Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su, ɗaure fuska Mubasshir yayi tamkar ba shi ke zuba murmushi da kallon love ba, "lafiya zaka zo kana mana wani gyaran murya." Dariya fahat yayi cike da zolaya ya ce, "naga wasu furannine yanzun nan kuma sun da ce da juna." Ya ƙarasa maganar yana cigaba da dariyar shakiyanci, ita ko Ayrah tashi tayi ta gudu sit ɗin ta bayan ta ajiye mai chocolate ɗin saboda wani kunya da ta ji ya rufe ta, hannu Fahat ya kai zai ɗauki chocolate ɗin da Ayrah ta ajiye Mubasshir yayi zunbur ya fisge daga hannun shi yana bin shi da harara. "Oh oh lover's don't kill me." Fahat ya kama waƙe waƙen shi yana zagayawa ya zauna, ta shi Mubasshir yayi zai bar gurin Fahat ya ruƙoshi yana faɗin, "haba abokina ina zaka kuma, ka zauna muyi karatun nan da na ce zaka koyamun. Kaka ce ta ke zaune taga ana shigo da kayayyakin abincin da sauran abubuwan buƙata na yau da kullum sai da suka gaba suka miƙa ma kaka wasu kuɗi suka ce mata daga Alhaji K Majeeed ne ya ce ana gaidaki, sosai kaka keta godiya tana sa albarka ita sosai taji soyayyyan mutumin nan yana shiga ran ta jin shi take tamkar ɗan da ta haifa duk da bata taɓa haihuwa, ga kuma uwa uba kamar da suke da ɗan lelen ta Mubasshirr. Bayan wani lokaci Mubasshir ne ya shigo gidan bakin shi ɗauke da Sallama, da sauri kaka ta taso ta rungume jikar na ta ta sumbace shi sannan ta ja shi zuwa ɗakin shi ta fara taimaka mai yana cire kaya tana jan shi da hira banɗaki ta shiga ta haɗa mai ruwan wanka ta ce mai yayi wanka ga abinci nan ta shirya mai kalar wanda ya fi so, murmushi yayi yana wani shagwaɓe fuska yana faɗin, "ayyah kaka ni fa banjin yin wankar nan, kawai muje ki bani abinci na ci." "Au yau ƙazantar ne ta ta shi, wuce muje kayi wanka ko yanzun nan in zo in yi ma." Da gudu ya shige bandakin yana kunkunai domin in da abun da Mubasshir yafi tsana tun yana yaro a ce za'a mai wanka, gashi bai son wankar sai kaka tayi da gaske yakeyi, falo kaka ta koma ta zauna tana kallon labarai ana hasko irin ɓarnar da ƴan ta'adda sukeyi a Nigeria, ta ce oh mu ko yaushe ƙasarmu zata zauna lafiya oho, tana rufe baki sai ga Mubasshir ya fito ya ƙariso falon kallon shi kaka tayi ta ce, "anya ka fita kuwa Mubasshiru.? Turo baki gaba yayi ya ce, "kai Kaka ni don Allah ki daina ɓatamun suna mana. "Anƙi ɗin haka naga damar cewa muje kan teburin cin abincin kayi ka ci ka wuce wurin aikin na ku, yauwa in faɗa maka ma ɗazu ubangidan naka ya zo ya kawo muna kayayyakin Abinci har da kuɗi, kai wannan mutumi dai Allah ya biyamai buƙatar shi duniya da lahira da ana samun irinsu a duniya masu taimako ai da an more." Shiru Mubasshir yayi sai murmushi da yake ta sakewa suka nufi gurin cin abinci har suka zauna kaka bashi labari takeyi amma yaƙi yayi magana, dungure mai kai kaka tayi ta fara balbalin faɗa tana cewa, "nifa wulaƙancin miskilancin nan naka ne ban so, miskili kafi mahaukaci ban haushi, ayi ta magana kanajin mutum, wannan matar ka ta shiga tara ba ma uku ba." 