An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B ( GIDAN ƘAMSHI)
ƊANƊANO! ƊANƊANO!! ƊANƊANO!!!
1
DAMATURU
Hadarine gagarumin gaske a garin namu na Damaturu, misalin ƙarfe huɗun yamma ne, amman yanayin duhun garin in ka kalla, zakayi tunanin asubane, ga wata sassanyar iska dake busawa tare da ƙananun yayyafin afumangai da aka soma yanzu. Jama'a sai gudu suke yi, yayin da da dama suka ƙara sauri.
YAHANASU:
Sauri_sauri gudu_gudu nake tafiya, bana fatan shan dukan ruwa. Hijabin dake jikina harya soma jiƙewa, dan yayyafin ya ƙaru sosai. Da sauri nasha kwanar lungun bayan layinmu, wanda inna ɓulla zai kaini, kusa da gida. A cikin lungun akwai wani tsohon kango, wanda ya kasance matattarar ƴan shaye_shaye. Zaman su a anguwar yana cima mazauna wannan anguwa tuwo a ƙwarya. Gashi matasan daga can wata anguwa suke zuwa. A guje nazo zan wuce wannan kangon. Banyi aune ba naji an fisgoni da matsiyacin ƙarfi. Ihun tsoro nayi, amman kafin in gama wangale bakina, naji an cusamun tsumma a bakin nawa. Jikina sai rawa yake yi kawai, ga kangon akwai duhu bana ganin mutanen dake ciki sosai. Ga wani irin mugun warin sigari dake tashi a wajan. Ban gama tantance fari da baƙiba, naji hannun wani matashi a jikina ya fisge hijabin dake jikina. Tare da daƙumo mun ƙirjina. Fitsarine ya soma zubowa a ƙasana, hawaye ya gama wanke mun fuskata. Kokawar ceton kaina na soma yi da wannan matashi, nice naushi, da yakushi, abun takaicin bakina a toshe yake. Ina cikin wannan dambarwa, naji an daddanne mun hannayena, cike da rashin imani wannan matashin yai mun mummunan fyaɗe. Zafin yagani da yayi ne, yasa na fisge hannayena a hannun matasan da suka daddanneni. Dutsen dake kusa da kaina na ɗauka da zafin nama, na rotsama wannan matashin a kai. Take kanshi ya fashe, jini ya wanke mun fuskata.
"Ta kashe Tijjani, kai mu ware tun kafin asirinmu ya tonu" Cewar matasan samarin. A guje suka fice a cikin kangon. Ruwa ake zubawa kamar da bakin ƙwarya. Jikina sai kakkarwa yake yi, da ƙyar nasa hannu biyu na ture wannan tsinannen matashin wanda tunda na buga mishi dutse bai motsa ba,. Da sauri na rarumi Hijabina na mayar jikina, da ƙyar na miƙe tsaye, raɗaɗi da yaji_yaji nake ji a ƙasana, zuchiyata kuwa dan tsoro kamar zata faso ƙirjina ta fito. Cikin jan ƙafa na fice a kangon. Bana ko ganin hanya sosai, sabida ɗimuwa, ga ruwa da akeyi, harda ƙanƙara, sai dukana ruwannan yake yi. Amman bana jin dukan ruwan sam, damuwata shine, darajata da wani tsinanne ya keta mun, shikenan nasan na shiga ƙuncin rayuwa da tasku kenan. Da ƙyar nasa hannu na tura get ɗin gidanmu na shiga. Babban gidane mai cike da jama'a sosai. Sai jan ƙafata nake yi kawai, da ƙyar na iso ƙofar ɗakinmu. Suna zaune suna kallo na faɗo ɗakin a jiƙe sharab, jikina sai ɓari yakeyi, idanuwana kuwa kamar garwashin wuta.
"Yahanasu lafiya kike kuwa da zaki tawo a cikin irin wannan ruwan mai ƙarfi?" Mahaifiyata ce ke magana, amman in buɗe baki nayi magana na kasa. Hannu na saka a ka, na shiga runtuma kuka mai tsuma zuchiya. Gabaki ɗaya na tashi hankalin ƴan uwana, duk sun miƙe tsaye suna kallona.
" Ya Innana jini a ƙafar Yahanasu" Cewar Fanda. Wakil Yayana ya dubeni yace.
