Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi ya sa ma ya iya banbanta su cikin sauki ita da Aleenah , kuma ya ke sake mata su na magana , amma shi har yanzu ba ta yi wani abu ba da zai ce son ta ne ya ke cikin zuciyarsa saboda wannan abun , shi dai kawai ya san ya damu da ita saboda amanarta a ka ba shi ya yi nisa duniyar tunaninsa ya ji kawai ta janye kanta da ga saman shoulder din sa , a hankali ta ida Hayewa saman gadon ta konta ta juya mishi baya ta saki kuka kassa kassa ya na jiyo sautin kukanta ya saki wani dan karamin tsaki cikin zuciyarsa ya na fadin " shikenan yanzu ni an hada ni da wani aikin " a hankali ya juyo ya na kallon ta ya ce " kukan me ki ke kuma ? " " to ba kai ne ba na tambaye ka ka kyale ni " " okay , zan fada miki yanzu daina kukan nan " da sauri ta mike zaune ta na murmushi ta ce " shikenan na daina " ta fada ta na kai hannu ta na goge hawayenta sai da ta zauna sannan ya ce mata " okay , abu na farko da ya kamata ki sani shi ne ba na son takura , dan haka duk shirmen da za ki yi ki ka ce za ki takura min zan bar miki gidan, kuma ko Cutie da Daddy ba za su san in da zan je bare ma su ce na dawo " nan take murmushin da ke saman face din ta ya bace jin ya kira sunan Cutie kamar za ta yi kuka ta ce " wai wacece Cutie ? har yanzu ba ka fada min ba " " Cutie is My momy , Cutie shi ne sunan da Daddy ke kiran ta da shi har mu ma mu ka dinga kiran ta da haka , shikenan ? kin ji dadi ? " wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta gyada mishi kai , sai yanzu ta tuno lokacin da su ka tafi wajen Malik ta ji ya furta sunan Cutie , to hankalinta bai kawo ba ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Muryarsa ya na fadin " yanzu konta ki yi barci " noke mishi kafada ta yi ta na fadin " no , ka bar ni na ci gaba da kallon ka mana , wai an taba fada maka ka na da kyau ? " " an sha fada min " ya fada ya na fara latsa wayarsa ci gaba da magana ta yi ta na fadin " har so na ke safiya ta yi domin na ci gaba da kallon kyakyawar fuskarka mai yaye dukkan kuncin da damuwar ruhina , please ka juyo ka kalli da fararen idanunka ma su sheqi da haske kamar wani sashi na wata " shi dai bawan Allah ya yi zaune ya na sauraron ikon Allah , har ya fara tambayar kansa anya ba wani abu ta ke sha ba ? yadda ta ke zaune ta na irin wadanan kalaman ko tsoro ba ta ji , ko shi ne ba zai iya ba kai tsaye haka , ta wani bangaran kuma ya na jin dadin kalamanta ya na ga kamar yabon sa ne ta ke yi haka dai ta yi zaune sai zuba ta ke mishi, shi kuma ya na aikinsa da wayarsa , bai da labari har barci ya yi gaba da ita sai da ya ji wajen ya yi tsit ya tabbatar to barci ya yi gaba da ita a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kalle ta , ta na barci cikin konciyar hankali , jelar gashinta ya bazun mata saman face a hankali ya kai hannu ya janye mata gashin ya zubawa face din ta ido , in kowa ganin ya ke su na kama ita da Aleenah shi ba ya ganin wannan kamar bai san me ya sa ba , sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta kafin ya tashi a hankali ya kashe lamps din dakin ya kunna bedside lamps sannan ya fito dakin ya janyo mata kofar ya tafi tashi bedroom din ▪INAYA 🕊👑 bayan ta baro part din MALIKAT INAS kai tsaye nasu part din ta koma , a nan floor na uku ta tardo Malik , ya na konce cikin bedroom din su , sanye da kayan barcinsa ya zubawa ceiling ido kamar mai tunanin wani abu wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta tako a hankali ta nufi toilet ta shiga wanka ta yi ta fito daure da towel a kirjinta ta na rike da wani dan karamin towel ta na goge gashin kanta har yanzu shi dai ya na yadda