Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
momy ki kyale ni na koya mishi zama , na ga alamun ya na neman ya wuce gona sa iri , nan ba gidansu ba ne bare ya ce abun da ya ke so za a yi , har ya isa ya ce min ina zan zauna " kwace Faaz ta yi da ga hannun Princess ta na fadin " ke dai ba ki da kirki , Faaz let's go , kyale ta " ta fada ta na jan Faaz su ka koma cikin corridor din wani dan karamin tsaki Princess ta ja kafin ta koma ta zauna , ta dauki wayarta ta fara latsawa ta na zama Junior ya shigo ya na sallama with a smile on her face ta amsa mishi , ta na fadin " Junior , yau ina ka shiga tun safe sai yanzu na gan ka ? " murmushi shi ma ya saki kafin ya karaso gefenta ya zauna gefenta , sannan ya ce " Lafiya ki na nema ta ? ko kin yi kewa ta ? " " Yeah " ta fada ta na wata yar karamar dariya dariya shi ma ya yi kafin ya ce " mu tafi shopping bayan sallar isha ? " noke mishi kafada ta yi kafin ta ce " No , ni dai na fi son ice cream , amma Cutie ta ce na daina shan ice cream cikin dare , zai sa ni ciwo " " shikenan , mu tafi garden mu yi hira , ko kin fi son zama nan ke kadai ? " ya kai karshen ya na mika mata hannu murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta daura hannunta saman nashi , su ka mike tsaye su ka baro part din Allah ya sani bai san me ya sa duk lokacin da su ke tare ya ke jin wani bakon yanayi cikin zuciyarsa , ya san da wuya ta gane abun da ya sa ya ke wadanan abubuwan , kuma ba lalle ba ne ta kamu da son shi saboda kallon dan uwa ta ke mishi , amma zai ci gaba da nuna mata so ko watarana za ta amince mishi tun da aure bai haramta tsakanin su ba ▪PRINCE 👑 MISALIN KARFE 12 NA DARE zaune ya ke cikin parlournsa sanye da kayan barci ash color , da laptop saman laps din sa ya na zaune a haka ya fara jiyo takunta a hankali ta fito corridor slowly ya dago kai ya kalle ta ta na sanye da wata yar karamar rigar barci pink color kamar yar baby doll haka , amma wannan simple ce ba ta da wani ado santala santalan cinyoyinta na waje , ta saki gashin kanta a baya ta na tafe ta na latsa wayarta tun da ta fara takowa ya tsare ta da ido babu ko kiftawa , ita ko , ko ta kansa ba ta yi ba ta nufi hanyar fita parlourn ta fice ya so ya taro ta amma ya ji harshensa ya yi mishi nauyi ya kassa cewa komai har ta sa kafa ta fita wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo ya ci gaba da aikinsa after some minutes ta dawo parlourn rike da wani plate da fruits a ciki , ta na rike da fork ta na ci cikin nitsuwa , har ta karaso gefensa dan nesa kadan ta zauna sai da ta zauna sannan ta mika mishi plate din ta na fadin " za ka sha ? " girgiza mata kai kawai ya yi ba tare da ya kalle ta ba dan daga kafadu ta yi alamun ba ta damu ba ta ci gaba da shan fruits din ta sai da ta kammala sannan ta tashi ta ajiye plate din saman dining table , ta nufi corridor ta shiga ta koma bedroom din ta , ta haye saman gadonta ta konta , ba jimawa barci ya yi gaba da ita shi kuwa , aikinsa ya ke cikin konciyar hankali har zuwa karfe 1 sannan ya tashi ya koma bedroom din sa ya konta ▪AFTER SOME DAYS da wassa wassa lokaci na tafiya har su ka share wajen sati guda a haka , yanzu Aleesherh ta daina sake mishi kamar da farko , kullum ta na cikin bedroom din ta ta na konce rike da waya , tun bai fara nuna damuwa a kai ba har ya fara nunawa ya na tambayar ta in ba ta da lafiya , amma ta ce mishi lafiyarta qlau , ba dan ya so ba ya shanye abun sa lokacin da Malik ya fada mishi za su tafi honey moon bai ce mishi komai ba dan shi kansa ya san ya bukatar hutu a yanzu , ko ba komai zai samu ya dan huta maganar Malik da Inaya kuma , har yanzu ba su sake komawa wajen duwatsun nan ba , kuma ba wanda su ka fadawa abun da ya faru Princess da Junior kuma kullum sun tafi shan ice cream ko shopping , ko su na garden su na hira Aleenah kuma , yanzu ta fara sakin jiki su na hira da Rianna , har ma da Princess , musaman da ya ke ta fi Prince sakin jiki , nan take su ka saba , su na hira kamar wasu friends , har shopping ta taba kai ta , tare da Azmat , duk da ba kullum ta ke zama ba , kullum ta na school , Malik kuwa ya yanke shawarar bayan dawowar Aleesherh za su koma school ita da Aleenah Ranar Friday , Prince da Aleesherh su ka tafi Honey Moon din su , ba Aleesherh kadai ba har shi kansa Prince sai da ya yi mamakin irin wajen da Malik ya kawo su , ya yi mamakin irin dukiyar da mahaifinsa ya kashe wajen sayen wajen nan , har wajen gina gidan da za su sauka , dan ba karamin gida ne ba , duk wall din sa na zallar glass ne abun har mamaki ya ban , sai dai wani shirme da ya yi musu , duk irin girman gidan bedroom guda ce a ciki , floor na kassa duk parlour ne da kitchen da dining room , sai wani balcony bakin ruwa , floor na biyu kuma bedroom din ce baki daya ▪ISLAND OF THAILAND 🏝 MISALIN KARFE 4 NA YAMMA ⛅ ▪ALEESHERH 👑💞 zaune ta ke a balcony saman wata lounge chair , da ga ita sai bra da wani dan wando kamar pant pink color , ta lumshe idanunta , wayarta na saman wata yar karamar table gefenta Music na tashi , da plate din fruits ta na a haka ta ji kamar inuwar mutum a gabanta ya tare mata rana , slowly ta ware idanunta , ba su sauka ko ina ba sai saman shi , ya na tsaye gabanta da ga shi sai short , ya daure gashinsa a baya , yanzu ya dawo black din sa kamar da farko a hankali ta gyara zamanta ta kai hannu ta dauki wayarta ta kashe Music din sannan ta kalle shi ta ce " me ya faru ka yi tsaye gabana ? ko wani abu ka ke bukata ? " " Yeah , ina son magana da ke " ya fada a sanyaye kafin ya fara takawa ya koma cikin gidan a hankali ta mike tsaye ta bi bayansa su ka koma cikin gidan , a nan parlourn ta gan shi zaune ya sunkuyar da kai a hankali ta karaso gefensa ta zauna ta na ce mishi " me ya faru ? " dago kai ya yi slowly ya kalle ta , cikin sanyin murya ya ce " Eesherh , please in wani abu na yi miki ki fada min , tun lokacin da mu ke Saudiya ki ka daina yi min magana , yanzu kwana biyu mu ka yi a nan amma ko so guda ba ki min magana ba , wlh ba na jin dadin hakan cikin zuciyata , in laifi na yi miki ki fada min na ba ki hakuri " wani dan karamin murmushi ta saki , tarkonta ya yi kamu , dama Inaya ta ba ta wannan shawarar na ta kyale shi ta daina kula shi , ta san halin yaronta , kuma ta tanka dai'dai ga shi yanzu da kansa ya yi mata magana hannu ta daura saman nashi ta ce " ni ba ka yi min komai ba , ba kai ka ce ba ka son hayaniya ba , shi ne kawai na daina takura maka " riko hannunta ya yi cikin nashi , ya dago a hankali ya manna mishi kiss ya na fadin " i'm sorry , ni ban ce kin takura min ba , just ban saba zama da mutane ba ne , amma zan koya ko dan saboda ke " " da gaske ? " ta fada ta na sakin wani dan karamin murmushi gyada mata kai kawai ya yi alamun Eh wata yar karamar dariya ta yi kafin ta matso ta rungume shi a hankali ya zagayo da hannayansa a bayanta ya rungume ta shi ma , ga shi ko ba wasu kayan kirki ne ba a jikinta , lokacin da hannayansa su ka sauka saman lalawsar fatar jikinta ba karamin shock ya ji ba , har mikewa gashin jikinsa ya yi , nan take ya ci gaba da shafa bayanta wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake shi a hankali ta dago da ga jikinsa amma har yanzu bai sake ta ba wani dan karamin murmushin gefen fuska ta yi kafin ta ce " sake ni na koma balcony " bai ce mata komai ba ya matso a hankali ya kai lips din sa saman nata ya manna mata kiss dan shi kadai ne abun da ke yawo a brain din sa a wannan lokacin ita kuwa ta na jin saukar lips din sa saman nata ta ji zuciyarta ta yi wata wawar bugawa ta na zaro idanu ba ta gama shan mamaki ba sai da ta ji tongue din sa cikin bakinta ya na neman cabko tongue din ta , ya fara tsotsayar tongue din ta kamar ya samu sweet ita dai ta yi zugum ta zuba mishi ido , ya lumshe idanunsa , duk ta ji ta kassa wani kwakwaran motsi sai da ya yi wajen five minutes rike da ita a haka kafin ta ji ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya sannan ya saki tongue din ta , a hankali ya zame bakinsa da ga cikin nata , sannan ya ware idanunsa a hankali , kai tsaye cikin nata su ka sauka a hankali ya janye hannayansa da ga bayanta , a sanyaye ya ce " i'm sorry , ban san me ya shige ni na yi hakan ba " gyada mishi kai kawai ta yi kafin ta mike tsaye a hankali ta ke takawa har ta koma balcony , saman lounge chair din ta , ta zauna ta saka Music ta saki wani cool murmushi ta ci gaba da shan iskanta , ranta fari kal kamar an yi mata albishir da gidan Aljannah ❤⚘ 𝐍𝐀𝐘𝐄𝐋⚘❤ THE BIGINING 🕊👑❤ ❤👑 𝑴𝑨𝑳𝑳𝑨𝑲𝑰𝑵 𝑴𝑬𝑬𝑹𝑨𝑯 ❤🕊 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i _______________________________________________ _ PAID BOOK *WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , ₦500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ƊIN* _______________________________________________ [ FREE PAGE ___ 23 🕊👑❤ ] ☆ ISLAND OF THAILAND 🏝 ☆ ▪PRINCE 👑🔥 kwance ya ke tsakiyar bed ɗinsu , da ga shi sai short ya zubawa ceiling ido kamar mai tunanin wani abu ya na kwance a haka Aleesherh ta fito da ga cikin toilet sanye da bathrobe sai da ta karaso wajen dressing mirror za ta shafa lotion ɗinta sannan ta lura da shi ta cikin mirror slowly ta juyo ta kalle shi da alamun akwai abun da ke damun sa takawa ta yi a hankali ta zauna bakin gadon , ta yarfa mishi ruwan gashinta da sauri ya rumtse idanunsa ya sake bude su a hankali ya na kallon ta daga mishi gera ta yi ta na faɗin " tunanin me ka ke yi haka ? Allah ya sa dai ba tunanin Tsohuwar girlfriend ɗinka ka ke ba " ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo ya kalle ta ya ce " no , just ba na jin jikina , like something na faruwa a gida " " yaushe za mu koma gida ? , ni ma ina kewar Aleenah " " har kin gaji da zama nan da ni ? " ya faɗa ya na miƙewa zaune sai da ta girgiza mishi kai ta na murmushi ta ce " na ga abun da za mu yi a nan mu na iya yin sa a cen , kai ma na san ka na son ka koma ka ji wane hali su momy su ke ciki " " haka ne , ina ji a jikina kamar wani mugun abu na faruwa , ina fatan tunanina ne kawai ba abun da ya faru " " in sha Allah ba abun da zai faru ma , yanzu tashi ka shirya mana breakfast , gaskiya yau kai za ka yi mana " ta kai karshen cikin ƴar shagwaba " ki fara ba ni nawa breakfast sai na je na shirya miki naki " ya faɗa ya na daga mata gera guda da sauri ta tashi da ga saman gadon ta na faɗin " no , yau dai sai ka yi azumi " ta faɗa ta na juyawa za ta bar wajen da sauri ya riko hannunta ya janyo ta , ta faɗo saman gadon , da sauri ya juya ya yi mata runfa da kirjinsa " kin dauƙa za ki iya tsere min ? " ya faɗa ƙassa ƙassa marairaice mishi fuska ta yi ta ce " haba baby , na gaji wlh ka bari na ɗan huta , jikina duk ciwo ya ke min " " zan yi miki tausa " " no , ba na so , haka jiya ma ka ce za ka yi min tausa amma ka danne ni , sai da na gaji da yi maka magiya ka kyale ni " " shikenan , na ga ai Honey moon mu ka zo , kuma gobe za mu koma Saudiya , ki bari na yi na karshe mana " " bari har zuwa dare , zai fi dadi , please baby " ta faɗa cike da shagwaba a hankali ya sunkuyo ya manna