kar wancan ya ƙariso, da sauri Abdallah yaja motar yana kallon fuskar ƙanwan ta shi da take firgice, kallon ta yake cike da tuhuma, "Ayrah mai kika je kika aikata.?
"Akheee kayi shiru."
Ta ƙarasa maganar tamkar wacce zata fashe da kuka, girgiza kai kawai yayi ya cigaba da tuƙin shi kasancewar shi mai sauƙin ƙai bai cika shiga abun da bai shafeshi ba ko aka nuna ba'a son ya sani.
Cikin huci Mubasshir ya koma yana mai yayyafa ma kaka ruwa wani irin ajiyar zuciya ta saki ta ɗaga ido tana kallon Mubasshir sai taji gaba ɗaya ya bata tausayi kwana biyun nan gaba ɗaya ta kasa kwantar da hankalin ta balle na shi ya kwanta, ta kai ta kawo yanzu har gizo ƴar uwar ta Hasseenat ta ke mata, wanda rabon ta da ita shekara arba'in kenan.
"Kaka mene yarimyar nan ta miki ne, ki faɗamun wallahi sai na hukuntata."
"Mubasshir da gaske dama wata yarinya ta zo gidan nan ba gizo take mun ba."
Zaro ido yayi yana kallon Kakar ta shi cike da mamakin abun da ta faɗa, "dama kaka kin san ta ne.?
"A'a b,a,n san ta ba."
Kaka ta ƙarisa maganar tata a rarraɓe tana zare ido.
Suna shiga haraban gidan Ayrah ta buɗe mota ta fice ko jakar makaranta bata ɗauka ba ta shige direct sai ɗakin Mommah tana zuwa ta faɗa jikin Mommah ta saka ihu, sosai hankalin Mommah ya tashi ta rungumeta tana tanbayarta da ido sai da Ayrah tayi kuka mai isar ta sannan ta dago ta ce ma Mommah, "ki zo mu je kiga wata Mommah irin ku ɗaya sai dai ita baƙar fata ce kin fita haske da ƙiba, zaki je in ce Akheee Abdallah ya kaimu.?
Ɗaga kai Mommah tayi, tsalle Ayrah ta yi ta fita da gudu taje ta dunga roƙon Abdallah ya ce ma ta kin san dai ba in da ake fita da Mommah sai dai Asibiti in su Ummi da Hajjah suka dawo basu gammu ba fa,? "ba abun da zai faru Akheee insha Allah zamu dawo kafun su dawo."
Fitowa sukayi suka tabbatar ba wanda ya gansu suka sa Mommah a mota suka fice daga gidan na su, suna fita su Hajjah na dawowa.
*************************
NIGERIA TARABA
Bayan Barrister ta sauka a hotel ta yi sallolin da ake bin ta ta zauna tana azkar kasancewar dare yayi sosai lokacin tea kawai ta sha ta haye gado tana addu'a sai barci.
Zaune take tana duba wasu takardun can ta kirata wata vedio call ta ce mata, "Mary ya ake ciki ne, nifa gaba ɗaya ina ji a jikina Momy tana nan da rai bata mutu ba, shiyasa gaba ɗaya hankalina ya ƙi kwanciya, amma ina so in zo Kadunan gobe ko jibi ina ta dai shirya plan ɗin yadda zan baro wannan ƙaddararren garin aikin banza an zo a ajiye mutum ana takura mai.!
Ta ƙarasa maganar tana jan zakii, can ta tashi ta gama haɗa kayan ta tass a wani ɗan trooley ta kwanta da shirin gobe da safe sai kaduna saboda ta riga tayi booking jirgin karfe shida na safe.
*************************
KADUNA
"To wai ke Marry garin yaya aka samu akasi haka kin san an ce awa 48 zata dawo cikin hayyacin ta kuma an riga an gama tsara komai akan lokacin na cika zakuje ku tono ta ya akayu kuka bari wasu suka tone ta, ga shi ita matar nan da muke zargin da sa hannun ta har yanzu taki faɗin komai."