ta bar shi ko motsi bai yi ba nan take jikinta ya ba ta akwai abun da ke damun sa ajiye towel din hannunta ta yi saman dressing mirror sannan ta tako a hankali ta zauna bakin gadon ta kai hannu saman face din sa wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke ya na lumshe idanunsa a tare ya daura hannu saman nata cikin sanyin murya ta ce mishi " baby , tunanin me ka ke yi haka ? " wani cool murmushi ya saki kafin ya ware idanunsa ya kalle ta ya ce " nothing , just ina tunanin jarabar da Prince zai yi wa yarinyar nan kafin ya fara sake mata , na san za ta sha wuya " wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " kar ka damu ba wata azabar da za ta sha , saboda ya na son ta , ni fa da ita da Twins din ta kassa gane su na yi , shi kuma kallo daya ya yi musu ya gane wacce ce matarsa " wata yar karamar dariya shi ma ya yi kafin ya ce " kamar ba ki san halin Prince ba , ko ya na son ta ba zai yarda da hakan ba , hannu ta kai ta fara shafa kansa ta na fadin " ai halinka ya dauko , kar ka damu in dai ba ta cika kunya ba cikin sauki za ta shawo kansa , kuma kai ma ka san halin Prince abu guntu ke jan hankalinsa , bare in sanyi ya kama shi ko ba ya so sai ya neme ta " ta kai karshen ta na wata yar karamar dariya dariya shi ma ya yi kafin ya kai hannu ya janyo ta jikinsa ta fado saman chest din sa , ya na kallon cikin idanunta ya ce " wane sanyi kuma ? ki ba shi kwana biyu kadai , zai fara .. " ya kai karshen ya na dago kansa a hankali ya manna mata kiss a wuya wata yar karamar dariya ta yi ta kai hannu a hankali ta fara balle button din rigar barcinsa , sannan ta ida Hayewa gadon ta konta a gefensa wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya juyo su na fuskantar juna , nan take labarin ya sauya a ka hau sabon wassa ( 😴😴 ni kuma na dauki takarduna na fito dan barci na ke ji ) WASHE GARI ⛅ ▪ALEESHERH 👑💞 da addu'ar barci a bakinta ta farka da ga barcinta , slowly ta ware idanunta ta fara bin dakin da kallo , ta ga ita kadai ce cikin dakin wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta sauko da ga saman gadon , nan ta ga wayarta ajiye saman bedside drawer cikin rudu ta kai hannu ta dauke ta dan ita ta na tune ta bar ta a part din MALIKAT INAS kunna wayar ta yi ta ga karfe 7 da mintina 12 wani cool murmushi ta saki kafin ta fara takawa a hankali ta nufi curtain din da ke fuska kofar shigowa dakin , ta janyo curtain na gefen dama ta rufe rabin glass din , dan wajen ya rage haske , sannan ta nufi toilet ta shiga Jim kadan ta fito sanye da bathrobe ta tsaya gaban dressing mirror ta fara kallon Lotion din da ke sama , ta zabi guda ta shafa sannan ta shiga dressing room after some minutes ta fito sanye da wata gown pink colour mai kyau , ta sha ruwan stone , ta saki gashin kanta har tsakiyar baya , da wasu dan kanana sun zubo mata a gaban goshi , sai tashin qamshi ta ke kai tsaye bedroom din ta fito ta fara bin wajen da kallo , kofofi shidda ne ta gani a wajen kuma duk su na rufe , kawai sai ta nufi hanyar fita corridor din ta fito ta na fitowa ta ga wata maid ta baro dining table ta na shirin komawa kitchen da sauri Aleesherh ta taro ta ba musu ta tsaya ta dawo ta zube saman guyiwowinta a gaban Aleesherh ta na gaishe ta cikin girmamawa wani dan karamin murmushi Aleesherh ta saki kafin ta ce " mike tsaye don Allah , kar ki sake min irin wannan abun , ba kin girme ni ba " ba musu ta mike tsaye kanta a sunkuye ta ce " haka ne ranki ya dade , na girme ki amma matsayin mu ba daya ba " " shikenan , ya sunanki ? " " Asmeet , ranki shi dade " " Asmeet , don Allah akwai kitchen a wajen nan ? " " Eh ranki ya dade " " mu je