ya shigemun kwakwalwata, hancina duk ya buɗe. Sai naji kamar kaina na juyawa. Ahankali na soma karanto addu'o'in tsari da kariya. Waje na samu sai da nayi bismillah na zauna.
Ina wuni Anty?" Nace da Kofur Zubaina da take tambayar Bulama Babba ya kan nashi. Cikin fara'a ta amsa mun gaisuwata. Bulama Babba yace.
"Inaga gajiyar aikine, amman sai nake jin sauyi sosai a jikina. Amman ciwon kan da sauƙi, ina yarannanne?" Zama yayi a doguwar kujera, Kofur Zubaina ta zauna a gefenshi tace.
"Asiya tana tsakar gida tana zance, Alhaji ne yazo wajanta. Nafisa kuma tana ciki tana chatting kasan ƴan mata da shegen son chart" Kai kawai ya girgiza ba tare da yace komai ba. Kofur Zubaina ta dubeni tace.
"Bari a kawo miki abinci ko Yahanasu? Kiyi haƙuri bamu daɗe da shigowa gidan ba. Zan kawo miki angonki har ɗaki zuwa anjima" Ni dai kaina na sunkuye bance mata ci kanki ba, sai adda'a nake jerowa dan kaina ji nake kamar zai buɗe. Abinci ta kawo mun a plate da ruwan gora. Ni da nake fama da zazzaɓi bakin nawa babu daɗi sam. Amman gudun kar rashin cin nawa ya jawo wata matsala, sai nayi bismillah na soma ci. Noma baifi biyar nayi ba, na ajjiye abincin nasha ruwa. A hankali nace.
Nagode Anty, ni zan tafi sai da safe" Wani murmushi tayi mai ma'anoni da dama tace.
"To shikenan Yaha, sai na kawo miki angonki. Murmushi kawai nayi na fice abuna, bakina ɗauke da adda'a dan ji nake tsigogin jikina sai miƙewa suke yi. A hankali nake tafiya har na isa ɗakina, ban zauna a falo ba, ciki na kutsa kaina na shiga. Sallar isha na gabatar, sannan nayi azkhar ɗina. Ban gushe ba na jawo Qur'ani na soma katanta baƙara. Ina cikin karatunne wayata ta soma ringing. Hannu nasa na jawo wayar. Dala ne yake kirana, cikin zumuɗi na ɗaga wayar tare da karawa a kunnuwana. Amon sautin tane ya cika mun kunnuwana.
"Yahanasu ina fatan dai kina lafiya kuma babu wata matsala ko? Dan Yanunu ta sanar dani irin tarbar da kuka samu a wajan Bulama Babba da matarshi. Ran Babanku Ba Bakura ya ɓaci sosai, dan bai daɗe da yin shiru ba, yau yayi faɗa sosai. Hajja gana tayi kuka kamar me" idanuna na lumshe, tausayin kaina da tausayin su Ba Bakura da su Ya Innana ya kama ni. Allah sarki uwa mai daɗi, jin muryarta ya sanyaya zuchiyata sosai, sai naji kewarta ta sake ɗaureni, cike da son kwantar musu da hankali nace mata.
"Ya Innana wallahi babu komai, ɗazu ma Bulama Babba yazo ɗakina ya kirani, muka je babban falon gidan mu ka ci abincin dare, dan bai jima da dawowa daga aiki ba." Murmushin jin daɗi tayi tace.
"Yanzu yana ina shi Bulaman?" Da sauri nace mata.
Ya ɗan fita ne, amman ba jimawa zaiyi ba." Sai na kawar da zancan da tambayar yadda su Yanunu suka isa gida.
"Lafiya lau, Yanunu gata nan tana baccin gajiya, Fanda kuma tana ɗakin Mamanku Bagulaji duk sai gobe zasu koma gidajensu." Ɗan murmusawa nayi nace.
