kan tauraruwar ɗan adam, lamta ta ɗari da tamanin da biyu. Fandau ƙarama, malamar makaranta ce itama, tana da aure. Sai Fanna Wacce bata soma aikin ba tukunna, kammala karatun nata kenan. Wakil da Yahanasu, da Fanna ne basui aure ba a ɗakin. Kuma suna daga cikin waɗanda za'a haɗa a aurar dasu. Surukan gidan duk suna cikin gidan, gidane mai bala'in girma wannan kenan. Sai kishiyar Innana mai suna Bugulaji, ita yaranda uku maza mace ɗaya. Ahmada shine babba, shike taimakon mahaifinsu da kula da gidan gonarshi, yana riƙe da ɓangaren masu gasa kifi su jera a kwali, shike kula da kifayen da ake kiwatawa, shi ya zaɓi taimakon mahaifinsu, amman yana da kwalin digri ɗinshi a fannin kanikanci, yana ɗaukar albashi mai tsokar gaske daga wajan mahaifin nashi, kasancewar kamfanin bushasshen kifin Ba Modu babba ne sosai. Ya na da mata da yaro ɗaya. sai mai bi mishi Dala, shi kuma likitan idanune, baida aure, suna daga cikin waɗanda za'a aurar, shi da Autarsu. sai autarsu Yabulu, ita kuma yanzu take kan haɗe digri ɗinta a fannin Jarida. Sai mai bin Ba Modu, Baana, matanshi biyu, Baguji, da Yana. Yaransu bawai. Mata huɗu maza uku. Ya Sufaim itace babba, sai mai bi mata, Aisa, Bulama ƙarami, Ba'a Kaka, Ya gana, ya gaji. Dukkansu suma ma'aikatan gwamnati ne. Tsabar son bokon wannan familyn ba'a aurar da yarinya har sai ta kammala digrinta na farko, ta soma aiki sannan sai tayi aure. Kuma basa bada auren ƴaƴansu mata a waje, mazan ma a cikin family suke zaɓa. Family ne mai kyau, da daɗi, ko wanne a waye yake. Basu da tarin dukiya mai yawa, amman suna da rufin asiri sosai. Kab matan yaran gidan suna cikin gidan tare da yaransu suma, waɗanda za'a kuma aurowar ma anan gidan zata zauna. Suna da tarbiya sosai yaran gidan, cikinsu ba wanda baiyi saukar Qur'ani ba, gasu da girmama juna sosai, ko wanne ɗaki akwai Bulama, kuma ko wanne Bulama yana da inkiya. Ba Bakura shine jagora kuma jaraba, shike riƙe da ikon gidan, sai umarnin da ya bayar ake zartarwa. Wannan kenan" Dawowa labari: Yahanasu. Da kuka na farka da safennan, banda firgita da iface ifacen dana dinga yi cikin dare. Da dama jama'ar dake ɗakin suna jinyar marasa lafiya, gani suke kamar makarai ke damuna. Tsabar ɗimuwace, da raɗaɗi, ko ina ciwo yake yi mini. Hajja Gana tayi kuka harta gaji, ko rintsawa ban barta tayi ba. "Yahanasu wannan kukan ya'isa haka zaki iya jama kanki wani ciwon kuma a ɓata goma ɗaya bata gyaru ba. Ga Ya Hajja Gana kin hanata cin abinci, kema babu abunda kika saka a bakinki." Wakil ne yake mun Magana cikin sigar rarrashi da kwantar da kai. Hajja Gana tace. "A'a Wakil batta ta koka, ni kaina kwana nayi ina faman kukan tausayin Yahanasu. In sha Allah za'a gano wanda yai mata wannan aika_aikar. Ƴan sandan kace suna hanyar zuwa ko?" Ta tambayeshi cikin sigar taushi. Kai ya ɗaga mata halamar "E" Ni dai sai faman kuka nake yi kamar wata ƙaramar yarinya" Hango su Mama Gana nayi, da su Ba Bakura, da sauran ƴan gidanmu. Wani irin yam_yam nake ji a jikina, takurewa nayi waje guda, na harhaɗe ƙafafuna. Ji nayi na muzanta, ina jin kamar tsirara kowa ke kallona, ina ganin kamar suna ganin mikin dake ƙasanane. Su kansu