Amman kiyi mata kisan mummuƙe, wannan nasan kin ƙware sosai a kai, nasan ba zaki bani kunya ba. In baki dage ba, itace zata dage a kanki. Kinga Adam yau zai dawo daga tafiya, na gama shan magunguna, na matsi duk na matsa, yau gidan zamu tayar ƙawata " Dariya nayi nace.
Ai ƙawata jiya duk da dai naji zafin rashin Bulama a gefe na, hakan bai hanani bacci ba, kuma cikin kwanciyar hankali na gudanar da burne layar da boka ya bani. Ai ni na daɗe banga aiki yanka wuƙa irin wannan ba. Ƙawata nagode, bani account number ki in tura miki dubu ashirin kya siya ma yara wani abun." Da murna Mabaruka ta bani account numbern ta, a take na tura mata kuɗin, mu kai sallama na fito. Sagira sai faman cin uban aiki take yi, tamkar baiwa. Kai tsaye gida na wuce. A zaure naci karo da Sagir zai fita. Yana ganina yaja dogon tsaki yace.
"Marasa tsoron Allah, da sannu zaku ga ƙarshenku yanda zai kasance" Da sauri nasha gabanshi, ina muzurai duk da ya kereni tsayi sosai. Na buɗe baki cikin faɗa da ɗaga murya nace.
Wai kai dan ubanka ina wasa da kai ne, harda mama kake zagin cewar bata tsoron Allah? To ubanka muke tsoro kenan ko"
"Ke wallahi in baki iya bakin ki ba, zan gwabgwabjeki ne wallahi, ba ƴar sanda ba, ko soja ce ke sai in tattakaki anan" Yana faɗan haka kafin ma ya rufe baki, na wanke shi da mari, ai kuwa kafin in sauke hannu ya rama. Nan kokawa ta kaure a tsakanina da Sagir mune har wajen layi, na ruƙunƙuneshi, sai dukan ƙafafunshi nake yi, shi kuma sai dundu yake faman zuba mun. Da ƙyar Mama tasa hannu ta janyomu cikin zaure, dan har magulmatan matan layinmu masu zaman gulma da tsugudidi sun soma taruwa.'
"Sagir ka kasheni ka huta nace shege matsiyaci. Yarinya itace cinmu itace shanmu, hatta kuɗin makaranta wake biya muku in ba itaba, amman ka rasa da wacce zaka yi rashin darajarka sai yarka, me yasa baka da tarbiyya ne, tunda ka fara shaye shaye kake neman fin ƙarfina, hawan jini kake son ɗaura mun ko? Shikenan. Cikin hargowa da ɗaɗɗaga hannaye yace.
"Ni gaskiya mama adena mun kutsu cikin rayuwata. Ba gara ɗan shaye shaye sau dubun dubata ba, da masu bin bokaye da ƴan tsubbu ba? Kija mata kunne wallahi ta kuma shiga harkata sai na sa huƙa na soki cikinta hangin cikinta sun futo, ƴal bura uba kai, batun makaranta da mijinta yake biya ya ma dena biya bama zuwa daga ni har musan yaudarace kawai" Yana gama rashin mutuncinshi ya bangaje Mama ya wuce."
Mama duk kece ai kika sangarta wannan yaron yanzu jibi abinda ya zama, kina ganinshi kinsan a bige yake. Ɗan iska sisina ya dena gani wallahi, su kuma munafukancan har sun soma taruwa suna kallo, alhalin ko wanne gida da abun kunyarsu, mu da sauƙi ɗan daba muke dashi ai, babu wacce ta taɓa zubar da cikin shege." Hannuna Mama taja zuwa cikin gidan, a tsakar gida muka zauna Asiya sai aikin suyar kaji take yi. Ga moltina katon guda, da ruwan swan katon guda a gefe. Mama cikin damuwa tace.
"Zubaina al'amarin Sagiru fa ya wuce intaha. Baya kwana yanzu a gidan sam, ga ɗiban albarka kashi kashi, yanzu ya gama boll da butocin gidan kin gansu can wasu har sun fashe. Kwararo kwararo suke shiga yawon shaye shayensu. Babban damuwata ma tafi yawa akan, Ƙaninku Musa. Jiya da asuba da mace naci karo a cikin ban ɗaki ta fito daga wankan salla fa. A cikin gidan ta kwana. Rashin mutumcin Musa har ya kai ya kwana da karuwa a gidan mahaifiyarshi? Hannu duk yanda akayi dangin mahaifinku suka sa musu, anga sune yarana maza, shine aka lalata musu rayuwa. Nama malam koke akansu, ya bani magani, yau zan soma zuba musu a abinci suci. Ko Allah zai nitsa mun su, su dawo cikin hankalinsu." Dubanta nayi, naga duk tabi ta damu nace.
Mama ki dena tada hankalinki a kansu, kina damu, kuma ki dena tsine musu, ƙila ma bakinki ne ya bisu duk suka lalace ɗin. Amman guda nawa Musa yake da har yake bin mata Mama? Kinga ba cikakkiyar lafiya bace dake, ki kwantar da hankalinki dan Allah. Mama mu bar wannan zancan. Bulama ma fa ya shiga tarko wallahi, yanzu kam komai ya kammala, sai yanda naso za'ayi. Murna ce ta kama Mama kamar ba ita bace take cikin damuwa yanzu, yanzu ba. Wayar Asiya ce ta soma kuka, a guje Mama ta kai mata wayar.