Ya sababbin Amaren gidanmu? Sai ranar da Bulama Babba ya kawo ni zan gansu, amman zan kira su Amada gobe sai duk su bani mu gaggaisa"
"Hakan yayi kyau, kuma suma zasu ji daɗi. Da ko ɗazu sun kakkawo mana amaren har ɗaki anga juna. Ke dai abinda nake so dake shine, ki yi haquri da dukkan abunda zaki gani, ki kuma runtse idanunki, da kunnuwanki. In Bulama na ɗakinki miji in baya ɗakinki Yaya. Sannan ki dinga ziyartar gidan Babanku Alhaji Munka'ilu, ɗazu ma Ba Modu ya kirawo mun Hajiya Ramlatun nayi mata godiya a bisa aiki data sama miki. Kai mutanen suna da karamci, Alhaji Munka'ilu mutum ne guda da ɓari gaskiya" Mun jima muna taɓa hira, daga baya ta miƙa ma Dala wayar, muka ɓige da hirarmu ta zumunci, sannan mu kai sallama. Ajjiyar zuchiya na sauke, tare da yin Murmushi. Jin muryar Ya Innana da Dala ya matuƙar faranta raina. Sallama nake ta faman jiyowa a cikin falo. Da sauri na zari hijabina na fita falon. Zubaina na gani a tsaye sai kalle kalle take yi tana jijjiga kanta. Bulama Babba kuma yana daga bayanta, kamar wani yaronta.
"Shige ciki ka zauna yallaɓai." Wuceta yayi, yaima kanshi masauki a 1 sitter. Zubaina ta dubeni tana sakarmun murmushi tace.
"Amarsu ga ango na kawo miki fa. Kiyi haƙuri abokanshi duk na wajan aikine, Ahmad kuma baya kusa balle ya rakoshi. Ki zauna mana" Zama nayi a kujera mafi kusa dashi.
"Masha Allah waje yayi kyau, cancaɗi. Yaha ga Bulama na kawo miki, zaiyi kwana bakwai a wajanki kamar yadda shari'a ta tanadar da hakan. Daga baya sai a soma rabon kwana kuma. Amman kiyi haƙuri ke zaki dinga yi muku girki. Kinga ni ma'aikaciyace bana zama sam. Kece a gidan ko da yaushe. Ango ni kam sai da safenku, ga kazarku nan" Ledar dake hannunta ta ajjiye a gefen ƙafarshi ta fice. Binta yayi a baya. Ajjiyar zuchiya na sauke kawai. Wai yau Bulama Babba aka rako ɗakina, da sunan mijina Allah me iko. Na tuno lokacin da nake zuwa ɗakinshi da kuka, a duk ranar da nayi ɓarna Ya Innana ta dake ni. Ranshi ba ƙaramin ɓaci yake yi da Ya Innana ba. Ita kuma tai ta mana dariya. Ina cikin tunaninnan naji shigowarshi, ba ko sallama.
"Ki ɗauki kazar ki je kici, in kuma kin ƙoshi sai ki adana, kije kiyi kwanciyarki." Jikina a mace na ɗauki kazar naje na adanata a kitchen, na koma ɗakina. Ƙarfe sha biyu, ƙarfe ɗaya, ƙarfe biyu. Bacci ya gagari idanuna, sai tunanin duniya dake shirin tarwatsa mun rayuwata. Lokaci guda, komai na rayuwata ya jagule, ada ina rayuwa cikin walwala da farin ciki. Amman lokaci guda ɓakin ciki da damuwa suka maye gurbin walwala da farin cikina. Zubda hawaye ya zama aikina, bani da aikin daya wuce tunanin halaka kaina. Tashi nayi na soma abinda zai fishsheni duniya da lahira. Wajajen ƙarfe biyu da arba'in na soma jin motsin kamar ana haƙar wani abu a tsakar gida. Tsoro ya kamani sosai, da sauri na haye gado na duƙunƙuna a cikin bargo. Adda'a kuwa bata subce a bakina ba. Duk tashin hankali baya hanani karanto adda'a, sabida da irin wannan ginin Ya Innana ta gina ruhinmu. Macece ita mai sani, tana da ilmi a ɓangaren addini, dan ko digri ɗinta a fannin addini tayi shi, a jami'atul madina. Sannan bata gushe ba sai da tayi mastas ɗinta duk a ɓangaren abinda ya shafi addini a misra. Kanuri mutanene masu son addini, da karatun Qur'ani. Suna bama karatun addini mahimmanci fiye dana bokon. Da haka wajajen uku da rabi na dare bacci ya ɗebeni. Mugayen mafarkai ne suka farkar dani, wajan huɗu da rabi na asuba.
Mrs Bukhari ce
*MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!*
Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online
Gakayanmu kamarhaka
Tafi budurwa duniyane
Tsumin lahaula
Gombar bujenki jagab
Shu Umar zumarmu
Mumuna da,aeki
Makalemata
Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara
Dahuwar kaza cicibin kala kala
Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata
Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari.
Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma
AMARYA
MAI JEGO
WACCE ZATAYI KOME
Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji.
Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure.
Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo.
_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 July 20 in sha Allah._
_1-NIHLATUL-KHAIR_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
_ZULFA_
👇🏽
*Ummu maher(miss green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
08104335144
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
07068606171
08179523215
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼
[26/07, 2:35 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
GAWURTATTU UKU
LAST FREE PAGE
10
Baccin da nake samu, baya wuce na awa biyu, wata ran na awa ɗaya ma nake samu, shi yasa kullum kaina a cikin ciwo yake. Adda'a na yi akan Allah yai mun tsari da abunda na gani a cikin mafarkina. Gabaki ɗaya jikina sai naji yana mun wani iri. Ba shiri na ɗauro alwala na soma karatun Qur'ani ba ƙaƙƙautawa, shi kaɗai ke iya sani samun nitsuwa, inna jini a makamancin irin wannan yanayin, duk da yau yanayin ya banbanta da irin yanayin da na saba shiga a baya. Ina zaune akan sallaya har akayi kiran sallah. Tashi nayi na gabatar da raka'atanil fajir, sannan nayi sallar asuba. Zama na gyara na dinga ragargazo mana adda'a ni da Bulama, tare da roƙon Allah ya bamu zaman lafiya da fahimtar juna, ya bani juriya da jumurin shanye duk abinda zai faru. Sai ƙarfe bakwai na tashi akan sallayarnan, bayan na yi azkhar. Kaina kamar zai tarwatse na fito falon. Ba kowa, nayi tunanin yana ciki ma, ashe baya nan. Kitchen na nufa, nayi jim na rasa me zanyi da safennan ni ba kayan miya ba. Gas na kunna na ɗaura ruwan tea, nasa kayan ƙamshi niƙakke wanda aka yishi musamman na tea ne wato tea spices. Daya tafasa na tace, na zuba madara. Na buɗe fantekar alkaki da nakiya na shaƙe plate dashi, na ɗaura komai a tire. Fitowata daga Kitchen yayi dai dai da shigowar Bulama Babba. Cikin shirin zuwa office sai ƙamshin yake yi. A hankali na isa inda yake, bayan na ajjiye tiren akan teburin dake tsakiyar ɗakin.
Ina kwana Bulama Babba?" Sai da ya zauna, ya amsa babu yabo, babu fallasa. Sannan yace.
"Inason zan kafa miki wasu sharaɗi, daga yau kece zaki dinga komai na aikin gidannan. Tun daga kan girki, kawo wankin yara, da wankin motata da motar Zubaina. Ke kuma bazaki tuƙa mota ba, dan haka ki ɗakko mun key ɗin motar, zan yi kyauta da'ita. Zan baki kuɗin cefane ki je kasuwa ki siyo kayan miya, da duk abunda baki dashi na girki. Sannan ki sani bama cin yaji, sannan kar kiyi burabusko dan Yara basaso" Tuni hawaye ya gama wanke mun fuskata, sai haɗiɗiyar yawu kawai nake yi. Jikina a mace na miƙe na shiga ɗaki dan ɗakko mishi key ɗin motata. Shi kuma ya gyara zama tare da jawo teburin da abincinshi yake kai zuwa gabanshi. Ina shiga ɗaki na ɗakko key ɗin motar na fito. A gabanshi na durƙusa na ajjiye mishi keyn a gaban tiren abincin nashi. Harna juya, ya kira sunana cikin sanyin murya. Da sauri na juyo. Idanunshi ya zuba mun, ni kuma na sauke nawa idon ƙasa, hawaye kawai nake zubarwa. Takowa yayi har inda nake, ya miƙo mun kuɗi, hannu nasa na amshi kuɗin.
"Kuɗin cefanan kenan, ki nemi kasuwa mafi kusa kiyi siyayyar, ki dafa tuwon shinkafa, miyar egusi. Ki zuba ma Zubaina da ƙannenta ishasshe. Da safe kuma ni bakwai da rabi nake fita office, ga su Bawa suma bakwai da rabi suke fita Zubaina ita fitarta takwas ne, wani sa'in kuma biyar na yamma take fita. Sai kisan lokacin da zaki dinga tashi. Saina dawo kinji ko? Akwai kazarki ta Amarci karki mance da'ita ta lalace" Bakina na rawa, zuchiyata sai tsalle take yi nace.