ganin yanayin kunya da tsarguwar da nayi, ya kaɗasu, sai sharar hawaye matan suke yi. Ba Bakura sai ajjiyar zuchiya kawai yake faman yi, idanunshi sun kaɗa sunyi jawur. Ya Innana ta matso kusa dani tana rarrashina da muryarta wacce take ƙarfafani. Take wani dangana da tawakkili ya saukarmun, hawayena na dinga ƙoƙarin sharewa, amman sai sabunta kansu suke yi. "Hajja Gana kunci abinci kuwa?" Ba Bakura ke tambayarta. "Babu wanda yaci abinci, ko runtsawa banyi ba. Yahanasu firgita tai ta yi da daddare, har daddanneta ma'aikatan jinyar suka yi, da ƙyar ta dawo nutsuwarta da naita tofeta da adda'a." Mama Gana ce ta matso gadon da nake kwance ina sauke ajjiyar zuchiya, na kasa ɗagowa in kalli kowa dan wata kunyace take kamani. "Taimaka mun Innana ki ɗagata ta jingina, tasha tea. Sai a nemo ruwan zafi ta gaggasa jikin nata" Ya Innana ta zaunar dani, ta jingina matashi a bayana. Mama Gana da kanta ta bani tea nasha, badan inason in sha ba, sai dan ganin na rage ma iyayena damuwar da suke ciki a kaina. Ƙwaƙwalwata ce, ta haskomon sanda wanna matashin ya keta rigata, yake shan ƙirjina. Ahhhhhh" Na saka ƙara mai doɗe dodon kunnuwa, ƙoƙarin durowa na ya soma yi. Su Bulama baƙi ne suka daddanneni, inata fisge fisge. Ma'aikatan kiwon lafiyane suka rufu a kaina. Allurar bacci suka zurkuɗa mun, luu naji bacci na ɗibana, dishi dishi nake ganin dangina." Ba Bukura: "Modu muje gida dukka maza mazan mu sauke ma Yahanasu Qur'ani mai girma, muyi addu'o'i ayi sadaka, mu yi tawassali da wannan aiyukan Allah ya dawo mata da nutsuwarta. Wakil kai kuma na wakiltaka kaji da ɓangaren ƴan sanda. Hajja Gana da Innana ku ku zauna da'ita. Bugulaji ku kuma a koma gida aita taya Yahanasu da Adda'a. Zanga likita kafin mu tafi" Yana gama magana yayi gaba, Ƙannenshi suka bi bayanshi, saida suka bar ɗakin matan suka fita su kuma. "Dr yaya halin da yarinyarnan take cikine? Hankula duk sun tashi" Dr ya dubi Ba Bakura yace. "A taya ta da adda'a. Ƙwaƙwalwarta babu wata matsala. Dan jiya dole likitan ƙwaƙwalwa saida yazo ya dubata. Ɗimaucewa tayi, wani sa'in yana iya fin hauka ma, sannan a tsorace take, tsoronne ya sanyata cikin ɗimuwa, a sakamakon abunda ya faru da'ita. Sabida ƙwaƙwalwar tata, tana hasko mata abunda ya faru da'ita, shi yake haddasa mata wannan firgita da ihun. Sannan daɗin daɗawa tana cikin zafin ciwo sosai, dan taji raunuka manya. Sai dai muna iyakar ƙoƙarinmu wajan bata kulawa." Jikinsu a mace mus suka bar asibitin. Gabaki ɗaya manya da yara, maza da mata, Ba Bakura yace su je falonsu ayi saukar tare. Kasancewar suna da yawa, yasa nan da nan suka sauke Qur'ani mai girma. Sukaita ma Yahanasu adda'a. Ba Bakura yayi tofi a ruwa a kofi, ya zuba a cikin gora, yace akai Asibiti, in Yahanasu ta farka a bata ta sha, a shafe mata jikinta da ruwan tofin. Sannan ya wakilta Bulama ƙarami a yanka rago, ayi sadaka, sannan a nemi miskinai a basu sadakar kuɗi. Duk yasa aka harhaɗa kuɗaɗen sadakar. Zukatan ƴan gidan duk a jagule. A cikin wannan yanayin na damuwa, gidansu Nasiru mai shirin auren Yahanasu suka ji abunda ya faru da Yahanasu. Ba shiri mahaifin Nasiru ya wakilta mahaifiyar Nasirun akan