Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kejin matuƙar faɗuwar gaba, haka dai ta daure ganin Mubasshir na ta farin ciki tamkar an mai albishir da gidan aljannah. 11:00pm Bayan an gama sauka gaba ɗaya aka taro a ƙayattaccen gurin da aka tanadar a wani bangare na gidan, an ƙawata gurin tamkar rana sabida hasken fitillun da ya haske ko ina, wanda ko alluran ka ce ta faɗi a gurin zaka iya gani, mutane cike a gurin ba masaka tsinke, kama daga manyan ƴan kasuwa, manyan malamai, manyan ƴan siyasa, manyan masu kuɗi, sai talakawa kowa da bangaren shi da kuma matsayin shi, duk jin kai irin na momyn Amal da taƙama da take da arziƙi da kyau sai ta raina kanta taji cewar ashe ita ba kowa ba ce, taga wanda suka takasu a dukiya kuma gashi suna harkokin su da talakawa tamkar ƴan uwan juna, sosai jikin ta yayi sanyi. Nan da nan aka fara gabatar da liyafan ta hanyar gabatar da ahalin gidan sannan aka fara magana kamar haka. "Insha Allah yanzu za'a gabatar da Mahaifiyar shaharren ɗan kasuwan nan wanda ya shahara a ƙasar Dubai dama ƙasashen duniya baki ɗaya wanda domin ta ne muka taru a nan domin yi mata addu'oi na musamman da fatan samun lafiya daga lalurar da take ciki," Nan guri ya ɗauki kabbara, sannan kowa ya natsu yana baza ido yaga wannan uwa mai sa'a da ta haifi babban mutum. "Mommah don Allah ki zo muje, kinga kaf jama'ar gurin nan domin ki suka zo kinji, cewan Ayrah yayin da familyn gaba ɗaya suka ɗunga zuwa suna lallaɓa Mommah da kyar ta taso jikin ta a sanyaye ga wani alamun tsoro da ya bayyana a fuskarta wanda wannan ne karo na farko da ta nuna haka tun tsawon shekarun da aka ɗauka ana gudanar mata da wannan taron addu'oin, gaba ɗaya idon jama'a ne ya ca ganin ahalin tafe sun mamaye ta kowa na annasshuwa da farin ciki, saboda rufe tan da sukayi ba a hango fuskar sosai sanye take da wani haɗaɗɗen baƙin abaya wanda ya fito da tsananin kyawunta sannan ba zaka taɓa yardan cewa ba balarabiya ba ce, suna ƙarisowa gurin gaba ɗaya jama'an gurin suka ɗago suna ƙara kabbara. Kusan a tare Didi da kaka suka miƙe, a zabure Didi ya fusge hannun shi daga ruƙon da Daddyn Amal yayi mai kawai sai ganin shi akayi akan gurin da su Mommah suke ya tura kowa yana zuwa gaban Mommah suka ƙure juna da ido take jikin Mommah ya fara rawa, Didi bai jira komai ba ya rungume Mommah ya fara faɗi, "matata ce! matata ce wallahi.! Jikin Daddyn Amal ba in da bai rawa, ganin abun da Didi ya aikata, kaka kuwa tuni itama ta isa gurin tana zuwa ta yanke jiki ta faɗi yayin da Mommah ita ma ta faɗi a gurin Didi kuwa anyi anyi a karɓi Mommah yaƙi sakin ta faɗi kawai yake, "wallahi matata ce ba zan bari ku ƙara rabamu ba.! ************************* NIGERIA KADUNA Zaune take tamkar an tsikareta ta miƙe ta kunna TV da ke ɗakin don ganin abun da duniya ke ciki, remote ta ɗauka ta kai tashar BBC dai dai lokacin da suke hasko wani labari da ya ɗauke mata hankali, in da ake faɗin cewa yaune babban ɗan kasuwar nan na ƙasar dubai yake gabatar da Addu'an da ake ma mahaifiyar shi don samun lafiyan ta sai