Ubangiji Allah ya dawo da kai lafiya, ya tsare gabanka da bayanka, adawo lafiya, kar ka mance da adda'ar fita a gida" Ina dasa aya na shige ɗakina, tare da faɗawa gado na saki wani marayan kuka.
Bulama Babba:
Kukan Yahanasu ba ƙaramin gasa mun zuchiya yayi ba. Amman na kasa rarrashinta ko jin tausayin halin data shiga. Asalima gani nake hukuncin da Zubaina ta yanke akan Yahanasun dai_dai ne. Tunda ko babu aure a tsakani, ni wanta ne, dan ta hidimtawa matata da ƴaƴana da suka kasance ƙannenta ai ba wani abu bane. Amman naso Zubaina ta bar mata motarta a hannunta, sai dai tayi fur fur fur, tace sai na karɓo key ɗin motar. Jin Zubaina nake yi a safiyar yau, ta mamaye ko ina na zuchiyata, bana ji, bana ganin kowa. Kuma inaji a shirye nake tsab in mata dukkan abinda zai faranta mata ranta. Numfashi na ja, na fice a ɗakin bana ko waige. A bakin mota na samu Zubaina. Key ɗin motar na damƙa mata, murmushi tayi nima na mayar mata.
Ga keyn nan, sannan na isar da saƙonki, harma na bata kuɗin cefane kamar yadda kika ce. So daga yau zata soma aikinta." Dariya tayi tace.
"Nima na samu in huta da maganar girki. Tunda mu ba zama muke yi ba, Asiya kuma itace dama mai girkin. Ita kuma aure zata yi nan kusa, Nafisa kuma uwar chart bata iya komai ba. Amman Bulama kayi ƙoƙarin siyo gado yau, sabida a kafa a ɗayan ɗakin, bai dace kaci gaba da kwana a katifa ba." Agogon hannunta ta duba, tace.
"Ya kamata ka tafi kar kayi latti ko?" Murmushi nayi, ji nake dan so kamar in cinye Zubaina, nace da'ita.
Sai abunda kika ce ai gimbiya" Far ta mun da idanuwa tace.
"To nace ka shiga motarka ka tafi. Ina jiran fitowar su Asiya ne, zan sauke su a makaranta." Sallama nayi mata na shiga motata na fice a gidan. Idanu na lumshe, kaina sai aiki yake yi tamkar agogo tsabar chazuwa, sai tunanin abubbuwa barkatai nake yi, a haka har na isa office.
Kofur Zubaina:
Ihu nayi bayan fitar motar Bulama, lallai wannan boka bala'ine. Ji yanda Bulama ya dawo yaro a gabana, duk abinda nace mishi sai kawai yayi, ba tambayar dalili balle gardama. Hmmm yanzune uwar Bulama zata ɗanɗani baƙin ciki, da yanzu ne wannan mayyar Mama Ganar tazo, wallahi da korar kare zan sa Ɗan nasu yayi musu. Yaha kuwa kashinta ya bushe a gidannan. Ina cikin wannan hali na farin ciki Asiya ta iso ita da yaran.
"Asiya maza ki shiga ɗakinku ki kwaso kayan wankin su Maryam dana ƙulle za'a kai wanki, dana Babansu duk ki kwasa ki kaima amarya, zata soma aikin Aljanna" Dani da Asiyan duk muka saka dariyar ƙeta. Maryam da Bawa kuma suka shige mota, sai surutu suke mun. Asiya da Nafisa na hango kici_kici da kayan wanki sun nufi BQ. Basu jima ba suka fito muka wuce.
"Anty kinga idanunta kuwa, sun kumbura da dukkan halamu kwana tayi tana shirgar kuka" Murmushi nayi nace.
Hmmm ba da ban na tashi tsaye ba, da nice zan kwana ina kukan. Yaushe zan iya. Ba dai burinsu su rabani da Bulama ba, shine yasa suka aura mishi ƙanwarshi ko? To ni na rabashi dasu, ɗan sauran umarninsu da yake bi, yanzu kam babu shi babu su, sai dai su suzo in da yake." Sai hirarmu muke mai daɗi da ƙannena, a makarantarsu na soma saukesu, sannan na sauke su Maryam, ni kuma na wuce office, dan yau operation zamu fita can kabala costine. Wasu ƴan daba ne, suka tada tarzoma jiya da daddare, kuma an shaida mana, yau zasu koma layin, banda kashe matasa uku da su ka yi, a cewarsu fansa ce suka ɗauka. Yau duk wanda ya ganni yasan ina cikin farin ciki, dan ko baki na kasa rufewa. Mama ce ta kirawo wayata.
"Zubaina ni na jiki shiru ba wani motsine wai? Nifa ko bacci wallahi ban samu mai kyau ba, tunda kika faɗa mun wannan lamarin." Dariya nayi na girgiza kai, lallai mama tana ji damu sosai, burinta ta gammu cikin farin ciki da walwala.
Mama ai aiki ya faɗa, banma yi amfani da maganin wajanki ba, na wannan tubin nayi amfani dashi. Amman Mama a cikin safiyar yau, naga abubbuwa kala kala, duk abinda nace ma Bulama cikin sauri yake yi mun. Hatta motar ita yarinyar da aka aura mishi, nasa ya karɓo motar, bazai yiwu ina hawa mota, itama tana hawa ba. Kuma daga yau, aikin girki, da wankin yara, harma da wankin motocinmu ya dawo kanta. Kuma ita kanta an rufe mata baki, babu wanda zata iya labartama halin da take ciki. Iyayen Bulama kuwa, zan iya sawa yayi musu korar kare in suka zo mun gida. Mama ni wannan bokan ma kaɗai ya isheni, babu buƙatar sai nayi amfani da maganin wajenki" Guɗa Mama ta shiga rangaɗawa, cike da jin daɗi. Na ɗaura da ce mata.
Dubu ɗari uku ya bani yace in sai kayan dannar ƙirji, ga dubu ɗari na ɗinki, gashi jiya da daddare mun fita ya jido mun uban atampopi da leshika a gidan Hajiya. Ni yanzu ma in ya dawo inason ya sake mun kayan ɗakina, ayi mun fenti. Dan yarinyar da aka aura mishi ita, an narka mata kuɗi a ɗakinta, kinsan suna da yawa, ga zuchiyar yi"
"Kai abu yayi kyau, kice harka ta buɗe sabuwa. Abun alfahari, gashi yau Alhaji Jabeer zai turo magabatanshi gidan Babanku Tanko, zasu ba da sadaki a tsaida rana. Bai daɗe da fita ba shi Alhaji Jabeer ɗin, yazo yana roƙonane akan yana son asa bikin karya wuce sati uku, zuwa wata guda. To shine na fayyace mishi cewar, mu dai ba masu hali bane, yarannan marayune wanda dangin ubansu suka watsar. Ke na farfaɗa mishi gaskiya da ƙarya. Mun kuwa yi nasara, dan yace hatta abincin da za'aci na biki zai kawo, shi dai Asiyar kawai yake buƙatar a wanke a kai mishi. Ai an gama aiki a kanshi, shi kam za'a yagi arziki sosai a hannunshi, gashi ba uwa ba uba, ballantana su zame mana ƙadangaren bakin tulu." Dariyar farin ciki nayi nace.
Kai abun yayi kyau, Alhaji Jabeer ai mai kuɗine ɗan kasuwane sosai, zata huta sosai in ta aureshi, kakarku ta yanke saƙa. Zan biyo gidan inna baro wajan aiki, sabida asan me za'a dafa ma baƙin a kai gidan Baba Tankon, in ba haka ba sai su iya kunyata mutane. Kinga da saurayin Nafisa ya shirya ba sai a ganganɗa a ɗauresu tare ba?" Mama tayi maza tace.
"Haba wannan yaron ai Nafisa tafi ƙarfinshi, karanbanine kawai irinna yaranmu mu yaku bayi. Ke dai sai kin zo" Da dariya na bi Mama mu kai sallama, ina jin farin cikin ƙanwata zata kasance ɗaya daga cikin matar manya, dan Alhaji Jabeer sanannene sosai, babban shagon sai da kayan dawakai yake dashi a Kasuwar Kurmi dake jihar Kano. A Kanon yake zaune da danginshi da iyalinshi, sanadine yai sanadin haɗuwarshi da Asiya, yabi wanka irinna matan Kaduna, da buɗewar idanu ya ruɗu, bai san kwata ya shiga ba"
Yahanasu:
Wankin da ƙannen Zubaina suka dure mun a gaba, na tusa a gaba, nayi shiru ina nazari. Wayata ce tayi ƙara, ina jawowa sai naga Ba Bakura ne yake kira na. A hanzarce na ɗaga cike da zabarin son inji muryarshi.
