Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gamsar da ni to zan janye maganar auren " Malik ya fada cikin tsare gida ya na matse gera alamun ba wassa wani dan karamin tsaki Prince ya ja ya na kauda kai , shi gaskiya ba ya son auren nan specially ma da ya ji wacece a ka ce zai aura ya na a haka ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " Nayel , da kai na ke magana , ka ba ni hujjojin na ce " murya cen kassan makoshi ya ce " babu " da kyair ma sautin ya fito , tun da ya ji Malik ya kira sunan shi kai tsaye to duk abun da zai ce ba zai iya kare kansa ba , maganar auren ta zauna kenan ba mai kwatar sa sai Cutie , ita kadai za ta iya shayo kan Malik ya janye maganar auren nan shi ko bai san Cutien da ya ke cewa ita ta kawo shawarar auren ma wani dan karamin murmushin gefen fuska Malik ya saki kafin ya ce " okay , ku shirya gobe za ku tafi Yemen kai da Junior , nan da one week za a yi auren kuma za a yi shi ne bisa tsarin al'adun masarautar Yemen " da sauri Junior ya ce " Uncle ina da magana please " " wace magana ? " Malik ya fada ya na tsare shi da ido sunkuyar da kai ya yi ya na fadin " umm Uncle , ni dai ba zan iya karbar auren nan ba , saboda akwai wadda na ke so " dan tabe baki Malik ya yi ya na kallon shi ya ce " really ? wacece ? zan je da kaina neman maka aurenta sai a yi auren rana guda da na Prince " sunkuyar da kai Junior ya yi ya fara wasu dan kame kame ya kassa fadawa Malik Abun da ke cikin zuciyarsa , ya na jin kunyarsa gaskiya su na a haka Inaya ta shigo cikin parlourn ta na sallama da murmushi a face din ta kai tsaye ta nufi gefen Malik ta zauna ta na fadin " hirar me ku ke yi haka ? " Malik ne ya ba ta amsa da cewa " hirar auren yaranki , Junior ya ce akwai wadda ya ke so ba zai karbi kyautar Al-Sayid ba " " Masha Allah , Junior ka fada mana wacece sai mu fara shirye shiryen auren a yi shi tare da na Prince " ta fada ta na kallon Junior Prince kuwa ya na jin ta kira sunansa ya dago kai a dubu dari ya na kallon ta kenan ta na sane da maganar auren ya , ke tambayar kansa shi dai Junior sai sosa bayan keya ya ke da hannu ya kassa fadin maganarsa kamar an rufe mishi baki ya ke ji wani dogon tsaki Prince ya ja kafin ya ce " Cutie , Princess ce ya ke so " a tare duk su ka juya su ka kalli Prince har shi kansa Junior pillow ya dauka ya kai mishi bugu a baya ya na fadin " me a ba ka gane ba cikin sirri ? " " wait ! Junior da gaske Princess ka ke so ? " Malik ya jefo mishi tambayar wasu yawu Junior ya hadiye kafin ya ce " um , um uncle , dama da..... " " ban ce ka yi min wani kame kame ba , Eh ko A'a za ka ce " gyada mishi kai kawai Junior ya yi dan ba zai iya bude baki ba wani cool murmushi Malik da Inaya su ka saki a tare , Malik har da wata yar karamar dariya ya na fadin " to ai faduwa ta zo dai'dai da zama , ta na dawowa za a daura auren " marairaice fuska Junior ya yi ya na fadin " Uncle , it's not sure ita ma ta na so na " Inaya ce ta amsa mishi da cewa " Kar ka damu , ba za mu fada mata an yi auren ba sai ka shawo kanta , kuma kai ma ka