AMMAN BIYAR ƊIN FARKO BA. AN RIGA AN DAƊE DA SOMA BIYAN LITTAFIN GAWURTATTU UKU, TUN KAFIN MU SOMA POSTING. WANNAN MUNA MAGANA NE DA WAƊANDA ZASU BIYA BAYAN MUN KAMMALA FREE PAGE ƊINMU. ( FATIMA SULAIMAN ITACE TA FARKO DATA SAI LITTAFAN GAWURTATTU UKU TUN KAFIN MU SOMA. TATA KYAUTAR TA MUSAMMAN CE) DOMUN ƘARIN BAYANI SAI KU TUNTUƁEMU A NUMBOBIN WAYAYOYINMU. MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU ✍🏻*
Yahanasu:
Haƙiƙa Kanuri suna ɗaya daga cikin ƙabilun da suka fi ko wacce ƙabila iya riƙon aure, dama gudanar da Al'adu a yayin Aure. Al'adun nasu sun haɗa da.
*BAWARAM* Kalmar Bawaram tana nufin Iyaye maza. Idan kuma a aure ne aka ce Bawaram tana nufin kayayyakin da ango yake yi wa dangin Amarya, waɗanda suka haɗa da kayan. Uwa, matar uba, da ma ƙannen uba, da yayyensu, babbar yar Amarya, kakannin, mai kitson Amarya, da uwar ɗakinta in tana dasu, duk sai ango yayi musu kaya.
*FAFURAI* Fafurai kuma, wani akwati ne da gidan Amarya suke yiwa Ango, abunda ake sawa a cikin akwatin sun haɗa da, shaddaji, da yaduna, huluna, da, takalma, agogo, turare, sallalaya, Qur'ani da sauransu. Kuɗi ake kashewa bana wasa ba, sabida dangin amarya suna son yiwa ango bajinta.
*WUSHE_WUSHE* kuma bikine da ake gudanarwa tsakanin ɓangaren amarya da ɓangaren ango, ana gobe ɗaurin aure. Ɓangarorin biyu sukanyi shigar al'ada irin ta Kanuri su haɗu a wani farfajiya, ko, waje mai fili dan gudanar da wannan bikin Al'ada. Mu a gidanmu muke gudanar da wannan biki, kasancewar gidan da girma. A wajan bikin ana keɓe Amarya da ango, a wani ƙayataccen gado, sa'ilin da makaɗan gargajiya ke kiɗa. Ƴan mata da abokan ango kuma, zasuita rausayawa a gaban ango da Amarya, irin rawar al'ada. Daga nan kuma sai liƙin kuɗi tare da yin hotuna kuma. Wushe_wushe na ɗaya daga cikin bikin auren Kanuri da yaruka da dama suka ara suka yafa a Najeria.
*QLATUL* Yana nufin wanke kai, mata kaɗai ake yima. Ana gudanar da wannan bikine, idan aure ya rage saura kwana uku. Yadda ake yinshi shine, Iyayen Amarya ke wanke mata kai da karkashi. Bayan an kammala wanke kan, ana yin kiɗan ƙwarya, wanda tsofaffin mata ke waƙa cikin harshen Kanuri. Shi wannan kiɗan ƙwaryar, irin na al'adar ƙabilar hausawane sak.
*KALAWA* Tamkar shaɗi yake, sai dai shi ba'a duka. Yanda ake yinshi, akushi ake tanada, da bushasshen karkashi, da ɗanyar shinkafa. Sai a ɗaura ango da Amarya akai su zauna. Dama an riga an ɗaura tuwon buski a wuta, ana saukewa da zafinshi za'a ɗebo, a zuba a tafukan Amarya da ango. Amarya da ango, sai su juye wannan buskin na hannunsu a cikin akushi. Ana yin haka har sau uku, sai a goge musu hannayensu, a shafe musu da bushashahen karkashi. Daga nan sai ƴan uwa da abokan arziki, su zo suyi musu kyaututtukan arziki, wasu har gida da mota ake basu, ga masu bada kuɗi, ko sarƙar gwal, ko kuma jari. Ma'anar bikinnan shine, kamar yadda suka jure zafin abincin da aka zuba musu a hannu, Allah yasa su jure zaman Aurensu fiye da hakan.