"Maza ɗaga ƙila baƙinne suka iso." Karɓar wayar Asiya tayi tace.
"Alhaji ne ke kira Mama, bari in ɗaga inji." Ɗagawa tayi ta kara akunnenta.
"Hello Alhajina, barka da hanya, kaddai har kun iso? Ɗan jim tayi halamar sauraronshi, kana tace.
"To barkanku da shigowa garin gwamna, da fatan zaka gane kwatancen gidan Kawu Tanko da nayi ma ko?" Sai tayi dariya tace dashi.
"To shikenan" Dubanta nake yi nace.
Yaya ake ciki sun iso ne?"
"E Anty suna kan gadar marabar jos. Bari inyi sauri nayo wanka, Mama ɗan ƙarashe mun aikin dan Allah" A guje Asiya ta shige banɗaki. Mama kuma ta shiga zuba pepper kickhen a cikin kula. Musa ne ya shigo da sallama. Yana ganina ya shiga dariya.
"Anty Zubaina kece da yamma haka a cikin gidan?"
Nice Musa ya karatun ana dai yi ko?" Dariya yayi yana sosa kai yace.
"Anayi dukkanmu har Sagiru duk muna zuwa, yanzu haka ma jarabawa muke yi, ta zangon ƙarshe, zamu shiga level 2. Washe baki nayi cikin yaudara irin ta polisawa ban nuna mishi Sagiru ya sakar musu ɓera a yayi ba.
To Allah yayi talmako" Mama ta daka mishi tsawa.
"Dalla zo ka kwashi kayannan ka shigar mata mota, ka karata can gidan Babanku Tanko, tunda Allah yasa ka dawo daga yawon barbaɗar taka. Ba dai karuwanci ka zaɓa ba Musa, gaka ga bariki ai, batun makaranta da kake zancan jarabawa, Sagiru ya fallashi asirinku bakwa karatun. Kan ku ku kaima ai maza ne ku, kuyi abinda kuke ganin ya fiye muku" Yana kunƙunni yaje ya amshi kular hannun Mama ya fice, yana zagin Sagiru. Ɗaya bayan ɗaya ya zuba duk kayan a mota.
To Mama bari muje, koma dai me ake ciki, zamu yi waya. Nasan ma Kawu Tankon zai kwaso dattin talaucinshi yazo yai miki bayanin komai ma" Dariya muka yi dukanmu muka fice a gidan. Kai tsaye zuwa anguwar dosa gidan Kawu Tanko. A ƙofar gida muka same shi, da almajirai manya yana biya musu karatu. Sana'arshi kenan tunda muka taso. Tsangayace dashi, wacce yake koyama yara karatun allo, kuma yakan tura ƙauye ƙauye a kawo mishi almajirai, har kangararru ana kawo mishi, kuma yana ladabtar dasu, ta hanyar duka, horo mai tsanani, da shan rubutu a ko wacce safiya, sannan suma suna yin karatu sosai, sai dai su basa bara, a ko da yaushe a cikin mari suke, iyayensu ke biyan kuɗin kulawa dasu. Da wannan sana'ar yake ciyar da matanshi biyu, da yaranshi fin goma sha. Duk da a halin yanzu duk ya aurar da yaranshi, maza da matan, jikokine cike da gidan dai.
"Zubaina yau kuma kune a tafe a gidan namu, harda kai Musa idanunka kenan, ina sauran ƴan uwan naku?
Sagiru ya fita, Asiya tana gidan Mama, Nafisa kuma tana gidana. Kawu mun same ku lafiya? Da fara'a yace.
"Lafiya lau Zubaina, ya mai gidan naki da yaran naki fa?"
Duk suna lafiya Kawu"
To to madallah. Isiya ma yana hanya, nayi kiranshi tun jiya nake shaida mishi batun masu kawo sadakin Asiya. Yau yace zai tawo, duk inda yake yanzu ƙila ya kusa isowa ma. Tunda mu biyu muka rage muku, dole duk wani abun in ya taso mune dai ko da bama so zamu shige muku gaba, sabida martabarku ma." Ana cikin haka sai ga Kawu Isiya ya iso, da wata shadda jemammiya a jikinshi ɗinkin malum malum. Sai uban sauri yake zabgowa, malum malum ɗinnan na cika da iska. Yana isowa ya cika wajan tab da warin hammata"
MRS BUKHARI
ANAN NA KAWO ƘARSHEN FREE PAGE, KU BIYONI DAN ƊAUKAR DARASIN DAKE CIKIN WANNAN LITTAFI. LABARIN YANZU ZA'A TSUNDUMA CIKINSHI GADAN_GADAN. KO YAYA WANNAN ZAMAN ZAI KAYA KUWA? KAR KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE, NERA ƊARI HUƊU NE, IN MA KUƊINKI BAI KAI BA KI NEMI ƊAYA DAGA CIKIN NUMBOBINMU ZAKI SAMU RAGI IN SHA ALLAH.
*MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!*
Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online
Gakayanmu kamarhaka
Tafi budurwa duniyane
Tsumin lahaula
Gombar bujenki jagab
Shu Umar zumarmu
Mumuna da,aeki
Makalemata
Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara
Dahuwar kaza cicibin kala kala
Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata
Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari.
Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma
AMARYA
MAI JEGO
WACCE ZATAYI KOME
Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji.
Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure.
Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo.
_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 July 20 in sha Allah._
_1-NIHLATUL-KHAIR_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
_ZULFA_
👇🏽
*Ummu maher(miss green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
08104335144
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
07068606171
08179523215
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels