Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , ₦500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ƊIN* *HAR ZUWA RANAR FRIDAY ZAI KASANCE ₦ 300* β€πŸ‘‘ 𝑴𝑨𝑳𝑳𝑨𝑲𝑰𝑡 𝑴𝑬𝑬𝑹𝑨𝑯 β€πŸ•Š https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i _______________________________________________ [ FREE PAGE ___ 26 πŸ•ŠπŸ‘‘β€ ] β˜† SAUDIYA CENTRAL PRISON β˜† β–ͺIZZAT zaune ta ke a waiting room saman chair ta zubawa kofar shigowa ido ta yi wajen five minutes zaune a haka kafin Izayn ya shigo dakin babu ko sallama ta na ganin shi ta mike tsaye ta na fadin " haba don Allah , tun dazu na ke jiran ka " bai ce mata komai ba ya fiddo wata yar karamar bottle da ga cikin aljihunsa da wasu ruwa farare a ciki ya mika mata ya na fadin " sai kin yi hankali wajen aiki da shi " hannu ta kai ta karba ta na fadin " Ba ku fada min abun da zan yi ba " a hankali ya tako dab da ita ya kai bakinsa saitin kunnenta ya fara yi mata rada ( πŸ€”πŸ€” ko me ya ke fada mata , da ga ji ba alkhairi ba ne ) da sauri ta ja da baya ta na girgiza mishi kai ta na fadin " gaskiya ba zan iya ba , a ka je a ka kama ni fa ? " ta fada a dan razane " ba za a kama ki ba , kawai ki san yadda za a yi laifin ya koma kan wani cikin fadar , wanda za a iya kama shi cikin sauki " shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba da alamun tunanin wani abu ta ke yi " ni zan tafi , ki san yadda za ki yi , da ga yanzu kar ki sake dawowa wajena " ya fada ya na juyawa zai fita da sauri ta ce mishi " why ? ba ka son na dinga zuwa ? " a hankali ya tsaya , ba tare da ya juyo ba ya ce " no , Ina son Mai girma Malik ya san da zamana cikin kassar Saudiya , da ga nan kuma ki jira ni a Daular , ba zan jima ba zan fito " ya na gama fadar haka ya fice sai da ta dauki lokaci zaune cikin prison din ta na tunaninta kafin ta baro , ta bi hanyar da ta ke bi kullum ta koma Daular β˜† DAULAR SAUDIYA β˜† β˜† MISALIN KARFE 8 NA DARE β˜† Yau dai duk ahalin Malik sun hadu a part din sa , a floor na uku , yau tare duk za su yi diner , da Diya , Nesrine , Tesnim , Abdoul , Rianna , Princess , Azmat , Aleesherh , Aleenah , har da Faaz , sannan uwa uba Malik da Inaya sai abinci su ke ci su na hirar su gwanin burgewa , musaman Malik ya jima bai tara ahalinsa haka ba su ka yi diner Ita dai Aleesherh ta yi shiru kanta na sunkuye ta na wassa da spoon din ta cikin plate din ta ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Muryar Inaya ta na fadin " Alee , lafiya tun dazu ba abun da ki ka ci sai wassa ki ke da spoon din ? ko ba ki jin jikinki ne ? " girgiza mata kai ta yi a hankali , ta na shirin magana Princess da ke zaune gefen Inaya ta riga ta cewa " Cutie , ba wani ciwo da ta ke , kawai ta na kewar Babynta ne " ta kai karshen ta na wata yar karamar dariya wani dan karamin murmushi Malik ya saki kafin ya ce " to sannu ke kuma , ina laifi dan ta na kewar mijinta , na ga ke ma naki tun da ya tafi bai kira ki ba " da sauri Abdoul ya ce " Malik , Yaushe Princess ta yi miji ba na da labari ? " ya tambaye shi dan shi yanzu duk yawancin abun da ke Faruwa cikin masarautar ba shi da labari saboda yanzu shi office din President ya koma da aiki , Diya kuma ya na a Fada murmushi mai dan sauti Malik ya yi kafin ya ce " ka tambaye ta ga ta nan zaune gefenka " da sauri ta ce " Alee , ba ki fadi abun da ke damun ki ba ? ko ciwo ki ke mu ke na duba ki ? " ta fada dan ta na san kawar da zancen sai da Inaya ta yi wata yar karamar dariya sannan ta ce " Alee , rabu da wannan , fada min me ke damun ki ? " murya a sanyaye ta ce " ni ma ban sani ba momy , tun da yamma nana ke jin gabana na faduwa , kamar wani mugun abu na shirin faruwa " a hankali Malik ya dafa shoulder din ta dan dama a gefen hangunsa ta ke zaune , cikin sanyin murya ya ce mata " ki kontar da hankalinki , ba abun da zai faru " ya na gama rufe bakinsa su ka jiyo wayar Diya ta na ringing a hankali ya mike tsaye ya na fadin " ku ci gaba bari na amsa " da to kawai su ka amsa mishi sh ka ci gaba da cin abincinsu ba wanda ya ce ufan dan Aleesherh ta kashe musu jiki Diya kuma Parlourn ya koma ya zauna , sannan ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ya na sallama cikin nitsuwa a daya bangaran Muryar wani Matashi na jiyo ya amsa mishi sallamarsa kafin ya ci gaba da fadin " Please ina son magana da mai Girma Malik " " Da shi ka ke magana " Diya ya fada sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " Ranka shi dade , na kira ne da ga kassar London a UK , dan sanar da kai Jet din Yarima ya tashi da Bomb , a cikin airport din kassar " " What ? " Diya ya fada da mugun karfi ya na mikewa tsaye har ya saki wayarsa ta fadi kassa nan take hankalin kowa ya dawo kansa , sai innallillahi wa'ina illaihi raji'un ya ke furtawa kassa kassa da sauri Malik ya mike ya nufe shi ya na fadin " Diya ? what happened ? " a rude Diya ya shiga ce mishi " Malik , Jet din su ne Prince ne , ya tashi da Bomb a cikin airport " wata razananiyar kara Aleesherh ta saki ba tare da ta sani ba ta na toshe bakinta da dukka hannayanta biyu da sauri Aleenah ta rungume ta kamar za ta yi kuka ta ce " sai da na ce muku ina ji a jikina wani abu zai faru " " please ku kontar da hankalinku , ba abun da ya faru da Prince , ba su cikin Jet din " fadin Malik a tare duk su ka ce mishi " ba ya cikin Jet din ? ta a ka yi ka sani ? " " sun ce a cikin airport ne , may be ba su kai ga shiga bomb ya tashi da Jet din " ya fada ya na son kontar musu da hankali su na a haka su ka jiyo wayar Aleesherh ta na ringing hannu Aleesherh ta kai saman table ta dauki wayar ta na kallon screen din lambar ta kassar UK ce , kawai sai ta kashe kiran dan a tunaninta dan su ce mata Jet din Prince ya tashi da Bomb ne su ka kira ta ko kuma su ce su na Hospital ta na kashe shi ko wani kiran ya sake shigowa wannan karan ba ta kashe ba , ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na jiran ta ji abun da za a ce mata kawai sai ta jiyo Muryarsa ya na fadin " Yaushe ki ka fara jin tsoro haka ? ba sace ki za a yi ba " da sauri ta mike tsaye ta na fadin " Baby ? ba abun da ya same ka ? " " please kontar da hankalinki , ba abun da ya same ni , please ki kai wa Daddy wayar ina son na yi mishi magana " a hankali ta fara kuka ta na fadin " don Allah ka dawo , kar wani abu ya same ka " " ki fara ba ni Daddy please " ya fada a sanyaye ba musu ta sauko wayar ta nufi Malik ta mika mishi ita , ta na zubar da hawaye hannu ya kai ya karbi wayar sannan ya kai ta a kunne ya na fadin " Prince , ba abun da ya same ka ? ina Junior ? " " ba abun da ya same ni Daddy , just Junior ya samu dan rauni a kansa , bayan haka ba abun da ya same mu " " shikenan Allah ya kara kiyaye gaba , yanzu yaushe za ku dawo " " kun san dai Jet Ι—ina ya tashi da Bomb ko ? sai kun turo mana wani jirgin za mu iya baro kassar " wata yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya ce " shikenan , gobe ina sa Helicopter ya je ya dauko ku " " okay Daddy , sannan please ku kula min da ita ba na son ta saka damuwa a ranta , sai na zo " ya na gama fadar haka ya katse kiran sauko wayarsa Malik ya yi a hankali sannan ya mikawa Aleesherh kayanta ya na fadin " kar ki damu , ba abun da ya same shi , gobe za su dawo , Princess ! please