"Yahanasu kiyi magana dan Allah kin tayar mana da hankali, meke faruwa, meya sameki?" Ya Innana mahaifiyarmu ta iso kusa dani, bata ce komai ba, taja hannuna zuwa uwar ɗakinta. Akan gadonta ta zaunar dani."
"Yahanasu ki cire kayan jikinki tukunna, koma menene ya sameki ki kasance mai juriya mana, kin ɗaga mana hankali ainun" Tausayina dana mahaifiyata yaimun dirar mikiya a zuchiyata, jikina ya tsananta rawa ainun, idanuna suka shiga kakkafewa. A gaggauce Ya Innana ta zare mun hijabina, ganin rigata a kekkece da tayi , ya tashi hankalinta sosai. Da sauri hannu na rawa ta ɗaga mun zanina. Matsawa baya tayi da sauri hannunta dafe a ƙirjinta, tana zubar hawaye. Jikinta ya mace mus tama rasa me zata yi mun dan ta bani kulawa. Duk girmana sai Innana ta dena ganinshi. Tana hawaye ta cire mun kayan jikina tas, bargo ta yafa mun. Sai naga ta rungumeni tana kuka mai fitar da wani irin sauti, mai tada hankali.
" Ya Innana, ku buɗe ƙofar dan Allah" Wakil ne yake magana. Maganar Wakil ita tasa Innana dakatawa da kukanta. Ban ɗakin ɗakinta ta shiga, bata jima ba ta fito, hannuna ta kama ta ɗagani tsaye. Rungumeta nayi ina kuka. Ni kaɗai da ire_iren waɗanda suka shiga ƙangin fyaɗene zasu gane irin raɗaɗi da azabar da nake ji." Mun kasa magana daga ni har Ya Innana, an rasa wanda zaice da wani kar yayi kuka. Har cikin bayan gidanta ta kaini, ta tara mun ruwa a bokiti, wanda take ta sawa a kittle.
"Ki gargasa jikinki, saimu tafi asibiti. Amman garin yaya hakan ta faru dake?" Firgicewa taga nayi, har ina zabura. Ba shiri tace.
"Shikenan ya'isa. Koma waye yai miki wannan aikin, wallahi kotu ita zata shiga tsakaninmu, wallahilƙudrat da zan ganshi saina kasheshi, sai dai aimun duk abinda za'ayi mun." Fita tayi fuu, ni kuwa sam na kasa yin wankan, asalima wani irin zazzaɓine yake shirin halakani
Ya In na na" Na ambaci sunanta a wawware. Ba shiri ta dawo har tana tuntuɓe"
Mutuwa zanyi Innana, zafi zai kasheni" Hannuna yana cikin nata, tana ɗigar hawaye tace.
"Bazaki mutu ba." Wanka ta soma yi muni, tana daddannamun jikina da tawul, saida tazo yimun tsarkine, hankalinta ya kuma tashi. Gashi jikina ya saki kamar zan sume mata. Da ƙyar muka fito a bayan gidan, doguwar rigarta ta buɗe durowa ta zura mun. Ta samun suwaita da hular sanyi, fita tayi da sauri.
Innana:
Tana fitowa yaranta suka baibayeta da tambayoyi.
"Wakil kayi maza kaje ka sanarma Ba Bakuri, za'a kaimu asibiti tunda Babanku baya gida, ko Bulama ƙarami sai ya kaimu" Kafin yace wani abu sai suka jiyo sallamar mahaifinsu Ba Modu a ƙofar ɗakin. Fanda ce ta amsa mishi a raunace. Shigowa yayi da fara'a kamar yadda yake a kullum, dan Ba Modu ma'abocin far'a ne sosai. Ganin iyalenshi a wani irin hali da rabon da ya gansu a halin, tun rasuwar Mahaifiyarsu Hajja Yahanasu wacce ta kasance kaka ga yaran gidan. Innana ya kalla hawayenta bai tsaya ba, daga kallonta kasan cewar tayi kuka ta ƙoshi, ga tashin hankali sosai a fuskata.
"Innana Lafiya kuwa ki ke zubar da hawayenki a gaban yara, meke faruwa?" Cikin muryar kuka tace.