"Wallahi oga ni kaina na ji mamaki yadda akayi har wani ya gano plan ɗim mu, amma zamu binciko duk yadda aka haihu a ragaya."
"Amma na ji mamaki wallahi da ka ce mun ba tabi mota ba, kuma ni a motar ta ta ce zata tafi fa, kasan wannan shegiyar matar akwai bala'in wayau amma ka bari zan ƙara dukan ruwan cikin ta mujji in jirgi zata biyo ta dawo sai a san yadda za'ayi, ok nagode yallaɓai.
Hajiya Hindu ne zaune a cell ɗin a raɓe a gefe ga jikin ta duk tabon duka, ga rashin barci gaba ɗaya ta lalace ga dangin ta gaba ɗaya ba mai zuwa in da take balle a kawo mata abinci, gashi an haɗata da tatattun mata irin ƴan duniyan nan, ranar tana ji tana gani su ka banƙareta suka biya buƙatar su da ita bayan haka suka lakaɗa mata duka, haka suke mata duk daren Allah, su biyar ne ita na shida duka sai sun biya buƙatar su da ita sannan su daka, hakan yasa har fargaban dare take ya zo, kullum cikin nadama take saboda abin da bata taɓa aikatawa ba tun da ƙuricciyar ta wai ta nemi mace ƴar uwar ta sai gashi wai tana ji tana gani ƴaƴan cikin ta suna aikata mata hakan tayi magana ta ci duka, ta kai ƙara gurin ƴan sanda ko bi takanta basuyi ba kasancewar tana gani wani a cikin su zai zo ya ɗauki wata a cikin ƴan matan su rage dare wataran ma sai asuba ake maidosu da abincin su mai rai da lafiya, yayin da tana gani suna ci ko loma ba zasu bata ba.✍️✍️
SHARE FISABILILLAH🙏
Zeeey yar mutann zazzzau ce🥰🥰🥰🥰
[10/5, 10:28 AM] Zzz Yar Mama: 😭
KISAN RUƊU😭
Wa ya yi kisan?
TSARAWA DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
*Leeyert Hijabs and Fancy Socks*
*At affordable price*
*Nation Wide Delivery*
*Hurry up and get yours here* 😊😊 *Location: Zaria*
*Email: www.raleeyaty@gmail.com*
*09132110903*
*akwae different design/style like : Egyptian hijabs, 2 cap hijabs,Rubber hijabs,Dubai Hijabs etc*
Page 20/21
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
NIGERIA TARABA
Fitowa Aneesa tayi riƙe da trolley ƙarami a hannun ta tana ja dai dai fitowar Momy Hafsat, tsayawa tayi tana kallon ta fuskar ta ɗauke da mamaki, "My baby ina zaki haka da sassafe riƙe da travelling bag.?
Jikin Aneeesa ne ya fara rawa sai kuma zuciyar ta ta fara gargaɗin ta tana faɗin ki natsu Aneesa karki sa ta zargi wani abu a gareki, marairaice fuska tayi tana faɗin, "Momy ina son zanje kaduna ne ance exam ɗin mu ya fito, sannan kuma ina kewar can don Allah kar ki ce zaki dakatar da ni na roƙeƙi Aunty ta," ta ƙarisa maganar haɗe da yin fuskar tausayi idanuwan ta na cikowa da kwallah, girgiza kai Aunty tayi cike da tausayin yarinyar ƴar uwar tata, domin kullum ƙara tausayin Aneesa takeyi musamman ganin in da kullum take ramewa ta ke lalacewa, ga shi har yau taki sakin jikin ta, "shikenan Aneesa kije Allah ya tsare amma ki tabbatar kina sauka kin kirani."
Da sauri ta rungume Momy Hafsat tana faɗin, "thank you Momy, sai na dawo."
Sosai Momy Hafsat ta ji daɗi ganin yau Aneesa tayi farin ciki tun bayan rasuwar Mahaifiyar ta, da kallo ta bita har ta fice ta bita da sauri ta ce bari driver ya kaita Airpot.