*KA'AJI* Ka'aji yana nufin turaren wuta, ango shi yake yi ma amarya.
*HUMRAM* Turarene na ruwa wanda ake shafawa a jiki, mai ɗauke da surruka masu dama. (Mai bukata tayi mun magana ina siyarwa) shima ango ke yinshi, ko ya bayar da kuɗi ayi ma amarya.
*KULECHAM* Mai ne mai ƙamshi, tare da ɗumbun sirrikan itatuwan gyaran fata, da laushin fata. ( Me so tayi mun magana ina saidawa)Shima ango ke bada kuɗin siyanshi.
*KALAM WURI* Wani abune ƙarami kamar kabbasa, wanda ake manne shi da kuɗi gaba ɗayanshi a bawa Amarya ta tafi dashi ɗakinta, a matsayin kyauta. Duk lokacin da buƙatar kuɗi ta taso mata, kuma babu kuɗi a hannunta, saita zari kuɗi daga cikin wannan kuɗaɗe ta kashe wutar gabanta. Ita wannan al'adar takwarar Amarya ce take yi, idan bata nan ta mutu, sai ƴaƴanta su wakilceta.
*KNDAI* kalmar kndal yaren kanuri ne. Kndal wani ɗan kwanone mai kama da akushi, wanda ake saƙashi da kaba ( ADUDU SUNANSHI DA HAUSA) Ana yi mishi ado da fure, sai a zuba goro, dabino, Shi wannan amarya ake ba ta tafi ɗakinta dashi. Idan mijin mai cin goro ne, sai ya dinga cin goro a ciki, in mai cin dabinone, sai yaci a ciki.
*KUSUSURAM* A binda ake nufi da wannan kalmar ana nufin kai kayan lefe. Yadda ake kai lefe a al'adar Kanuri. Idan aka tashi kai lefe gidan iyayen Amarya. A al'adar Kanuri ana haɗawa da tinkiya, masu ƙaramin ƙarfi kenan, masu dashi kuma bijimin sa suke haɗawa dashi. Za'a ɗaura atampa a wuyan dabbar a yayin da za'a kai kayan lefen. Wannan atampa da aka ɗaura a wuyan dabbar idan anje gidan iyayen Amarya suna ba da ita kyauta ga wanda ko waɗanda suka riƙo dabbar, aka tawo da lefen.
*WUSHE WUSHE YAA'YE* Shi kuma ana yinshi ne a ranar Alhamis Yadda akeyi shine. Dangin Amarya zasu haɗu su yi nakiya, a yayin da ɓarayin ango kuma zasu kawo musu goro tare da yi musu sannu da aiki, sai ɓarayin Amarya su ba su wannan nakiyar.
*NALLE* Sa lalle kenan yake nufi, ranar talata akeyinshi. Ɓangaren ango zasu kai buhun lalle, da katon_katon na minti, da huhun goro, da tarkace dai iri iri.
*TULUR* Tulur a Kanuri yana nufin bakwai. Shi tulur a auren Kanuri kuma yana nufin zaman bakwai da mace ɗaya ko biyu suke yi a gidan amarya na tsawon kwanaki bakwai. A wannan zaman waɗannan mata zasu dinga ma Amarya share_share girki, wanke_wanke da dai sauransu, ita kuma zata samu damar kula da mijinta. Bayan kwanakin sun cika ango yana yiwa waɗannan matan kyautar Atampa da sabulai da turare, wani ma harda ƴan kuɗaɗe.
*KSAI LEWA* Gaisuwar iyaye. Ana yinsa ne a washegarin ɗaurin aure, inda ango da abokanshi zasu kai ziyarar gaisuwa zuwa gidan iyayen Amarya, tare da godiyar bashi ɗiya da'akayi.
*KAULU* Wannan al'adar angwaye kaɗai ta shafa, washe garin ɗaurin auren shima akeyi. Karkashi ake damawa da ruwa, sai mahaifin Ango ko ƙanin mahaifinshi, wani lokacin ko mai gidanshi na wajan aiki. Sai a shafe hannayenshii da wannan ruwan damammen karkashin. ( Wannan fata ne, na duk abinda zai samu ya yauƙaƙa, ma'ana yayi albarka)
*GANGA KURA* Shi kiɗan gargajiya ne, wanda dangin ango da dangin amarya, ke haɗuwa a waje guda, su rausaya a tsakani, tare da yima juna liƙi.