Ba Bakura barka da safiya, ina kwana?" Murmushinshi da muka sanshi dashi yayi mun yace.
"Yaha ya baƙunta, ina dai fatan ba wani matsala da kika gani ko? In kuma akwai ki sanar tun wuri aiwa tubkar hanci, ni ba surukinki bane, ni ubanki ne, ki saki jikinki" Dauriya na aro na yafa, a ƙoƙarina na son ganin na rungumi ƙaddarorin rayuwata, na sani duk abinda ya faru da bawa rubutaccen al'amarine, kuma ko ba komai Bulama Babba gudan jininane, nasan sharrin matarshi ne kawai wannan, amman na hango tausayina ɓaro ɓaro a idanu da muryar shi. Sannan fatana shine in daidaita BULAMA BABBA da mahaifanshi, ba in ƙara nisantashi dasu ba, nasan suna buƙatar ɗansu, kuma suna kewarshi. Muryar Hajja Gana na ce ta katseni.
"Yahanasu kin tashi lafiya, ya tunani an dena dai ko? Murmushi nayi mata, na gaisheta cike da girmamawa, ta amsa cikin fara'a.
"Ina shi Bulama Babban ba dai fita yayi ya barki ba ko?"
Ya fita, amman yace bazai daɗe ba. Kinsan aikin banki basa ɗaga ma mutum ƙafa ne shi yasa" Gabana sai faɗuwa yake yi, a karon farko dana yi ƙarya da girmana kenan. Allah yana gani inason in kare BULAMA BABBA daga fishin iyayenshi ne. Kuma hakan dana faɗa ya matuƙar faranta musu rai, dan ina jiyo Ba Bakura yana faɗin. "Masha Allah" Da haka su kai mun sallama. Hijabi na zura, na kulle ɗakina na nufi bakin get, na tarar da mai gadi a zaune a farar kujerar roba, yana jin rediyo.
"Hajiya zaki fita ne?" Ya tambayeni yana yunƙurin buɗe mun get.
E fita zanyi, inason zuwa kasuwar kayan abinci, ko kasan wata mafi kusa?"
"E akwai kasuwar dogo, kasuwace ta kayan masarufi, kuma kayansu ba laifi akwai dama" Godiya nayi mishi na fita. A takaice na fi awa uku a kasuwa ina siyayya, duk na gama jigata, gashi ba ishasshiyar lafiya gareni ba sam. Ina dawowa nayi sallah, bayan mai gadi ya taimaka ya shigar mun da kayan ciki. Sai na fito da wanki shima na shiga yinsu, sauƙin dana samu kayan babu datti, wasu ma kamar ba'a saka ba. Sai da nayi sallar la'asar sannan na ɗaura girkin dare, tuwo da miyar duka na ɗaura lokaci guda. Jikina ko ina ciwo yake yi mini, amman inata sauri in samu in kammala girkin tun kamun Masu gidan su dawo.
KOFUR ZUBAINA:
Misalin ƙarfe huɗun yamma na tashi a aiki. Kai tsaye gidan Mabaruka na wuce. A tsakar gida na same su dukka da yaran da Sagira, wacce take ta uban wanke wanke. Mabaruka kuwa tana zaune a tabarma, taci kwalliya kamar zata gasar zaɓin sarauniyar kyau. Tana ganina ta shiga washe baki.
" Ƴar sanda abokiyar kowa, ƙawata kece tafe da maraice haka?" Zama nayi a gefenta, muka gaisa da Sagira, idanu muka haɗe ni da Mabaruka ta kashe mun idanu, nima na kashe mata nawa.
Ƙawata farin ciki ne yasa na kasa haƙurin mu game maganar a waya, nace ya kamata in yo tattaki inzo godiya ƙawata, kwalliya ta biya kuɗin sabulu dai. Na sakata na wala, kar kiso ki shiga zuchiyata kiga ƙyallin da take yi, Hmmm nifa sai yanzune na samu abunda nake so" Shewa Mabaruka tayi tace.
"Muje ciki, in ɗauraki akan wasu surrukan ƙawata." Tafawa mu kayi, naja hannunta zuwa cikin ɗakinta, da yasha gyara sai ƙamahin turaren wutan gab gab yake yi. Zama muka yi tace.
" Tunda kinsan Bulama na hannunki, fishi ko nuna kishi, ko tsangwamar kishiya ba naki bane. Ki kasance mai yawan fara'a sosai in kika ganta, musamman a gabanshi.