"Ba Modu Yahanasu ce wani azzalumin yai mata fyaɗe, tana ɗakina a cikin mawuyacin hali, har firgita take yi" Tana kaiwa nan ta sake fashewa da kuka mai zafi" Tashin hankalin da iyalan ɗakinnan suka shiga ba'a magana. A tare suka shiga ɗakin dan ganin Yahanasu."
Yahanasu:
Ihu na ƙwalla mai ƙarfin gaske, ina yunƙurin tashi, dan ba ƙaramin firgitani shigowarsu tayi ba. Muna haɗa idanu da Wakil na sanƙare a wajen, numfashina ya ɗauke"
Innana:
"Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun. Allah ka tsinema wanda yaci mutuncin yarinyarnan ya keta mata haddinta. Ya Allah ita kuma ka rufa mata asirinta ka bata miji na gari" Kuka take yi mai zafi. Da sauri Ba Modu ya isa kan Yahanasu, shima hawayen yake fitarwa, taɓata yayi, tabbas babu sauran rai a jikinta. Da sauri ya fice a ɗakin ya nufi shashen babban wansu Bakura a firgice.
Sallama ya shiga yi, da kiɗimammiyar murya, hawaye bai dena gudana a idanunshi ba har sanda matar wanshi Hajja Gana ta fito. Ganinshi a wannan mawuyacin yanayinne yasa ta koma da sauri ta kirawo wan nashi. A hanzarce ya fito, tabarau ɗinshi a hannu, ganin ɗan uwan nashi na kuka ya gigita mishi duniya ainun.
"Modu menene ya saka zubar hawaye duk jarumtarka?"
"BaKura, Yahanasu akaima mugun aika_aika fyaɗe akai mata. Tana ɗakin Uwarta a sume" Sun kiɗima sun razana ainun, Hajja Gana kuwa, fashewa tayi da kuka, abunka da mace, kuma uwa. A gaggauce suka nufi ɗakin Innana dukkansu.
"Wakil maza ka samu Bulama a kawo mota ƙofar ɗakinnan, a ɗauki Yahanasu" Baice komai ba ya fita. Cikin ƙanƙanin lokaci gafatanin ƴan gidan suka san halin da ake ciki. Cirko cirko suka yi a tsakar gidan ko wacce fuskarta cike da alhini. Bulama da Wakil ne suka saka Yahanasu a mota, a gidan baya suka shinfiɗeta. Baguji kishiyar Innana ta shiga gidan bayan tana kuka, taima Yahanasu matashin kai da cinyarta. Bakura ya shiga gaban mota, shi da Bulama ƙarami. Da sauri motar ta fice. Modu ya dubi mata da yaran gidan yace.
"Kuyi haƙuri, kuma ku sata a adda'a kawai. Innana ki shige muje Wakil ya kaimu asibitin. Fanda ke kuma ki shiga cikin gida. Jiki a mace suka wuce garejin mota.
A bakin titi suka hango dandazon jama'a yara dama manya. Har babu hanyar wucewa a ƙafa ma, balle kuma ababen hawa. Bakura ne ya sauke glass ɗin motar ya yafito wani matashi da hannu, matashin ya iso wajan.
"Lafiya meke faruwa ne haka"
"Wallahi Baba wani ɗan shaye_shaye ne, aka ciro gawarshi a cikin kangon lungun gidan lado, shine jama'a suka taru" Jinjina kai Bakura yayi yace.
"Allah ya kyauta. Taimaka yaro ka buɗa mana hanya, mara lafiya ne damu" Da sauri matashinnan ya kutsa kai cikin dandazon mutanennan yasa aka bubbuɗa musu, suka wuce. Specialist (General Hospital damaturu suka shiga da sauri, dan anan suke ganin likita. Cikin gaggawa, ma'aikatan kiwon lafiya suka fito da gadon tura marasa lafiya, aka ɗaura Yahanasu akai. Dai_dai shigowar motar su Wakil. Gudu_gudu Nurses suka shige da Yahanasu ɗakin jinya na mata, Dr Zangina yana biye dasu a baya.
Baka jin maganar kowa a wajan, sai amon kukan Baguji da Hajja Gana, Innana kuwa, bata da kuzarin yin kuka mai sauti, hawayene kawai ke gudana a kumatunta. Wakil yana gefe yayi jigum, Bakura da Ba Modu kuwa, sai ajjiyar zuchiya kawai suke ta yawaita saukewa, iya tashin hankali suna cikinshi sosai.
"Wai a cikin ruwan da akeyi ɗazu ta shigo gidanne, a ina abun ya sameta, kuma tasan su waye, a cikinku Modu wa yarinyarnan taima wani bayani ?" Bakura ne yake musu wannan tambayoyin a jere. Ba Modu yace.
"Bakura ni kaina banda masaniya akan komai gaskiya,shigata gidan na tarar dasu a falo cikin damuwa. Innana ta faɗa miki wani abune?" Ajjiyar zuchiya Innana ta sauke sannan tace.
"Nayi yinƙurin tambayarta, amman a ɗimauce take ainun bata iya bani amsar komai ba, sai firgitata dana kuma yi" Bakura yace.
"Bulama Ƙarami a nemi ofishin ƴan sanda mafi kusa ayi report maza. Shi Wakil ya tsaya ko za'a buƙaci wani abun.
"To Ba BaKura" Sa kai yayi, ya fice da hanzari. Yana fita sai ga wata tawagar. Bagulaji da Ahmada wan Yahanasu, da Dala tafe suma a kiɗime, nan duk aka haɗu akai tsattsaye ana jiran fitowar likita. Matan suka rufu akan Innana wacce take ta faman hawaye, sai rarrashinta suke yi. Bakura yace.
"Za'ayi duk wani bincike daya kamata ayi. Wannan abun baza mu barshi ba, duk wanda aka kama da yin wannan aika_aikar wallahi bazan raga mishi ba. Maman nawa za'aima wannan cin zarafin?" Yana cikin sababin Dr Zangina ya fito.
"Amm mutum ɗaya zata iya shiga ta zauna da'ita. Anyi mata allurar bacci mai ƙarfi, sai gobe da rana zata farfaɗo. Sannan dan Allah a kiyaye yin motsi da wani abu mai ƙara, dan gudun firgitata. Bakura ku same ni a office da Modu" Bakura ya dubi Innana yace.
"Innana ke da su Baguji duk kubi Dala ya mayar daku gida. Hajja Gana ke ki shiga ki zauna da Yahanasun, in yaso saiki kwana da'ita. Mu kuma zamu je a soma bincike." Harga Allah Innana ranta baiso hukuncin Bakura ba sam. Gani take yi a irin wannan lokacin bai kamata ace za'ayi mata wata kara ba. Ya kamata a barta kusa da ɗiyarta, wala Allah ta samu sassaucin zugin zuchiya. Ko da ta koma gidanma, me zata yi acan? Ita dai ba bacci zata yi ba, ba iya cin abinci zata yi ba. Amman tasan Bakura shine uba, Babban wa dake zartar da ko wanne irin hukunci akan kowa, kuma dole kabi ko baiyi maka ba. Duk da dai ya kasance adali mai ƙaunar ganin farin cikin kowa. Da jan ƙafa tabi ayarin su Baguji suka tafi. Hajja Gana kuma ta shiga ɗakin majinyatan jikinta a mace.
"A gaskiya wanda yai ma yarinyarnan fyaɗen azzalumine sosai, dan yayi mata muguwar illa. Sai da nayi mata ɗinki uku, ga raunuka wanda suke buƙatar kulawa, shi yasa take cikin firgici. Bacci take amman tana firgita, duk ƙarfin allurar da akayi mata. Fatanmu shine inta farfaɗo ta dawo dai_dai. Dan akwai yiwuwar ƙwaƙwalwarta ta taɓu. Amma zuwa gobe likitan kwakwalwa in yazo, za'a kaita gwajin ƙwaƙwalwa. Allah ya bada haƙuri. A wannan karon sai da Bakura ya zubar da hawayenshi sosai. Ba Modu kuwa sai cizan leɓe kawai yake yi, zuchiyarshi na tafarfasa. Babu wanda yace da kowa komai, Bakura na gaba. Ba modu na bayanshi, duk sun goya hannayensu a baya. Suna fitowa farfajiyar babban asibitin, motar ƴan sanda ta shigo, motar Bulama na gaba. Bakura yaja tunga ya tsaya, jirine ke shirin jefar dashi, da sauri Ba modu ya riƙeshi.
