Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cikin sanyin murya ya ce mata " ba abun da zai faru da ke in har ina raye , yanzu mu je mu yi breakfast , na san ki na jin yunwa ko ? " gyada mishi kai ta yi a hankali alamun Eh a hankali ya sunkuyo ya manna mata kiss a forehead sannan ya riko hannunta su ka baro bedroom din ya na rike da hannunta har su ka baro corridor su ka nufi dining room in da ya hango tray din da ta ajiye wata yar karamar dariya ta yi kafin ta kontar da kanta saman shoulder din sa ta ce " ba dole na iya ba , ba na son barin dama ko da guda ce ta mallake zuciyarka " a hankali ya zagayo da hannunsa a bayanta ya na fadin " kin riga da kin mallake ta my Beautie , sai dai in zuciya biyu gare ni ban sani ba " dariya kawai ta yi ta lumshe idanunta girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " No my Honey , ci abun ka , ka sha coffee tun bai yi sanyi ba " bai ce mata komai ba ya dauki coffeen ya fara sha ita kuma ta dauki sandwich guda ta fara ci , ta na kwance a jikinsa sai da ya kammala sannan ya janye hannunsa da ga saman bayanta ya ajiye mug din ya mike tsaye ya na fadin " Na gode my Beautie " ya kai karshen ya na manna mata kiss saman forehead sannan ya juya ya nufi parlour ya zauna ya na jiran ta kammala ci bai yi one minute da zama ba ta mike ta dauki plate din fruits da na banana bread ta ajiye saman table din , ta dauki sauran ta na fadin " Honey , zan meda dishes din Kitchen " gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba , ita kuma ta fito parlourn ta na fita kawai na ga ya saki wayarsa , jini ya fara fitowa da ga hancinsa a hankali ya kai hannu ya taba jinin dan ya tabbatar da gaske jini ne ya ke ji hankalinsa bai gama tashi ba sau da ya fara tari ya na furzo jini a tare , ya ji wuyansa ya rike kamar an shake shi ya kassa nunfashi ya na ciki wannan halin Aleesherh ta dawo parlourn ta na murmushi ta na ganin halin da ya ke ciki ta saki wata yar siririyar kara ta nufe shi da gudu ta na fadin " Honey , me ya faru ? me ya same ka ? " murya a disashe ya ce mata " kiro min Cutie " ya fada a rarrabe girgiza mishi kai ta shiga yi ta na kuka ta na fadin " Honey , don Allah me ke faruwa ? duba jini ka ke zubarwa , wayo ni na shiga uku " da karfi ya dago kai ya ce mata " je ki kira min Cutie na ce ! " ya fada da karfi har sai da ta razana ta rumtse idanunta ba shiri ta sake shi ta tashi da gudu ta fice parlourn ta na kuka ta na fita kawai na ga ya lumshe idanunsa ya yi baya ya fadi saman sofar ko motsi ba ya yi ko da ta karaso bakin kofar shiga part din ta tsaya ta na tambayar Malik daya da ga cikin su ne ya ce mata ya na floor na uku da gudu ta shiga building din ta nufi lift kai tsaye a floor na uku ya tsaya ya na budewa ta shigo parlourn da gudu ko sallama babu da sauri Malik da Inaya da ke zaune a kassa saman carpet su na breakfast su ka mike tsatsaye cikin rudu Inaya ta ce mata " Alee ? me ya faru ? lafiya ki ka yi irin wannan shigowar ? " wasu yawu ta hadiye kafin ta ce " Momy , momy , shi ya ce na kira ku , ban san abun da ke faruwa ba " sai da kofar lift din ta rufe sannan Aleesherh ta samu damar ce mishi " Daddy , ban san abun da ya same shi ba , mu kammala breakfast ne na tafi kai dishes kitchen kawai na tardo ya na tari ya na furza jini har ta hancinsa " ta fada ta na kuka hawaye na zubo mata bibiyu da sauri Malik ya daga kafa ya fita har ya na hadawa da gudu har ya iso kofar fita building din kawai ya jiyo Muryar Inaya ta na kwalla mishi kira da karfi cak ya tsaya ya juyo , nan ya gan ta zaune a kassa cikin lift din da Aleesherh kwance a kassa kanta na sama cinyar Inaya da alamun ta sume wani dan karamin tsaki Malik ya ja kafin ya juya ya fice da gudu dan shi hankalinsa na waje guda wajen babynsa bayan ya fita ne ya ke ce wa dayan security ya je ya dauki Aleesherh ya kai ta Word room ko da su ka fito kai tsaye word room su ka nufa shi dai Faaz ya na zaune cikin garden ya na kallon duk abun da ke faruwa , ya na murmushi har da fruits a gabansa ya na sha ban san da ga ina fruits din su ke ba bangaran Malik kuwa , kai tsaye part din Prince ya nufa , ya shigo parlourn kamar an turo shi da ga sama idanunsa na sauka kan Prince ya ji zuciyarsa ta yi wata muguwar bugawa har sai da ya ga dishi dishi lokaci guda da sauri ya nufe shi ya zube saman guyiwowinsa , ya kai hannayansa dukka biyu saman face d'in Prince ya fara jijiga kansa ya na fadin " Nayel ? Nayel open your eyes , please ka tashi don Allah , kar ka tafi ka bar ni , please my Nayel wake up " lokaci guda idanunsa su ka ciko da ruwa kamar zai yi kuka da sauri ya mike tsaye ya kai hannu ya goge ruwan tun kafin ma su zubo , ya sa hannu ya dauki Prince ya saba shi saman shoulder sannan ya fito part din da shi ya nufi word room (😿😿abun da ya faru ya tuno min lokacin da Rouksar ta zubawa Malik poison , amma shi a lokacin kunfa ce ta fito da ga bakinsa , yanzu Prince jini ne , duk yadda a ka yi abun da Aleenah ta zuba cikin coffeensa ne ya yi wannan abun , yanzu ya za ta kare ? ga kuma Aleesherh ta sume ? 🏃♀️ bari na yi nan to , mu hadu gobe ) An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 23 of 23