san halin Princess ta na da saukin kai , cikin sauki za ka shayo kanta " wata yar karamar dariya Junior ya yi ya na sunkuyar da kai Prince kuwa tsaki ya ja ya na fadin " Fine , da alamun hade min kai ku ke son yi yau " " Kai malam aure ne dai sai ka yi shi sai dai ka mutu " " yanzu Cutie ba za ki ce wani abu ba ? " ya fada ya na kallon Inaya daga mishi kafadu ta yi alamun ba ta sani ba bushewa da dariya Junior ya yi har da tapi hararrar shi Prince ya yi ya na fadin " yi min shiru kai kuma ko na shake ka wajen nan " " Ba ni na karto man ba , rataya a ka ba ni " ya fada ya na mikewa tsaye ya nufi lift da gudu ya na dariya da sauri Prince ya mike ya bi bayansa sai dai kafin ya riko sa har kofar lift din ta rufe wani tsaki ya ja kafin ya juya ya koma cikin parlourn ya na dawo da kallonsa kan Malik da Inaya kawai ya gan su rungume da juna ya na yi mata magana cikin rada " Daddy , da mutum fa a wajen " ya fada ya na dan zaro musu idanu hararrar Malik ya yi kafin ya ce " in ka ji haushi sai ka yi aure kai ma , My Cutie , tashi mu tafi na yi miki tausa " cike da shagwaba Inaya ta ce mishi " Baby ni gaskiya yunwa na ke ji " kiss ya yi mata a forehead ya na fadin " don't worry , tashi mu tafi " ba musu ta tashi shi ma ya mike tsaye ya riko hannunta su ka nufi lift su ka shiga, su ka bar Prince zaune a nan ya na kallon ikon Allah su na sane sarai da shi amma su ke zuba soyayyarsu ko kunyar sa ba su ji ( hmmmm in dai Malik ne ba ka ga komai ba ๐Ÿคฃ ) โ–ชWASHE GARI โ›… โ–ชMASARAUTAR YEMEN ๐Ÿ‘‘ Zaune Aleesherh ta ke cikin parlourn su , sanye da wata tsadadiyar gown blue ta daura wata farar Alkyaba da ga sama , ta yi mata kyau Over duk da ba ta yi make up ko kadan ba , amma fuskar ta na a daure kamar wadda uwarta da ubanta su ka rasu ta na zaune a haka Aleenah ta fito da ga cikin wardrobe sanye da kaya tak tak irin nata sai dai ita gown din ta white color ce , fuskarta babu yabo ba fallasa sai sha-aninta ta ke su na a haka Sayida Ahlame ta shigo ta na yi musu waya da murmushi a face din ta ta ce " ku tasso mu tafi su na fadar Al-Sayid " ba musu Aleesherh da Aleenah su ka mike su ka bi bayanta a cen kuma Fadar Al-Sayid zaune Junior ya ke cikin fadar ya na Sanye da wasu suit blue ma su mugun kyau kuma gaskiya sun kama shi sai jan sa da hira Al-Sayid ya ke su na a haka har Sayida Ahlame ta shigo rike da hannayan Aleenah da Aleesherh ta karaso cikin fadar ta zaunar da su saman chair din da ke fuskantar wadda Junior ke zaune , dama yau fadar ba mutane dayawa a ciki da ga Al-Sayid sai Sayida Fadwah da Sayida Ahlame sai kuma wasu biyun na hannun daman Al-Sayid wanda su ka kawo shawarar auren ma bayan ta zaunar da su Sayida Ahlame ta koma saman chair din ta da ke gefen damar kujerar ta Al-Sayid ta zauna , Sayida Fadwah kuma ta na a gefen hagu sai da ta zauna sannan Al-Sayid ya ce wa Junior " wadanan su ne yaran nawa , mai blue din riga ita ce babbar Aleesherh , dayar kuma sunanta Aleenah " wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " Amma ranka shi dade ba ni ne a ka aiko ya gan