Waɗannan al'adun suna daga cikin jigon da ya sa Kanuri suka fi ƙabilu da dama juriya wajan riƙon aure. Sabida kuɗaɗe masu tsokar gaske ake kashewa wajan hidimar biki, hakan yana daga cikin dalilin da yasa sauran ƙabilu suke tsoron auren matan Kanuri, sabida tsadarsu. Kuma hakan yasa matan kanurai sai sun gansame suke aure. Domun samarin ba ƙaramin tanadi suke shafe shekaru suna yi ba kafin akai ga yin aure. Wannan yasa ba'a saki a cikin ƙabilar Kanuri sabida tsadar da aure yake dashi. Namiji na tunanin in ya saki matarshi, sai ya kuma kashe miliyoyi kafin ya samu nasarar mallakar wata macen.
Dukkannin wannan al'adun sai da aka gudanar dasu, waɗanda ake gudanarwa a tsakanin ango da amarya ne kaɗai, ban samu halarta ba, kasancewar nawa gogan yayi mun nisa. Amman Ba Bakura yayi rawar gani, dukkannin wani abu da ango ke yi, saida yasa akayi mun. Hajja Gana, itama tayi ƙoƙari sosai a nata ɓangaren. Ba Modu shima ya kashe kuɗi sosai a cikin akwatin Ango, kasancewar su Ba Bakura sunyi ƙoƙari sosai a kaina, shima saiya zage, ya zuba tsadaddun kaya na alfarma. Ya danƙa akwatin a hannun Mama Gana. Bayan an kai ko wacce Amarya gidanta. Munsha kukan rabuwa da juna sosai, amaren su Bulama ƙarami suma duk an kakkawosu. ni kuma washe gari ake shirin kaini nawa gidan, jina nake yi wani sukuku, a daren ranar da ake gobe zamu tafi, Ya Innana ta mun nasiha, tare da ɗorani akan wani karatu, na iya jawo hankalin miji zuwa gareka, ta bani wasu turaruka haɗi na musamman, tace in adanasu, da sun ƙare inyi kiran waya na sanar da'ita, za'a turamun da wasu, ranar kusan raba dare nayi ina kuka. Motoci uku Ba Bakura ya tada na ƴan rakiyana, motar kaya tuni tayi gaba.
Ina gurfane a gaban Ba Bakura, sanye nake cikin lafaya ja jawur, mai adon Golding, wuyana da kunnena maƙale da ƙaramar sarƙar gold wacce aka saka mun a cikin kayan lefe. Ƴar duma duma ce ni sosai, dan nafi kowa ƙiba a gidan. Gajerace ni, kuma baƙa wulik, dan abune mai matuƙar wuya ka ga farin kanuri. Hancina gajerene, kuma mai ɗan faɗi, fashin goshi ne, tunda daga goshina har ƙarshen hancina, da wasu zane bibbiyu masu faɗi a gefen fuskata, haka yake a zane a fuskar ko wanne ɗa a cikin gidan. Su Ba Bakura ko fuskarsu babu masaka tsinke da zane, nasu irin na asalin kanurai mazauna tsakiyar ƙauyene. Ina da gashi mai laushi, da ɗan tsayi dai_dai misafi na zahiri, dan jelar kitsona bata wuce tsayin wuyana ba. Idanuna manya ne, bakina kuma ɗan madaidaicine, mai kaurin labɓa leɓennan baƙiƙƙirin dashi, ina da wushirya a tsakiyar haƙorana da suka kasance mai ruwan madara. Kirjina cike yake da mama, amma bani da tudun madaunai, bani da shape asalima nafi girma ta sama ba ta ƙasa ba, saɓanin mata masu diri da suka fi faɗi ta ƙasa. A taƙaice bana cikin sahun kyawawan mata sam na kaina na sani. Kuma nasan ni mummunace sai dai Alhamdulillah na samu ilimin addini mai zurfi.