taje gidan taji me ake ciki. A kunyace Bagulaji tayi ma mahaifiyar Nasiru bayanin halin da Yahanasu take ciki. Kuma tace zasu je asibitin zuwa dare su dubo Yahanasun. Lokaci ɗaya zancen Anyi ma Yahanasu fyaɗe ya bazu a anguwa, labari har ma'aikatar su Yahanasu sunji labari. Zuga guda suka je dubiya asibiti. Amman sun tarar da su Hajja Gana a waje, a zazzaune, dan ba lokacin dubiya bane lokacin, jajanta musu sukayi, suka ajjiye ledar lemo da ayabar da suka harhaɗa kuɗi suka sai mata. Ofishin ƴan doka: Wasu Tsofaffi mata da miji na gani zaune a ofishin D p o matar sai matsar hawaye take yi. Shi kuma namijin sai ajjiyar zuchiya yake saukewa. "Kuka ba naki bane, yin wannan kukan yana nuni da cewar kina bin bayan mummunan aikin da ɗanki ya aikata ko? Fyaɗe yayi mata fa, ita kuma zafin keta mata haddi da yayi yasa ta kwaɗa mishi dutse ya mutu. Ai yafi mishi sauƙi daya mutu, dan da iyayen yarinyar daya ma ɗanyan aikinnan sun kama shi da rai, da ɗanye zasu cinyeshi." Mahaifin matashin da yayi ma Yahanasu fyaɗe yace. "Ranka shi daɗe, maganar gawar yaron, a taimaka mana muje asibiti mu ɗauka, ayima yaronnan sutura. Ko a yanzu yaga aya, tunda da yanzu yana cikin makwancinshi, mutuwar wulaƙqnci da ƙasƙancin da yayi ma ya'isa, mu kammu dama ya riga ya zame mana ƙarfen ƙafane, ni bana jin takaicin mutuwarshi sam, na dai fi son ayi mana alfarma a bamu gawar mu binneta, abunda ya shuka shi zai girba ba, kuma duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka." D P O yace. "Zaku iya ɗaukar gawar ɗanku, tunda likitoci sun gama bincike, maniyyin da aka samu a jikin yaron, maniyyin ita yarinyar da yaima fyaɗene, ƙwararru sun auna. Da ƙyar aka samu yarinyar ta tabbatar ma mai jinyarta, cewar ita ta kashe yaron. Babu wata doka da zata yi aiki akai, sabida a cikin ɗimuwa da fitar hayyaci take, babu wata doka da zata hau kanta, domun a hanyar ceton nata ran ne ta kashe taƙadarin ɗanku dake neman tata rayuwar, kuma duk mutumin da yayi kisa domun kuɓutar da kanshi daga kisa, bashi da laifi, kamar yadda ba'a shari'a da mahaukaci, haka ba'a zartar da hukunci akan ire_iren su Yahanasu. In kuma kuna ganin a turaku kotu to" Cikin sauri iyayen wannan mamaci suka ce, babu wani kotu da zasu je, su sun yafe, kuma a ta ya su roƙon gafarar iyayen Yahanasu. Haka suka fita harda godiya a hakanma.Da haka wannan zancan ya mutu mus, ba'a ƙara tado dashi ba. Lokaci yaita tafiya cikin damuwa da zulumi. Babu laifi Yahanasu tana samun sauƙi, kuma ta dawo cikin hayyacinta. Sai dai ta zama shiru_shiru bata son magana sam. Ranar da iyayen Nasiru suka zo dubata, kasa magana tayi dasu sai hawaye, Nasiru ya tausaya mata ganin yanda tai wata iriyar muguwar rama, kamar ba Yahanasu ba. Kwananta goma a asibiti aka sallameta, suka dawo gida, da jikin nata ya ɗan yi ƙwaɓi sai ta soma yin azumin daya wajabta a kanta na kisan kai da tayi. Wannan kenan. YAHANASU: Ina kwance akan gadon Ya Innana ina karanta littafin addu'o'i, Ya Innana ta shigo da sallama, ita da Fanna. Waje ta samu ta zauna a kan gadon, Fanna kuma ta zauna a kujerar dake cikin uwar ɗakin. "Yahanasu, abunda zan sake somawa dashi shine. Haƙuri da yarda