mata kiss a forehead da kumatu sannan ya sauka da ga saman ta ya na faɗin " Je ki shirya zan kawo miki breakfast ɗinki Gimbiyata " wani cool murmushi ta saki kafin ta mike zaune ta zuba mishi ido har ya baro bedroom ɗin Sannan ta tashi ta shiga dressing room shiryawa ta yi cikin kananan kaya pink color ta karaso ta zauna gaban dressing mirror ta fara shafa lotion ɗinta ta na zaune a haka ya dawo cikin bedroom din , rike da wani tray ya shirya mata breakfast maimakon ya ajiye saman table sai ya ajiye saman dressing mirror a gabanta , ya tsaya a bayanta ya na kallon su ta cikin mirror wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta ce " lafiya ka ke min irin wannan kallon ? " " nothing , just you look so beautiful " " no , we look perfect " " perfect ? " " yeah , we are perfect , ko ba ka gani ba ne ? sai ma mun samu Baby , ma su kama da kai " " ina fatan hakan ta kasance " ya faɗa ya na juyawa ya koma bakin gadon ya zauna ya zuba mata ido ta na nan zaune a gaban dressing mirror ta fara cin breakfast ɗin ta na ce mishi " Honey , yanzu in mu ka samu baby wani suna ka ke son mu saka mishi ? " sai da ya ja lokaci kafin ya bude baki a hankali ya ce " Nayab " " wow , sunan ya na da dadi " " yeah , sunan Little brother ɗina ne " da sauri ta juyo ta na kallon shi , ita dai duk zaman da ta yi a Saudiya ko so guda ba ta ji an kira wani da Nayab ba , kuma bayan Princess ba ta ga wani mai kama da shi , dan in har little brother ɗinsa ne kamar yadda ya Ce tabbas sai ya yi kama da shi ko da ta jini ce a sanyaye ta ce mishi " amma ba cikin masarautar ya ke ba ko ? " girgiza mata kai ya yi a hankali sannan ya ce " he is die tun lokacin da mu ka shigo duniya , na so na tasso tare da shi , mu yi karatu tare , mu yi wassa da dariya , ina tunanin ya rayuwata za ta kasance in da yanzu ya na raye " ba karamin sanyi jikinta ya yi ba jin abun da ya ce ga shi ko yanayinsa duk ya yi sanyi , a hankali ta mike ta karaso gefensa ta zauna ta kontar da kanta saman shoulder din sa , a sanyaye ta ce " i'm sorry my baby " zagayo da hannayansa ya yi a bayanta ya rungume ta ya na sauke ajiyar zuciya mai nauyi a takaice haka su ka share yinin ranar manne da junansu , ta na zuba mishi kalaman soyayya da shagwaba , shi kuma ya na biye mata , har dare ya tardo su a haka , da ga nan kuma labarin ya sauya , ni dai ina gefe ina kallon su dan al'amarin nasu ya fi karfina , da alamun shi ma Prince ya gado Malik dan dare su ka bi su na aiki guda har barci ya dauke ni su na kan aiki washe gari misalin karfe 10 na safe Helicopter ya zo daukar su , sai da su ka rufe gidan da kayan abincin da su ka zo da su dan kar su baci , su ka gyara komai yadda su ka tardo shi sannan su ka baro Island din ☆ MASARAUTAR SAUDIYA 👑🔥 ☆ yau dai masarautar duk cikin grief su ke , mutuwar MALIKAT INAS ba karamin girgiza masarautar ya yi ba , duk wata masarautar da ke karkashin Saudiya sai da Sarkinta ya turowa Malik sakon gaisuwa , har da Al-Sayid Malik dai tun lokacin da a ka yi jana'izar MALIKAT INAS , a ka kai ta gidanta na gaskiya , ya juya ya koma part din sa , a floor na hudu ya wuce dan kar a takura mishi , duk wanda ya zo gaisuwa da ga wajen Diya ya ke tsayawa Inaya kuma ta na part din MALIKAT INAS tare da RIANNA , Tesnim da Nesrine , da Princess , ta na kwance ta tada kai da cinyar Inaya su na zaune ba me ce wa kowa ufan , idanunsu duk sun yi jazir sun kunbura su na zaune a haka Prince da Aleesherh su ka shigo da sallama a bakinsa , ya san a wannan lokacin momynsa na wajen MALIKAT INAS , shi ya sa kawai ya wuto , ga shi ko tun lokacin da ya shigo masarautar ya ke jin zuciyarsa ba dadi , ya wuto nan dan ya tabbatar kowa ya