Ta tafi da awa biyu sai ga Barrisster Khasheefat ta iso gidan kasancewar ta samu address ɗin gidan tun daga kaduna, tarba ta musamman Momy Hafsat tayi ma Barrister kasancewar Momy Hafsat akwai kirki sosai, bayan ta kammala ne ta gabatar da kan ta ga Momy Hafsat da kuma abun da ya kawota cewan tana so ta tattauna da Aneesa zata mata wasu tanbayoyi.
"Ayyah Barrister gashi kun sha bam-bam domin yau Aneesa ta tafi kaduna."
"What kaduna kuma amma Hajiya me taje yi kaduna,? "eh to ta ce mun dai wai jarabawar su ya fito sannan tana kewar kaduna tana so ta je ta ɗan ɗebe kewa."
Girgiza kai Barister Khasheeefat tayi ta ce, "tabbass hasashe na yana son zama gaskiya Hajiya, amma don Allah zan iya miki wasu tanbayoyi.?
"Sosai ma kuwa Barrisster mai zai hana ina sauraran ki."
"Yau kimanin sati biyu kenan da rasuwar marigayiya, shin zaki iya faɗamin alaƙar ki da ita,? "marigayiya dai ƴar uwa ta ce uwar mu ɗaya uban mu ɗaya da ita, ita ce autar mu."
"Masha Allah, amma daga lokacin da ƴar uwar ki ta haifi ƴar ta Aneesa har zuwa yau baki taɓa lura cewa ƴar batayi kama da kowa ba kaf cikin zuri'ar ku har zuwa dangin mahaifin ta, sannan a ɗan zaman nan da kukayi da ita baki fuskanci wasu halaye a tattare da yarinyar ba.?
"In ban da abinki Barrisater so nawa akan yi haka, kiga mutum ya haifi ɗa bai yi kama da shi ba, balle wani a cikin dangi, kawai dai mu abin da muka ɗauka daga Allah ne, sannan kuma gaskiya ɗan zama na da Aneesa banga wani abun aibu ba game da ita, yarinya ce dai mai son shiru shiru bata da hayaniya."
"Ok Hajiya ko zan iya ganin ɗakin da take,? "ba damuwa zo muje."
Tashi Barister tayi ta bi Hajiya zuwa ɗakin da Aneesa take zaune, kallon ɗakin Barrister takeyi ko ina da ina can ta nufi drawer da ke ɗakin, ta buɗe wayam suka gani ba komai a cikin drawer zaro ido sukayi a tare Barrister ta waigo tana kallon Momy, ƙarisowa Momy tayi ita ma tana kallon drawer cike da mamaki, "Hajiya dama Aneesa ba zata dawo bane naga ta kwashe kayanta gaba ɗaya, me hakan ke nufi.?
"Ni kaina mamakin da nakeyi kenan, me hakan ke nufi, kuma ni ƙaramin jaka naga ta fita da shi fa amma abun da mamaki.!
"Shikenan Hajiya nagode ni zan koma, ba damuwa."
"Tom Barrisster Allah ya tsare ya kiyaye hanya ya bada sa'a."
Momy ta ƙarisa maganar jikin ta sanyaye ta biyo bayan Barrister suka fito.
*************************
KADUNA
Saukan Aneesa Airport yayi dai dai da isowar Su Marry da jerry, dukan su basufi sa'oin Aneesa ba yarane ƙanana ƙarisowa Aneesa tayi gurinsu fuskarta ɗauke da murmushi, "hi freand," "well come freand."
Cewar Jerry yana miƙa mata hannu suka gaisa, ƙarisawa jikin motar da suka zo da shi sukayi shiga sukayi suka fice daga Airpot ɗin.
*************************
Wata matashiyar budurwace wacce ba zata wuce shekara talatin ba ta turo kofa ta shigo, bakin ta ɗauke da sallama, ɗago kai matar da take zaune a kan sallaya tayi tare da amsa mata sallamar.
"Hajiya sannu da hutawa, ya ƙarfin jikin kuma.?
"da sauki ƴan mata, dama ina so in tanbayeki ne, wai ya akayi na zo nan sannan me ya sameni a gefen cikina kamar yankar wuƙa.?
Murmushi budurwan nan tayi sanan ta gyara zama, "Hajiya labari ne mai tsawo zan faɗa miki amma ba yanzu ba."
"Amma meyasa ba zaki faɗamun yanzu ba, sannan meyasa kullum kuke kulleni a ɗaki kunki barina in tafi ko in san a ina nake, kun ki bani waya in kira kowa nawa, ina so in ji halin da ƴata take ciki, ban kuma san tsawon kwana nawa na ɗauka a hannun ku ba, in kuɗi kuke so ko wani abu ku faɗamun mana."
Murmushi budurwan ta ƙarayi, "hajiya karki damu lokaci kaɗan ya rage, ƴar ki kuma tana cikin ƙoshin lafiya yanzu haka yau ta sauka a kaduna daga Taraba gurin ƴar uwar ki, na barki lafiya."
Da kallo matar ta bi yarinyar kafin ta miƙe ta nannaɗe daddumar ta koma bakin gado ta zauna ta rafka tagumi.
*************************
Zaune suke su biyar Aneesa ta haɗa rai tana ta masifa, kowan su ya yi shiru, shigowar wani mutum ne babban mutum kuma yasa dukan su suka miƙe kallon shi Aneesa tayi ta ce mai, "especter ya ake ciki akwai wani imformation ne.?
"Eh to yanzu haka Barrister Khasheefat ta je Taraba, tun shekaranjiya na so in faɗamiki na dunga kiran wayar ki bai zuwa, to ashe ma kin baro can ɗin, bana so ku haɗu da ita kwata-kwata don ita ɗin akwai basira da kwarewa in har kai ka kasance mara gaskiya in dai kuka haɗu saai ta gano ka, gashi yau saura kwana biyar a shiga kotu."
"Espector kenan kar ka wani ji ka damu ko mu haɗu da ita ko kar mu haɗu duk ɗaya saboda duk wayanta bata isa ta gane waye Aneesa ba domin ni na fi dila wayau ma, yanzu ya batun maigadin gida kunyi waya da shi kuwa, fatan ba damuwa.?
"Eh to munyi waya da shi ya faɗamun Barrister fa ta je gurin shi amma dai bai yarda ya ce komai ba."
"Shikenan yanzu muje in ga matar nan sai mu san wani mataki ya da ce in ɗauka a kan ta.
Duka suka dunguma suka nufi ɗakin da aka kulle matan.
*************************
DUBAI
Papa ne ya ce ma Hajja, "wancan kamar su Mommah yara ita da su Abdallah ina zasu.?
Papa ya faɗa cike da ruɗewa ya juya kan motar ya bisu da gudu ya sha gaban motar na su suka taka wani birki saura kaɗan suyi karo, a firgice suka fito daga motar Ayrah na riƙe da hannun Mommah, Papa ya buɗe ran shi ɓace yana isowa ya tsinke Abdallah da mari ya ɗaga hannu zai ƙara mai Hajja ta riƙe shi, "haba Papa ka tsaya ka tanbayi ina zasu mai ya fito da su mana.
"Yaron nan bai da hankali, yana sane ba lafiya ce da ita ba ina zai ɗauketa ya kaita, in ita da Ayrah basu da hankali shima bai da hankali ne, zaku wuce muje gida kokuwa"
Dafe da kumatu Abdallah yake yana wassafa irin dukan da zai ma Ayrah don ita ta ja mishi, ita ko Ayrah ba in da jikin ta bai rawa ta rungume Mommah sosai, tana jin tsoron kar ta samu nata rabon.
Bayan kwana biyu abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa har da marin da Mubasshir yayi wa Ayrah da warning sosai akan karta ƙara shiga harkan shi, kuma hakan bai sa tayi zuciya da shi ba kullum cikin ƙara burgeta yakeyi.
In da gefe guda kuma komai ya koma dai dai tsakanin kaka da Mubasshir suna zaune cikin walwala kaka ta sauke duk wata damuwa saboda wanzuwar farin cikin Mubasshir in da in ta koma ɗaki gefe guda zata ci kukan ta ta share hawaye.
*************************
CAMEEROON
Daddyn Amal ne ya yi parking motan shi a haraban gidan su in da Amal da Didi suka fito daga motar suka nufi wani ɓarayi na daban a gidan dama kafin su dawo ya riga yayi waya cewa a gyara mai shashin boys queters nan ya kai Didi da kan shi ya taimaka ma Didi yayi wanka ya bashi wasu kaya ya sa ya watsar da yagaggun da ya cire ya kawo abinci ya bashi kin ci yayi sai da Amal ta sa hannu sannan shima ya sa ya fara ci, sosai Daddyn Amal yake jin tausayin Didi ya kuma yi alƙawari zai taimake shi insha Allah da iya ƙarfin shi, bayan ya kammala ya kamo hannun Amal zasu fita da sauri Didi ya taso ya biyosu, da kyar da ya lallaɓa Didi da Amal suka rabu zasu fita kenan sai ga Momyn Amal ta shigo ta dawo daga gurin aiki, ai zabura tayi ta koma bayan daddyn Amal ganin Didi ya na zazzare ido nuna shi ta farayi da hannu tana faɗin, "daddyn Amal mai ya kawo mahaukaci gidan mu ka fara jajibe-jajiben naka ko kai da ƴar ka, wallahi ba zan zauna gida ɗaya da mahaukaci ba ya je ya naƙasani sai dai ku zaɓa ko ni ko shi.
*************************
NIGERIA KADUNA
Yau ta kama monday 20/6/2022 misalin ƙarfe takwas da rabi na safe, yau ne ake gabatar da shari'a akan mutuwar Hajiya Saudat Mubasshir mailafiya a babban kotun da ke cikin garin Kaduna, kotu ta cika makil har waje jama'a ne in bakajin ƙarar komai sai na fankoki da yake aiki, in da mgatakarda ya miƙe ya fara magana kamar haka, "yau ne kotu zata saurari ƙarar Aneesa Mubasshir Mailafiya in da take ƙarar Mahaifiyar Baban ta wato Hajiya Hindu Usman mailafiya akan zargin ta da ta keyi gurin kashe mata mahaifiya nagode."
Magatakarda ya ƙarisa magana yana miƙama Alƙali takardun hannun shi sannan ya duka alaman girmamawa sannan ya zauna, in da alkali ya umarci lauyoyi su tashi su gabatar da kan su, Barrister Mansur ne ya miƙe, "sunana Barrister Mansur iliya nine lauyan wacce take ƙara nagode."
Shiru kotu tayi na ɗan wasu daƙiƙu, Alkali ya ɗago kai ya ce, "ina lauyan wacce ake ƙara.?
"Bata iso ba ya mai girma mai shari'a.
Cewar Barrister Mansur yana wani sake murmushi mai ɗauke da ma'anoni.✍️✍️✍️
yanzu aka fara wasan fa kudai kawai ku cigaba da bin alkalamin ƴar mutan zazzau🥰🥰
Inna ga ruwan comment kuga wani update ɗin da safe, insha Allah yanzu zaku dunga jini kullum komai ya zama normal insha Allah, fata na da ku kawai ku tayani addu'an Allah ya cikamun burina na alkhairi🙏son so fisabilillah.
SHARE FISABILILLAH🙏
Zeeey yar mutan zazxau ce🥰🥰
[10/5, 10:28 AM] Zzz Yar Mama: 😭
KISAN RUƊU😭
Wa ya yi kisan?
TSARAWA DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
*Leeyert Hijabs and Fancy Socks*
*At affordable price*
*Nation Wide Delivery*
*Hurry up and get yours here* 😊😊 *Location: Zaria*
*Email: www.raleeyaty@gmail.com*
*09132110903*
*akwae different design/style like : Egyptian hijabs, 2 cap hijabs,Rubber hijabs,Dubai Hijabs etc*
Page 22/23
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
Sosai take gudu a motar tata tamkar zata tashi sama saboda lura da tayi cewa tamkar wasu na binta duk basajar da tayi na fitowa da motar mahaifiyar ta saboda irin haka amma sai da aka samu matsalan da ta guda canza hanya tayi ta nufi hanyar Murtala squre madadin ta bi Ahmadu Bello way sosai take gudu yankewa ta kuma yi ta bi ta Sultan road tana hawa titin sultan road kasancewar safiya ce ba cunkuson mutane hakan ya sa suka cimmata suka sha gaban ta kaɗan ya rage su bugi juna ta taka birki da sauri futuwa sukayi suka zagaye motar, fitowa ita ma tayi tana binsu da kallo, "lafiya kuke ta bina tun ɗazu.?
"Oh baki ma san meyasa muke binki ba ko? kawo takardun da kike ƙoƙarin zuwa kotu ki gabatar da shi a matsayin shaidu."
Murmushi Barrister Khasheefat tayi cike da rashin tsoro ta ce, "ba zan bada ba ɗin.
Bata gama rufe baki ba ɗayan dake ta bayan ta ya kwaɗa mata ƙarfen da ke hannun shi tuni ta faɗi ta sume a gurin da sauri suka nufi motar tata suka fara bincikewa sai da suka kwashe duk wasu takardu da ke cikin motar suka dawo suka ɗauki wayar ta da ke yashe a ƙasa sannan suka juya suka fita suka haye motar su, suna barin gurin Barrister Zainab ta ƙariso gurin da gudu a ruɗe ta fara girgizata, da sauri ta kinkimeta ta ɗora ta akan mota ta ja ta nufi asibitin da suka fi kusa wato Garden City hospital.
*************************
KOTU
Bayan shafe wasu mintoci da Alkali yayi ba tare da ya tanka ba, sai can ya ɗago ya fara magana cewa, "shin wacce ake ƙara tana da wani uzuri da zata gamsar da kotu game da rashin isowar lauyan ta har tsawon wannan lokaci.?
Alkali ya ƙarisa maganar shi yana kallon Hajiya Hindu da ta koɗe ta ƙanjame tamkar mai ciwon ƙanjamau, dukar da kan ta tayi ta ce "ya maigirma mai shari'a ina rokon wannan kotu mai albarka da ta taimaka a ɗaga shari'an nan har zuwa wani ɗan lokaci domin sanin mai ya hana lauya ta zuwa, duk da nasan cewa akwai kwakkwaran dalili domin ita ɗin jajirtacciyace hakanan ba zata ƙi zuwa ba dalili ba."
"Ba zai taɓa yuwuwa ba takan rashin zuwan lauyan ki da tayi da gangan ba wani dalili a ce a ɗaga mana shari'a hakan ya nuna cewa baku da gaskiya kenan daga ke har lauyan ta ki.!
Barrister Mansur ya faɗa haka cike da kumfar baki, nan da nan kotu ta kaure da hayaniya kowa na faɗin albarkacin bakin shi in da da yawa daga cikin mutane zagin Hajiya Hindu akeyi, ita ko sosai a gurin ta ke ƙara jin wani tarin nadama na ƙara shigarta Nadaman da baida amfani agareta, Alƙali na ya buga gudumar shi alamun ayi shiru nan da nan kotu tayi tsit, Alƙali ya fara magana cewa "wannan kotu mai adalci ta ɗaga wannan shari'ar zuwa nan da 24/6/2022 bisa roƙar alfarma da wacce ake ƙara tayi, sannan kai kuma Barrisster Mansur ka kiyaye harshenka gurin yi ma kotu katsalandan a cikin abun da bai shafeka ba don gaba ka ƙara irin haka kotu zata cika tara haɗa da ɗauri."