da ƙaddara. Bana jin daɗin ganinki a cikin wannan yanayin. Sai ciwon damuwa ya kamaki ai. Jiya Yaguji har ɗakinnan ta shigo ta sameki, amman kinƙi ce mata komai. Kiyi haƙuri abunda zai faru ya riga ya faru, saimu rungumi ƙaddara baki ɗayanmu, ni na fiki jin zafin yadda rayuwa tayi dake, amman ki sani hakan ba wai yana nufin ƙarshen rayuwarki ba ne. Jibi akwai taro da Ba Bakura ya tara, duk ƴan uwa za'a taru. Abunda ya tsayar da Mama Gana kenan bata koma ba. Maganar janye aure da iyayen Nasiru suka yi, suka ce a dakace su kuma. Karya baki tsoro, rayuwarnan cike take tab da ƙalubale, kiyi haƙuri, hakan karya dame ki, in ma rasa Nasirun ki ka yi, Allah zai ɓullo miki da mafiyinshi, kuma in dai har ya gujeki, ki sani dama ba masoyinki bane, sai ki gode ma Allah da ya sa akai walƙiya." Murmusawa nayi na dubi Ya Innana. Ni dama aure da sha'anin maza duk ya fice mun a raina. Inason ni kaina a bani lokaci in samu cikakkiyar nutsuwa tukunna. Mikin dake zuchiyata dai har abada bazai gogu ba nasan wannan. Ya Innana, na karɓi dukkan ƙaddarar da rayuwa zata zo mun dashi a gaba ma. Allah shike tsara mana rayuwa ba mu ba. Duk yanda kuke so haka zanyi. Maganar dakatar da maganar biki da iyayen Nasiru suka yo aike kuma. Ya Innana, ni a tawa fahimtar iyayen Nasiru basa son ya Aureni ne, shima kanshi ya dena sona, ƙila dama ba son gaskiya yake yi mun ba, gangar jikina kawai yake so. Sun mance cewar babu wani bawa dazai iya tsallake wani abun da kanshi, face wanda ubangiji buwayi gagara misali ya tsallakar dashi ba. Ni a sanar da iyayen Nasiru cewar na haƙura na janye gabaki ɗaya. Tun kafin su su ce muku hakan, dan nasan zaku ji ciwo gaya. Ku taya ni da adda'a Ya Innana, ina cikin damuwa mai yawan gaske, zuchiyata zafi take yi mun" Ya Innana ta dubeni da kyau tace "Naji daɗi da kika fahimci inda surukanki suka dosa, janyewarki, da danganarki ta matuƙar faranta mun. Kuma nasan lallai turbar haƙuri da juriyar dana ɗauraku akai, lallai kun hau. Na sani na baku tartibiyar tarbiyya da akeson ko wacce uwa ta baiwa ƴaƴanta. Mun baku ilimin Arabi da Boko. Yahanasu ni kaina zanfi son ki manta da Nasiru ki shiga sabuwar rayuwa. Allah yayi muku albarka duka" Da Ameen" muka amsa ni da Fanna. Haka dai lamurana suka ci gaba da tafiya. Duk wani jin daɗi da ake ganin jin daɗine, ni bana sonshi, bana kallonshi ma a matsayin jin daɗi. Bana son hayaniyar kowa, kuma ban cika son fitowa in haɗu da jama'a ba, tsoron kowa nake ji, gabana faɗuwa yake yi, ko da ƙaramin ƙara naji a gefena, ko wata sowa. Wayata ma kashewa nayi, na tura a jakata. Yau gidan namu an tashi da shirin gudanar da taron da Ba Bakura ya haɗa. Har munyi wanka, mun karya Ba Modu kawai muke jira." Ba Bakura: Waya ce a hannunshi, yana ta faman kiran wayar Bulama Babba. Amman tana ringin ba'a ɗagawa. Sunturi ya shiga yi a babban falon nashi. Idanunshi sun kaɗa sunyi jawur. Ya rasa meya canja mai tunanin ɗanshi, da har ya gujesu haka. Aita kiran wayarshi bazai ɗaga ba, kuma shi bazai kira ba. Zuwa duba iyaye da dangima sai ya bushi iska yake yi. Zama yayi akan kujera, yana kallon lokacin da Bulama Babba yake rarrafenshi a falon. Da kuma