"Bakura kayi a hankali, kayi haƙuri ƙaddara ta riga fata, adda'ar samun lafiya zamu yi mata. Shi kuma Naseer ba lallai bane ya aureta, dan wannan lamarin babbane, ni tunda abun ya faru nake hasaso fuskar iyayen yaronnan." Bakura bai iya tankawa ba, har ƴan sandannan suka iso garesu.
"Ba Bakura ga ƴan sandan sun iso, suna buƙatar ganin Yahanasun, kuma suna son ganin likitan daya dubata. Kuma zasu gudanar da bincike, da zaran Yahanasu ta samu damar yin magana. A wannan karon Ba modu har yafi Bakura dauriya. Wucewa suka yi ciki, su kuma su Bakura suna tsaye a wajan, har suka fito, Bulama ya mayar dasu gida. Gidan a hargitse yake sosai, duk wanda ka gani a cikin damuwa da taraddin halin da Yahanasu take ciki yake. Bakura ya wuce ɓarayinshi, Ba modu kuma ya shiga ɗakin Ya Innana. A falo ya tarad da Fanda, da Fanna data tawo gada gidan mijinta a kiɗime, sakamakon kiranta da Bulama ƙarami yayi, ya sanar da'ita halin da ake ciki.
"Fanna kece a tafe, sai kika ji abunda ya faru da ƴar uwar taki ko?" Fanna tace.
"Bawa (Baba) Naji amman a wanne halin take ne?" Zama yayi ya dubesu yace.
"Adda'arku take buƙata kawai, zata samu lafiya da izinin Allah. Sannan ƴan sanda zasu yi duk binciken daya dace, dan zaƙulo duk masu ruwa da tsaki a cikin wannan mummumunar aika_aikar. Ki daure ki koma ɗakinki, gobe saiki wuce asibitin daga can gidan naki. Gobe ƴan gidannan ma zasu je. Ina Innana?" Fanda tace.
"Tunda ta shigo ta shige ciki, ta kulle ƙofar, munyi bugun duniya taƙi ko da kulamu ne, Yaya Ahmada ma ya shigo ya ganta, amman bata bashi dama ba"
"Kuyi mata uziri kunsan a kiɗime take, dole a bita da laluma, bari in sameta." Wucewa yayi ya barsu a falon. Kwankwasa ƙofa yayi tare da kiran sunanta. Jin muryarshi yasa ta taso da wuri ta buɗe. Hijabine a jikinta, idar da sallahnta kenan. Hannunta ya riƙe suka koma ciki, a bakin gado yai mata masauki, ya zauna dab da'ita, hannunshi a cikin nata.
"Innana nasan kwatanta tashin hankali da damuwar da kike ciki ɓata lokacine. Amman muyi haƙuri dukkanmu mu tungumi ƙaddarar data faɗa kan Yahanasu. Muyi mata adda'ar samun lafiya, da rayuwa mai ɗaurewa a gaba, kuma duk abinda ya kama na bincike, zamu gudanar dashi da izinin Allah" Cikin rauni tace.
"Yara suka ce, anga jakar Yahanasu a cikin kangon gidan Lado. Harda ƙyallen atampar dake jikinta. Dala yace kar a taɓa har sai hukuma tazo" Gabanshi ya faɗi da ƙarfi, hawayen dake shirin zubo mishi ne, ya haɗiye, yace.
"A kangon lungun gidan Lado? Kaddai wannan yaron da aka tsinci gawarshi yana ɗaya daga cikin waɗanda suka keta ma Yahanasuna haddi? Ina zuwa bari in samu Bakura, muje mu samu Dala a wajan, kafin ƴan sandan su zo" Da sauri ya fita a shashen, harda gudu_gudu yake haɗawa. Da Ba Bakura da Baana ƙaninsu, sai Ahmada, da Ba'a kaka, sai Bulama Fari. Ko wanne ɗaki suna da Bulama, ko wanne Bulama da inkiyarshi. Tare duk suka ɗunguma zuwa kangon lungun gidan na Lado. A wajan suka samu Dala, da Abokinshi Mustapha suna tsaye. Shiga cikin kangon suka yi. Ga jakarta a yashe a ƙasa, ga kyallen rigarta yagagge a ƙasa, ga tsumman da aka rufe bakinta dashi, sai jini malala a ƙasa. Suna cikin kangon, sai ga ƴan sanda da Bulama Ƙarami sun shigo. Motar ƴan sandance, ta jawo hankalin mutanen anguwa, har suka soma fitowa, sabida a tunaninsu wannan matashin daya mutu a kangonne ƴan sanda suka zo dan ganin kangon. Malam Mato ne ya shigo cikin kangon, ya dubi Ba Bakura yace.