'Kai! kaka don Allah ki shiru haka ki bani abinci in ci yunwa nake ji.! Ya ƙarasa maganar yana sauke numfashi irin da kyar yakai maganar, hararan shi tayi ta ɗibi abincin ta fara ba shi amma duk da haka bai hanata cigaba da mitan ba, shiko cin abincin shi yakeyi hankali kwance sai zuba murmushi yake yi, sai da ya ƙoshi sannan ya fara ɗiba yana ba kaka itama. Ayrah ce zaune tana buga game a system ɗin Anwar ta daddage, in da shi kuma Anwar yana can yana ta fama neman system ɗin shi bayan ya tashi daga barci zaiyi Assignment ɗin da aka basu a makaranta, can ya zabura yayo sashin su Hajjjah da gudu yana kwalama Ayrah kira, ita ko ina ko jin shi batayi ba gabaɗaya ta lula cikin duniyar game, bata ankara ba sai jin saukan dundu tayi a bayan ta, wani ihu da ta saka sai da ƴan gidan gabaɗaya suka hallara a falon yayin da tuni Anwar ya sungume system ɗin shi ya gudu ɗakin shi ya sa key don ya san yau ya kira ruwa, "wayyo Allah ya ɓallamun kwakkwalwar baya na shikenan bayan ya ɓurme.! Riƙeta Ummi keyi amma haka take ƙara mimmikewa tana faɗin an ɓallamata baya, da kyar aka samu ta natsu amma fa taki daina kukan. Zuwan Mubasshir babbab plaza ɗin su kenan ya nufi ɗaya daga cikin shagunan da yake zama, gaida ogan yayi ya fara gyare gyaren abun da ya kamata ya gyara ya koma ya zauna fannin gurin biyan kuɗi, zaman shi ba daɗewa sai ga Aminullah ya shigo shagon kasancewar yau yana zagaye shagunan cikin plazan na su, gabaɗaya miƙewa sukayi, tun da ya shigo gabaɗaya idon shi yana kan Mubasshirr yana matuƙar mamakin irin tsananin kaman da sukeyi haka ƴan shagon suma cike da mamaki suke kallon su don su basu taɓa lura da kamannin su ba sai yau da suke guri ɗaya a tare, gurin shi Aminullah ya nufa ya ce mai, "ya sunan ka.? Cike da miskilanci shima Mubasshir ya bashi amsa yana faɗin, "Mubasshir Mubasshir mailafiya." "Amma kai ba ɗan ƙasar nan bane ko? meye ma'anar mailafiya? "Ban sani ba ko niɗin ba ɗan nan ƙasar ba ne ko ɗan nan ne nidai kawai na tashi na gannin a nan ƙasar, ban san kuma ma'anar mailafiya ba nidai haka kaka ta ta ce sunana." "Ok nice, zauna muyi lisaafi ko ba kaine Cashire ba." "Eh nine tom." Gabaɗaya ƴan shagon suna ta jin mamakin yadda akayi Aminullah da Mubasahir yau sukayi wannan dogon maganar kasancewar duka miskilaye ne. ************************* NIGERIA KADUNA Yau ta kama ranar alhamis kwana uku da ɗaga shari'ar da akeyi. Nisawa Momy tayi bayan ta gama kallon duk abun da ya faru a kotu, akan shari'ar da akeyi na cewa ta mutu, alhalin ita gata a raye. "Amma baiwar Allah maiye ribar ki na tsareni a nan alhalin ga halin da mahaifiyar mijina ta ke ciki shin ke baki da imanine,? ki barni in fita in je in warware wannan zargin *kisan ruɗun* da akeyi domin wannan al'amari ne mai matuƙar firgitarwa." "Hajiya kiyi haƙuri zaki fita daga nan amma sai ranar da aka yanke ma Hajiya Hindu hukuncin kisa, domin ita ɗin azzaluma ce bata cancanci tausayi ba, domin ba ɗigon tausayi ko kaɗan a zuciyar ta, tabbass ta wannan hanyar ne kawai zan iya ɗaukar fansar ran mahaifiyata da