dai wannan karon abun ya zo da abun al'ajabi mai ɗunbin yawa, nan kawai aka hasko hoton Didi ya rungume Mommah ƙam ƙam yaƙi sakin ta, a zabure Hajiya Saudat ta miƙe tana faɗin Daddy, sai kuma ta fara tunanin ina ta taɓa ganin hoton wannan matar, bata gama tunani ba aka hasko hoton Mubasshir yayana kuka riƙee da wata tsohuwa, gabanta ne yayi wani mummunan faɗuwa lokaci guda taji kan ta na juyawa. ************************* UNGUWAR DOSA Mallam ne yake zaune a fallon shi yana kallon labarai a BBC, miƙewa yayi zunbur yana faɗin, "Usmanu da Hassenat dama kuna raye,! bai gama rufe baki ba aka nuno kaka ƙara zare ido yayi cikin matuƙar kaɗuwa yana ƙara faɗin "Halimatu.! ************************* "Aneeesa zo kiga wani abu da ake nunowa a Tv wallahi wasu ne in da kika san ƴan gidanku sai dai su waɗɗannan larabawa ne a Dubai suke kuma larabci naji sunayi, ƙurama tv ido Aneeesa tayi tanajin wani faɗuwar gaba lokacin da aka nuno Mubasshir da kuma Baffa wanda irin su ɗaya da Daddyn ta sai dai kawai banbancin fata su larabawa ne su kuma hausawa, tsaki tayii ta juya abun ta. Washe gari lahadi ta kama sauran kwana ɗaya a shiga kotu, sosai hankalin Mahaifiyar Barrister Khasheefat ya tashi ganin tana neman rasa ƴar ta tilo, Barrusteer Zainab ce ta shigo ɗakin da sallamar ta ta gaida hajiya tayi mata ya mai jiki, Hajiya ta amsa fuskar ta ɗauke da murmushi, "hajiya gashi gobene komawar su kotu gashi har yanzu bata farfaɗo ba, kuma har yanzu likitocin basu ce komai ba.? Barrister Zainab ta ƙarisa maganar cikin damuwa, "to har yanzu dai basu ce komai ba ƴata amma sun ce ko yaushe zata iya farfaɗowa, mun gode sosai da ɗawainiyar da kike tayi da mu. "Ba komai Hajiya bari in je in ƙara ganin likitan muji ya ake ciki." Ta ƙarisa maganar tana fita daga ɗakin, tana zuwa officee ɗin doctor peter direct ta shiga, washe baki ya fara yi yana faɗin, "Ajiya sannu da zuwa. "Yauwa doctor ya ake ciki ne,? "Ai baka da damuwan komai ko yau na ƙara yimata alluran barci na tsawon kwana biyu over dose ma nayi mata." Ya ƙarisa maganar yana ƙara washe baki. "Yauwa doctor naji daɗi sosai. Kuɗi ta ciro daga jakarta ta miƙa mai tayi mai sallama ta tafi, da sauri Hajiyan Barristee Khasheefat ta juya tana mai matuƙar mamakin Barrister Zainab can tayi murmushi kawai ta girgiza kai. ************************* Monday 27/06/2022 yau ta kama zaman kotu, kotu ta cika tai maƙil can sai ga alkali ya shigo gaba ɗaya kotu aka mike sai bayan da alkali ya zauna kowa ya zauna, nan magatakarda ya miƙe ya fara gabatar da ƙaran da akeyi, bayan ya zauna Alkali ya buƙaci ganin lauyoyin masu ƙara da wacce ake ƙara, tuni Barrister Mansur ya tashi ya gabatar da kan shi a matsayin lauyan wacce take ƙara ya koma ya zauna yana murmushi domin yauma da alama ba lauyan hajiya hindu, alƙali ya ɗago kai ya ce, "ko ina lauyan wacce ake ƙara.? Caraf Barrister Mansur ya ce "ya mai girma mai shari'a bata zo ba ma yau...... bai gama rufe baki ba sukaji an ce, "gani nan ya maigirma mai shari'a nice lauyar wacce ake ƙara.