Ba Bakura
"Mama Gana, ga Yahanasu na danƙata a hannunki, ki danƙata a hannun Bulama Babba. Ki sanar mishi inya wulaƙanta Yahanasu, tamkar mu iyayenshi ya wulaƙanta, kuma bazan yafe mishi ba. Ki zauna da'ita ke da Yanunu kuyi mata Tulur ɗinta, ( zaman bakwai) Bana son a tauyeta. Sannan ki kaita gidan Abokina Alh Munka'ilu, zan baki number wayarshi, zai samo mata aiki, gidanshi yana nan ta wajan SULTAN BELLO Babban masallacin juma'a na Kaduna. Yahanasu Allah ya zaunar dake lafiya a gidan aurenki, Allah ya miki albarka bisa umarninmu da kika bi, nima zanzo da kaina inga ɗakin ki in sha Allah. Motar da zaki shiga a kaiki a ciki, na mallaka miki ita, ki dinga zuwa wajan aiki da'ita. Kuje Mama Gana" Fitowa akayi dani, sai zagaye akeyi dani wajan iyayena maza, kowannne cikinsu kalmar haƙuri da juriya dai suke ta faman nanata mun. Daga bisani muka shiga mota, mu ka ɗau hanyar Kaduna. Tafiya ce wacce bazan taɓa mancewa a cikin tarihin rayuwata ba, kamar yadda yau ta kasance ranar da babu wani abun da zai zo ya gogemun ita a zuchiyata. Damuwar da nake ciki, ya wuci gaban gwatance ko misalin da mai karatu zai fahimta. Idanuna a buɗe suke, ina kallon jejunan da muke wucewa da gudu, a zahiri inka kalleni abunda zaka yi tunani kenan, amman a baɗini kuma, tunanin rayuwar da zan tsinci kaina a ciki nake yi. Yanzu har aka gama shagalin bikinnan Babu Bulama Babba, babu labarin ya bugo waya, kuma yasan da zaman bikin yaran gidan, dan bikine da aka tsaida lokaci shekara guda daya wuce. Kuma tun daga lokacin da aka sa bikin, aka sanar mishi. Ajjiyar zuchiya na sauke, na dawo da dubana cikin motar, Hajja Fati ce a gefena da jaririyarta a hannu tana bata nono, sai Mama Gana a kusa da'ita. A gaban motar kuma, Bulama ƙarami ne yake janmu, suna zaune shi da Yanunu, sabida tsabar soyayyar ƴan uwantaka ne yasa ya baro filleliyar amaryarshi, yake son rako ƙanwarshi. Hawayene ya gangaro a kumatuna. Allah sarki gidanmu me daɗi, wani sa'in haka zamu haɗu a babban falon Ba Bakura mazanmu da matanmu, mu zuba biski miyar kuka a babban farantin silver maita ci, ana barkwanci, maƙaryata irinsu Bulama ɓaki suita bamu labaran ƙarya, ana dariya. Surutattun ciki kuwa dama ni da Yaguji ne, baki kamar na cakwaikwaiwa, haka za muita faman zuba. Murmushi ne ya suɓuce mun a lokaci ɗaya. Haka mukaita shatata gudu kamar me. Bamu muka tsaya ba sai a wata tasha a Bauchi. A tashar muka fito akayi Sallah, Wakil ya sai mana balango da gurasa, da abun sha. Muka kuma ɗaukar hanyar Kaduna, Ta Bauchi muka ratse muka bi, sabida hanyace samɓal mai kyau, hanyar samunaka a dagargaje take, duk da munyi zagaye, amman tafiyar tayi sauri, misalin ƙarfe biyar ɗin yamma sai gamu a Kaduna. Bulama ɓaki ya juyo yace.
"Mama Gana, nifa na mance layin gidan Bulama Babba fa, sau ɗaya na taɓa zuwa. Mama Gana tace.
"Hmmm ai dole kowa ma ya mance, ni kaina bansan layinba. Ka kira Wakil a waya, su shige gaba mubi bayansu, in ya san gidan. Suna cikin Magana sai Mama Gana tace.
"Shikenan ma, kaga ga motar kayan Yahanasun ma a gabanmu, su Bagulaji ne a ciki, bisu ita ai duka haihuwar matar Bulama Babban tazo." Gabana ya tsananta faɗuwa, muna tafe tiryan_tiryan har muka shiga Kakuri maƙera, kwanar layin BABBAN DODO muka shiga, layin masallacin idi. Anguwace wacce ta tara ƙabilu iri daban daban, ta kuma tara masu kuɗi da talakawa a waje guda. A bakin wani ɗan madaidaicin gidan ƙasa muka tsaya, masu motar kaya sai faman hon suke. Mama Gana ta fita a cikin motar, ni dai da idanu na bita.