zo ki kai ta bedroom Ι—inki ta kwana a nan gobe sai ta koma part Ι—inta " da to kawai Princess ta amsa mata kafin ta karaso ta riko hannun Aleesherh su ka shiga corridor ta wuce bedroom din ta da ita sai da su ka bar wajen sannan Malik ya kalli sauran mutanan wajen ya da ce " please ku kontar da hankalinku , ba abun da ya same su " da to kawai su ka amsa mishi sannan su ka yi mishi sallama kowane ya tafi part din sa sai da Malik ya kwantar wa Diya hankali ya tabbatar mishi ba abun da ya faru da su , sannan ya raka shi har part din sa su na tattaunawa a kan abun da ya shafi masarautar , akwai wata shawara ta musaman da su ka yanke amma ba za su fadawa kowa ita ba sai an yi arba-in na rasuwar MALIKAT INAS ( ko ma minene mu na jira mu ji 😌😌 ) bayan ya raka shi kai tsaye part din su ya koma , ya wuce bedroom din sa ya na shiga ko ya tardo Inaya zaune bakin gadon ta zubawa kofar shigowar ido da alamun tunanin wani abu ya ke a hankali ya juya ya rufe kofar ya saka mata security , sannan ya tako a hankali ya zauna gefenta sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " ina tunanin mutum guda ne ya yi wannan aikin , wanda ya ke son ganin bayan Prince shi ne ya yi sanadiyar Ammie " wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce " ni ban ma san abun da zan ce a kai ba , duk yadda a ka yi wanda ke mana wannan aikin ya na a tare da mu , in ba haka ba ta ya ya san Prince ya tafi UK , har ma ya na shirin dawowa " " haka ne , yanzu me ki ke so mu yi ? " a hankali ta juyo ta kalle shi , ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " me fa za mu yi ? mu zuba ido mu ga abun da su ke shirin yi mana " wata yar karamar dariya ya yi kafin ya janyo ta jikinsa , sannan ya kwanta ya yi mata runfa da kirjinsa ya na kallon cikin idanunta ya ce " so ki ke na zauna su cutar min da ku ? " " ba abun da za su iya yi , ka manta su wa ke tare da familynka " ta na gama fadar haka na ga idanunta sun sauya kamar juyawar page su ka koma White , sannan su ka dawo dai'dai lokaci guda murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " tun da haka ne abun , yanzu ya za a yi da ni ? yunwa na ke ji My Cutie " hararrar wassa ta yi mishi ta na fadin " tsakani da Allah baby ba yanzu mu ka yi diner ba ? kuma ka ce yunwa ka ke ji ? " " Noooo ! ni fa ba irin wannan yunwar na ke ji ba , tun jiya fa ba ki kula da ni ba , ba dole na ji yunwa ba , yanzu dai ki san yadda za ki yi a kai " bushewa da dariya ta yi kafin ta zagayo da hannayanta a wuyansa kafin ma ta ce wani abu ya toshe mata baki da nasa bakin ya fara yi mata kiss ( πŸšΆβ™€οΈπŸšΆβ™€οΈπŸšΆβ™€οΈ Ni kuma na dauki takarduna na fice , wannan game din ba irin namu ba ne πŸ€£πŸ‘Œ ) β–ͺALEESHERH πŸ‘‘πŸ’ž bayan sun shiga bedroom din Princess , ta zaunar da ita bakin gadonta ta na fadin " zauna, bari na je na hada miki ruwa ki yi wanka " da to kawai Aleesherh ta amsa mata , da ga haka ta juya ta shiga toilet ta na shiga Aleesherh ta dago wayarta , ta shiga kiran layin da Prince ya kira ta da shi dan yanzu Muryarsa kawai ta ke da bukatar ji ko ringing biyu kiran bai yi ba ko ya daga ya na sallama kassa kassa kamar an yi mishi dole wani dan karamin murmushi ta saki ta na sauke ajiyar zuciya a tare kafin ta amsa mishi sallamarsa cikin nitsuwa ya ce mata " har kin kammala diner ? " " Eh baby " ta fada a sanyaye " shikenan , yanzu tashi ki yi wanka sai ki kwanta ki huta " " ba zan iya ba , ni so na ke kawai ka dawo , da yanzu wani abu ya same ka na san ba zan iya jurewa ba " " na sani , that's why ma na kassa shiga jirgin ina na kokarin kiran ki na fada miki za ni dawo , da ba dan ke ba da na san yanzu wata maganar a ke daban , na gode da ki ke cece ni " wata yar karamar dariya ta yi , kafin ta shagwabe fuska kamar ta na gabansa ta ce " na ji shikenan , amma da ga gobe in ka dawo ba zan sake barin ka ka tafi kai kadai ba , kullum tare za mu tafi ko ina ne ma " " okay , I love you my Beautie " " I love you too my Baby " " okay now tafi ki yi barci , sai da safe " , ya na gama fadar haka bai jira amsarta ba ya katse kiran sauko wayar ta yi a hankali ta ajiye saman bedside drawer ta na ajiye ta ko Princess ta ce mata " shikenan ? har kun ida hirar ? ba irin wannan jan ajin ? ki dan ja shi da hira , ki na zuba mishi shagwaba , ki na kiransa da wadanan kananan sunayan like my Angel , My Chocolate , Sweet , Candy , Honey ya ji ba ya son kashe kiran ma ba ki daya kamar ya janyo ki ta cikin wayar ya rungume " wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi kafin ta ce " yanzu wannan da na yi bai isa ba ? " " hmmmm , shiga ki yi wanka ki zo na gwada miki yadda a ke yi Mrs Prince " ta fada ta na karasowa bakin gadon ta zauna ba musu ta tashi ta shiga toilet ta yi wanka ta yi wajen 45 minutes kafin ta fito sanye da bathrobe , a lokacin har Princess ta fiddo mata kayan barcinta ta saka karbar kayan Aleesherh ta yi ta shiga dressing room din ta , ta saka kayan sannan ta fito , nan ta isko Princess zaune tsakiyar gadon ta na rike da wayarta ta na latsawa karasowa ta yi bakin gadon ta zauna ta na fadin " me ki ke yi da wayata ? " murmushi mai dan sauti Princess ta yi kafin ta ce " zuba ido ki ga yadda a ke yi " ba ta ce komai ba ta yi shiru ta zuba mata ido ta na murmushi ta na a haka ta jiyo wayarta ta fara ringing da alamun kira ne ta ke sai dai kiran ya katse ta sake yin wani , wannan karan bai yi ringing biyu ba Prince ya daga ya na sallama amsa mishi sallamar Princess ta yi kafin ta ce " Prince , ka na lafiya ? ba abun da ya same ka ? tun dazu na ke kiran ka sai yanzu za ka dauka ? hankalina har ya fara tashi " cikin nitsuwa ya ce mata " don't worry , na shiga wanka ne , ba abun da ya faru da ni " " and Junior ? please ba shi wayar ina son na yi mishi magana " ta fada ta na marairaice murya da okay kawai ya amsa mata , kafin na ji wajen shiru kamar ya na taku a haka na jiyo Muryar Junior ya na fadin " Hello ! My Princess " wani cool murmushi ta saki ta na fadin " Junior , ba abun da ya same ka ? " " Hmmmm , ki daina kirana da Junior yanzu " " na ji shikenan My Heartbeat , yanzu fada min , ya jikinka ? ba ka ji ciwo ba ? please ka yi sauri ka dawo " ta fada cikin yar shagwaba " uhm , har kin fara kewa ta kenan ? " " ba dole na yi kewa ba , rabin raina ya tafi ya bar ni , tun safe ba abun da na yi kawai ina kwance ina tunanin ka , kuma ka ce ba zan yi kewa ba , yanzu ni dai ka yi saurin dawowa gobe " wata yar dariya ya yi sannan ya ce mata " ni fa ba gobe zan dawo ba , Prince ne kadai zai dawo gobe , ni sai Thursday " " what ? sai jibi ? no gaskiya ban yarda ba , so ka ke a kwantar da ni jinya ? ko yanzu zazzabi na ke sai da Daddy ya ban magani na sha " ta fada cike da shagwaba har da turo dan karamin bakinta dama gwana ce " shikenan , yanzu idan na dawo me za ki shirya min ? " " ka fara dawowa , ba zan rasa abun da zan shirya maka ba , ko da kuwa kaina ne " " Really ? " ya fada cike da zumudi wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " sai da safe ni barci na ke ji " da sauri ya ce mata " no , kar ki kashe , please ki fada min mana , kin san yadda ki ka tayar min da hankali ? , yanzu kin sa dole gobe sai na dawo " " idan ka na son ganin ko minene zan shirya maka , to