✍️✍️✍️🤪🤪🤣 Sai ku biyoni kuji shin wacce lauyan kodai Barrister Khasheefat ta farfaɗo ne, ko ya za'a ƙare a Dubai kuma to in naga comment ƙila kuga amsar ku da daren nan koda asubahi🤣🤣🤣🤪🤪🤪. Zeey yar mutan zazzau ce🥰🥰🥰 [10/5, 10:29 AM] Zzz Yar Mama: 😭 KISAN RUƊU😭 Wa ya yi kisan? TSARAWA DA RUBUTAWA ZAINAB SALIHU YARIMA (sarauniyar kanawa) Page 28/29 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM NIGERIA KADUNA Gaba ɗaya mutanen da ke cikin kotun ne suka ƙurama dattijuwar matar da take tsaye a gaban kotu da shiga irin na lauyoyi duk da shekarun ta sun ji hakan bai hana kyawunta da kamanin ta da Barrister Khasheefat fitowa ba, gyara zaman glass ɗin idon ta tayi haɗi da gyara tsayuwar ta fuskar ta ɗauke da murmushi ta fara gabatar da kan ta, "sunana Barrister Madina Abdulwahab ni ce lauya mai kare wacce ake ƙara nagode." Komawa tayi ta zauna har a lokacin fuskarta ɗauke da murmushi. Alƙali ne ya fara magana kamar haka, "yau ne kotu zata cigaba da sauraran ƙaran Aneesa Mubasshir mai lafiya bisa kisan mahaifiyarta da take zargin Hajiya Hindu Usman mailafiya tayi, mun ɗaga shari'a bisa wasu dalilai, gashi kuma Allah ya kawo mu lokacin da zamu cigaba da sauraran shari'a saboda haka kotu tana sauraran lauyoyin guda biyu gurin gabatar da shaidun su." Alƙali yana ƙarasa magana ya duƙar da kai yaci gaba da rubuce-rubucen shi, Barriater Mansur ne ya tashi ya ce, "in kotu ta bani dama ina da wasu tanbayoyi da zamma wacce ake ƙara daga nan kuma zan gabatar da wasu daga cikin shaidu na" "Kotu ta baka dama kuma tana sauraranka." "Nagode ya mai girma mai shari'a, takawa ya cigaba da yi zuwa gaban kantar da ake adana masu laifi ya tsaya yana kare ma Hajiya Hindu kallo, wacce in har ba ka san ta ba neba zaka taɓa ganeta ba, "Hjiya ko zamu iya jin sunanki da kuma alaƙar ki da marigayiya Hajiya Saudat.? "Eh ni sunana Hajiya Hindu, ni kuma sirikar marigayiya ce wato mahaifiyar mijin ta," "ok ko zaki iya faɗa mana dalilin da yasa kika kashe marigayi a matsayin ta na sirikarki.? Daburcewa Hajiya Hindu tayi jin tanbayar da yayi mata, "objection my lord ya kamata lauyan wacce take ƙara ya gyara kalaman shi domin har yanzu ba'a tabbatar da cewa Hajiya Hindu ita tayi wannan kisa ba nagode." Cewar Barrister Madina, "ƙorafi ya karɓu, Barrister Mansur ka kiyaye. "Za'a kiyaye my lord, Hajiya to ko me zaki iya cewa game da zargin da ake miki.? "Wallahi bani na kashe ta ba na dai taka sahun Ɓarawo ne, domin kirata tayi da wayar ta da cewar in zo ɗakin ta tana son muyi wata magana, da kamar ba zanje ba saboda bama shiri da ita kwata-kwata amma sai na nufi ɗakin nata a cikin daren shigana kenan na ganta tana fitar da numfashi wuƙa a cake a cikin ta shine cikin ruɗewa na isa gareta nayi ƙoƙarin cire wuƙar shine Aneeesa ta iso ta ganni." "Ok amma ko mai zaki iya cewa game da maganganun da kike faɗa kullum akan ita wannan sirikar taki na cewa kece ajalinta, kuma kin sha faɗar wannan maganar a gaban mutane mabam-bamta,? "wallahi kawai a bakine amma ba zan taɓa iya kashe ko dabba ba da hannuna balle a ce mutum." Hajiya Hindu ta faɗa cike da nadama. "In har maigirma alƙali ya bani izini ina son in gabatar ma da kotu shaiduna wanda Hajiya Hindu ta sha faɗan cewar ita ce ajalin Hajiya Saudat a gabansu." "Kotu ta baka dama, haka dai Barrister Mansur ya cigaba da gabatar da shaidu ɗaya bayan ɗaya har guda biyar, bayan haka ne ya ce, "da waɗan nan kwararan shaidun nawa kotu zata tabbatar da cewa Hajiya Hindu ita tayi kisan nan, domin ko a jikin wuƙar zanen yatsun ta ne da aka gwada, nagode ya mai shari'a," komawa Barrister Mansur yayi ya zauna. "Kotu duk taji bayanan ka, sannan lauyar wacce ake ƙara ko kina da abun cewa.? "Eh ya maigirma mai shari'a, cewar Barrister Madina, "in kotu ta bani dama ina buƙatar ganin Aneesa.? "Kotu ta baki dama. Aneeesa ce ta zo gurin da aka tanada don masu laifi ta tsaya tana bin Hajiya Hindu da kallon tsana, "malama Aneeesa ranar takwas ga watan shida kinyi waya da ƙawar ki mai suna marry akan su kama Hajiya Sa'adat akan kina zarginta da zuwa haƙo gawar Mahaifiyar ki, bayan kunje haƙo gawar baku samu ganin gawar a gurin ba, sannan ranar tara ga watan shida kin tura abokanan ki da espector Ado gurin maigadin gidan ku kin sa an bashi wasu maƙudan kuɗaɗe bayan sunyi wasu maganganun sirri da su, sannan a ranar sha takwas ga watan shida kin yi ma guggon ki ƙaryan zaki dawao kaduna don duba jarabawa alhalin jarabawa ma bai ko kusan fita ba, bayan zuwan ki kin buƙaci kiga Barrister Zainab in da kika ƙara mata kuɗaɗe masu yawa akan aje a cigaba da ma Barrister Khasheeefat Alluran barci saboda kar ta zo kotu, saboda haka ina buƙatar ki ɗauki tanbayoyina ɗaya bayan ɗaya ki amsamun su, meye dalilin ki na aikata duk waɗannan nan abubuwan, sannan alamu ya nuna kina da masaniya game da kisar Mahaifiyar taki, sannan kuma mai kukaje yi maƙabarta haƙo gawa bayan wanda ya mutu ya ruga ya mutu ba zai dawo ba? saboda haka ina jiran amsoshi na." "Objection my lord wasu daga cikin tanbayoyin ko kusa bai shafi wannan shari'ar ba ya kamata Barruster Madina ta kiyaye." "Ƙorafi bai karɓu ba, Barrister kotu na sauraran ki cigaba. Wani zufa ne ya fara karyo ma Aneeesa da Barrister Mansur, daburcewa Aneesa ta farayi tana faɗin, "to ai ni duk ban son akan abun da kike magana ba, domin ni ban san wata Barrister zainab ba da espector Ado, sannan ni kawai na dawo ne daga Taraba don na gaji da zama a can nafi sabawa da nan." "Ya isa malama Aneeesa alamun sun nuna cewa ba zaki bani haɗin kai ba gurin faɗin gaskiya, saboda haka, in kotu ta bani dama zan gabatar mata da sahidu na bisa tanbayoyin da nayi ma Aneeeesa." Aneeeesa na jin haka tayi suuu ta faɗi a gurin alamun ta sume, nan da nan kotu ta hargitse lauyan ta ne ya miƙe yana faɗin, "ya maigirma mai shari'a muna buƙatar alfarma a gurrin kotu akan ta ɗaga shari'ar nan har zuwa wacce take ƙara ta samu lafiya, bisa ciwon ta na zuciya da ya tashi," cike da mamki Hajiya Hindu ke kallon Barrister Mansur da Aneeesa na ƙaryan da suka shirya lokaci guda, murmushi Barrister Madina tayi tana girgiza kai, guduman da Alƙali ya buga