tayi sanadiya.! Matashiyar budurwar ta ƙarisa maganar tana mai fashewa da kuka da sauri ta fice daga ɗakin, ta bar Hajiya Saudat cikin tsananin ruɗani da rashin fahimtar in da maganar wannan yarinyar ta dosa. "Ku sake ta amma ina so ku tabbatar kun samun ido a duk wani motsin ta.! Cewar Aneesa tana mai da glass ɗin idon ta da ya rufe mata kusan rabin fuska, jakar ta ta ɗauka ta rataya ta ce musu, "guys mu haɗu a kotu gobe, duk abun da ake ciki muyi chat kawai, kunsan yanzu dole sai da iya ta ku saboda dangin Momy suna gari, ga Daddah ma zata zo gobe, yau batun maigadi da driver na ce ku ƙara musu kuɗi saboda kun san ɗan adam gobe kuma za'a koma kotu, koda naji an ce har yanzu waccen lauyan bata farfaɗo ba, ga dukkan alamu ba mu kaɗai muke son ganin bayan Hajiya Hindu ba, any where dai koma su waye sun taimake mu ai." Tana ƙarisa maganar ta ta fice ta tafi. Yau kwana uku kenan har yanzu Khasheefat bata farfaɗo ba, gashi gobe za'a shiga kotu, sosai hankalin Hajiya Hindu ya tashi, saboda p.a ɗin Barrister yazo ya faɗa mata halin da ake ciki.✍️✍️✍️✍️ SHARE FISABILILLAH🙏🙏 FANS KUYI HAƘURI DA NI FA CIWON BARCI NA DA CIWON RASHIN SON YIN TYPING ƊINA YA DAWO SABODA HAKA KUYI TA ADDU'A CIWON NAN YA BARNI IN TA SYBURBUƊO MUKU TYPING🤣🤣🤣🤣GASHI SAI DA LABARI YA ƊAUKO CHAKWAKIYA GASKIYA NA TAUSAYAMUKU IN CIWON NAN YAƘI ZAN MAIDA LITTAFIN NAN NA KUƊI TABBASS KILA INNA JI KUƊI NA SUBURBUƊOWA TA ACCOUNT ƊINA INJI ƘARFIN YIN TYPING ƊIN LOXXX🤣🤣🤣🤪🤪 Zeey yar mutan zaxxau ce🥰🥰🥰 [10/5, 10:28 AM] Zzz Yar Mama: 😭 KISAN RUƊU😭 Wa ya yi kisan? TSARAWA DA RUBUTAWA ZAINAB SALIHU YARIMA (sarauniyar kanawa) TABBASS BANJI DAƊIN RASHIN COMMENT ƊIN KU *KISAN RUƊU FANS GROUP DA KISAN RUƊU COMMENT GROUP* INA SO IN FAƊA MUKU TABBASS WALLAHI IN BAKU GYARA BA ZAN MAIDA LITTAFIN NAN NA KUƊI DUK MAI SON JIN ƘARSHEN LABARI SAI TA SIYA, SHEKARANJIYA KUNYI MATUƘAR ƁATAMMUN RAI HAR NAJI KAMAR IN AJIYE RUBUTA LABARIN IN RUBUTA LABARINA NA KUƊI DA NAKE SON IN YI INNA GAMA WANNAN AMMA NA MUKU UZURI DAGA WANNAN PAGE ƊIN IN BAKU GYARA BA TABBAS ZAN ƊAU MATAKI AH TO, YA ZA'AYI IN GANE CEWAR KUNA FAHIMTAR SAƘON DA NAKE SON ISARWA BATARE DA KUNA YIN COMMENT BA, TO GASKIYA DAI KU GYARA. Page 24/25 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM DUBAI Yau ta kama Asabar ba makaranta, kaka ce ta fito daga ɗakin ta tana hamma ta nufi kichen ta fara haɗa musu abun karyawa domin taga lokaci ya kusa ƙurewa gashi karfe tara Mubasshir zai fita shago, fita tayi ta nufi ɗakin shi kwance ta ganshi yayi ɗai-ɗai yana barci hankalin shi kwance murmushi tayi ta girgiza kai, banɗakin da ke manne a jikin ɗakin ta shiga ta haɗa mai ruwan wanka ta fito ta sameshi kamar yadda ta barshi, shafa fuskar shi ta farayi tana kiran sunan shi a hankali, danshin ruwan da ke hannun ta yasa shi farkawa da sauri yana taɓe fuska cike da shagwaɓa ya ce, "kaka don Allah barci ki barni.! yana gama maganar ya ƙara juya kwanciya, "kaga wallahi zaka makarafa yau, kalli agogo ƙarfe takwas da rabi." Ai da gudu ya duro