"Me gadi ya kanaji ana hon, amman kaƙi ka buɗe mana get" Cewar Mama Gana kenan, dan ta'isa wajan ta samu mai gadin na tambayarsu daga ina"
"Hajiya kiyi haƙuri dan Allah, da gani nasan ku ƴan uwan oga ne, amman uwar gida tace mun duk wanda yazo a irin ranakun asabar da lahadi, kar in barshi ya shigar mata gida, sabida ranar hutunsune" Cikin Faɗa Mama Gana tace.
"Dalla rufa ma mutane baki, dokar banza, muna iyayen nashi? Wakil ku bani waya in kira shi Bulaman" Wakil yace.
"Mama da shi mai gadin ya kira a wayarshi, in yaso ya baki, ko yaga number na ba ɗagawa zaiyi ba" Ai nan ta soma ruwan jarabar, ita mai gadi kawai ya buɗe mata get mu shiga. Ni kuwa ina daga cikin mota sai hawaye. Da ƙyar Ya Bagulaji ta shawo kan Mama Gana ta yarda aka kira Bulama Babba a wayar mai gadi. Wayarshi ya ɗaga ya kira Bulama Babba, ringin biyu abun mamaki ya ɗaga.
"Mai gida, kana da baƙi a bakin get, ƴan uwanka ne, duk zanen fuskokinsu irin naka ne, ga kamanni." Bamu ji mai Bulama Babba yace ba, mai gadin yace ma su Mama Gana"
"Yace yana zuwa" Jigum_jigum duk suka yi a wajan.
Bulama Babba:
Da mamaki na miƙe tsaye, na ajjiye Maryam da take hannuna akan doguwar kujera. Zubaina ta kalleni tace.
"Kuma Abban Maryam kana ganin ba gidan da suke nema bane suka rasa ba? Ko kana tunanin danginka zasu shawo tafiya tun daga Damaturu ba tare da sunyi kiran waya ba?" Kai na girgiza mata nace.
Bana tunanin sune, duk da yace akwai kama, kuma suma duk suna da zane a fuskokinsu, bari dai inje in duba" Ina kaiwa nan, na nufi ƙofar fita, a Guje Bawa Ba Bakura Ƙarami ya biyoni.
"Abba zan bika" Kallon yaron nayi, ina jinjina irin tsananin kamanninshi da Ba Bakura takawaranshi. Bance mai komai ba, muka nufi get, ina fitowa nayi arba da ƴan uwana gudan jinina, da iyayena. Farin cikin daya ziyarci zuchiyata ya wuce gaban a musalta, sai washe musu baki kawai nake yi, in kalli wannan in kalli wancan."
"Kaga kasa me gadi ya buɗe mana get mu shiga daga ciki ko, amman in fa matar taka zata baka damar yin hakan" Maganar mama Gana ta dira a zuchiyata, naji zafi ainun. Ni banga laifin Zubaina ba, banga dalilin da yasa ƴan uwana ke ganin laifinta ba. Motocin da naga ni a ƙofar gidan, abun ya matuƙar ɗaure mun kai ainun. Umarni naba mai gadi ya buɗe musu get, duk motocin suka shiga ciki, ina jaye da Ba Bakura Ƙarami, dubana yayi yace.
"Abba waɗannan su suwaye?" Ni kaina naji kunya da wannan tambayar da Ba Bakura ƙarami yaimun, kafin in bashi amsa, Mama Gana tace.
"Allah wadaran naka ya lalace, yaronka ɗan shekara takwas, bai san ɗanginka ba, to yaushe ka kaisu suka shiga dangi balle su saba damu. Albasa dai batai halin ruwa ba. Dalla shige gaba ka nuna mana hanyar shiga cikin gidan, tun kafin ranka ya ɓaci" Da sauri nayi gaba, suka bi bayana. Duk da jarabar da Mama Gana take yi, bai hanani jin daɗi da sanyin ganin ƴan uwana, sunyi gayyar kawo mun ziyara ba. Amman dai naji kunya, dan ƙannena sun kikkira wayata har sun gaji sun watsar dani, sabida bana ɗagawa. Da sallama na shiga falon.