ne yasa kowa ya natsu. "Bisa ƴar matsalan da aka samu kotu ta ɗaga wannan shari'a har zuwa ranar ɗaya ga watan bakwai wato ranar jumma'a." Nan alƙali ya buga gudumar shi kowa ya miƙe, aka fara firfita. "Ranki ya daɗe ranki ya daɗe, kin tashi lafiya, wallahi naji mamaki gaba ɗaya sai na daburce ganin ki a gabana ranki ya daɗe, ai da kinyi waya kin ce mun a ƙara ɗaga shari'a sai ita yarinya ta ƙara jin sauki dole zan daga sai kuma ki zo da kanki haka, don Allah ranki ya daɗe a yi haƙuri in kuna gaban mu ai ba zamu iya zartar da hukunci ba." Cewar Alƙali yana karɓan takardu Hajiya haɗi da buɗe mata mota ta shiga ta zauna fuskarta ɗauke da murmushi ta ce, "Alƙali Abubakar karka wani damu wallahi a hakan ma kayi ƙoƙari domin wannan shari'ar tattare ta ke da ruɗani a cikin ta, koma dai ya ne sai mun haɗe a zama na gaba. ************************* DUBAI BIRNIN ABU DHABI Sosai kafin gari ya waye labari ya karaɗa ƙasar cewa anga mahaifin shahararren ɗan kasuwan nan duk da har yanzu ba wani majiya mai ƙarfi da ya tabbatar da hakan. MAJEEED FAMILY Gaba ɗaya zaune suke a fallon kowa yayi jugum-jugum suna jiran farfaɗowar mutane guda uku wanda manyan likitocin da aka gayyato domin su dubasu sun bada tabbacin cewa, sun shiga wani yanayi ne na firgici wanda in har suka farfaɗo zasu tuno da duk wani memoryn su da suka manta a baya, hakan ta sa suke zaune tun daren jiya ba wanda ya runtsa a cikin su sallah kawai ke tadasu, kowa zuciyar shi da abun da ke saƙa mai, yayin da jikin Momyn Amal ya ƙarayin sanyi da fargaban in dai Didi ya kasance ahalin waɗannan mutane ita kam ta kaɗe sabida irin wukaƙancin da tayi mai ta tabbata marai rabo kuwa, in da gefe guda kuwa Amal ko jirgau ta ƙiyi a gurin Didi tana zaune gefen gadon da yake, tari Mommah ta fara yi tana futar da wani irin baƙin abu daga bakin ta gabaɗayansu da gudu suka nufeta. ************************ NIGERIA ZARIA BAYAN DUTSEN MADARKACI. Boka zalumu ne yayi zumbur ya miƙe ya fara soshe-soshe yana faɗin, "tom zasuyi tsiyan! kul ku bari mana a'a to an zo wajen, dubun ta cika fa mai sama'u ya kawo lokacin shi ya gama aramana lokacin.! kwasa yayi a guje ya falli hanya dai dai da fitowar shi kan titi wata mota ta ɓullo gashi cikin dare anyi ruwa aiko motar tayi sama da shi.✍️✍️✍️✍️ rashin nepa ya hana muku typing jiya a cigaba da gashi suburbuɗo comment kuna ganin typing ehe🥱😎🤣😎😎 SHARE FISABILILLAH🙏 Zeeeey yar mutan zazzau ce🥰🥰🥰 [10/5, 10:29 AM] Zzz Yar Mama: 😭 KISAN RUƊU😭 Wa ya yi kisan? TSARAWA DA RUBUTAWA ZAINAB SALIHU YARIMA (sarauniyar kanawa) GODIYA Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kafa alƙalamina domin rubuta wannan labari, ya ubangiji ka haneni rubuta ba dai-dai ba, ka bani ikon rubuta abun da al'umma zasu anfana da shi. SADAUKARWA Littafin nan tun daga farkon shi har ƙarshen shi sadaukarwa ce wa kaina ni Zainab, kuma littafin free ne, sai dai duk wanda ya karanta ina buƙatar ya sani a addu'a Allah ya biyamun buƙatuna na alheri, ya yayemun damuwa ta. GARGADI Wannan labarin ƙirƙirarren labarine, ban