ya shige banɗaki ya rufo, girgiza kai kaka tayi tana murmushi Allah ya shiryan mun kai ta ce ta tashi ta fita. ALHAJI MAJEEED FAMILY Ayrah ce kwance tana juyi a kan makeken gadon ta gab da zata zo ƙarshen gado ƙiris ya rage ta faɗo Ummi ta shigo ɗaki a karo na huɗu kenan tana tashin ta tana komawa, da gudu Ummi ta ƙariso cikin ɗakin gani Ayrah ta juyo sai ji kakeyi kummm ta bugu da ties, wani ƙara ta saka ta mike zunbur tana juye-juye duk da haka idon ta akwai barci, riƙeta Ummi tayi ta ce mata, "ki natsu, ba ke mugun barci ba a ce duk girman gadon nan sai kin faɗo, kinga ai yanzu kin tashi ko ba don Allah ba karo na huɗu kenan ina zuwa ina tashin ki kinƙi tashi, wuce muje kiyi wanka da brush muna jiran ki a sashin su Hajjah kin dai san yau Jumma'a ake shirya liyafar girmamawa da addu'oin wa Mommah, sannan da kai ziyara gidajen Marayu, kuma dai kin san yau gidan cika yake da baki har da abokanan kasuwancin mahaifinku daga wasu ƙasashen zuwa sukeyi." Turo baki Ayrah tayi cike da shagwaɓa ta ce, "Ummi ni yau ba zanje ba kawai ku tafi abunku ku barni in yi barcina." Ta ƙarasa maganar tana shigewa banɗakin. Kowa ya hallara a teburin cin abinci, Ayrah kawai ake jira, tuni Anwar ya cika yayi fam kasancewar shi acici ga wani ƙugi da cikin shi yakeyi na kiran yunwa, shiko Aminullah sai danne-dannen wayar shi yakeyi, can sai ga Ayrah nan ta dosa gurin idon ta ba kan wanda ya faɗa irin Anwar da ya cika yayi fam tana dosowa ya fara aika mata da sakon harara tuni ta fara ƙunshe dariayar ta, tana ƙarisowa gab da shi tayi mai gwalo ta wuce nan ya ƙara ƙuluwa bai san lokacin da ya sa mata ƙafa tayi baya zata faɗi da sauri Papi ya taro ta shida Baffa, wani harara Mommah ta aika ma da Anwar da shi, faɗa Papi ya fara "wai kai Anwar ban san ran da zaka girma ba yanzu da ta faɗi taji ciwo fa kace mene eye!" Papi ya faɗa cikin ɓacin rai yayin da Ayrah ta ƙara narkewa a jikin Mommah tana shesshekan kuka, bubbuga bayan ta Papi ya fara yi yana faɗin "sorry amarya ta rabu da shi kinji. "Uhmm abun naku ƴar san kai ne da danne laifi ƙiri ƙiri kuna kallo ita ta fara taƙalan shi amma ku wani rufe mun miji da faɗa kaji maigidana yi haƙuri." Hajjah ta ƙarasa maganarta tana hararan Ayrah, daga nan akayi Bissmillah aka fara cin abinci. Bayan an kammala cin Abincin ne kowa ya tashi ya nufi aikin da zaiyi domin iyalan wannan gida suna girmama ranar da suka ware don yi ma Mommah addu'oin da sauran su sosai kowa yayi busy daga ma'aikatan gidan har ƴan gidan ban da Ayrah da ana gama cin abinci ta gudu sashin su taje ta cigaba da barcin ta. ************************* "Kaka na mance fa Manager companyn mu wanda nake baki labarin muna kama ya gayyaceni liyafar addu'a da cin Abinci da ake gabatar ma da kakan su duk ranar jumma'ar ƙarshen wata, kuma tare nake so muje da ke kinji kaka don Allah karkice ba zakije ba." Ya ƙarisa maganar yana marairaice fuska tamkar zaiyi kuka, shafa kan shi kaka tayi ta ce mai "karka damu ɗanlelen kaka tare zamuje insha Allah. ************************* CAMEROON