lokacin da yake raba dare yana aiki a falon. Yarone mai ƙulafacin iyaye da ƴan uwa sosai. Ko lokacin da ya tafi Kaduna karatu, ba'ayi tunanin zai iyaba ma. Amman a haka ya daure, sai dai fa kullum sai yayi kiran waya. Lokacin da ya soma ɗaukar albashi kuwa, ƙannenshi mata sunji daɗi sosai, mutum ne wanda abun hannunshi sam basu dameshi ba. Wani irin jiri Ba Bakura yake ji daga zaune, sanadiyyar damuwar juya musu baya da Bulama Babba yayi hawan jini ya dokeshi, ko da yaushe a cikin shan magani yake. Sabida shaƙuwarshi da Bulama Babba ta dabance, dan aboki ya ɗaukeshi ba ɗa ba. Hajja Gana ce ta shigo cike da sallama, tana sanye da lafaya mai kalar baƙi da fari, tasha ƙunshi baƙi, ga ƙamshi na tashi ta ko ta ko ina a jikinta. ( Kunsan kanuri ma ba baya ba wajan ƙamshi da ƙunshi) Kallon me gidan nata tayi, kallon shari'a, kawar da damuwarta tayi ta nemi waje ta zauna, sannan tace. "Bulama ya ɗauki wayarka kuwa, ko har yanzu matarshi bata bashi izinin ɗaukar wayarmu bane?" A raunace take maganar muryarta tana rawa tamkar mazari. Kallonta Ba Bakura yayi, yace. "Tun jiya nake faman kiran wayarshi, har yau bai ɗaga ba, yanzu na gama kiranshi amma ina. Bana neman dukiya a wajan Bulama Babba dan da dukiyata yaci yasha, yai karatu, har ya zama mutum, yayi aure. Tunda matarshi da yaranshi yana ganin sun isheshi rayuwa, ai shikenan. Bazan sake ɗaga waya in kira Bulama ba, ko zuwa yayi karki sake ki kawoshi gareni, in kuwa ki ka yi Hajja Gana zaki ga fishin Bakura. Duniya ce ai mai ido a tsakar ka, akwai ranar da zai gane babu abunda yakai Ahali daɗi." Tari ne yaci ƙarfinshi. Hajja Gana kuwa, sai haɗiɗiyar zuchiya kawai take yi, ta rasa me zata ce. Iya damuwa da tunani, harma da kukan babu wanda bata gaji dayi ba. Tana ji tana gani, ɗanta data ɗauki ragamar kula da rayuwarta, yau an wayi gari ya fifita wata mace sama da'ita mahaifiyarshi. Sallamar Ba Modu da iyalanshi ne ya katse musu damuwar da suke ciki. Sun zauna ba'a jima ba, Mama Gana ta shigo. Ba Baana da nashi iyalan suma sun shigo. Falo ya cika dam da iyaye da yara. Kowa ya saurara yana jiran Ba Bakura. Ba Bakura: "Modu ka buɗe mana wannan taron da adda'a domun kawar da shaiɗan, da naiman albarka." Ba Modu ya tashi tsaye ya gabatar da adda'a mai tsayin gaske, aka shafa ya zauna. Falon ya sake ɗaukar shiru na wasu daɗiɗu kowa da tunanin dake cikin zuchiyarshi. Ba Bakura kawai ake saurare ya soma magana......✍🏻 Mrs Bukhari ce GIDAN ƘAMSHI. Hajiya in kina neman turaren wuta, turaren kaya, turaren tsugunno, turaren wadrope, turaren mopping, turaren labule, humrori nau'i daban daban, KULACCHAM masu ɗan karen daɗi dan gyaran fatarki, Room freshner masu ƙamshin daɗi. To ki nemi Mrs Bukhari in dai harkar ƙamshine kin samu. Turarena na manyan mata ne, ba daku ake yi ba kucakai. _GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 _1-NIHLATUL-KHAIR_ 👇🏽 *(Ummu Affan)* _2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_ 👇🏽 *Badi'at Mrs bukhari* _ZULFA_ 👇🏽 *Ummu maher(miss green)* _Littafi ɗaya;400_ _Littafi biyu;800_ _Littafi uku;1000_ Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 Masu tura kati

Chapter 2 of 11