ki gwada min please " gyada mata kai kawai Asmeet ta yi kafin ta fara takowa ta yi gaba kai tsaye su ka nufi hanyar fita wajen su ka fito harabar part din , su na fitowa su ka yi dama nan ta ga wata door ta zallar glass , su na isa door din ta bude nan ta ga kitchen din cike da maids har wajen goma , kitchen din a share a goge kamar ka ci abinci a kassa , sai aiki su ke yi duk su na ganin Aleesherh kowace ta tsaya cak su ka sunkuyar da kai su na gaishe ta kai ka ce ita ce MALIKAT INAYA da murmushi a face din ta ta amsa musu , sannan ta fada musu abun da ta ke bukata ta shirya wa Prince breakfast , sannan ta ce musu da ga yau duk abincinsa ita za ta shirya shi da to kawai su ka amsa mata sannan su ka fiddo mata abubuwa da ta fada cikin nitsuwa ta fara hada mishi breakfast da coffee cike da so , bayan ta kammala ta shirya komai saman tray sannan ta dauki kayanta ta fice ta bar su su ka ci gaba da aikinsu da sallama a bakinta ta shigo parlourn duk da ba ta san in ya na nan ko ba ya nan ta na shigowa ta gan shi zaune saman sofa sanye da kananan kaya , wandon jeans da rigarsa duk Blue color , ya na rike da wayarsa da hannu guda ya na latsawa Princess ta na konce gefensa ta tada kai da laps din sa , hannunta da hannunsa na sakale cikin na juna , ta lumshe idanunta da wani dan karamin murmushi a face din ta Dam Aleesherh ta ji zuciyarta ta buga ganin su a haka , har wasu ruwa su ka ciko mata a ido , kishi ta rufe mata ido ta kassa ganin kamar da ke tsakanin prince da princess , dan kamar an tsaga kara su ke , yadda ta ke da Aleenah haka ya ke da Princess , Sai dai ita kawai mace ce nan take jikinta ya yi sanyi , ta sunkuyar da kai , ta karaso wajen ta nufi dining table ta ajiye tray din sannan ta juya ta shiga corridor da gudu duk wani takunta ya na sane , kawai ba ya son magana ne sai da ta shiga bedroom din ta sannan ya ce wa Princess " kin gani ko yanzu kin saka ta kuka ? to sai ki je ki ba ta hakuri dan ni ba in da zan je " wata yar karamar dariya Princess ta yi kafin ta saki hannunsa ta mike zaune ta na fadin " Prince , babynka ta cika kishi , yanzu ba ta ga kamar da ke tsakanin mu ba ? " " duk dai laifinki ne , yanzu tashi ki je " ba musu ta tashi ta na dariya ta nufi corridor ta shiga ta na isowa bakin kofar dakin Aleesherh ta jiyo Muryarta ta na kuka a hankali ta shiga cikin dakin ta nade hannayanta a kirji ta zuba mata ido sai kuka ta ke baiwar Allah ta boye fuskarta cikin pillow sai da ta kare mata kallo sannan ta tako a hankali ta na fadin " to shi kuma kukan na minene ? ko ni ma ba na da izinin zama kusa da dan uwana ? " ko sauraron ta Aleesherh ba ta yi ta ci gaba da kukanta a hankali ta karaso bakin gadon ta zauna ta kai hannu ta dafa shoulder din Aleesherh ta na fadin " za ki daina kukan nan ko sai raina ya baci ? " sai a lokacin Aleesherh ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya ta goge face din ta cikin pillow din , ta dago kai a hankali ta kalli Princess ta na zama Princess ta saki wani dan karamin murmushi ta ce mata " kukan kuma na minene ? ni fa sister din ki ce , ta ya za ki yi kishi da ni ? " " sister ? " ta fada cikin rudu " yeah , i'm Nailah or Princess , Twins din Prince , ko ba ki ga mu na kama ba ? " ta kai karshen ta na daga mata gera ita sai yanzu ta samu damar kallon ta da kyau kuma gaskiya su na kama har hazel eyes din su , a sanyaye ta ce mata " amma ni bai fada min ba ya na da twins ba " " shi fa Prince bai cika magana a kan rayuwarsa ba , da kin tambaye shi ya na da sister ko brother zai fada miki , amma in ba ki tambaye shi ba ba zai fada miki ba , now tell me what's your name ? " " Aleesherh " " Aleesherh , sunan ya yi dadi , yanzu tashi mu je ki yi breakfast ko ba ki jin yunwa ? " mikewa tsaye ta yi ta nufi toilet ta shiga wanke face din ta ta yi sannan ta fito , Princess na tsaye bakin kofar dakin ta na jiran ta a hankali ta karaso wajen , riko hannunta Princess ta yi sannan su ka fito bedroom din a tare su ka fito su ka fito parlour , nan su ka tardo shi zaune a dining table ya na shan coffeen da ta hada mishi ba karamin dadi ba ta ji ganin ya na shan coffeen har ta saki wani dan karamin murmushin gefen fuska dining table din su ka karaso Princess ta zauna gefen Prince , Aleesherh kuma ta zauna saman chair din da ke fuskantar tashi ta na kallon shi su na zama ko Junior ya shigo parlourn ya na sallama ya na sanye da suit blue da murmushi a face din sa ya karaso wajen ya na fadin " yau kuma a nan a ke breakfast ? " " Good morning Junior " Princess ta fada ta na murmushi chair din da ke gefenta ya janyo ya zauna ya na fadin " me ki ke yi a nan tun da safe haka ? a ka je ki ka tardo su cikin wani yanayi fa ? " ya kai karshen ya na daga mata gera wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " to ni ina ruwana , kuma Cutie ta ce min Prince na nan shi ya sa na taho wajensa " " shikenan tashi mu tafi " ya fada ya na mikewa tsaye cikin rudu ta ce " mu tafi ina kuma ? ba wajen Prince ka zo ba ? ni tafiya zan yi " girgiza mata kai ya yi ya na fadin " no , ni dama ke na zo nema , akwai wani sabon restaurant da ya bude cikin gari zan so ki raka ni " " da gaske ? su na saida ice cream ? " ta fada cikin yar shagwaba " to ai shagon ice cream ne baki daya , shi ya sa na ce mu je ki raka ni " ya fada dan ya san halinta da mugun son ice cream da sauri ta mike ta sunkuyo a hankali ta manna wa Prince kiss a kumatu ta riko hannun Junior su ka bar wajen , sai murmushi ya ke ya samu abun da ya ke so Prince kuwa ko a jikinsa sai shan coffeensa ya ke , Aleesherh kuma ta tsare su da ido ta na murmushi sai da su ka fita sannan ta ce wa Prince " Baby , amma wannan mijinta ne ko ? " slowly ya dago sexy eyes din sa ya kalle ta , murya cen kassan makoshi ya ce " kin ga na yi miki kama da baby ? " " to ai ni ba wancen babyn na ke nufi ba , ina nufin masoyi haka , ko ka fi son na kira ka da Honey ? " shiru ya yi bai ce mata komai ya dauki wayarsa ya fara latsawa ci gaba da magana ta yi ta na fadin " Honey , ba ka ba ni amsa ba , kuma yaushe za mu tafi honey moon ? " wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " wai me na ce miki jiya ? " marairaice mishi fuska ta yi kafin ta ce " sorry , ni just ina son mu yi hira ne " shiru ya yi bai ce mata komai ya ci gaba da aikinsa , ya ga alamun wannan bakinta bai iya shiru ba , da ma Aleenah ya fadawa Al-Sayid ya aura mishi dan ya ga ta fi wannan sanyi ya yi nisa duniyar tunaninsa kawai ya ji ta zauna a kujerar da Princess ta tashi , a hankali ta kai lips din ta saman kumatunsa ta manna mishi kiss nan take ya ji wani bakon yanayi cikin zuciyarsa lokacin da Princess ta yi mishi kiss ba abun da ya ji , yanzu kuma ita da ta yi mishi har wani shock ya ji cikin jikinsa ita kuwa ba ta ma san ya na yi ba , ta janyo tray din breakfast din da ta shirya mishi ta fara cin kayanta dan ta lura coffeen ne kadai ya ke bukata slowly ya dago kai ya kalle ta , ta na cin abincin cike da nitsuwa nan take ya tsargu da kallon ta , har ya manta aikin da ya ke da wayarsa , haka ita ma sarai ta ke lure da shi amma ba ta tanka ba , tun da ya ce ba ya son takura yanzu kam za ta fara yi mishi fuska kamar lokacin da su ke Yemen _______________________________________________ _ PAID BOOK *WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , ₦500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ƊIN* [ PAGE ___ 17 🕊👑❤ ] sai da ta koshi sannan ta sha ruwa kadan , ta dauki Tray din sannan ta juyo ta kalle shi ta ce " ina son na tafi wajen Aleenah " gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba murmushi kadan ta yi kafin ta juya ta bar wajen rike da tray din , sai da ta meda shi kitchen sannan ta baro part din shi ma ta na fita ya mike ya baro part din kai tsaye Garden ya nufa kassan daya da ga cikin runfuna ya zauna dan yanzu wajen ya kara girma , sun kara runfunan saboda shan iska , zama ya yi saman sofa three seaters , ya fara latsa wayarsa ya na a haka Azmat ta fito da ga cikin part din Diya za ta tafi wajen Nesrine da ke part din MALIKAT INAS ta na hango shi ta saki wani dan karamin murmushi ta fassa tafiya part din Malikat Inas , ta juya ta nufi garden din da Sallama a bakinta ta shigo wajen ta na sakin murmushi da ga in da ya ke ko dago kai bai yi ba , amma sarai ya ji ta , sallamarta ma cikin zuciya ya amsa mata ita a hankali ta karaso saman sofar da ya ke zaune ta zauna , ta na kallon shi ta ce " Prince , shi ne ka dawo amma ko nema ta ba za ka yi ba ? ko ba ka yi kewar sister d'in ka ba ? " ta kai karshen ta na turo dan karamin bakinta ko sannu bai ce mata ba ya ci gaba da aikinsa " amma Prince wannan karan tare za mu koma U.S ko ? ina son na tafi U.S ko so guda ne " wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya dago kai ya kalle ta ya ce " Azmat , please let me , aiki na ke " shagwabe mishi fuska ta yi ta na turo dan karamin bakinta ta ce " Amma Prince , yanzu fa wajen one year rabon da ka gan ni , na kawo maka hira shi ne ka ke kora ta ? ni gaskiya babu in da zan je " wani siririn tsaki ya ja kafin ya kauda kai ya ci gaba da aikinsa , ta na neman ta takura mishi gaskiya ita ma ba ta ce mishi komai ba ta matso ta na lekon wayarsa duk da ba ta san abun da ya ke ba shi kuwa ya yi shiru bai ce mata komai ba dan ya san in ya yi mata magana za ta kara takura mishi , gwara ya yi shiru ko za ta kyale shi in ta na kallon cikin wayar ▪ALEESHERH 👑💞 bayan ta baro part din su kai tsaye part din MALIKAT INAS ta nufa da sallama a bakinta ta shigo parlourn , ta tardo Nesrine da Tesnim zaune su na hira , MALIKAT INAS kuma ta na cikin bedroom din ta , RIANNA ta na cen ta na fama da Faaz da sauri Nesrine ta taro ta ta na fadin " Aleesherh ? da ga ina ki ke haka ? ko koro ki Prince ya yi ? " ta fada dan duk gashin kanta a waje ya ke babu ko Alkyaba a saman kayanta cikin rudu ta fara bin jikinta da kallo ta na son ta ga minene su ka gani sai da ta gama dube duben ta ba ta ga komai ba ta juya ta kalle su ta ce " Momy , ni ban ga komai ba " " Aleesherh , ke fa yanzu matar aure ce , ko ba ki duba matsayin mijinki cikin masarautar nan bai kamata ki fito haka ba , at least sai ki saka Alkyaba da ga sama in ba ki son saka veil , dubi gashinki duk ya na waje " Fadin Tesnim sai a lokacin ta tuno ashe babu veil a kanta , nan take kunya ta kamata ta sunkuyar da kai , murya a sanyaye ta ce " sorry momy , mantawa na yi " wani dan karamin murmushi Tesnim ta saki kafin ta mike tsaye ta na fadin " jirani a nan " ta fada ta na takawa ta nufi corridor ta shiga ita dai Aleesherh ta na tsaye kamar wata gunki , sai wassa ta ke da yatsun hannunta ta na tsaye a haka Tesnim ta fito da ga cikin corridor rike da wata Alkyaba ta MALIKAT INAS , white color mai kyau da laushi da ga gani ta auduga ce , an yi mata zanen tambarin masarauta Saudiya kanana da zare pink color har wani kyali su ke a haka ta karaso wajen Aleesherh ta saka mata Alkyabar da kanta

Chapter 14 of 23