yarda wani ko wata su juyamun labarina ko su ɗoramun a wata manhaja ba tare da izinina ba ko su siyar mu da labarina ba saboda haƙƙinane basirata ce saboda haka don Allah a kiyaye. FATAN ALHERI ZUWA GAREKA Yaya na mai ƙaramun ƙwarin gwiwa koda yaushe HUSSAINI M YERO(GARKUWAN UBAN GARIN ZAZZAU). Page 30/31 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM ************************* DUBAI ABU DHABI Tare ta ke ba kakkautawa, Hajja ce ta kalli Papi ta ce mai, "ya kamata ayi ma sheikh Sudaes waya tun da ya ce in ta farfaɗo a kira shi, domin yana ganin alamun sihiri a tattare da ita." "Kuma hakane kinga duk na ruɗe bari in kirashi, Asalamu Alaikum sheikh eh ta farfaɗo tom sai ka zo." Bayan kamar minti goma sai ga shaikh Sudaes nan ya iso, har yanzu kuma Mommah tana kakarin amai, sheikh sudaes ya ce a nemo mishi bagaruwa guda sha ɗaya ko ashirin da ɗaya, ko arba'in da ɗaya duk wanda dai aka samu yana buƙatar shi yanzu in an samo yana so ayi garin shi sannan a samo mai ruwan zam-zam, nan da nan kuwa akaje aka nemo aka daka bayan an gama aka kawo mai ruwan zam-zam ɗin ya ɗibi garin bagaruwan ya zuba a cikin zam zam ɗin ya fara karanto addu'oi kamar haka *AYATUL KURSIYYU ƘAFA (110)ƊARI DA GOMA, LI'ILAFI ƘAFA (41) ARBA'IN DA ƊAYA, FALAƘI KAFA (41)ARBA'IN DA ƊAYA, NASI KAFA ARBA'IN DA ƊAYA,* ƴar uwa wannan addu'a ce mai matuƙar muhimmanci ga masu fama da sihiri ko shafan aljanu insha Allah in kika lazamci yin wannan kina sha har na tsawon kwana bakwai zakiga waraka da yardan Allah, Allah ka rabamu da sharrin mutum da na aljan domin yanzu duniya ta zama abun da ta zama, kai baka damu da kowa ba amma wani yana nan yana baƙin ciki da rayuwarka. Bayan Sheikh Sudaes ya kammala yin addu'an ya miƙama Hajja ya ce ta bata ta sha sauran a ajiye har tsawon kwana bakwai tana sha insha Allah duk wani sihiri da yake jikin ta zai karye, duk da ma ya lura sihirin ya riga ya karye, domin ko yawan saukan Alqur'ani mai girman da ake yin mata shima wani fa'ida ne kuma waraka ce babba da ya taimaka gurin kawo ƙarshen sihirin dake tare da ita, sallama yayi musu ya tafi Ayrah ce ta ƙarɓi ruwan addu'an taje ta ba Mommah ta sha tana gama sha ta cigaba da yin wani baƙin amai tamkar zata amayar da komai na cikin ta gwanin ban tausayi, kamar haɗin baki sai ga Kaka da Didi sun farfaɗo, da sauri kaka ta miƙe tana faɗin ina Hasseenat kar dai a ce mafarkin da nake yawan yi ne ba ita na gani ba, da sauri Mubasshir ya ƙarasa kusa da kaka ya riƙota yana faɗin, "kaka ki kwantar da hankalinki ba mafarki kikeyi ba kin ganta can." Ya ƙarisa maganar yana jawo hannun kaka zuwa gurin da Mommah take bayan ta gama Amai ɗin ta kwanta sai barci mai nauyi ya ɗauketa, sosai kaka ta tsaya ta tsurama mommah ido cike da tausayin ƴar uwar tata nan ta faɗa tunanin shekaru masu yawa da suka shuɗe, ɓarayin Didi shi kuma yana zaune yana ta bin kowa da ke gurin da kallo, tsayawa yayi yana kallon Mubasshir tamkar ɗan shi Mubasshir da yake ƙarami, ko yanzu ina suke a wani hali suke ciki ƙilama yanzu ya manta da shi, sai kuma da sauri ya kai duban shi gurin Baffa ƙureshi da ido yayi, haka ɓarayin Baffa shima gaba ɗaya ya kasa sukuni in ban da kallon Didi ba abun da yakeyi sosai yaji yana matuƙar son mutumin so mai tsanani ga wani tsantsan kama da sukeyi sai dai kawai ya nuna ma Didi hasken fata, ita ko Amal tana nan maƙale a gefen Didi ta riƙe mai hannu gam tamkar wani zai rabasu, "Didi ka tashi mu tafi gidan mu ni ban son waɗannan mutanen tun da suka saka kuka," Amal ta ƙarisa maganar tana girgiza hannun Didin, waigowa yayi yana kallon yarinyar tunani ya fara a zuciyar shi yana faɗin to ita wannan yarinyar kuma wacece da ta ki jirgiwa kusa da ni, rau rau Amal tayi zatayi kuka, da sauri Anwar da tun ɗazu hankalin shi ya ɗauke gurin kallon yarinyar domin shi dai yarinyar ta burgeshi gata baƙa amma irin baƙin kyau ɗin nan shi kuma a rayuwar shi yana son bakin mutum ya ta so ya zo gurin su Didi ya zauna ya ce ma Amal, "ki zo ki bar Kaka ya huta bai jin daɗi ne, magana ya mata da yaran france don ya ga kamar shi takeyi Allah yasa ya ɗan iya yaren don an koya musu a makaranta, kallon shi tayi sai ta murguɗa mai baki, dariya yayi sai yaga ta ƙara mai kyau. haka dai har lokacin sallah magrib tayi gaba ɗaya mazan suka tashi suka nufi massalaci in da matan suka gabatar da na su a gida, har a lokacin Mommah barci takeyi ba wanda ya tashe ta saboda an kira Sheikh Sudaes ya ce kar a tada ta bayan komai ya lafa aka bar zance akan cewa zuwa da safe za'ayi zama kowa ya warware abun da ke game da shi da dangantakar su. ************************* NIGERIA KADUNA Sosai hankali Aneeesa ya tashi, ta dubi Barrister Mansur ta ce mai, "wai ita wannnan matar ɗin wacece ita da naga har alƙali da aka tashi girmamata yakeyi? Ta ƙarisa maganar tana kallon Barrister Mansur da Barrister zainab da Espector Idi da sukayi tsuru tsuru ba abun da ake hangowa a idanuwan su sai tsaɓan tsoro da firgici, da kyar Barrister zainab ta iya buɗe baki ta ce ma Aneeesa, "tabbass mun yi tuya mun mance da Albasa domin ina tabbatar miki da cewa Hajiya a tarihin ta bata taɓa shari'a an kada ita ba tun lokacin da da take lauya har ta zo ta zama alƙaliya, saboda tsaban gaskiyar ta da ruƙon amanarta da jajircewa domin ita ko cin hanci bata karɓa hakan yasa aka bata shugaban Alƙalai na ƙasa baki daya, a gurin ta ai Barrister Khasheeefat ta koyi wannan jajircewar da kafiyan da bin ƙoƙƙofi, gashi yanzu munyi ƙoƙari mun kaita ƙasa gashi kuma muna neman ɓallo ma kanmu ruwa domin gwabzawa da Hajiaya tamkar faɗa da aljani ne kun ga kenan faɗa da aljani ba daɗi baza kuma ka tsinci komai ba sai wahala, ni gaskiya yanzu ku cireni daga tafiyar nan ba hannuna." Barrrister Zainab tana gama maganarta ta ɗauki jakarta ta fice, gaba ɗaya jikin su yayi sanyi Barrister Mansur ne ya kalli Aneeesa ya ce, "Aneeesa ya kamata ki haƙura da wannan ɗaukan fansa ko iya haka kika tsaya kin san Hajiya Hindu taji jiki ni da ke da kowa ma da ke gurin nan yasan ba Hajiya ta kashe miki mahaifiya ba asali ma mahaifiyar ta ki ba ta mutu ba, abun

Chapter 8 of 11