na lafiya Princess na jiyo Muryarsa ta tashi da gudu ta nufe shi ta rungume shi ta na sakin kuka ba karamar faduwa gabansa ya yi ba jin kukanta , musaman yanayin face din da ya ga mutanan wajen da sauri ya ɗago ta da ga jikinsa ya na faɗin " Cutie , momy , Princess , what happened ? me ya faru ? " ya fada hankali a tashe a hankali Inaya ta mike tsaye ta ce wa Aleesherh " Alee , shiga Wajen Leenah " sai da ta juya ta kalli Prince a sanyaye , sannan ta fara takawa ta shiga corridor ɗin ta na shiga Prince ya nufo Inaya ya na faɗin " Cutie , me ya faru wai ? ya na ga duk ku na cikin damuwa ? please ku fada min , hankalina duk ya tashi , tun jiya na ke jin zuciyata wani iri , please ku fada min abun da ke faruwa " Princess ce ta amsa mishi da cewa " Prince , Ammie is die , tun bayan tafiyarku ta kwanta ciwo , jiya kuma ta tafi ta bar mu , Akhie , I miss Her " ta faɗa ta na kuka shi dai Bawan Allah ya yi mutuwar tsaye , shi dama ya ji jikinsa ba lafiya ba , amma bai yi tunanin Ammie ce ba , tun ya na karami ba karamin so ta ke nuna mishi ba , duk ita ta sangarta shi lokacin da ya ke karami har ya ke yi wa Malik jaraba , duk yawancin shawarwarin da ya yanke cikin rayuwarsa da sa hannunta , ko auren nan nashi da Aleesherh , ita ta kwantar mishi da hankali ta ce ya yarda cikin kankanin lokaci zai shaƙu da ita , ga shi ko maganarta ta tabbata , yanzu kuma a ce ta tafi lokaci guda ya yi nisa duniyar tunaninsa ya jiyo Muryar Inaya ta na fadin " Prince , ya kamata ka tafi wajen Daddynka , na san zai ji sanyi idan ya gan ka , ya na Floor na hudu " gyada mata kai kawai ya yi kafin ya juya ya fice ya na taku kamar an zare mishi lakar jiki ya na fita Inaya da Princess su ka koma su ka zauna bangaran Aleesherh kuma kai tsaye bedroom din Aleenah ta wuce ta na yi mata sallama ta na zaune tsakiyar gadon idanunta sun yi jazir da alamun kuka ta sha cikin rudu Aleesherh ta karaso wajenta ta na fadin " Aleen , lafiya na ga idanunki sun yi ja haka ? " ta kai karshen ta na zama bakin gadon wani dan karamin murmushi Aleenah ta saki kafin ta ce " Amarya , sai yau ki ka yi niyar dawowa " " please Aleenah , ki ba ni amsar tambayata , me ya faru ne ? na ga kowa yanayinsa kamar sun yi kuka " " Kakar mijinki ce ta rasu Jiya " " innallillahi wa'ina illaihi raji'un " Aleesherh ta faɗa a dan razane ta na zaro idanu shi ya sa ta ga duk mutanan wajen sun yi sanyi , kamar an aiko musu sakon mutuwa ashe mutuwar ce a ka yi , ta san yanzu Prince ɗinta ya na cen cikin wani hali dan ya faɗa mata yadda ya ke son Ammiensa , ta so ta na kusa da shi ta kwantar mishi da hankali a hankali ta kwanta ta ɗaura kanta saman cinyar Aleenah ta lumshe idanunta wani ɗan karamin murmushi Aleenah ta saki kafin ta kai hannu saman kanta ta fara shafawa a hankali ☆ MALIK 👑 ☆ zaune ya ke tsakiyar gadonsu , ya daura Pillow saman cinyoyinsa , hannayansa na saman pillown , ya zubawa waje guda ido , idanunsa sun yi jazir har sun kunbura da alamun ya sha kuka ko ya sha hawaye a hankali Prince ya turo kofar dakin ya shigo ya na sallama cen ƙassan maƙoshi ko motsi Malik bai yi ba , ko sallamarsa cikin zuciyarsa ya amsa mishi ita , ba ya jin ya na da karfin yin wani motsi a yanzu a hankali ya karaso bakin gadon ya tsaya ya na kallon Malik ya ce " Daddy ? " wata doguwar ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya kauda kai gefe , ya kai hannu ya goge ruwan da su ka tarun mishi a ido sannan ya juyo ya kalli Prince ya saki wani cool murmushi ya ce " ya ? har kun gama honey moon ɗin ? na zata sai na tafi cigiya da kaina " zama ya yi bakin gadon sannan ya ce " ba kai ne ka ba mu One week kaɗai ba , da ma two weeks ka

Chapter 17 of 23