"Mama Gana Ya Bagulaji bismilla ku shigo, ah Yahanasu ƴar lukuta, dama har dake?" Na tambaya cikin farin ciki. Cikin zumuɗi na soma kiran Zubaina, sabida mun shigo bata falon.
Maryam zo ga Babanninki" A guje Maryam tazo, amman Wakil yayi yayi da'ita taje taƙi.
"Ku shiga ga waje ku zazzauna. Bari in kira Zubaina" Zama suka yi, sai ƙarema falon kallo suke yi, tsugunnawa nayi cikin fara'a na soma gaishesu ɗaya bayan ɗaya. Su kuma yara_yaran suka gaisheni.
Mama Gana ya su Ba Bakura, da Hajja, da su Ba Modu?" A fusace tace.
"In kana son kanka da arziki karka kuma tambayata kowa, ba abunda muka zo yi ba kenan. Mandiyar bata jimu bane, data kasa zuwa ta gaishe da iyayen mijinta? Ko da yake ina muka samu darajar hakan a wajanka, balle ita." Murmushi nayi na miƙe, na nufi ciki. A kitchen na samu Zubaina a tsaye ita da ƙannenta mata biyu, da muke riƙonsu. Asiya, da Nafisa. Zubaina ta dubeni tace.
"Wai shin suwaye haka na gansu bataliya guda, tun daga tsakar gida nake ta faman jin yare? Kuma dana leƙa sai naga motoci, harda motar kayan ɗaki? Da fara'a a yalwace a fuskata nace
Ke dai bari kawai Zubaina. Asiya ku kaima Baƙi ruwa da jus maza. Ku ɗauki ruwa catoon biyu, lemo ma haka. Dawo da dubana nayi kan Zubaina nace.
Zuba musu dambun kajinnan in kai musu"
"Amman tambayarka nake yi su waye ko?"
Iyayenane da ƙannena suka zo ganinmu, ina tunanin ko dan sun jini shirune, basu san aiki bane yai mun yawa ba. Nafi shekara biyu ban leƙa Damaturu ba. Ki yi maza kizo ku gaisa, bari in kai musu dambun." Kular da aka zuba dambun kajin na sura dukanta, na kwashi kwanuka na fita na bar Zubaina da sakakken baki."
Zubaina:
Kusun uwa ni za'a kawo ma iskanci ni da gidana? Yanzu meye abunyi, yaya zanyi da baƙinnan, Allah yasa ba zuwa suka yi dan su tuni asirina ba. Hmm amman bari in kira Mabaruka" Zufar data tsattsafomun na sharce, cikina tun shigowar wannan baƙin ya juya, tsabaragen tashin hankali. Ɗakina na wuce da sauri, na zari waya na kira Mabaruka.
"Kofur Zubaina ya gidan, yau kece akan layi ran Sunday, ko dai oga baya gidane. Cikin ƙasa ƙasa da murya nace.
Mabaruka ina cikin matsala babba, dangin Bulama ne suka zo daga Damaturu har mota uku, mazan su da matansu. Ni bansan ma ta yanda zan iya tunkararsu ba, kinsan fa sun tsaneni, sun riga sun gane ni na raba Bulama dasu. In ban rabashi da wannan bataliyar ɗangin nashi ba, yaya zanyi ma. Duk fa albashin daya samu a kansu yake ƙarewa, bini bini kuma gyaji yace zashi Damaturu, almurar uwarshi kuwa, ko da yaushe a cikin kiranshi take, in ma bata kira ba, shi zai kira. Amman tunda naiwa tubkar hanci wallahi ƙawata ko Damaturu na ambata, sai kiga yanayinshi ya canja. Muna fa zaman zamanmu suka tawo bataliya guda" Mabaruka tace.
"Ciɓiri nannagi ƙawata, ai kuwa mai ƙwatarki a hannun waɗannan kanuran sai Allah. Shawara, ki sauke kanki kiyi musu tarbar mutunci, danki shafe zarginki da suke yi a zuchiyarsu, shima ko ba komai zaki ƙara daraja a idanunshi, ƙawata ke fa kika koya mun kissa, ni wajan malamai nafi ganewa, amman ai kissa na wajanki" Dariya nayi, na share zufar data ɓata mun fuska, nace.