su ba " ya fada dan kar ma Al-Sayid ya yi mishi maganar ya zaba ya rasa amsar da zai ba shi cikin rudu Al-Sayid ya ce " kamar ya ? ba kai ne Yaron Malik Nawfel ba ? " girgiza mishi kai Junior ya yi ya na fadin " no , ni cousin din sa ne , amma wajen Malik na ke zaune , shi ya sa ma ya ce mu taho tare " " to ina dan uwan naka ya yi ? " " sorry uncle , ya na wani kira ne mai mahimanci amma yanzu zai shigo " da to kawai Al-Sayid ya amsa mishi ya na kallon kofar fadar ya na jiran ya ga wanene zai shigo dan shi fa ko Malik din a Tv kawai ya taba ganin sa bare yaronsa da bayan familynsa ba wanda ya san sunansa sun yi wajen two minutes zaune a haka ba wanda ya ce wa kowa ufan , Har Al-Sayid ya bude baki zai yi magana su ka jiyo Muryar Prince ya na sallama cike da nitsuwa dam Aleesherh ta ji zuciyarta ta buga har sai da ta wani lumshe idanu amma sam ba ta yi kokarin dago kai ba bare ta ga in da gaske shi ne ko ba shi ba ne cikin rudu Al-Sayid ya kare mishi kallo dan ya gane fuskarsa sarai , amma bai kawo komai a ransa ba kawai ya yi tunanin ko wani littafin ya zo nema a libraryn masarautar ya na sanye da wasu suit white color shi kuma , ma su bala'in kyau kamar dai irin na Junior sai da ya karaso wajen Chair din da Junior ke zaune ya tsaya ya na fadin " ina mika gaisuwata ga shugaban wannan kassar mai Albarka " da murmushi a face din sa Al-Sayid ya ce " ina amsawa , yau kuma me ya kawo Prince wannan fadar ? ko dai wani littafin ka zo nema ? " da sauri Junior ya kalli Prince ya na zaro idanu , ya na tambayar kansa ya a ka yi Al-Sayid ya san sunansa Prince kenan dama ya taba zuwa fadar Yemen girgiza mishi kai Prince ya yi kafin ya ce " zan so na fara gabatar da kaina , sunana Prince Nayel Hicam Bin Jaabar , d'a ga Malik Nawfel Hicham bin Jaabar , zan so na mika sakon godiyata kai tsaye ga Al-Sayid da wannan gayatar " ya fada cike da izza baki sake Al-Sayid da sauran mutanan fadarsa biyu ke kallon Prince , kenan dama ya zo fadar ba su da labari Junior kuma sai tabe baki ya ke jin kalaman Prince ya na fadin " sannu Prince , izzar taka a nan ma sai ka nuna ta ? zan yi maganin ka in ka koma " cike da kula Al-Sayid ya ce mishi ya zauna ba musu Prince ya zauna gefen Junior ita dai Aleesherh ta na jin duk abun da ke faruwa amma ta kassa dago kai , ta na gudun ta dago kai ta ga ba abun da ta yi zato ba ne ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Aleenah ta na bubuga cinyarta ta na fadin " Alee , Daddy na mike magana " a razane ta dago kai dan ita sam ba ta ji abun da ya ke cewa ba ta na dagowa ko idanunta su ka sauka saman Prince da ke zaune ya tsare ta da ido shi ma tun zamansa ya ke jiran ta dago kai amma ta ki dama Aleenah karya ta ke mata dan ta lura da irin kallon da Prince ke yi wa Aleesherh , shi ya sa ta ce ta dago kai su ga juna cikin nitsuwa Al-Sayid ya ce wa Prince " ya kamata ku tafi part din da a ka gyara muku ku huta , zan sa a kai muku abinci " Junior ya amsa mishi da cewa " a'a Uncle , taf....... " bai karasa maganarsa ba Prince ya katse shi da cewa " mun gode ranka shi dade , amma mun riga da mun kama bedrooms a hotel , so a cen za mu sauka " wannan karan Sayida Ahlame ce ta karbi zancen da cewa " a'a , gaskiya ba za ku kwana a hotel ba , mun riga da mun shirya muku part , dan haka sai ku tashi ku tafi , Aleesherh ko za ki kai su part din ? " gyada mata kai Aleesherh ta yi kafin ta mike tsaye a hankali ta na fadin " bismillah " ba musu Junior da Prince su ka mike su ka yi wa Al-Sayid sallama sannan su ka bi bayanta su ka baro fadar sai da su ka yi dan nisa da Fadar sannan Junior ya cewa Prince " lafiya ka ce za mu zauna ? Daddy fa ya ce da mun zo mu koma , ni gaskiya ba Niyyar zama " wani dan karamin tsaki Prince ya ja kafin ya ce " kai don Allah yi min shiru , ba duk kai ne ka janyo min ba , da ba ka bawa Daddy wayar a lokacin da na kira ka ba da ba zai ce na dawo ba , dan haka malam sai dai ka yi hakuri har na yi sign din contract din da ya kawo ni Yemen , in ya kira ka ce mishi Al-Sayid ne ya matsa mu zauna " " no , ni gaskiya ba zan yi wannan karyar ba , ka san halin Daddy " " Junior ka san Allah na fi ka duk shirmen da ka ke ji , in har na rasa wannan contract a karo na biyu saboda kai , Allah sai na hana ka samun sukuni a rayuwarka " bushewa da dariya Junior ya yi har da tapi , kafin ya ce " ba dan Daddy ya yi maka auren dole ba za ka sauke haushin sama na , da ga na fadi gaskiya " wani dan karamin tsaki Prince ya ja kafin ya juya ya na kallon gabansa nan ya tuno ashe ta na a wajen shi ko bai san duk maganarsu ta jiyo ta , kuma sun yi mugun tuno mata ita da Aleenah , haka su ke wannan jayayar in ta ce za ta yi wani abu sai da su karaso bakin kofar part din ta sa hannu ta tura kofar sannan ta koma gefe ta tsaya kai a sunkuye ta ce musu " bismillah " godiya Junior ya yi mata kafin ya shiga part din kai tsaye , shi kuwa Prince ya tsaya ya zuba mata ido ganin har yanzu ya na tsaye a gabanta ya sa ta dago kai slowly , kai tsaye idanunta cikin nashi su ka sauka kauda kai ta yi a hankali kafin ta juya za ta bar wajen cikin nitsuwa ya taro ta da fadin " wa ya ba ki izinin tafiya ? " ba tare da ta juyo ba ta ce " na ga wanda ya ba ni umarnin kawo ku wajen nan ba ya nan bare ya ce min kar na tafi " " All right , za ki iya tafiya za mu hadu a gaba " ya na gama fadar haka ya fara takawa ya shiga cikin part din ta na jin ya fara takawa ita ma ta ci gaba da tafiyarta , kai tsaye part din su ta koma ko da ta shiga ta tardo Aleenah zaune bakin gadonsu ba ta ce mata komai ba ta fiddo wayarta , ta sa music ta kai karar karshe sannan ta tilla wayar saman gadon ta kai hannu ta cire Alkyabarta ta tilla gefen wayar cikin rudu Aleenah ta tsaya ta na kallon ta ta na jiran ta ga abun da za ta yi ba zato ba tsanmani kawai ta ga Aleesherh ta fara rawa har da kama sautin wakar ta na girgije wa da kyau ita dai Aleenah ta yi zaune ta na kallon ikon God su na a haka Sayida Ahlame ta shigo wajen cak ta tsaya ta na kallon Aleesherh sai rawarta ta ke cikin konciyar hankali ta na murmushi cikin rudu ta karaso wajen ta na fadin " Alee , lafiya ki ke