GABON Daddyn Amal ne ke ta lallaɓa Amal cewan zasu tafi Dubai an gayyace shi liyafar addu'a a gidan maigidan shi na Dubai kuma tare zai tafi da iyalan shi amma Amal ta kafe in dai ba da Didi za'a ba bazata ba, har dukan ta sai da maman ta tayi amma a banza, haka dai Daddy ya haƙura yaje yayi cuku-cuku da kyar ya samu Visan Didi ya kama zasu bi jirgin ƙarfe huɗu na asuban gobe. ************************* NIGERIA Yau ta kama jumma'a ranar da za'a koma kotu, sai aka samu sanarwan gaggawa daga alƙali cewan ya ƙara ɗaga shari'an zuwa ranar Monday, sosai su Aneeesa basu ji daɗin hakan ba ko kaɗan, yayin da gefe guda kuma har yanzu Barrister Khasheefat bata farfaɗo daga comma ɗin da ta shiga ba.✍️✍️✍️ KUYI MANAGE DA WANNAN KUMA DUK RASHIN COMMMENT ƊIN KU YA JA MUKU🙄🙄 SHARE FISABILILLAH🙏 Zeey yar mutan zazzau ce🥰 [10/5, 10:28 AM] Zzz Yar Mama: 😭 KISAN RUƊU😭 Wa ya yi kisan? TSARAWA DA RUBUTAWA ZAINAB SALIHU YARIMA (sarauniyar kanawa) Page 28/29 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM NIGERIA KADUNA Gaba ɗaya mutanen da ke cikin kotun ne suka ƙurama dattijuwar matar da take tsaye a gaban kotu da shiga irin na lauyoyi duk da shekarun ta sun ji hakan bai hana kyawunta da kamanin ta da Barrister Khasheefat fitowa ba, gyara zaman glass ɗin idon ta tayi haɗi da gyara tsayuwar ta fuskar ta ɗauke da murmushi ta fara gabatar da kan ta, "sunana Barrister Madina Abdulwahab ni ce lauya mai kare wacce ake ƙara nagode." Komawa tayi ta zauna har a lokacin fuskarta ɗauke da murmushi. Alƙali ne ya fara magana kamar haka, "yau ne kotu zata cigaba da sauraran ƙaran Aneesa Mubasshir mai lafiya bisa kisan mahaifiyarta da take zargin Hajiya Hindu Usman mailafiya tayi, mun ɗaga shari'a bisa wasu dalilai, gashi kuma Allah ya kawo mu lokacin da zamu cigaba da sauraran shari'a saboda haka kotu tana sauraran lauyoyin guda biyu gurin gabatar da shaidun su." Alƙali yana ƙarasa magana ya duƙar da kai yaci gaba da rubuce-rubucen shi, Barriater Mansur ne ya tashi ya ce, "in kotu ta bani dama ina da wasu tanbayoyi da zamma wacce ake ƙara daga nan kuma zan gabatar da wasu daga cikin shaidu na" "Kotu ta baka dama kuma tana sauraranka." "Nagode ya mai girma mai shari'a, takawa ya cigaba da yi zuwa gaban kantar da ake adana masu laifi ya tsaya yana kare ma Hajiya Hindu kallo, wacce in har ba ka san ta ba neba zaka taɓa ganeta ba, "Hjiya ko zamu iya jin sunanki da kuma alaƙar ki da marigayiya Hajiya Saudat.? "Eh ni sunana Hajiya Hindu, ni kuma sirikar marigayiya ce wato mahaifiyar mijin ta," "ok ko zaki iya faɗa mana dalilin da yasa kika kashe marigayi a matsayin ta na sirikarki.? Daburcewa Hajiya Hindu tayi jin tanbayar da yayi mata, "objection my lord ya kamata lauyan wacce take ƙara ya gyara kalaman shi domin har yanzu ba'a tabbatar da cewa Hajiya Hindu ita tayi wannan kisa ba nagode." Cewar Barrister Madina, "ƙorafi ya karɓu, Barrister Mansur ka kiyaye. "Za'a kiyaye my lord, Hajiya to ko me zaki iya cewa game da zargin da ake miki.? "Wallahi