Ai ƙawata, wallahi ganin yawansu ne ya firgitani, amman kin ɗaurani a layi, sai munyi waya, gashi can sai faman kwaɗamun kira yake yi, kinsan baya ƙaunar in matsa a kusa dashi" Sallama nayi da Mabaruka, tare da sauke ajjiyar zuchiya. Da sauri na amsa kiran Bulama, nayi falo da sauri ina ƙaƙaro murmushin da kallo ɗaya za'ai mun a gane na bogi ne. Zuchiyata har wani tafarfasa take yi. A gefen Bulama na rusina, kamar yadda na ganshi a rusine. Cike da fara'a na soma gaishesu muryata na rawa. Amman ɗaiɗaiku daga cikinsu ne ma suka amsa mun, ƙannenshi kuwa, ban kalli kowa ba, jira nake su gaisheni, amman naji shiru.
Kin sansu ai duka na sani, Hajja Fati da Yanunu ne kawai baki sani ba. Yanunu ƙanwar mahaifiyar su Yahanasu ne, Hajja Fati kuma ƙawar Ita Yahanasunce." Dariyar yaƙe nayi nace.
Ayya sannunku da zuwa, gaskiya kun shawo hanya, bari in shiga kitchen su Asiya su kama mun muyi abinci, in yaso Nafisa saita gyara musu BQ." Da sauri na fita a falon har ina tuntuɓe, tsabaragen ruɗewa, babu komai a idanun dangin Bulama sai tsagwaron tsanata. Wallahi nima na tsanesu sosai, kuma in dai ina numfashi Bulama ya rabu dasu kenan, dan bazai ƙare a kansu su kaɗai ba. Su Asiya na tarar a kitchen suna surutai.
"Cab Anty wannan baƙi haka cikin gida, sai kace wasu marasa hankali" Cewar Asiya kenan. Baki na taɓe nace
Kinsan ƴan ƙauye akwai rashin kan gado. Yanzu dai ku ɗaura farar taliya, ku zuba ma mayunwata a kula, ku fito da miyar kajinnan a firgi, ku tsuga ruwa dan tayi auki, da kun gama sai in kai musu."
Bulama:
"Waini Bulama Babba naga wasu mata masu ƙirar samudawa a gidan naka, harma sunfi hamshaƙiyar matar taka girma, su kuma daga ina? Da fara'a nace.
"Ya Bagulaji ƙannen Zubaina ne fa, ni nake riƙesu suna karatune, sabida ɗawaikiya tayi ma mahaifiyarsu yawa, Babansu shekara guda kenan da rasuwarshi, shine nace su matan bari in riƙe su, in basu ilimi, in sun samu mazajen aure sai in aurar dasu, su kuma mazan suna can gidansu Zubainar." Mama Gana tace.
"Ba shakka fa, wayyo shugaban ƴan jin ƙai na ƙasa da ƙasa sannu. Lallai Bulama Babba matarka kwai makira, ta rabaka da iyayenka da danginta. Amman ta saki jiki sai hidima kake da danginta ko? Sau nawa Ba Bakura yayi kiran wayarka baka ɗagawa, uwarka harta haƙura ta dena kiranka. Babu ruwanka da ƙannenka, Babaninka ma haka. Bikin ƙannenka da akayi, haka akaita sa idanu, amman Bulama Babba daga kai har matarka babu ku, babu wasiƙa, sabida iskanci da wulakanci. Kamar mu iyayenka, shine wai take cewa a share mana BQ sabida ƙasƙanci, duk faɗin falonnan baku da ɗakin saukar baƙi kenan?" A ɗarare nace
Mama Gana sabida tana tunanin zaku fi sakewa acanne sabida ku surukanta ne, shi yasa. Kuma anan ɗin babu ɗakin baƙi, ɗakuna ukune a falon. Nawa, saina ƙannenta, da nata shikenan"
"Uhm ba shakka. Ai tunda kai kana da naka, suma tsintattun magen suna da nasu, ta kwana gidan sauƙi."
MRS BUKHARI CE
*MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!*
Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online
Gakayanmu kamarhaka
Tafi budurwa duniyane
Tsumin lahaula
Gombar bujenki jagab
Shu Umar zumarmu
Mumuna da,aeki
Makalemata
Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara
Dahuwar kaza cicibin kala kala
Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata
Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan