Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bakinta ba tare da ta ce komai ba " Aleenah , ina son ki taimakawa yar uwarki ta shirya mishi diner yau " fadin Al-Sayid da to kawai ta amsa mishi kanta na sunkuye ta na shan fruits Aleesherh kuwa sai shan tsami ta ke , kai ka ce ba saboda shi ne ta yi kuka kawai dan ya ki yi mata magana ta na a haka ta jiyo Muryar Sayida Ahlame ta na fadin " ranka shi dade , gaskiya yaron nan ya na da nitsuwa dubi yadda ya ke magana cike da girmamawa , na so ya na da dan uwana da na ba shi Aleenah " ta fada ta na kallon Aleenah har Al-Sayid ya bude baki zai yi magana Sayida Fadwah ta riga shi cewa " me ya sa ba za a ba shi Aleenah ba ma a kan Aleesherh " a tare Aleesherh da Aleenah su ka dago kai su ka kalle ta " na ga Aleesherh ita ce babba , ta ya za a ba shi auren Aleenah al'halin ita ba ta da auren , amma tun da shi kansa bai san wadda na ba shi ba kuma Aleesherh ta ce ba ta son auren , in har Aleenah ta amince sai a yi auren da ita " fadin Al-Sayid ya na kallon Aleenah alamun tambaya dam Aleesherh ta ji zuciyarta ta buga ta na kallon Aleenah har zaro idanu ta ke haka ita ma kallon Aleesherh ta ke zuciyarta na duka uku uku kar a je Al-Sayid ya dawo da auren kan ta , ta san Aleesherh ba za ta taba yahe mata hakan ba saboda son da ta ke wa Prince a fusace Aleesherh ta mike ta nufi kofar fita da sauri ta fice sai kiran sunanta Al-Sayid da Sayida Ahlame su ke amma ina ba ta jin su sai da ta fita sannan Al-Sayid ya kalli Aleenah ya ce " Aleenah ba ki ba ni amsa ba ? tun da ita ba ta so sai na aura miki shi ? ko ya ki ka gani ? " da sauri Sayida Fadwah ta ce " ba sai ka tambaye ta ba ta amince , na ga kai ne da iko da su ba akasin haka ba " ta fada dan burinta guda a janye maganar auren Aleesherh da Prince , ko wani za ta aura ta fi son ta auri Abdoul-Jalil wanda ke matsayin nephew din ta da sauri Aleenah ta ce " no , Daddy wlh ba na so , ba na so " ta fada kamar za ta yi kuka wata yar karamar dariya Al-Sayid ya yi kafin ya ce " kontar da hankalinki , ni dama wassa na ke miki , na riga da na ba shi Aleesherh ba zan sauya ba ko da ba ta son shi sai an yi auren " wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke har sai da ta lumshe idanunta kafin ta mike tsaye ta na fadin " Daddy na koshi " " shikenan " Al-Sayid ya fada a takaice , da ga haka ta sa kafa ta bar wajen ta bi bayan Aleesherh sai da ta fita sannan Al-Sayid ya ce wa Sayida Ahlame " Za ki iya tafiya ke ma ! " ba musu ta tashi ta yi musu sallama sannan ta tafi ya rage da ga shi sai Sayida Fadwah cikin nitsuwa ya ce mata " Fadwah , ban san me ki ke nufi da maganarki ba , amma zan so ki sani Auren Aleesherh da prince ba abun da zai hana shi , na sani Abdoul-Jalil kamar d'a ya ke a gare ki kuma na ji dadi da har ki ka nema mishi auren Aleesherh , to Allah ya yi Aleesherh matar Prince ce , da kin yi min wannan maganar tun da farko da sai na ba shi ita , amma na riga da na bawa Prince , amma in har ya na son Aleenah ni ba ni da matsala zan ba shi auren ta " " zan iya tafiya ? " ta fada cikin sanyin murya gyada mata kai kawai ya yi dan ya san halinta in ba ta son abu to shikenan ba za ta so shi ba har abada a hankali ta tashi ta fice parlourn ta bar shi nan zaune ▪ALEENAH 💕 bayan ta baro parlourn Al-Sayid kai tsaye part din su ta koma ta na shiga ta ga Aleesherh konce tsakiyar gadon ta yi rub da ciki karasowa ta yi ta zauna bakin gadon ta na fadin " Alee , in har da gaske ki na son shi ya kamata ki fito ki fada masa wannan shan tsami da ki ke mishi ba shi ne solution ba , yanzu ba dan Daddy wassa ya ke mana ba da yanzu ya fasa aura miki shi " shiru Aleesherh ta yi ba ta ce mata komai ba ganin ba ta amsa mata ba kawai sai ta daga kafadunta ta tashi ta koma saman sofa ta zauna ta na kallon ta ▪MISALIN KARFE 8 NA DARE ▪PRINCE zaune ya ke cikin part din su ya na sanye da wasu pajama white color , da laptop saman cinyoyinshi ya na aiki Junior na konce gefensa ya na rike da wayarsa ya na latsawa su na a haka wani dogari ya iso wajen ya na yi musu knocking a hankali Junior ya sauko da ga saman gadon ya nufi kofar ya na rike da wayarsa ya na isowa ya bude kofar cikin girmamawa dogarin ya ce mishi " ina mika sakon gaisuwata ga shugaban , Gimbiya Aleesherh ta aiko da sako zuwa ga Prince " ya fada ya na mika mishi wata paper da duka hannayansa biyu hannu Junior ya kai ya karba ya na yi mishi godiya kafin ya juya ya dawo dakin ya na bude paper din ya fara karanto abun da ke ciki sai da ya gama sannan ya saki wani dan karamin murmushi ya na fadin " Prince , babynka ta shirya maka diner a garden " wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " wane baby ? ni babu in da zan je kuma sanyi na ji " da sauri Junior ya nufi dressing room ya shiga jim kadan ya fito rike da wata jacket white color ya karaso wajen Prince ya mika mishi ya na fadin " ko wane problem ya na da solution , dan haka malam tashi ka tafi wajen madam ta shirya maka abinci " marairaice mishi fuska Prince ya yi ya na fadin " please kyale ni , wlh sanyi na ke ji , kuma ka san cikin sauki zazzabi ke kama ni in ina jin sanyi " " wlh ko ka tashi ka tafi ko na kira uncle na hada maka karya da gaskiya , kuma ka fi kowa sanin halinsa dan haka tashi ka tafi , it is just for ten minutes , ba ka san awa nawa ta share ta na shirya maka abincin nan ba , kuma ka ce ba ka zuwa , ka yi mata adalci ? " tsaki Prince ya ja kafin ya sauko da ga saman gadon ya karbi jacket din ya saka , ko sannu bai ce wa Junior ba ya sa kafa ya fice bushewa da dariya Junior ya yi kafin ya zauna wajen da ya tashi ya dauki laptop din ya ci gaba da aikinsa Prince kuwa, kai tsaye hanyar garden ya nufa tun da ya shigo ya fara hango ta zauna saman chair ta na rike da wayarta ta na latsawa , gabanta wata table shinfide da wani farin tissu , table din ta na cike da abinci , da fruits da juice wajen ya na zagaye da lamps white color ma su mugun kyau , wajen dai ya yi tsab kamar so romantic da sallama a bakinsa ya iso wajen hannayansa na cikin aljihun jacket ba tare da ta dago kai ba ta amsa mishi sallamarsa ta ce mishi " sannu da zuwa , bismillah " ta kai karshen ta na ajiye wayarta ba musu ya zauna ya zuba mata ido ba tare da ya ce komai ba " what ? bari min irin wannan kallon ni ma matsa min a ka yi na shirya maka abincin nan " " kenan ba da son kanki ki ya yi wannan abun ba ? " ya tambaye ta sai da ta dauki lokaci kafin ta ce " Eh , why zan dauki lokaci kan wanda bai damu ba ? na fada maka ? ni wlh auren nan matsa min kawai a ka yi na yi shi ba dan haka ba ni zuciyata na da wanda ta ke so " dan tabe baki ya yi kafin ya ce " do you know what's love ? " sai da ta saki murmushi sannan ta ce " no , ban san minene so ba , a kansa na san minene so , ni mutunce mai karancin yarda da mutum ko a school Aleenah ce kadai friend's di ta , amma shi , tun lokacin da idanuna su ka sauka cikin nashi na ke jin kamar na mallaka mishi rayuwata baki daya , shi ne namiji na farko da zuciyata ta amince da shi , duk abun da ya ke burge ni ya ke da ga yanayin maganarsa har zuwa Tafiyarsa komai burge ni ya ke , ni kaina ban san ya a ka yi na kamu da son shi haka ba , na yi kokarin fada mishi abun da ke cikin zuciyata amma ya nuna min ya fi karfin soyayyata " ta qarashe maganar ta na daukar plate ta fara serving din sa shi dai ya yi zaune ya zuba mata ido ya ma rasa abun da zai ce , da ga gani ta na fama da soyayya amma ko wane ? kenan shi ya sa ta ke ja da baya da shi akwai wanda ta ke so , in haka ya kamata ta yi wa Al-Sayid magana kar a aura mata wanda ba ta so sai da ta gama serving din sa ta ajiye mishi plate din gabansa sannan ta dauki wayarta ta fara latsawa bai fara cin abincin ba , ya ce mata " me ya sa ba za ki fada wa Al-Sayid ba akwai wanda ki ke so ? " " na fada mishi , ya ce min na kawo shi ya gan shi , da na je fada mishi abun da ke cikin zuciyata ya koro ni , na koma na tarda ya bar garin ma , that's why ma na hakura " https://chat.whatsapp.com/DWOwxaJuwFcGR1BPqBgf0s _______________________________________________ [ FREE PAGE ___ 13 🕊👑❤ ] jin abun da ta ce ya tuno mishi abun da ya faru lokacin da ta je bedroom din sa a hotel ta na ce mishi ya saurare ta amma ya ki ji , har ya kore ta a fusace , ba dai shi ta ke so ba ? ya tambayi kansa cikin nitsuwa ya ce mata " zan iya sanin ko wanene wanda ki ke so ? " wata yar karamar dariya ta yi ba tare da ta kalle shi ba ta ce " in na fada maka za ka sa ya so ni ne ? ko in na fada maka zai sauya gaskiyar da ba ya so na ? na fada maka ko kar na fada maka duk ba abun da zai anfanar " bai ce mata komai ya fiddo hannu da ga cikin aljihun jacket din sa , ya dauki spoon ya fara cin abincin ta na ganin ya fara ci ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayarta gefe , amma kafin ta ajiye sai da ta saka musu music irin slow music haka sannan ta ajiye wayar , ta yi serving kanta ita ma ta fara ci cikin nitsuwa ta yi nisa duniyar tunaninta ta dago kai a hankali ta kalle shi , nan ta ga hannunsa sai rawa ya ke da kyair ma ya ke iya rike spoon din ta na shirin magana ta ga ya saki spoon din , ya kankame kansa waje guda da sauri ta mike ta nufe shi ta na fadin " are you okay ? ba dai allergy gare ka ba ? " a rarrabe ya ce mata " no , sanyi na ke ji ? " " sanyi kuma ? to ai nan ba wani sanyi a ke yi ba , ko dai ba ka da lafiya ? " ta kai karshen ta na kai hannu saman kumatunsa nan ta ji jikinsa ya yi mugun zafi har sai da ta janye shi da sauri a rude ta ce mishi " ka san ba ka da lafiya me ya sa ka taho , ai sai ka min text ka ce ba ka da lafiya zan gane " " na san kin dauki lokaci wajen shirya wannan abun , in ban zo ba , ba za ki ji dadi ba " maganarsa ba karamin dadi ta yi mata ba cikin zuciyarta , hakan na nufin ya damu da ita ? dafa shoulder din sa ta yi ta na fadin " shikenan , tashi mu koma ciki ka konta " kassa amsa mata ya yi kawai mikewa tsaye ya yi a hankali ya na dafa table , har rawar jiki ya ke riko hannunsa ta yi ta taimaka mishi su ka koma cikin kai tsaye part din su ta meda shi , Junior na ganin su ya yi sauri ya mike ya na fadin " Prince , me ya faru ? " Aleesherh ce ta amsa mishi da cewa " sanyi ya ce ya ke ji , kuma jikinsa ya yi zafi sosai " " i'm sorry " ya fada ya na riko hannun Prince ya taimaka mishi ya konta saman gadon ya janyo duvet ya rufe shi har zuwa wuya dama shi ya tafi ya kwatantawa Aleesherh ba zai iya zuwa ba , cikin sauki sanyi ke kama shi a hankali ta karaso ta tsaya bakin gadon ta na fadin " bari na hada maka hot chocolate , za ka ji sauki da ga baya " girgiza mata kai ya yi ya na fadin " no , kar ki damu kanki , na gode " ya na gama fadar haka ya janyo duvet din ya rufe jikinsa baki daya ya konta saman shoulder cikin sanyin murya Junior ya ce mata " don't worry , nan da five minutes zai dawo dai'dai , za ki iya tafiya dare ya yi , sai da safe " a sanyaye ta ce mishi " sai da safe " da ga haka ta juya ta fice sai da ta fita sannan Prince ya fiddo kansa ya na kallon Junior ya ce " duk laifinka ne , sai ka tafi ka kawo lemon " bushewa da dariya Junior ya yi kafin ya zagayo daya gefen ya konta ya na fadin " ya a ka yi ma ku karaso nan da sauri haka , na zata sai ka zuba mata love sannan ku dawo " tsaki kawai Prince ya yi kafin ya meda kansa cikin duvet din har ya fara nadamar bin maganar Junior ya tilla ▪ALEESHERH 👑💞 bayan ta baro part din su Prince kai tsaye part din su ta koma ta na sakin murmushi ita kadai ta na shigowa ta tardo Aleenah konce saman gadonsu sanye da wata yar karamar rigar barcinta pink color karasowa Aleesherh ta yi cikin dakin ta nufi toilet ta shiga ta yi wanka, Sannan ta fito ta shirya ita ma cikin irin rigar barci irin ta Aleenah amma ita white color ta karaso bakin gadon ta konta gefen yar uwarta ta na fadin " Aleen , barci ki ke ? " " No " ta fada a takaice wani dan karamin murmushi Aleesherh ta sakin mishi mata kafin ta ce " kin san wani ? yau Prince ya nuna min ya damu da ni shi ma , da ga yanzu ki ma zan nuna mishi na damu da shi ,may be da ga haka har ya fara so na " shiru Aleenah ta yi ba ta ce mata komai ba ta zuba mata ido kallon ta Aleesherh ta yi ta na fadin " lafiya ki ka yi shiru ? ko ke ma ba ki da lafiya ? , na lura kwana biyu duk yanayin ya yi sanyi " " Alee , na san ki na farinciki da wannan auren za ki auri wanda zuciyarki ke so , kuma ina farinciki da hakan sosai ma , just ina tunanin abun da zai faru in a ka yi aurenku , hakan na nufin za ki tafi ki bar ni , ban san ya zan yi ba in ba ki nan " ta kai karshen kamar za ta yi kuka nan take Aleesherh ta ji jikinta ya yi sanyi , ita duk ta manta da wannan maganar , yanzu in a ka yi auren dole ta rabu da Aleen din ta , ba ta san ma in za su sake haduwa in ta koma Saudiya da sauri ta matso ta rungume ta dan ba ta da abun da za ta ce mata ta ji sanyi cikin zuciyata , ita kanta zafin rabuwarsu ta ke ji cikin zuciyarta sannu sannu har barci ya yi gaba da su a haka ____________________________________________________________ WASHE GARI ⛅ Tsaye ta bakin kofar part din su Prince , ta na rike da tray din breakfast din su sai knocking ta ke amma ba su bude mata ba har ta fidda rai kawai ta ga an bude mata kofar sai ta ga Junior ne tsaye ya shirya cikin suit black color wani dan karamin murmushi ya sakin mata kafin ya ce " Sorry , ina saka kaya ne , barka da safya " " Good morning , na kawo muku breakfast ne " ta fada ta na mika musu tray din hannu ya kai karba ya na mata godiya ya juya ya koma cikin dakin a hankali ta biyo bayansa ta na fadin " ya jikinsa ? " " tun da har kin zo nan , me zai hana ki duba shi da kanki ? kin ga ni yanzu fita zan yi , na bar miki amanarsa , ki kula da shi please , amma sai kin yi hakuri wlh kamar baby ya ke in ba ya jin jikinsa " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " zan gwada " dariya shi ma ya yi kafin ya fice part din sai da ya fita sannan ta tako a hankali ta tsaya bakin gadon , ta kai hannu a hankali ta janye duvet din jikinsa, har yanzu ya na sanye da jacket din sa ta jiya wata doguwar mika ya yi ya na daga hannayansa, kafin ya juya, murya a disashe ya ce " Cutie , ki kyale ni barci na ke ji " wani dan karamin murmushi ta saki ta na kallon shi gaskiya ba karamin tafiya da ita ya yi ba , specially ma sunan Cutien da ya ce , ga wata sanyayar Muryarsa cen kassan makoshi , yanzu kenan haka kullum za ta dinga tashi da wannan zazzakar Muryarsa ? gaskiya ya kamata ta shawo kansa kafin a yi auren hannu ta kai a hankali ta dan bubuga shoulder din sa ta na fadin " wake up safiya ta yi " wani dan karamin kukan kura ya yi kafin ya zabura ya mike tsaye saman gadon lokaci guda har sai da ta firgita ta na ja da baya sai da ya dauki lokaci a tsaye kafin ya diro da ga saman gadon ya na kallon ta ya ce " coffee " da hannu ta nuna mishi table dan ba ta da bakin magana a hankali ya juya ya fara takawa ya nufi sofa , ya zauna ya janyo table din gabansa ya dauki mug din coffee ya fara sha ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara takawa ta fice part din ta bar shi nan ya na shan coffeen sai da ya shanye coffeen nan sannan ya tashi ya shiga toilet jim kadan ya fito sanye da bathrobe ya wuce dressing room ya shirya cikin suit white color , ya dauki wayoyinsa da laptop din sa ya fice , kai tsaye Daular ya baro baki daya ▪MASARAUTAR SAUDIYA 👑🔥 ▪INAYA 👑🕊 kamar dai kullum yau ma ta na a parlourn MALIKAT INAS , yau dai Malik ya raka Diya Fada Faaz da RIANNA kuma su na zaune a kassa saman carpet ta na rike da book ta na koya mishi karatu dan jiya ma sai da ta kira wata prof din ta koya mishi amma ta tsere ba ta ma ce musu komai ba MALIKAT INAS kuma ta na zaune ta na kallon su su na a haka su ka jiyo Muryar Princess da karfi ta na kwallawa MALIKAT INAS kira a tare duk su ka juya su na kallon kofar shigowa parlourn Inaya har sai da ta ji zuciyarta ta buga shikenan jaraba ta zo kowa ya yi zugum ya na jiran shigowarta da sallama a bakinta ta shigo parlourn ta na fadin " I'm here " da sauri RIANNA ta mike ta nufe ta ta rungume ta tsam ta na dariya mikewa ita ma MALIKAT INAS ta yi ta nufo su ta rungume su dukka biyu dariya Princess ta yi ta na fadin " Ammie , momy , na yi kewar ku sosai " RIANNA ce ta amsa mata da cewa " Mu haka our Princess , mun yi kewar ki over " " to a sake ni " ta fada cikin shagwaba ba musu su ka sake ta , MALIKAT INAS ta riko hannunta ta na fadin " gaskiya wannan karan a part di na za ki zauna " har ta bude baki za ta yi magana ta jiyo Muryar Faaz ya na fadin " momy , ki kyale ta ki zo ki koya min ni " ya fada cike da shagwaba kare mishi kallo da kyau Princess ta yi kafin ta kwace hannunta da ga cikin na MALIKAT INAS ta karaso gabansa ta tsugunna ta na kallon shi da kyau sai da ta kare mishi kallo sannan ta ce wa RIANNA " momy , wanene wannan kuma ? " sai da ta yi wata yar karamar dariya sannan ta ce " kar ki damu zan fada miki da ga baya " " okay " ta fada a takaice kafin ta kai hannu ta murde mishi kunne ta na fadin " saurare ni da kyau , a nan gidan ni ce baby , in har na kama ka ka na yi wa momyna shirme da shagwaba , sai na sa an cire maka kai , ka ji ni ko ? " kuka ya sakin mata ya na fadin " sake min kunnena , momy ta sake min kunne " da karfi Princess ta ce " yi min shiru ko na mare ka a wajen nan ! " ta fada ta na matse gera alamun ba wassa ai ba shiri ya shanye kukansa ya na kallon ta " Princess , na san halinki ba ki da kirki , please kyale shi , me kuma ya yi miki ? " RIANNA ta fada ta na karasowa wajen su , ta kwace kunnen Faaz da ga cikin hannun Princess , da sauri Faaz ya mike ya fada jikinta ya na kuka mikewa tsaye Princess ta yi ta na fadin " ki kyale ni momy na koya mishi zama , tun da na zo yanzu , zan gyara wa kowa zaman sa a masarautar nan " " sannu to , ke kuma a wa , za ki wuce ciki ko sai na tashi gare ki ? " Inaya ta fada ta na tsare da ta idanu turo dan karamin bakinta ta yi ta na fadin " ni ai ba wajen ki na zo ba , ki kyale ni , kuma ina Daddyna ya ke , ina son ganin sa " " Daddynki ya na fada , ki yi hakuri zai zo har nan ya gan ki

Chapter 11 of 23