Alƙali na gama magana ya buga guduman shi gabaɗaya kowa ya miƙe, nan mutane suka fara firfita bayan alƙali ya fita kowa da abun da yake faɗi, yayin da ƴan sanda suka tasa ƙeyar Hajiya Hindu suka tafi da ita.
*************************
CAMEROON GABON
Farin ciki ne da yalwar arziƙi ya ƙara bunƙasa gurin daddyn Amal tun bayan zuwan Didi gidan na shi, komawar shi Dubai na farko zuwa saro kaya kasancewar yana safarar gwala-gwalai ne daga Dubai zuwa Cameroon in da ubangidan shi kuma shugaban Company Majeeed jewery yake ƙara mai kaya akan wanda ya siya in ya siyar sai ya kawo kuɗin, duk da har yau bai taɓa ido biyu da shugaban Majeed jewery ba duk wani cinikayya sunayin shi ne da Aminullah Babban ɗan mai company wanda kuma shine manaja na company, bayan ɗauko Didi da yayi ne ya koma Dubai don ƙara kawo wasu kayayyakin yana zuwa aka ninka ninki biyu na kayan da ake bashi sannan Company ta bashi kyautar Sarƙan gold na karramawa a matsayin jajjirtaccen customer mai cika alƙawari, haka dadyn Amal ya dawo Cameroon cikin farin ciki, da kuma wani tunani da ya ɗarsu a ran shi domin tun da yayi ido biyu da Aminullah suna tattaunawa ya gama ƙare mai kallo ya tabbatar da cewa da Didi suke kama sai dai shi Didi Baƙi ne sosai saɓanin Aminullah da yake fari balarabe, tun bayan dawon daddyn Amal ya kudurci zai ɗauki Didi yaje ya kaishi ga likitan kwakkwalwa, tun daga ranar suka fara zuwa ganin likita duk ranar jumma'a nan da nan Didi ya murmure yayi ƙiɓa ga wani shaƙuwa mai tsanani da ya shiga tsakanin shi da Amal haka Daddyn Amal ya ɗauki Didi tamkar Mahaifin shi duk in zai fita kasuwa sai ya biya ya duba shi, gefe guda kuma Momyn Amal kullum burin ta ya zatayi Didi ya bar gidan, gane hakan ya sa daddyn Amal nemo wani mutumi yana kula da Didi yana biyan shi, hakan ba ƙarami ƙara ɓatama momyn Amal rai yayi ba.
*************************
DUBAI
Tun Mubasshir bai kula Ayrah har ya zo ya fara kulata saboda na cin ta, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Ayrah ba.
Yau ma kamar kullum zuwa tayi ta zauna a gefen Mubasshir ta ce mai, "Akhee Mubasshir ga chocolate."
Kallon ta yayi cike da miskilanci ya ce mata, "an faɗamiki kowa irin ki ne sha zumami."
Ɓata rai ta yi ta fara bubbuga kafa da kuka da hawaye, kallon ta yayi ya zaro ido saboda in akwai abun da Mubasshir ya tsana yaga ana kuka to duk hankalin shi zai tashi, to tun da Ayrah ta gano haka ita abun sai ya zo mata a dai dai domin in dai arhan hawaye ne da saurin kuka ba na biyun ta, "meye haka ce miki nayi ba zan sha ba, wai ke meyasa ma kuka bai miki wuya ki dunga ɓata ƙyakkyawar fuskar ki, bakya yin kyau fa in kina kuka."
Ya ƙarisa maganar yana ciro hankicif a aljihun shi yana goge mata fuskar kan kallon juna sukeyi ido cikin ido kallo ne mai ciƙe da ma'anoni na wanda suka faɗa cikin soyayya ba tare da sun gane hakan ba, gyaran murya Fahat yayi da sauri suka dawo hayyacin