bani na kashe ta ba na dai taka sahun Ɓarawo ne, domin kirata tayi da wayar ta da cewar in zo ɗakin ta tana son muyi wata magana, da kamar ba zanje ba saboda bama shiri da ita kwata-kwata amma sai na nufi ɗakin nata a cikin daren shigana kenan na ganta tana fitar da numfashi wuƙa a cake a cikin ta shine cikin ruɗewa na isa gareta nayi ƙoƙarin cire wuƙar shine Aneeesa ta iso ta ganni." "Ok amma ko mai zaki iya cewa game da maganganun da kike faɗa kullum akan ita wannan sirikar taki na cewa kece ajalinta, kuma kin sha faɗar wannan maganar a gaban mutane mabam-bamta,? "wallahi kawai a bakine amma ba zan taɓa iya kashe ko dabba ba da hannuna balle a ce mutum." Hajiya Hindu ta faɗa cike da nadama. "In har maigirma alƙali ya bani izini ina son in gabatar ma da kotu shaiduna wanda Hajiya Hindu ta sha faɗan cewar ita ce ajalin Hajiya Saudat a gabansu." "Kotu ta baka dama, haka dai Barrister Mansur ya cigaba da gabatar da shaidu ɗaya bayan ɗaya har guda biyar, bayan haka ne ya ce, "da waɗan nan kwararan shaidun nawa kotu zata tabbatar da cewa Hajiya Hindu ita tayi kisan nan, domin ko a jikin wuƙar zanen yatsun ta ne da aka gwada, nagode ya mai shari'a," komawa Barrister Mansur yayi ya zauna. "Kotu duk taji bayanan ka, sannan lauyar wacce ake ƙara ko kina da abun cewa.? "Eh ya maigirma mai shari'a, cewar Barrister Madina, "in kotu ta bani dama ina buƙatar ganin Aneesa.? "Kotu ta baki dama. Aneeesa ce ta zo gurin da aka tanada don masu laifi ta tsaya tana bin Hajiya Hindu da kallon tsana, "malama Aneeesa ranar takwas ga watan shida kinyi waya da ƙawar ki mai suna marry akan su kama Hajiya Sa'adat akan kina zarginta da zuwa haƙo gawar Mahaifiyar ki, bayan kunje haƙo gawar baku samu ganin gawar a gurin ba, sannan ranar tara ga watan shida kin tura abokanan ki da espector Ado gurin maigadin gidan ku kin sa an bashi wasu maƙudan kuɗaɗe bayan sunyi wasu maganganun sirri da su, sannan a ranar sha takwas ga watan shida kin yi ma guggon ki ƙaryan zaki dawao kaduna don duba jarabawa alhalin jarabawa ma bai ko kusan fita ba, bayan zuwan ki kin buƙaci kiga Barrister Zainab in da kika ƙara mata kuɗaɗe masu yawa akan aje a cigaba da ma Barrister Khasheeefat Alluran barci saboda kar ta zo kotu, saboda haka ina buƙatar ki ɗauki tanbayoyina ɗaya bayan ɗaya ki amsamun su, meye dalilin ki na aikata duk waɗannan nan abubuwan, sannan alamu ya nuna kina da masaniya game da kisar Mahaifiyar taki, sannan kuma mai kukaje yi maƙabarta haƙo gawa bayan wanda ya mutu ya ruga ya mutu ba zai dawo ba? saboda haka ina jiran amsoshi na." "Objection my lord wasu daga cikin tanbayoyin ko kusa bai shafi wannan shari'ar ba ya kamata Barruster Madina ta kiyaye." "Ƙorafi bai karɓu ba, Barrister kotu na sauraran ki cigaba. Wani zufa ne ya fara karyo ma Aneeesa da Barrister Mansur, daburcewa Aneesa ta farayi tana faɗin, "to ai ni duk ban son akan abun da kike magana ba, domin ni ban san wata Barrister zainab ba da espector Ado, sannan ni kawai na dawo ne daga Taraba don na gaji da zama