Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
🔥🔥 ▪MALIK 👑🔥 a zaune su ke cikin parlourn MALIKAT INAS shi da Cutiensa , da RIANNA da MALIKAT INAS da Faaz kamar kullum Diya kuma yau ya koma Fada dan tun lokacin da ya konta ciwo Abdoul ne ke kula da komai yau to ya koma dan ya na son a gyara masarautar kafin dawowar su Prince su na zaune a haka wata mata ta shigo parlourn ta na sallama ta na sanye da wasu suit black color , ta medical glass a idanunta , ta na rike da wata bag a shekaru ba za ta wuce 30 years ba ko 35 haka RIANNA na ganin ta ta mike tsaye ta nufe ta ta na fadin " Prof barka da zuwa , bismillah shigo " ta kai karshen ta na mika mata hannu ba musu ita ma ta dago hannu su ka gaisa sannan RIANNA ta karaso da ita cikin parlourn cikin rudu ko wane ke kallon ta dan su ba su san ta ba kamar ko RIANNA ta san kallon me su ke sai ta ce musu " wannan ita ce prof din da na dauka za ta dinga yi wa Faaz class a nan gida kafin ya saba na kai shi school cikin sauran yara " sai a lokacin ko wane ya gane abun da ke faruwa Faaz kuma ya na jin abun da ta ce ya mike tsaye ya na fadin " no , ni ba na so , ba in da zan tafi " cikin sigar rarrashi Rianna ta ce mishi " kar ka damu ba in da za ka tafi , a nan cikin bedroom din ka za ta koya maka , okay ? " da sauri ya girgiza mata kai ya na shirin magana Rianna ta riga shi cewa " no , keep quiet ! in ba so ka ke ka bata min rai ba ka yi shiru ku tafi ta koya maka " kunbure fuska ya yi ya na turo dan karamin bakinsa ya fara takawa ya nufi corridor kallon prof din Rianna ta yi ta na fadin " bismillah mu je na kai ki bedroom din sa " gyada mata kai kawai prof din ta yi kafin ta fara takawa su ka shiga corridor sai da su ka shiga sannan Malik ya ce wa MALIKAT INAS " Ammie, wai yaron nan ba zai koma gidan marayu ba ? na ga RIANNA duk ta sangarta shi " a sanyaye MALIKAT INAS ta ce " to me ka ke so na ce ? ka san halin yar uwarka , ko na ce ta meda shi ba za ta yarda ba saboda ta na son shi " ta na gama rufe bakinta ko Rianna ta fito da ga cikin corridor ta na murmushi ta koma in da ta tasso ta zauna a hankali Malik ya juyo ya kalli Cutien sa ya ce " Junior ya kira ni ya ce wai Al-Sayid ya ce su zauna har lokacin da za a yi bikin auren prince " wata yar karamar dariya ta yi ta na kallon shi ita ta san halin yaronta duk lokacin da ya yi karya ta na iya gano shi sai da ta gama dariyarta sannan ta ce " wane Al-Sayid kuma ? kawai bai shirya dawowa ba ne , kawai ya yi anfani da damarsa ce ya koma in da ya fito " wani dan karamin tsaki Malik ya yi dan al'amarin Prince ya fi karfinsa " zai dawo ya same ni " ya fada a dakile ita dai Inaya dariya kawai ta ke yi bari na leko su Faaz kafin nan zaune ya ke bakin gadonsa ya nade hannayansa a kirji sai hura kumatu ya ke prof din na zaune geffensa rike da wani book ta na murmushi ta ce mishi " yawwa yanzu zan so na sani in ka taba zuwa school ko so guda ? " " No " ya fada a takaice " kenan ba ka san alphabet ba ? " ta tambaye shi murya cike da sanyi a hankali ya juyo ya wurga mata wani mugun kallo ya na fadin " ke na yi miki kama da wanda bai san alphabet ba ? in har ki ka bude baki ki ka sake min magana sai na kashe ki a wajen nan sakara kawai " tsit prof ta yi ta na kallon ikon Allah ta na tambayar kanta ko dai aljanu ne su ka shige jikinsa sai da ta saita nitsuwar ta sannan ta ce " okay , yanzu fada min sunanka " tass ta ji saukar mari a face din ta , baki sake ta ke kallon shi ta dafe kunci, wai da gaske shi ne ya mare ta ko dai aljanu ne su ka mare ta ? dan ita ba ta ga lokacin da ya daga hannu ba a hankali ya mike tsaye ya nufi kofar fita dakin ya sa hannu ya tura ta ya saka mata security sannan ya juyo ya na kallon ta , wata yar karamar dariya ya yi kafin ya daga hannayansa dukka biyu sama kamar da wassa kawai na ga wasu kananan kwari sun fara fitowa da ga cikin tafin hannayansa wata razananiyar kara Prof ta saki ta ida Hayewa saman gadon ta na ja da baya , shi kuwa sai dariya ya ke kwarin nan na kara fitowa da ga cikin hannayansa duk su ka nufe ta su ka fara Hayewa saman gadon sai da ya ga kwarin sun kusa taba ta sannan ya damke hannayansa ya sauko su kassa , batt kwarin nan su ka bace kamar ba a taba yin su ba ita kuwa baiwar Allah sai kara ta ke saki kamar ta yi kuka a hankali ya tako bakin gadon ya na fadin " yi min shiru ko in kashe ki wajen nan ! " ai ko da sauri ta daura yatsa saman lips din ta ta na girgiza mishi kai kamar ta yi kuka , gaskiya ta razana wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " Aunty , ki na ji ni ba na son wannan karatun , in kin fita ki cewa momy ke ba za iya koyar da ni ba , kin ji ko ? " ya fada cike da shagwaba gyada mishi kai kawai ta yi da sauri alamun Eh zama ya yi bakin gadon ya na fadin " shikenan tun da kin yarda za ki iya tafiya , in kuma ki fadawa wani abun da ya faru sai na kashe ki " da sauri ta sauko da ga saman gadon ta dauki bag din , ita littafin ma da ta fiddo ta manta da shi ta nufi kofar fita dakin da ya ke ta ga wajen da ya danna kofar ta rufe kawai ta sake dannawa kofar ta bude ta fice da sauri Kamar ta ga wani abun tsoro a nan parlourn kuma su na zaune su na hirar su cikin konciyar hankali su na a haka kawai su ka ga prof ta fito da sauri ta nufi kofar fita parlourn ko ta kan su ba ta bi ba , ga yanayin ta duk ya sauya cikin rudu RIANNA ta mike ta na fadin " Prof lafiya na ga kun fito ? har kun gama ? " ba tare da ta tsaya ba ta ce " ki yi hakuri ranki shi dade amma ba zan iya koyar da shi ba , ina da aikin yi , na gode " ta na gama fadar haka ta sa kafa ta fice cike da rudu RIANNA ta ke kallon Prof har sai da ta fita sannan ta nufi corridor ta shiga ta na kwallawa Faaz kira ko da ta shigo bedroom din sa ta gan shi zaune a kassa sai kuka ya ke ya dafe kumatunsa da hannu guda karasowa wajen sa RIANNA ta yi ta sa hannu ta mikar da shi tsaye ta na fadin " Faaz me ya faru ? wani abu ta yi maka ? " ya na kuka ya ke ce mata " momy ba ta da kirki, bugu na ta yi , ce wa ta yi na karanta mata alphabet na ce ban iya ba shi ne ta shiga bugu na , da na ce zan fadawa momyna ta sa a cire mata kai shi ne ta tashi ta tafi ta na ce min shege " ya kai karshen ya na kara sautin kukansa cikin sigar rarrashi RIANNA ta ce mishi " shikenan , i'm sorry , i'm sorry daina kukan nan please , bari zan sa a cire mata kai kamar yadda ka ce , ka na so ? " da sauri ya gyada mata kai ya na kai hannu ya fara goge hawayensa kiss ta yi mishi saman forehead kafin ta rungume shi ta na fadin " shikenan stop crying now " rungume ta shi ma ya yi ya na kukan karya da wani kyakyawan murmushi a face din sa ( 🤔🤔 TO FA , A NA DARA GA DARE YA YI , GA DUKKAN ALAMU FAAZ BA DA MANUFA MAI KYAU YA SHIGO DAULAR NAN BA , TUKUNNA MA WANENE SHI ? SU WA SU KA AIKO SHI ? ME YA KE SHIRIN AIKATAWA ? HMMMM NI DAI NA KOMA GEFE GASKIYA ) ▪INAYA 🔥 bayan RIANNA ta shiga corridor ta mike tsaye ta na fadin " Ammie bari na je na duba su " da sauri Malik ya riko hannunta ya na fadin " no , bar ta da babynta , mu tafi " ya kai karshen ya na mikewa tsaye da sauri ta ce mishi " amma baby ka bari na ga kar a je wani abu ta yi mishi " " to ina ruwanki Ah ? wuce mu tafi ko kuma na ja ki da karfi , kin kuma san in na ce na ja