rawa haka ? " Aleenah ce ta ba ta amsa da cewa " momy , saurayin da ta ce muku ta na son shi , to shi ne Prince " dan zaro idanu Sayida Ahlame ta yi ta na kallon Aleesherh sai rawa ta ke wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta riko hannunta ta na fadin " rawar ta isa haka madam , zo zauna na yi miki magana " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " momy i'm so happy , i can't imagine , don Allah ko mafarki na ke kar ku tashe ni " hannu Sayida Ahlame ta daga za ta marin ta ta na fadin " ni zan tashe ki to yar rainin hankali kawai " dariya kawai Aleesherh ta yi kafin ta zauna bakin gadon ta na kallon Sayida Ahlame sai da ta zauna sannan Sayida Ahlame ta ce mata " yanzu an kawo miki scrub ki yi kafin ki shiga wanka , kuma Ammie ta ce ta turo miki perfume da wasu abubuwa ban San ko minene ba dan ba ta fada min ba , Al-Sayid ya ce next Friday za a yi auren in da rai da lafiya " ta na gama fadar haka ta juya ta fice hannu Aleesherh ta kai ta boye fuskarta ta na murmushi kafin ta yi baya ta konta saman gadon zuciyarta cike da farinciki kamar ta tashi sama ta ke ji Aleenah dai duk ta yi sanyi , sai latsa wayarta ta ke cikin konciyar hankali , ta ma rasa me ke yi mata dadi a duniyar nan ba ki daya , kuma ta kasa tantance abun da ke damun ta , ko dai kishi ta ke ? ๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค” TO FA ALEENAH ZA TA FARA KISHI DA ALEESHERH KO YA ? โคโš˜ ๐๐€๐˜๐„๐‹โš˜โค ________________ แด›สœแด‡ ส€แด‡แด›แดœส€ษด แดา“ แด‡xษชสŸแด‡แด… แด˜ส€ษชษดแด„แด‡ THE BIGINING ๐Ÿ•Š๐Ÿ‘‘โค ๐Ÿ•Š๐Ÿ’ž ( ๐™ฐ ๐™ท๐™ด๐™ฐ๐š๐šƒ ๐šƒ๐™พ๐š„๐™ฒ๐™ท๐™ธ๐™ฝ๐™ถ ๐™ป๐™พ๐š…๐™ด ๐š‚๐šƒ๐™พ๐š๐šˆ , ๐š๐™พ๐™ผ๐™ฐ๐™ฝ๐šƒ๐™ธ๐™ฒ , ๐™ธ๐™ฝ๐™น๐š„๐š‚๐šƒ๐™ธ๐™ฒ๐™ด & ๐™ณ๐™ด๐š‚๐šƒ๐™ธ๐™ฝ๐šˆ) ๐Ÿ’ž๐Ÿ•Š โค๐Ÿ‘‘ ๐‘ด๐‘จ๐‘ณ๐‘ณ๐‘จ๐‘ฒ๐‘ฐ๐‘ต.๐‘จ๐‘ด๐‘ฌ๐‘ฌ๐‘น๐‘จ๐‘ฏ ๐‘จ๐‘ฉ๐‘ซ๐‘ถ๐‘ผ๐‘ณ๐‘จ๐’€๐‘ฐ๐Ÿ‘‘โค ( ๐‘จ.๐‘ฒ.๐‘จ ๐‘ด๐‘ฌ๐‘ฌ๐‘น๐‘จ๐‘ฏ ) โค๐Ÿ•Š TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK _______________________________________________ โ–ช๏ธŽPAID BOOK N500 [ FREE PAGE ___ 11 ๐Ÿ•Š๐Ÿ‘‘โค ] MISALIN KARFE 8 NA DARE โ–ชPRINCE ๐Ÿ‘‘ a hankali ya ke tafiya cikin harabar masarautar , ya na sanye da trouser white color da t-shirt blue , ya na rike da wani file a hannunsa ya na dubawa ya na tsaka da tafiyarsa ya ji karar sword kamar a na wassan takobi a hankali ya dago kai ya kalli saitin da ya ke jiyo karar nan idanunsa su ka sauka saman ta , ta na sanye da wasu Tracksuit pink color , ta daure gashin kanta a baya , ta na rike da sword su na wassa ita da wani dogari , ba karya kuma gaskiya ta iya Aleenah ta na zaune saman wata chair ta na kallon su haka shi ma ya tsaya ya zuba musu ido ya kassa janye idanunsa ya rasa dalili a hankali ya rufe file din sa ya fara takawa cike da izza ya nufe su ya na isowa ya mikawa Aleenah file din cikin rudu ta kai hannu ta karba ta na kallon shi , shi kuma ya na kallon su Aleesherh cikin nitsuwa ya katse su da cewa " ina son na gwada ni ma " cak su ka tsaya su ka juyo ita da dogarin su na kallon shi , ta na ganin sa ta kara tsuke fuska ba musu dogarin ya karaso ya bawa