gobe ka dawo , ina tabbatar maka sai ka mutu ba ka ji irin wannan dadin ba " ta na gama fadar haka ta katse kiran , ta mikawa Aleesherh wayarta kafin ma ta kai hannu ta karba ta ji wani kiran ya shigo cikin nitsuwa Princess ta ce mata " kar ki dauka , duk kiran da za a yi " " why ? " Aleesherh ta tambaye ta ta na meda wayarta saman bedside drawer ja da baya Princess ta yi ta jingina bayanta da forehead din gadon ta ce mata " just dan na yi excited din shi " ta fada ta na daga kafadunta alamun ba ta damu ba ( 🀣🀣🀣 sannu da kokari , ai kam aikinki ya cika , kin samu abun da ki ke so ) *WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , ₦500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ƊIN* *HAR ZUWA RANAR FRIDAY ZAI KASANCE ₦ 300* ❀⚘ ππ€π˜π„π‹βš˜β€ THE BIGINING πŸ•ŠπŸ‘‘β€ β€πŸ‘‘ 𝑴𝑨𝑳𝑳𝑨𝑲𝑰𝑡 𝑴𝑬𝑬𝑹𝑨𝑯 β€πŸ•Š https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i _____________________________________________ [ FREE PAGE ___ 27 πŸ•ŠπŸ‘‘β€ ] cikin rudu Aleesherh ta ce mata " Excited ? you are married ? " " Yessss , we are married , tun lokacin da ku ka tafi honey moon a ka Ι—aura mana aure , ni ma jiya ne Daddy ke faΙ—a min " " Wow , congratulations , i wish you to stay together in love and peace " " na gode , ke ma ina miki fatan hakan , ke da Prince , Allah ya ba babys dayawa " da sauri ta katse ta da cewa " what ? babys dayawa ? no gaskiya , ni da ga Nayab ba zan kara wani babyn ba , da babys Ι—in za na ji ko Daddynsu ? " " Nayab ? ina ki ka jiyo wannan sunan ? " Princess ta tambaye ta a sanyaye " Prince ne ya fada min sunan dan uwanku ne , ya ce min shi ne ke tsakanin ku ke da shi , ina son na dawo mishi da Nayab cikin familynsa , i think shi ne kadai gift din da zan iya yi mishi a wannan duniyar " ta kai karshen ta na Ι—aura hannu saman cikinta " haka ne , Prince ya na son babys sosai , may be dan bai da babyn ne ba ki lura da hakan ba , ina tabbatar miki in har ku ka samu baby ba karamin farinciki zai yi ba " wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta gyara kwanciyarta saman gadon ta na fadin " Good night , barci na ke ji " da okay kawai Princess ta amsa mata kafin ta kashe musu lamps din dakin ta kunna bedside lamps , ba jimawa barci ya yi gaba Aleesherh kuma sai muzurai ta ke da ido ba wani barci da ta ke ji kawai tunanin masoyinta ne ya hana ta sukuni misalin karfe 12 na dare haka , ta yi nisa duniyar tunaninta kawai ta fara jiyo wayarta ta na ringing hannu ta kai ta dauki wayar da alamun ta manta abun da Princess ta ce mata , kawai ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na sallama kassa kassa a daya bangaran , cikin nitsuwa ya amsa mata sallamarta kafin ya Ι—aura da cewa " me ki ke jira ba ki yi barci ba ? " wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta mike zaune ta jingina bayanta da forehead din gadon ta ce mishi " ni ma ban sani ba , na kassa yin barci ne " " fadi gaskiya , tunani na ki ke yi ko ? " murmushi mai dan sauti ta yi jin abun da ya ce , kenan ya san abun da ta ke yi , cikin yar shagwaba ta ce mishi " Yes , ina tunanin ka , that's why ma na kassa barci , amma tun da yanzu na ji Muryarka , cikin sauki zan yi kwana " " muryata kaΙ—ai ? shikenan kashe kiran bari na yi miki video call " gyada mishi kai ta yi a hankali kamar ya na gabanta , sannan ta sauko wayar a hankali ta katse kiran sannan ta sauko da ga saman gadon ta fara takawa a hankali ta fito bedroom din a haka har ta karaso cikin parlourn ta zauna ta na jiran kiransa ta na zama ko ta ga video call ya shigo wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta dauki

Chapter 20 of 23