ki da karfi ba za ki ji dadi ba ko ? " hararrar shi ta yi ta na turo dan bakinta kafin su bar wajen ya na rike da hannunta ita dai MALIKAT INAS ta na zaune ta na kallon dramarsu sai da su ka fita sannan ta tashi ta shiga bedroom din ta bangaran su Malik kuwa ko da su ka fito a tunaninta building din su za su koma kawai sai ta ga ya nufi wani part din da ita , dama akwai wasu part dayawa da babu kowa a ciki , specially ma MALIKAT HOUDA , MALIKAT Jaoudatt su ka rasu duk a ka rushe part din su a ka yi sabi , amma ba wanda ya shiga cikin su ko da su ka shiga parlourn ya saki hannunta ya nufi hanyar bedrooms da sauri ta ce mishi " me kuma mu ke yi a nan ? " bai ce mata komai ba ya ci gaba da tafiyarsa ya shiga corridor din , ta na tsaye ta na kallon shi ko motsi ba ta yi ba ta na tsaye a haka ya fito ya na fadin " mu tafi " da sauri ta riko hannunshi ta na fadin " no , wai me mu ke yi a nan ? " a hankali ya juyo ya zagayo da hannunshi a kugunta ya janyo ta jikinsa cikin sanyin murya ya ce mata " wai ke me ya sa rigimar ki ta fi ki yawa Ah ? kin san ai duk abun da ke faruwa fada miki zan yi ko ? to part din da Prince ne zai sauka da matarsa , ina son na shirya mishi surprise kafin ya dawo , shikenan ? kin ji dadi ba fada miki ? " turo dan bakinta ta yi , cikin yar shagwaba ta ce " to ai ba ka fada min wace irin surprise ba " " za ki gani , yanzu dai mu tafi na yi miki wanka " noke mishi kafada ta yi ta na fadin " no , ni ba na so na yi fushi da kai " ta kai karshen ta na raba jikinta da nashi ta fara takawa ta yi gaba bin bayanta ya yi ya na fadin " fushi kuma My Cutie ? me na yi za ki min fushi ? " sarai ta ji shi amma ta share ta ci gaba da tafiyarta har su ka fito harabar masarautar ya na biye da ita sai magiya ya ke mata amma ta ki tsayawa a haka har su ka karaso building din su ta wuce floor na hudu kai tsaye sai da su ka shigo parlourn sannan ya riko hannunta ya juyo ta su na fuskantar juna ya na juyo ta ya ga idanunta sun koma white baki daya ba karamar razana ya yi ba har sai da ya saki kara ya saki hannunta ba shiri bushewa da dariya ta yi ta na tapi , a hankali idanunta su ka fara dawowa dai'dai Black din ya fito bawan Allah har ya manta last time da ya ga wadanan idanun nata duk ya bi ya tsorata sai nunfashi ya ke ja da karfi ya na dafe saitin zuciyarsa sai da ya saisaita nitsuwarsa sannan ya ce " haba Cutie , ta ya za ki min irin wannan wassan ? da yanzu zuciyata ta buga fa ? " sai da ta tsagaita dariyarta sannan ta ce " i'm sorry baby , ni ma ban san na yi ba , sorry " wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya raba ta geffenta ya nufi corridor da sauri ta ce mishi " baby ba dai fushi ka yi ba ? " sarai ya ji ta amma ya ci gaba da tafiyarsa har ya shiga bedroom din su ya na shiga ita ma ta shigo da gudu ta nufe shi ta rungume shi ta baya ta na fadin " baby I'm sorry , ni ma ba da gangan na yi hakan ba , please kar ka yi fushi " ba tare da ya juyo ba ya ce mata " ya ki ke so na yi ? wlh kin ba ni tsoro kin sani ko ? da yanzu zuciyata ta buga fa ? me za ki ce ? " " i'm sorry " " i'm sorry fa ba ya sauya abun da ya faru , wani lokacin ma sai dai ya kara bacin rai , ni yanzu sake ni na je na yi wanka " " please baby kar ka yi fushi " ta fada kamar za ta yi kuka bai ce mata komai ba ya sa hannu ya zame hannayanta da ga saman kirjinsa ya juyo ya rungume ta ya na fadin " ki ka min kuka sai na cinye wannan bakin a wajen nan " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ida lafewa a jikinsa ta rungume shi tsam ( TO NI BARI NA KOMA WAJEN AMARYAR MU ) TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK _______________________________________________ ▪︎PAID BOOK N500 [ FREE PAGE ___ 12 🕊👑❤ ] ▪MASARAUTAR YEMEN 👑 ▪PRINCE 👑🔥 slowly ya ware idanunsa ya na karanto addu'ar barci ya na gama karanto addu'ar ya ce " Coffeeeeeeeeee ! " da dan karfi ai ko ya na gama rufe bakinsa Junior ya tilla mishi pillow a fuska ya na fadin " tashi ka yi kayanka nan ba gida ba ne " wani dan karamin tsaki ya ja ya na daura hannu saman forehead din sa ya ce " please Junior , kai ma ka sani ba na iya tashi in ban samu coffee ba " " wlh sai ka tashi ka yi abun ka , ba in da zan je " ya na gama fadar haka ya ida janyo duvet ya rufe duk jikinsa har kai wani siririn tsaki ya ja kafin ya sauko da kafafunsa kassa ya mike zaune ya mike tsaye ya na tangal tangal kamar me maye amma a haka ya dinga jan kafa ya na lumshe idanu a hankali har ya fito part din su shi kan shi bai san in da zai tafi ba , ya saba tun lokacin da ya ke karami da coffee ya ke tashi , duk lokacin da Inaya ta kawo wa Malik coffee in dai su na tare to sai ya sha da haka har ya saba ya na tsaka da tafiyarsa kawai ya ji mutum ya buge shi a kirji wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " Sorry , ina ne kitchen su ke ? " ya fada idanunsa a dan lumshe bai ma san wanene gabansa ba kare mishi kallo da kyau Aleenah ta yi , a sanyaye ta ce mishi " me ka ke bukata ? " " coffee " ya fada a takaice kafin ya juya ya koma part din su dan a tunaninsa wata maid ce da kallo Aleenah ta raka shi har sai da ya bar wajen sannan ta juya kai tsaye part din su ta koma Aleesherh ta na zaune saman gadonsu rike wayarta ta na latsawa sai da ta karaso gaban gadon sannan ta tsaya ta na fadin " Alee je ki kai wa Prince Coffee " cikin ko in kula Aleesherh ta ce mata " ni yar aikinsa ce da zan kai mishi coffee ? " " please Alee , i think ba shi da lafiya ba ki ga yadda ya ke tafiya ba kamar me maye ko ganin abun da ke gabansa ba ya yi " slowly ta dago kai ta ce " da gaske ki ke ? " gyada mata kai Aleenah ta yi alamun Eh shiru ta yi ba ta ce mata komai ba na dan lokaci kafin ta saki wani cool murmushi ta sauko da ga saman gadon da sauri ta ajiye wayarta saman bedside drawer ta fice da gudu sai da ta fita sannan Aleenah ta tako a hankali ta zauna bakin gadon , kawai sai na ga ta saki kuka kassa kassa ta na sunkuyar da kai , ko lafiya ta ke kukan nan ? ga shi ta kassa fadin abun da ke damun ta bare na yi rahoto , gwara na bi bayan Aleesherh dan murmushin da ta yi ban yarda da shi ba bayan ta baro Part din su kai tsaye kitchen ta nufa , ba sai na fada muku ba kun san yadda yanayin wajen zai kasance , kitchen din na da girma gaskiya ga shi ko cike da maid sai girki su ke yi , wannan kitchen din ta mutanan fada ne kadai da familyn Al-Sayid ba ta bi ta kan Maids din ba kawai ta shiga hada mishi coffee da kanta bayan ta gama ta shirya mishi fruits saman tray da glass cike da milk sannan ta dauki tray din ta fito kitchen din su dai Maid su na tsaye su na kallon ikon Allah yadda ta ke gyara breakfast din cike da so , a iya sanin su cikin shekara bai wuce so guda ta ke shigowa kitchen din ya a ka yi ta iya hada irin wannan lafiyayen coffee bare ma sun san ita ba ta shan coffee bayan ta baro kitchen kai tsaye part din su Prince ta nufa ta na shiga ta gan shi zaune saman sofa , ya daga kai sama ya na murza shi da hannu idanunsa a lumshe da alamun kansa ya fara ciwo har ta bude baki zai yi magana ta jiyo Muryarsa ya na fadin " wlh Junior mu ka koma Saudiya sai na yi ball da kai , yanzu ga shi kaina na min ciwo " a hankali ta daga kai ta kalli Junior da ke ta sharar barcinsa wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ajiye tray din saman table ta dauki mug din coffeen ta riko hannunsa ta saka mishi mug din a ciki bai kawo komai a ransa ba ya fara shan coffeen dan in bai coffeen nan ba akwai matsala ita kuma a hankali ta zagayo bayan sofar ta kai hannayanta saman kansa ta fara murza mishi shi cikin konciyar hankali nan take ya fara sauke ajiyar zuciya a jere , sai da ya gama shan coffeen tas sannan ya jingina bayansa da sofar ya daga kai sama sai da ya yi wajen two minutes a haka kafin ya ware idanunsa slowly ba su sauka ko ina ba sai saman face din ta , ta daure ta tamau kamar hadari , kawai sai ji ya yi ya kassa janye idanunsa da ga saman face din ta ganin ya tsare ta da ido ya sa ta kauda kai gefe ta na fadin " kanka ya daina maka ciwo ? ina so na tafi " slowly ya motsa lips din sa kamar an yi mishi dole ya ce " ni na saka ki ? " " No , amma rashin tausayina bai kai haka ba , kai ka ce min na kawo maka coffee kawai taimakon ka ne na yi " ta na gama fadar haka ta janye hannayanta da ga saman kansa ta nufi hanyar fita bin bayanta da kallo ya yi har sai da ta kai bakin kofar sannan ya ce " Na gode " wani dan karamin murmushi ta saki amma ba ta tsaya ba ta sa kafa ta fice sai da ta fita sannan ya meda idanunsa ya lumshe , ya san Sarai ba ita ya yi wa magana da farko ba saboda yanayin Muryarsu ba daya ba ce , shi kansa ya rasa ta ya ya ke gane su cikin sauki haka bayan su na kama tak kamar an tsaga kara , amma kallo daya ya ke musu ya gane su ya yi nisa duniyar tunaninsa ya ji a na yi mishi knocking sai da ya ja tsaki sannan ya ware idanunshi ya kalli saitin kofar wani dogari ne a tsaye ya na ganin ya juyo ya ce " ranka shi dade mai girma Al-Sayid ya na jiran ku a parlournsa ku yi breakfast " gyada mishi kai kawai Prince ya yi kafin ya mike tsaye ya nufi toilet ya shiga Jim kadan ya fito daure da towel a kugunshi ya nufi dressing room dan jiya ya yi musu online shopping na kayan da za su saka kafin su koma Saudiya jim kadan ya fito sanye da kananan kaya wandon Jeans da T-shirt duk white color, da fararen sneakers a kafafunsa bedside drawer ya nufa ya dauki wayarsa ya saka cikin aljihunsa sannan ya nufi kofar fita ko neman Junior bai yi ba , ya na dunkule cikin bargo sai barci ya ke bayan ya baro part din su kai tsaye parlourn Al-Sayid ya nufa dan jiya wajen zagaye zagayen shi har ya iso parlourn ba shi da labari da sallama a bakinsa ya shigo parlourn , nan ya tardo duk Familyn Al-Sayid har da su Twins din sa , su na zaune tsakiyar parlourn a kassa saman carpet , ga abinci tsakiyar su da alamun yanzu za su breakfast Al-Sayid na ganin shi ya saki wani cool murmushi ya na fadin " sannu da zuwa Prince , bismillah zauna , yau tare za mu yi breakfast " cikin girmamawa Prince ya ce " ina godiya sosai da irin wannan karramawar , na san ba kowa ke samun Alfarmar cin abincin da familyn shugaban kassar nan mai Albarka , na gode amma ina sauri ne zan fita , idan har mai girma Al-Sayid ba shi da matsala da hakan " gyada mishi kai Al-Sayid ya yi a hankali ya na murmushi gaskiya ba karamin tafiya da zuciyarsa Prince ya yi ba , tun ba yau ba , tun lokacin da ya zo masarautar neman littafi yanayin da ya ke magana ya yi mugun burge shi godiya Prince ya mishi kafin ya juya ya yi tafiyarsa da sauri Sayida Ahlame ta tabo Aleesherh da ke zaune gefenta ta ce " ba za ki raka shi ba ? " tsuke fuska Aleesherh ta yi kafin ta ce " ni na kawo shi ne ? " " Aleesherh ba na son wannan yanayin maganar taki " Al-Sayid ya fada cikin tsare gida kauda kai gefe ta yi ta na turo dan

Chapter 10 of 23