a can nafi sabawa da nan." "Ya isa malama Aneeesa alamun sun nuna cewa ba zaki bani haɗin kai ba gurin faɗin gaskiya, saboda haka, in kotu ta bani dama zan gabatar mata da sahidu na bisa tanbayoyin da nayi ma Aneeeesa." Aneeeesa na jin haka tayi suuu ta faɗi a gurin alamun ta sume, nan da nan kotu ta hargitse lauyan ta ne ya miƙe yana faɗin, "ya maigirma mai shari'a muna buƙatar alfarma a gurrin kotu akan ta ɗaga shari'ar nan har zuwa wacce take ƙara ta samu lafiya, bisa ciwon ta na zuciya da ya tashi," cike da mamki Hajiya Hindu ke kallon Barrister Mansur da Aneeesa na ƙaryan da suka shirya lokaci guda, murmushi Barrister Madina tayi tana girgiza kai, guduman da Alƙali ya buga ne yasa kowa ya natsu. "Bisa ƴar matsalan da aka samu kotu ta ɗaga wannan shari'a [10/5, 10:28 AM] Zzz Yar Mama: 😭 KISAN RUƊU😭 Wa ya yi kisan? TSARAWA DA RUBUTAWA ZAINAB SALIHU YARIMA (sarauniyar kanawa) Sister kinyi mana guntun page yen-yen-yen🙄🙄😎😎nayi in na ce muku nayi in kajin mutanen fa to dai dai da ku nake ehe kowa yayi mai kyau zaiga mai kyau ah to in kun gyara halinku nima na gyara nawa posting kullum readmore biyar ehe in baku gyara ba a cigaba da tafiya a gantale eheeee.!🤣🤣😎😎 Page 26/27 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM DUBAI Gaba ɗaya mutanen gidan basu samu sukunin zama ba sai ƙarfe biyu na rana, sannan kowa yaje yayi wanka aka fara shiri dukan su mazan gidan gaba ɗaya kaya iri ɗaya suka sa, kasancewar yanzu wani shaƙuwa ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin Aminullah da Mubasshir hakan yasa ma aka maido Mubasshir office ɗin shi, shiyasa aka tanadar ma Mubasshir kaya iri ɗaya da na ƴan gidan, haka ma Baffa yasa aka ajiye ma kakan Mubasshir irin kayan da su Hajjah zasu sa saboda yace yanzu sun zama ɗaya da su kaka ranar zai gabatar da su kaka a matsayin wasu daga cikin family ɗinsu kasancewar haka yakeji a ran shi game da Kaka. Bangaren su Didi kuwa sun iso Dubai tun ƙarfe goma na safe an saukesu a sashin baƙi na musamman, kasancewar ahalin gidan mutanene masu karamci basa raina na ƙasa da su, komai an tanadar domin bakin na su, Didi ne yake zaune a haraban gidan ta baya shi da Amal tana ta mai hira yana ansawa kasancewar yanzu Didi har magana yakeyi saboda ganin likita da suke yawan yi, amma yawanci kafi jin hiranshi da Amal, duk da har yanzu bai tuna kome game da rayuwar shi na baya, kuma ba zaka taɓa gane mahaukaci bane in har ba kaji hiran shi da Amal ba ne irin shirmen maganar rashin hankalin da yakeyi. Gefe guda kuma ranar gaba ɗaya an rasa gane kan Mommah har wanka ma ranar taƙiyi, balle ta bari a shiryata, da kyar dai aka samu aka shiryata, tuni manyan malamai mahaddata ƙur'ani suka fara gabatar da karatun saukar da akeyi kafun a fara duk wani liyafa bayan an idar da sallah isha. Mubasshir ma da kaka sun iso suma sun sauka a masauki mai kyau da Ayrah ta tanadar musu in da ta basu kayan da aka tanada domin su, sunyi matuƙar farin ciki duk da cewa gaba ɗaya tun da suka iso gidan kaka

Chapter 7 of 11