Prince sword din hannunsa karba Prince ya yi ya karaso wajen da ya baro su na fuskantar juna shi da Aleesherh " ina fatan kin iya kare kanki dan ba zan raga miki ba " " hm " ta fada cen kassan makoshi kafin ta kai mishi hari da sauri ya dago takobinsa ya kare kansa , da ga haka su ka shiga wassan a tare cikin kwarewa dan Prince ma ba baya ba ya iya wassan takobi dan tun lokacin da ya fara tasowa ya ke yi mu dai ni da Aleenah mun yi zaune mun zubawa ikon God ido , kamar ba su gajiya yaran nan su na cikin wassan nasu ya samo ta a damtse har sai da ta yanke jini ya fara zuba a tare shi da ita duk su ka saki sword din su , ita ta na dafe hannu shi kuma ya nufo ta ya na fadin " i'm sorry , ba ki ji ciwo sosai ba ? " ya fada ya na shirin taba ta da sauri ta ja da baya ta na fadin " don't touch me ! " ta fada cikin tsare gida " why , we'll Get married soon , i think i have the right to touch you " " no , Daddy bai ce ni za ka aura , ba ka tunanin da Aleenah zai hada ka ? ka zo kuma ka taba ni , ba na bukatar taimakon ka " hannu ya kai ya riko damtsenta da ya yanke ya janyo ta dab da shi , sannan ya sake ta , ya kai hannunsa a bayan aljihunsa ya na fadin " ya ba ni auren ku , kuma na karba dan haka ba shi da ikon zaba min wace zan aura cikinku , wadda na zaba ita zan aura " ya fada ya na fiddo wani farin hanckie , ya daure mata wajen yankar da shi sannan ya ce mata " in kin shiga ki ce a yi miki dress a wajen " ya na gama fadar haka ya raba ta gefenta ya nufi Aleenah ya mika mata hannu alamar ta ba shi file din sa ba musu ko ta ba shi file din ya sa kafa ya bar wajen sai da su ka yi nisa sannan Aleenah ta karaso gefen Aleesherh ta na fadin " ni akwai wani abu da ban gane ba , ki na son shi amma sai nuna mishi ki ke kamar kin tsane shi , why ? " wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi kafin ta ce " ba ki ga yanayinsa ba ne ? , da ga gani ya na da takama da izza , in na tunkare shi kai tsaye na ce ina son shi zai ce ba ni da kamun kai , kawai ina nuna mishi ne ni ma ina ji da kaina kamar shi , za ki gani sannu sannu shi da kansa zai bude baki ya ce na burge shi , amma da yanzu da ina biye da shi ina rokon shi ya so ji zai yi ma ya tsane ni saboda na takura mishi , ki jira ki gani , da sannu tsintsu ke yin gidansa , ni kuma zan mallake zuciyarsa " ta fada cike da kwarin guyiwa alamun ta san abun da ta ke ita dai Aleenah ta yi tsaye ta na kallon ta dan kaifin tunanin Aleesherh ya ninka nata sau uku ba biyu ba , da ita ce ba za taba tunanin yin wannan abun ba , yadda ta ga Aleesherh na kuka saboda son shi , da ita ce kai tsaye kawai za ta fada mishi abun da ke cikin zuciyarta , amma ita Aleesherh sai ta zagayo ta wata hanyar daba dan ta fara mallake zuciyarsa kafin ta fada mishi abun da ke cikin ranta ( ๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž NI DAI INA TEAM PRINCE , GWADA KI GANI YARINYA , KO KALLO BA KI ISHE SHI BA , ๐Ÿ˜”๐Ÿ˜” KO DA YA KE YANZU YA FARA NUNA DAMUWA A KANTA , PRINCE KAR KA BAN KUNYA PLEASE ๐Ÿ˜ข ) โ–ชMASARAUTAR SAUDIYA

Chapter 9 of 23