"Alh Bakura, ashe kaima kaji abinda ya faru a wannan anguwa? Yanzu haka gawar tana gidana, yara sunje kiran ƴan sanda, ina cikin gida, Mata suka ce sunji motar hukuma ta shigo" Ɗan sanda da jin haka yace.
"Alh muna son a nuna mana gawarnan, dan akwai binciken da zamu gudanar akan gawar. Kai kuma Ayuba, a ɗauki jaka da ƙyallen kayan asa a mota." Umarnin mai gidanshi Ayuba yabi. Daga kangon kuma, suka rankaya gidan Alh Mato dan ganin wannan gawar. Yarone saurayi santalele a kwance, kanshi a tsage, har zuwa lokacin jini na ɗan zuba, kanshi wani irin askine mara daraja, ga zip ɗin wandonshi a zuge. Wannan Kofur ya zuba ma gawarnan idanu ƙur, sannan yace.
"Alh Zamu tafi da gawarnan asibiti, in an samu iyayenshi, sai ai musu kwatance ofishinmu akwai binciken da za'a gudanar mai zafi akanshi. Ayuba a ɗauki gawarnan asa a mota." Gawar aka ɗauka zuwa cikin mota, al'umma sun haɗu a layin anyi cirko _cirko. Suna fitowa motar ƴan sandan da Alh Mato yasa a kira suka iso suma. Kofur Madaki yai magana dasu, suka juya. Kallon su Ba Bakura yayi yace.
"Alh a lokacin da abun ya faru, Yahanasun waya soma ganinta?" Ba Modu yace.
"Mahaifiyarta ce ta ganta"
"Good, ina buƙatar ganin mahaifiyar tata, ku kuma Ayuba ku jirani a wajan motarnan. Kai Kofur madaki wajan Innana akayi, yai mata tambaoyi da dama, daga ƙarshe ya karɓi riga da hijabin jikin Yahanasu, yai musu sallama ya tafi. Ko da dare yayi, gari yayi tsit, idanuwa da dama bacci sam ya gagari idanuwansu. Ba Bakura, Innana, Ba Modu, kusan akan sallaya suka raba darensu, suna roƙon Allah kan Allah ya toni asirin duk wanda ke da sa hannu a cikin wannan lamarin. Innana a kan sallaya ta kwana, kuka kuwa tayi shi, har fuskata ta kumbura tayi suntum da'ita gwanin tausayi." Tun sassafe, gidan ya tashi da kaya_kaya kamar yadda ake tashi a kullum. Mata da yaran gidan, sai zuwa ɗakinsu Yahanasu suke, suna sake jajantama Innana halin da Yahanasu take ciki. Da misalin goman safe sai ga Mama Gana ita da ɗanta Ya Ari, sun iso daga Yobe. Ƙanwace ga Ba Bakura, Ya ga Ba Modu, ita ta cika nono ya karɓa. A ɓanrayin Ba Bakura ta sauka. A falonshi ta yada zango sai sharar hawaye take ta faman yi.
"Yanzu Ba Bakura ashe abunda ya faru kenan? Oh na tausayama wannan yarinya." Ba Bakura yace.
"Waya faɗa miki Mama Gana?" Cikin kuka tace.
"Bulama Fari ne ya faɗamun a waya, shine fa nace bari in tawo, ayi komai dani zaifi. Ina shi Modu ɗin?"
"Modu yana cikin gida, gara da kika zo ma. Dan inason in Yahanasu Allah ya bata lafiya akwai taron da nake son haɗawa a gidannan, akan ita Yahanasunne kuma, kinga gara da kika tawo" Tana share Hawaye tace.
"Ina Hajja Gana banji ɗuriyarta ba. Kafin ya bata amsa, matan ƙannen nata suka shigo da sallama dan su kwashi gaisuwa. Mama Gana macece mai zafi da saurin fishi, gata da hargowa, haƙuri kowa yake yi da'ita. Dan inta zo